Kenza eBookz

Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee - Chapter 29

Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee - Chapter 29

Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 29: Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 29. Kafafunta dake rufe cikin doguwar rigar dake…

4,491 words

Kafafunta dake rufe cikin doguwar rigar dake jikinta ash Kala wadda batada adon komai sedai daidai jikinta take ta sauka qasa sosai harma tana dan ja da kasa kadan mayafin rigar ne kadai yakeda adon dayake qawata rigar da fuskar da zata saka kayan ya tsayar da idanuwansa yana kalla amma babu ta inda kafarta ta fito se sautin.

Dagowa yayi a natse ya maida kallansa kan fuskarta zuciyarsa na dauka Wani irin Zafin mamaki da jin abinda bai taba ji ba a bayi sedai yayan sarautar ne kadai sukeda iko da wannan damar dan haka mamakinsa ya dan qaru yana bude idanuwansa da kyau a kanta.

Fuskarta dake bayyane ya zubawa idanuwansa yana kasa daukesu daga kanta mamakinsa na sauka ahankali tamkar wutar da aka zubawa ruwa,

Bin fuskarta yake sakeyi da kallan dayake sake saka zuciyarsa mamaki da jin Wani irin yanayin daya sakasa kasa dauke kallansa akanta.

Shiru gurin ya sake dauka musamman da Bahar din bata sake ko motsawa ba har tsawon mintina kafin ya dauke idanuwansa daga kan kyakkyawar fuskarta ta jinin GHAZ ya juya a natse batareda yace komaiba ya wuce zuciyarsa na riqe kamanninta da kai tsaye suka isa gareta.

Yana barin gurin Maa sakinah ta Kama hannunta suka nufi kofar da take aka bude musu ita gabaki sbd girmamawa suka shige aka rufe.

Babban palon dayake na farkon isa suka shiga Maa sakinah ta sake ajiyan zuciyar samun isowa gida cikin Amintci.

Dakinta kai tsaye ta wuce da Bahar,

Komai na dakin a gyare yake sbd babu ranar da baa Shara so biyu a kunna qamshi, Ac ne kadai baa kunne ba sai wuta dan haka kai tsaye remote ta dauka ta kunna komai Wanda take haske ya haske dakin gabaki daya tamkar fitowan rana,

Makeken bedroom ne dayake dauke da royalbed me kyau da girma sosai sai Sauran set din royalbed din su wardrobe da dresser tareda bedside da wata lallausan Turkish carpet da table sai couch masu Laushi da tsari,

Duk wani jin dadi da tsarin dayake bayyanarda Hutu da kwanciyan hankali shine a dakin komai a tsaf ga sanyin ac din ya fara ratso wa yana kokarin Kama dakin.

Zaunar da ita Maa sakinah tayi tareda zare mata rufar kanta a hankali gashinta dayake rufe ya zubo a hankali yana bayyana Maa ta sake sauke ajiyan zuciya tana kallan baiwar data shigo dakin dauke da babban tray da kayan sanyi da fruits masu sanyi ta bude baki tace

‘Ki hada ruwan wanka masu dumi’ Gyada kai baiwar da ake da Salmah tayi tana ajiye tray din ta juya kanta a qasa ta nufi toilet din dayake dakin na Maa ta shige dan hada ruwan wankan. #MAMUH

HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070

Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali*_HAYATEEM_* Mamuhgee

71 Ruwan wanka me tsafta,qamshi da dumi aka hada mata Maa sakinah ta taimaka mata har bakin toilet din ta shigar da ita ta Baro bathroom din ta kalli Salmah tace ta taimaka mata gurin tubewa da nuna mata komai.

Salmah ce ta shiga har ciki ta taimaka mata sosai a gurin nuna mata komai da sabulun da zatai wanka dashi me qamshi da kyau da tsada tukuna taje ta kawo mata towels har guda biyu masu dan girma kafin ta fice dan zuwa hado mata abincin da Maa tace a hado mata.

Duk da baa irin wannan daular da duniyar ta tashi ba batada duhun kai dan haka a sanyaye tayi wankan ta fito tareda alwala tana daure da towel daya ta rifo jikinta da Wani Dayan gashinta dayake a sake har lokacin duk ya dan jiqe.

Tana qarasowa Maa sakinah ta miqe ta kamota ta zaunar a gaban mirror tana goge mata fatar jikinta da towel din cikin kulawa tareda bude baki a sanyaye da nutsuwa tace

‘BAHAR,Bahar kiyi hakuri ki zama me tawakkali da karban kaddarar ubangiji a dik yanda tazo miki, Mahaifinki bake kadaice kikai rashinsa ba Muma mun rasa Wani bangare ne na jikin mu rashinsa a wannan duniyar, Muna tsananin kaunarsa fiyeda kanmu amma Allah baiyi zamu sake cigaba da rayuwa ba ya rabamu dashi a daidai lokacinda muke saka ran mun sake haduwa, Addua da dangana itace kadai abinda zaki sakawa iyayenki dashi, Karki manta dangana da hakurin da zakiyi shine zai baki kwarin gwiwa da nutsuwar yi musu addua da fatar rahamar ubangiji ako da Yaushe dan haka a yanzu sassautawa zuciyarki kada ki saka quncin dazai hanaki ringa aika musu adduar ki ako yaushe, Anan cikinmu kinsani rayuwar gata da kauna zakiyi sbd muna tsananin so da kaunarki,

Ki saka a ranki cewa ke din hasken rayuwa da idaniyar mu ce koda baki ga hakan daga kowa ba a yanzu zaki gani daga gareni kafin yan uwan mahaifinki susanki susan ke wacece,

Ke Amanata ce da zan bawa kowace irin kauna da kariya da karfina da rayuwata, Ke hasken idaniyata ce da zuciyata Bahar ki Bari na kaunaceki kaman nice na haifeki da cikina idan har kika sassautawa zuciyarki banason ganinki a wannan yanayin.’

Qarasa maganar tayi tana goge mata kyakkyawar fuskarta me daukan ido sbd bata shiga rana Sam a cikin duhun masarautar GHAZ ta tashi ta rayu ta kuma girma da towel tana daukan body oil na Neutrogena tana shafa mata a jikinta cikin kulawa da gata.

Tana gama shafa mata ta Kama gashinta dan busar mata dashi inda yake a jiqe kafin ta Kama mata shi ba sosai ba da band.

Babu Kayan da zata bata tasaka sbd kayansu bazasu mata ba su manya ne ita kuma budurwa ce me qaramin jiki hakama batada ikon bata wasu kayan ta saka idan ba Wanda duk Wanda baida matsayi yake sakawa ba a masarautar dan haka rigarta me tsayi ta bata hakanan ta saka tukuna ta tashi tafara sallah ita kuma ta fada toilet dan wanka da sallah.

Sallolin dake kanta tafara jerowa a hankali harta kammala ta daga hannu zata fara addua kawai Wani irin kuka me tsananin karfin daya ratsa zuciyarta data qame jin Wani irin azababben radadi na ratsata ya kubce mata ta cusa fuskarta a tafin hannuwan tana wata irin jijjiga kukan na tsananta sbd ta tabbata dai ta rasa mahaifinta dashi kadai ne ya rage mata,ta rasa Abaa dinta sai lahira, Ta rasa rayuwarta,ta rasa haskenta,ta rasa hope da kuzarin da shi kadai gareta a dare daya, Abaa ya tafi yabarta a duniyar da batasan komai da kowaba idan bashi ba gashi ta tsinci kanta a inda batajin zata iya rayuwa.

Kuka takeyi sosai mai tsima zuciya da tada tsigar jiki tana jin kirjinta na mata Wani tsananin ciwon da kaman gangar jikinta bazata daukaba.

Maa dake toilet tana jinta tayi shiru jikinta na mutuwa da tsananin tausayinta da jin kaman ta zare kuncin Bahar din ta dawo dashi kanta sbd yarinyar ta samu sassauci da nutsuwan zuciyar da bata taba samuba.

Kasa fitowa Maa tayi ko bayan data gama komai sbd bawa Bahar din damar fidda kukan quncin dayake zuciyarta tin jiyan da mahaifinta ya bar duniya.

Sai Bayan mintina masu tsayi ta fito itama idanuwanta jajir ta zauna ta shirya tana gamawa gefen Bahar din tazo ta tada tata sallar a natse.

Shiru Bahar din take Zaune idanuwanta sunyi jajir sun kumbura hancinta ma yayi jajir sbd kuka ta samu dan sassaucin nauyin daya danne kirjinta ta Lumshe idanuwa tareda kwantar da kanta a hannun couch din dayake gefenta.

Maa ma tana gama sallar aka fara shigowa da abinci aka a gabansu nan qasa kan carpet din dasuke,

Kallan Bahar Maa tayi tana zuba mata abincin Wanda yake lafiyayye da vegetables tareda fruits da madara me Zafi da zuma tace

‘Bahar kici abinci kinji’

Bude idanuwanta tayi ahankali cikin sanyi tareda tasowa daga kwancen da kanta yake sbd Sam rayuwarta bata iya gaddama da hayaniya ba dan haka bazata iya tsayawa cewa aa ba Maa din taci gaba da rokonta ya zamansa anyi hayaniyar hakan dan haka kai tsaye juyowa tayi jiki a mace tareda dago manyan idonta da sukai ja ta kalli Maa sakina a sanyaye.

Jin dadi Maa tayi har cikin zuciyarta na yanda Bahar din batai mata gardama ba dan haka apple tafara yanke mata fatar ta bata kafin ta zuba mata abincin jikinta har rawa yakeyi sbd sauri Wanda ya saka Bahar ta zuba mata ido tana kallanta tausayinta na shigarta dan haka takai apple din bakinta ta fara ci ahankali.

Abincin ma a bakinta Maa sakina a ringa bata har taci bada yawa ba Maa ta dauki madarar me Zafi ta bata Tasha itama kafin itama taci abincin a natse tana gamawa aka fice da kayan.

Sallar ishai da akai ne ya sakasu miqewa suka gabatar da sallar a tare,

Suna gamawa sukai shiru a Zaune babu me cewa komai har tsawon sama da awa daya zuwa lokacin Wani gajiyayyen baccin dole ya dauke Bahar a gurin sbd maganin dayake cikin madarar na saka bacci sbd zuciya da kwakwalwanta su samu hutawa daga qunci idan ta farka zata ji sassaucin komai insh Allah.

Salmah ta kira ta Kama mata ita suka kwantar da ita a lafiyayyan gadon dakin Maa ta rufeta da bargo me tsananin Laushi ta zauna gefen gadon ta tofa mata addua tukuna ta miqe ta fice daga dakin dan waya da tenya data kirata tana sallah.

Palo ta dawo ta zauna a natse ta saka kiran tenya din wadda tariga ta Baro asibiti itama ta dawo masaukinsu.

Waya sukai sosai tsawon lokaci Akan yanayin jikin Ayanaah har suka gama ko kadan Maa sakinah bata fada komai daya danganci Abaas bama bare rasuwarsa bare ma azo kan Bahar wadda zata rayu a hannunsu tamkar matsayin baiwar masarautar sbd kawar da kowace irin zargi da bincike akanta dan haka kafin ma su dawo zata kula da ita da bata kauna tareda tattali.

Suna gama wayar Zaunawa tayi na dan lokaci tana duba abubuwa a wayarta kafin ta tashi ta koma dakin tayi abinda zatai ta kwanta Dayan gefen gadon cikin nutsuwa tana kallan fuskar Bahar dake bacci sosai a cikin sanyi da nutsuwa.

****Washe gari da safe da dan sassaucin data tsammata Bahar ta tashi dan haka taji itama ta sake samun nutsuwa,

Breakfast sukai a tare kaman jiyan a bakinta ta bata kafin ta hada mata ruwan wanka da kanta wannan karanma itace ta taya Bahar din ta wanke matan kanta tas Wanda yayi qura kafin ta fito tabarta tayi wanka ta fito.

Busar mata da gashinta tayi ta sake bata rigarta ta saka wadda tayi mugun yi mata yawan gaske amma tinda babu inda zata fita hakan ba damuwa bane.

Shiru suka wuni tsit babu dogon motsin komai sbd Sam Bahar bata iya maganar komai idanuwanta koyaushe a guri daya suke tsayawa da tinani Wanda hakanne yake saka Maa sakinah damuwa dan haka tafara kokarin ajiye tata damuwan tana Janta a jikinta sosai tareda ringa mata hirar mahaifinta tin yana yaronsa.

Da wannan tafara saka Bahar din ringa bata dukkanin hankalinta sbd koyaushe hirar mahaifinta idan zaa wuni a kwana Ana mata baa gajiya dan haka tafara sabawa ahankali ahankali da hirar Maa sakinah wadda ta dage sosai da nunawa Bahar menene kauna da walwala.

Kullum tana waya da tenya taji yaya jikin Ayanah wadda ayanzu ake maganar sati uku da rasuwar Abaas din amma bata farfado ba.

******lokaci da kwanaki sosai sun tafi Wanda ya saka kauna me sanyi da sabo tareda yar shaquwa shiga tsakanin Bahar da Maa sakinah wadda ta fara kawo wata rayuwar cikin matacciyar rayuwarta datake ganin bazata taba gyaruwa ba.

Maa sakinah ta sakata bude mata zuciyarta datake a kulle ta shige sbd itace mutum ta farko dataji tana yiwa kauna da shaquwa Bayan mahaifinta kaf duniyarta sai kuma Salmah wadda itama take kulawa sosai da ita tana hayata hira da labarai bisa umarnin Maa sbd Bahar din na buqatan sabawa da mutane.

Farin ciki ne ya cike rayuwar Maa ganin Bahar din tafara kokarin fuskantar rayuwa harma tana zuwa kitchen tareda Salmah sbd tayata ayyukan dasuke yi tareda Sauran bayin bangaren na wishmah hakama tana mata magana yanzu sosai.

Ana cikin wannan halin na farin cikin da Maa sakinah ke yi kwatsam kiran tenya ya shigo mata tareda albishir me dadin cewa Ayanah ta farfado hakama tareda cikakkiyar lafiyayyar memory dinta kawai Sauran rashin karfin jiki ne data rasa ya rage mata Wanda shima insha Allah tana qarasa warware wa zasu dawo gabaki dayansu kowane lokaci. #MAMUH

KUYI HAKURI MASOYAN ABAAS DA MASU GANIN KASHE KASHEN YAYI YAWA WANDA BANAJIN KUN FAHIMCENI KO KUN FAHIMCI LABARIN, Amma dai koma yayane ina Bau hakuri tareda miqo taaziyata gareku Allah yaji qansa ya huci zuciyarku kunji Rabin ran Mamuh🙏💋

HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070

Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali_*HAYATEEM*_ Mamuhgee

72 Yau tinda Bahar ta tashi kaman yanda take komai a natse rashin hayaniya sbd rayuwar data Saba da ita ba hayaniya dan hakanne komai nata kamar a sanyaye yake ba hayaniyar,

Aikin gyaran dakin Maa sakinah tafara sbd yanzu aiki takeyi kaman su Salmah bata iya Zaunawa shiru bata komai sbd zama a cikinsu Salmah din yana dan debe mata kewa hakama itama Maa sakinah ganin tana sakewa da fita tinani sosai idan tana zama cikinsu ya saka bata hanata ba tinda daman a cikin nasu zata fake da bata kariya batareda ansan ko ita din wacece ba dan haka sai ta barta tana komai tareda su suma suna kokarin Janta sosai tana sabawa da komai,

Kayan sakawa da batada su da kuma ma koda tanada su Maa tasan tayaya zatai shigar da batasan me zata fada ba Akan hakan dan haka saita barta itama tana saka uniform kamar su Salmah wainda da kanta taje ta karbo mata su Kala biyar sabbi daidai jikinta,

Ita kanta Bahar din tafi jin nutsuwar tsayawa ga matsayin dasu Salmah suke dashi sbd tafi tafi son ta kasance a matsayin da shine ya kamace ya kuma zai barta tayi rayuwa qasa qasa batareda shiga wata daula ko shiga mutanen da bazata iya kallan kanta a cikinsu ba dan haka kaman yanda Wanda ya kawosu ya buqaci rashinta da rashin bayyanar da ita ga wadda itace takeda alaqa sa mahaifinta itama sai taji tafi kowa ma buqatar rayuwarta a cikin bayi kuma a matsayinsu hakama bata jin tana buqatar kowa a rayuwarta tinda ta Riga ta rasa mahaifinta sha shine kowa a rayuwarta hakama kwata kwata sai batajin kowannensu a cikin ranta da zata ma iya jin feelings na alaqa komai a tsakaninsu.

Maa ce kadai take ji a zuciya da rayuwarta harma tana jin ahankali tana samun kauna ta uwa mace da Allah bai taba bata ba musamman da haryanxu data zabi zamowa mai aiki a cikin bayi Maa bata taba Dena tattali da bata kulawan da daace ba a cikin duhu da kunci ta taso ba da babu abinda zai Haba gatan lalatata sbd hatta gashinta Maa ce take wanke mata shi da wasu irin tsaftattun kayan wanke kai da oils na gashi na al’adar qasar masu kyau da qara duhu da tsayin gashi tareda santsinsa Wanda zaku iya samun irinsa sak a gurin (SHUWA INCENSE AND MORE 07042293384/09118783317) wainda suke fiddo mata kyau da tsayin gashinta fiyeda baya sbd rashin gyara, Hakama bangaren lafiyar fatarta ma kayan wanka na musamman na matan Masarautar Maa dinta ta tanadar mata wainda dasu take wanka duk da bawai na musamman bane amma suna kawo sauyi sosai a fatarta da kwata kwata a baya bata Wani samun duka wainnan gyaran tinda ba sune a gaban rayuwarta data mahaifinta ba.

Hakama Maa bata barinta ficewa Ayyuka sai ta tsaya sunyi breakfast tare kafin tayi wanka ta saka uniform dinta ta fice gurinsu Salmah.

Yauma kamar kullum dakin ta gama gyara wa a natse ta kunna ac salma ta koya mata ta kunna qamshin da ake kunnawa me sanyi da nutsuwa kafin ta zare kayan jikinta na bacci wata doguwar rigar Maa dince datai mata yawa sosai da ita yake bacci koyaushe dan haka zarewa tayi ta daura babban towel din da Maa ta tabbatar mata da sune nata kusan Kala biyar.

Bathroom din dakin ta shige ahankali tareda rufo kofar tana isa inda brush dinta yake tafara yin brush din da brush me tsadar da suke jere a toilet din kusan guda biyar tana gamawa ta sake wanke bakinta da harshenta da mint mouthwash me qamshin tukuna ta isa ahankali ta shige ruwan Zafin dake cike da bathtub suna fidda qamshi mara tashi sosai.

Wankan kusan mintina kalilan tayi ta fito ta goge jikinta iya mai kadai ta shafa sai qamshi a jikinta ta miqe ta saka uniform dinta a natse kaman koyaushe,

Salmah ce ta kawo breakfast din data saba ta ajiye a kan table ta dauko shimfidar cin abinci ta shimfida Akan lafiyayyar carpet din tsakiyar dakin tukuna ta saukar da abincin ta jera ta fice.

Abincin sukaci Maa na sake fadawa Bahar ta kula da kanta sosai kada taji rauni a gurin aiki hakama ta ringa cin abinci sosai.

Dago kyawawan idanuwanta tayi ta kalli Maa din cikeda girmamawa da kauna tareda shaquwa ta Gyada kai tana karban cup din madara me Zafin datake kokarin bata a baki ta amsa takai bakinta tafara sha ahankali ta bude Baki tace

‘Maa Nagode,Abaa ma ya gode’

Murmushi Maa din tayi a duk lokacinda Bahar zatai godia sai tace Abaa dinta shima ya gode,

Tissue ta dauka tana gogewa Bahar din baki inda madarar ta bata a gefen bakinta tana cewa

‘Nima na gode wa Abaa daya haifo mun Ayanaah Bahar’

Sakewa fuskar Bahar din tayi tareda sakin Wani sanyayyan murmushi me sanyi tace

‘Hadda Maama Dina amma’

Dariya me sauti Maa sakinah tace sake tana cewa

‘To ai daman da ita nake nufi tinda itace ma ta kawo mana Bahar din duniya’

Wani sanyi Bahar taji ya ratsata a yanzu datake irin wainnan maganganun da Wani a rayuwarta dan haka Wani murmushin ta kuma sakewa tana qarasa shanye madararta zata miqe Maa ta riqe hannunta ta sake goge mata bakinta tana sake cewa

‘Bahar ki kula sosai ki kiyaye masarautar nan akwai tsanani sosai a cikinta da hadari dan haka ki kula sosai kinji’

Gyada kai tayi tareda daukan tissue itama ta gogewa Maa din gefen Fuska tukuna ta miqe ta tattara Kayan ta fice Maa na Binta da ido tana jin inama zaa bata dama ta tafiyarta da Bahar suje inda babu takura su shimfida rayuwar da zata bawa Bahar kauna fiyeda wadda zata bata anan sbd anan din karkashin dokoki da tsanani me karfi suke.

Tana fitowa kai tsaye kitchen din bangaren nasu ta nufa da Kayan tana shigowa dukkaninsu suka gaidata duk da wasu sun girmeta wasu kuma iyakacinsu shekarunta duka duka su shida ne sai ita ta bakwai kuma babu qyashi ko baqin ciki bare fitinar komai a tsakaninsu dukan dan hakan ne suke ciki kwanciyan hankali da hidimar su ba damuwan komai,

Gaidasu tayi itama batareda ta amsa tasu gaisuwan ba sbd batasan tayaya zata amsa ba tinda matsayinsu daya su dukan.

Ajiye Kayan hannunta tayi a cikin sink tana kunna ruwa tafara wankesu a hankali tareda Salmah data matso tana tayata tana bata Wani labarin a hankali fuskarta a sake da dariya ita kuwa tana saurarenta a natse fuskarta ma na dan sakewa da abinda take saurare daga bakin Salmah din.

Suna gama wanke Kayan tas Sauran suka fice zuwa ayyukan gyare gyaren Paluka da Sauran dakunan Wishmah harma dana Tenya dik da basa nan baa taba tsallake gyaran dakuna da toilets dinsu ba,

Su Bahar kuwa su uku aka Bari kitchen din suna Dora girki Wanda a yanzu daga su sai Maa ne ake wa.

Salmah da Naima ne sukeda qwarewa a aikin abincin dan haka Bahar datake koya haryanzu a gurinsu iyakacinta yanka musu abubuwa da niqawa idan ance tayi sbd sun koya mata abubuwa da dama sosai kuma tana iyawa din tunda batada iyawa Akan komai.

Girkin sukeyi Salmah da naima na kokarin bata Labaran masarautar da mutanen dake cikinta wainda Sam wasu abubuwan jinsu kadai takeyi bata Wani gane wa dan ita tafi gane wa koyan abinda yake gabanta.

Simple abinci sukai kusan Kala uku Wanda zaa ci har dare sbd Bayan girkin wanki zasu tafi cak bangaren laundry na masarautar.

Koda suka gama suka kai komai a dining suka jere tareda sake gyara koina qamshi da sanyi tareda tsit kawai ke tashi a bangaren, Kitchen suka sake gyara wa tamkar baa yi aikin komai a cikinsa ba sukaci abinci a dakinsu dake bangaren suka gama hadda ita suka fito suka sake tabbatarda tsaftar koina tukuna suka fiddo kayan wankin dake bangaren tsaf suka fice dasu zuwa laundry su hudu suka bar mutum uku sbd baa tafi tafi duka abar bangaren ba masu hidima ko daya.

Hadda ita Bahar din suka fito wadda yaune Karan farko data fara fitowa daga bangaren dan haka a gefen Salmah take tana kasa sakewa sosai sbd batada sabo haryanzu na mutane sosai Bayan su da shima sai ahankali ta dan iya sabuwa da sakewa a cikinsu dan haka yanzu data fito takejin yanayi na rashin son rabuwa da mutane sosai.

Salmah ce yake tura babban basket me kafafun da suka turo wankin a ciki suna tafiya cikeda nutsuwa da Kamun kai suna yar fira sama sama.

Tafiya me tazara ce daga bangaren zuwa inda laundry yake dan haka tafiya tafiyarsu da ba cikin gaggawa da rawar jiki sukeyinta ba sai batai tsayiba.

Suna isa babban guri ne dayake tsare da gararen wanki da hannu da kuma washing machines da gurin goge kaya dama gurin da zaka shirya su aleda Bayan gogewan da inda ma ake tirara kaya da qamshi kafin gogewa ko Bayan gogewan ma,

Gurin Bahar ta kalla tana sake dan dawo da kallanta kan Salmah dake nuna mata inda suka nufa,

Wankin hannu zasuyi duk babu mutane da yawa sosai sbd kowace bangaren dake masarautar na mata da imebeti da ‘yaya da manyan Masarauta dake cikin masarautar anan ake tahowa Ayi masu wanki da guga.

Fara wankin sukai Wanda Itama Bahar ta saka hannu duk da shima ba wani iyawa tayi sosai ba sbd koda suke a cikin qunci mahaifinta ne me mata wanki daga baya da ciwo ya hanasa kuma cikin Yaransa na fadar ne ke mata sai wasu lokutan takeyi da kanta. #MAMUH

HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070

Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali*_HAYATEEM_* Mamuhgee

73 Sai yamma sosai Ana gap da magrib suka gama komai suka dawo komai an wanke an gode tareda tirara wa da qamshi me dadi hatta bedsheets da Sauran abubuwan an wanke an goge an shiryo a rufe cikin keda me kyau,

Fitowa sukai suka hanyar komawa Bahar dake gefen Salmah tana rungume da hannuwanta ta dan Kama jikinta a natse sbd Wani irin sanyi dayake ratsata na wankin datai me dan wahalar da bata saba da ita ba Sam sbd qunci ne kadai a rayuwarta Banda wahala batasanta ba sam.

Yanda take jin sanyin sosai ya sake sakata dan sake Kama jikinta a natse cikin sanyi batareda ta furta ba kokuma barin a gane sanyin takeji sbd baida kowane amfani tinda sabuwar rayuwar data samu kanta ne a ciki daurewa kawai ne zatai koma menene zai shiga gabanta ta Fuskancesa ta amshesa.

Suna doso hanyar isa bangarensu na wishmah da Sauran matan sultan din bayin dake hanyar suka fara sauke kansu a hankali cikin tsananin girmamawa a kuma lokacin suma taga su Salmah na matsa wa baya suka rabe tareda tsayawa cak suna yin qasa da kansu cikeda girmamawan da hatta gangar jikinsu na nuna hakan dan haka itama a natse taja Bayan tareda Kaucewa hanya amma ta kasa sunkuyar da kan nata duk da bawai ta damu da son gani ko sanin waye ake bawa girman ba kawo tayi ne sbd yan uwanta sunyi.

Qamshin ASIM ne ya doso gurin yana ratsa hancinsu daya sakasu sake yin qasa da kansu sosai,

ASIM daya fito daga bangaren mahaifiyarsa zuciyarsa na Wani irin zafi da baqin cikin labarin dawowan Ayanah ghaz daya samesu tareta sultan Wanda sukeda cikakkiyar tabbacin Ayanah ghaz ta dawo masarautar to tabbas NUAB ya gama dawowa sbd a daidai wannan lokacin bazai taba barin mahaifiyarsa ba.

Kokarin ficewa daga hanyar yakeyi idanuwansa sun sauya yanayi sbd baqin ciki me tsananin dayake ransa,

Tin kafin ya qaraso idanuwansa dake cikin fushi suka sauka Akan kyakkyawar fuskarta da bata sauke ba amman bashi ko hanyar daya fitoba take kallo hanyar inda zasu nufa take kalla har lokacin hannuwanta na riqe da kafadunta sbd sanyin dayake sake ratsata sosai ta matsu ta koma ko kitchen ne ta zauna dumin dayake cikinsa ya dan ratsata sbd koina Bayan kitchen a bangaren ac ne dashi kuma sanyi ze qara mata sosai.

Kafeta da idanunwansa yayi yana qarasa isowa inda suke zai gifta su amma idanuwan nasa sun kasa daukewa daga gareta yana mata kallan tsaftar dabai mata ba a ranar farko daya fara sakata idanwansa,

Uniform din dasuke jikinta yabi da kallo a cikin nutsuwa da bada dukkanin lissafin kwakwalwansa datake sakawa zuciyarsa Wani irin yanayin dayaji bacin rai da fushinsa yana sauka ahankali batareda yasan meya ke shirin faruwa dashi ba sbd wannan fuskar itace take yawo a cikin Kansa da zuciyarsa tin ranar daya ganta din bai sake ganinta ba sai yau din,

Juyo da idanuwanta tayi daidai yana kawowa gap da ita idanuwanta suka sauka akansa kallo daya tayi masa ta dauke idanuwan nata sbd kasa iya cigaba da kallansa sbd Wani irin kallan dayake mata da dukkanin imaninsa da zuciyarsa.

Gifta su yayi zai wuce sai kuma kafafuwansa suka dakata sbd zuciyarsa data kasa hakura din ta tafi batareda ta samu abinda takejin tana buqata ba,

Bude baki yayi batareda ya juyoba da muryansa mai iko da mulki a cikinta yace

‘Bayin wane bangaren ne??

Sake qasa da kai sukai cikin girmamawa da ladabi Naimah tace

‘Bangaren wishmah’

Shiru yayi Wani abu ya sake sokar zuciyarsa ya juyo a natse ya sake saukar da idanuwansa Akan Bahar din wannan Karan yana tabbatarda zuciyarsa da kowace macen duniya bata taba shigaba ko a mafarkinsa baiwar take shiga ahankali kuma shiga me karfin gaske da kaifi,

Dauke idanuwansa yayi daga kan Bahar din wadda har lokacin bata dago ta kallesa ba Wanda hakan ne yaji ya sake kashesa akanta dan kuwa babu macen da rayuwarsa kaf ya hadu da ita data iya nuna darajar kanta fiyeda matsayin dashi yakeda shi na matsayin me mulkin BOYEM ta gobe ba shakka ba fargaba kamar ma batasan matsayin nasa ba da karfin da Masarautar take dashi a duniya ba.

Salman ne dayake bayansa ya qaraso gurinsu ya kalli naimah datai magana yace su fadi sunayensu daya bayan daya.

Ahankali suka ringa fadar sunayen nasu har zuwa kan Bahar din wadda itama kai tsaye ta bude baki a natse cikin tsananin sanyi da nutsuwarta ta furta sunanta ‘BAHAR’

Kafe idanuwansa yayi a fuskarta da bakinta daya fidda sautin sunan nata,

Readers Also Read