Kenza eBookz

Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee - Chapter 31

Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee - Chapter 31

Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 31: Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 31. Ayau dinma a tare suka fito da yammar dan…

4,485 words

Ayau dinma a tare suka fito da yammar dan tafiya zuciyar ASIM fes Akan tunanin daya yanke na isar wa da sultan sakon ya shirya karban imebetin farko kafin aurensa dan kuwa yanason Bahar ta zama tasa har abada ya shirya tsaf Akan fuskantar komai dazai hanasa mallakarta Bare babu tinda baiwa ce batada ikon kanta hakama bame ikon Hana hakan koda kuwa shi sultan dinne sbd halascin Masarauta ne.

Acan fadar sultan ma kai tsaye sako ne da yammar ya isa bangaren LEUL me boyem na takarda basa auren LEYLAH YUNAR BOYEM a matsayin tukuicin Barka da dawowansa gida Bayan shekaru.

Aleey ne ya karbi sakon kuma shine ya bude ya fara ganin abinda yake ciki dan haka sunkuyar da Kansa yafara yi a natse yana kasa fadawa NUAB din sbd sanin aure daya ma dayake Kansa bai karbasa ba yama manta dashi kila bare aure na biyu Wanda yake na sarauta ne har abada NUAB din bazai karbesa ba.

Jin shirun aleey din ya saka NUAB din dayake Zaune sanye da fararen kayan sanyi a jikinsa dagowa ya zuba masa fararen idanuwansa baice komaiba ya miqa masa hannu sbd yasan koma menene aleey shakkar isar masa dashi yakeyi bare kuma daga sultan sakon yake.

Da sanyin jiki tareda girmamawa Aleey ya miqa masa takardar me dauke da stamp ma masarautar Wanda shine sakon auren da zai fita a matsayin sanarwar hadin auren.

Karantar sakon yayi har karshe yana ganawa ya dunqule takardar ya jefar yana jin ransa da zuciyarta na mummunan baci da wata irin tafasa baisan waye ma yarinyar da ubanta da ake magana akai ba.

Acan ma sakon ya isa ga mahaifiyarsa wadd akai tsaye ta kirasa a waya tana nemansa sbd sanin zai iya samun sultan Akan hakan dan haka ta buqaci ganinsa da gaggawa dan kuwa ita hadin auren yayi mata dan kuwa bazata qi yar Zuhrah ba tinda Allah bai bata ikon cika burinta ba Akan ‘danta.

Koda kiran Ammin ya shigo wayarsa zuciyarsa takai qololuwan fusata dan haka miqewa yayi kai tsaye ya fito su Aleey na bayansa a kame sbd ganin bacin ransa a saman qoli yake.

Tinkaro gefen sukai daidai ASIM ma ya iso tareda sakaman dasu Bahar ja bayansa amma ita tana daga gefensa.

Aleey a karo na biyu idanuwansa a Yauma sun sake tabbatar masa da abinda ya kasa yadda dashi a Karan farko ganin Bahar a tareda ASIM dan haka satar kallan NUAB yayi daidai Wanda yake gaban ya dan tsaya tareda kallan ASIM Wanda ya dakata sbd tinanin gaidasa aleey zeyi kaman daga sama aleey din yace

‘Barka da yamma Ms Ayanah Bahar’

ASIM da maganar ta kashesa cikin iko da isa yace

‘Baiwa tace ta musamman bakin Ka ya San yanda zai fada sunanta…..

NUAB dayake gap da saka kai bangaren Amminsa dakatawa yayi cak tareda dan dago idanuwansa da suke jajir sbd fushin dayake tafe dashi sbd yaji lokacinda aleey a Ambaci sunan sedai bai tsammaci amsar data fito daga bakin ASIM ALMAZZ ba…. #MAMUH

HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070

Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali*_HAYATEEM_* Mamuhgee

76 A cikin nutsuwa da wata irin izza ya juyo a hankali idanuwansa dake jajir suna dagowa tamkar Wanda suke a buge sbd wani zazzafan yanayin dayake cikinsu na abinda ya gama kunno wutar jininsa da kuma abinda kunnuwansa suka ji masa yarinyar da igiyoyin aurensa uku suke kanta da sai ayanzu ne ma da aka ambaceta yake tina hakan Wani yake kira da baiwarsa.

Akan fuskar Aleey ya fara sauke idanuwansa sbd ya samu direction kai tsaye na wacece Bahar din a cikin bayin dake tsaye cikeda Wani irin tsoron ganin maza biyu masu BOYEM da kanta tsaye a gurin daya niimarsa ta dauki Zafi take,

Aleey da NUAB din yana dakatawa shima ya dakata da maganar da zaiyi yana qasa da Kansa dan kuwa yasan duk abinda ya Dakatar da tafiyar NUAB mai zafi ne dan haka gabaki dayansu Yaransa qasa sukai da kai kowannesu shirye da raba ASIM da rayuwarsa batareda shakkar komai da abinda zai iya biyowa idan NUAB yace Ayi to yi din zasuyi.

Kallan bayin yayi da idanuwansa masu girgiza Wanda aka kalla dasu a Karan farko ya bi bayi da kallan tsaf yagansu gabaki daya da uniform da komai iri daya,

Gabaki dayansu kasa riqe kallansa daya sauka akansu sukai duk da kansu na qasa cikeda fargaba da tsananin girmamawa zubewa qasa sukai gabaki daya bayin kaf.

BAHAR saida kowa ya zubewa tukuna ta motsa zata zube qasa din itama zuciyarta na Wani irin nauyi da radadin baqin cikin kasancewanta anan a Karan farko,

Sauka gwiwowinta zasuyi qasa ASIM da zuciyarsa bazata taba daukan ganin macen dayake tsananin so kuma macen da zata zama imebētinsa zuwa wishmarsa ta durqusawa NUAB dan haka kai tsaye hannu ya miqa zai riqota dan hanata kafafunta kaiwa qasa.

Hannunsa na isa gareta aleey yayiwa hannunsa Wani irin riqo da hannunsa daya tareda dagowa da sauri da Wani irin mamakin dayake hade da bacin ran da bai bayyana duka ba sbd babu kuma Wanda yake da ikon kai hannunsa jikin Bahar da aurensu yake kanta ko waye kuwa.

NUAB kuwa da zuciyarsa ta gama qara fusata hakan daya faru ya tabbatar masa waye Bahar din dan haka idanuwansa ya rintse da karfi tareda budesu akanta ya miqa hannu cikin wani irin fushin daya saka su aleey sake yin qasa da idanuwansu ya damqi hannunta ya jata yana Juyawa daga inda ya fito tareda fasa shiga gurin Ammin nasa.

ASIM da zuciyarsa ta gama quluwa tana wata irin tafarfasa fizge hannunsa yayi cikin tsantsan tiriri da kishin dayaji na Neman kashe zuciyarsa da dukkanin gangar jikinsa ya daga hannu zai shararawa Aleey lafiyayyan Marin rashin da’ar da yayi masa daya daga cikin securities dinne ya sake riqe hannunsa Wanda bai tsaya wata wata ba ya sakarwa security din wata mummunan Marin daya saka fuskarsa jajir.

Sauran securities din cikin girmamawan da batada amfani garesa suka dan saukar masa da kai bisa umarnin aleey daya kallesa ya bude baki yace

‘Allah ya Huci zuciyar Li’ul ASIM’

Yana gama fadan hakan ya juya yabar gurin yana ban Bayan ubangidansa da gabaki daya rahamarsa ta dauke sbd Zafin dayake tafasa a jininsa na fushin dayake hawan gobara a yanayinsa,

Sauran suma gabaki dayansu bayansu suka bi Ana barin ASIM a gurin cikeda Wani irin tafasa da jininsa ke yi a gurin sbd NUAB ya gama wulaqantasa da bayyanarda shirin yaqi a tsakaninsu dan kuwa hakan da yayi masa zai iya bayyanar da tasa zazzafar qiyayyar sbd abinda yayi a gurin yafi yaqi da gabar dake tsakaninsu na gadar mulki,

Zai iya hakura Bayan yaqi da dukkanin kokari idan yayi ya rasa mulkin BOYEM amma kuma Akan Bahar bayajin a bayyane ma zai iya barin ko uwar NUAB din a raye bare NUAB din dan kuwa sedai ya rasa ransa gurin yaqar hakan dan kuwa Bahar tasa ce akanta zai iya fuskantar kowa, Zai iya tsayawa gaban kowa ya bugi kirjin ita tasa ce dan haka NUAB koma me yake nufi da hakan da yayi a yanzu dan kawai tana baiwar mahaifiyarsa to tabbas zai nuna masa baiwa ce ita daga shi har ita sunada iko da ita cikakke dan haka zai shayar dashi mamakin da zai girgiza dan kuwa a ganin idonsa zata zama macensa imebētinsa.

Barin gurin yayi Salman na biye dashi shima tasa zuciyar kaman zata fashe suka isa bangaren queen haile ASIM din ya shige idanuwansa jajir baya ganin komai daidai tsabar baqin cikin dayake Neman kashesa.

HAILE dake Zaune tareda su Aslam suna hutawa a palon hutawanta Kayan marmari da abubuwan hutawan cike Jere a gabansu duk da ba Wani dadin rai suke cikinsa ba dan kuwa suna Zaune a gurin labarin auren ‘yar mai girma YUNAR daya bawa NUAB Yazo kunnuwansu ya lalata gabaki daya Sauran dan farin cikin rayuwar daya rage musu zuwa sabon baqin ciki me girman gaske dayake Neman makantar da HAILE wadda ta dago jajayen idanuwanta ta kalli Aslam wadda tafara zantika cikin tsananin tashin hankali da baqin ciki me girman gaske hannuwanta har suna rawa idanuwanta jajir take cewa

‘Auren yar YUNAR ga NUAB yana nufin zai tsaya masa a gurin karban mulkin BOYEM, YUNAR zai zabi tsayawa duk Wanda ya zama Siriknsa a cikin magadan biyu, Tayaya zai zabi NUAB ‘dan mistress Akan ASIM Wanda a bayyane da duniya shine dan dayafi da’a da kwantarwa manya kai, ASIM shine Wanda ya cancanta ya bawa aurar yarsa, ASIM ne ya kamata ya zabi tsayawa Akan karban mulkin BOYEM me zaisa ya zabi dan ta’adda? Baisan halinsa da rayuwar da yakeyi ba Wanda yana buqatar sani dan kuwa Mamee muna tsananin buqatar ‘yar YUNAR ta kasance Matar ASIM ba NUAB ba, Mame kota halin yaya kada ki bari dan Allah NUAB ya samu Leylah YUNAR a matsayin mata idan ba ASIM ba sbd aurensa da ‘yar nada kashi casain na alaman nasara Akan ASIM mame dan Allah kada ki bar hakan ta faru…..’

Yanda take maganar cikin tashin hankali da mummunan baqin cikin daya danne zuciyarta kaman zatai bindiga ta buga ya saka meryam ma hankalinta tsananta tashi da Wani irin zallar tsoro da zullumin daya saka idanuwanta jajir dan kuwa faduwar ASIM yana nufin tasu faduwar a abinda suke tsananin so tamkar mutuwa.

HAILE da zuciya ta gama cinyeta Wani zazzafan radadi zuciyarta ke yi dan kuwa idan ma adalci zaayi ASIM dinne ya fara zuwa duniya dan haka shine ya kamata a fara bawa macen a daura masa aure kafin daga baya Ayi maganar NUAB Wanda batajin ma yanada niyar auren a rayuwarsa dan kuwa ta’addancinsa kadai ya sakawa gaba, Tayaya sultan zai mata wannnan mummunan cin fuskar a Idon duniya ya zabi fara yiwa dan mistress dinsa aure Akan ‘dan sunnarsa, Tayaya zata iya barin YUNAR ya tsayawa NUAB ba danta ba? Tayaya zasu iya barin NUAB ya samu wannnan saar ta auren ‘yar YUNAR Bayan ga ASIM dinta….

Jajir idanuwanta sukai Wanda tsananin ja da baqin cikin dayake cike dasu da jini da zuciyarta idanuwanta har wasu ruwan da ba hawaye ba suka tara,

Shigowan ASIM din Wanda tamkar jininsa zai Kama da wuta hannuwansa har wani rawa sukeyi ya sakasu kallansa su dukan kowa idanuwansa na tsananta ja sbd suna ganin tsantsan fushinsa da bacin ransa tareda baqin cikinsa a bayyane kenan shima ya samu labarin,

Zaunawa yayi a kujera yana kasa bude baki sbd fushinsa yayi yawan da bazai iya magana kai tsaye ba,

Shiru sukai dukkaninsu kowa da baqin cikin dayake cinsa,

Sai Bayan mintina masu tsayin gaske ya bude Baki cikin radadi me bayyana yace

‘Ko zan rasa rayuwata bazan Bari NUAB ya shiga tsakanina da abinda nakeso ba, Akanta na shirya bayyanannan yaqi dashi da mahaifinsa sbd shine yake tsayawa haukar NUAB din kowace iri dan haka wannan Karan mutuwa ce kadai zata rabani da ita’

HAILE da kalaman sukai mata Wani irin dadi da Jin sassauci tace

‘Ko ni bazan taba barin ya sameta ba koda hakan na nufin aikata kowane irin aiki saina tabbatarda sun rabu rabuwa da har abada’

Aslam ma Jin tayi sanyi na samun sassauci na dan ratsata ta kalli ASIM din tanajin nutsuwar daya kasance yana son Leylah din dan sun dauka bazai sota ba bazai kishin kasa samunta ba dan haka dukkaninsu suka Ji sun dan samu relief na zasu Hana auren da dalili me karfin gaske.

********kai tsaye bangarensa ya nufa da ita bata ma ganin gabanta sbd yanda yake riqe da hannunta datake Jin azabar riqon da yayi mata amma idanuwanta da zuciyarta sun rufe da ‘dacin da harma bata Jin komai dan haka bata bude idanuwanta sai lokacin da taji ya saki hannunta da karfi tayi baya idanuwanta na budewa jajir itama sbd har cikin ranta bata kaunar ganinsa dan ganinsa ba mummunan auren dayake tsakaninsu tinawa ba hadda rasuwar mahaifinta dan haka kokarin sake rintse idanuwanta takeyi cikeda baqin cikin kasancewa tareda shi…….

Saukar hannunsa Akan rigar dake jikinta ya fizgo da karfin gaske yana rabata biyu daga jikinta ya sakata bude idanuwanta masu girman gaske da kyau sunyi ja ta sauke akansa tana riqe hannunsa da karfin gaske tareda bude baki a Karan farko muryanta ya sauka kunnunesa da tsananin fushi tana kallan cikin tsakiyar idanuwansa da kowa baya iya kalla tace

‘Ābidehali?¿

Jajayen idanuwansa ya dago da Wani irin tsananin Zafi da fushi tareda bacin ran gaske ya kalli bakinta daya furta kalmar da duk duniya babu Wanda ya taba furta masa hatta uwa da ubansa kuwa kaf duniyarsa babu Wanda ya taba kallan fuskarsa ya furta masa wannan kalman da zata iya ajalin dik Wanda ya furtata,

Yana da hankali take tambayarsa???? Shi LEUL take tambayar yanada hankali??? Menene hankali? Batasan koda Yazo duniya baida hankali ba? Batasan baisan menene hankalin ba? Ina ta samu zarrar yi masa wannan kalmar?

Qarasa fizge rigar yayi cikin wani irin sabon rashin hankalin dayaji yana shigarsa data ambata sbd Allah ne kadai yasan yanda ya danni mahaukaciyar zuciyar tasa bai yaga Kayan jikin nata tin acan ba. #MAMUH

HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070

Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali*_HAYATEEM_* Mamuhgee

77 Dago idanuwanta tayi da suka tsananta Wani irin Jan da hawaye masu tsananin radadi suna cikowa a cikinsu ta kallesa hannuwanta na kare jikinta duk da akwai wata qaramar halfvest din a cikinsu,

Ayau ta fuskanci tozarci da baqin cikin da bazata taba mantawa ba daga Wanda batajin har abada zata manta,

Wani mummunan baqin ciki ta Hadiye ta bude baki zatai magana ya juya ya bar gurin har lokacin hannuwansa har wani rawa sukeyi yana isa kofa ya fice tareda rufe kofar da karfin gaske daya sakata rintse idanuwanta tana silalewa qasa ahankali wasu hawaye masu tsananin zafi suna gangarowa daga idanuwanta.

Su aleey dake palo a tsatsaye babu Wanda ya dago kai a cikinsu kowa Kansa sake yin qasa yayi daya fito din tamkar guguwan wuta zata tashi haka fuskarsa tayi Wani ja ya fice daga palon suka biyo bayansa,

Suna fitowa kallan securities din aleey yayi yace su tsaya su tsare bangaren tinda princess din GHAZ tana ciki.

Komawa sukai bakin kofar shiga ta farko data shiga palon suka tsare shi kuma aleey yabi Bayan NUAB din zuwa gurin kiran Amminsa da shine ya fiddosa tin farko.

Tin kafin su isa aleey a fidda wayar sa ya Turawa Maa sakina sakon taje bangaren NUAB Princess din GHAZ tana can.

Maa sakinah dake Zaune tana kallan time a agogon wayarta na rashin dawowan Bahar har lokacin zuciyarta cikin wani zullumi da rashin sukuni take dan haka miqewa tayi tana nufar dakin bayin bangaren dake Bayan kitchen dinsu dan dubowa.

Tana shiga kitchen zata bi ta kofar kitchen din zuwa dakin nasu sakon aleey ya shigo wayarta tana dubawa kirjinta yayi Wani dummm Wani sabon zullumin da fargaban idan ba Wani abin ne ya samu Bahar din ba dan haka dawowa tayi tana fitowa daga kitchen shi kuma NUAB a lokacin ya shigo harya saka kai a palon farko ya shige dan haka basu hadu ba ita kuma kofa ta nufa kai tsaye ta fice,

Aleey dayake kofar gurin ta hadu dashi baice mata komaiba sbd baya magana ko wace iri idan baisan Meye a zuciyar LEUL dinsa ba dan haka kai tsaye bata tsaya ba itama sanin bazai taba fadar komai ba batareda izini ko umarnin NUAB ba dan haka cikin wani sanyin jiki da kafafu ta nufi bangaren nasa dan dubo meya samu Bahar dinta.

Ko daya isa securities da suka San matsayinta a gurin maigidansu dama Bahar din basu hanata ba kai tsaye bude mata kofa sukai da girmamawa me girma ta shige.

Tana shiga babban lafiyayyan palon nasa dayake tsit komai na palon tsarin rayuwarsa ce ta Russia da taste dinsa, Qamshinsa ne koina yake cike da niimar iskar da kake shaqa dan babu abinda bai gama kamuwa da tsadadden qamshinsa ba da baa jinsa a gurin kowa,

Kallan koina tayi tana rasa ina ma zata ga Bahar din dan haka kai tsaye bude muryanta tayi ta Ambaci sunan Bahar din wadda sautin muryan Maa din na shiga kunnenta ta fasa wani kuka Mara sauti a hankali sbd bazata iya fitowa ba babu Riga a jikinta.

Sake kiran sunanta Maa tayi tana tinkarar dakin datasan ba shine na NUAB ba dan nasa dakin sam idan bame gyaransa ba babu me shiga shima Wanda yake gyaran a cikin Yaransa ne babu bawa ko daya dasuka yadda dashi Akan komai na maigidansu dan haka sune securities sune kuma bayinsa ba wata dama ko yar qanqanin da kowa yakeda ita ta iya cutatar dashi sbd sun tare tako Ina rayuwarsa da tasu rayuwar.

Maa sakinah na isa dakin kai tsaye murdawa tayi ta bude idanuwanta suka sauka kan Bahar din wadda take durqushe a qasa ta rufe jikinta da tafin hannuwanta.

Faduwa gaban Maa yayi da karfin gaske har kafafunta na rawa ta ta iso gurinta da sauri tana isowa ta janyota jikinta ta rungume da karfi tana Jin faduwan gabanta na tsananta tace

‘Bahar meya sameki? Meya faru na ganki hakan? Ya akai?

Lafewa jikin Maa din tayi tana fasa sabon kuka tareda qanqameta tana bude baki tace

‘Inason barin nan Maa,Inason komawa ANJOM maa.’

Saurin sake rungumeta Maa tayi tana Jin zuciyarta na sosuwa da abinda ya faru koma menene,

Bata taba Jin zata tirsasa Bahar a zuciya da rayuwar NUAB ba sbd dukkaninsu babu Wanda zata iya yiwa dole Akan dan uwansa, Bahar amanarta ce da Abaas ya damqa a hannuwanta data karba zata riqe da rayuwarta da karfinta harsai rayuwarta tabar jikinta,

Dukkanin soyayya da kaunar datake wa Ayanah zata bawa Bahar irin wannan kaunar ne sbd daga ranar da Ayanah tasan waye Bahar zatai baqin ciki da kukan tsanar kanta da ‘yar Abaas dinta ta kasance a qarqashinta da sunan baiwa.

Idanuwanta da sukai ja ta rintse tana budewa ahankali ta saukesu Akan Bahar da fuskarta tayi ja sbd kukan datake yi sosai a jikinta.

Mayafin dake rufe da ita ta zare tana share mata hawaye a hankali tareda Jin itama a Karan farko zaman BOYEM ya isheta ANJOM takejin son komawa indai zata rayu da Bahar acan ta bata farin ciki da kulawa tareda kauna har zuwa lokacinda shi NUAB din yaji yayi niyar fadawa mahaifiyarsa waye Bahar.

Miqewa tayi tsaye tareda miqar da Bahar din tsaye tareda ficewa kai tsaye cikin bacin rai ta isa dakin NUAB da babu me shiga.

Shigarta kai tsaye babu inda ta dosa a dakin sai closet dinsa da kayansa sama da Kala dari suke a Jere babu Wanda ba original designer ba,

Babu zabi ko kallansu data tsaya kai tsaye shirt ta dauko fara qal ta juyo har lokacin nauyi ne danne da kirjinta,

Dakin ta koma ta isa har gurin Bahar din wadda take cikin yanayi da nauyi da radadi a kirji,

Da kanta ta saka mata rigar wadda tayi mata mugun yawa sosai amma hakanan ta kamo hannunta suka fito,

Suna fitowa kofar palon cikin tsananin girmamawa me girman gaske yaran NUAB din suka dan sauke kai suna kasa barinta ta wuce da Bahar sbd babu umarnin hakan daga shugabansu daya ajiyeta a gurin.

Kallansu tayi zuciyarta na Wani irin cika da mummunan bacin rai da fushin dabai taba bayyanar mata ba sbd hakuri da rashin yanci ta bude zatai magana dayansu ya saka kiran Aleey ya sanar dashi.

Kashe wayar aleey yayi da sauri yana tahowa,

Koda ya iso Maa sakinah na fada sosai Wanda babu Wanda ya dago a cikinsu kansu na qasa suna sauraronta cikin girmamawa amma bazasu iya bude kofar ba.

Aleey na isowa da sauri yayi qasa da idanuwansa daga kan Bahar sbd kai tsaye rigar dake jikinta da hadda itace ta saka yaran gabaki daya qasa da kai suna kasa dagowa.

Da Kansa aleey ya budewa Maa din kofa yana bata hakuri a natse.

Ficewa tayi har lokacin hannun Bahar din yana hannunta a zuciyarta ta yanke shawarar komawa ANJOM sbd samarwa Bahar nutsuwa da kwanciyan hankalin datake buqata, A yanzu tanada dukiyar zinarin da zata maida garin ANJOM garin dayake a baya dan haka zata tafi da Bahar ta bata rayuwar Jin dadin data cancanta samu.

Koda suka iso bangaren kai tsaye daki suka shige babu kowa a palon,

Suna shiga Zaunawa tayi tareda zaunar da bahar gefenta sukai shiru babu me cewa komai kowannensu idanuwansa a quntace kaman zuciyoyinsu suke a quntace.

******Acan palon Ammi kuwa NUAB dinne ta kalla da dukkanin nutsuwa da zuciyarta ta bude Baki tareda Dora hannunta daya Akan nasa tace

‘Hayateem ka samu sakon auren da aka Baka na sani Wanda ina tsananin son auren nan har cikin Raina kuma nayi Naam dashi amma Ka sani bazan taba tirsasa Ka matiqar Baka raayi sbd bazan taba son Ka auri Leylah yunar Ka quntatar da rayuwarta da rashin soyayyarka sbd tamkar ‘yar daba Haifa haka nake jinta a zuciyata……..

Dago jajayen idanuwansa da suka sake tsananta da ja yayi ya kalleta bakinsa cikin wani irin nauyi da rashin kasa danne abinda yakeji yace

‘Saboda tana jinin ZUHRAH GHAZ???? Kin karya alkawarin hadin auren dayake tsakaninki da Abaas ne? Idan Baki karya ba tayaya zan auri ‘yaya biyu daga duka yan uwanki Ammi?? Ammi ban taba shaawar aure ko rayuwa da mace ba anan kusa? Wannan auren sarauta ne Wanda babu shi a cikin tsarin rayuwata har abada, Bazan taba mulkin BOYEM ba sbd BOYEM bata cikin rayuwata har abada, sultan ya aiko mun sakon auren Wanda a yau zan mayar masa da amsar ban karbi kyautar aurenba’

Wani irin zufa ne ya fara gangarowa goshin Ammin sbd Jin zuciyarta na bugawa da karfin gaske Jin sunan Zuhrah a bakin NUAB Wanda bata taba fadawa labarinta ba amma yasan Zuhrah da bazata iya fuskantar iya hana Leylah yar Zuhrahn ba abinda take so ba sbd haka take Jin Leylah har jininta sbd ita kaddararta Akan soyayyar datake wa yan uwanta ne da duk abinda zasu haifa.

Kallansa tayi tareda sake Kama hannunsa ta hada da nata ta bude baki tace

‘Kafin komai Hayateem Kamun alkawarin bazaka taba hayaniya da tashin hankali da mahaifinka ba sbd bazai taba janye wannan auren ba matiqar ba zaka cika sharadinsa ba na abinda yake so kila, Kamun Alkawari Hayateem bazakai tashin hankali ko fitina ba kowace iri da sultan’

Kafesa da ido tayi tana maimaita maganar wadda ta sakasa zame hannunsa ahankali daga nata tareda rungumeta jikinsa batareda ya iya cewa komaiba sbd yasan tsoronta Akan kada sultan ya sake rabasu ya koresa daga masarautar Wanda a yanzu sultan baida wannan karfin dazai rabasa da mahaifiyarsa.

Numfashi me Zafin gaske ya sauke ahankali ba sauti tareda sumbatar tsakiyar kanta kafin ya saketa a natse ya miqe ya fice yabarta Zaune cikeda zullumi da tsoron gaske kashi uku,

Yaya NUAB ya San Zuhrah? Da gaske yasan zuhran jininta ce? Ya akai yasan alkawarin dake tsakanin sa da Abaas? Yaga Abaas ne? Meya yasa yake mata maganar Alkwarin auren da basuda tabbacin Abaas din ya samu yancin haihuwa?????? #MAMUH

HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070

Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laoualiHAYATEEM Mamuhgee

78 Yana barin kanta ya tsananta Juyawa tana kasa yadda da maganar NUAB din wadda yayi mata wadda magana ce da akai a ANJOM basu taba tada ita ba anan tinda suka samu sauyin rayuwar da babu farin ciki a cikinta, NUAB bai taba sanin komai Akan Abaas dinta ba Bayan sunansa da matsayinsa na rabin rayuwarta datake wa so fiyeda tata rayuwar,

Ayau yana maganar alkawarin auren dayake tsakaninsu na shekarun da tin Abaas din yana yaro,

Miqewa tayi kanta da kirjinta na nauyin rashin iya samun kwarin gwiwan bawa NUAB daman kasa auren Leylah wadda batajin a yanzu batada zabin daya wuce ta tirsasa hakan dan kuwa Leylah zata dawo gareta shikenan jinin Zuhrah yana hannunta.

****** Yana Baro bangaren Ammin kai tsaye bangarensa ya nufa yana isa bai damu da dubawa ko tana nan ba ko bata nan dan haka sallah sukai tareda Yaransa kafin ya shige bangaren nasa ya sake daukan tsit, Sai ishai ya fito cikin fararen armanis sukai sallar ishai din yana gamawa kai tsaye bangaren sultan ya nufa har lokacin idanuwansa basu dawo daidai ba kaman yanda tiririn zuciyarsa bai sauka ba,

A daidai wannan lokacin shima ASIM kai tsaye kasa hakura yayi ya kwana a ranar batareda ya isar da buqatarsa dayake son a tashi Washe gari da ita na buqatan imebētinsa ta farko dan haka shiryawa yayi a Daren ya nufi bangaren sultan da tsananin taurin zuciya da karfin burin dayake a shirye dashi.

Koda sakon isowan NUAB daya fara isowa fa sultan yana Zaune palonsa ma hutawa Lumshe idanuwansa yayi cikin nutsuwa tareda sauke ajiyan zuciya sbd yasan daman Ayau din sai Yazo sbd babu yanda zai karbi aure irin wannan kai tsaye shi kuwa damar sake tsananta masa abubuwa Akan cikar burinsa ne ya samu sbd yakai lokacinda yake buqatan sauka mulkin dan bawa macen dayake tsananin so har a cikin jininsa Sauran lokacinsa daya rage a duniya sbd bata dukkanin farin ciki da walwalan da bata sani ba a lokacin kuruciya dan haka a yanzu tako wane halin saiya tabbatarda NUAB ALMAZZ ya karbi mulkin qasar BOYEM da hannunsa dan kuwa shine kadai Wanda Zai iya riqe mulkin a tsaye da dukkanin adalci da tsayuwar da qasar BOYEM taje buqata ta kuma daba dashi daga kowane sultan datai a tarihi hakama yana buqatar yayi wannan auren na YUNAR daya basa na kyautar yarsa sbd yunar zai tsaya masa da karfin nasa ikon a gurin mulkar BOYEM tareda basa dukkanin kariya ta Sharrin mulkin sarautar da baisan ta ina zai fara zuwa ba dan haka yana Bayan auren shima.

Har palon Sultan kadir ya rako LEUL din tareda komawa waje ya basu guri.

Zama cikin nutsuwa NUAB yayi tareda dagowa da idanuwansa da suke sak na mahaifin nasa suna cikeda Sauran fushin dayake cikinsu ya kalli sultan tareda danne zuciyarsa dan Hana kasa furta abinda bai daceba ga alkawarin Amminsa daya hau Kansa a yau din na kada yayi fitina kowace iri da sultan din.

Bude bakinsa yayi da muryansa me cikakken iko da nutsuwa yace

‘Barka da dare me BOYEM, Barka da hutawa daga gajiyan tafiya’

Cikin iko da milki sultan ya saukar da idanuwansa Akan NUAB din tareda sauke ajiyan zuciya me sanyi tukuna ya bude baki ya amsa da cewa

‘Barka NUAB ALMAZZ, Wannan ziyarar kai tsaye akwai dalilin yinta Wanda zaka iya fada kai tsaye.’

Sake dago manyan idanuwansa NUAB yayi Wanda suka sauka Akan sultan sbd baya buqatar kasancewansa a gabansa kenan ya fada abinda ya kawosa kawai,

Baya buqatan shima qara mintina Akan abinda ya kawosa dan haka takardar hannunsa daya shigo da ita ya Dora a kan table din gaban sultan din tareda dauke hannunsa ya mayar da bayansa ya jingina ya dago ya bude baki a natse yace

Readers Also Read