Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee - Chapter 33
Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 33: Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 33. Numfashi ya sauke ahankali tareda dakatawa ta…
4,470 words
Numfashi ya sauke ahankali tareda dakatawa ta saka hannunta karkashin nasa ta dafe tana Juyawa cikeda baqin ciki da mutuwar jiki.
Shikuwa Juyawa yayi ya fice tareda rufe dakin yabarta yana Jin kukanta na fara fidda sauti ya tafiyarsa bai damuba.
A palon ya zauna ya kira aleey ta waya aka Jere masa breakfast ya zauna yayi anan aleey yake sanar dasu manyan securities dinsu da suka Baro Russia a Daren jiyan sun iso.
Izinin zuwa a shigo dasu masarautar NUAB din ya bayar aikuwa haka su aleey suka isar da pass dinsu a gate Wanda haka wasu irin mahaukatan motocin da zasu iya tada gari suka ringa shigowa masarautar a jere da wasu irin bindigogin da labarin su suka isarwa manyan fada a take,
Hankalin su fara tashi yayi sunajin shakka na kokarin shirya zukatansu da rayuwarsu na tsayuwar da suke da shirin yi Akan bazaa bawa NUAB mulki ba duk uban daya taru dan haka wasi wasi yafara shigarsu sbd yaran GHAZ din da suka iso masarautar masu yawa ne hakama babu Wanda alamar ma yasan menene imani yake bayyane a fuskarsa daukan ran kowa a masarautar ba abin wahala bane a garesu.
Sultan ya samu labarin isowansu dan haka take shikuma ya saka Hannu a takarda biyu yace a fitar a dare a tashi dasu a masarautar Washe gari wato ta imebetin ASIM wadda zaa shirya masa da gaggawa a abasa hakama data auren NUAB da Leylah yunar.
Tinda NUAB ya fito a ranar yana Zaune a palonsa hankali kwance a natse cikin iko da Izzar dayake jiran komai ma kaman yanda Yaransa suke cike a bangaren hakama a ranar aka fara aikin ware Wani makeken bangaren tsohon sultan zaa rushesa gabaki daya a fara masa sabon ginin irin gidansa sak dayake russia.
Babu Wanda ya shigo ko hanyar bangaren hakama babu Wanda ya fita shi Kansa Ayau Zaune yake bangarensa babu inda ya fita ko gurin Amminsa a Karan farko bai fita yaje ba a waya yayi magana da ita yana Zaune hankali kwance har dare.
A Daren takardun sakon biyu suka fito a lafiyayyun trays zuwa bangaren mahaifiyar NUAB da mahaifiyar ASIM.
Sakon na doso bangaren HAILE saleem dayake tsaye bakin bangaren saurin zubewa qasa yayi yana sunkuyar da Kai jikinsa gabaki daya yana daukan wata irin rawa sbd bazai iya karban sakon ba dan isar dashi ciki dan haka baiwar kusa dashi data fito yayi da sauri yace ta kirawo fetto sbd yasan tana fitowa itace zata Kai sakon. #MAMUH
HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070
Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali
HAYATEEM Mamuhgee
81 HAILE da gabaki daya yayanta a lokacin Zaune suke a palonta sun cin abincin dare Wanda aka jere a gabansu fiyeda Kala biyar da tarin fruits masu sanyi da tsafta a jere suma sai lafiyayyun juices d Aka hada musu fresh me sanyi,
Cin abincin sukeyi amma hankalinsu duka yana kan ASIM daya ce sultan ya amsa masa buqatarsa ta basa macen dayake tsananin so dan haka zuciyarsa a fes take Jiyan,
Tin jiyan bai damu da NUAB da Sauran kowace matsalarsa ba karban Bahar a matsayin tasa cikakkiya shine a gaban zuciyarsa dayake tsananin fatan Ayau burinsa ya cika din,
A nan bangaren mahaifiyarsa ya wuni da tsananin jiran fitowan sakonsa daga sultan Wanda yakeson Ana aikuwa ba bata lokaci akai saqon bangaren wishmah sbd baiwar dayake so acan take hakama wadda zata shiryata a matsayin imebeti itama acan take dan haka da gaggawa yake son sakon yaje can ba bata lokaci ko qanqani,
HAILE ma zuciyarta sai Wani irin rawa da harbawa takeyi da tsananin farin cikin daya hanata gabaki daya kaiwa sultan ziyara a ranar daga ita har yayanta zaman gadin isowan sakon auren sukeyi Wanda babu Wanda bayajin Dakawar zuciya Akan hakan sbd sun matsu sultan ya fidda umarnin tin kafin labarin ya sauya.
Suna Zaune dinne jiran wannan umarni kaman zukatansu zasu fado sbd matsuwa da zullumi kwatsam sai ga sakon Kira ya tahowa fetto daga waje Wanda jikinta take ya dauki rawar farin cikin karbowa HAILE da yayanta abinda Ayau suke tsananin Buri na umarnin auren danta daga sultan.
Fetto na fitowa sakon na isowa dan haka da sauri ta qaraso tana zubewa qasa gaban manzon sakon tana masa Barka da isowa tareda kirari ga sakon na sultan.
Hannuwanta biyu ta dago tana miqawa dan amsar sakon Wanda ya saka Salman sake saukar da Kansa qasa zuciyarsa na Wani irin tsima da tsananin tashin hankali yana ma kasa kallan sakon.
Fetto kuwa tsabar Murna jikinta har wani rawa yakeyi ta amsa tareda zuba godia ta juya ta shige ciki da sakon.
Ko data iso palon da suke Zaune gabaki dayansu suna cin abinci har lokacin ASIM ne idanuwansa suke fara sauka Akan hannuwanta biyu dake dauke da takardar fadar sultan dan haka ajiye cup din hannunsa yayi a hankali yana kafe idanuwansa Akan hannuwan nata ba kyaftawa zuciyarsa na cikewa da Wani irin farin cikin da tinda yake bai taba jinsaba.
Aslam da meryam kallan yanayinsa sukeyi da mamaki kafin suka Waiwaya suna kallan inda yake kalla da wannan yanayin da suma basu taba ganinsa a ciki ba.
HAILE ma juyawan tayi ahankali ta kalli inda suke kalla gabaki dayansu taga fetto na qarasowa dauke da takardar da dole daga sultan ta fito tana daukan ido sbd kyallin kalar gold dake jikinta.
Wani irin farin cikin taji itama ya cikata Wanda ya sakata ajiye spoon din hannunta taba daukan tissue ta goge baki tareda miqewa tsaye take suma yayan nata suka fara miqewa daidai nan fetto ta iso da takardar wadda ta miqawa ASIM.
Cikeda farin cikinsa dayake sake bayyana ya karba tareda budewa a hankali yana karantawa jikinsa har tsima yakeyi ganin cikakken izinin mallakar Bahar a matsayin imebētinsa wadda samunta a rayuwarsa shine matakin farko na nasarar rayuwarsa da zai fara daga yanzu,
Sunanta daya aikawa sultan shine a bayyane Baro Baro a rubuce cewan ta zama imebetinsa daga yau dan haka rufe takardar yayi hannunsa na dan rawa ya miqawa fetto ya kalleta da dukkanin idanuwansa yace
‘Ki Kai bangaren wishmah wannan sakon na tenya ne a gobe nake buqatan wara haka imebeti dina tana bangarena’
Da tsananin mamaki fetto ta kallesa tana amsar sakon hannuwanta na dan rawa sbd shock da fiyayyan mamakin Jin sunan imebeti a bakinsa Bayan Leylah jinin sarauta ce meya hadata da sunan imebeti kuma?
HAILE kallansa tayi tana dan Kama Fuska zatai magana Aslam da bazata iya jiran bayani ba karban takardar hannun fetto tayi tana budewa Kai tsaye tafara karantawa rubutun Wanda yake a rubuce da yarensu da manyan baqaqe masu kalar zinari na alkalamin sultan me mulki.
Meryam data Riga Aslam gama karanta sakon Wani irin sanyi kafafunta sukai me tsananin gaske suna kasa daukanta ta zame ahankali tana Zaunawa idanuwanta na dagowa da Wani mugun kallo tana kallan ASIM dan tabbatarda farin cikine bayyane a fuskarsa na abinda yake rubucen.
Aslam miqa masa takardar tayi tana masa Wani kallan mamaki me tsananin gaske ta bude baki tace
‘Kaga menene a ciki? Ka fahimci abin dayake cikin sakon kuwa? Kasan me aka aiko maka?
Miqawa fetto sakon ya kuma yi yace ta fice ta Kai ya kalli Aslam zaiyi magana HAILE datake Jin yanayin zuciyarta na sauyawa ta Dakatar dashi da cewa
‘Menene yake rubuce a ciki? Ba auren Leylah bane a cikin sakon?
Meryam datake Jin kanta na Juyawa ce ta iya bude Baki jikinta na tsananta mutuwa da Wani irin yanayin da bazata iya fassarawa ba tace
‘Imebēti aka basa a maimakon auren Leylah’
Aslam data kasa Hadiye tsananin baqin ciki da fushin dayake taso mata ta Dora da cewa
‘Kuma da alama yasan da hakan sbd farin cikin dayake bayyana a fuskarsa,
HAILE dataji kaman bata fahimci zancen da kyau ba kallan ASIM din tayi da duka idanuwanta fes a Kansa zuciyarta na sauya bugawa ta bude Baki tace
‘Imebetin?shi sultan dinne yaga ya kamata ya baka imebeti Bayan ya bawa ‘dan mistress dinsa auren jinin yunar?
Juyowa tayi Akan Aslam da meryam tace
‘Sunan ASIM dinne kuwa kuka gani a rubuce ciki kokuwa sbd sakon bazai taba kasancewa nasa ba dan ba yanda zaayi yana matsayin me jiran gadon kujeran BOYEM ya fara da imebeti batareda yayi aure ba hakama yayansa manya su fara zuwa daga imebēti, Tayaya hakan zai taba yiyiwa? Ba sakonsa bane?
Aslam data gama kaiwa qarshen baqin ciki dafe goshinta tayi tana bude idanuwanta jajir tace
‘Mamee yana sane fa,kuma da alama shine a buqaci hakan’
Kafesa da ido HAILE tayi sbd tanason ji daga bakinta idan sakarai ta haifa bata saniba
Kallan Hailen yayi yana matsowa gabanta ya Kama hannunta cikin tausasa harshe yace
‘Mamee ba imebeti ce kadai ba sonta nakeyi so me tsananin da zan iya komai akanta ciki hadda rasa rayuwata, Ba jinin sarauta bace baiwa ce dan haka Banda zabin daya wuce karbanta a matsayin imebē…….
Bai qarasa ba HAILE ta sauke masa Wani lafiyayyan Marin daya saka meryam miqewa tsaye da sauri Aslam ma cikin sabon tashin hankali take kallan Hailen da idanuwanta jajir.
Kasa dagowa ASIM din yayi idanuwansa na rikidewa zuwa jajir zuciyarsa na cikewa da Wani irin ‘daci da baqin ciki me girma.
HAILE ma kasa dauke idanuwanta daga Kansa tayi hannuwanta na wata irin rawa zuciyarta na tafarfasan da bata taba ba kowace gabar jikinta wutar baqin ciki ne take ciketa tana rasa abin fada.
Bata taba sanin sakarai mara tinani da hankali ta haifa a rayuwarta ba sai yau,
Baya tayi ahankali tareda Juyawa ta sake juyowa ta kalli ASIM din ta bude Baki kirjinta na tsananta nauyi tace
‘Me zakai da imebēti Banda zuciyarka ta mutu? Har akwai abinda wata baiwa take dashi Wanda yakai na Leylah? Baiwa zaka fara haifar yayan Ka da zasu gaji sarauta daga gareka? Wane soyayyar kake magana? Ka sani wlh tallahi indai ina raye bazan Bari Ka fara karban imebēti ba batareda Ka auri jinin sarauta ba musamman wannan da kake ikirarin kana so da zata iya sakaka rufe ido Ka zabi gaibu Akan jinin Leylah datake jinin boyem.
Dagowa yayi idanuwansa jajir ya kalli mameen ya bude baki yace
‘Mamee zan auri jinin BOYEM daga baya amma a yanzu ina tsananin son wannan ita zan mallaketa….
Aslam data rasa abin cewa Juyawa tayi cikin tsananin baqin ciki taba barin palon hakama meryam da zuciyarta ke gap da bugawa ficewa tayi.
HAILE ma cikin baqin ciki ta juya tabar gurin tana yanke hukunci a ranta baiwar kowace iri ce zata bar duniya dan bazata taba zama imebetin ASIM ba a yanzu.
Fetto kuwa tana fitowa Kai tsaye bayi hudu ne suke biye da ita zuwa bangaren wishmah dan miqa sakon ga tenya zuciyarta cikeda baqin ciki itama da damuwa dan ba hakan sukeso ba.
Suna tinkaro bangaren securities din dake gurin suka miqe tsaye kowannensu ba rahama a fuskarsa dan kuwa ko wane yare ma wainnan basa ji sai turanci kawai dan haka basada lokaci ko iya tambayar komai.
Kokarin isowa sukeyi ba tsammani sukaji Wata irin azabar data zubar da su qasa tana ratsa kwakwalwansu wadda tama kasa daukan azabar.
Fetto ce ta iya juyowa taga bayin a zube qasa gabaki dayansu jini a kafafunsa sbd harbin da akaiwa gefen kafarsu batareda ta ratsa qashinsu ba.
Juyawa taji idanuwanta da kanta sunyi sakon dayake hannunta yana faduwa qasa ta dago komai na jikinta na masifar rawar mummunan firgita da tashin hankali batasan lokacinda ta zube ba zata fasa Ihun hankalinta dayake kokarin barin jikinta ganin meya samu bayin Bayan.
Wata irin damqa akai mata tamkar daurin kasar da zaa yanka akai mata tareda soka mata wata allurar data sumar da ita aka bar gurin da ita Sauran bayin ma sbd Hana hayaniya tashi a kofar bangaren na Ammin daukansu akai aka aika su clinic din cikin masarauta suna barin gurin gabaki daya tareda daukan sakon suka kaiwa aleey Wanda bai Bari ya isa ga NUAB ba ya kona sa suka cigaba da shaaninsu tsit kake ji.
Kadir ne ya iso gefen sultan a cikin Daren ya rankwafo cikin nutsuwa ya sanar masa abinda ya faru din.
Numfashi Mara sauti sultan ya sake yana dago manyan idanuwansa daga abinda yake karantawa a Wani file ya bude baki Kai tsaye yace a sake aika Wani sakon Kai tsaye a gurin tenya ta tabbatarda an fara shirin imebētin ASIM din a gobe hakama a hada tareda sabuwar takardar auren NUAB din akaiwa mahaifiyarsa.
Sabuwar takarda kadir ya fitar wadda a cikin Daren ta isa bangaren wishmah batareda sanin Bangaren NUAB ba.
Isowan sakon Wanda ya saka Ayanah zubawa takardar idanuwanta da tsananin yanayin da takasa gane wa kawai dai tasan tana farin cikin auren yar Zuhrah da NUAB dinta Wanda take Jin ma a gaggauce take son Ayi auren dan haka cikin godia da farin ciki ta amsa sakon.
Tenya ma cikeda mamaki take kallan nata sakon Wanda ya sakata shiga wasi wasin Kai tsaye menene dalilin ASIM na buqatan imebetin kuma shine ya zabeta da kansa.
Maa sakinah dake fitowa daki kallan tenya tayi tareda kallan takarda hannunta wadda idonsa suka sauka Kai tsaye Akan abinda sakon yake isarwa da sunan Bahar. #MAMUH
HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070
Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laoualiHAYATEEM Mamuhgee
82 Kasa yadda da abinda idanuwanta Maa sakinah tayi sbd kanta dataji yana Neman juyewa ta zagayo ta gaban tenya din tana sake tabbatarda abinda yake gani a rubuce ta bude Bakinta da Wani irin sauti tace
‘Wace Bahar din ce zaa bawa ASIM a matsayin imebeti?
Da mamaki tenya ta dago ta kalli sakinah tareda cewa
‘Wace baiwar ce Bahar? A wane bangare take? Anan bangaren take ne aka aiko mun sakon anan kokuwa ma tana ina ne ni Bansaniba ma’
Sakinah datake kasa yadda ga bugun zuciyarta na mugun tsananta harbawa da karfi tareda Wani irin tsoro me girman gaske sbd batama San tayaya wannan Masifar ta qullo ta bullo ba,
Wani faduwan gaban ta sake ji tana tinawa da Bahar tayi aiki a bangaren ASIM din Wanda sai yanzu taje dawo da tinanin Kai tsaye shine ya buqaceta dasu naima da komawa bangarensa aiki.
Kallanta tenya keyi sosai da kyau ganin yanda zufa yafara tsiyayo mata tana shiga tinanin datake sake shigar da ita tinani da zullumi itama.
Kasa cewa komai Maa sakina tayi ta bar gurin ta nufi dakinta zufanta na sake tsananta tareda tashin hankalinta sbd bata San wane yaqin tashin duniya ne wannan zaayi ba ace matar da igiyoyin auren NUAB suke kanta itace dan uwansa yake so a matsayin imebeti,
Tayaya wannan muguwar kwamacalar zata fara? Tayaya ma zata fara zuwa isar da wannan mugun sakon da zai Yadu zuwa safe kuma babu Wanda duk duniya ya isa ya Hana hakan tinda har sultan ya Riga ya saka hannu babu abinda zai Haba Ayi hakan.
Wani nauyi kirjinta yayi me tsananin gaske ta fara kaida kawo tsakiyar dakinta tana Jin har numfashinta yana daukewa sbd matiqar aka fara shirinta aka fara wanketa da ruwan lallen dazai wanketa tas to ta tabbata dai ta ASIM ce Wanda ko ita matiqar NUAB ya Bari akaiwa Bahar dinta hakan batajin zata iya yafe masa wannan laifin har abada dan kuwa ba amanarta ce ita kadai ba Bahar din shine ma asalin Wanda amanar tata taje hannunsa.
Tenya ajiye tata takardar sakon tayi sbd sai gobe amma dai a cikin Daren ta aika sakon a shirya bangaren wanke imebetin da tsiminta tareda wanketa a inda sai kamanninta sun sauya sbd yanda zata koma,
Farin cikin Dayan sakon tafara tareda Leylah cikin farin ciki me yawa da tsananin gaske,
Ayanah ma datake cikin tinanika da saka ido sosai Akan sauyin datake gani a tattare da Sakinah bawai dan zata cutatar da ita ba sedai tana ganin kaman akwai abinda sakinah take boye mata na damuwa ayanzu dan koyaushe bata iya hada ido sosai da ita kaman baya hakama gabaki daya hankalinta yana kan sabuwar baiwar datake tsananin son sake gani Akan abu biyu datake son sake gani da ji akanta amma ayanzu farin ciki mai tsananin gaske ta samu kanta na auren Wanda shine zai hadata da yar uwarta Rabin jikinta da sukai shekaru masu yawan gaske basu hadu ba,
Tsananin farin cikinta na ganin Zuhrah ne, Zata ganta zata kalleta a gabanta koda kuwa basu furta su yan uwa bane zasu kasance a gaban juna a matsayin sirikan da zasu hada iri zasu hada zuria yayansu zasu auri juna zumuncinsu da suka rasa sbd rashin yanci zai dawo daga karshe zata rungume yar uwarta da zuciyanta da ruhinta suke tsananin buqata,
Wannan sune babban abinda ya saka farin cikin auren yake dake kame kowane saqo na zuciyarta da gangar jikinta dan haka Kai tsaye takejin tamkar tafi kowa matsuwa da Ayi auren.
Leylah kuwa Jin tayi farin cikinta yana danne baqin cikin datake cikinsa na Bahar da NUAB amma a yanzu sassauci da farin ciki take jin zuciyarta fes.
Maa sakinah kuwa kallan lokacin Daren takeyi tana Jin zuciyarta na sake tsinkewa da tashin hankali,
Bahar take tsananin son gani a lokacin sbd tafara ji daga gareta ko akwai maganar data taba shiga tsakaninta da ASIM hakama taga halinda take ciki sbd matiqar sakon ya kai bangaren NUAB a Daren to batajin akwai Wanda Zai iya rintsawa kaf masarautar amma koina tsit takeji dan haka take saka ran sakon bai isa can ba.
Zulluminta na qaruwa tana sake kallan Agogo tana danne zuciyarta Akan ta jira safiya waye sbd yanzu dare yayi,
Haka dare ya fara ratsowa tana Zaune daram a kujera ta kasa motsawa bare kwanciya sbd kowane lokacin Jin takeyi yaqi Zai iya narkewa a masarautar dan haka hankalinta yake tashi sbd ita Bahar din kadai takeji,
Daqyar taga gari ya fara haske dan haka ta fito ta fice Kai tsaye batareda kowa ya tashi ba ta nufi bangaren NUAB.
Tin daga nesa ta fahimci sabbin da qarin securities dinsa masu yawa ya qaru duk da ya halinta baya a tsaye guri daya Kai tsaye kofa suka bude mata ta shige Bayan ta gama ware ido a cikinsu bataga alamar zancen ya iso bangaren ba dan haka tana sako Kai makeken lafiyayyan palon Kai tsaye dakin Bahar din ta nufa ta budesa ta fada batareda tinanin komai ba.
Ko data shiga Bahar din na Zaune Akan daddumar datai sallar asuba bata tashi ba tayi shiru ta zubawa gabanta idanuwanta da sukai jajir sbd kukan kadaici da kewan mahaifinta ta kwana tanayi Wanda ya saka fuskarta kumbura sosai.
Shigowan Maa ya sakata dagowa a natse cikin sanyi tana ganin itace wasu hawaye masu tsananin dumi suna gangaro mata ta miqe tsaye tana qasa da kanta cikeda sanyin jiki sbd jinta takeyi tamkar a kejin da babu iska ko kadan sbd gabaki daya ko hasken rana bata sake gani ba tinda ta shigo bangaren.
Kama hannunta Maa sakinah tayi cikin nutsuwa ta jata zuwa bakin sofa suka zauna ta dan sake kama hannunta cikin kulawa da tausasa harshe tareda boye damuwan datazo da ita tace
‘Bahar ba nace ki rage yawan kukan nan ba?? Baida amfani zaki kamu da wata ciwon idan Kina yawan kukan nan ki Dena’
Wasu hawayen ne suka ciko idanuwanta amma basu gangaro ba ta dago kyawawan idanuwanta zatai magana aka bude dakin Kai tsaye a natse Wanda ya sakata dauke kallanta daga kofar wasu hawayen masu tsananin baqin ciki suna gangaro mata ta fasa wani sabon siririn kuka a hankali zuciyarta na cikewa da baqin cikin samun kanta a rayuwar da Sam bazata iya ba da kuma samun Wanda take ganin asalin asali baisan menene hankali ba,
Maa sakinah cikin nutsuwa ta juya sedai batasan lokacinda ta dawo da fuskarta ba cikin wata irin rikicewa da kunya da takaicin kasa riqe kanta datai tazo bangaren a daidai wannan lokacin.
Farin wandon bacci ne a jikinsa dogo har qasa amma babu Riga a jikin nasa hakama wandon bai hau daman cikinsa da kyau ba iya inda qugunsa ya fara ya tsaya Ana ganin tambarin sunan farin tomford tight short din dayake jikinsa ta saman Wanda Zai iya saka mata da yawa rikicewan ganinsa a hakan,
Gashin kansa me tsayi ne daure da qaramin black Band a tsakiyar kansa bai Wani kamu ba sosai fatar jikinsa sai daukan ido takeyi,
Akan kunnuwansa dake bacci yaji shigowan mutum palon dan hakane ya fito kuma Kai tsaye nan ya bude dan dubawa sbd ya fahimci yarinyar na tasting din patience nasa bai tsammanin ganin Maa sakinah ba dan haka dakatawa tayi daya kofar tareda bude bakinsa ya gaidata ta amsa batareda ta juyoba duk a rikice sbd ta kasa iya juyowa kallansa a hakan.
Ko bahar din bai kalla ba ya juya yabar dakin yana kallan time a agogon dayake palon ya koma bedroom dinsa.
Maa sakinah kasa magana tayi sukai shiru dukkaninsu na tsawon mintina kafin Maa sakinah tayi karfin halin fidda takardar data dauko tazo da ita ta budewa Bahar din tace
‘Bahar akwai wata doguwar magana ne a tsakaninki da Li’ul ASIM?
Numfashi Bahar ta sauke a sanyaye ta girgiza Kai,
‘Kinsan takardar menene wannan Bahar? Abinda yasa na fara tambayar ki wannan takardar daga sultan ta fito dauke da sunanki da sunan Li’ul ASIM an zartar da hukuncin basa ke a matsayin imebētinsa…..
Cak hawayen Bahar din suka tsaya daga tsiyaya ta dago ta kalli Maa sakinah cikin wani irin sabon mamakin da bata taba shigaba.
Takardar ta kalla da idanuwanta tana kokarin karanta abinda yake rubuce amma ganinta ya kasa zama daidai ta sake kallan Maa sakinah tace
‘Maa dan Allah zan koma GHAZ bazan iya rayuwa anan ba dan Allah Inason komawa’
Cikin sabon nauyin daya danne kirjin sakinah ta girgiza Kai idonta yana ja tace
‘Bahar bazaki taba komawaba a yanzu sbd akwai aure a kanki Wanda babu Wanda ya San dashi hakama yanzu gashi Kina a matsayin imebetin ASIM Wanda kinma riga kin zama a rubuce dan haka babu abinda zai fidda ki BOYEM kuma matiqar dai a raye kikeso fitar’
Girgiza Kai Bahar tayi tana jin jikinta yana daukan zafi tace
‘Maa babu ko daya a cikin biyun danake so auren da imebetin bazan iya rayuwa anan ba’
Dakatar da ita Maa sakinah tayi sbd da alama zancen bai iso nan ba dan haka bata fatan ya iso tana nan dan haka Miqewa tayi sbd maida takardar kafin ma asan ta dauko hakama ko yayane hankalinta ya kwanta datasan babu maganar komai data hada Bahar dashi ASIM din data danganci kowace kalmar soyayya wadda zata iya zama cikin matsalar hakan amma tinda babu taji dan sauki zata jira taga idan NUAB zai iya kubutar da Bahar din daga wannan mummunan kaddarar dake shirin hawanta ga kuma nasa auren na biyu dake shirin hawa kansa shima.
Miqewa tayi zata fice Bahar tayi saurin miqewa tana gyara babbar rufar sallar dake jikinta tana biyota a baya.
Wucewa Maa sakinah tayi batama San Bahar din na bayanta ba saida suka Kai tsakiyar palon Maa ta juyo tana kallanta da mamaki tareda rage sautinta tace
‘Bahar ki koma zamanki a nan yanzu shine babban tsaron da zaki samu da kariyar da kaf BOYEM sultan ne kadai ya isa ya fiddo ki amma bayanshi babu Wanda ya isa.
Girgiza Kai Bahar tayi tana cewa
‘Bazan iya zama ba ni kadai Maa dan Allah mu tafi tare’
Girgiza Kai Maa din ke kokarin yi Bahar tayi saurin yin gaba cikeda tsananin damuwan bazata iya tsayawaba ma bare ta zauna idanuwanta na sake cikowa da hawaye. #MAMUH
HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070
Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laoualiHAYATEEM Mamuhgee
83 Fitowa Bahar tayi da sauri daga kofar palon tana kokarin qarasa fitowa securities suka miqe gabaki dayansu suna tabbatarda tsare kowace kofar batareda sun dauke idanuwansu akanta ba,
Jin tayi kaman zata Dora hannu akai ta zunduma Ihun da ko zuciyarta zata samu sassaucin abinda take ji ta juyo ta kalli Maa tareda fara tsiyayar hawaye ta riqeta da dan karfi tana cewa
‘Maa kada ki barni anan dan Allah ki tafi dani Zuciyana fashewa zeyi dan Allah Maa’
Yar hayaniyar ce ta fidda aleey Wanda kunnuwansu suke sharp shima Akan kowace motsin bangaren daga waje.
Ganin Bahar ya sakasa qarasowa yana dauke idanuwansa daga kallanta shima ya bude Baki ya gaida Maa kafin ya gaida Bahar din wadda batama jin komai tsananin quncin barin bangaren take ji.
Waya Aleey ya fidda ya saka kiran NUAB yana dauka cikin baccin daya koma take aleey ya sanar masa abinda yake faruwa a kofar na Bahar ta tsaya Akan saita bi Maa.
Katse wayar yayi tareda saukowa gadonsa ya fito wannan Karan babu komai a jikinsa Bayan tight short din Wanda ya saka lafiyayyar fatar jikinsa bayyana sosai tana Wani daukan ido tareda kakkarfan jikinsa A yanda yake yana bacci a hakan ya fito babu abinda ya damesa yana fitowa dukkaninsu suka sauke Kai sbd girmamawa suna gaidasa.
Akan Bahar idanuwansa masu tada tsigan jiki a daidai lokacin sbd baccin daya taso suka sauka tana jin saukan idanuwansa akanta taqi juyowa saima sake riqe hannun Maa tayi wadda itama bata juyoba tana cigaba da tsiyayo hawaye.
Kallan seconds yayi mata batareda yace komai ba kafin ya kalli aleey yace a barta ta tafi kawai sbd yasan bama Wanda Zai iya komai akanta.
Bai bude Baki ya furta ba kallan aleey kawai yayi ya Juya Wanda aleey yasan me hakan ke nufi ya kalli securities yace su bari ta tafi kawai.
Bada hanya sukai suna bata hakurin da bataji bata gani fatarta kawai tabar gurin.
Suna barin bangaren ta sake riqe hannun Maa da dan karfi tana goge hawayenta da hannu daya zuciyarta na dan samun sassauci.
Suna isa bangaren wishmah Kai tsaye daki suka wuce Bahar na shiga ta sauke ajiyan zuciya me sanyi a boye tana Zaunawa kan sofa ta dafe goshinta tana rufe ido tinaninta na dawowa damuwa da tsananin jin tsanar nan din yana sake shigarta da gaske takeyi ANJOM take so tafi son can Akan nan din.
Maa sakinah toilet ta shiga tana fitowa ta samu ta dan kwanta dan kanta ciwo yake itama sosai sbd bata rintsa ba kuma a yanzu ma da Bahar din ta biyota tsoronta da zulluminta yafi qaruwa.
Baccin da bata tsammata bane ya saceta me karfi Wanda Bahar ma data dade Zaune shiru cikin damuwa Salmah na shigowa gyaran dakin da zata fita sai kawai ta miqe a sanyaye da babbar doguwar Riga a jikinta ta bita zuwa kitchen cikinsu ko zata samu dan sassaucin damuwan datake ciki.
Karfe goma na safe NUAB ya da securities dinsa suka bar cikin masarauta zuwa Wani business da shine dole zaiyi sealin nasa hankalinsa kwance ya tafi sbd yasan koma me ASIM zeyi hukuncin da zai masa ko mahaifinsa bazai qwacesaba dan haka ya tafi ba shakkar komai.