Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee - Chapter 4
Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 4: Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 4. Wuqar da kawai aka fizge fatar wuyan tareda…
4,465 words
Wuqar da kawai aka fizge fatar wuyan tareda jijiyan Asamah kaman wucewan iska Wanda ya saka jinin bartsi sosai ta kalla a hannun Wanda yayi aikin batareda bata lokacin su ba sbd zabinta ne.
Wurgar da Abaas sukai a gaban yan uwansa da gawar Asamah dake gangaro da jini,
Mutuwan Zaune dukkaninsu sukai tareda dauke wuta sbd babu Wanda a jikinsu jinin bai bartsanwa ba,
Abaas daya kasa matsawa yana kwance a inda suka jehosa kaman mataciyar dabba rufe idanuwansa yayi hawaye na zubowa idanuwansa yana kasa motsawa.
Babu Wanda yace musu komai haka suka juya suka bar gurin shugaban cikinsu ma dago murya yace
‘Kusra bata tada Alkawari idan tayi dan haka ku tafi an cika mata burinta ko bata raye amma wannan damar itace ta cika Alkawari idan mun sake haduwa daku kun zamo namu’
Har suka bace wa gurin babu Wanda ya motsa a cikinsu Ayanah sbd babu wanda ya dawo hayyacinsa,
Sakinah dake Bayan Ayanah motsawa tayi ahankali tareda qarasowa gaban gawar Asamah ta saka hannunta yana rawa sosai ta shafe idanuwanta suka rufe tana fasa kuka mai tsima zuciya itama.
A lokacinne Zuhrah ta fasa kukan itama me karfin gaske tana fadawa jikin Ayanah.
Nurat da bata hayyacinta miqewa tayi da sauri a zare tana bin hanyar daji kafafunta na hardewa tana qwala kiran sunan Abaansu.
Ganin tana Neman nisa ne ya saka Abaas miqewa da gudu yana kamota ya rungume yana kiran sunanta da karfi da fashewa da sabon kuka.
A lokacin ne Ayanah da Zuhrah suka taso suma suna riqeta tana kwacewa cikin wani irin ihu na gushewan hankali Wanda ya saka yan uwanta suna fasa sabon kuka me taba zuciya dukkaninsu suna qara riqeta sbd zaucewa takeyi. Sakinah ma kukan take fasawa itama tana rungume dukansu.
Ihun Nurat ke fasawa tana fizge fizge tana yakushin kanta da karfi tana kwala kiran Abaa dajin na amsawa sosai.
Qin Sakinta sukai suna sake saka karfinsu su duka suna riqeta sosai kukansu na qaruwa.
Sun jima a cikin wannan sabon tashin hankalin kafin Nurat din ta zube qasa suma suka zube gabaki dayansu har lokacin basu iya Sakinta ba sbd kada ta gudu.
Shiru sukai sai ajiyan zuciyar kukansu dake sauka akai akai na tsawon lokaci shima kafin suka miqe hannun Zuhrah na riqe dana Nurat din suka bar gurin.
Gabas suka kalla suka sake miqa suna kutsawa hanya batareda sunsan inda suka dosa ba.
Yunwa da azaba ce kawai a cike da rayuwarsu a lokacin tareda mafi girman baqin ciki da qunci,
Wuni suka sake shudewa suna zagayen dajin sun rasa hanyar fita bare komawa ANJOM duk da sunsan garin ya zama na kusra yanzu.
Cikin dare sosai suka sake samun wani guri suka zauna tareda maqale da junansu suka dunqule guri daya dukkaninsu suna cikin jikin Ayanah wadda ita kuma sakinah ce ta bata kariya ta bayanta ta hanyar zauna wa ta jingina da bayanta.
Shiru sukai ko dogon numfashin basa yi sbd tsoro da fargaba tareda damuwa.
Darensu na jiya ta tina Wanda suke tareda Asamah ta basu kariya da kulawa a lokacinda suka yanke rahama daga duk wata samun kulawa koman kankantarta,
Maganar Asamah datai musu Daren jiyan ta tina a lokacinda ta Shafa fuskan Abaas.
‘Ayanah akwai rayuwa me tsauri da qalubale a gabanmu dan haka idan matiqar muna son kada a rabamu da Abaas daga cikinmu to tabbas muna buqatan maidasa mace sbd qalubalen da zamu fuskanta zaa iya kaiwa matakin da zaa rabamu sbd shi namiji ne mu kuma mata dan haka sbd Kaucewa hakan muna buqatan boye jinsinsa sbd tseratar da rayuwarsa tareda tabbacin zamansa a tareda ku kada komai ya rabaku’ #MAMUH #SLAVERY #HISTORICAL #ROYALTY #BEST LOVE #BEST SISTERS #BOYEM #NUAB ALMAZ BOYEM
HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070
Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali
*_HAYATEEM_* Mamuhgee
9
*_PRIME SCENT_* 08103155915 Shin Kina neman duniyar kamshi ta turarukan wutan da in kin kunna zaki ji ki kamar a Royal palace din larabawa? Ko kuma kina neman wanda zaki kunna ya kaiki garden full of vibrant, mind & soul soothing fresh scents? Ko kuwa wanda zai baki rich and luxurious scent na elites? Ko kuwa kina neman qamshi mai sauke fushi da gajiyar da oga ya kwaso ne? Are you looking for qamshin da duk inda kika shiga sai kin janyo attention din mutane, ko kuwa wanda in an matso kusa dake sai an lumshe ido tare da sauke ajiyar zuciya na jin dadi da kwanciyar hankali tare da samun nutsuwa? Hajiya ta albishirinki! Ga PRIME SCENT Duniyar kamshin da babu kamarsa, Duniyar kamshin da ko kin bada kayanki ko curtains naki wanki baza su Dena bada kamshi me nutsuwa da dadin shaqa ba, PRIME SCENT sune kankat ba na biyunsu. 08103155915 ********
Rintse idanuwanta Ayanah tayi ahankali tana sake rungumesa jikinta tareda Sauran kannan nata sbd boye jinsinsa da tabbas zatai a yanzu har zuwa lokacinda bata sani ba nakasta rayuwansa ne nakasa me munin da babu ranar gyara,
Jin takeyi kaman bazata iya hakan ba amma kuma bazata iya barin a rabasu ba har abada sbd suna rabuwa babu Wanda zai iya rayuwa a cikinsu batareda juna ba,
Sake qanqamesu tayi a matiqar sanyaye tana jin da gaske yanzu kam ta zama uwa, Ta zama uwar da batasan komaiba sai yayanta,su kadai ne rayuwarta da duniyarta.
Suna gurin a maqale guri daya kaman ba mutane ba har suka ga duhu ya fara dan ragewa alaman asuba tayi harta gota,
Basu saki juna ba saida gari ya qara haske sosai suna iya ganin koina da komai tukuna suka warware juna,
Ayanah ce ta umarce suyi sallah a yanda suke sbd basuda gurin tsafta ce jikinsu dan babu ruwa babu komai qasar ba babu sosai hakukuwane suka fi yawa sun cike koina.
Shiru sukai tsawon lokaci babu magana Bare motsawa Bayan sunyi sallolin dake kansu.
Shiru tsit babu ko kukan kowace irin dabba a dajin Wanda hakan alama ce ta dajin baida kyau sbd kukan dabbobi ko tsuntsaye yana rage tsoron daji.
Rana ce ta fara ketowa me tsananin zafi suna Zaune a gurin har lokacin dan haka Ayanah ta juyo ahankali ta fara kallan Nurat dake kwance jikin Zuhrah tana maganganu kadan kadan har lokacin na zautuwa tana ambatar sunan Amma da Abaa.
Lumshe jajayen idanuwanta da suka bushe qayau tayi suna mata wani irin radadi tana dan Hadiye wani Numfashi me cikeda radadi shima kafin ta sunkuyar da kanta tana kasa kallan Abaas Wanda shi da Zuhrah harma da sakinah ita suke kalla sbd fahimtar akwai abinda takeson fada amma ta kasa.
Hanyar da zasu bi ta dago ta kalla idanuwanta na cikowa da hawaye sbd batasan rayuwar da zasu Tatar ba a hanyar idan suka qarasa Binta Wanda tasan duk inda suke basa nesa da ruwa ko lambum wani gari sbd sanyin da suka kwana yana fesowa na alaman hakan Shiyasa koda garin ya waye kaman zasu sanqare sbd sanyi.
Dawo da fuskanta tayi amma ta kasa kallan Abaas Wanda ya tsareta da ido jikinsa na tsananin sanyi hannunsa na rawa ya riqe gwiwowinsa da hannuwansa dake rawar sbd take ya gane abinda yake ranta amma zuciyarta na tareda sbd shima da abin ya kwana a ransa tsoro da fargaba me tsananin yanda zaa iya rabasa da yan uwansa amma kuma duk da baida shekaru amma kasancewansa namijin GHAZ daya bayan mahaifinsa sauyasa zuwa mace shine mafi girman qasqanci da zuriar GHAZ suka samu ko Bayan ransu duka tin daga kakanni,
Shi rayuwarsa ta mutu ne daga lokacinda zai koma mace, Ya rasa darajarsa,ya rasa sunansa,ya rasa yancinsa da damarsa ta zama GHAZ na har abada sbd yana cikin tsatsauran al’adarsu matiqar namiji ya zama tamkar mace kokuma zamowa mace ko shigar danganci mace to har abada bazai taba karban gadon matsayin shugabancin Ahalin GHAZ ba bare ANJOM.
Rawa jikinsa yafara cikeda wani irin radadi da ciwon daya saka idanuwansa cikowa da hawaye masu Zafin gaske yana qanqame kafafunsa,
Zuhrah data fahimci hakan kallan Ayanah dake sauke kai itama hawaye na gangaro mata da tsananin tsoro da faraba tace
‘Ayanah saimunyi hakan zamu rayu tareda shi, Bazan iya rayuwa ba idan aka rabamu dashi, Ayanah koma menene zamuyi masa shi dan rayuwa tareda shi koda hakan na nufin komawansa mace har ranar da Allah zai dauki rayuwarsa ko tamu…
Kuka ta fasa mai sanyi tana cewa
‘AMMA kada kice bazaki iya ba’
Wani irin kuka me karfi Ayanah da Abaas din suka fashe dashi a lokaci daya kowannesu na saka kansa cikin kafafunsa sbd AMMAN data Ambaci Ayanah dashi Wanda daga lokacin ta tabbatarda ita ta gama karban Ayanah a matsayin Uwa duk da ba shekaru masu tsayi tsakaninsu amma dai ta Riga ta maye musu gurbin Ammah kaman yanda su Abaa ke cewa ita uwarsu sbd tsanani son da uwa kewa ‘da take musu suma suna mata tsananin son fa ‘da kewa uwa.
Sakinah ma kuka takeyi sosai sbd rayuwarsa me suna da Abaas zai rasa daga yau shikenan.
Kuka sukeyi sosai a tsakaninsu harda Nurat da bata cikakken hayyacinta kukan takeyi sosai cikeda tausayi me karya zuciya.
Tsananin Zafin rana ke dukansu ga kuka da suka kasa Denawa sai hakan ya fara raunana lafiyansu dan haka daqyar sukai shiru Ayanah sai a lokacin ta dago ta kalli Abaas Wanda kansa ke qasa har qasa lokacin burinsa na zamowa namiji,dan uwa kuma uba dayake fatan wata rana zuriarsa data Ayanah ko daya daga cikin yan uwansa yana narkewa tareda bin iska a yau,zai mutu batareda samun wannan cikar burinba.
Sakina ce cikin tsananin kukan da tasan illa da nakasun da rayuwarsa zata samu daga yau ta saka hannu tana zare ‘yan kunnan azurfan dasuke kunnenta duka guda biyu ta kamo hannun Ayanah dake kuka sosai ta saka mata su ahankali tana Juyawa baya jikinta a sanyaye sbd ita har yanzu baiwar su ce bazata kalla yanda zaa yaga qimar uwayen gidanta ba.
Qanqame abin kunnayen Ayanah tayi a hannunta tana dauke kanta daga kallansu su duka kukanta na Neman tsananta amma dole zata aikatawa dan uwanta hakan.
Zuhrah ce da itama kukan takeyi ta miqe tsaye tareda Kama hannun Ayanah ta kasa maganar da zatai sbd kukan dake zuwar mata sabo mai ciwo dan haka juyawa tayi itama tana Dora hannunta a kirjinta dake ciwo da nauyi.
Rarrafowa Ayanah tayi cikin mummunan gaban Abaas din tareda daga hannuwanta dake rawa sosai takai tafukan hannayenta fuskansa ta tallafo ta kallesa ya Lumshe idanuwansa yana kasa barin taga tsananin rauni da baqin ciki tareda quncin dayake cikinsu sbd kada ya qarasa karya zuciyarta da gangar jikinta.
Bakinta takai kan gefen fuskansa ta sumbacesa hawaye na gangaro mata kafin ta sake dorawa kan goshinsa ta sumbacesa hawayenta na diga kan goshin nasa.
Zuhrah ma cikin karfin Hali tana danne zuciyarta ta juyo ta durqusa gabansa ta Kama hannuwansa biyu ta sumbacesu duka kafin ta sumbaci tsakiyar kansa da gashinsa me tsayi kaman mace yake daure har lokacin.
Tafin hannu Ayanah ta bude ta kalli yan kunnayen kafin ta daga ahankali tareda Kama kunnansa,
Bude idanuwansa yayi ya sauke Akan fuskan Ayanah din wadda cikin idanuwansa take kallo tana masa kallan tsananin kaunar dake nuni da har abada idan kowa zai gujesa su suna tareda dashi har mutuwa sbd su a gurinsu rasa kowace darajarsa ba ta ‘da namiji.
Baice komaiba Bayan rufe idanuwansa da yayi ahankali sbd su kadai yake buqata a rayuwarsa daman kuma idan yana tareda su shikenan zai iya jure komai.
Hannunta ta Dora a kunnansa cikin radadin zuciya ta huda kunnan nasa da karfin da na karfin hali ne,
Zuhrah kaman a zuciyarta haka taji hujin kunnan shi kuwa ko motsawa beyiba sai wasu hawayen da bana radadi bane suka gangaro masa.
Haka Ayanah ta huda Dayan kunnan tana bar masa yan kunnayen a kunnuwansa.
Tallafe fuskansa ta sake yi da hannuwanta tana kallan idanuwansa dake rufe yana riqe kukansa me tsanani dake zuwar masa.
Itama kokarin riqe nata takeyi har saida Zuhrah ta saka hannunta cikin riqe nata kukan itama ta zare daurin gashinsa take gashin ya sauka har kafadarsa,
Wani irin kuka me karfi da gunji suka sake a tareda dukkaninsu suna rungumesa.
Har lokacin Sakinah bata juyoba itama kuka takeyi sosai a yanda take,
Nurat ma kukan ta fasa tana fadawa cikinsu tareda ambatar Ayanah da AMMA itama.
Rigar Zuhrah me dan adon Kayan mata suka zare aka saka masa tasa kuma Zuhrah din ta saka.
Sakinah ce ta matsa kadan gaba ta Debo wani ganye shar ta kawo Ayanah ce ta murza ganyen da hannuwanta biyu ta goga a fuskan Abaas din Wanda bazai bazai taba barin gashi ya fito a fuskansa ba.
Sake rungumesa Ayanah tayi suka sake samun Yar nutsuwa da dangana kafin suka miqe suna kama hannuwan juna suka bi hanya ahankali cikin galabaita Wanda babu ta yanda zaka zan akwai namiji a cikinsu..
Koda rana ta fadi babu me iya tsayuwa sosai a cikinsu sbd tafiya da azaba, Kafafunsu dukansu babu Wanda bai fashe ba,
Kaman a mafarki suka fara hango ruwa me yawan gaske yake dukkaninsu suka Ji sun samu dan kuzarin daya qare musu.
Ruwan suka nufa suna jin maqoshi da jininsu na sake qafewa.
Ana magrib suka isa ruwan Wanda da rarrafe dukkaninsu suka qaraso sbd qarewar karfi gabaki daya, Nurat bata iya qarasowa ba sbd ranta dake gap da fita dan haka Abaas ne yayi saurin diban ruwan da hannuwansa biyu yana kawo wa inda take yana bata a baki batareda damuwa sa qazantar dake ruwan ba.
Daqyar yake takawa yana kai mata ruwa yana zuba mata a baki har shima ya gaza ya fadi yana zubewa a gurin. #MAMUH
HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070
Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali08131349365
*_HAYATEEM_* Mamuhgee
10
*_PRIME SCENT_* 08103155915 Shin Kina neman duniyar kamshi ta turarukan wutan da in kin kunna zaki ji ki kamar a Royal palace din larabawa? Ko kuma kina neman wanda zaki kunna ya kaiki garden full of vibrant, mind & soul soothing fresh scents? Ko kuwa wanda zai baki rich and luxurious scent na elites? Ko kuwa kina neman qamshi mai sauke fushi da gajiyar da oga ya kwaso ne? Are you looking for qamshin da duk inda kika shiga sai kin janyo attention din mutane, ko kuwa wanda in an matso kusa dake sai an lumshe ido tare da sauke ajiyar zuciya na jin dadi da kwanciyar hankali tare da samun nutsuwa? Hajiya ta albishirinki! Ga PRIME SCENT Duniyar kamshin da babu kamarsa, Duniyar kamshin da ko kin bada kayanki ko curtains naki wanki baza su Dena bada kamshi me nutsuwa da dadin shaqa ba, PRIME SCENT sune kankat ba na biyunsu. 08103155915 ********
Ayanah datai tsananin laushi itama ce ta qaraso gurinsa da rarrafe cikin sauri tana kokarin kamo sa amma hannuwanta rawa sukeyi sosai gashi bata da kuzari sai kuma ta kasa iya Dena kokarin rungumosa jikinta idanuwanta da sukai surfi sosai suna kasa ko hawaye.
Sakinah ce da itama taje Numfashi daqyar ta matso ta fara Debo ruwan itama a hannunta tana tahowa tana zubewa a bakinsa suka samu yasha sosai numfashin sa ya fara daidaita ya rufe idanuwa yana lashe lips dinsa da suka bushe qayau harsun fara tsagewa.
Ayanah ma Sakinar ce ta kawo ruwan ta ringa bata ta dan samu karfi da kuzari itama tana lashe bakinta daya bushe ya tsatsage.
Acan bakin ruwan sakinah tasha ruwan sosai itama kafin ta zube a gurin a kwanta tana sauke Numfashi bakinta itama yana samun sassaucin azabar yankewan bushewa.
Zuhrah kuwa daman tana bakin ruwan tin dazi a kife Jin takeyi kaman ta fada ruwan ta sanyaye jikinta da bakinta da suka bushe har sun yayyanke musamman kafafunsu da basuda kyalla sun fashe kace kaca sunyi wata irin Dauda da munin kalla.
Ba iya kafafunsu ne da munin kallo ba sbd Dauda me yawa hadda su sbd dauda ce sosai a jikinsu tareda jinin da sukayo gwagwarmaya dashi daya bushe a jikinsu tin daga kan na Ammansu dama Abaansu da Ayanah ta taba saina Asamah dama Sauran wainda aka kakkashe tin farkon barowansu babu me Kyan gani a cikinsu sbd sun koma wata halittar sbd dauda da kyama.
Dukkaninsu kwance suke a gurin babu Wanda ya motsa Numfashi suke sauke wa a hankali ba kuzari kuma ma idan sun miqe basu San tayaya zasu tsallaka ruwan ba bare dan haka magana ce ta sake zagayawa dajin zasu yi Neman hanyar da zata fiddasu inda ba ruwa su fice daga nahiyar gabaki daya su fada inda garururwa da Jamaa suke.
Shiru sukai kowa idanuwansa na kasa qaqaro hawayen tashin hankalin inda zasu sake komawa dan Neman hanya.
Kasa tashi kowannensu yayi a gurin anan suka kwana kwance gaban ruwan kowa a inda yake zube anan ya kwana sai asuba suka dan iya tashi suka hade guri daya suka dunqule sbd tsananin sanyin ruwan dayake ratsa su.
Daqyar suka iya sallah Bayan gari yayi haske suka sake Zaunawa guri daya a hade kaman kashin awaki,
Shiru sukai suna tinanin yanda zasu sake komawa su kutsa cikin dajin Wanda basu San ranar fitar sa ba,
Tsananin tsoronsu haduwa da Kusra da suke cikinsa dan haka suke Jin kaman suyita zama bakin ruwan har ransu yabar jikinsu.
Zuhrah da har jikinta ya fara rawa sbd tsananin tsoro da tashin hankali tareda tina azababbiyar tafiyar kallan Ayanah tayi da idanuwanta da sukai ja sosai ta bude baki cikin tsananin tsoro da sallamawa tace
‘Ayanah wannan itace karshen kaddararmu, Mu karbeta kada mu koma dajin nan, Mu fada ruwan nan rayuwarmu tazo Karshe mu huta dan Allah, Bazan iya ba Ayanah, Mutuwar tafi mana biyu Hutu da sauki dan Allah Ayanah mu fada ruwan nan mu tafi mubar duniyar nan wlh bazamu iya ba, Koina bazamu kai ba zamu rasa kanmu dan haka dan Allah mu yankewa kanmu wahala…..
Abaas na Jin hakan yaji zuciyarsa na Aminta da yadda da hakan dan haka Ayanah yake kalla idanuwansa cikeda hawayen rauni da ‘qunci yana Jiran jin tace ta amince da hakan,
Kallansu Ayanah tayi tana jin zuciyarta na yadda da hakan itama sbd tabbas din bazasu iyaba dan haka gwara su mutu anan tin kafin azabar da ukubar tayi yawan da babu iyaka.
Ganin yanayin Ayanah din na itama tana ganin hakan shine zai fi musu yasa Zuhrah Jin dan dadi dan har zuciyarsu gabaki daya sun zabi mutuwar sbd itace hutun karshe da zasu samu a wannan duniyar dan haka miqewa tayi tana Juyawa ta kalli ruwan tana Lumshe idanuwanta zuciyarta cikeda samun nutsuwa ta juya gurin Nurat dake Zaune quri babu alaman tasan komai dayake gudana a rayuwanta yanzu ta durqusa gabanta ta kamo fuskanta da tafukan hannuwanta biyu takai bakinta ta sumbaci gefen fuskanta da gashinta kafin ta hade goshinsu tana cewa
‘Nurat inda su Abaa da Amma suka tafi zamu tafi zamu bar nan bazamu iyaba,ke kin rasa hankalinki bazaki taba gane azabar da zamu shiga ba amma kuma zaki kasance cikin hadari dan haka mu tafi….
Kama hannun Nurat tayi ta miqar da ita ta kalli Abaas ta miqa masa hannu shima ya Kama ya miqe tsaye,
Ayanah suka tsaya akanta suna kallan da jiranta,
Abaas da Zuhrah din tare suka miqa hannu ta kallesu tana miqa hannunta ta Kama nasu zata miqe Sakinah tayi saurin riqeta tana girgiza mata kai tace
‘Idan kun zabi mutuwa Akan rayuwa zan biku Nima na zabi mutuwar sedai idan kukai hakan sadaukarwar iyayenku dan kawai ku rayu ta zama ta banza, Sadaukarwar Asamah ta zama ta banza itama, Ayanah ki tina su Abaa basu da burin daya wuce ku rayu kota yayane, Ku tsira kota yaya ne, Duka duniyar kowa dake gwagwarmaya yana yi dan cika burin magadansa da magabatansa amma ko kwanaki masu yawa baa yiba zaku kashe kanku sbd kasa rungumar jarabawa.,
Idan har jinin iyayenku ne jinin GHAZ yake yawo a jinin jijiyoyin jikinku to tabbas zakuyi kowace irin gwagwarmaya ku jure ku rayu dan tabbatarda burin iyayenku ya cika kun tsira sun rayu kun samu rayuwa da zaku tina baya ya zama tarihi, Wannan shine ya kamata ya zama sabon Alkwarin jini da duk wani jinin GHAZ zai taso a cikinsa na duk zuriar GHAZ da zasu zo a gaba wato juriya ga dukkanin tsananin rayuwa kowane iri ne ka tsira ka rayu,
Karku manta kune jinin GHAZ na karshe Wanda kuna barin duniya dukkaninku to shikenan jinin GHAZ Yazo Yazo karshe kun shafe a duniya sedai a tarihi idan an ambaceku dan haka Kuyi hakuri Kuyi juriya Kuyi gwagwarmaya kuci gaba da jagorantar GHAZ ku yada zuriar da zata ci gaba da jan sunan GHAZ a duniya.’
Kuka Zuhrah keyi sosai da maganganun da suka shige su amma ita har lokacin tana jin tafi son mutuwar sbd bazata iya rayuwar da dabbobi ma sunfi su yanci da gata da rufin asiri tareda kwanciyan hankaliba,
Kallan Ayanah dake kuka sosai kaman ranta zai fita cikeda da gajiwa take kukan idanuwanta sunyi kumburanda kaman zasu fado su tsiyaye.
Maida kallanta kan Abaas tayi Wanda shima kukan yakeyi sosai hannuwansa na kakkarwa,
Nurat ta juyo itama ta kalla wadda ta koma abar tausayi yanzu sbd bata iya cewa komai zuru tayi da idanuwanta dake bayyanarda tsananin qunci da Neman Hutu na barin duniyar sedai batada tinani na kanta yanzu sai yanda akai da ita.
Itama Zuhrah jin tayi kaman kanta da zuciyarta bazasu dauka ba dan haka ta fara ja da baya tana hawaye.
Miqewa Ayanah tayi batareda tasan tanada Sauran karfinba tayi kan Zuhrah din da sauri sedai Juyawa zuhran tayi tana nufar ruwan da gudu zata fada,
Abaas ne shima yayi kanta da gudu hakama sakinah Ayanah Sakinah kuwa Nurat ta riqe sbd kada itama ta juye ta bisu ta fada ruwan.
Har Zuhrah ta fada ruwan Abaas ya Riga Ayanah isa gareta ya riqota tana fizge wa tana kuka me karfi tana rokonsu su tafi.
Rungumeta Abaas tayi sosai jikinsa yana bude baki cikin karfin Halin dake zuciyarsa data fara bushewa yace
‘Zuhrah zamu jure,zamu jajirce,zamu tsira,zamu rayu insha Allah zaku ma mu sake amsa sunanmu GHAZ wata ran….
Girgiza kai takeyi tana cewa
‘Aa Aa Abaas bazamu sake amsa sunanmu ba har abada gwara mu tafi dan Allah’
Girgiza mata kai yakeyi shima yana sake daurewa kukan dayake zuwar masa
Ayanah ma rungumesu tayi dukansu tana maimaita abinda Abaas ya fada Akan sun rungumi hukuncin ubangiji duk tsananin tsanani zasu jure zasu jajirce zasu rayu a cikin kowane Hali dadi ko wuya.
Kuka Zuhrah keyi sosai tana girgiza kai a hakan haka har suka fito ruwan suna samun guri suka zauna suna yin shiru tsawon lokaci kafin suka kalli juna suka sake daukanwa kansu alkwarin jurewa da rungumar kaddara tareda kasancewa da juna sbd duk masifa da munin rayuwan da zasu fuskanta idan suna tare da juna zasu jure dan rabu wa da junansu shine mafi muni da girman kaddarar da suke tinanin zai samesu Wanda gwara musu mutuwa Akan hakan.
Fitowa rana ya saka suka miqe suna sake cika cikinsu da ruwan sosai suka bar gurin Bayan sun jiqa kayansu sosai da ruwa har suna tsiyaya ta yanda zasu yi tafiya me tsayi basu azabtu da tsananin Zafin rana da kishirwa ba.
Komawa sukai cikin dajin suna kallan hanyar gabas suka miqa suna riqe hannun juna Nurat kuma tana hannun Abaas ya riqe hannunta gam cikin nasa.
Wuni sukai suna tafiya har rana ta fadi duhu yayi suka nema guri suka zauna babu me iya numfashin arziki sbd wahalar yunwa da kishirwa.
Dukkaninsu sunyi galabaitar da baa magana dan haka tinda suka zube a gurin babu Wanda ya sake motsi kaman matacci har gari ya kuma wayewa yayi haske.
Numfashinsu fara Neman gagararsu yakeyi amma a hakan suka tashi suka sake bin hanya suna kasa ko riqe juna wannan Karan,
Wuni suka sake yi suna yawo a dajin batareda ma sun San inda suke jefa kafafunsu ba gashi kaman dajin dayake da wani sirri dan baka iya gane gurin fita..
Kwanaki suka dauka suna ragaita a mummunan dajin Wanda zuwa lokacin tini suka fara cin ganyen duk icen da suka samu Wanda yafara maidasu kaman wasu dabbobi,
Kamanninsu sun sauya daga mutane zuwa wasu kalar, Fatar su ta koma kaman busashiyar dabinon daya fito cikin qasar sahara,
Bakinsu ya bushe ya far fashe jinin dayake fitarwa shi Kansa ya bushe,
Wata irin dauda da qasa tareda qazanta ce kala kala a jikinsu Wanda bushewan da sukai qayau yake rage warin dake tashi a jikinsu,
Zuwa lokacin dukkaninsu sun gama cire rai daga rayuwa harda Sakina kanta me basu kwarin gwiwa wannan Karan mutuwar take fata da son ta dauke su sbd rayuwa dai ta qare musu a inda ko gawarsu basuda me kalla yayi musu fatan rahama sedai tsutsa su cinye namansu iska ya busar da saura sbd ko dabbar da zata cinye namansu a dajin babu. #MAMUH #BEST STORY #ROYALTY #SLAVERY #BEST LOVE #BOYEM
HAYATEEM by Mamuhgee 700 0022419171 AccessBank Maraym Sani gummi 09033181070
Yan Nijar kuma 89825722 Depot my nita Nissaiba laouali_*HAYATEEM*_ Mamuhgee
11
*_PRIME SCENT_* 08103155915 Shin Kina neman duniyar kamshi ta turarukan wutan da in kin kunna zaki ji ki kamar a Royal palace din larabawa? Ko kuma kina neman wanda zaki kunna ya kaiki garden full of vibrant, mind & soul soothing fresh scents? Ko kuwa wanda zai baki rich and luxurious scent na elites? Ko kuwa kina neman qamshi mai sauke fushi da gajiyar da oga ya kwaso ne? Are you looking for qamshin da duk inda kika shiga sai kin janyo attention din mutane, ko kuwa wanda in an matso kusa dake sai an lumshe ido tare da sauke ajiyar zuciya na jin dadi da kwanciyar hankali tare da samun nutsuwa? Hajiya ta albishirinki! Ga PRIME SCENT Duniyar kamshin da babu kamarsa, Duniyar kamshin da ko kin bada kayanki ko curtains naki wanki baza su Dena bada kamshi me nutsuwa da dadin shaqa ba, PRIME SCENT sune kankat ba na biyunsu. 08103155915 ********
Idanuwan Ayanah da suka koma manya sbd gabaki daya naman fuskanta daya tafi babu shi sai qashi zalla Wanda Kana kallanta zaka dauke idonka akanta sbd gabaki dayansu haka suka koma babu Kyan gani sbd babban cin kamannninsu da wanda qwarangwal fata ne da dan abinda baa rasa ba sai Sauran rai dayake jikinsu,
Kallan kannenta dake kwance gefenta dukansu kaman gawar dataqi rami takeson yi amma ganinta yayi Raunin da bata iya gane wa sosai dan haka bushashen hannunta ta motsa daqyar yakai kan fuskan Abaas wanda wasu haqoran wahala kawai ta iya Ji a fuskan tasa wainda sune kadai a tsaye sbd babu komai a fuskan tasa idanuwansa sunyi zurfin data kasa iya tantance ramin ido ne ko kuwa ramin bakinsa dan haka ta sauke wani wahalallen Numfashi daqyar tana taba Zuhrah wadda cikinta ya hade da bayanta ta koma halittar da zata iya firgita qananun yaran gata.