Kenza eBookz

Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee - Chapter 60

Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee - Chapter 60

Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 60: Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 60. Boiled veggies and potatoes ta zuba musu da…

4,387 words

Boiled veggies and potatoes ta zuba musu da kidney sauce dataji zallan kidney din ta zuba musu sai dafaffiyan madaranta da tea dinsa suka ci suka qara da chips kadan dayaji red ketchup suna gamawa ta qarasa shanye madaranta tana barin gurin sbd aleey dazai shigo taji yana waya da NUAB din.

Tana shigewa da mintina kusan uku zuwa hudu tukuna NUAB din yace aleey din ya shigo.

A dining ya samesa yace ya zauna su qarasa breakfast din tare.

Zaunawa aleey yayi yana jin dukkanin kuzarinsa da nutsuwansa na dawowa akan hanya sbd ganin yanayin NUAB din da damuwansa ta boye matiqar sosai sbd yana iya hangota a can qasan idanuwansa da yanayinsa amma a karan farko daya danne fushi da bacin rai tareda damuwansa ba kaman yanda ya saba ba fushinsa da zafinsa koyaushe a bayyane yake shiyasa koyaushe ko su da suke tareda shi kunnuwansu da fuskokinsu basa rabo da ja na fushi da bacin rai.

Breakfast din sukeyi suna magana a natse akan abubuwan dake gabansu na business dinsu kaman babu abinda ya faru.

Suna gamawa bayi ne dasuke bangaren tin dazu da suka kawo kayan basu tafi ba suka shigo bayan NUAB ya shige aleey ya basu daman shiga suka gyara koina tareda sakin qamshi yana shigewa cikin sanyin aircon dake gauraye palon.

Wanka sukai suka fito a shirye ta sako dagowar hijabinta akan kayansa data sako a ciki fuskanta fresh kaman baby ba tabo ko daya.

Shi kuwa kwarjininsa da asalin kyau da haskensa tareda haibarsa da fresh din da shima yake qarawa bayyana sukai suna hana kowace idanuwa kallansa a cikin fadawa da boys dinsa koda ya fito.

Aleey ne dayake harabar bangaren yana waya a natse da yaren French a shirye yana jiran fitowan Sultan me boyem din ya juyo jin qamshinsa yasan ya fito. #MAMUH 09033181070 [08/01, 5:09 pm] Dasoo: HAYATEEM Mamuhgee

157 Kallo daya aleey din yayi musu ya sauke kansa yana jin ransa fes dan haka kashe wayarsa yayi yana takowa ya nufo gurinsu ya gaidata cikeda kulawa tabude baki ta amsa tana janye dan janye hannunta daga na NUAB din dayake riqe dashi amma bai saketa ba saima juyowa da yayi ya kalleta da wata irin kulawa sa kasala damuwa na dan taso masa sbd bangaren Amminsa da zasu tafi baisan tayaya zai fuskancetaba.

Babu security din daya dago kansa har sultan din ya fice daga bangaren fadawansa na masarauta suna jere a bakin bangaren suna jiransa a natse dan hakan shine aikinsu.

Suma suna ganinsa tareda Bahar qasa sukai da kawunansu duka musamman da hannunta yana cikin nasa a sarqe ya kasa sakinta sai dagowa kwata kwata ta zama haramun ga duk wanda yake biye dashi din.

Kaman wainda zasu gaisuwan sirikai haka kaf fadawan da securities din suke biye dashi nesa kadan shi kuma yana gaba da ita sai aleey da keelah.

Bangaren Amminsa suka nufa dan haka daga inda hanyar ta fara ta zuwa bangaren duka kowa ya tsaya iya shi dasu aleey ne suka wuce gaba.

Suna isa kofar bangaren ta zare hannunta daga cikin nasa tana kallansa da wani irin sanyi ta girgiza masa kai sbd bazata iya shiga bangaren Ammin ba tareda shi ba.

Zuba mata idanuwansa yayi sbd shima ganin yakeyi bazai iya fuskantar Amminsa batareda ita ba sbd baitaba samun sabani ko irin wannan yanayin ba da Amminsa ba tinda yazo duniyaba dan haka sai yakejin kowace lissafi ta kwace masa akan hakan, Ya rasa girmansa da tinaninsa da zafinsa da mulkinsa da komaima duka akan muryan da Ammi ta daga akansa sbd bacin rai bayan yanada tabbacin itama tinda take babu wanda ya taba sakata wannan daga muryan da fushin idan ba shiba.

Kallansa Bahar tayi tareda sanyaya idanuwanta akansa ta bude baki da qaramin sauti me taushi tace

'Zaka iya sbd Amminka ce'

Baice komaiba ya saka kai cikin bangaren kai tsaye yana wucewa take bayin ciki suka fara jerowa suna fitowa.

Itama bahar shiga tayi sedai baya iya wucewa ciki ba kai tsaye kitchen tafara nufa tana jin fargaban haduwa da Ammin ta bude fridge ta dauki fruits da batasan me zatai da suba ta zuba a plate me kyau ta fito kitchen din ta nufi palon ta shiga kirjinta na sake harbawa.

Maa tenya ce a palon zaune tareda maa sakina dan haka maa sakinah bata juyowaba kallo daya tayi mata taci gaba da wayar datakeyi ita kuwa maa tenya juyowa tayi gabaki daya tana kallanta cikeda mamakin inda ta fito sbd tin dazu take nemanta sbd Ammin data saka a kirata.

Cikin tsananin nauyin kafafu ta qaraso gurinsu ta kasa kallansu cikin sanyi ta gaidasu.

Maa ce ta amsa batareda ta kalletaba tenya kuwa sai datai shiru kafin ta amsa mata tana daidai nan Ammi ta fito daga palonta tareda NUAB wanda gaida Ammin yayi kawai bai iya cewa komaiba ya fito suka fito tare batareda sakewan fuska daga Ammin ba sbd tana kan maganarta na idan bai sauko dinba bazata taba shiryawa dashi ba duk da kuwa a zuciyarta tana jin tsananin damuwan kalaman nata akansa sbd karfin hali kawai takeyi tana masa zafin sbd irin NUAB din baya ganewa ta sanyi sai da hakan.

Bahar datake tsaye ta saukewa idanuwanta tana kalla da kyau a natse sbd ance baa ganta ba a dazun to ina taje tinda safen..

Sauke idanuwa Bahar tayi tareda kanta a qasa tana kasa kallan Ammin jikinta na sanyi zuciyarta na bugawa wanda hakan ya saka Ammin dakatawa cak tsaye tana kallanta kafin ta dawo da kallanta akan NUAB daya dakata shima ganin yanda kowa yai tsuru ana kallan Bahar din wadda itama kusan take bada kanta ta hanyar kasa kallan ko daya daga cikinsu.

Ammi ce ta bude baki kai tsaye cikin daure fuska sosai tace

'Daga ina kika fito? Ina kikaje na aika nemanki akace bakya nan??

Dagowa tayi ahankali tana kasa kallan Ammin tace

'Ammi...' shiru tayi tana rasa abin fada sbd bata iya karya ba bata saba yiba kuma faduwan da gabanta yakeyi akan kallan da Ammin ke mata ya saka ta rikice sai kawai idanuwanta sukai rau rau.

Baci ran Ammin yayi ta daka wata tsawa me karfin gaske tana cewa

'Karma ki fara hawaye a gurin tambayarki nayi daga inda kike'

Maa sakinah ce ta bude baki zatai magana NUAB ya daga mata hannu a natse yana qarasowa gaban Bahar din ya saka hannunsa a natse ya kama nata ya janyota xuwa gaban Ammin suka tsaya ya dago jajayen idanuwansa da sukai ja sosai zuciyarsa na wata irin radadin yanda Amminsa ta sauya masa a lokaci daya ya bude baki yace

'Tana tareda ni,daga gurina ta fito,nine na buqaci zuwan nata Ammi'

Wani irin mamaki ne me karfi da girman gaske ya cike Ammin sbd bata taba dauka zai iya bada amsarba kuma bata taba kawo tinanin Bahar ta sake ko kallan inda NUAB din yake bare zuwa garesaba dan haka amsar taxo mata a bazata da wani irin takaici da nauyi me girma.

Tenya ma dataji hakan nauyin maganar taji tana tsananin fatar tambayar Ammin ta tsaya daga nan sbd idan ta sake wata tambayar dukansu zasu ji abinda zai sakasu kunyarsa bawai shi yaji kunyarsu ba dan haka ta saka bakinta a maganar da cewa Bahar ta wuce ciki.

Maa sakinah ma datai niyar saka baki shiru tayi sbd abar maganar a iya nan kada Ammi ta zaqe aji kunya.

Ammin ma rasa abin fada taji kawai ta kama fushin datake kai ta bude baki tana kallansa bayan bahar ta wuce tace

'Ya mukai da kai akan Bahar?? Menene kake kokarin yi?? Meyasa zaka ringa kebewa da ita? Daga yau na yanke kowace irin kebewanku harsai ka fara sanin darajar mahaifinka da sanin yanda zaka bisa kafin na baka marainiyar Allah.

Shiru yayi tareda kafe Ammin da idanuwansa da sukai wani irin ja akan wanda suke ciki sbd a karo na biyu a lokaci daya Amminsa ta sake yanka masa zuciya da kalamanta, A yau shi sabon mutum ne daya zabi farin ciki da umarnin mahaifiyarsa koda kuwa a zuciyarsa yanada qin hakan dan haka koda ya fito a yau ya fito a matsayin 'dan daya karbi farin ciki da zabin mahaifiyarsa ya zabi aurenta da sultan da shi kansa sultan din sbd Ammi tanasonsa dan haka daga nan ayau daya fito bangaren sultan din zashi a karo na farko yaje ya gaidasa a matsayin uba kuma mijin mahaifiya amma sai gashi ayanzu Ammi ta sake yankarsa da sabbin maganganu masu zafi.

Numfashi ya sauke a hankali mai sanyi da rashin sauti kafin ya bude baki ya furta

'Nagode Ammi,ki wuni lafiya'

Juyawa yayi yaiwa su Maa sai anjima suma ya fice daga bangaren batareda yaji a zuciyarsa kalman Ammin ko daya a ransa ta shiga ba bare tasiri akan Bahar dan kuwa idan har zata kasa rabuwa da sultan akan soyayyar datake masa bayajin tanajin abinda yakeji akan tata 'yar itama dahar zai iya ko kuma kwana a rayuwansa batareda ita ba bare rabuwa ko ace an shiga tsakaninsa da ita bayan igiyoyin aurensa dake kanta.

Yana ficewa kai tsaye kaman yanda ya tashi da sabuwar niyar bin sultan yasar a matsayin uba daga yau din sbd Amminsa kai tsaye bangarensa ya nufa take aka isar da sultan zuwan LEUL boyem din shima daya kwana da tsantsar kewan kaunar soyayya daga 'dan nasa cikin jin nutsuwa da sanyin jin zancen ya karba ziyaran ta NUAB din.

A karan farko da suka zauna a matsayin uba da 'da a natse aka gabatar musu da zazzafan tea na jinin boyems aka jere nuab baisha ba sbd a koshe yake sultan ne kadai yasha a natse yana amsa gaisuwan NUAB din wadda yayi masa a taqaice shima sukai shiru sai daga baya NUAB ya kira aleey ya shigo da takardar sanarwa auren iyayen nasa daya buga tareda saka stamp dinsa na sultan a jiki aleey ya ajiyeta a gaban sultan din kan table cikin girmamawa yana juyawa.

Kallo daya sultan yasar yayiwa takardar ta sake wani murmushi me sanyi yana ajiye cup din hannunsa a natse sbd batareda NUAB din ya furtaba a taqaice ya amsa auren da zuciyarsa.

Ajiyan zuciya ya sauke bai dauki takardarba ta sarauta ya sake fidda sadakin Ammin a karo na biyu ya ajiye a gaban NUAB din yace

'Ina sake gabatar maka da sadakin mai girma Ayanaah ghaz'

Kallan zinarin yayi tareda miqa hannu zai dauka cikin nutsuwa da izzar mulki sai Sultan din ya sake ajiye masa wasu silallan zinarin masu kauri a jere yace

'Wannan sadakin neman auren mahaifiyarka daya ne Sakinah wa Amintacce na Kadir a matsayin tukuicinta daga gareni na toroka gareni.'

Dakatawa NUAB din yayi cak daga daukan sadakin Amminsa yana dagowa a natse cikin kamewa ya kalli sultan din wanda shima shi yake kalla.

A daidai wannan lokacin kuwa Haile tana zaune Asim ya sameta da labarin zai bar boyem take taji kaman an zare mata hankali cikin mummunan rikicewa ta kallesa tana rasa abin fada daga ita harsu Aslam da ayanzu sun zama daga ido sai kunne.

Suna kallo ya fice dan haka a cikin mummunan yanayi ta miqe ta shirya ta nufi bangaren sultan dan tattauna matsayin da suke dashi a ayanzu masaurautar ita da yayanta.

Tana isa bakin bangaren sultan da bayinta dake take bayanta su kusan hudu ta tadda securities din NUAB alaman yana ciki dan haka bata tsaya ba tana kokarin saka kai kadir ya fito da takardar sanarwar auren sultan yasar da ayanah ghaz wadda idanuwanta suka sauka akai ta dakatar dashi ta fixgi takardar tana budewa gabaki daya ta karanta ganinta na neman disashewa daidai nan itama maraki ta iso bakin bangaren tazo ga sultan. #MAMUH 09033181070 [09/01, 12:50 am] Dasoo: HAYATEEM Mamuhgee

158 Jiri ne me karfin gaske ya dibi hailen tayi baya da sauri bayinta suka tarota shi kuwa kadir da babu abinda zai tsaidasa ko hanasa isarsa wannan sakon daya fi masa komai daukan sakon yayi yana barin gurin dan isar dashi ga yan jaridun masarauta dake jiransa dan harya kirasu.

Maraki data kawo gurin da mamaki me girma ta kalli haile tana boye mamakin nata sbd tasan koma menene ya kusa saka haile faduwa me girma ne kuma akan sarauta ne sbd ita burinta akan neman mulki ya qare sabanin ita burinta na shekaru shine sultan yasota kona qanqanin lokaci ne.

Rawa kafafuwa da hannuwan haile suka fara ahankali ta gyara tsayuwanta tana son hana mugun tashin hankalinta fita agaban maraki data iso amma lamarin neman fin karfinta yakeyi sbd abu ne da bata taba ko a mafarko kawo zai yiyuba musamman tinda sun manyanta sunada 'dan daya zama har sultan me zasuyi da wani daura aure a tsakaninsu, Me hakan ke nufi? Me sultan yake nufi? Irin wannan son yakewa ayanah tin farko kokuwa dai 'danta ne ya sakasa aurenta dole? Dan kuwa sultan bazai kai wannan shekarun ba yayi shaawan auren wata ayanah daya gama yayinta bayan idan yaso zai saka a kawo masa imebētis ko nawa yakeso idan ma wani abin yake buqata.

Maraki datake kokarin saka kai a palon na sultan cikin karfin hali haile ta katseta da cewa

'Gwara ma kada kiyi saurin shiga sbd ayau baida lokacin kowa a duniya bayan matar daya aura batareda sanin kowaba a duniyar sai yanzu ne zancen zai bayyanarwa duniya a karan farko sultan dayayi mulkin boyem ya aure wishmarsa.'

Cak maraki ta dakata tana qin juyowa sbd yanda zancen ya daketa kuma tana jin kaman ba daidai zancen dataji yake ba dan kuwa ba abin yadda bane da hankali da tinaninta zai dauka ace a yanzu sultan yayi aure aurenma da wishmah dinsa wadda batada alaqa ko daya da zamowa jinin boyem.

Wani irin abu ta hadiye daga bakinta me daci zuwa maqoshinta ya wuce zuwa kirjinta ya tsaya cak ta dan juyo ahankali tareda kallan haile wadda itama ta tako tana danne balai da masifar datake ji ta iso gaban maraki din ta wuceta zuwa ciki batareda ta iya ce mata komaiba.

Binta da idanuwanta da sukai jajir itama maraki tayi tana jin kaman ma numfashinta toshewa yakeyi ta daga kafafunta taci gaba da takawan itama zuwa ciki sbd gwara ma ta gansa din taji meyake faruwa daga garesa.

Kusan a tare suka isa palon hutawarsa a natse wanda yayi daidai da miqewan NUAB tsaye a natse hannuwansa biyu dauke da sadakin mahaifiyarsa da sadakin Maa dinsa wadda ya danne zuciyarsa ya kalli rayuwarta ya amince mata da auren sbd ta cancanci hakan ta cancanta kowane irin farin ciki a rayuwa.

Dakatawa sukai dukansu su biyu cak a tsaye daga qarasowa gurin sultan din sbd ganin NUAB wanda basu taba tsammanin samu a ciki ba hakama babu wadda ta taba ganinsa kusa da kusa a hakan a cikinsu dan haka kwarjinsa me tsananin gaske da haiba tareda wata irin kamewa da ikon izzarsa ya saka ko kallansa da kyau basu iya yiba,

Shi kansa bai wani lura dasu din dakyau ba sbd badan da adon zinaren dake jikinsu yana daukan ido ba ya dauka bayi ne farko dan haka bai iya ko kallansu ba ya saka kai ya fice ikonsa da izzarsa na sake bayyana a kowace irin takunsa harya bace daga palon gabaki daya.

Qarasowa sukai haile ce a gaba zuciyarta na neman zazzagowa sbd tsananin tashin hankali da baqin cikin datake ji ta zauna a natse kan kujeran dake kusa dashi ita kuma maraki ta qaraso tana zaunawa wadda ke kallansa,

Da idanuwansa masu kyau da haske yake binsu da kallan nutsuwa kafin ya dauki cup na tea dinsa yana cigaba da sha.

Maraki ce ta fara bude baki cikin girmamawa me girma da nutsuwa tafara gaidasa cikin tsantsar basa girma da daraja.

Amsawa yayi yana dagowa ya kalleta itama shi din take kalla kafin tayi qasa da idanuwanta tana jin batada maqiyi da abin tsana a duniyarta kaf face ayanah ghaz data kawo soyayya a zuciyar sultan wanda a baya baisan menene soyayyarba kawai zaune yake dashi a matsayin matansa yana sauke musu haqqinsu da rashin nuna banbanci da fidda kauna sbd baidan menene so ba amma a yanzu ko kallan dasuke samu daga garesa na girmamawan zama ne sai na mutuntawar zamtowansu matansa amma babu shauqi ko kadan a acikin muamalarsu.

Haile ma gaidasa tayi cikin girmamawan da bata kai ta Maraki ba taba son masa maganar asad amma batason maraki taji dan haka ta dauko masa maganar aurensa datake tsananin son ji daga garesa dan tabbatarda abinda ta gani tin kafin lissafin kanta ya kunce dan haka tambayar data jefa masa tayi daidai da shigowan Ayanah ghaz wadda ta sako kai palon da sallama me tsananin sanyi da nutsuwa tareda kwanciyan hankali.

Dukansu maida idanuwansu sukai akanta suna kallanta da duka imaninsu da hankali da zuciya tinaninsu bako kyaftawa.

Shi kansa sultan din ita yake kalla yana tsayar da tinani da kallansa akan yanayin daya gani a tattare da ita kaman na fushi dik da fushin mae yawa bane.

Dukkaninsu sunyi kusan fin rabin shekara basu ganta a idanuwansu ba dan haka wata irin fresh da yarinta da kaman take qara komawa suke kallo a tattare da ita dai kuma wani irin haske sosai me yawa data qara tamkar bata isa haihuwan sultan NUAB ba..

Wani nauyi ne ya sake danne kirjin haile ta rikice ta juyo da sauri ta kalli sultan tana neman magana amma ganin irin kallan daya kewa ayanah din ya sakata jin kanta na juyewa batasan lokacinda ta ambaci sunan maraki ba wadda bata iya cewa komaiba kuma kallo daya tayiwa ayanah ta dauke idanuwanta akanta sbd zuciyarta datai tsananin nauyi tanajin kaman zata mutu sbd baqin ciki.

Cikin nutsuwa ya kalli Ayanah din yace ta iso ta zauna zeyi magana dasu su dukan.

Takowa tayi a natse ta qaraso tareda zaunawa kujeran nesa dashi qamshinta ya ratso musu tsakiya yana shiga hancin kowannensu take suka sake shiga wani hali haile na neman kamuwa da bugawan zuciya amma maganar da sultan din zaiyi tafi matsuwan taji kafin ta mutu da baqin ciki.

Bude baki ayanah tayi a natse cikin kamun kai ta gaidasu sbd dukansu sun girmeta hakama a gaba suke da ita a gurinsa.

Babu wadda ta iya amsawa a cikinsu dan haka itama bata damu b shiru tayi tana kallan sultan dayake kokarin fara magana.

Maganganun nutsar da tinani da zuciya yafara jero musu daki daki kafin ya furta maganar aurensa daga karshe ya danar dasu maganar aurensa da ayanah wadda ta sauke kanta a hankali.

Haile data kasa yadda da abinda kunnuwanta ke ji mata Sultan ya sake qara aure kuma aurenma da imebēti baiwa wadda aka siyo da kudi aka gama kwanciya da ita a matsayin baiwa.

Ayanah din ta juya ta kalla idanuwanta na yin jajir tanason bude baki tayi magana amma ta kasa me zata fada dan haka hannuwanta dake dan rawa ta kame ta qame ta dawo da kallanta akan sultan din tace

'Inaga ba wani abin farin cikin fada bane aure da imebēti, Idan an gama shagalin bayyanawa duniya maganar auren inada magana akan Asim idan yana nan a matsayin dan ka kenan'

Shiru sultan yayi sbd yanayinta tana maganar ya gama tabbatar masa bata cikin hayyacinta dan haka akan maraki ya maida kallansa wadda ta dago ta kallesa da idanuwanta jajir ba kyan gani.

Batace komaiba sai miqewa datai tsaye a cikin sanyi tai musu allah ya sanya alkhairi ta juya ta fice tabar palon. Itama haile dake jin kaman zata kuwata miqewa tayi tabar palon dan zatafi komai farin ciki a yanzu ace mata balai ya fadawa sultan da Ayanah din sun mutu lokaci daya.

Suna ficewa sultan babu wanda ya bi koda kallo a cikinsu ayanah ma jikin amace da yanda sukai ta miqe ta fice tana kasa zama duk da taso magana dashi.

Suna ficewa dukansu babu abinda yaji ya damesa wayarsa kawai ya daga yana kunnawa sbd kiran da zaiyi.

****Labarin Auren Sultan yasar da Mahaifiyar sultan LEUL NUAB boyem me mulkin boyem a yanxu ya bayyana take masarauta da boyem ta dauka harma da labari da kafafen yada xumunta take aka ringa mamaki da farin cikin hakan tareda shiga nazari me girma dan kuwa abu ne da baa taba yiba baa kuma taba tinanin zaa taba yinsa ba a masarautar boyem din dan haka aka fara kira anata taya murna da farin ciki ga sultan dama sultan NUAB dan haka sai abin ya zama kaman wata babbar hidimar datazo bagatan.

A cikin ahalin sultan yasar kuwa a matsayin shock me girma zancen yazo musu musamman iyalan haile da suke a zaune jigum jigum suna rasa inda zasu saka kansu suji sanyi ga Asim da labarin ya samesa shima shock da wani sabon mutuwan jiki ya samu dan haka tafiyarsa babu fashi bazai taba iya cigaba da rayuwa a boyem din ba dan haka yaketa fama da tinanin yanda zai sanar da leylah koda zatai raayin iya cigaba da rayuwa dashi su tafi tare sbd a yanzu sai yanajin kaman ita kadaice ahalinsa dayake dashi.

A bangaren Ammi kuwa sosai sukai mamakin da NUAB ya fidda zancen wanda yake nuni daya amsa auren dan haka suka samu kansa a cikin yanayin jin dadi da kwanciyan hankali musamman Bahar dik da tana daki gabaki daya wunin ranar ta kasa fitowa sbd Ammi.

Leylah ma duk da batajin wani dadin jikinta haka ta bayyanarda farin cikinta sosai dan haka koda mum dinta ta iso bangaren sukam farin ciki suke ciki sosai da godewa Allah da komai a yanzu ya daidaita ba sauran fargaba ko shakka a yanxu dukansu aure sukeyi na kwanciyan hankali da nutsuwa dan haka sujjada zuhrah tayi ta godewa Allah daya nuna musu wannan ranar daga karshe dai duniya zata sheda ayanah cikakkiyar matar aure ce ba imebēti ba.

Su kansu su maa zuciyoyinsu fes suke da farin ciki da nutsuwa dan haka a walwalwa sukai wunin sabanin sauran bangaroran a cikin matsanancin halin baqin ciki da tsaka me wuya suke sbd ko haile da yayanta sunsan tinda sultan ya auri ayanah babu sauran kowace irin daman kowace mace a zuciyarsa sedai suci gaba da cin darajar igiyoyin aure. #MAMUH 09033181070 [09/01, 2:30 pm] Dasoo: HAYATEEM Mamuhgee

159 Masarautar sbd wannan lamarin me girma daya faru zamtowa tayi tamkar ana wata sabuwar hidima me girma sbd bayi sama da dari dubu aka yanta tareda fidda dukiya me yawa akai sadaka da hidima sosai wadda ta saka koina ya dauki hayaniya da farin ciki.

A canma bangaren aikin masarauta zaman fada aka ringa yi akan hakan kusan kwana hudu anata fama tukuna komai ya lafa hidimar ta rage.

A kwanaki hudun nan basu taba haduwa ba ko a waya sbd sam baya kiranta sedai ya tura mata text sbd ya hana kansa jin muryanta da zata iya sauke duk wani lissafinsa gashi ayyuka sun hau kansa baida lokaci sam sam dan kuwa aikin office ma na fada kaman bazai barsa kwata kwata baya samun hutu dan hakane ya nesanta kansa daga jinta kafin ya warware ayyukan gabansa da kusan a office yake kwana.

Ita kanta duk yanda tayi kewan jin muryansa hakura tayi sbd ta fahimci bazai iya jin muryanta ba bai gantava kuma hakan zai taba aikin dayake gabansa dan haka bata taba gwada kira ba sedai text din kawai.

Ammi ganin ko kofar palo bata taba fita ba a kwanakin ya sakata dauke idanuwanta akanta data saka sosai tareda kafewa da tsarewa dan ko shi kansa a kwanakin bai shigoba sam iyakacinsa da Ammin a waya su gaisa shikenan sbd ba time hakama yana hana kansa ganin Bahar ne a yanzu dayaje buqatar time me yawa na aikin.

Leylah ta samu sauki sosai ta fara sakewa sosai dan kuwa ganin yanda Bahar take maqale da waya a hannunta tana duba text din mijinta tana replying nasa ya sakata fara bawa sakwannin Asim mahimmanci dan shima kusan kullum saiya mata da safe kafin kuma kullum da daddare saiyazo wanda hakan ya saka ya dan fara sabawa da maa sakinah sbd yanda ta daukesa 'da dagaske sbd leylah.

A ranar daya cika kwanaki biyar tana zaune ta gana sallan ishai dinta kenan kira ya shigo wayarta tanaji kaman bazata duba ba ta miqe daga daddumar sallah datake ta nufi wayar.

Ganin wanda yake kiran ya sakata tsayawa cak tana zubawa wayar ido harta yanke bata iya motsawaba sbd mamaki dan kuwa rabonta da jinsa da ganinsa kwana biyar yau cif.

Text dinsa ne ya shigo wanda ya sakata daukan wayar tana budewa tareda zaunawa a sofa sbd kafafunta da suke mutuwa da wani sanyayyan farin.

Bude sakon tayi wanda taga kalmominsa qataice.

'Tea'

Karantawa ta sake yi tareda sake wani kyakkyawar murmushi Sanyi me nutsuwa yana ratsa zuciyarta.

Ajiye wayarta tayi tana zare hijabinta ta nufi kofa zata fice sai kuma ta dawo ta dauki wayarta sbd duba wasu abubuwan ta sake nufar kofa ta fice zuciyarta na sake cikewa da sanyi kowane second.

Leylah data ga irin murmushi da sanyin daya ratsa Bahar din tana zaune tana rubutawa Asim amsar sakon daya aiko mata itama akan sai ya gamo da Mameensa zai shigo zuwa anjiman ya ganta kafin ya wuce bangarensa.

Miqewa tayi tana bin bayan Bahar din da cewa

'Menene kike wannan farin cikin haka har jikinki yana nunawa'

Wata murmushin Bahar ta sake sakewa tana qarasa ficewa da cewa

'Ba komai'

Ko data fito ba kowa a palo koina tsit kowa na dakinsa Ammi ma da alama ta shige kenan sbd yanzu raba kwana suka sake yi bata zuwa koina gurin sultan sai ranar kwananta wanda sai gobe bayan kwana shida hakan zata zagayo mata sbd 3days suke yi hakama a kwanakin daga haile har Maraki ba wadda ta taba zuwa kwana gurinsa har gwara haile taje so daya sukai ba dadi sosai da kuma sako maganar Asim wanda kai tsaye sultan ya fada mata itace ta lalata rayuwar Asim din dan haka matiqar rayuwa a wani gurin daban zai bawa rayuwar Asim sabuwar maana da sanin darajar kai ya basa go ahead da cikakkiyar damar tafiya koina ne kuma zai tsaya masa a amatsayin uba dan haka daga yau din ya dakatar da ita daga kawo masa magana kowace iri ce akan Asim shi zai tsayawa Asim din daga yanxu ya cireta a ciki ta tsaya matsayinta kawai na uwa sauran yayan nata kuwa taje daman nata baida sauran kowace irin matsala dasu bayan Nysa dake aurenta.

Readers Also Read