Kenza eBookz

Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee - Chapter 63

Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee - Chapter 63

Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 63: Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 63. Tambayarsa maanar abinda ya fada tayi a natse…

4,460 words

Tambayarsa maanar abinda ya fada tayi a natse shima cikin nutsuwan ya kalli cikin idanuwanta ya fada mata duk inda zaiyi rayuwa ta tabbata da ita zaiyi a duk inda take so bayan boyem.

Ajiyan zuciya ta sauke tana jin farin ciki na ratsata da batasan lokacinda ta saka hannuwanta biyu ta zagayo wuyansa ba ta rungume tana lumshe idanuwanta farin cikinta na bayyanuwa.

Suna isa bangarensa a palonsa suka zuba ya zaunar da ita a cinyarsa yana kama fuskanta kai tsaye ya hade da tasa yana hade bakinsu yafara mata wani lafiyayyan kiss me tsananin shauqi da nutsuwan da basu taba samuba a tsakaninsu yana mannota jikinsa.

Acan dakin maa tenya kuwa wayar mai girma Sultan NUAB ce ta shigo wayarta inda kai tsaye ba kowace irin kwana a zancensa ya sanar da ita ba kowa ya bawa matarsa ya tafi da ita Anjom ba bayan ita kuma duk abinda sukeyi ayisa a gama kafin isowansa daurin auren wanda matiqar kafarsa ta sauka qasar babu abinda zai sakasa barin Queen dinsa.

Mamakinsa zuwa yanzu ya dena bata shock ko bugawan zuciya dan haka da angama kawai ta bisa dan haka ta tabbatarda suna isa akan bahar zatafi maida hankalin aikinta dan kuwa zatai mata gyaran da idan ta dawo zata jima a gyaren sbd a yanzu zasu dade batareda suna ganin juna ba. #MAMUH 09033181070: HAYATEEM Mamuhgee

166 Duk yanda suka shagala basu bari sun wuce lokacinda zaa gane bata bangaren Maminsa ba dan haka babu abinda ma yayi mata kawai yar soyayyarsu sukai ya dawo da ita har kofar bangaren ya sake rungumeta yana kissing gefen fuskanta tareda jin kaman bazai iya jiran ranar daurin aurenba zai wuce gaba yabi bayansu idan suka wuce.

Daqyar sukai sallama ta shige ya juya yana jin qamshinta da nasa na tashi duka a jikinsa ya sauke ajiyan zuciya yana jin farin ciki mara iyaka cikasa wanda ya manta rabansa ma dashi.

Itama tana shiga ba kowa dan haka a kofar dakin maa tenya ta tsaya ta sanar da ita dawowanta sbd batason ta shiga jikinta duka qamshinsa yakeyi ta silale ta wuce dakinsu.

Ko data je Bahar na kan waya da NUAB yana fada mata yanda zata kula da kanta ita kuma tana kwance kaman mara lafiya a dunqule cikeda kasala da mutuwan jiki muryanta na fita a kasalance tana neman hanasa zaman lafiyar zuciya da gangar jiki.

Leylah zare hijab dinta kawai tayi tana nufar toilet harta fito suna wayar itama zuwa tayi ta kwanta xuciyarta fes tana jin yau damuwanta da duka baqin cikinta yakau.

Washe gari da shirin tafiya da farin ciki suka tashi musamman ayanah da sakinah da sukejin finally zasu koma qasarsu suyi rayuwa, Qasar da suka cire rai daga saka zuwanta a rayuwarsu sai gashi sun tafi yanzuma zasu koma gida da farin cikin da yariga yayi gibin da bazai taba cika ba sbd wainda aka bar gida taredasu aka fara tafiyar dasu, Anfara dasu baa gama dasu ba wanda kaman koyaushe gibin da Abaas da Nurat suka bar musu bazai taba cikewaba duk kuwa farin cikin da zasu samu a rayuwa.

Sultan NUAB ya shigo bangaren da karfe goma na safiyar ya shiga ya gaisa da iyayen nasa kafin yayi magana da Ammi tsawon lokaci kafin ya fito ya fice.

Harya shigo ya fice Queen din boyem tana bacci bata farka ba har lokacin shima kuma daman baima saka ran ganinta ba sbd yasan bata farkaba dan sunyi magana da asuba yasan zata jima bata farkaba sbd yanda suka jima suna maganar a waya da asuban.

Karfe sha daya na rana ta farka tayi wanka dasu brush da sauransu ta fito tana jin jikinta ya samu karfi.

Shiryawa tayi ta fito ta nufi dakin Ammi ta gaidata Ammin na binta da ido ta fito tayi dakin Maa tenya ta tadda maa sakinah acan suna magana dan haka anan tayi zamanta salmah ta kawo mata abincinta anan taci tana shiga firarsu a natse ba hayaniya.

Tana gamawa mum zuhrah nashigowa sbd lokacin tafiyansu ya kusa.

Karfe daya da rabi jirginsu zai tashi dan haka karfe goma sha biyu da arbain harma da mintina akai Bayi suka fara fidda kayansu inda motocin dake jere suna jiran fitowansu ana sakawa.

Gama fidda kayansu akai kaf kafin suka fito kowannensu a shirye cikin nutsuwa da mulki da wayewan da duka ta ratsesu tareda daula.

Tin daga iyayen har yayan designers ne a kafafuwa da hannuwansu maana shoes and bags dinsu dan kuwa su chanel ne da Lv dasu Dior ke hannuwansu daban daban wainda kudin kowace zai baka mamaki idan kaji,

Bahar kai tsaye ita da maa tenya da sakinah wucewa gaba sukai sedai zuhrah da Ammi da leylah ne suka tafi har bangaren haile dan yi mata bankwana amma bata iya ganinsu ba sedai meryam tace musu bacci takeyi bata jin dadi,

Haka suka fito batareda sun gantaba suka wucewansu zuwa mota,

Motoci ne a jere na alfarma da suke daukan ido saina securities acan gaba suma a jere suna jira dan kuwa ba qananun securities aka hadasu dasu ba dan kuwa kusan zuciyoyin masu boyem ne dika aka hada guri daya da babu wanda bai bada nasa securities dinba akan matarsa musamman NUAB da wasu manyan murdaddun securities aleey ya bayar,

Sultan ma ya bada securities ga ayanah duk da yasan na NUAB ya ishesu, Shi kansa Asim bai nutsuba saida ya bada securities biyu wa tasa matar hakama Zuhrah kusan bayi biyar zata dasu daga bangarenta bayan wainda suke acan anjom da aka tanada masu yawa da tsari da sanin komai na aikinsu.

Motocin suka shiga dan zuwa airport,

Aleey ne ya iso da motar da NUAB kadai ne yake shigarta tasa ce ta hawansa ya kara a gaban bahar da kansa ya tuqota ba kowane driver ba, Ko ubangidansa baya tuqawa sbd akwai drivern NUAB din da dashi suka taho tun daga Moscow amma ayau NUAB shi ya bawa umarnin ya tabbatarda isar dasu Airport da kansa dan hakane ma ya zabi daukanta da kan nasa dan tabbatuwar hakan ya faru.

Ammi motar tata mijin da aka bude mata ta shiga batareda ta shiga ta Aleey ba daya fito ya bude musu kofar.

Bahar ce ta saka kafarta a natse ta shiga motar ya rufe yana komawa ya shiga ya tada sukabi bayan sauran motocin a natse suka fice daga masarautar boyem.

Ko da suka isa airport ba sautan time sozai dan haka kai tsaye wucewa sukai ciki suna duba time wanda Allah yasa basu wani bata lokaci ba jirginsu ya daga qasar.

***Tafiyan wuni guda sukai me kafin duka sauka a inda duk gajiyansu basu tsaya sun kwana ba haka suka dauki hanya da wata sabuwar private bus data da komai da suke buqata a ciki suka wuce Anjom nanma motocin securities dinsu na biye dasu da wani irin tsaro.

Tinda suka kama hanyar da dukansu sukaga bata ruwa bace mamaki da shakku masu karfi suka rufesu musamman ganin hanyar titi ce suke bi wanda yake sabo a bayyane bawai tsohon aiki ba da alama kenan an bude hanyar zuwa garinsu ba dole saita hanyar ruwa ba.

Ga mamakinsu hadda motocin kasuwa dake tafiya wasu kuma fitowa daga hanyar garin tareda mashin mashin harma da masu tafiya a qafa jefi jefi wanda yeke nuni da hanyar zuwa garin jamaa sosai ne suke kokuma garin kasuwanci.

Kasa mahana kowacensu tayi suka zuba idanuwansu suna bi da kallan ikon Allah da mamaki da farin ciki duka a zuciyoyinsu lokaci daya.

Symbol suka gani shima babba dayake dauke da sunan garinsu baro baro hade da sunan masarautar garin ta ahalinsu wato ANJOM GHAZ.

Bahar kanta farin cikine takeyi sosai ganin garinta da mahaifinta ya dawo cikakken gari a yanzu abinda Abaa dinta yaso Allah bai basa damar cika wannan burinba gashi bayan ransa an samu cika hakan.

Basu sake shiga mamaki ba saida suka iso cikin garin wanda yake garin gaske ayanzu hakama manyan shaguna da malls malls da manyan gurare daban daban hakama ga wutan lantarki.

Baban ginin dayafi kowane gini a garin suka tsaya mai hawa biyu da wani irin girman gaske gate har mataki biyu da securities da fadawan da aka dauka aiki aka qara da securities da tarin bayin hidima suka tsaya ginin na dauke da sunan GHAZ Empire acan sama da manyan baqaqe na kalan zinari yana daukan ido da haskawa.

Bude musu gate din farko akai suka shige aka rufe suka isa gate na biyu aka budesa shima motar ta shige sauran motar securities kuwa a harabar gate din farko ta tsaya tareda bayin da suka taho dasu sedai su suka isa da kafa zuwa ciki bayin.

Su kuwa ana parking a babban harabar gurin da girmansa yayi yawan da zai dauki motoci fiye da takwas a bakin babbar kofar shiga main entrance ta farko wadda kana shigarta bangarora ke kashi kashi da suke a tsare cikin wani irin kyakkawan gini da tsarin zamani na turawa da daula aka tsaya dasu aka bude motar suka fito.

Suna fitowa bayin dake jere suna jiran isowansu kansu a qasa suka fara musu barka da sauka cikeda girmamawa kafin suka fara daukan kayansu a natse suna wucewa ciki dasu.

Shigowa sukai wanda tin daga nan babbar jakadiyar gidan datake bada umarni ga bayi itace tayiwa kowa iso bangarensa da babu bangaren da babu duniyar jin dadi a cikinta.

Bangaren Ayanaah shine bangaren mafi girman gaske wanda yake dauke da dakuna kusan guda biyar da palo uku sai toilet a kowane daki da kitchen da dining room me girma da babu luxury dun da baa zuba ba.

Bayan bangaren Ayanah sai bangaren da Sakinah zata zauna wanda yake komai iri daya dana ayanah sedai ita 3 bedrooms ne da palos guda biyu da babban master bedroom mai hade da palo,

Bangaren Zuhrah ma irin hakan ne saina Bahar wanda yake shima iri daya sak sai babban bangaren da aka ware can gate din farko akai hadaddiya wadatacciyar fada me tsari datake dauke da offices kusan guda biyar masu tsari da kuma babban dakin taro maana meeting da sauransu.

Acan baya kuma bangaren bayi ne da maaikatan gidan da kuma bangare daya daban dakin securities dinsu ne a jere da suma daidai gwargwado ba abinda babu.

A jikin bangaren Ammi wani lafiyayyan bangaren da Sultan zai zauna yake wanda yake tamkar shine bangaren da daace Abaas yana raye zai zauna sbd shine na namijin gidan,

Akwai palon daya hada bangaren dana Ammi wanda ta cikinsa kawai zata fada bangarensa hankali kwance.

A bisa tsarin ginin asalin iya jinin GHAZ din akai ginin aka warewa kowa bangarensa kaman rabon gado, Ayanah,zuhrah da bahar wadda ita kadaice a cikin yaya take asalin jinin ghaz sbd mahaifinta ne ita bawai mahaifiyarta ba kaman yanda su su NUAB da leylah sedai ace jinin boyem ne su.

Sakinah ta zama jinin ghaz kaman yanda suke fada dan hakanne akai gunin da ita wanda koda aure ko ba aure tanada bangaren data mallaka a cikin masarautar ghaz da itace asalinta yanxu. #MAMUH 09033181070 HAYATEEM Mamuhgee

167 A bangaren Ammi dukansu suka sauka banda zuhrah data sauka nata bangaren da bayinta da tini suka fara aikin jera kayanta a wardrobe suna sake gyara komai daidai da yanda tsarinta yakeso.

Suma a bangaren Ammin Dakin Ammin shine a kurya me hade da palo me tsari sai sauran bedrooms din a jere a hallway saina maa tenya a main babban palo wanda hake hade da qaramin palo a cikinsa shima sbd itace zata zauna din din shiyasa nata yake hade da palonta dan haka nasu dakunan basuda palo.

Akwai gajiya me tsananin gaske a tattare dasu dan haka kowa daki ya shige dan rage gajiya da ibada.

Wanka da ruwan zafi tayi masu cire gajiya, Tara ruwan ma tasaka Naimah tayi mata a bathtub kafin taxo ta shiga tana rufe idanuwa sbd ratsata da ruwan sukai suna fara rage gajiyan datake ji musamman kafafunta da suka dan kumbura kadan sbd zama.

Wanka tayi sosai a natse bayan ta gasa jikinta tukuna tai brush da sabbin komai da aka jere musu na buqata a toilet dinsu komai a kwai.

Tana fitowa sama sama tayi shirin ta saka riga da wando masu kauri da hula ta saka doguwar riga akai tayi sallar asuba da akai suna hanyar anjom din.

Tana idarwa tea me zafi ta saka aka kawo mata har daki sika hado da cake me laushin gaske sabo da akai tinda uwar asubar, Tas ta shanye tea din kafin taci cake din daya tasha ruwa kafan ta kwanta tana shigewa barko tareda kashe wutar dakin ta qarawa ac din karfi kadan take bacci me karfin gaske ya rufeta sbd ko gani batayi sosai sbd baccin.

Kusan kowama hakan yayi ya kwanta dan suna cikin gajiya matiqa.

Kasancewan masu anjom suna gidan ya saka kowace motsi me hayaniya ya dauke a gidan sbd a basu daman hutawa dakyau.

Babu wanda ya farko ko fito a cikinsu sai bayan karfe daya kusan ma biyu,

Sallah da wanka ta sake yi sai a lokacin ta janyo wayarta tana kunnawa tareda kunna wifi na gidan sbd basuda layikan qasar dole iya wifi zasuyi amfani dashi suyi amfani dasu WhatsApp da sauransu.

Password din aka kawo mata daki ta saka take sakonsa kuwa ya shigo wanda tana gama karantawa murmushi me sanyi ta sake tana lumshe idanuwanta sbd tafar jin kewansa me tsanani a yanzu da basama qasa daya.

Kiransa ta saka ta WhatsApp yana dauka a natse cikin wani irin sanyi suka sauke ajiyan zuciya tare tana qarawa da murmushi me sautin daya shiga kunnuwansa ya sakasa sake lumshe fararen idanuwansa yana ambatar cikakken sunanta cikin nutsuwan da itama saida tsigar jikinta ta tashi ta bude baki daqyar ta amsa tana gaidasa cikin basa girmansa na miji kuma sultan.

Yanda tayi gaisuwan ya sakasa fidda wani murmushi me nutsuwa yana amsawa tareda fara binta da tambayan hanya da gajiya da baqunta da kuma missing nasa.

Amsa masa tai duka a kasalance tana fada masa missing kuwa tanajin kaman idan ta dade batama gansa ba Amminta bazata sake gane lafiyanta ba.

Murmushi me sautin nutsuwa ya sake sakewa yana jin kalman tata har cikin kwakwalwansa yace

'GHAZs princess kada ki janyo aikin da bazaki iyaba fa sbd Anjom bata da nisa gareni matiqar kina can'

Itama murmushin ta sake tana cewa

'Hmmn anan dai ai ko kazo ko masaukinka bamada'

Murmushi kawai ya sake bai bata amsar maganar ba sbd shida yakeda mata da uwa a gari a masarauta ai zancenta neman magana ne kawai.

Fira suka cigaba dayi a natse a kasalance har tsawon lokaci ba hayaniya ba daga murya har suka gama tukuna ta ajiye wayarta tana fitowa tabar leylah na shiga wanka dan ko anan a daki daya suke yanxu da suka saba.

A palo ta tadda su Ammi duka sun fito kusan kowa waya yakeyi banda maa sakinah datake dining tana sake gyara yanda tsarin abincin da ake jere musu a dining tana bada umarnin abubuwan da zasu kawo.

Gurin maa sakinah din ta nufa tana tayata aikin tana dan lafewa gefenta sbd sam tafara jin ta rasa me ke mata daidai.

Suna gamawa daidai su Ammi sun gama waya dan haka taje ta zauna gefen Ammi tana musu sannu da gajiyan hanya tana dan sake neman kokarin kwanciya.

Dining suka suka nufa dukansu suna zaunawa leylah nafitowa itama dan hakaa tare sukaci lafiyayyan abincin da aka cike dining dasu kusan kala uku.

Suna gamawa a palo suka zauna kowa da abimda yakeyi itada dai tana kwance lafe gefen Ammi jikinta yayi dumi kaman me shigar zazzabi Ammin na jinta tayi shiru tana shiga nazarinta sbd gabaki daya ta sauya da qananun ciwo da kasala.

Batai mata tinanin komaiba musamman ciki sbd batajin tayi haduwa sosai da NUAB da zatai saurin samun ciki hakama yaushe rabon su ma da juna dan haka ta ringa mata fadan ta rage san jiki da yawan kwanciya.

Maa sakinah ce kadai tafara zargin akwai wani abu a jikin Bahar din sbd yanda ko cin abincinta ya sauya sam batason abinci sosai yanxu sai tea da abincin ruwa ruwa,

Maa tenya ma bata kawo tinanin komaiba sbd ta dauka abubuwan datake basu ne yake saka kasalan da yawan sauye sauyen appetite tinda yanawa wasu matan hakan.

Leylah ma maa sakinah na ankare da ita duk da ita kwata kwata laulayinta ya bace gabaki daya kawai cika take sake yi tana kiba.

*****kwanaki sikai suna hutawa dakyau sunje ziyarar bangaren kabarin iyaye da dan uwansu sunyo musu addua tareda fidda sadaka me yawa aka rabawa yan gari hakama sun fita sun zagayo gari sun dubo gari kuma gari ya dauki dawowan asalin masu garin dan haka ake jin tamkar haske da rahamar garin ta qarasa dawowa mutane sunyi farin ciki da murna sosai wasuma hadda kuka.

Su kuwa tinda suka dawo basu sake fita koina ba sbd yawo baya cikin dabiun jinin kowane dan sarauta kuma basu saba daman dan haka maa tenya bude aikinta tayi tafara cigaba dan ma bikin na sake matsowa.

Hidimarsu suka maida hankali suka fara sosai ta biki hankali kwance anata kashe dukiya me yawa da zama busy dan kuwa sosai aka fara gayyato mutane,

Ita kanta yayanta dukansu sun taho suna anjom sun iso da wuri kuma zasu kwana biyu suga mahaifiyarsu da kyau ko bayan bikin kafin su koma kuma kowa da hannu bibbiyu da kauna da sakewa aka tarbesu ba babbanci a tsakaninsu dasu Bahar dasu da yayansu yan mata da suka taho dasu duka dan haka gidan ya sake cika sosai da samun hayaniya.

Daga sultan har NUAB har Asim babu wanda a cikinsu baya cikin tsananin matsuwa da zuwan ranar daurin auren musamman Asim da baya komai bayan shirin barin boyem daya gama daga anjom bayajin zai dawo daga can zasu wuce da matarsa gaba dan haka ya zama busy sosai da kuma dagewa gurin cusawa mahaifiyarsa sabawa da rashinsa dan kuwa zamansa din baida amfani gwara tafiyar ya fara aiki ko wasu businesses din tinda nan a zaune yake zaman banza sbd babu jinin boyem dazai taba aiki a wani guri cikin qasar boyem hakama a cikin masarautar ma bazai taba samun aikin ba sbd NUAB ne me mulki hakama a yanzu da Kowa rayuwan aure zaiyi ya zabi yinta a wani gurin daban kawai da iyayensa daban dana NUAB da BAHAR.

Haile da har lokacin ta kasa yadda da 'danta barinta zaiyi hakama sultan barinta zaiyi zarewa tayi gabaki daya kwana takeyi kuka wuni takeyi baqin ciki da qunci,

Umarni da duk wani tashin hankalinta bai saka Asim ya janye barin boyem ba wanda dan haka ta koma roko da magiya amma ya kasa fasawa sbd wasu manyan dalilinsa da bai bude mata ba amma hakan shine mafi daidai kuma yana shirye da tafiya da ita dan itama ta samu sauyin guri ta samu salamar zuciya idan zata yadda da hakan amma sam taqi yadda haukacewa kawai take neman yi takai har cikin baccinta take ambatar sunan Ayanah ghaz tana maimaitawa tana hawaye.

Sultan ma ya zaunar da ita ya sake sanar da ita tafiyarsa wadda ta sakata rasa dukkanin sauran hankalinta musamman dayake fada mata zai jima kafin ya dawo hakama idan ya dawo nan din itama zai jima mata kafin ya sake komawa anjom.

Kaman daga sama yana gama fada mata maganar ta bude baki tana kallansa da idanuwanta da suka bushe jajir tace

'Sultan dan Allah ka saki ayanah ghaz ka barta tinda ta riga ta koma qasarta, Zaka iya mun hakan ni mahaifiyar 'yayanka?? Kaman zan mutu nakeji,zuciyata zata buga,baqin ciki da qunci zai kasheni'

Kallanta ya tsayar da idanuwansa yanayi a natse cikin nazarin yanayinta daya fara kamata ya karanta dakyau kafin komai sbd tabbatarda lafiyarta kalau.

Ganin alamu sun nuna kalau take ya dauke idanuwansa daga kanta yana ajiye wayarsa gefensa ya bude bakinsa yace ta tafi kawai.

Sake maimaita abinda ta fada masa tayi tana kallansa idanuwanta na sake ja

Bude baki yayi yace

'Kije kiyi hakuri bazaki samu abinda kike fadan ba, Bana auren mace na saketa a rayuwata musamman macen dana jarabtu kafin samu,babu abinda zai sameki ki cire damuwa ki danga duka quncinki zai yaye'

Yana gama fada mata hakan ya nuna mata kofar ficewa da hannunsa daya dan yana buqatan tafiyar tata dan yanda kalamanta suka sosa zuciyarsa dan bai taba tsammanin kai tsaye magana irin wannan daga gareta ba.

Bata iya cewa komaiba ta fice tana hadiye wani qullutu me nauyi da daci daga maqoshinta tana komawa bangarenta.

Wuni tayi a daki babu wanda ya sake ganinta hatta yayanta duk yawonsu sun kasa ganinta tana daki ta rufe taqi fitowa.

Kasa nutsuwa hankalinsu yayi suka ringa jin damuwa dan haka suka zauna jigum jigum gashi Asim ma bayanan ya fita tin safe yana wajen masarautar ma.

Sai dare ta bude kofar dakin ta fito Ga mamakinsu tayi wanka tayi shirinta tsaf ta kira babbar baiwarta ta sakata ta dafa mata shayin sultan zataje tiraka yau din.

Aslam na jin hakan ta miqe taje ta karba aikin ta dafa masa da kanta ta shirya komai tana farin cikin dawowan mamin tasu daidai dik da ba doguwan walwala a fuskanta kaman ma ta gama saddakar da rayuwa meryam ke gani a tareda ita din. ##MAMUH 09033181070HAYATEEM Mamuhgee

168 Aslam na gama hadawa ta kawo ta ajiyesa yana shirye a cikin wasu lafiyayyun tea set masu kyan gaske sabbi harma da dabino da zuma masu kyau duka ta jere ta ajiyewa Mamin wadda tace su tafi kawai idan ta gama abinda take zata kai masa.

Karfe goma sha daya ta baro bangarenta ta isa bangaren sultan din ita kadai sai baiwarta daya data dauko mata kayan suna isowa ta karba ta shige kadir ma dayaga zuwanta tini yabar bangaren ya tafiyarsa bangarensa saida safe kuma.

Ko data shiga sultan din ya gama komai na shirin bacci yana zaune dakin ba haske sosai yana waya a natse cikin kamala da kwanciyan hankali da Ayanah ghaz wadda take jin nutsuwan wayan dashi itama.

Haile daga fahimci da waye yake wayar wani abun ya sake zuwa ya danne maqoshinta amma kuma tinawa da daga yau baqin cikinta ya qare ya sakata ajiye kayan hannunta a kan table din gabansa tana bude baki tayi magana wadda ta sauka kai tsaye a cikin kunnuwan Ayanah.

Wani iri Ayanaah din taji musamman data kalli lokaci sai kawai taji kirjinta yayi nauyi itama da wani kishinsa me sanyi amma kuma tasan basu kyautaba sbd daga yanzu tasan matiqar yana boyem daidai irin wannan lokacin to na matansa dan haka cikin nutsuwa tai nasa saida safe bata jira amsarsa ba ta kashe wayar tana ajiyewa a gefenta tareda sauke numfashi me sanyi tana hana kanta jin komai.

Shima acan bangaren baiji komaiba sbd hailen dan haka ajiye wayar yayi gefensa yana kallanta a natse.

Zaunawa tayi gefensa gap dashi sosai tana dagowa ta bude baki cikin bayyanarda nadama ta basa hakurin abinda ta fada a dazun.

Sai a lokacin yaji tausayinta me yawa ya shigesa da ratsasa musamman da ramarta da figewanta duka suka bayyanar masa ya kafeta da ido yana jin inama zai iya fada mata nasiha taji ta dauka akan bazai taba wulaqantata ba ko tozartata akan aurensa kodan darajar shekarun da sukai tare da manyan yayansu dake tsakaninsu amma yasan babu abinda zai fada mata taji bare yadda wanda dazatai hakan data samu nutsuwa da kwanciyan hankali tareda zaman lafiya.

Numfashi ya sauke yana karban banhakurinta tareda miqa hannu ya karbi tea din datake miqo masa yana mata godia kadan a natse yakai bakinsa ya bude yafara sha duk da baya buqatansa dan bai jima da gama sha ba amma sbd ya bata nutsuwa da kwanciyan hankali sai yasha din.

Idanuwanta cikowa suka fara yi da hawaye masu tsananin radadi da quna tareda dacin shedar da wannan rana wanda shine ya janyo musu wannan kaddarar.

Tana kallo ya ringa sha ahankali harya shanye rabi ya ajiye a natse tareda dawowa da bayansa yana jingina ya kalleta hawaye na gangarowa daga idanuwanta mamaki ya kamasa bude baki zaiyi magana ta taresa dukkanin imaninta na barin kirjinta ta share hawayenta tana kallansa itama dakyau ta bude baki tace

'Meyasa ka zabi ayanah ghaz akan kowace mace Sultan?? Meyasa ka lalata rayuwan mata da yawa da basada adadi ka qare akan ayanah ghaz? Meyasa se ayanah ghaz? Baiwa ce qanqantacciya,imebēti ce macen da ake kwanciya da ita dan biyan buqata,wishmah ma data zama batai darajar mu da muke da aurenka akanmu, Meye ne jinin ghaz suke dashi da kowa yake sonsu yake mutuwa akansu? Menene a jininsu bayan mummunan kaddara da baqar rayuwa, Meyasa zuciyarka bata iya bani soyayyarta ba bayan shekarun da mukai a tare muka tara yaya sai akan baiwar datake ragin kusrawa.....

Rufe idanuwansa yayi a natse kalmarta ta qarshe tana yiwa zuciyarsa yanka me karfin da idanuwansa suka sauya hadda fuskansa sbd radadin yankan,

Bude idanuwansa yayi batareda ya kalleta ba sbd gabaki daya jin yayi babu abinda ya tsana a daidai wannan lokacin bayan iya kallanta dan haka baice komaiba wayarsa ya daga ya saka kiran Asim sbd yace yaxo ya tafi da mahaifiyarsa dan da alama akwai matsala me girma a cikin kwakwalwanta, Bazai tankawa kowace irin haukanta ba kaman yanda bazai iya cigaba da saurara ba dan haka gwara danta yaxo ya tafi da ita salin alin.

Koda kiran ya fara shiga wayar Asim a lokacin Asim din ya dawo yana tsaye kofar office din NUAB zai shiga a karan farko da zasu fuskanci juna sbd tafiyarsa tagama kammaluwa stamp na sultan din boyem na yaddar barin boyem a matsayinsa na jinin boyem yake nema kadai a takardarsa ta li'uli Asim ya sakasa zuwa dan haka tin safe ya sanar da Aleey a waya cewan ya sanar da Sultan LEUL din yana son ganinsa ba bata lokaci kuwa cikin girmamawa Aleey din ya amsa da yes ya kuma isar da sakon ga NUAB wanda yace koyaushe Asim din ya tashi free yake da zuwa ganinsa ba shamaki.

Bayan aleey ya sanar dashi godia kawai yayi bai samu zuwa ba sbd bai zauna ba sai daren ya kira yaji har lokacin NUAB yana office shiyasa ya fito yazo sbd gobe tinda safe zai bar boyem ya fara wucewa amma ba anjom ba sai antashi daurin auren zai tafi anjom daga can ya wuce da iyalinsa dan ita ma komai na tafiyanta ya mata.

Shigowan kiran sultan yayi daidai da zai shiga office din Aleey na tareda shi cikin sakewa da girmamawa dan haka daga wayar yake kokarin yi a natse da mamakin ganin kiran Sultan a lokacinda baa taba kiran kowa dan idan dare yayi irin hakan baa kiransa baya kira shima.

Yankewan kiran ya sakasa dakatawa yana sake shiga mamaki kafin ya saka kiran wanda tafara ringing amma ba alaman zai dauka.

Readers Also Read