Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee - Chapter 65
Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 65: Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 65. Asim wanda a cikin wuni da kwanan ya sauya…
4,490 words
Asim wanda a cikin wuni da kwanan ya sauya gabaki daya ya zauce daga zaune ya koma mara madafa da rashin ina zai saka kansa yanayinsa babu wanda bazai kallesa ya tausaya masa ba sbd abin biyu yake akansa, Halinda mahaifinsa yake ciki na tashi ko akasinsa da kuma mahaifiyarsa da itace tayi aikin hakama manyan fada sun zauna sun hada kan laifukanta da Aleey ne ya badasu da cikakkun shedunsu na kisar data ringa yi da hannuwanta a rufe batareda an bayyana, Haka suka hada laifukan rayukan data dauka masu yawan gaske da yunkurin kisan dataiwa sultan aka fiddawa duniya wanda take masaurautar ta dauki zafi harma da wajen masaurautar akan saita amsa hukunci daidai da laifinta maana kisan dataiwa bayin Allah marasa galihu dan kawai suna bayi ba akan laifin komaiba.
Zafi masarautar ta dauka sosai da sultan NUAB wanda zuwa yanzu komai ya cake a cikin kansa da zafin gaske sbd maganar kwanaki akeyi sultan har lokacin yana cikin mummunan hali gasu Amminsa sun fara kokarin gane halinda ake ciki sbd zuwa yanzu ba lokacinda bata kiran wayarsa bata samu hakama daga NUAB din har Asim sun sauya sosai damuwansu a bayyane take qarara ko a wayar dan haka hankalin Ammi da matansu yafara tashi,
Zuhrah ce kadai tasan meyake faruwa dai tenya kuma sun kasa nunawa ma bare fada suna cikin mummunan tsoro da tashin hankali suma musamman da cikin leylah kwatsam ya bayyanar musu ta hanyar somewa data kusan yi a lokacinda taji abinda yake faruwa itama a bakin shuraim wanda baya boyem amma ya koma tini shima.
Likita aka kira ya dubata take ya tabbatar musu da ciki ne a jikinta,
Bayan wucewan likita murnar cikin sukai duk da ita tana cikin shock hakama takasa fada itama sai kawai ta samu kanta da tsananin son kasancewa da Asim wanda a yanzu yafi kowa shiga tsaka me wuya da mummunan hali dan kuwa yana ji yana gani hukuncin kisa ya hau kan mahaifiyarsa wadda itama tana samun sakon hukuncin da aka yanke mata yanke jiki tayi ta fadi tana somewa.
'Yayan nata ma babu wanda bai yanke jiki ya suma ba jin hukuncin wanda tini Sultan LEUL NUAB ya saka stamp dinsa a jiki har an fidda duniya ta dauka dan haka iyayenta da suka tsufa sosai da nysa yarta da jikokinta tini suka kamo hanyar qasar boyem cikin mummunan tashin hankali me tsanani.
Asim ya rufe kansa a bangarensa yayi kuka ya buga kansa ya kusa mutuwa sbd ciwon dayake ji a kirjinsa ya rasa ya zaiyi da rayuwarsa dayake fatan ya mutu akan abinda yake ji.
Shi kansa NUAB babu wanda ganinsa ya taba zuciyarsa idan ba Asim ba wanda yake kwatanta radadin dayake ji sbd sanin matsayin uwa da girman soyayyarta a zuciyar kowane 'da.
Leylah shiryawa tayi akan uk zata tafi ta samu Asim acan daga can zasu dawo bikin.
Babu wanda yayi mamaki ko yunqurin hana tafiyar a cikin iyayen sbd kusan bame walwala a cikin wani hali sike,
Dukansu suna son tafiya boyem din amma kuma sbd babu dalilin tafiyar ya saka suka danne sukai shiru tinda basusan meyake faruwaba,
Tenya da sukasan meyake faruwa basuda ikon fada haka dai gidan ya koma tamkar gidan zaman takaba ba walwala ba farin ciki.
Bahar ma ahankali ahankali ciwo yake kokarin ya zama nata dan kuwa koyaushe a kwance take batason hayaniya ko son shiga mutane sosai, Tsakanin kewansa da sonsa ne yake sake tsananta halinda take ciki har kuka take masa a waya idan ya kira sbd batason jinsa a cikin damuwan datake jinsa a ciki,
Kukanta da daga hankalinta akan kasa yadda da babu abinda yake damunsa sai suka hadu da damuwansa suke neman tsayar da duniyarsa cak.
Ana gobe ne ranar hukuncin Queen haile a ranar Leylah ta iso boyem da dare drivern bangaren mum dinta ne yaje airport ya daukota suka iso.
Ko data iso masaurautar koina yayi shiru ana cikin tsananin alhinin abinda zai faru goben dan haka kai tsaye bangaren mijinta ta nufa bayi biyu na biye da ita janye da akwatinta da jakar hannunta.
Idanuwanta jajir ta isa bangaren batareda jin duk gajiyan data debo ba sbd tashin hankalin datake ciki ya wuce gajiyan.
Koina duhu ne a bangaren dan haka kai tsaye dakinta ta isa ta aje komai ta fito ta nufi dakinsa,
Baya nan dan haka komawa tayi dakinta tayi sallolin dake kanta bata tsaya shan ko ruwa ba ta fice zuwa bangaren Aslam sbd kyautata zatan yana can.
Acan din kuwa ta samesu su uku cikin mummunan yanayin da take idanuwanta suka ciko da hawaye suna fara sauka ta qaraso cikinsu tana zaunawa gefensa tareda kallansu daya bayan daya tana kokarin gaidasu da jajanta lamarin wanda ba wanda iya doguwan magana a cikinsu sedai kawai gyada kai da sukeyi.
Shine kadai ya iya zuba mata ido yana kallanta yana rasa abin fada idanuwansa jajir yayi wata muguwar rama a cikin kwanaki kalilan dan kuwa abinci me suna abinci ya manta rabansa dashi a bakinsa ruwa kawai sai tea ne suke shiga bakinsa da cikinsa.
Hannunta ta miqa ahankali ta dora akan nasa tana kamawa ahankali tareda sakar masa wani soft tabawan dake bayyanarda dukkanin kulawanta da damuwanta tareda jajenta da tausayawanta.
Shiru sikai dukansu bame cewa komai sbd abin fada ya gama qare musu,
Suna zaune anan su nysa da kakanninsu suka iso tareda wasu daga yayan nysah din dan haka kuka da damuwa me zafi ta dawo sabuwa haka suka ringa kuka mai tsananin gaske suna rokon Allah ya kawo mata sauki da mafita akan wannan mummunan lamarin da zasu shedar gobe.
Asim kuwa zuwa yanzu tsananin damuwansa ya koma akan sultan ya farka kafin goben ko akwai sassaucin da zata samu daga hukuncin me tsaurin da suka kasa dauka.
Duk wanda yake masarautar kwanan damuwa da zullumi tareda baqin ciki ya yi hakama kaman kiftawan ido sukaga daren ya wuce gari ya waye,
Karfe hudu da rabi ne lokacin hukuncin haile dan haka aka bawa zuriarta damar shiga gurinta su gana,
Dukkaninsu suka shiga bayan kuka mai jijjiga zukata babu abinda sukeyi tinda suka hadu sbd babu ma me abin fada,
Ita kanta wani irin dana sani da kuka ne me yawan gaske takeyi musamman ganin yayanta da iyayenta da jikokinta suna wani irin kuka wanda tasan ta riga ta bata musu sunan da harsu mutu bazasu dena wannan kukan da fuskantar matsala ba.
******damuwa da qunci sun hana sultan NUAB da kadir kowace irin nutsuwa da gane komai dan haka suma babu wanda rama bata kamasa ba ta kwanakin hakama kowannensu ya kasa matsawa daga gadin sultan din,
Wanka da sallah kadai ke fidda NUAB daga bangaren hakama komai na masarautar ya tsaya cak sbd bama me ganin sultan NUAB din.
****Ayau din kaman a mafarki karfe uku da mintina ana gap da sallar laasar Sultan yasar ya farfado sedai bai iya magana ba idanuwansa ne kadai suka bude a cikin yanayi na rashin kuzari ko lafiya yana fidda numfashi a hankali.
Farfadowan nasa tamkar a mafarki dukkaninsu suka jita dan haka take akai gaggawan kiran likitoci suka iso kansa.
Dubasa sukai cikin ikon Allah ya farka din batareda wasu manyan complications din ba bayan rashin karfi da kuzarin jiki wanda zai jima a hakan sbd garkuwan jikinsa da kusan poison din ya illata sai a hankali ahankali lafiya da kuzarin gangar jikinsa zai dawo daidai dan ko tafiya ba yanxu ba se a gaba ahankali dan haka wheelchair zaa kawo.
Duka wannan bayanin radadinsa kadan ne a zikatansu tinda ya farka zai rayu kuma insha Allah dan haka ajiyan zuciya da wani irin numfashi NUAB ya ringa ajiye a bayyane yana jin wani nauyin daya danne kirjinsa yana sauka zuwa cikinsa yana fashewa. #MAMUH 09033181070HAYATEEM Mamuhgee
172 Koda labarin farfadowan sultan ya fita take msarautar da wajenta ma aka ringa sauke ajiyan zuciya ana farin ciki da murna tareda jiran kuma me zai faru akan abinda zaiji akan haile ayau din da zata fuskanci hukuncinta.
Asim da yana bangaren sultan ya farfado zubewa qasa yayi a natse yayiwa Allah sujjada sbd tin jiya yake rokon ubangiji ya farfado da sultan din kafin lokacin qaddamar da hukuncin yayi kuma gashi Allah ya amsa masa dan haka dashi da NUAB ne suka kimtsa sultan din yana kwance idanuwansa a rufe zuciyarsa a toshe ba tinanin komai face gangar jikinsa dayake ji kaman ba tasa ba.
Su aslam ma farin ciki ne ya shigesu wanda suka manta ma yaya dandanonsa yake suka dungumo duba sultan din.
Kaf yayan sultan din suna masarautar sun iso dan haka masarautar take ciki,
Haka suka ringa zuwa dubasa daya bayan daya suna ficewa banda aslam da meryam da nysah da suka zube qasa kansu a qasa batareda laakari da bai gama dawowa daidai ma dazai fahimci komaiba suka fasa masa wani kuka me tsima rai suna rokon ya nemawa mahaifiyarsu sassauci daga sultan NUAB wanda baya dakin ya fice gabaki daya daga bangaren sbd sauran yayan sultan da zasu shigo dan haka gurin zaiyi hayaniya ko yayane.
Yana barin bangaren bangarensa ya koma sai a lokacin ya samu damar kiran Amminsa da kansa ya sanar da ita abinda yake faruwa cikin kwantar mata da hankali.
A tsaye take amma kafafuwanta sukai wani irin sanyi da sanqarewan data zame ta zauna kan kujera da karfi tana dora hannunta daya akan kirjinta cikin tsananin jin wani irin radadin datasan zafi da ciwonsa a baya sbd radadi ne kadai datake kasu idan wani abin ya samu daya daga cikin jininta su abaas da nurat da zuhrah.
Ja idanuwanta ke rikidewa sunayi ta kasa bude baki tace komai ta kashe wayar kawai tana sakinta idanuwanta na neman rufewa da duhu tayi saurin jingina bayanta tana rufe ido dan numfashinta dake neman toshewa.
Maa sakinah ya kira ya sanar da ita abinda ya faru da kuma fada mata ta kula da Ammin kada ta shiga wani halin hakama duk tsanan kada Ammin taxo Anjom zaa taho da sultan din anan zai qarasa jinyarsa dan haka su jira kowane lokaci zaa iya isowa da sultan.
Tashi hankalin maa sakinah yayi ta fito a rikice jikinta na rawa ta fadawa tenya da zuhrah abinda yake faruwa sai a lokacin suka samu damar fidda tashin hankalisu da suketa dannewa dan haka suka taru suna shiga damuwar bayyane da tsoro da mamakin haile.
Ammi dai kusan kasa dauka zuciyarta tayi sbd numfashinta daya ringa sarkewa yana neman daukewa dole sukai gaggawan neman likita ya iso ya fara bata taimakon gaggawa daya kamata.
Bahar da saida jikin Ammin ya rikice tasan meyake faruwa kusan itama zubewa tayi saida Maa sakinah ta riqeta jikinta tana kallanta da kulawa tace
'Ki kula da kanki fa'
Tsoro me tsananin gaske ta shiga na kwatanta halinda LEUL ya shiga a kwanakin batareda kowa da zai kula dashi ba a kwanakin musamman daya boye musu ya shiga tashin hankali da quncinsa shi kadai Ga kuma halinda Ammi take shiga ayanzu..
Zazzabi me karfi ma taji yana rufeta sosai dan haka kafafunta suka tsananta rawa ta kasa tsayuwa ta sake zubewa jikin maa sakinah tana jin mararta na wani irin murdawa da karfi take jini kawai ya balle mata.
Zuhrah ce ta fara lura da jinin dayake biyo kafafunta ta kalla da kyau tana bude baki cikeda sabon tashin hankali tace
'Me nake gani ni zuhrah?
Maa sakinah da tenya tare suka kalla inda take kalla take suka qarasa rikicewa da tashin hankali mai tsananin gaske sakinah na cewa
'Ciki ne fa a jikinta ita kanta batasan dashiba mun shiga uku ze fita?
Ita kanta Ammi dake kwance tana jin hakan yunqurawa tayi cikin wani irin karfin hali tana cewa ayi gaggawan kiran likitocin da aka tanadarwa masarautar suzo a taimaketa kada cikin ya zube indai shine da gaske.
Waya zuhrah ta fidda hannuwanta na rawa tenya kuwa da kanta zata bazata iya jiran kira ba sakinah kuwa riqota tayi hakama Ammin dole ta miqe cikin karfin hali suka kama Bahar din wadda jikinta ke rawa sosai tana jin wata irin azaba a mararta mara iyaka amma zuciyarta shi kadai takeson jin muryansa a lokacin.
Koda doctors biyu suka iso tafara jin jiki sosai wani zufa take fiddawa tana qanqame Ammi da azaba me tsananin gaske amma ta kasa bude baki tace komai.
Kiransa ne ya shigo wayar Ammi a lokacin wanda take itama ta kasa dagawa dan batason ya sani dan haka kasa dauka tayi suna jiran tsammanin jiran abinda likitocin keyi gurin tsaida cikin zullumi da fargaba.
A daidai wannan lokacin koina ya dauki tsit a masarautar boyem sbd lokacin fitowa da haile yayi zaa kaita bangaren azabar bayi acan zaa yanke mata hukuncinta ta hanyar rataya amma baa gaban jamaa ba sbd sirrinta yanayinta sbd yayanta wainda zuwa yanzu ma Aslam tana kwance jiri ya debeta ta sume tana bangarenta batasan inda kanta yake ba bayi biyu ne akanta.
Shiga akai fitowa da ita anan ne sultan duk da baya iya magana sosai ya bude baki ya nema mata sassauci daga NUAB wanda ya zubawa sultan din ido yana kallansa sbd yanda yake maganar cikin tausaya mata sbd yayansu da kuma zaman auren da sukai.
Dauke idanuwansa yayi daga sultan yana maidawa akan Asim wanda yake tsaya a gefensu idanuwansa jajir ya dago kansa ya sauke idanuwansa akan NUAB wanda shi yake kalla.
Shiru sukai dukkaninsu kafin Asim ya motsa ahankali ga tsananin mamakin NUAB da sultan da kadir dake tsaye takowa yayi cikin sanyi da nutsuwa ya inda NUAB yake zaune ya sai kawai yakai gwiwowinsa qasa ya zube da karfi gabaki daya yana yin qasa da kansa cikin bayyanarda mafi qasqancin yanayi a gaban dan uwansa akan mahaifiyarsa ya dago ya kalli NUAB din wanda yake kallansa da mamaki me tsanani da shock.
Sultan ma dayake kwance cikin wani irin mamakin da karfin hali ya miqawa kadir hannunsa yana son ya tadasa zaune yana son magana daqyar.
Shi kansa kadir shock din ya shiga sbd babu wani jinin boyem da duk duniya yake durqusawa wani idan ba ubangijinsa daya haliccesa ba gurin ibada.
Hannuwansa biyu yakai yana kokarin dafa kafafun NUAB zai bayyanarda tsantsan rokonsa akan sassauci wa mahaifiyarsa NUAB ya riqd hannunsa cak da karfin gaske yana kallansa shima nasa idanuwan suna ja sosai har hannuwansa suna rawa ya bude baki da yanayi me bayyanarda zafin abinda Asim din yayi yace
'Kada ka yadda ka sake durqusawa kowa duk duniya haka, Kai namiji ne da babu abinda zaka bayyanarda rauninka irin haka harka durqusawa waninka koshi waye'
Sakinsa yayi yana cikin zafi me tsanani a bayyane yana jin baqin cikin shedar da hakan ga wanda yake kalla a matsayin wanda zai mulki boyem.
Shiru dukkaninsu sukai sultan na kallan Asim din a karo na farko da wata irin tsantsar tausayawa me karfin gaske da kauna yana jin inama zai iya sauya kaddararsa zuwa me kyau da aminci ba irin wannan da mahaifiyarsu ta saka su a ciki ba gashi zata tafi tabarsu da kuncin da zai lalata rayuwarsu shikenan ba har abada.
Kadir NUAB ya kalla yace ya karbo masa sako a hannun Aleey.
Asim kasa dagowa yayi ya kalli mahaifinsa da NUAB din sbd jikinsa dake wata irin rawa kowace daqiqa dake wucewa ayau da bushewan jinin jikinsa take tafiya,da hankali da tinani da kwakwalwansa suke tafiya duka yana jin yana rasa kansa wanda bazai taba dawowa daidaiba.....
Zaunawa NUAB yayi tareda nunawa Asim din guri ya zauna ya dago ya kalli sultan wanda shi yake kalla ya bude baki cikin nutsuwa da sanyi da bayyanarda soft yanayinsa na tsananin kaunar jininsa da bai taba bayyanarwa kowa duniya ba hatta mahaifiyarsa batasan yanada wannan bangaren na tsananin son jininsa zuciyarsa sai ayau gaban mahaifinsa da dan uwansa dake kallansa suna neman alfarma da dukkanin sassauci da rahamarsa.
'Ka tin a ranar farko daka bani kurjeranka dan nayi mulkin qasarka ka roke ni alfarma daya daya akan 'danka Asim na inganta rayuwarsa na basa girma da matsayi da mutuncin daya kamace a karkashin mulki na, Ban baka amsaba sbd ban taba karban kujeran mulkin boyem da riqewa har abada ba, Shine yake da buri da shauqi da nacin mulkinta tin kuruciyar, A baya yana son mulkin ne sbd raayin mahaifiyarsa wanda matiqar yana bin kowace irin rayuwan da zata sakasa har abada bazan bari ya mulki boyem ba nima kaman yanda kaima har abada bazaka basa ba, Ayau sabon mutum ne a gabanmu, Ayau baya tareda kowane raayi na mahaifiyarsa saina kansa, Ya kasance me kishi da sanin darajar kai da fatan kawo sauyin cigaba a rayuwansa wanda hakan na nufin zai kawo cigaba da sauyin da ake nema ga alumma,
Mulki da sarauta ba nawa bane, Ba burina bane, Yanci da walwalata nake nema bayan kawo sauyi da cigaban da masarautar ke nema kuma wanda mahaifina yake fatan a kawo boyem na kawosu na sauya su dan haka kaddarata zata tsaya ne daga nan sbd zaman boyem da mulkinta ba nawa bane.,
Dawo da idanuwansa da sukai jajir yayi akan Asim wanda yake wata jijjiga me sanyi har lokacin sbd duniyarsa kowane second collapsing takeyi da wani sauti daya ratsa kunnuwansu su duka tsigar jikinsu suka miqe ya ajiye takardun daya amsa daga hannun kadir ya ajiye gabansa yace
'Bazan iya janye hukuncin mahaifiyarka ba sbd hukunci ne daya fito daga bangaren sharia da hukunci na saka hannu ne kawai, A yanxu babu wanda zai iya janye hukunta kaf duniya amma idan ka saka hannu anan a yanxu zaka zama sultan Asim Almazz zaka iya daga ranar hukuncin zuwa lokacinda zuciyarka zata iya dauka......
Shock ne me firgicin gaske ya shiga dukkaninsu a lokaci daya da sultan baisan lokacinda ya tashi zaune da kyau ba yana kallan NUAB din hannuwansa na rawa,
Kadir ma firgita ya shiga ya juyo gabaki daya yana kallan NUAB din,
Asim kuwa rinte idanuwansa yayi ya bude jikinsa bai dena rawa ba saima wata irin tsananta da yayi abin yana yawa kafin kowanensu yayi kowace yunkuri aka buga kofar bedroom din.
Aleey ne a tsaye idanuwansa jajir ya kalli kadir daya bude ya sanar dashi mummunan labarin daya zo dashi dan isarwa na rasuwan Haile wadda koda aka isa daukanta Allah ya mata rasuwa sanadin bugawan zuciya suke saka rai. #MAMUH 09033181070HAYATEEM Mamuhgee
173 Kaman saukan aradu haka kadir yaji zancen ya dakesa ya juyo da sauri ya kalli sultan wanda duka kofar suke kalla kuma sultan yaji abinda aka fada sbd hankalinsa da idanuwansa dake kofar dan haka rife idanuwansa da sukai jajir yayi a hankali yana jingina bayansa da gado hannuwansa na fara rawa kadan kadan.
Asim kadir ya juya da dukkanin idanuwansa ya kalli wanda ya zubawa takardar gabansa idanuwa yana jin babu komai na kaunar sarauta dayayi saura a zuciyarsa yanxu dan hakanne shima yake da raayin barin boyem yayi rayuwan da babu dauri a cikinta,
Takowa kadir yayi ya tsaya gaban sultan NUAB yana qasa da kansa cikin tsananin girmamawa ya bude baki da alhini yace
'Allah ya karbi rayuwar Queen haile koda akaje.......
Bai qarasa ba Asim ya dago cikin mugun slow na rashewan da duniyarsa ke yi a take ya kallesa yana miqewa da wani irin sauri ganinsa na daukewa ya juya baya ko ganin gabansa ya fice daga dakin koina nasa na jijjigar rawa me karfi.
Yana tinkarar bangaren nata da securities din da aka zuba suka janye sun bar bangaren ana cewa ta rasu sbd babu sauran abinda ya rage musu suyi
Wani sautin ihun kukan Meryam ne da nysah ke amsa kuwwa da amo tin daga nesa ya fara jiyowa kafafunsa suka fara neman sarewa daqyar ya iso bangaren yana shigowa a palonta na farko ya tadda gawarta a rufe gaban yan uwansa dake wani irin kuka me ratsa rai da kunnuwa da tashin hankali.
Zubewa yayi kan kafafunsa yana rintse idanuwansa hawaye na qafewa daga idanuwanta jikinsa na rawa cira ya rarrafo ya iso gaban gawar ya saka hannu ya bude fuskanta yana budewa ya saki rufar yana sunkuyar da kansa tareda dunqule hannuwansa dake fizga yana kasa dagowa.
Gabaki daya yan uwansa su ukun kuka sukeyi mai tsananin gaske kaman rayukansu zasu fita sbd iya su yayanta ne kadai suka sani tukuna dan an hana kowa zuwa bangaren.
Jikinsa Nysah ta fada ta qanqamesa tana kukan da sam bayajin komai shi sbd jinsa da ganinsa sun dauke dip na wucin gadi.
Babu wanda yayi yunkurin shigowa saida aka basu lokaci suna kukansu da tashin hankalinsu na farko tukuna aka janyesu ana ficewa dasu.
Acan ma dakin sultan bayan ficewan Asim kadir ya bude ido ya kalla yana buqatan a kawo wheelchair dinsa a ajiye a kusa sbd dole zaije gurin gawar haile yayi mata addua a matsayinsa na mijinta da harta bar duniya akwai aure a tsakaninsu.
NUAB kuwa shiru yayi yana kasa motsawa bare tashi daga zaunen dayake yana kallo Sultan ya saka kadir ya dauke takardar gabansa ya fice da ita dan qonawa sbd maganar saukansa mulki sam bama zata fita daga dakin ba bare wani yaji dan kuwa a yanxu babu sultan din da boyem take tsananin buqata da so kamarsa dan haka ko baya boyem matiqar yana raye NUAB bazai taba sauka mulki ba sai lokacin saukansa yayi hakama dole a yanxu bazaiyi zaman dindindin a anjom ba zai dawo boyem da Ayanah sbd su tsaya a karkashin mulkin 'dansu dan basa cikakkiyar albarkarsu a ko yaushe.
******kaman yanda masarautar take cikin shiru da jimamin halinda Sultan ya shiga haka ta sake daukan wani shirun na rasuwan haile wadda tini akace ayi shirinta dan janaizarta batareda bata lokaci ba dan babu amfanin sake kwananta a duniya ba rufeba akan tsarin musulunci.
Fadar irin mummunan halin da Yayanta suke ciki da iyayenta da Asim bame yiyuwa bane dan kuwa a abinda bai wuce awanni ba take suka sauya mummunar kama,
Suna ji suna gani akaiwa mahaifiyarsu sutura sai a lokacin aka turo sultan akan kujera baida kuzari ko kadan da lafiya har zuwa bangarenta cikin palonta gaban gawarta da aka gama shiryawa aka fito da ita,
Yayanta ne a zagaye da ita koda ya iso dan haka kowa ficewa yayi aka barsa daga shi sai yayan nata sukai mata addua.
Sun dan dauki lokaci a ciki kafin sultan ya fito aka turasa zuwa komawa bangarensa sbd bazai iya fita janaizar ba daqyar yake jan numfashinsa daidai ma.
Karfe biyar da mintina akai janaizar haile wadda ta tara dubban jamaa dik da anyi janaizar a lokacinda mutane ma basu gama ankarewa da labarin rasuwan tata ba.
Ankaita gidanta na gaskia an dawo kowa ya shige bangarensa sbd bazaayi zaman gaisuwan ba a bisa ga umarnin daya fito daga sultan yasar.
Shi kansa Asim ba iya matan kadai ba shima bangarensa ya shige ba shiga ba fita baya buqatan fitowa ko ganin kowa.
Leylah ce a tareda shi cikin tsananin damuwa da kulawa tana masa addua tana kokarin basa juriya da karfin zuciya da basa addua sbd kada damuwa ta sakasa mantawa da riqe fadan Allah a bakinsa.
Haka aka wuni a masarautar tsit kaman ba rasuwa akaiba tin karfe 8 da mintina kowane sahu ya dauke a cikin masarautar gabaki daya babu motsi ko sautin komai.
NUAB yana bangaren mahaifinsa tareda shi saida ya tabbatar angama basa dukkanin kulawan daya kamata dasu maganinsa tukuna ya fito ya fice zuwa bangarensa ya nufi bathroom kai tsaye ya cire komai na jikinsa ya sakarwa kansa ruwa yana rufe idanuwansa ahankali yana sauke numfashi me dumi sbd daga karshe Allah me iko yayi yanda yakeso ga duka wanda yaso.
Yana fitowa wanka shirin bacci yayi ya haye lafiyayyan gadonsa ya dauki wayarsa dake kan gefen gadonsa ya nemo numbern ghaz princess ya saka kira.
Bata shiga ba dan haka bai damuba ya sake saka kiran har so kusan biyar amma sam kiran baya tafiya,
Time ya juya ya kalla yaga dare yayi dan haka bazai kira maa sakinah ba yaji ko lafiya baya samunta zai bari sai gobe tukuna duk da a yanzu sun saba babu daren da suke iya bacci batareda sunyi magana ba ko a wannan kwanakin dayake cikin damuwa da tension babu daren da basa waya.
Ajiye wayar yayi yana kwantawa ahankali tareda rufe idanuwansa cikin nutsuwa yana sake fidda numfashi da ajiyan zuciyar da tin rana yake saukewa baisan dalili ba.
A daidai wannan lokacin kuwa acan anjom likitoci sunyi nasarar tsayar da ciki bahar din dayake kokarin zubewa cikin ikon Allah,
Su Ammi dake cikin tashin hankali kashi kashi suna jin an samu tsaida cikin ajiyan zuciya suka ringa jerowa a tare suna godewa Allah musamman Ammin datake jin kaman wani barin jikin nata ne zata sake rasawa idan ta rasa jinin dayake asalin jininta dana Abaas kaman yanda suke fada dan kuwa hada yayansu aure ba shine asalin hada zuriarba abinda zaa haifa dinne.
Bacci mai karfi ne ya sauke Bahar din bayan azababbiyar wuyar data sha wanda ta dauka itama mutuwan zatai,
Bayan wucewan doctors din da gama fada musu hutu sosai na kwana biyu take buqata cikin ya sake tsayawa daidai ba abinda take buqata sai cire damuwa kwata kwata daga ranta.
Suna tafiya shiga dakin Ammi tayi tana isa bakin gadon da bahar din ke kwance tana bacci ta zauna tana dafa goshinta tareda shafawa tana jin tsananin kaunarta da tausayinta na wahalar datasha.
Tenya ce ta kwashi kayan jinin da aka lalata sosai ta fita dasu ta bawa su Naima su wanke.
Basu iya fadawa NUAB abinda ake ciki ba dan haka suma boyo suka hau sbd hana sabon tashin hankalin da zasu iya gani idan ya sani.
Kulawa da wani irin tattali na musamman aka fara nunawa bahar din wadda bata farka ba sai asuba,
Maa sakinah ce ta kwana tareda ita dan haka ruwan wanka masu zafi ta hada mata ta shiga ta dan gasa jininta ta jima kafin ta fito ruwan tayi wanka da alwala ta fito tayi sallah tana idarwa tea me zafi da baa saka shuga ba sedai zuma aka kawo mata da naman da aka dafa mata tin dare akai warming taci kadan tasha magani ta koma ta kwanta take wani baccin ya kuma dauketa.
Koda garin ya waye har rana Bahar na bacci dan haka suka sake tsayuwa akan kulawa da ita da cikin da yanzu shine hankalinsu ya taallaka akai,
Ammi ma hankalinta a rabe biyu yake matiqar gaske sbd bugun zuciyarta ya kasa dawowa daidai idan ba sultan taje ta duba yanda yake ba.
Su kansu su maa sakinah da suka fahimci hakan kuma ko babu komai tana tsananin buqatan kasancewa dashi a wannan lokacin da baida kowa a cikin matansa sai ita ga rashin lafiya dan haka maa sakinah ta nuna mata ta wuce boyem din kawai ita zata tsaya da bahar har saita warke sosai dan babu yanda zaayi doguwan tafiya da ita a wannan halin datake ciki.
Su zuhrah ma hakan sukaga ya kamata dan haka suka karfafa tafiyan tata,
Ita kanta Bahar tana tsananin son Ammin ta tafi sbd sultan da NUAB suna buqatarta.