Kenza eBookz

Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee - Chapter 70

Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee - Chapter 70

Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 70: Hayateem book 1 And 2 complete by mamuhgee Chapter 70. Bikin da zaayi din baa wani dabbaka sa ba sbd…

1,236 words

Bikin da zaayi din baa wani dabbaka sa ba sbd biki ne na buqatan shigowan kusrawa kuma cikin saa sai gasu sun kawo jiki sedai babu khams a cikinsu ko yaransa sbd duk sun manyanta wasu ma sun mutu gabaki daya basuda wani yawa yanzu sunyi ta haduwa da kaddarorinda shi kansa khams din baida hannu daya a yanxu.

A hakan ana gama bikin aka tattara duka wani kusra da wainda ma basu zo ba kaman khams kenan aka yankewa duk wani jinin kusrawa hukuncin bauta ta rai da rai maana zama bayi har qarshen rayuwarsu da karshen jininsu a duk inda suke na qasar boyem da zagayenta.

Wannan hukuncin ya saka da yawansu rasa ransu sakamakon neman guduwa daga asalin garinsu da NUAB ya bada umarnin duk wanda ya nemi guduwa ko gardawa a cire kansa daga wuyansa.

A cikin manyan askarawan da aka tura kusrawa haka suka rikita garin gaba daya suka ringa yiwa maza fyade sbd basa buqatar matan.

Yayan khams su hudu maza haka aka kwantar dasu a gabansa akai musu mummunan fyaden da dayan a take a gurin ya rasu yana kallan mahaifinsa da bai iya motsawaba sbd zuciyarsa data buga take a gurin ya mutu a zaune baa saniba.

Mutuwan shugaba khams ya saka duk wani kusra yayi surrender suka karbi kaddararsu da hukuncinsu akan zama bayin boyem har qarshen zuriarsu.

*****Bayan gama duka wannan abubuwan komai ya lafa duniya ta sake samun lafiya take Mai girma SULTAN LEUL NUAB ALMAZZ BOYEM ya sake bude kofofin gudanar da lafiyayyan mulkin kwanciyan hankali da cigaban qasarsa da koina ake tsananin alfahari da farin cikin samunsa a matsayin sultan na qasar.

Duka yanda yake a matsayin sarkin dake mulkin qasa guda bai taba rasa damar zuba zazzafar soyayya da queen dinsa ba wadda gabaki daya zarewansu sukeyi suna mantawa da mulkin dayake kansu idan dai suna tare.

Rayuwar aurenta takeyi kaman kowace mace itace take girkinda mijinta xaici da kanta duk kuwa da tarin bayin da suke dashi a bangaren nasu.

Yanzu da iyayensu basa tareda su itada leylah tsananin kaunar junansu sukeyi da zama aminan juna kaman yanda shi kansa NUAB Asim ne ya zama amininsa na farko bayan Aleey da keelah wainda suke ba iya yaransa ba kadai Aminansa ne abokansa da suke family dinsa.

******cikin leylah ne ya fara isa haihuwa dan haka ta tattara ta koma anjom haihuwan dan ko zuhrah na can ta koma da zama sbd yunar ma ya koma kuwait bayan angama hidimar komai amma idan zai dawo dole zata tattara ta koma boyem tinda itama ta dawo boyem din kenan tinda yana can yana kuwait yanzu sbd dansa shuraim daya shiga sarautar shima gadan gadan.

Bayan tafiyar leylah da wata daya ta haifi baby girl da masarautar boyem kaf ta dauki murna da farin ciki musamman su Aslam dake gap da aure ansamu dai sultan NUAB ya bada aurensu ga manyan fada biyu manya.

Bahar ba irin yanda taso tafiya amma NUAB kai tsaye ya hana hakama su Ammi ma sunata son daman kada taxo din tana fama da tsohom cikin.

Gagarumin suna akai na HAILE ASIM ALMAZZ BOYEM wadda ake kira da NURAT wadda mahaifinta ke tsananin sonta fiyeda kowa da kansa da duka abinda ya mallaka.

NUAB da kansa ya taka har Anjom da muqarabansa ya dubo Nurat tareda zube mata kyautar zinari me yawan gaske.

Yana dawowa daga anjom haka ya dauke matarsa suka tafi Moscow sbd tata haihuwan.

Sun isa suka bude babin sabuwan soyayya da rayuwanda suke so ko sati uku basuyiba nakuda ta taso mata suna cikin love dan haka a rikice sukai asibiti yana riqe da hannunta yana zuba mata kiss motsi kadan.

Kusan dashi akai labour din bayan isarsu asibiti sbd shine yake bata karfin gwiwa yana kissin duk inda ya samu a fuska da lips dinta har aka samu ta haihu bayan doguwan naquda ta wuni daya.

MUHAMMAD ABAAS NUAB ALMAZZ shime sunan da mahaifinsa ya ambacesa dashi bayan an miqo masa shi bayan fitowansa duniya yana jin kaman duka can baya duniyarsa bata cika ba sai yanzu da hannuwansa suka dauki gudan jininsa a jikinsa wanda babu abinda ya baro nasa na kamanni.

Ita kanta bahar bayan ta dawo daidai data daukesa kasa dauke idanuwanta tayi daga kansa tana kai bakinta tayi kissing din goshinsa tana dagowa daddynsa ya sauke mata kiss me nutsuwa itama a nata goshin yana rugumesu gabaki dayansu yana tabbatarda sune rayuwa,bugun zuciya,ruhi da hasken kalbim dinsa.

Sati biyu sukai a Moscow likitoci suka gama tabbatar masa da lafiyarta data 'dansa kafin suka tattaro suka dawo wanda tini su Ammi dukansu sun tattaro sun dawo boyem din suma kenan.

A tsakanin Ammi da maa sakinah rasa waye yafi jin kaman zuciyarsa ma bazata iya daukan farin ciki ba akai a cikinsu.

Sultan yasar aka kaiwa shi ya dagasa ya rungume a jikinsa ya sumbacesa yayi masa adduoin da yayiwa mahaifinsa ranar da aka haifesa shima aka kawo masa shi kaman irin hakan.

Tarin zafafan danyan zinari aka fara kawowa daga koina da duniya daban daban ga LEUL MUHAMMAD ABAAS wanda duniya ta dauki haihuwan da tabbatar dashi a matsayin da mafi daraja a qasar boyem yanxu da mahaifinsa yake sultan.

Anyi taro da hidimar bikin sunan MUHAMMAD ABAAS an zubar da dukiya anyi barin zinari da hatta Aleey kadai dukiyar daya zubar ya ringa bayarwa tukuicin wannan haihuwan da shine akaiwa bazata fadu ba gashi shima anata kokarin fara hidimar bikinsa da zaaje uk ayo da neesah a kawo masa ita nan boyem a babban bangaren da ubangidansa ya gina masa a kusa da nasa.

Bayan gama sunan Muhammad da wata biyu cif suka tattara uk dukansu hadda su Ammi da sultan da kusan kowa bikin aleey da amaryarsa neesah wadda suke tsananin farin cikin kasancewa gidan aure daya itada aminiyarta.

Ana gama bikin kowa ya dawo banda uban gayya me boyem daya wuce Moscow da matarsa da tinda ta haihu baa basa itaba tana bangaren Ammi sai yanzu iyalinsa suka dawo hannunsa.

Wannan karan kaman yanda suke cin wani lafiyayyan amarci da zuba rayuwa haka aleey yake zubata da tasa.

Basu koma boyem ba saida sabon cikin neesah dan haka suna komawa dole da bahar da neesah din aka dawo da karatunsu a qasar boyem din sbd sultan NUAB dai bazai iya zama a qasar da babu matarsa da 'dansa ba. Daganan sai muce ALHAMDULLH. #MAMUGEE 09033181070 HAYATEEM NA KUDI NE

ALHAMDLLH ALHAMDLLAH ALHAMDLLAH

MUN GAMA LAFIYA INSHA ALLAH KAMAN YANDA MUKA FARA LAFIYA INA ROKON ALLAH YA YAFE KURAKUREN DAKE CIKI DA MUKA AIKATA,LADAR KUMA IDAN AKWAI ALLAH YA RABA MANA GABAKI DAYA AMIN.

KAMAN KOYAUSHE INA FATAR BAZAKU CE KOMAI GAMEDA KAMMALAWAN BA SBD BAYAN HAKAN BANSAN ME ZAMU CIGABA DA RUBUTAWA BA TINDA LABARIN DAI DA KANSA YA QARE SO PLS KADA KUCE ANGAMA DA WURI KOKUMA BAKUSO AKA TSAYA BA ANAN,

INA MIQA GODIYA DA KAUNA A GAREKU DA KUKA KASANCE DANI HAR KARSHENSA ALLAH YA SAKA MUKU DA MAFIFICIN ALKHAIRINSA, ALLAH YABAR KAUNA YA SAKE BAMU IKON KASANCEWA TARE A CIKIN SABON NOVEL DA ZAMU FARA BAYAN SALLAH INSHA ALLAH IDAN ALLAH YA BAMU IKON KAIWA CIKIN LAFIYA DA ABINCINSA.

MY ECHOES PEOPLE ALLAH YABAR TARE INA MUKU SON SO,LOVE YOU OVER, MY AREWABOOK/AREWAPEN ALLAH YA BIYAKU KUMA LOVE YOU LODI LODI,

YAN BATI MA ALLAH YABAR KAUNA YASA KU SIYA NEXT DA KUDINKU KU DENA WAHALA KUNA WAHALAR DANI LOL.

THANKS MAMUHGEE 09033181070

Readers Also Read