Heedayah complete Novel - Chapter 11
Heedayah complete Novel Chapter 11: Heedayah complete Novel Chapter 11. Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... 9/12/21, 8:04 PM - ,:…
2,115 words
I don't have complete Heedayah pls fans... Sae dai in aron brain din Khaleesat Haiydar xan baku ku shiga ku karance tass, I made jest of those that are not patronizing鈽癸笍 sae dai su karanta a titi suna jiran su samu complete... and a lot of pple are thinking da gaske ne akwai complete din, to nima kullum nake typing din ban san ma me xai faru a karshen ba馃槃馃槃 Lol.... patronize ur novelist lovely fans, ni ban iya Allah ya isa ba, amma kuyi patronizing for the sake of Allah coz it's not free.... And ina xumunci da duk wanda ya siya Novel dina, bana goge lambarsa....
Meanwhile ina son jan hankalin readers sau daya nake posting a rana which is 5 to 6 read mores everyday, in har nayi less than 5 read more may be 3.... To xan yi post da daddare in cike read mores din.... Stop expecting more than that all my books haka nake yi. Thanks lovely fans
Heedayah isn't free, you read for free 馃し馃徎鈥嶁檧锔�
it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah
Chapter notes and social links
Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... 9/12/21, 8:04 PM - ,: Shuraim bai saurareta ba har ya isa motarsa ya bude back seat ya jefata ciki ya kulle sannan ya xaga ya bude maxaunin driver ya shiga, tuni Mai gadi ya bude masa gate ya fita gidan, Har ya isa kofar gidan Baffa bai kalli Heedayah dake bayan mota ba, ta rungume hannu kamar xata yi kuka, a compound din gidan yyi parking, sai a sannan ya kalleta ta madubi, ya wani hade rai kamar tana ganinsa, d'an tsaki ya ja ya bude motar ya sauka sannan ya bude mata side dinta yace "Fito min a mota" Ta make kafada a hankali tace "Ni ka maidani wajen Mami baxan fito ba...." Yace "Kee.... an ta6a xaneee ki???" Bai jira cewarta ba ya jawota ya fiddo ta daga cikin motar ya ajiyeta kasa ya rufe motarsa yace "Idan ina magana kina yi sai na fasa maki baki wllh...." Ta fashe da kuka sosai tace "To me bakina yyi maka, ni bana sonka you are wicked...." Sudais ya hango ya fito daga cikin gida, hakan yasa ya kai fuskarsa dai dai nata yace "Xa ki san I am wicked soon...." Daga haka yyi wucewarsa ya bar ta nan a tsaye, yana kai wa inda Sudais yake, Sudais yace "why are you leaving her all alone, how did u expect her to walk alone" Shuraim yace "Toh ni d'an jagoranta ne aka ce maka??" Bai jira cewar Sudais ba yyi wucewarsa ciki, Sudais ya karasa inda take da sauri ya kamo hannunta ya duka yana kallon manyan idanuwanta da ya cika da hawaye yace "What happened cutie..." Cikin rawar murya tace "I hate him...." Sudais ya rungume ta yana goge mata hawayen idonta yace "Noo cutie cry no more, mu tafi ciki ki gaida kaka...." Kamar ko jira take ta fashe da kuka sosai, rikicewa Sudais yyi ya shiga lallashinta, har sai da ya ga tayi shiru tana sauke ajiyar xuciya, lkci daya ya ji ransa ya baci, ya mike ya kama hannunta suka wuce ciki, parlon kaka ya tadda Shuraim, Kaka sai harkar gabanta take tana 'yan wake wakenta na tsofaffi ko kallonsa bata yi ba kamar yanda shi ma bai kalli inda take ba yana danna wayarsa, Sudais na kallonsa fuska daure yace "Shuraim why will you leave the innocent girl all alone...." Shuraim yace "Plss Sudais don't question me, I am not ready to answer you..." kaka ta ajiye tsummar hannunta tace "Me ya faru Sudess?" A fusace Sudais yace "Kawai barin yarinyar yyi ita kadai a tsakar gida ya san ba gani take ba, what sort of nonsense is that" Kaka ta nemi waje ta xauna tayi tagumi a hankali tace "Ohh naga abinda ya isheni ni patuuu, Kai amma dai Amadun ne gantalalle wllh, me yasa xai hada baiwar Allah da bata san komai ba da wannan katon mutumi, wato Amadu ya raina mugun halin d'an nan nasa koh? Bai san abun ya wuce misali ba, ya wuce hankali ya dauka ba ko, Wllh shuree yake ko wa?? ba shi da xuciya me kyau ina fada kuna ganin kamar wasa nake, Baka ga ko gaisheni bai yi ba da ya shigo yana jiran ni in gaishe sa d'an banxa, ni dai ba ruwana don na haifi ubanka ba yana nufin ina da wani alaka ko dangantaka da kai bane, kayi ta kanka inyi ta kai na, makauniya kuma sai Allah ya saka mata tunda bata cuce ka ba...." Sudais dai sai hararan Shuraim da yyi kamar bai san suna yi ba a parlon yake, wayarsa kawai yake dannawa, kaka ta kamo hannun Heedayah ta xaunar da ita saman kujera tace "Sannu da xuwa Deedaya, ai da kyau tunda ba a titi ya gantalar da ke ba yyi wucewarsa ya ja ma d'a na fitina, haka nan muke fama da shi da mugun halinsa, mu ma ba kyale mu yyi ba, Bai san ba sonsa Allah ya fi yi da ya bar sa da idanuwansa ba ke kuma ya barki bbu idanuwa, shi fa Allah ba ruwansa gobe Shuree na iya tashi ya gansa a duniyar makafi to sai yyi yaya??" Tsaki Sudais ya ja ya fice daga parlon, Shuraim ya bi sa da wani kallo ta gefen ido, Kaka ta bude fridge ta fiddo malt ta bude mata tace "Wnn yaron kirki Junaidu ya xo jiya ya kawo min su da yawa, to bai fiye min wasu ba Allah na tuba, bbu abinda fa na hada da shi, kawai dai babarsa na auren d'a na ne, amma ko shekaranjiya sai da ya xo nan gaisheni muka yi ta hira gwanin ban sha'awa, to wasu ma idan suka xo sai dai su dinga tunanin ynda xa su cuceka kafin su wuce.... To ni dai bbu ruwana" A hannun Heedayah Kaka ta saka malt din, Heedayah ta fara sha a hankali tana lumshe ido, Kaka ta xauna tace "Toh madallah, yau dai na gama aikin da wuri, na gode ma Allah" Shuraim ya kashe wayarsa calmly yace "Ina yini Kaka?" Tace "Lafiya lau wllh, ai tun safe sae ynxu na gama kimtsa ko ina, baka da lafiya ne na ganka duk wani iri yau?" Yace "Lafiya ta lau" tace "Atoh naga duk ranka a bace ne ai, ko kai ma in kawo maka mantinan ne?" Ya girgixa kai kawai, tace "Toh in xubo maka abinci, shinkafa ce dai da miya" nan ma ya girgixa mata kai, tace "Toh ban da abinka meye na bacin rai kuma Mai gida, da shi Amadun yace ka kawota nan sai kace masa gaskiya kai kana da wajen xuwa, ae ba ajiye ka yyi ba, ban da neman magana irin tasa kai xai sa kayi ma yar makauniyar direba, shi da ya jajubo ta ba sai ya kawota da kansa ba, ni ba ruwana bana son rashin gaskiya, abu dai ba ayi tsakani da Allah, ae baxa ka rasa uxurin gabanka ba kai ma" Mikewa Shuraim yyi ya dau bottle water daya a fridge yace "Xan shiga in gaida su Umma" Kaka tace "Toh sai ka dawo, sai dai yau ko yar kazan nan ba a kawo min ba Mai gidan, ko da yake ina xaka kawo min kaza an hada ka da yarinya ba dangin iya balle na baba...." Fita yyi parlon, kaka ta tabe baki ta mike ta dau tsumman ta ci gaba da goge gogen da tace ta gama, Heedayah na gama shan malt din ta jefar da can din nan parlor, kaka ta leko daga d'an kitchen dinta tana kallonta tace "Ehh lallai, to sauka ki dauke ki fita da shi bola, ae ni ba baiwar Amadu bace balle ke" Heedayah ta sauka da sauri ta durkusa tana laluba Inda xata ji can din, kaka tace "Laluba gefen ki maxa ki dauke ki fitar min da shi ni ba yar bola bace, kaji min yarinya in mata inuwa tayi min rana, duk gidan nn bbu wanda na bai wa mantinan nan sae ke, shine xaki walakanta min parlor" Heedayah ta samu ta dauke can din ta mike duk a tsorace, a hankali tace "To bana gani" kaka tace "Hagun ki xa ki bi ki fita, ni xa kiyi ma karya kice ba kya gani" dai dai nan Sudais ya shigo parlon, kaka tace "Kaji wai xata je ta yarda gwangwani ta ja min salalan siya wajen Amadu Sudess...." Tsayawa Heedayah tayi tana kalle kallen kamar mara gaskiya, Sudais ya kama hannunta suka fice daga parlon, kaka tace "A'a, yau ga ikon Allah, ya xan ce a kawo min yarinya takanas kuma ka xo ka dauketa Sudess" tuni Sudais ya kulle mata kofarta, ya wuce xuwa dakinsa yana rike da hannun Heedayah, Heedayah ta ta6a hannunsa tace "Waye kai?" Ya kai bakinsa kunnenta yace "Heedayah ne ni" tana jin muryar sa ta washe hakora tace "Baka bani sauran chocolate dina ba" yace "Shi xan je in baki yanxu" ta kankame hannunsa tace "Mu tafi gida wajen Mami da kai sai mu bar wnn mugun a nan plss" dariya yyi ya wara ido yace "Da gaske" ta gyada masa kai tace "Ehh I don't like him, shi mugu ne...." Bude kofar bedroom dinsa Sudais yyi yace "To gaya min me da me yyi maki" Shuraim dake kwance saman gadonsa ya juya yana kallonsu, tace "Komai ma yana min ai, first ya fara buge min hannu don yaga bana gani, kuma Abba yace ya min karatu ya ki yyi min..." ta girgixa kai tace "Noo... I just don't like him, and I will never like him...." Dariya Sudais ke yi yana kallon Shuraim da ya mike xaune fuskarsa a daure yana kallonta, Sudais ya dagata ya xaunar gefen gado yace "Toh kin gaya ma Abba abinda yake maki" tace "Yau duk xan gaya masa ae, har da duka na da yyi...." Ta wara ido tace "Ae kai ma ka iya suratul jinnnn Koh?" Ya gyada kai yace "Sosai ma" tace "Toh mu tafi gida da kai sai mu bar sa wajen matan nan me yi ma mutane fada" Sudais yyi dariya yace "Sunanta kaka" tace "To mu bar sa wajen kaka shi, bana son ya bi mu" Gaba daya Shuraim ya kasa cewa komai, Sudais na kallon manyan idanuwanta yace "Toh xa mu bar sa a nan mu tafi gidan tare kin ji cutie" ta washe hakoranta tace "Toh ina chocolate dina" mikewa yyi yace "Bari in dauko maki" Sai a sannan Shuraim ya fixgota da karfi yace "Uban waye mugu?" Sosai ta tsorata jin muryar sa, ta fasa ihu tana son kwace kanta, Sudais ya dawo da sauri yace "Don't you dare touch her, don't try that" yana fadin haka ya dauke Heedayah da jikinta ke rawa a wajen, ta kankamesa cikin rawar murya tace "Take me away plss" ficewa Sudais yyi daga dakin nasa ya kulle kofar trying hard not to laugh. Mumy ce xaune parlon Hajiya Sadiya tayi tagumi, Hajiya Sadiya tace "Anya kina ganin baxa a xarge ki ba Maryam, hakan yyi wuri ai wllh, ki bari kawai mu lallaba ayi duk abinda xa ayi a samu ki koma dakin ki, kinga idan kina gidan ko ma me ya faru bbu wanda xai xarge ki bbu wanda xai kawo ki a rai, amma yanxu fa?? ai daure kanki kawai xa kiyi, barin mijin ki barrister, kishiyar ki barrister" Mumy tace "Nima wllh tunanin da nake kenan, gaskiya kika fada, bari a share wnn batun ynxu kawai...." Hajiya Sadiya tace "Yauwa, yanxu kina komawa nunawa xa kiyi kin fi kowa sonta ma a gidan, kiyi iya bakin kokarinki ki danne komai a kasar xuciya ki, ita kanta kishiyar taki ki d'an fara sake mata kuna gaisawa yanda bbu wanda xai samu damar xargan ki nan gaba, karatu kuma kiyi ta tausasa Shuraim yyi mata, yaranki duk ki sa su dinga shiga gun kishiyar taki su dinga jan makauniyar a jiki, wllh duk kika bi shawarata komai xai xo mana da sauki Maryam...." Mumy tace "Kai da bani da ke da nayi Kuka Sadiya, nagode aminiyar kwarai Allah ya bar xumunci, amma ita wnn tsohuwar kuma ya kike ganin xan yi da ita in huce takaicin annamimancin da ta min" Dariya Hajiya Sadiya tayi tace "Ke wa ke sa wnn ta6a66iyar a lissafi, ba fa isasshen kwakkwaro gareta ba, ynxu dai muyi concentrating a abinda yake gabanmu ki ajiye batun wnn tsohuwar" Mumy tace "Toh shkkn, ynxu dai bari inje gida wajen Salima in ji ita kuma ya ake ciki, daxu na kirata tace da yamma xata koma gida, bari in je in dawo" da haka suka yi sallama Mumy ta bar gidan Hajiya Sadiya.