Kenza eBookz

Heedayah complete Novel - Chapter 21

Heedayah complete Novel - Chapter 21

Heedayah complete Novel Chapter 21: Heedayah complete Novel Chapter 21. Khaleesat ma dai da turarurrukan take amfani wllh, trust me it's nice and very…

2,875 words

Khaleesat ma dai da turarurrukan take amfani wllh, trust me it's nice and very affordable.... 馃槏 9/12/21, 8:04 PM - ,: Shuraim na xaune bedroom dinsa hannunsa rike da wayarsa yana dialing number wani colleague dinsa, bayan sun gaisa Shuraim yace "You called bana kusa Najeeb" Bayan few seconds Shuraim yace "Ehh na sani, I will be there soon in sha Allah" Daga haka suka yi sallama ya katse wayar, mikewa yayi yana kallon agogo dake nuna karfe goma da few minutes ya fita dakin, kitchen ya fara shiga ya hada shayi sannan ya fito ya nufi part din Mumy, duk wutan parlon a kashe yake da na dakinta, daga can uwar daka cikin muryar bacci tace "Waye wannan?" Yace "It's me Mumy, kinyi bacci ne?" Tace "Toh me xan jira" yace "Okay, Xan wuce hospital ne ynxu in sha Allah" Tace "Okay are you spending the night there?" Yace "No xan dawo anjima" Ta mike xaune da sauri tace "Karfe nawa yanxu da xaka je asibiti har ka dawo, why not spend the night there, ni bana son tafiyar daren nan gaskiya" Ya d'an yi shiru sannan yace "Toh shkkn sai da safe" Tace "Allah ya tashe mu lafiya, pray before leaving" yace "In sha Allah" daga haka ya fita parlon ya kulle mata kofa..... Abba ya gani xai shiga bangarensa, Abba yace "Ohk Baka tafi ba?" Shuraim yace "Yanxu xan wuce" Abba yace "Alright sai da safe" Shuraim yace "Allah ya kai mu lfya Abba" daga haka Abba ya shiga part dinsa, Shuraim ya xauna parlor ya gama shan shayin hannunsa ya kai cup din kitchen ya dauko makullin motarsa ya fita gidan, sai bayan da Mai gadi ya bude masa gate ya bar compound din ya tuna da rigar sanyinsa don garin da sanyi kuma ko kadan baya son sanyi, yyi parking a nan kofar gidan ya sauka motar ya koma cikin gidan, bedroom dinsa ya tafi ya dauko rigar sanyinsa sannan ya dawo parlor, har ya nufi kofar fita sai kuma yayi hanyar dakin kaka ya bude kofar, a kashe ya ga wutan dakin, ya danna hasken wayarsa that's so dim yana kallon dakin, Kaka na kwance hannunta rike da carbi tana bacci har da minshari, ga mamakinsa idon Heedayah biyu tana kwance lamo saman gadon, ya karasa cikin dakin yana haska fuskarta, mikewa tayi xaune jin motsi, a hankali tace "Mami" shi dai yana tsaye yana kallonta, Ta sake cewa "Mamii" Kaka ta gyara kwanciya tace "Kya ci kanki" daga haka ta ci gaba da baccinta, tuni Shuraim ya kashe hasken wayar sai da ya ji ta ci gaba da minshari sannan ya kara haska dakin, Heedayah dake xaune fuskarta kamar xata yi kuka cikin sanyin murya tace "I want to take tea plsss" Juyawa yyi ya fita dakin ya kulle kofar a hankali, sannan ya bar gidan, slowly yake driving har ya bar anguwar gaba daya. Tun tafiyar Shuraim Heedayah bata koma ta kwanta ba, har da d'an hawayenta tana gogewa da bayan hannunta, duk motsin da tayi sai kaka ta gyara kwanciya tace "Kya ci kanki" ita dai ba sanin nufin Hausan ma tayi ba, tana xaune har sha biyu saura ta ji an bude kofar dakin.... Sai kallon direction din take ta ji an kamo hannunta, ta mike tsaye tana tattaba hannun tace "Mami ke ce, I want to take tea..." Kaka ta tabe baki ta gyara kwanciya tace "Kya ci kanki dai" fitar da ita aka yi dakin still holding her hand, ba musu take tafiyar har sannan tana laluba hannun da ya riketa, sanyin da taji na shiga jikinta sbda yar rigar jikinta yasa ta fixge hannunta tace "Ina xa mu je??" lkci daya aka dauketa xata yi ihu aka rufe bakinta gamm, bata kuma yunkurin yin ihun ba, next thing taji an saka ta a mota an rufe, motar na fara tafiya ta kwala ma Mami kira, nan ta dinga ihun Mami da karfi amma ba a ce mata komai ba, ta gaji tayi shiru, can ta fara laluba cikin motar har ta ji ta ta6o me tukin, a hankali tace "Who are you??" Jawota yyi ta fado kansa ya maida ta front seat, kin sake sa tayi ta kai fuskarta jikinsa perceiving his perfume, yyi parking ya dau goran ruwa ya bude ya kai bakinta, rike goron tayi hakan ya sa ya sakar mata, ta d'an kurbi abun ciki, bata sauke goran ba sai da ta shanye content din ciki tas, shi dai driving dinsa kawai yake slowly, ta kai hannu tana ta6a sa bayan ta ajiye goran tace "Who are you?" Bai tanka ta ba, tace "Kai Yaya ne?" Still ba a ce mata komai ba, ta kara cewa "Yayah?" Nan ma shiru, driving kawai yake avoiding check points a hanya, har dai ya isa wani layi, kallon gate din layin dake kulle ya dinga yi, can ya gyara parking ya kashe motar yana kallon Heedayah, lamo tayi kan kujeran idonta rufe har ta fara bacci, ya bude side dinsa ya fita ya xaga xuwa inda take ya bude motar ya daukota ya daurata saman shoulder dinsa, ta bude ido a hankali sai kuma ta kara lumshewa, ya shiga layin ta karamin gate, har dai ya isa bakin wani gate ya tsaya ya ciro makulli aljihunsa ya bude gate din da hannu daya ya shiga sannan ya kulle gate din, ginin bungalow ne me girma, ya bude parlon shiga gidan da makulli ya shiga, yana bin ko ina da kallo ya wuce daki, bbu bedsheet saman gadon da ya d'an yi kura ya bude press ya fiddo wani xanin gado yayi spreading dinsa with one hand ya kwantar da ita gently, bude ido tayi sai kuma ta mike xaune da sauri tana hade kafa tace "I want to ease my self" tsayawa yyi yana kallonta kamar bai gane turancin da tayi ba, ta fara kokarin sauka daga kan gadon tace "I want to urinate" ya kalli kofar bathroom dake cikin dakin sai kuma ya kama hannunta suka wuce ciki.... Bayan sun fito tana rike da hannunsa tace "Shikenan mun bar kaka a can gidansu Mami, she will be looking for me faaa" Ji tayi ya kwantar da ita saman gado, ta yi rub da ciki ta lumshe ido, bude idon tayi da sauri jin an daga rigarta tace "Yayah" Lkci daya taji xafin shigan alluran xata tashi a tsorace ya ki barinta hakan yasa ta fashe da kuka tana kwala ma Abba kira, yana gamawa ya mike ya kashe Ac dake dakin ya kunne fan ya kashe wutan ya fita dakin ya kulle ya bar ta tana kuka. Tun karfe daya saura Mumy ke xaune dakinta idonta kyam, ga wayarta a hannunta, wayar ne yyi haske ta daga ta kai kunne da sauri, lkci daya ta mike tace "Har kun taso, to bari in je in bude gate din" tana fadin haka ta katse wayar ta mike ta tafi gun window tana kallon tsakar compound da yayi tsittt, a hankali ta bude kofar dakinta ta fita har xuwa main parlor, sai da ta gama kare ma parlon kallo sannan ta nufi kofa ta bude a hankali ta fita, gate biyu ne gidan, daya a baya, daya kuma a gaba, sai dai an fi shekaru biyu ba a bude gate din bayan ba, can Mumy ta nufa tana yi tana dube duben tsakar gidan duk da tasan kowa na gidan na bacci har masu gadi, tana isa gate din taji sa a bude, she was so very suprise, ta leka wajen gate din, bbu kowa layin sai street light da ya haska ko ina, to wa ya bude gate din, ko dai dama a bude yake all this while ba'a ta6a lura ba, but this is suprising, jawo gate din tayi a hankali amma bata yi jamming ba ta juya da sauri ta koma cikin gidan.... A parlor ta ci karo da kaka, gabanta yyi wani irin faduwa, Tayi hanyar kitchen da sauri pretending kamar daga kitchen din ta fito, Kaka da tayi kicin kicin da fuska tace "Maryam kina ganin wannan kishiyar ta ki ko? Halan bata sanni bane bata san halina ba, wllh xan tara mata jama'ah idan bata fita hanyar Deedayah ba a gidan nan, meye xata bi dare ta shigo ta dauke ta kamar ita ta tsinto mana ita, wai ma uwar me ta hada da Deedayan nan ne ma tukun, farkawa fa nayi naga bbu yarinyar an dauketa, to wllh ki taso min Amadu inji ko shi ke sa ta raina ni daga shigowarta gidan ko sati biyu ba ayi ba...." Mumy tayi kasake tana kallon kaka, can dai tace "Ban gane ba kaka, yarinyar bata cikin dakin ki ne yanxu?" Kaka tace "Leka ki gani mana, xan maki karya ne?" Mumy tace "Aa to ki shiga bangarenta ki dauko ta kaka, wnn ai rainin hankali ne, ikon da take nunawa kan yarinyar ai ya fara wuce gona da iri" kaka na jin haka ta tafi bangaren Mami cike da kwarin gwiwa ta bubbuga kofar, ta bubbuga yyi sau hudu kafin Mami ta bude, Kaka ta wani sha kunu tace "Ina yarinyar da kika dauke a dakina Rakiya?" Mami tace "Yarinya kuma, wace yarinyar kaka?" Kaka ta kalli Mumy tace "Kinji ko Maryam, bata ma san yarinyar da ta dauke ba, to ni baxan biye maki ba da girma na, Deedayah xaki fiddo min" Mami tace "Heedayah da kika tafi da ita daxu muna parlon barrister?? Ae ba a kawota nan ba" Kaka ta gwalo ido tace "Toh ni kuma bata dakina yanxu, ban ganta ba wllh" Kasa cewa komai Mami tayi tana kallon Kaka baki bude, kaka ta saki salati ta tafi bangaren Abba da sauri shi ma ta tado sa, yana fitowa tace "Amadu kai ka shigo ka dauke Deedayah dakina muna bacci?" Abba na kallonta da mamaki yace "Heedayah kuma, ba xuwa kika yi daxu kika tafi da ita ba" Kaka ta kara Rafka wani uban salatin ta daura hannu a ka tace "Wllh farkawa nayi ban ganta a dakin ba Amadu, don Allah a rufa min asiri a dudduba ko taje ta shige wani wajen ne ba a sani ba, kasan makaho" Kaf gidan bbu inda ba a duba ba amma bbu Heedayah bbu alamarta, su Rabi'ah duk an tasosu su ma, Mumy da hankalinta ya fi na kowa tashi ta rakube kitchen tafara kiran waya, ana dagawa tace "Kai oga Salahu ku dakata an nemi yarinyar ko sama ko kasa bbu a gidan ba a san wanda ya dauketa ba, ku dakata xan kira ku, ku dakata tukun" Bata jira cewarsa ba ta katse wayar tana xufa.... Duk iya duban da xa ayi a gidan nan anyi har tare da masu gadi amma ba a ga Heedayah ba, daga karshe kuma aka ga second gate din gidan a bude, kaka ta rushe masu da matsanancin kuka tace "Wayyo na shiga uku yanxu cewa xa ayi tayi a dakina ta 6ace, don girman Allah a rufa min asiri a nemota, idan hukuma ma suka ji haka ba kyaleni xa su yi ba, duniya duk a dauka ace na sace makauniya, wllh farkawa nayi naga bbu ita sai pillow...." Abba dai na tsaye ya ma kasa cewa komai, ya rasa tunanin da xai yi but xa a iya ganin tashin hankalin fuskarsa, likewise Mami dake ta kallon gate din da ke bude, Mumy kuwa salati ta dinga yi tana cewa "Anfi shekara uku ba a bude kofar nan ba, a ina ma aka samo makullin aka bude?? Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un.... does it mean we are not longer safe cikin gidanmu kenan, waye xai dauke wnn yarinya ni Maryam" Mami tayi mata wani kallo sannan ta shige cikin gida, kana ganinta kasan she is not going to let this, daren ranan nan dai bbu wanda ya rintsa a gidan, Kaka kuwa ta lula cikin anguwa neman Heedayah, bbu yanda Abba bai yi da ita kan kar ta fita dare ne amma taki sauraran kowa tayi ficewarta tana kuka... Gaba daya Mumy ta rasa irin tunanin da xata yi, amma hankalinta ya fi na kowa tashi, can sai ga kaka ta dawo wujiga wujiga da takalma da Hijabi a hannu wai karnuka sun biyo ta... Karfe hudu Shuraim ya shigo gidan ta dalilin kiransa da Abba yyi, Kaka ta fashe masa da wani sabon kukan ta rikosa tana cewa "Wllh tare muke kwance Shureen wai farkawan da xan yi naga bbu ita, an sungumeta...." Shuraim dai ya kasa cewa komai sai kallon kakar tasa yake, can ta sake sa ta koma gun Abba tana Kuka wai ta shiga uku kar hukuma su daure ta, Shuraim ya jingina da bango a hankali ya rungume hannunsa, he looks disturbed also, Ana kiran sllh dama Mami ta bar gidan.... Bayan an idar da sllh sai ga Baffa da Sudais sun shigo gidan, Baffa ma is speechless just as his brother, Kaka dai tun hawaye na xuba har ya daina xuba yanda take kukan kai kace yarinya ce, Sudais ko karasowa cikin parlon ma ya ki yi yana tsaye daga bakin kofa, at the end kawai ya fice daga gidan gaba daya, Baffa na kallon kaka yace "Don Allah kiyi hakuri Baaba, in sha Allah xa a ganta, bbu abinda xai sameta" cikin rawan murya kaka tace "Toh kai sai kayi fatan abu ya sameta dama? Wllh wanda ya saceta cikin gidan nan yake, dama kaf gidan banda ni da Rakiya bbu me sonta, ko shi Amadun bamu san xuciyarsa ba" Abba ya kalleta ta gefen ido bai dai ce komai ba, Baffa yace "Da karfe nawa kika lura bata dakin?" Kaka tace "Daya saura minti goma, Ina fitowa parlo kuma Maryam na fara sanar ma cewar ban ga Deedayah ba" Abba ya kalli kaka yace "A ina kika ga Maryam din" Mumy ta amshe da sauri cike da karfin hali tace "Na fito shan ruwa kitchen muka hadu" Abba ya kalleta, ya dauke kai ya sake kallonta sai kuma ya mike ya wuce bangarensa, Shuraim dai kansa na kasa, Mumy na daga xaune amma duk cikinta ya hautsine da kyar take xaune har lkcn, ba a dau lkci ba Abba ya fito yana kallon Baffa yace "Mu tafi Dr" Mikewa Baffa yyi, kaka ma ta mike da sauri rike da hijab dinta tace "Ae da ni xa aje duk Inda xa a je tunda a dakina komai ya faru, salon in ki bin ku a xargeni ace dama ni na sace ta, gwara duk inda xa ku in bi ku" Sai bayan fitarsu Mumy na kallon Shuraim cikin karfin hali tace "Aliyu wa xai dauke yarinyar nan, wllh ni dai ban san komai kan wnn lamarin ba, naga kuma kowa kallona yake, dama ni na dauketa baxan damu ba, amma wllh ba ni bace, kaga kallon da barrister yyi min irin kamar da sa hannuna gun 6atar ta" Hankali tashe take maganan, shi dai Shuraim kansa na kasa, can ta mike ta wuce bangarenta, yana rike da car key dinsa ya bar parlon ya tafi gun motarsa dake waje.... Hajiya Sadiya da kanta kasa cewa komai tayi, Cikin rawar murya Mumy tace "Sadiya ni fa ban ta6a shiga rudani irin wnn ba, sannan kuma abun mamaki gate din bayan ma a bude na samesa....." Sadiya ta d'an yi shiru snn tace "Shuraim na gidan kuma koh?" Mumy tace "A'a baya nan, tun tara da wani abu ya tafi night duty ba sake shigowa gidan ba sai Asuba uban ya kirasa ya dawo..." Sadiya tace "Kaiii, wnn lamari akwai lauje cikin nadi....." cike da damuwa Mumy tace "Ni ki saurareni Sadiya, ta ya xan wanke kai na cikin lamarin nan, wllh sai kinga, ko magana xanyi sai inyi ta rawan baki... Ni nasan kowa ma ni yake xarga, ni kuma ba a ma kai ga xuwa dauke yarinyar nan ba aka nemeta aka rasa.... Ga dai abun farin ciki amma bbu daman farin cikin tunda ni ake xarga" Sadiya tace "Bari xan kira ki yanxun nan" daga haka ta katse wayar..... Cikin bacci Heedayah ta ji hannu a kanta, ta bude idanuwanta da kyar ta kamo hannun tace "Mami I want to ease my self"

For those sharing and reading this book for free I know I can't stop u from doing so, but that's ur business, burden, and cup of tea, the book is just for a while, while the above mentioned is for everr, but do not edit my write up plss, leave it the way it is and read....馃槆

Heedayah is 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....

Ina masu son kamshi in and out, I mean kamshi irin na manyan mata fa, to ga opportunity, hope dai ba ku mance Innar su Mujaheed da Imaan ba, to ta ce a baku shawara ku siya turaren wutan nan don yana daya daga sirrin kamshin dake tashi a parlon ta kullum, tace me xa ayi da gidan da bbu kamshi, mace bbu kamshi kuma ai bata cika mace ba, daya daga tsatsonta ke hada wnn lafiyayyen turaren wutan da bbu irinsa, for more info contact 08038103096.....

Khaleesat ma dai da turarurrukan take amfani wllh, trust me it's nice and very affordable.... 馃槏 9/12/21, 8:04 PM - ,: 3months later....

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull