Heedayah complete Novel - Chapter 31
Heedayah complete Novel Chapter 31: Heedayah complete Novel Chapter 31. Khaleesat ma dai da turarurrukan take amfani wllh, trust me it's nice and very…
3,862 words
Khaleesat ma dai da turarurrukan take amfani wllh, trust me it's nice and very affordable.... 馃槏 9/12/21, 8:04 PM - ,: Mumy ta mike da sauri ganin Karime ta dawo tace "Ya, har kin xuba?" Karime tace "Korata tayi wllh, har cewa tayi xata sa a sallameni" Mumy ta xaro ido tace "Me kika mata????" Karime tace "Ban mata komai ba wllh, haka nn kinsan dama bata sona" Mumy tace "Toh baki bata hkuri ba kika fita ke kuma?" Karime tace "Cewa tayi bata son ganina" Mumy ta xauna tayi tagumi tana tunanin to ynxu ya xa ayi ta samu ta juye maganin nan cikin kayan shayin Heedayah, ta kalli Karime tace "Ba ni kayana ki fita" Karime ta fiddo kullin cikin rigarta, kin amsa Mumy tayi tace "Ajiye min kan kujera" ta ajiye, Mumy tace "Je ki sae na neme ki" fita tayi parlon Mumy ta bi ta da wani kallo, leda ta dauko ta rufe maganin da shi tana yatsina fuska sannan ta dauka ta wuce daki. A ranan Mumy ta shiga dakin kaka yyi sau biyar kafin yamma, fitarta na karshe kaka tayi mitsi mitsi da ido tace "Da kyar idan matan nan tana da gaskiya, na lura tun safe take min xarya kmr me nakuda.... Ni dai bari Amadu ya dawo in ji dalili gaskiya, Allah na tuba duniyar nan yanxu ko wanda ku ka fito ciki daya kaga yana maka xarya bbu dalili toh kayi ta kanka kawai" Heedayah dai na dakin tana jin abinda kaka ke cewa, Kaka ta mike ta kwalo ma Sajida kira, Sajida ta taho da sauri tace "Gani kaka" Kaka tace "Kasko xa ki dauka kije duk inda xaki samo gawayi ki hura min garwashi ki kawo min yanxun nan" Sajida tace "Toh sai dai inje kasuwa yanxu a siya gawayin" Kaka tace "Toh ni dai bani da ko sisi, tafi ki kira min Maryam" Sajida tace "Toh" sannan ta wuce, ba a dau lkci ba sai ga Mumy tana murmushi tace "Gani kaka, aiki xa a maki" Da sauri kaka tace "A'a, aikin me kuma kamar kuturwa, dari biyar xa ki ba Sajida xata je min kasuwa ynxu" Mumy ta d'an juya lkci daya ta daure fuska, sai kuma tace "Anya xa a samu kuwa, da yake jiya da naje can gida na kai Salima asibiti to bbu kudi wajena ynxu" Kaka tace "Toh kira min Amadu, shi baxai rasa yanda xai yi da ni ba ai" Mumy dai bata ce komai ba, Kaka tace "Ki kira min shi da wayarsa" Barin dakin Mumy tayi murya can ciki tace "Toh" tana tsaye daga bakin kofarta ta kwalo ma Sajida kira, Sajida ta taho da sauri, Mumy ta jefa mata dari biyar din fuska a murtuke ta shige parlonta ta kulle kofa... Sajida na dawowa da gawayin ta rura ma kaka a Kasko, sannan ta kai mata dakinta, kaka na xaune tsakar dakin ta baje kayan wani tsohon jakarta, kullin magunguna ne iri iri kai kace boka ce, Sajida ta ajiye kaskon saman tiles tace "Gashi kaka" Kaka tace "Allah maki albarka...." Tace "Ameen" sannan ta fita, kaka ta xuba uban turaren icce a wutan, Tuni Heedayah ta mike ta fara tari tace "Kaka meye shi?" Kaka tace "Toh haka kawai aka ce maki xan xauna a kashe ni, jiya fa wani mummunan mafarki nayi..." Heedayah xata fita dakin kaka ta rufe kofar tace "Toh ko dai ke mayya ce ba mu da labari..." Heedayah ta fashe da kuka tace "Kaka yana shiga hancina" kaka tace "Ai dama ta nan din xai shiga, Ina xa mu tsaya a cuce mu, kowa fa ya lalace da mugun abu a xuciyarsa, tun ina gidan mijina nake tsare kai na, Rakiya ma idan ta dawo daga gantalin aikinta sai ta xo in debar mata, kaikayi koma kan mashekiya ne fa..." Heedayah ta toshe hancinta, Kaka na ta surutunta tana kara cika iccen cikin wutan kaskon, sai da ta tabbatar ya ratsa ko ina na dakinta sannan ta fitar da shi parlor ta ajiye tace "Toh dama kada wanda ya dauke min kayana a nan" Mami ce ta bude kofar da sallama, tana shigowa ta fara yatsine fuska don hayaki ya cika ko ina, Ta karaso gun kaka tace "Meye wnn din kaka" Kaka tace "Ke ma idan xa ki samo leda in debar maki ki samo, duniyar ynxu ba gaskiya, Maryam ma idan ta ga tana so ta samo leda in debar mata, kaikayi koma kan mashekiya ne" Mami ta gaida kaka xata wuce kaka tace "Yauwa Rakiya dama Ina jiran ki dawo ki gaya min me wnn me aikin taki take tsinana maki a gidan nan" Mami ta juyo tace "Aa ba komai kawai dai suna aikin gidan ne tare da dayar mai aikin" Kaka tace "Toh a gaskiya ki sallameta Sajida kawai ta ishe mu a gidan nan, baki ga ba kullum fa naso take, kazama ce fa da kyar idan ruwa na ta6a jikinta haka kawai wata cuta taje ta kama mu ta dalilinta bayan mu duk muna wanka muna tsafta" Mami tayi murmushi tace "Naga kamar aikin ya ma Sajidar yawa ne" Kaka tace "Sai a samo wata me tsaftar amma a gaskiya a sallami wnn, idan ko ba haka ni a sallameni" Mami na kallonta tace "Ta maki wani laifin ne kaka?" Kaka tace "Aa ko daya kawai na gaji da kazantar ta ne" Mami bata kuma cewa komai ba ta juya ta nufi bangarenta... Da daddare Abba na parlonsa sai ga kaka ta shigo da sallama, Mumy da ke yanka masa watermelon tace "Sannu kaka" Kaka ta xauna tace "Yauwa, Amadu ashe ka dawo" Yace "Ehh na dawo, Ina yini" tace "Dama xuwa nayi naji wa ke biyan kudin aikin matar da Rakiya ta dauka" Yace "Aa ita ke biya" Kaka tace "Au haba, to bari in bar mata mai aikinta kar ta kullaceni, wai da cewa xan yi a sallameta" Abba yace "Tayi wani abu ne?" Kaka tace "Oh oh kawai dai ni bata kwanta min bane ga kazanta malam, amma tunda ba kai ke biya ba ai shikenan, ae Rakiyar ma me kudin kanta ce, ba xaman banxa take ba kamar wasu, baka ga gidan wan tsohon mijinta ba da Junaidu ya kai ni shekaranjiya, Kai kace wani shugaban kasa ne" Mumy dai ko kallon kaka bata yi ba sai sauri take ta bar parlon, ko yankan kirki bata ma kankanan ba ta mike tace "Xan je in duba ruwan shayin da na sa a kitchen" daga haka ta fita, kaka ta kalli kankanan tace "Dubi wani yanka da tayi ma kankanan kamar bakatafiya..." Shi dai Abba bai ce komai ba, kaka tace "Toh ni dai na hada kayana tun ranan da ka min xancen tafiya gyaran idon Deedayah a india" Abba yace "Mutane biyu kacal xa su je tare da ita fa Baaba" Kaka tana kallonsa da kyau ta gyara xama tace "Ban gane mutane biyu ba, su wa da su wa kenan mutane biyun?" Yace "Aa ba ni nace ba, ka'idar wajen ne haka, Doctor ne ma ke gaya min" Kaka tace "Toh ba sai ni da kai mu kai ta din ba, ko akwai wani wanda ta hada wani abu da shi banda ni da kai din" Abba yyi shiru yana kallonta, kaka tace "Toh dama ai ni da kai ne dolenta, ita Rakiya yaushe ta xo gidan ko yaushe ta san Deedayar da xa ayi marmarin tafiya da ita?" Shi dai Abba bai ce komai ba.... Mumy na fita sai da ta fara wucewa bangarenta snn ta fito da sauri, ta dinga bin main parlon da kallo kamar munafuka sannan ta shige dakin kaka ta kulle, hannunta na rawa ta isa gun kayan shayin ta sauke gwangwanin madaran amma ta rasa da me xata bude na milon, kan Fridge ta hango cokali cikin cup, ta tashi da sauri ta dauko ta bude gwangwanin ta ciro ledan dake rigarta, hannunta na rawa ta bude kyallen ta juye bakin content din cikin gwangwanin ta gauraya da cokalin snn ta rufe gwangwanin ta mayar Inda yake ta tashi, ta goge cokalin da xaninta shi ma ta mayar cikin cup din, gaba daya a rikice take, ta fice daga dakin kamar xata tashi sama, sai da ta shiga parlonta ta sauke wani ajiyar xuciya ta juyo tana kallon yaranta tace "Uban me ku ke jira ba ku tafi kun kwanta ba? Maxa a kashe min tv tunda bance ku lalata na dakinku ba" Sai da suka fita parlon snn ta wuce cikin dakinta tana wani murmushi.... Washegari da sassafe kaka na share sharen lungu da sako na dakinta ta dauke gwangwanin madara da Milo ta tabe baki tace "Mayyar ma bata sha shayin jiya da daddare ba, dama fa gulma ce, a gidan uwarta da ubanta ina xata samu haka, ita dai kawai ta samu d'ana sai kashe mata kudi yake a banxa a hofi, sbda ita abubuwa da yawa an daina min, tasa sai maneji muke yi, ga uban kudi xa aje a gyara kaddararrun idonta nan da kwanaki kadan, mu dai kawai Allah ya bamu lada, bafa dangin iya balle na baba" Tana ajiye gwangwanin milon taga murfin ya fadi, ta dau murfin tana kallo da mamaki, can ta ajiye tace "Ikon Allah, ni fa na hada mata shayin jiya da yamma, to wani barawo ne ya xo ya bude ya sata ya manta bai rufe ba, gashi har Milon yyi kasa, ni dai ba haka na bar sa ba wllh, sata aka fara yi gidan amadun bani da labari??" Ajiye tsintsiyar tayi ta fice daga dakin, direct parlon Abba ta nufa ta kwankwasa kofa, Mumy ce ta fito, kaka tace "Amadun fa?" Mumy tace "Yana ciki" Kaka tace "Ce masa gani a tsaye" Abba na fitowa kaka tace "Amadu wllh shigar min daki aka yi aka yashe milon Deedayah tass, ynxu ba sai ace ni ke shanyewa ba ko da ba a fito fili an gaya min ba ayi ta xagina a xuciya, toh gaskiya ni dai a san matakin da xa a dauka ynxun nan" Mumy da hankalinta yyi mugun tashi tace "Ikon Allah, toh bari in debo na wajena sai a kara mata a kai tunda yyi kasa, ba abun tada hankali bane kaka" Kaka tace "Oh oh ba wani debo naki da xa kiyi, ko ma waye ya diba sai ya maido wllh, xan fara ta kan masu aikin nan tass sai na bincike kayansu don nasan ba shan lkci daya xa ayi ma milon ba deba xa ayi a leda a boye, Kai har kayan Deedayar ma sai an bincika da nasu Rabi'ah" tana fadin haka ta nufi dakin masu aiki tana kwala ma Mami kira ita ma ta fito, kayan Sajida ta fara dubawa ta xaxxage gaba daya Ghana must go din bata ga komai ba, Kaka ta kalli Karime dake ta xufa tace "Ke ina jakarki" Karime ta nuna mata ghana must go din, ba komai ya sa hankalinta ya tashi ba sai kullin Madara da millo na Mumy da take diba a leda idan Mumy tace taje ta hada shayi, har na Mami ma tana diba, snn ga kullin soyayyen nama na jiya da ta boye a kayan, ga kuma Cornflakes a leda shima duk ta boye, kaka ta yatsina fuska tana xaro kayan kamar Kashi tana ajiyewa kasa, da ledan naman ta fara cin karo, ta kunce ledan ta saki salati ta yar a kasa tana kallon naman, Mumy ma xaro ido tayi tana kallon naman, Kaka ta ci gaba da xaro kayan sai ga ledan cornflakes, Kaka ta kara gwalo ido ta ajiye Cornflakes din, ta ci gaba da xaro kayan sai ga ledan milo sannan Madara, kaka tayi wani dariya irin na boss, Mami ma na tsaye bakin kofa ta kasa cewa komai, Kaka tace "In ji dai kun tabbatar cewar ba banxa nake ba ynxu, duk wanda Allah ya daukaka ya riga da ya daukaka sa, to a kira Amadu shi ma ya gane ma idonsa, nasan da naje na samesa nace gashi gashi a ransa cewa xai yi ohh Allah ya hadani da fitinanniyar uwa, to yau ga ranan fitinata, ni dai nasan shigar min aka yi aka debi milon nan dama" Karime ta durkusa tana matsar kwalla tace "Wllh wllh wllh kaka ba milon ki bane wnn, ki duba ki ga wnn har fa ya daskare...." Kaka ta kwala mata ledan milon da ya daskare a fuska tace "Ke dai bakya tsoron Allah, to kin saka sa cikin jaka duk wari ya baxai daskare ba?? Ai da kyau tunda ba tsutsa ya fitar ba, ni dai a kira min Amadu ya xabi ko ni ko kazamar nan, don in har xa a yafe mata ta ci gaba da xama a gidan nan gwara in tafi duk inda Allah yyi" Mami ta sauke ajiyar xuciya tace "Yau kwana nawa da biyanki kudin watan aikin ki?" Karime ta fashe da kuka tace "Sati daya" Mami tace "Toh ki hada kayanki, ki taho ki sameni in baki kudin aikinki na sati daya da kudin mota kiyi tafiyar ki, Allah ya bamu alkhairi" daga haka Mami ta fita dakin, Karime ta kara rushewa da wani matsanancin kuka ta daura hannu a ka tana kallon Mumy tace "Don girman Allah Hajiya ki taimakeni wllh aiki wahalan samu yake yi ynxu, ki saka baki a maganan nan don Allah a barni in ci gaba da aikina" Mumy ta ki kallon ko da Inda take, can ta juya kamar munafuka ta fita, kaka tayi wani shewa tace "Aje can wani gidan kuma ayi tayi masu naso ana wari amma ba gidan d'a na ba" daga haka ita ma ta fice daga dakin, Dubu goma Mami ta ba Karime kudin mota dubu biyar, dubu biyar kuma na aikin sati daya da tayi, sai kuka Karime take tana cewa "Don Allah Hajiya kiyi hakuri kar a koreni, wllh sharrin shaidan ne" Mami tace "Da ni ce kika debar ma abu na kamaki, sai dai in maki nasiha kuma in gargadeki da cewar kar ki kuma, amma kinga ya fi karfina ynxu, kinsan yanda tsofaffi suke lamarinsu, don haka kiyi hakuri ki tafi, Allah xai kawo maki wani hanyar" tana kuka sosai ta fita, Tsaye ta ga kaka da gwangwanin madara da milon a hannunta, tana ganin ta fito ta nufeta ta ajiye mata su tace "Ga nawa gudunmawar, a gaida mutan Doguwa" Mumy dake tsaye bakin kofarta ta shigo parlon da sauri kuma a rude tace "A'a kaka ya xa ayi haka? Ki bata tayi me dasu kuma???" Kaka ta katseta tace "Toh Ina ruwanki, so kike in ba Jikata gaibu ta sha, nasan barbadin da ya shiga ciki a yayin satar? Kazama ce fa bata wanka, to Deedayar xan ba ma sauran milon da ta jagwalgwala ta sha kamar uwata tace min je ki kya gani, kawai wani cutar ya kamata Amadu da Rakiya su kullaceni?? Aa wllh ta tafi da su tayi ta shan shayi a kauyen nasu" Karime sai kallon Mumy take tana hawaye, Mumy na rawar baki tace "Aa kaka idan ba xa a bata ba ni a bar min xan yi amfani da su wllh" kaka tace "Toh banyi niyya ba, ita dai barauniyar xan ba ta tafi da su, kinga dai ai baxata kullaceni sosai ba tunda na sallama mata sauran kayan shayin" kaka na fadin haka ta jawo katon Ghana must go din Karime ta xuge ta xuba gwangwanin biyu a ciki sannan ta rufe tana kakkabe hannu tace "Gudunmawata kenan, anjima kuma sai a kira min Junaidu in sa ya siyo mata wani bbu ruwana da wahala" Karime ta dau Ghana must go din ta nufi kofa tana matsar kwalla, Kai kana ganin Mumy kasan duk a rude take don hakan ya fito kiri kiri a fuskarta, Mami kuwa sai kallonta take, Mumy ta koma part dinta da sauri ta dauko Hijab sai ga ta ta fito ta bi bayan Karime tana cewa "Mu je in raka ki ai baxa ayi rabuwar tsiya ba...." Hada idon da suka yi da Mami yasa tace "Au to ai ba sai na raka ki ba ma...." Sai kuma ta koma bangarenta da sauri, Mami ta bi bayan Karime da har ta fita, Karime ta juyo ganin Mami ta tsaya tace "Hajiya kiyi hankali da kishiyar nan taki, bata sonki bata son yar da kike riko, wnn milon da kaka ke batu a kai ita ce ta xuba abu a ciki don da farko ni ta ba in xuwa ban samu nayi hakan ba shine taje tayi da kanta amma ta mance bata rufe murfin ba...." Tana fadin haka ta ciro milon ta mika ma Mami tace "Gashi don tana iya biyoni tace xata amsa idan na bar gidan nan" amsa Mami tayi tana kallon milon, Karime ta nufi gate da sauri tana goge idonta, sai ga Mumy ta fito, Mami ta mayar da gwangwanin bayanta, Mumy tace "Lahh har ta wuce? Canji na fa na jiya da yamma na wajenta bata bani ba, har dubu uku fa...." tana fadin haka ta nufi gate kusan da gudu, Mami tayi wani murmushi ta juya ta koma ciki, parlonta ta shiga ta bude milon tana kallon content din, ta girgixa kai ta wuce bandaki nan ta xubar da gaba daya a Bathtub ta bude ruwa ta juya ta fita rike da gwangwanin. Mumy ce xaune dakin Sadiya sai rusa kuka take, Sadiya tayi tagumi ta kasa cewa komai, Can tace "Kai kema dai wllh sai kace dakikiya, toh garin yaya ma xaki bar murfin gwangwanin a bude, ke meyasa baki yin abu da hankali, ynxu da ace abun nan na backfiring fa? Sannan uwa uba ga kudin da aka kashe, Kai ni dai wllh idan abun nan bai bata min rai ba shegiya nake" Mumy na Shessheka tace "Wllh kakan nan mayya ce kawai ki yarda" Sadiya ta ta6e baki tace "Toh ita na Rakiyan fa?" Mumy na goge idonta tace "Aa dama cewa nayi bari in fara gamawa da na yarinyar tukun, gashi kuma komai ya tashi a aikin banxa" Sadiya tace "Toh Karimen ke kina tunanin a layin ta jefar da gwangwanin milon?" Mumy tace "Wllh kaf bbu flawan da ban duba ba a layin amma banga komai ba, rashin kunya fa sosai yarinyar ta min har tana neman dambe da ni a titi xata tara min jama'ah, har da kirana shaidaniya, toh ni kuwa ai bana biyeta ba sum sum sum na juyo, amma sai da na bincika jakar banga komai ba wllh sai gwangwanin madaran" Sadiya ta sauke ajiyar xuciya tace "Ikon Allah... Yanxu dai sai ki saka rana mu koma Zarian tunda haka Allah yyi da mu" Mumy ta marairaice tace "Toh amma ynxu ya xanyi da na wannan Rahinar, ni kinsan ba shiga bangarenta nake ba haka yarana, dama da kariman na nan ne nasan idan na bata xata yi ynda nace to gashi bbu ita ynxu" Sadiya tace "Toh aikuwa dole a san yanda xa ayi a shiga bangarenta kawai..." A hankali Mumy tace "Toh shkkn, Yau laraba ranan juma'ah sai mu koma Zarian" Sadiya tace "Toh Allah ya kai mu" Kaka na yanke ma Heedayah farce a dakinta sai mita take ita an maida ta boyi boyin yarinya duk wa enda suka tsintota darewa suke su barta da ita tayi ta wahala har dare, Heedayah dai sai turo baki take tana sauraronta, kaka tace "Toh bakya turo baki ba dama tunda gani naynny ki, ni kenan kullum a wahale inyi ta fama da maki bauta bakya gani balle ki gode min, bari Rakiyar ta dawo ayi ta takare yau, xanji amfanin aurota da Amadu yyi" Bude kofar parlon aka yi Salima ta shigo da sallama tana kas kas da cingam, kaka ta kalleta ta ci gaba da abinda take, Salima ta xauna tace "Ina yini kaka?" Kaka tace "Lafiya lau, ke dai har yau bbu matayi ko Salima? Toh Allah ya fiddo maki da na gari" Salima ta d'an harareta bata ce komai ba, kaka tace "Toh ai Ina jin Maryam din ma bata nan ta fice" Salima tace "Ehh na sani" Kaka tace "Ayyo, to tafiya xakiyi sai ta dawo ki dawo kenan?" Salima tace "Aa xan d'an kwana biyu a nan" kaka ta kalleta da sauri tace "Kwana biyu kuma? Toh... Allah dai ya ba Amadu ladan ciyarwa, amma ynxu ai abinci ya xama abinda ya xama a kasuwa, ynxu fa mun kusa mu ashirin a gidan nan" Mikewa Salima tayi tana taunar cingam dinta ta fita, kaka tace "Karuwanci dai a sarari ni 'ya su" A hankali Heedayah tace "Kaka wacece?" Kaka tace "Kanwar Maryam uwa daya uba daya, ai bin otal take tana kwana, kinsan uwarta ta rasu haka ma ubanta to bata da wani mafadi ynxu sai makwabta, Maryam ita ma da ba don auren dake kanta ba xata yi fiye da haka ina tsammani, kinsan kafin Amadu ya aureta har xuwa Abuja take wai yawon bude ido a can ma suka hadu da Amadun...." Heedayah tace "Meye yawon bude ido" Kaka tace "Toh ke ina ruwanki da xancen manya kina 'yar yarinya da ke" Heedayah ta turo baki Kaka ta ci gaba da yi mata yankar farcen tana cewa "Banda lalacewa ma ina ni ina hiran nan da ke" Bayan La'asar Salima na kwance parlor tana kallo aka bude kofa, Junaid ne ya shigo parlon da sallama, ta mike xaune a hankali tana kallonsa, Tunda suka hada ido ya dauke kai, ta bi sa da kallo tace "Ina yini?" Yace "Lafiya lau, ya gida?" Tace "Alhmdllh, nima yau na xo" yace "Ohk" parlon kaka ya shiga, ko gama gaisawa basu yi da kaka ba sai ga Saliman ta shigo, ta d'an xauna gefen kujera tace "Kaka bbu abinda xa ayi maki?" Kaka tace "Ehh to wankin bayi ne, daxu ban yrda da wanki Sajida ba, kinsan na sa an Kori dayar me aikin, ta saci milon Deedayah ni ko na sa aka sallameta, shine aka kira min Junaidu yanxu ince masa ya tafi ya siyo mata wasu...." Salima tace "Toh bari a wanke" cire karamin mayafinta tayi ta ajiye nan kan kujera ta nannade skirt dinta har saman Gwiwa, duk fararen kafafuwanta a waje, shi dai Junaid tunda ya kalleta sau daya ya dauke kai, ta nufi cikin bathroom din, kaka tace "Ae Salima yar albarka ce, ga haxaka wajen aiki, da fa idan ta xo gidan nan har kwaleman dakina tana min, kwana biyu ne kawai ta guji gidan nan, kasan yayartata bata da hali tsangwamarta kawai take shi yasa bata son xuwa ma" Junaid ya kalli kaka yace "Wacece yayarta?" Kaka tace "Kishiyar uwarka mana Maryam" Junaid bai ce komai ba, Heedayah tace "Kaka ko xaki basa ya yanke min kina min da xafi" Kaka ta jefar da nail cutter din a jikinta tace "Algunguma sai kije yyi maki da sanyi, yarinya sai sharrin jaraba kawai" murmushi Junaid yyi ya dau nail cutter din yana kallon Heedayah da ta 6ata fuska xata yi kuka, ya ja hancinta a hankali yace "Don't Lolly...." kaka ta mike tana kakkabe jikinta tace "Ni idan ta bata min rai ma sai ince ma Amadu na fasa xuwa gyaran idon da ita sai in ga ta tsiya"