Kenza eBookz

Heedayah complete Novel - Chapter 4

Heedayah complete Novel - Chapter 4

Heedayah complete Novel Chapter 4: Heedayah complete Novel Chapter 4. Kaka ta rike ha6a tana kallon Mumy tace "Lallai ba lafiya, Kar ki yarda, ba mu san…

3,321 words

Kaka ta rike ha6a tana kallon Mumy tace "Lallai ba lafiya, Kar ki yarda, ba mu san irinta ba, kuma ba ma bukatan sani, ba ruwana da jajibe jajibe gaskiya, to meye kuma na tsinto yarinya kamar wanda nace ma je ka kagani, to ni dai ba ruwana, mu je ayi meeting din gaba daya, ai kin ga ko shigowa gaisheni ma bai yi ba tunda ya tsinto wata uwar tasa a titi jiya, kuma ace min lafiya qlau, a'a wllh ba lafiya" sosai hankalin Mumy ya kwanta jin furucin Kaka, Kaka ta mike ta nufi kofa Mumy na biye da ita tana murmushi, Shuraim ya bi su da kallo kafin ya mike shi ma ya fita parlon. Babban parlor ne me dauke da tsadaddun kujeru ba masu hayaniya ba, Hajiya Amina da kishiyarta Hajiya Hauwa na xaune parlon sai Safiyya, Nafisa da Aisha 'ya yan Hajiya Amina, Jamila da Zainab 'ya yan Hajiya Hauwa su ma na xaune parlon, Khadijah da Rabi'ah duk suna parlon su ma, Abba na xaune tare da Heedayah da ya xaunar gefensa, Alhaji Umar ma na xaune idonsa a kan tv dake nuna tashar Aljazeera, a tare Hajiya Maryam ta shigo parlon da kaka da ta tsuke fuska, Abba dai kallon mahaifiyar tasa kawai yake har ta xauna, Shuraim ne ya shigo da sallama ya nemi kusa da Khadijah ya xauna sannan ya gaida su Hajiya Amina da Baffansa, d'a murmushi ya amsa gaisuwar cousins din nasa mata dake kallonsa gaba daya, Baffa ya rage volume din TV din yace "Ina Sudais?" Safiyya tace "Bai dawo training ba" Baffa ya gyada kai alamar gamsuwa, Abba na kallon kaka yyi kasa da kai yace "An tashi lafiya kaka?" Kaka tace "A'a ba ruwana, lafiya lau na tashi" tana magana ne tana kallon Heedayah kasa kasa, Rabi'ah da Khadijah suka gaisheta su ma, tace "To duk ku tashi ku fita, ko kun ga sa'annin ku a nan, wannan ai ba maganan yara bane, babban magana ce, Yaron kirkin nan kadai ya cancanci xama a nan, duk ku fita" Hajiya Hauwa tayi murmushi tana kallon Shuraim da ya sunkuyar da kansa, Mikewa su Khadijah suka yi gaba daya har da su Safiyya suka fita bbu halin ko yi mata kallon banxa, shiru ne ya biyo baya a parlon, Baffa ya bude wajen da addu'a, bayan haka ya kalli Hajiya Maryam yace "Why did u invite our mother in here?" Ta gyara xama tace "Bcos it's necessary, she needs to know what's happening" Bai kuma cewa komai ba, bayan few seconds ya daura da cewa "Ba wani abu ya tara mu nan ba... jiya da maraice Barrister ya dawo gida da wata baiwar Allah wanda hakan ya kawo rashin fahimta a can gidansa, ga kuma yarinyar dai xaune kusa da shi...." ya fadi haka yana nuna Heedayah wanda duk kana ganinta kasan a tsorace take, Ya ci gaba kamar haka "Duba da irin xamanin da muka tsinci kan mu na yanxu a gaskiya hakan ba shawara bace me kyau it's risky bringing the little girl home, sai dai me??? Mu duba wannan yarinya, har nawa take gaba daya, duk magidancin kwarai ya ga yarinyar nan that looks helpless a hanya ba lallai ya iya wuceta bai yi making effort din taimakon ta ba, ko min kankantar taimakon kuwa, sai dai shi barrister nasan taimakon ya yanko sa da girma ne tunda har gidansa ya kawo wannan baiwar Allah, wanda ba kowa xai yi hakan ba a xamanin nan na yau gaskiya, ba wai ina nufin hakan da yyi kuskure bane amma in the other way round xa a iya kiransa da kuskure...." Kaka dake ta hararan Baffa ta yi kwafa tana girgixa kafa, Baffa ya ci gaba "Amma kuma xai iya yiwuwa yaga kawota gidan shine kadai mafita duba da cewa she is unsighted.... Har xuwa lkcn da Allah xai bayyana iyayenta" Calmly Hajiya Maryam tace "Idan Allah bai bayyana iyayen nata ba fa?" Baffa yace "Wannan kuma baxa a rasa yanda xa ayi ba in sha Allah, Hajiya kar ki manta one knows not where his or her reward lies, sannan muna da baya, we should always try positioning things in our shoes" Girgixa kai tayi irin ba mutunci tace "Toh ni ban hanasa riketa ba Doctor, Amma Wallahil Azeem ba ni xan rike masa ita ba,... Ya nemi inda xai kai ta, ko kuma ya bar ta nan wajen ku ai duk daya ne..." Da sauri Hajiya Amina ta kalleta da wani expression, Kaka ta kyabe baki tace "To duk kun gama??" Duk aka yi shiru ana kallonta, ta gyara xama tace "Toh maza tun muna mu bakwai ba mu dawo mu takwas ba a parlon nan Amadu ya maida wnn yarinya inda ya dauko ta, mu ba gantalallu bane, bamu sa6a kwashe kwashe ba a dangi, baxa kuma a fara ta kan d'a na ba...." Shiru ne ya biyo bayan abinda Kaka tace a parlon, Abba da Baffa sai kallonta suke, Hajiya Maryam taji kamar ta tashi ta rungume kaka don farin ciki, Hajiya Amina kuwa sai murmushi take kasa kasa, Hajiya Hauwa dai sai kallon Heedayah da ta makale jikin Abba take, Bude kofar aka yi wani matashi ya shigo da sallama, sanye yake da sport wears, they have many resemblance in common with Shuraim, sai dai ya girme ma Shuraim da shekara daya duk da ba wai hakan ya nuna bane, bin occupant din parlon yyi da kallo, coz he knew nothing about the meeting, ya kalli kaka da ta tsuke fuska ganinsa tace "Kai ka ji wani neman fitina gun Mutumin nan ko sudais...." xaunawa yyi gefenta coz yasan she will brief everything a nan take kafin ma ace masa komai a parlon, ta gyara xama tace "Kanin ubanka dai ya xama abinda ya xama, Wai kaji yarinya ya tsinto ya kawo gida ba dangin iya balle na baba, har yana ikirarin bbu wanda ya isa ya hanasa abinda yyi niyya bai san magana xai dawo kunne na ba, Toh mu xuba da shi, idan shi ya haifeni ai yanxu kowa xai sani, kuma nace masa maxa ya mayar da ita kada raina ya bace...." Murya can kasa Sudais yace "Wacce yarinya ce?" Heedayah ta nuna masa rai bace tace "Gata can kamar mage...." Sudais ya kalli Heedayah da ta makale Abba, sannan ya kalli Abba da Baffansa da suka kasa cewa komai, ya maida dubansa kan Kaka, lkci daya ya hade rai yace "Toh meye don an taimaki wannan yar yarinyar, ni na ma xata wani babban abu ne ya faru a gidan, ynxu ba fata ba yau ace Safiyya ko Jamila sun 6ace baki son wani ya taimaka masu kenan? Kika san dalilin da yasa Allah ya rabata da iyayenta?? Ke da xaki yi fatan Allah ya bayyana su...." Katse sa tayi da sauri tace "Kun ji min fitsararren yaro ko?? to ce maka nayi ban yi addu'ar Allah ya bayyana iyayen nata bane?? Ni dai ba ruwana ka daina min sharri, dama kwana biyu na fita harkan ka a gidan nan sam baka da mutunci ka rainani...." Ya mike yace "A'a ni ban rainaki ba kaka ke dai baki son gaskiya, kawai ki bar Abba ya rike yarinyar a ci gaba da neman iyayenta, ynxu idan ya mayar da ita kika san hannun wanda xata fada, kinsan fa idan ta fada hannun mugaye ke ma kina da kwamasho me girma, sannan kin fi kowa cewa aji tsoron Allah, kuma ga lamarin da ya kamata mutum ya ji tsoron Allah nan...." Tagumi kaka tayi tace "Kuna dai ganin Aliyu ko?? To ba komai rayuwa ce ai" Hajiya Maryam dake ta xufa sai kallon Sudais take tana hadiye abu da kyar, Baffa dai ya jinginar da kansa da kujera yana kallon d'an nasa, Abba kam kansa na kasa shi ma yana saurarensa, Hajiya Amina duk uwar hararan da take xabga ma d'an nata yaki kallon direction dinta, Hajiya Hauwa banda murmushi bbu abinda take, Sudais na kallon kaka yace "Kawai dai yanxu sbda tsoron Allah ki bari Abba ya nemo iyayenta, kuma ta xauna har sanda Allah xai bayyana su...." Kaka tace "To ni dai ba ruwana, dama Maryam ce tace bata yadda ba banda haka ni meye nawa?? ai d'a na kowa ne bawa sai me shi, me ta min da xan koreta banda abun ka sudais? Amadu yayi ta rikonta har Mahadi ya bayyana ma bbu abinda ya sha min kai ni dai...." Sudais ya shafa kansa yace "Idan ya kai xuciyar ki ce masa xa kiyi kin amince ya riketa" A mugun fusace tace "To ya rike ta mana, ni ina ruwana, ai d'a na kowa ne, amma gaskiya ka daina min rashin kunya xan hada ka da ubanka, kaf ka raina ni tamkar ynda uwar ka ta raina ni" ya d'an bude ido ya juya ya nufi kofa xai fita Kaka tace "Allah yyi min tsari da kai ni dai katon banxa" Abba ya mike xai fita rike da Heedayah, Hajiya Maryam ta mike da sauri tace "Wllh to ka nemi inda xaka kai ta ba gidana da na yarana ba..." Kaka ta bude baki tace "Naga bala'i, gidanki kuma Maryam?? Ta ina hakan ya faru" Baffa yace "Wait Ahmad it's better kasan inda yarinyar nan xata xauna, u can't force her to hold the little girl, it's not even possible, tunda tace baxata riketa ba baxa ayi mata dole ba" Abba ya juya yana kallonsu gaba daya kafin yace komai Hajiya Hauwa tace "Babu damu Barrister, ka kawo min ita ni xan riketa in sha Allah har iyayenta su bayyana, Allah ya shige mana gaba, yayi mana mai kyau..." da sauri kaka ta katseta tana wurwurga ido tace "Ki riketa a wani gidan Kuluwa??? Kaji min mata ba tsoron Allah kamar gidanta, Haka kawai ba mu san ko mayya bace yarinya dare daya ta karar damu a gidan a shiga uku xaki wani ce xaki riketa, shi dai Ahmadun da yaga xai iya ya tafi can ya karata, ni dai Allah ya rufa min asiri ba shi kadai na haifa ba, in dai har ina gidan nan yarinyar nan baxata xauna ba, idan ko xata xauna sai dai a sallameni in tafi, bbu ruwana da kwashe kwashe ta kaina nake" tana fadin haka ta juya masu baya kamar karamar yarinya, Baffa dai sai kallon D'an uwan nasa yake, Hajiya Maryam kuwa sai hararansa take tana girgixa kafa tana wani murmushi irin ba shi da wata mafita kuma ai, ya gyada kai yana kallonta da kyau yace "Shikenan, Xan auro warce xata rike ta a satin nan in sha Allah" Daga haka ya fice daga parlon rike da Heedayah, kasa motsi Hajiya Maryam tayi jin abinda yace ta bi sa da kallo baki bude, Kaka tayi wani dariya tace "Atoh dai, tun ba yau ba dama nake cewa kayi aure ka ki, yanxu ai gashi xaka yi ba don Allah ba, xaman ka da Maryam ko kaddara, gwara ka auro warce xata rike yar da amana don a ynxu kam yarinyar bata da maraba da marainiya, tsinanne ne kadai xai ki taimakon ta...." Ta gefen ido Baffa ya kalli mahaifiyar tasa yyi saurin sunkuyar da kai. 9/12/21, 8:04 PM - ,: 鈿� _Heedayah_鈿�

_By Khaleesat Haiydar_鉁嶐煆�

7......

Sudais na tsaye compound din gidan nasu Abba ya fito rike da hannun Heedayah, Sudais ya nufe sa ya gaishesa da ladabi, Abba yace "Lafiya Aliyu, ya weekend?" Sudais yace "Alhmdllh sir...." Yana kallon Heedayah ya kai hannu kanta yace "How are you?" Shiru tayi bata ce komai ba, Abba yace "Talk to him Heedayah" tana rike da hannun Abba a hankali tace "I am fine" Sudais ya mata murmushi yace "Good girl...." ya kalli Abba yace "Allah ya bayyana iyayenta" Abba yace "Ameen My son" jin taku a bayansu Sudais ya juya, Shuraim ne ke tahowa yana tafiyar kamar bai son yi, wani kallo Abba yyi masa ya kalli Shuraim yace "Xan wuce gida ynxu, anjima ka taho can gidan ka sameni" Sudais yace "In sha Allah...." Daga haka Abba ya bar wajen xuwa gun motarsa tare da Heedayah, Sudais na kallon Shuraim da ya bi Abbansa da ido yace "Kai ma baka bada goyon bayan taimakon yarinyar da Abba ke son yi ba kenan, coz naga kallon da ya maka" Shuraim ya bude hannu yace "But.... She's blind, ta ina xa a fara kula da ita, is it even possible...." Sake baki Sudais yyi yana kallonsa a bit shock, can ya juya da sauri ya kalli parking space yaga Abba is helping her Into the car, ya kara kallon Shuraim yace "Blind? How is that?? Who told you that, ban gane ba" Shuraim ya shafa kansa yace "Yes makauniya ce..." Yana fadin haka ya juya ya koma ciki ya bar Sudais a wajen baki bude, Sudais ya kara satan kallon motar Abba har ya fita compound din.... A hankali Abba ke driving yana yi yana waigen Heedayah dake shan yoghurt da ya siya mata, muryar ta ya ji tace "Abba gida xa mu je ynxu wajen Ammina?" Ya gyada mata kai kamar tana ganinsa yace "In sha Allah" wani babban eatery ya shiga yyi parking yana kallon agogon wrist dinsa da ke nuna karfe sha biyu saura, wayarsa ya dauka yyi dialing number ya kai kunne, bayan few seconds yace "Hope you aren't going to keep me waiting Barrister" bin motar da ya shigo eatery din a dai dai lkcn yyi da kallo sannan ya katse wayar, Heedayah tace "Abba mun kai gida?" Ya shafa kanta yace "A'a, I want to see a frnd now, xa ki jirani har in dawo koh?" Ta gyada masa kai a hankali, kamo hannunta yyi yana murmushi ganin she looks sad and insecure, kamar dai tafiya xai yi ya barta din nan, mika mata wayarsa yyi yace "Ki rike min wayata har in dawo ynxu, kin ji?" Ta kara gyada masa kai, ya bude motar ya sauka sannan ya rufe ya nufi entrance din eatery din, Table din dake dauke da wata mata that is in her early fifty ya nufa, kana ganinta kaga well educated bafillatana cikin shiga ta kamala, ya ja kujera ya xauna yace "Good morning Barrister" Ta ajiye wayar hannunta da take operating tana kallonsa ta cikin siririn glass din idonta tace "Morning, ya family, ya weekend?" ya gyada kai yace "Alhmdllh mun gode Allah" tace "Hope ba aiki xaka hadani da shi ba kace xaka yi tafiya, coz nima tafiyan xanyi gobe in sha Allah" yayi 'yar dariya yace "Not at all, how are the children?" Tace "They are all alhmdllh, ya su Rabi'ah?" yace "Lfya lau" tace "Toh Maa sha Allah" shiru ne ya biyo baya, bayan few seconds ya kalleta yace "Ba aiki xan baki ba, na dai xo maki da magana mai muhimmanci ne Hajiya Rahinah..." kallonsa tayi ita ma tace "Ohk Am all ears in sha Allah barrister, Allah kuma yasa dai lafiya" yace "Sai alkhairi, Hajiya Rahinah na gayyatoki nan ne.... To ask for ur hand in marriage" Da wani irin mamaki take kallonsa wanda hakan bai bata damar iya ce masa komai ba, yyi kasa da murya yace "Yes nasan xa ki yi mamaki but ba abun mamaki bane, I want to marry you..." Ta yi wani yake tace "Haba Barrister, do you even know what u are saying, ni ynxu auren me xan kuma yi? Me nake nema a rayuwa...." Ya katse ta yace "Aure shine rufin asirinki let me tell you idan baki sani ba, idan kika yi aure kimarki da darajar ki xai fi haka a gun jama'ah, I have known you for more than 15 years now tun mijin ki na da rai...." Bude handbag dinta tayi ta ciro tissue don nan da nan har hawaye ya kawo idonta, ya girgixa kai yace "I don't mean to hurt you ko in fama maki ciwon xuciyar ki Rahinah, kar ki manta tun ba yanxu ba na sha baki shawaran kiyi aure sai ki ce min sai kinyi shawara, to yanxu na yanke shawarar auren ki for 3 reasons, which I will let you know ko ba yanxu ba" tace "I am sorry Ahmad bana tunanin xan yi aure har karshen rayuwata, rabuwan tashin hankali nayi da mijina ba wai normal rabuwa, bana da ra'ayin aure har abada" ya katse ta ya d'an buga table din gabansu yace "Stop this nonsense Rahinah..." A d'an fusace tace "In koma gida ince ma yarana xan yi aure? Me ye nake nema a duniya a yanxu? Me yarana suka rage ni da shi da xai sa inji ina sha'awar yin aure? Plss come off this barrister" Ya lumshe ido ya bude yace "Noo Rahinah, ba don kin rasa komai xaki yi aure ba sai don auren shine suturar ya mace...." Tana goge hawayen idonta tace "Idan ma sbda tafiye tafiyen da nake yi ne ko sbda Aikina ni naji xan ajiye in xauna gidana dama Junaid ya fi son haka, tun ba yau ba yake son in daina aikina coz ban rasa komai daga garesu ba, ni kuma xaman kadaici ne dama bana so" Kallonta kawai yake, ya sauke boyayyen ajiyar xuciya yace "I'm sorry I am making you cry this much, I'm sorry Rahinah" tayi murmushin karfin hali tace "It's okay...." A hankali yace "Xa mu ci gaba da magana amma ba ynxu ba, it's almost time for zuhur, but...." Jin yyi shiru ta kallesa tace "But?" Ya sakar mata murmushi yace "Ban hakura ba, anyway that aside xan baki yarinya ki tafi da ita, for now marainiya ce bata da kowa...." Da mamaki take kallonsa tace "Ban gane ba, a ina ka samo ta..." Briefly ya 6ata labarin Heedayah, wanda hakan yasa jikinta yyi sanyi tace "Allah sarki, Allah ya bayyana iyayenta, I will go with her in sha Allah" yace "Yes I know u will Rahinah, sai dai I didn't made mention of her blindness to you, she's blind" xaro ido tayi tace "Blind??" A hankali ya gyada mata kai, tace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un" yace "Tana mota ita kadai, mu tafi ki ganta" a tare suka fita eatery din, sai da suka kusa motarsa a hankali tace "Matar ka tace baxata riketa ba kenan?" Ya juya ya kalleta ya d'an yi murmushi yace "Ehh" Ta girgixa kai tace "Toh Allah ya kyauta" yace "Ameen, amma a gidana Heedayah xata xauna, she will stay with u just for few days let me settle down things" Bude mota yyi Heedayah ta juya direction din da sauri fuskarta duk hawaye tace "Abba" ya kamo hannunta yace "Kuka kike yi daughter" cikin rawar murya tace "Naga baka dawo ba" ya share mata ido yace "I'm back dear, xaki bi Maminki gida yanxu kin ji?" Tace "Abba ina xaka je?" Yace "Xan je in siyo maki sabbin kaya ko baki so" tayi shiru bata ce komai ba, Hajiya Rahinah dake ta kallon Heedayah da tausayi tace "Ba dadewa xai yi ba baby, mu je gida kafin ya kawo maki kayan" daga haka ta sauketa a motar, ya kalleta yana murmushi yace "Thanks Barrister, sai na xo anjima" ta gyada masa kai ta nufi motarta da Heedayah, sai da ya ga fitansu sannan ya ja motarsa ya bar Haraban eatery din shi ma. Hajiya Rahinah na parking a parking space ta bude motar ta fito, wata yarinya da baxata haura sha hudu ba ta iso gun motar tace "Mami sannu da dawowa" Tana mika mata handbag dinta tace "Thanks dear, har kin gama assignment din?" Tace "Ehh na gama" Mami ta xaga xuwa side din Heedayah tace "Junaid ya xo kuwa?" Yarinyar ta girgixa kai tace "A'a.." bude motar tayi ta sakko da Heedayah, xaro ido yarinyar nata tayi tace "Mami who is she?" Mami tace "Bakuwa" daga haka ta rufe motar tana rike da hannun Heedayah ta nufi entrance din shiga cikin gidan 'yar ta Farida na biye da ita a baya...

07087865788 9/12/21, 8:04 PM - ,: 鈿� _Heedayah_鈿�

_By Khaleesat Haiydar_鉁嶐煆�

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull