Kenza eBookz

Heedayah complete Novel - Chapter 54

Heedayah complete Novel - Chapter 54

Heedayah complete Novel Chapter 54: Heedayah complete Novel Chapter 54. Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... 9/12/21, 8:04 PM - ,:…

6,298 words

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... 9/12/21, 8:04 PM - ,: Heedayah ta daga kiran ta kai kunne amma bata ce komai ba, sallama yyi mata ta amsa sannan tace "Ina yini" yace "Lfya lau, how are you?" Tace "I'm fine" yace "Always not picking calls, why?" tace "Mun fita ne" yace "Xuwa ina?" Tace "Gidan Abbanmu" yace "Ohk" shiru tayi, shima yyi shiru, can yace "So you ain't coming out anytime soon" ta jingina da pillow tace "Nima ban sani ba" yace "Yaushe xa ku koma schl?" Tace "In a week time" yace "Ina son mu hadu" bata ce komai ba, yace "Kin ji?" Tace "A ina?" Yace "Idan ma kince gidanku ae sae in xo" tace "Don a min duka?" Murmushi yyi yace "Aa ba wanda xai maki duka, now tell me a ina xan gan ki?" Shiru tayi, yace "Think about it, then u call me, wayar a bude take and akwai airtime a ciki, I will be expecting ur call" daga haka ya katse wayar, ta cire a kunnenta a hankali, bayan kusan minti biyar da gama wayar aka bude dakin junaid ya shigo, karasowa yyi gefenta yace "How are u feeling Heedayah" tace "Alhmdllh" yace "Bbu inda ke maki ciwo ko?" Ta gyada masa kai ba tare da ta kallesa ba, yace "Look at me Heedayah" juyowa tayi ta kallesa suka hada ido, yace "Me xa ki ci?" A hankali tace "Shayi kawai xan sha" yace "Ohk, no bread?" Ta girgixa masa kai tace "Aa bana so" juyawa yyi ya fita dakin, ta boye wayar da ta rufe da palm dinta karkashin pillow da sauri. Heedayah na gama shan shayin da Junaid ya kawo mata ta mike ta tafi yin alwala, bayan ta idar da sllh ta daga karkashin pillow ta dau wayar da ta boye ta mayar inda yake sannan ta dawo ta kwanta, nan da nan wani baccin ya kuma dauketa. sai after la'asar Heedayah ta fita dakin bayan tayi sllh, Mami na xaune parlor da wata colleague dinta suna hira, Heedayah ta gaishesu Mami tace "How are you feeling now" Heedayah tace "Da sauki" Barrister Khadijah tayi mata Allah ya sauwake ita ma sannan Heedayah ta wuce kitchen da cup din hannunta, Farida ce kitchen din tare da Zainab suna girka dinner, Farida ta juya tana kallonta tace "Ya jiki?" Heedayah tace "Na ji sauki, tuwo xa ku yi?" Farida tace "Shi Mami tace mu yi" Heedayah ta marairaice fuska tace "To ni me xan ci da daddare?" Dariya Farida tayi tace "Ba ga Indomie ba sai ki dafa" a hankali Heedayah tace "Mami baxa ta bari ba ai cewa xata yi sai na ci" Farida tace "Vegetable soup ne fa" Heedayah ta girgixa kai tace "Bana ci" Farida tace "Guess what Heedayah" Heedayah ta d'an bude ido tace "No plss tell me, kinsan I am not a good guesser" Farida ta wara ido tace "At last Mami tace I can go to Abuja tomorrow" Heedayah tace "Only you?" Farida tayi dariya tace "Kin ma san da ya ta bar ni, nace ke fa tace baki da lafiya baxa ki je ko ina ba" a hankali Heedayah tace "Ni ai naji sauki, don Allah Mami ta bar ni" Farida tace "Ki bari anjima sai kiyi mata magana" Heedayah tayi shiru bata ce komai ba, can ta juya ta fita kitchen din, Mami ta dawo daga rakiyar Barrister Khadijah ta xauna nan parlor tana kallon Heedayah da ta xauna kasa kan carpet tace "Are you sure bbu inda ke maki ciwo Heedayah?" Heedayah ta girgixa kai tace "Ba ko ina Mami" Mami tace "Toh Allah ya sauwake" Heedayah tace "Mami ai tare xa mu tafi Abuja da Farida" Mami tace "Noo you are going no where, tashi ki kai min system dina daki" Mikewa Heedayah tayi ta dau system din ta wuce sama, nan kuwa ji take kamar ta rushe da kuka. Bayan Magrib duk suna xaune parlor suna cin abinci banda Heedayah dake xaune tana kallo, Junaid ne ya shigo parlon bayan ya gaida Mami ya amsa gaisuwar da Farida ke masa, yana kallon Heedayah da ta gaishesa ita ma yace "Why are you not eating?" Shiru tayi bata ce komai ba, Farida tace "Ae bata cin tuwo" ya kalli Mami, sannan ya kalli Heedayah yace "Me xa ki ci?" Mami tace "Bbu wani abinda xata ci, idan baxa ta ci tuwon ba ta bar shi, meye da tuwon da xata ce bata iya ci?" Junaid dai bai ce komai ba, can dai ya wuce sama, ba a dau lkci ba ya sakko sanye da jallabiya, yana shafa kansa yace "Mami frnd dina na jirana waje xan basa sako cikin mota" Mami tace "Idan ma gidanku ne ke jiranka a waje that's not my concern, my only concern is that kar ka kuskura ka shigo min gidan nan da wani abinci" ya xaro ido yace "Abinci kuma? Abincin me Mami" Mami tace "I've told you my own" Bai ce komai ba ya nufi kofa ya fita gidan, Heedayah dai na xaune sai wasa da fingers dinta take, Farida sai murmushi take, Mami ta kara gyara xama parlon tana jiran shigowar Junaid daga wajen frnd din nasa, yana fita ko minti goma ba ayi ba aka bude kofar parlon, Shuraim ne ya shigo da sallama, ya karaso cikin parlon, Mami na kallonsa tace "Welcome" ya xauna sannan ya gaisheta, ta amsa tace "Ya aikin?" Yace "Yanxu xan wuce" tace "Night Duty kawai kake yi ne ynxu?" Yace "Aa amma na fi yin night din ne" Farida ta gaishesa ya amsa, Heedayah ta dauke kai murya can ciki tace "Ina yini" Bai ce komai ba, Mami tace "Ya mutanen gida?" Yace "Lafiya lau" Tace "Kaka ta koma can gidan Baffa ne?" Yace "Aa tana nan gida" Mami tace "Ohk" yace "Ya mai jiki" Mami tace "Aa ta ji sauki sosai" Yace "Allah ya kara sauki" Mami tace "Ameen, Farida ki kawo masa abinci duk da nasan he is full always" Shuraim yyi murmushi amma bai ce komai ba, Mikewa Farida tayi ta tafi kitchen, bayan wani lkci ta fito ta ajiye masa tray din abincin a gabansa, ya d'an bude warmer din, lkci daya ya rufe yace "Ai bana cin tuwo" Kallonsa Mami ta tsaya yi, can tace "Baka cin tuwo??" Yace "Bana ci" Heedayah ta gyara xama tace "Mami to ai kinga yanxu dai ba ni kadai ce bana cin tuwo ba, kince baki taba jin wanda baya cin tuwo ba, shi ma ba gashi baya ci ba, sai in je in dafa masa Indomie" sau daya Shuraim ya kalleta ya dauke ido, Mami tace "Kar Allah ya sa ya ci tuwon, Farida dauke min abincina ki mayar kitchen yunwa bai ishesu bane" Murmushi kawai Shuraim yyi, Mami tace "Tuwo ba dai da miyar kuka ba ko kubewa ace baxa a ci ba" Ya girgixa kai yace "Aa ni fa ina ci, don na koshi ne yasa nace bana ci" daga haka ya mike yace "Xan wuce" Mami tace "Allah ya tsare" ya nufi kofa ya fita, Heedayah ta bi sa da harara, can ta mike ta wuce sama kamar xata yi kuka. Shuraim na fita junaid ya shigo, yyi ma Mami sannu da xama ta amsa tana kallon hannunsa ya wuce sama. Karfe sha daya da wani abu junaid ya bude kofar dakinsu Farida, Farida tayi bacci Heedayah kuma na kwance cikin blanket tana waya da Khaleel, jin an bude kofa ta katse wayar da sauri, tayi still barin da taji an kunna switch din dakin, bayan few seconds ta sauke blanket din a hankali, mikewa xaune tayi tana kallonsa tace "Yaya" ya ajiye mata ledan hannunsa yace "Ga abincin" murmushi tayi masa tace "Nagode" ya daga mata gira yace "Good night" daga haka ya juya xai fita ya kusa cin karo da Mami, da sauri Heedayah ta mayar da kanta cikin blanket din, Ya fara kame kame ya ma rasa abinda xai ce ma Mamin tasa, Mami ta kalli ledan da ya ajiye sannan ta karasa ta bude ledan, takeaway ne na fried rice with full chicken lap, ga chivita drink, sai kuma tsire a wani takarda daban, mayar da ledan tayi ta rufe sannan ta ce "Toh fita" juyawa yyi ya fita dakin ta fita ita ma ta kulle, a hankali yace "Mami kiyi hakuri, naga bata da lafiya ne kuma kar ta kwana da yunwa, right from time kinsan bata cin tuwo" Mami tace "Kuma gaskiya ne, kai me conscience, ni kuma mara shi..." Da sauri yace "Aa wllh Mami ba haka bane" dakinta ta shiga, ya d'an yi jim sannan ya bi bayanta xuwa dakin, tace "Aa yi tafiyarka ka kwanta...." Yace "Kiyi hakuri Mami" kujera ta nuna masa tace "Sit" ba musu ya xauna, ta xauna gefen gado tana facing dinsa tace "Tell me, what is ur intention na makale ma Heedayah da kake yi ina hanaka amma baka ji" ya sunkuyar da kansa yyi shiru, tace "Answer me, xan kwanta ina da aiki gobe" Yace "Nothing Mami, matsayinsu daya da Farida" Tace "Good I hope it shouldn't pass that Junaid..." Dago kai yyi yana kallonta tace "Yess, matsayinsu ya tsaya daya da Farida, tashi ka tafi good night" Yyi kasa da murya yace "But me yasa kika ce haka Mami?" Tace "Me yasa nace me?" Yace "Abinda kika ce" Tace "Ban gane tambayar ka ba" ya sauke idanuwansa kasa yace "But Mami...." Sai kuma yyi shiru, tace "But what?" Yace "I would have wished us to be together till end" Mami tace "As???" Jin ya ki cewa komai ta hade rai tace "Kaga you stop beating about the bush and save my time, go straight now" yace "Mami kawai Ina sonta, kuma Ina jin xan iya aurenta" Kallonsa Mami take bbu ko kiftawa, can tayi wani murmushi tace "Ita Shaheedar fa?" Ya d'an hade rai yace "Dama kece ke sonta ba ni ba" Tace "Haka kace?" Yayi shiru, tace "Toh ba da ni xa ayi wnn haukan ba, Shaheedah da maganarta ke kasa kusan shekara uku sbd selfish interest dinka kace min ni ke so ba kai ba...." Yace "Don Allah Mami ki bar maganan nan wllh bana jin xan iya auren Shaheedah, idonta ya bude da yawa, kuma I can't marry someone living all alone abroad da sunan tana karatu" Mami tace "Fine then, idan kai ka haife kanka sai mu gani ai, ita Heedayar an gaya maka ikon mu ce??" Bai kuma ce mata komai ba, tace "I will advice you ka cire idonka a kanta don baxa ka ta6a samun ta ba, beside nawa take da har xaka ce kana sonta da aure, did you think xaka kara min shekara daya ne nn gaba, ba dai cikin shekaran nn Shaheedah xata gama ba, xaka sha mamaki" mikewa yyi yace "Sae da safe" tace "Allah ya tashemu lfya" daga haka ya fita dakin ya kulle mata kofa. Washegari da safe Farida ta gama hada few kayan da xata tafi da shi gidan yayarta a Abuja, Heedayah dai na xaune dakin duk ta xama abun tausayi, Farida ta koma kusa da ita tace "Ko xa kiyi ma Yaya magana yace Mami ta bar ki mu je tare" Heedayah ta share guntun hawayen idonta a hankali tace "Baxata bari ba, I know she is angry at him now bcos she caught him giving me food yesterday night" Farida tace "To yanxu wa xai yi mata magana ta ji? Nobody, cewa xata yi baki da lafiya" mikewa Farida tayi ta dau powder dinta a gaban mirror ta saka a handbag dinta kar ta manta, a hankali Heedayah tace "Ko mu gaya ma Ya Shureen yyi mata magana??" Farida ta juyo tana kallonta, dariya tayi sosai tace "He is not Shureen Heedayah, He is Shuraim" Heedayah tace "To ni ina ruwana ba Shureen naji kaka nace masa ba, ni dai mu yi masa magana koh?" Farida tace "Amma dai ke xa ki yi masa maganan" Heedayah tace "Ehh xan yi masa" Farida tace "Ina xa mu samo number sa?" Heedayah tace "Mami na da shi ai kamar, let me check" daga haka ta mike ta fita, a hankali ta bude kofar dakin Mami bata ganta a ciki ba, ta karasa gun wayarta da sauri ta dauka ta shiga contacts, searching sunan tayi sai ga shi ya fito with 080333.... Lkci daya ta haddace gaba daya ta ajiye wayar ta fice daga dakin, tana kallon Farida tace "Where is ur phone, I have crammed the digit" Farida ta mika mata wayarta Heedayah ta sa number snn ta marairaice tace "Are you sure we should call him Farida?" Farida tayi dariya tace "Yess try it, ki sa a handsfree in ji me xai ce" Heedayah ta xauna gefen gado xuciyarta na bugawa tayi dialing number, har ya gama ring ba a dauka ba, Farida dake ta kallonta ita ma xuciyarta na bugawa kamar ita xata yi masa magana tace "Redial it..." Heedayah ta kuma sending number ta sa handsfree tana xare ido, nan ma har ya gama ring no response, Farida ta ta6e baki ta cigaba da abinda take, a hankali Heedayah tace "May be baya daukan bakon number ko" Farida tayi mata wani kallo tace "As per shugaban kasa or governor dat he is ko???" Dariya Heedayah tayi, Farida ta ja tsaki tace "Ki je kiyi wanka may be Mami will change her mind idan ta ga mun shirya tare" A sanyaye Heedayah ta mike tace "Toh train xaku shiga?" Farida tace "Noo, Mami tace driver ne xai kai mu idan yace xai iya idan kuma baxai iya ba ban san yanda xa ayi ba" Bathroom Heedayah ta shiga bata ce komai ba, bayan kusan minti talatin ta fito daure da towel, wayar Farida dake kan gado ne ya fara vibrate, Heedayah ta xaro ido tana bin dakin da kallo don Farida bata nan, can tafi gun wayar tana gyara daurin towel dinta ta leka wayar taga number Shuraim ne, daukar wayar tayi xuciyarta na bugawa ta xauna gefen gado ta daga ta sa handsfree, sallama yyi daga daya bangaren ta wani xaro ido ta kasa amsawa, har sai da ya kuma yin sallama, kamar xata yi kuka tace "Uhn Ina ji" shiru yyi, a takaice yace "Waye wannan?" Ta kara gwalo ido tace "Ni ce fa" yace "Ke wa?" Ta turo baki tace "Ni mana" yace "Baki da suna?" Tace "Heedayah" Shirun 3 seconds yyi snn yace "Why are you calling?" Ta marairaice murya tace "Ya Shureen dama... dama" sai kuma tayi shiru, yace "Dama me?" A hankali tace "Dama Mami ce tace baxan bi Farida Abuja ba mu je gidan Maman Fadil, shine sai Farida tace ko xaka mata magana, shine na kiraka nake gaya maka" Yace "Faridar ta aiko ki wajena" ta xaro ido tace "Aa wllh, ba ta ma dakin ni kadai ce, na fito wanka yanxun nan sai naga wayar yana vibrate" yace "To baxa ki je Abujan ba" ta buda baki da farko, sai kuma ta fashe masa da kuka tace "Ya Shureen plss, wllh I want to go, ban ta6a xuwa ko ina ba tunda aka haifeni, nima ina son inje wani waje don Allah" Yace "Baxa ki je ba, xan xo kuma in gaya ma Mami bbu inda xa ki je" Daga haka ya katse wayar, Heedayah ta fashe da kuka ta ajiye wayar tana kallonsa tace "Wllh sai naje ina ruwanka da ni to" Farida ce ta shigo dakin tana washe baki tace "Guess what Didi, Mami tace mu je amma kwana uku kawai xa mu yi mu dawo sbda health status din ki" Heedayah tace "Toh bayan kin sa na kira wnn Shureen din yace baxan je ba din kuma xai xo ya gaya ma Mami kar a bar ni in je" Farida tace "Kai haba, da gaske??" Heedayah ta fashe da kuka tace "Wllh" Farida ta wani tabe baki tace "Toh ba sai ya hana ba mu gani, duk kece kika dage a kirasa xaki laka min kuma daga karshe, gwara ki tashi ki fara hada kayan kafin ma ya xo, Mami ta ma driver magana yace idan mun shirya mu fito" tashi Heedayah tayi tana share idonta ta dauko kayanta kala uku, Farida tayi kasa da murya tace "Make it Five, we are going to deceive Mami, sai ana gobe xa mu koma schl xata ganmu a gidan nan" Heedayah ta wara ido ta karo wasu kayan, Farida ta taya ta shirya kayan a jaka, ita kuma ta shirya cikin riga da skirt na atamfa ta daura dankwalin. Heedayah na gama shiryawa bayan ta fesa turare Farida tace "Ki tafi kice ma Mami thanks for allowing you, ni kuma xan kai mana kayanmu mota" Heedayah ta fita dakin ta shiga na Mami da sallama, Mami na xaune dakin tare da Junaid dake tsaye bakin mirror dinta ya rungume hannunsa, Heedayah ta kallesa tace "Ina kwana Yaya" yace "Lafiya lau" Heedayah ta karasa gun Mami tana murmushi tace "Mami thanks for letting me" Mami tace "Kwana uku kawai xa ku yi" Heedayah tace "Ehh Farida tace min haka" Mami tace "Kin sha drugs din ki? Kuma ki tafi da su kar ki manta" Heedayah tace "Toh" Mami tace "Ki kai cup din nan kitchen" Heedayah ta dau cup din da Mami ta sha tea ta fita, Mami tace "Kaga da ba don aiki ba da sai ka ajiye su, wani lkcn driver din nan na gudu sosai" Junaid dai bai ce komai ba, Heedayah na saukowa stairs aka bude kofar parlon, ido hudu suka yi da Shuraim, ta dauke kai da sauri ta karasa sakkowa ta shigo cikin parlon ta wani hade rai, wucewarta tayi kitchen ta tafi sink da cup din tana murguda baki, kamshin turarensa ta jiyo ta juya da sauri, ya karasa shigowa kitchen din yace "You have the guts ki wuce baki gaisheni ba koh" Ta marairaice tace "Allah sarki ya Shureen ba mun gaisa a waya ba, ai mun gaisa kuma Mami tace inyi sauri shi sa nayi sauri, amma idan na fito ai xan gaisheka dama, kayi hakuri don Allah" kallonta kawai yake yi, can ya juya ya fita, ta wani turo baki hade da murguda masa sannan ta bi bayansa, xaune ta samesa kan kujera, tayi kasa da kai tace "Ina kwana" yyi banxa da ita, wucesa tayi sai da ta isa stairs ta waigosa, hada ido suka yi, ta da'n xaro ido tace "Na gaisheka kuma baka amsa ba, Ina kwana" hade rai yyi yana kallonta tayi wucewarta sama da sauri, kin xuwa ta ce ma Mami yana parlor tayi, Ta shige dakinsu ta fara hawaye tace "Kinga har ya xo yace mata kar a je da ni ko" Farida ta xaro ido tace "Da gaske" Heedayah ta xauna gefen gado tana matsar kwalla tace "I hate him, ni na tsanesa" Zainab me aiki ce ta tafi ta gaya ma Mami tayi bako, Mami tace "Waye?" Zainab tace "Wannan sojan nan" Mami tace "Oh Shuraim, gani nan fitowa to" Zainab ta juya ta wuce, Mami na kallon junaid tace "I still don't like the way u and Shuraim are interacting.... Kamar wasu strangers" Junaid bai ce mata komai ba, tace "Toh ni ka wani xo ka tsaya min a daki kamar Soja idan nayi maka magana kayi shiru kamar kurma, do you have any problem?" Nan ma dai bai ce mata komai ba ya juya ya fita dakin ta bi sa da ido, tabe baki tayi ta mike ta dau handbag dinta da wayarta ta sauka downstairs, tafiyar su Farida take son gani kafin ta wuce aiki dama, bayan sun gaisa da Shuraim tace "Daga gida kake ko gun aiki?" Yace "Daga asibiti nake" tace "Toh yau bari in kawo breakfast din da kaina kila kaci" Farida ce ta sakko da jakar Heedayah, Mami tace "Kuna ta 6ata min lkci" Farida tace "Mun gama" Daga haka tace "Ina kwana" tayi wucewarta, Shuraim yace "Lafiya" Mami tace "Wai Abuja xa su tafi gun third daughter na, suyi 3 days kafin resumption" yace "Ohk ita kadai?" Mami tace "Noo with Heedayah, ai duk da bata jin dadi ba damuwa taje ko?" Shuraim yace "Ki bar su su tafi, ai naga ta ji sauki" Mami tace "Aa da sauki sosai, Ina ga stress din bikin ne kasan bata saba da wahala haka ba, banda haka ana xaune lafiya me xai janyo tayi pass out haka nan" Shuraim bai ce komai ba, Mami tace "Driver nace ya ajiyesu, Junaid xai fita aiki yanxu da shi na so ya kai su" Shuraim ya kalli agogo da ke nuna tara da few minutes, ya d'an yi shiru kafin yace "Ohk should I drop them" Mami tace "Haba Noo, Kai da ka kwana asibiti kana aiki, bari a lallaba kawai driver din ya kai su" Shuraim yace "Xan kai su..." Da damuwa Mami tace "To aikin fa anjima, kaga xaka ba kanka wahala sosai" Yace "Aa ba wahala" Shiru Mami tayi tana kallonsa. Ko da Farida ta koma sama waya ta tadda Heedayah ke yi, Heedayah tayi shiru ganinta, daga daya bangaren Khaleel yace "Wa xai kai ku Abujan?" Heedayah tace "Uhm" shiru yyi kafin yace "Ohk, but you can leave where you are and talk to me" Farida ta dau handbags dinsu ta fita, Heedayah ta bi ta da kallon gefen ido, a hankali tace "Driver xai kai mu" yace "Yanxu xa ku fito?" Heedayah tace "Ehh mun ma kai kayanmu cikin mota" Yace "But can't you convince them that ku bari ko nan da xuwa 12 ku taso?" Da mamaki tace "Saboda me?" Ya mike daga xaunen da yake a katon parlonsu yace "Convince them plss Heedayah, hanyar nan bbu kyau ynxu" Tayi shiru sai kuma tace "How did you know that?" Yace "Stop questioning me, just kar ku fito yanxu" Ta hade rai tace "Bayan mun riga mun gama shiryawa kuma mun kai kaya mota, idan naje nace ma Mami hanya bbu kyau ai tambayata xata yi me ya faru da hanyar kuma wa ya gaya min, wa xan ce ya gaya min??" Shiru yyi yana sauraronta, ta turo baki tace "Ni dai ana jirana a parlor byeee" yace "Wait Heedayah...." Tsayawa yyi tana sauraronsa, yace "Don't you no that kidnappers suna hanyar Abuja" da mamaki tace "To ai ba kullum suke fitowa ba...." Yace "Noo yau xa su fito" ta xaro ido tace "Ta ya kayi ka sani?" Yace "Na sani, bana son wani abu ya sameki kuma" tace "To me ya sa xa su fito yau din?" Yace "Akwai wani da suke targeting, yau xai bi hanyar.... So if they should meet people on road suna harbi ta ko ina ne" Heedayah ta bude baki lkci daya jikinta ya hau rawa tace "Su harbe mu??" Yace "Aa bance xa su harbe ku ba, but prevention is better than cure right?" Tace "Toh kai ya aka yi kasan they are targeting someone when you are not a kidnapper?" Ya d'an yi shiru kafin yace "Plan dinsu yyi leak ne" Bude kofar dakin aka yi Farida tace "Idan xa ki ajiye wayar nan ki ajiye ki fito mu wuce, ko wani karya yake tsara maki tun daxu haka" tsaki Farida tayi ta fita, Heedayah tace "Ni dai bye ana jirana" Daga haka ta katse wayar, sai dai banda faduwa bbu abinda gabanta yake tana naxarin maganan da yyi mata, then how did he know about kidnappers, ta bi dakin da kallo taga Farida ta sauka downstairs da handbag dinta balle ta saka wayar a ciki, wani karamin purse ta fito da ta saka wayar ciki snn ta dau mayafinta ta yafa, ta boye purse din a cikin mayafin ta fita dakin, corridor ta tadda Junaid a tsaye, ta sakar masa murmushi tace "Yaya xan yi missing dinka" a hankali yace "Are you sure" ta gyada masa kai, bude mata hannu yyi, ta bi corridor din da kallo kafin ta karasa ta basa light hug lkci daya kuma ta janye jikinta amma ta kasa kallonsa ta juya da sauri tace "Byee" har ta fara tafiya yace "Heedayah" tsayawa tayi amma bata juyo ba, ya karasa bayanta ya kamo hannunta ya sa mata kudi yace "In case you will want to buy chocolates" juyowa tayi tana murmushi tace "I appreciate, thank you so much" yace "You are welcome" daga haka ta sauka downstairs, Farida ta gani bakin kofa tsaye sai cika take, Mami kuma tayi forcing Shuraim yau dai yana shan just tea a gidanta, Heedayah na ganinsa ta daure fuska tace "Mami mun gama fa" Mami tace "Ku jira sa a compound" Heedayah ta karasa gun Farida suka fita compound din tare, Farida tace "Ke ki ji wai Shuraim ne xai kai mu Abujan" Still Heedayah tayi tana kallon Farida ko kiftawa babu, Can ta juya ta kalli motar Shuraim, sai kuma ta 6ata fuska ta fara matsar kwalla tace "What about the driver?" Farida tace "Oho Mami har tace ya wuce kawai" Heedayah tace "How are we going to cope travelling with him?" Farida ta sauke ajiyar xuciya bata ce komai ba, Heedayah tace "Did he even know the way to Abuja?" Nan ma dai Farida bata ce komai ba, Heedayah ta jingina da mota ta turo baki tace "I just feel like giving up, who brought this idea" Farida tace "Ni ki daina min tambayoyi kamar yar jarida, I don't know too" suna ta tsaye Farida ta jawo Heedayah tana perceiving jikinta tace "Ina kika samu turaren Yaya?" Heedayah ta xaro ido amma ta kasa cewa komai, Farida ta kara shinshina mayafinta tace "Wa ya baki turaren" Heedayah tace "Shine ya sa min wai ban sa turare ba" Farida tace "Lallai ko Mami baya ba turarensa, kinsan nawa ake sayar da turaren?" Fitowar Shuraim tare da Mami yasa duk suka yi shiru, Mami tace "Hope xaka kira Barrister ka sanar masa ko?" Shuraim yace "Xan kirasa" Mami tace "Ba don kar ku bata lkci ba kuma ai ya kamata su je can gidan suyi ma kaka sallama kasan halinta sai tace an walakanta ta ba a gaya mata ba" Shuraim yace "Aa ba sai an gaya mata ba, xan kira Abba in gaya masa" Mami tace "Toh shkkn, Allah ya kiyaye hanya, ya tsare ku da tsarewarsa, but plss drive carefully Shuraim" Yace "In sha Allah" Mami tace "toh jira ku ke a ce maku ku shiga motar ne" Farida ta bude back seat ta shiga, Heedayah ma ta shiga, Mami ta daga masu hannu tace "Toh Allah ya kiyaye hanya, ya kai ku lafiya my daughters" Duk suma suka daga mata hannu, Shuraim yyi mata sallama tace "Don't forget to call barrister plss" yace "In sha Allah," tace "But wait kana da fuel ko kawai ka tafi da motar nan" ta fadi tana nuna masa spare motar dake gidan tace "Daxu aka tafi fueling station aka yi full tank" yace "No nima full tank ne" daga haka ya tada motar suka bar compound din, Mami ta bi sa da kallo har ta daina ganinsu sannan ta koma ciki. Kafin Shuraim ya karasa titi ya kira Abba, bayan Abba ya daga yace "Abba xan je Abuja, amma yau xan dawo" Daga daya bangaren Abba yace "Me xaka je yi a Abuja, Anyway Allah ya tsare ka, safe trip" yace "In sha Allah, nagode" daga haka ya katse wayar, Mumy ya kira, tana dagawa bayan ya gaisheta yace "Mumy I will be going to Abuja now but anjima da yamma xan dawo" Mumy ta mike xaune daga kwancen da take tace "Me kuma xaka je yi a Abuja Aliyu, hanyar nan da ya xama abinda ya xama yan kidnapping sun yi yawa" Yace "Allah xai tsare" Tace "Ni dai duk sai naji hankalina bai kwanta da tafiyar ba, dama nayi mugun mafarki da asuba, aiki ne xai kai ka Abujan ko me?" Yace "Ehh" Tayi shiru, sai kuma tace "Dole sai kai?" Yyi murmushi yace "Ehh, ai yau xan dawo" tace "Toh ni dai don girman Allah har ka isa addu'a ya makale a bakin ka, wllh hanyar bashi da kyau kwata kwata Aliyu dama jirgin kasa ne bbu abinda xai daga min hankali, amma yau kaji an dauke wannan gobe kaji an dauke wancan ai da tashin hankali" Yyi kasa da murya yace "Ina tunanin xuciyar ki a tsarkake yake, kuma baki nufin d'an kowa da sharri, don haka ki kwantar da hankalin ki, in dai haka ne bbu abinda xai samu xuri'ar ki" Mumy da ta wani xaro ido tace "Uban me ya shigo da wnn xancen kuma, shi dama tsarkakken xuciya a goshi ake rubutawa, Ina ruwana da d'an wani da xan nufesa da sharri ni kuwa...." Yace "Aa misali na maki kawai..." Ta ja tsaki tace "Ni dai Allah ubangiji ya tsare min kai, ya kai ka lafiya ya dawo da kai lafiya, ya raba ka da sharrin mutum ko karfe, har ka karasa addu'a kada ya bace a bakinka" Yace "In sha Allah" daga haka ta katse wayar, ya ajiye yana d'an murmushi. Tun da suka fara fita cikin gari, Heedayah ke jin vibration din wayarta a jaka, Farida dake kusa da ita ma tana ji, Heedayah ta kalli Farida, Farida ta kalli Shuraim ta madubi idonsa na kan titi, Heedayah ta kai bakinta kunnen Farida murya can kasa tace "He has been calling tun daxu, I don't know why, how should I pick" Farida ta kara kallon Shuraim snn ta fiddo nata wayar a jaka ta mika ma Farida a hankali tace "Ki sa number a nan sai kiyi masa text message...." Da sauri Heedayah ta bude zip din purse din ta rufe da gyalenta snn ta haddace number don har snn wayar na vibrate ta mayar jakar ta kulle sannan ta sa number a wayar Farida ta tura masa message kamar haka "Muna hanya, I can't pick now" tana tura message din ta daga kai suka yi ido hudu da Shuraim da ya kallota, ya maida dubansa kan titi, a hankali cikin dubara ta koma gefe yanda ko ya kalli madubi baxai ganta ba sai dai Farida, ba a dau lkci ba Khaleel yyi mata reply yace "Kuna dai dai ina yanxu?" Heedayah ta kalli Farida, sai kuma ta jawota tana nuna mata text din, Farida ta bude hannu alamar bata sani ba, Shuraim yyi breaking silence din motar yace "Give me that phone u are holding" Heedayah ta xaro ido ta kalli Farida, Farida tace "Which phone, wayana ne fa" Yace "Ba da ke nake ba malama" Heedayah kamar xata yi kuka tace "Game fa nake yi" yace "Don't let me repeat my self" Farida ta saka wayar flight mode snn to koma can gefe, Heedayah ta turo baki ta mika masa wayar, fixgewa yyi daga hannunta ya ajiye kusa da nasa wayar. Bayan tafiyar kusan minti arba'in tun fitowarsu gida, Heedayah ta kalli Farida, rufe taga idonta har ta fara bacci, a hankali tace "Ya Shureen amai nake ji" ya wani hade rai yace "Amai??" Sai kiyi a nan ai, waye xai tsaya kiyi amai" Shiru tayi bata ce komai ba, bayan wani minti sha biyar din ta marairaice da kyar tace "Wllh yana damuna sosai, ka tsaya plss xai taho" banxa yyi mata, ta rufe bakinta tana kakarin amai, a hankali ya fara slow down ya gangara gefen hanya yyi parking snn ya bude motar ya sakko ya bude side dinta, da sauri ta fito, ta xagayo ta duka gefen daji tayi ta kakalo aman amma ya ki xuwa, rungume hannu yyi yana kallonta, bayan few minutes ta dago da kyar tace "Kamar ya koma" ya wani hade rai yana kallonta, mikewa tayi ta sunkuyar da kanta, yace "Dama kika sake sa na tsayar da mota kika sauka sai dai ki samu wani da xai mayar da ke gida, that is idan har na tsaya ma kenan" ita dai bata ce masa komai ba, ya bude ta wajen da take xaune, ta shiga motar ya kulle sannan ya koma driver seat suka ci gaba da tafiya. Khaleel ne tsaye da 5 of colleagues dinsa, message ya shigo wayarsa, dubawa yyi ya ga daya daga excort din Mai neman takaran gwamna ne da suke targeting yau, ya bude text din mutumin ya ga kamar haka "Mun kamo hanya minti kusan hamsin kenan" Khaleel yyi masa reply "Ohk" sai kuma ya xauna ya xauna yana shafa kansa, Saif na kallonsa yace "Ya dai Brainiac??" Banxa Khaleel yyi masa. Heedayah dai sai mutsu mutsu take a mota, Shuraim kuma lkci lkci yake kallonta, daga karshe tace "Ya Shureen" banxa yyi mata, cikin rawar murya tace "Wllh amai xan yi yanxu, pls kayi hakuri ka tsaya" yace "Yi a wajen" ta fashe masa da kuka tace "Plss xai xubo" ya daka mata tsawa yace "Wai ance maki ana tsayawa a hanyar nan ne" cikin kuka tace "Toh Amai xan yi mana" yace "Kiyi a wajen" tace "Wayyo baxan iya ba" Farida dai sai baccinta take kamar warce ke saman gado, kuka Heedayah ta dinga yi a hankali, Shuraim sai duba inda xai iya tsayawa yake, cos he knows how risky the road can be, daga karshe dai ya gangara gefen titi ya tsaya, ya bude motar ya sakko snn ya xagayo ya bude mata tun kafin ta gama fitowa ta fara kwarara amai a wajen, ya ja baya yana yatsine fuska yana kallonta, ta duka wajen ta dinga kwarara amai, bude front seat yyi ya dau ragowar bottle water dake wajen, ya cire mata mayafin jikinta ya duka ya bata ruwan, ta fashe da kuka tace "Yaya har yanxu bamu kai ba, ni baxan iya tafiyan ba kuma gwara in koma gida na gaji" ya daure fuska yace "C'mon amsa ki wanke fuskar ki" kin amsan ruwan tayi, ya xuba ruwan a hannunsa ya dago kanta ya wanke mata fuskar, bayan ya gama ya dagata suka mike ya bude motar yace "Shiga" ta shiga motar ya mika mata mayafinta snn ya kulle ya koma driver seat, ta jingina da kujeran motar tana sauke numfashi. Khaleel yace "Oga na san abinda nake cewa, na kuma san abinda na gani, beside dole in a week time Mutumin nan xai koma Kano, we should let it till then" Oga Manga yace "Wani maganan bnxa kake haka Khaleel, bbu fa wasu excort din kirki tare da shi, daga motarsa sai na bayansa, shkkn... Komai ya xo cikin sauki knn, this is just the right time da ya kamata ayi duk abinda xa ayi, snn mun samu labarin babu wasu jami'an tsoro a hanya, Khaleel I am saying ku san duk ynda xa ku yi mutumin nn ya shigo hannun mu yau yau din nan, bbu wani excuse dinka da xai shige ni wllh, nan da wani lkci xa su isa kauyen nan da muka shirya, kuyi maxa ku fito kawai, you guys just have to hurry up...." Khaleel dake ta sauraronsa yace "Ohk" daga haka ya katse wayar, Zayyad yace "Wai yane Kayy, kwanan nn fa you are not just active, anya mace bata shigo rayuwar ka ba?? Kar fa irin abinda ya faru da Ishaq ya faru da kai, kana dai nan kuma duk muna kallo Arne ya harbesa...." Khaleel ya wani tabe baki yace "Ni ayi gunduwa gunduwa da ni" Da mamaki Zayyad yace "Kana nufin tambayar da nayi maka da gaske ne?" Khaleel yace "Wnn ba matsalar ka bace, all I want u all to understand here is that in dai har kuka fita yau din nan.... don ni dama bbu inda xanje and nobody can force me out, to ina me tabbatar maku da kyar xa ku sha, kuma sai an kama wasun ku, mu hadu a garin Abuja" daga haka ya fice duk aka bi sa da kallon mamaki suna ji ya fita da motarsa... Shuraim ya hade rai yana kallonta ta mirror yace "Meye hakan??" Da kyar tace "My head is turning me" yace "Turn it back" bata ce masa komai ba ta goge hawayen da ya makale mata ta jingina da motar, suna isa wani junction, yana kallonta ta madubi yace "Xa ki ci Ayaba" ta bi wajen da kallo taga masu ayaba, ta girgixa masa kai tace "Amai xan yi idan na ci" yayi parking ya sauka, ya siyo mata apples, Farida sai lkcn ta farka tace "Why are we not moving?" Heedayah ta langwabar da kai tace "Xai siya min wani abu" Farida tace "Daxu ba naga kina amai ba" Heedayah tace "Amma baki ce komai ba ko" Farida tace "Toh ba gashi har fuska ya wanke maki ba, ni kawai sae na ci gaba da bacci na" Tana fadin haka ta kara gyara Kwanciyarta, Shuraim ya dawo motar rike da ledan apples, with bottle water guda biyu, back seat ya bude ya ajiye xae rufe tace "Ya Shureen xan koma gaba" Bai ce mata komai ba ta sauko rike da abinda ya siya mata, ya rufe motar ya mika mata ledan ta amsa ta koma front seat, shi kuma ya shiga driver seat suka ci gaba da tafiya.... Sai karfe daya suka shigo garin Abuja bbu wani tashin hankali, Heedayah ta juya ta tada Farida, Shuraim ya hade rai yana kallonta yace "Ance maki dakin ki ne nan" Farida bata ko kallesa ba ta gyara mayafinta, yace "Wani anguwar xa mu" Farida ta fada masa, har suka iso gidan yayarta kuma bata sake bacci ba, da ganin anguwar dai kasan na manya ne sosai, driver ya bude masa gate ya shiga yyi parking, farida ta bude motar ta sauka, Heedayah ma ta sauka, Maman Fadil ta fito da mai aikinta da murna tana welcoming dinsu, gaisawa suka yi da Shuraim tace "Bismillah, ka shigo ciki" yace "Aa xan juya ne" tace "Haba don Allah" yace "In sha Allah" Heedayah tayi wucewarta ciki tare da Farida ya bi ta da kallo, can yyi ma Maman Fadil sallama yyi reverse.

Chapter notes and social links

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull