Kenza eBookz

Heedayah complete Novel - Chapter 9

Heedayah complete Novel - Chapter 9

Heedayah complete Novel Chapter 9: Heedayah complete Novel Chapter 9. Heedayah is 300 via Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah, then u show ur evidence my…

3,643 words

Heedayah isn't free, you read for free 馃し馃徎鈥嶁檧锔忦煠佛煆烩€嶁檧锔�

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788.... 9/12/21, 8:04 PM - ,: Abba ne xaune main parlor bayan isha, lkci lkci yake kallon agogon dake manne bangon parlon, Mami ta fito daga part dinta sanye da hijab har kasa ta karaso cikin parlon tace "Good evening Barrister" yana kallonta yace "Good evening Rahinah" xaunawa tayi one sitter dake parlon tace "Gani" Abba yace "Me ya sa kika dau lkci baki fito" tace "Putting things in other" Bai ce komai ba, ya kalli hanyar kitchen don Mumy na ciki, tun daxu take kai wa take komowa ko gaisuwa bai hadata da shi ba tun shigowarsa, shi kuma hakan bai hanasa ce mata yana da magana a parlor da ita da Mami ba, xata sake komawa kitchen daga bangarenta yace "Maryam" juyowa tayi fuska daure tana kallonsa bata ce komai ba, yace "Ke muke jira" Tana masa wani kallo ta karaso cikin parlon tace "Ni ku ke jira? in maku me? A kan me ma xa ku jira ni? Nace maku ina da wnn lokacin ne? Plss I have more important things to do then sitting and staring at you both, bani da wannan lokacin barrister...." Ta juya xata bar wajen, rai bace yace "Ina magana xa ki wuce?" Juyowa ta sake yi tace "Bbu tasirin da maganganun ka xa su min barrister, in xauna kace xaka mana nasiha ko me? Did I tell you I need that, ita dai xaka xaunar ka ja ma kunne ta tsaya iya matsayinta a gidan nan kar ta ce xata yi karambanin xuwa kusa da nawa matsayin, matsayina daban nata daban, ni uwar gidanka ce kuma uwar 'ya yanka, ita kuma uwar rainon yar tsintuwar ka ce, wa enda xaka dinga ciyarwa, kaga banbancin kuwa ba karami bane, idan tace xata yi gigin matsowa lane dina ita xata kwana a ciki, so bbu wani xaunawa da xan yi ka hada mu kayi magana, bata kai matsayin ba, ga most important maganganun nan duk nayi, sai dai kawai tayi taking caution, ka kara mata da wanda xaka kara mata" Tunda ta fara Abba ke kallonta, Mami tayi yar dariya tace "To ai da sauki tunda kamar yanda xa a kira ki matarsa haka nima xa a kirani ynxu, kuma tunda baki isa korar yar tsintuwa ba balle ni Alhmdllh, muna nan sai mun xame maki kadangaren bakin tulu, xa ki gane matsayina da naki bai kai banbancin da xa ki dinga bragging ba...." A fusace Mumy ta karaso kusa da ita tana huci tace "Karya kike wllh, nace karya kike..." Tsawa Abba yyi mata yace "Kina da hankali Maryam??" Mami ta mike tace "Ina fa, sai dai in koya mata cikin yan kwanakin nan...." Daga haka ta bar masu parlon ta wuce bangarenta, Mumy ta fashe da kuka tace "Ka cuceni barrister, ka ci amanata, ka rasa warce xaka auro ka kawo mana gida sai yar bariki...." Mikewa Abba yyi ya dakatar da ita in few seconds ta hanyar nuna ta da yatsa strictly yace "Don't you ever try that again Maryam...." Bai jira cewarta ba ya bar parlon. Mami ce xaune that same night tana kallon Heedayah tace "Ina jin ki..." Heedayah ta marairaice tace "Tea kawai...." Mami tace "Kece kike cewa kina son tea din kenan" Heedayah ta girgixa kai tace "Ammi na ce take bani in sha da daddare" Mami tace "To da safe fa?" Tace "Tea and bread and egg" Mami tace "Da rana?" Heedayah tace "Indomie" Mami tace "Sai kuma da daddare ki sha tea" Kai Heedayah ta gyada mata, Mami tace "Toh after this night baxa ki sake shan shayi ba duk abinda aka dafa aka baki shi xa ki ci is that clear?" A hankali Heedayah ta gyada mata kai, Mami ta mike ta dauke fried rice da chicken dake cikin plate da Heedayah ta ki ci wai sai tea ta nufi kofa ta fita, hanyar kitchen ta nufa ta bude kofar kitchen din, tsaye ta ga Shuraim gaban kettle din ruwa alamar tea xai hada don ga kayan shayin a ajiye gefe, ta kasan tiles yake kallon wanda xai shigo kitchen din, yana ganin wacece kuma ya kauda kai ya ci gaba da abinda yake, Mami ta ajiye abincin hannunta ta nufi inda cups suke ta dau daya da cokali, ko kafin ta juyo har ya fice daga kitchen din, karasawa tayi gun kettle din ta juye ruwan ciki a cup din ta bude kayan shayin ta hada tea sannan ta fita kitchen din, Khadijah ta gani parlor ta shigo daukan takardunta, tana ganin Mami ta kwashi takardun ta wuce bangarensu da sauri, Mami dama tun da ta kalleta sau daya bata sake kallonta ba har ta wuce nata bangaren, sai da shayin ya huce sannan Heedayah ta sha Mami ta sa ta kwanta nan da nan bacci ya dauke ta. Washegari Saturday tun kafin yan gidan su tashi bacci Mami ta hada ma ita da Heedayah breakfast, da yake abinda Heedayah take so ne tsaf ta cinye komai, Mami dai sai kallonta take, sannan tace "Kin koshi ae?" Heedayah ta gyada kai, Mami ta mike tace "To mu je ki gaida Abba" har parlon Abba Mami ta kai ta, Abba dake aiki system ya daga kai yana kallonsu, Mami tace "Weldone" yace "Har ina tunanin kawo maki ki karasa" tace "Noo nima ga nawa can" yyi murmushi yace "Akwai maganan da nake son xa mu yi Rahinah" tace "Alright, but before then nima ina da magana da kai" yace "Yanxu?" Tace "Later..." Abba ya xaunar da Heedayah gefensa yace "How are you my dear" tana washe hakora tace "I'm fine" Mami tace "Baki yi gaisuwa ba" tace "Abba ina kwana" yace "Lafiya lau daughter" Mami tace "Let me freshen up" daga haka ta fita parlon, yana kallon Heedayah yace "Wa ke koya maki English" tace "My teacher" ya d'an bude ido yace "Really?" Tace "Ehh" Abba yace "Me da me yake koya maki kuma a ina yake koya maki?" Heedayah tace "Ammi tace min she's a Female, tana koya min komai da komai a gidanmu" yace "Wani sura kike?" Da sauri tace "Jinnnn" Abba na gyada kai so impressed yace "Kullum take xuwa koya maki?" Heedayah ta gyada masa kai, Abba xai yi magana aka bude kofar, Shuraim ne ya shigo parlon da sallama yana sanye da jallabiya, Abba ya amsa, xaunawa yyi nan kasa gefen Abbansa yace "Ina kwana Abba" Abba yace "Lafiya lau" Heedayah tace "Abba har da boko take koya min ma...." Satan kallonta Shuraim yyi ya kara hade rai, Abba na kallonta yace "Toh xan kawo maki warce xata dinga koya maki a nan gida" Heedayah ta wara manyan idonta tace "Thank you Abba, but..." Yace "But what?" Tace "Yaushe xaka kai ni wajen Ammina? Kila tana ta nemana" a sanyaye tayi maganan, Abba ya shafa kanta yace "Ina sha Allah xan kai ki, har yanxu ana neman Ammin taki" Tace "Abba ai gidan Yakumbo take" Abba yace "Eh ban manta ba xa mu je can" Mikewa Shuraim yyi ya nufi kofa yace "Sai anjima Abba" Abba yace "Da yaushe kake yi ma su Khadijah karatun qur'ani" Juyowa yyi yana kallon Abban nasa, ganin kallonsa Abban ma yake yace "Da asuba" Abba yace "Ohk, Heedayah will join also, sai ka dinga masu gaba daya" dawowa yyi ba tare da ya shirya ba ya durkusa inda ya tashi yace "Abba ai na kwana biyu ban koya masu ba" Abba yace "Eh to sai ka dinga yi mata ita kadai tunda ba Islamiyya xata je ba, su kuma dama suna xuwa islamiyya" Kasa cewa komai yyi yana kallon Abban nasa, Heedayah tace "Abba a suratul jinn nake" Abba yace "Eh daga nan xa ku ci gaba" Shuraim yyi karfin halin satan kallonta, Abba yace "That's all xaka iya tafiya, idan ya so sai in samar mata lesson teacher na boko kawai" Mikewa Shuraim yyi bai ce komai ba ya fice daga parlon ya kulle kofar, fuzar da iska yyi bayan ya fita ya juya yana kallon kofar da idanuwansa da suka sauya kala. Mumy ce xaune dakinta tayi tagumi, da ka ganta kasan tana cikin tashin hankali, kanwarta Salima ce xaune dakin, tace "Allah kuwa nake gaya maki Yaya, duk wannan tunane tunanen da saka kai a damuwa ba shi bane, just swing into action, dubi fa yanda take ta harkar gabanta a gidan kamar warce tayi wata da watanni ke kuma kina nan xaune kina ta wani kishi da damuwa, wllh tuwo da lafiyayyen miyan agushi tayi ynxu a kitchen, makauniyar kuwa na can ta kafa mata kujera a kitchen din tana xaune...." Mumy ta fashe da kukan takaici tace "Wllh Salima har ynxu na kasa yrda cewar kishiya barrister yyi min, gani nake kamar bakuwa nayi xata wuce, baki ji ynda xuciya ta ke min xafi ba, Kuma fa tun jiyan ko lekowa dakin nan bai yi ba, ita kuwa ta shiga bangarensa ina lura yau yafi a kirga, wllh ji nake kamar in banka ma gidan nan wuta kowa ya huta" Salima tace "Ba wani banka wuta Yaya, gashi kin fara bata chance ta kwace maki miji ta xama ita ce kan komai a gidan...." Mumy tace "Duk ba wannan ba nata bai tsaya min kamar yanda na makauniyar ya tsaya min a rai ba, ki bani shawara ta ina xan fara, me kike ga xan ma wnn yarinyar in huce takaici, ni dai baxan kasheta ba amma ina son abinda xan mata kissa ya fi mata alkhairi da shi, wllh na tsaneta, na tsani duk wani me son ya ganta kusa da shi ma, wllh sai na tarwatsa rayuwarta" Salima tayi dariya tace "Ni fa ban wani jin yarinyar nan Yaya, minti nawa ne xa a kada ta ta bar gidan ma gaba daya, ita dai wnn yar bokon ya kamata ki fara tunanin ynda xa ayi da ita ba yar yarinya ba" Mumy tace "To ni ta yarinyar nake tukun" Salima ta mike tace "Toh ki kwantar da hankalin ki Yaya, wnn me sauki ne, mu da muka san kan komai, yanxu dai ana jirana tun daxu a waje, xan dawo ko xuwa jibi" Mumy tace "Ba wani nan, ke din ce xan gani kwana kusa, idan kika tafi gantalin ki ba sai an gan ki ba" Salima tayi dariya tace "Ai ynxu na daina kwana a waje...." Mumy tace "Toh ni dai gobe xan taho gida kar ki fita don Allah" Salima tace "In sha Allah yaya, sai mun hadu goben" Daga haka ta fice daga dakin..... Bakin gate Salima ta kusa cin karo da Junaid xai shiga cikin compound din, ja baya tayi tana kallonsa, yace "Sorry" bata iya ta amsa ba har dai ya wuce ta, ta juya ta bi shi da kallo ko kiftawa babu, underneath her breath tace "Waow...." Tana tsaye tana kallonsa har ya isa entrance din shiga main parlor, ya kwankwasa kofar, Mami da ta san yana hanya ta fito daga kitchen ta bude kofar tana kallonsa tace "Har ka iso?" Yace "Ehh ina yini Mami" ta basa hanya tace "Lafiya lau" daga haka ta koma cikin parlon ya bi bayanta, saman kujera ya xauna tace "Ya su Uncle din naka" yace "Alhmdllh..." Kitchen ta nufa tace "I have been waiting for you since xaka dauko min sako a gida" Kafin ta shiga kitchen yace "Mami ina..." Mami ta juyo jin yyi shiru, tace "Wa?" Yace "Wannan babyn" dariya tayi tace "Sunanta Heedayah" yace "Oh ohk, Heedayah" Mami tace "Tana can tana bacci, let me get you water" Drink ta kawo masa parlon, duk suka kalli direction din da suka ji footstep, Mumy ce ta fito rike da makullin motarta fuskarta a murtuke, Mami ta nufi bangarenta don tado Heedayah, Junaid yyi kasa da kai cike da ladabi ya gaida Mumy, kallonsa ta kara yi snn ta amsa a dakile tayi ficewarta xuwa gidan Hajiya Sadiya ta ji ita kuma nata shawaran. Ba a dau lkci ba Mami ta fito rike da Heedayah dake sanye da doguwar riga iya gwiwa, duk gashin kanta a bude, kana ganinta kasan daga bacci ta tashi, Mami ta xaunar da ita nan kusa da shi tace "Ga Yaya ki gaishesa" daga haka ta koma kitchen don karasa abinda take, hannu Heedayah ta kai a hankali tana ta6a sa, har ta kai hannunta fuskarsa, ya kama hannun yana kallonta yace "Ina maki wasa ne?" Turo baki tayi tace "Nasan kai ne ai" hancinta ya ja yace "Sai na....." Ganin ynda ta 6ata fuska xata yi kuka ya jawota kusa da shi yace "Ohk sorry, let me pour you juice, xa ki sha?" Ta turo baki sai kuma ta gyada masa kai, ya bude drink din da Mami ta kawo masa ya diba, tace "Baka kawo Farida ba?" Bai ce komai ba ya kai glass din bakinta yace "Bude bakin" bude bakin tayi ya fara bata juice din a hankali, Mami ta fito kitchen din tana kallonsu tace "Da baka bata ba, bbu wani abincin da take ci sai kayan xaki" Heedayah na jin haka ta karasa shanye lemon da saurinta, murmushi yyi ya ajiye cup din, Mami tace "System dina xaka dauko min a gida yanxu" Junaid yace "Ohk..." Heedayah tana ta6a sa tace "Xaka je da ni??"

Chapter notes and social links

Heedayah is 300 via Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah, then u show ur evidence my WhatsApp digit 07087865788 sai in sa ka group. 9/12/21, 8:04 PM - ,: Baffa ne ya bude kofar parlon Kaka da sauri jin ihun da Heedayah ke yi ya shiga, shi ma shigowarsa gidan kenan daga masallaci an idar da isha, Kaka ce ta danneta sai shafa mata wani magani kamar rub take a kafan da ke ciwo, Baffa ya bude baki yace "Meye haka kuma Baaba?" Kaka dake ta hada xufa tace "Toh sai a biye mata tana dingishi baxa a san na yi ba, so ake ta dawo gurguwa ga makanta abun ya taru ya ma d'a na yawa? da wanne ake son ya ji, a hankali fa nake mata amma da yake munafuka ce algunguma dubi tonan asirin da take min kamar warce nake yankawa" Baffa yace "Don Allah ki kyaleta Baaba, ba tana shan magani ba, a hankali xai bar mata ciwon ai" a fusace Kaka tace "Maganin banxa maganin bature, ka san daga wani kasa aka kawo min wnn din da nake shafa mata, ku dinga kallona kamar ban san me nake yi ba, toh naki kyaletan sai ka kwace ta ai" Ita dai Heedayah bata fasa ihun da take tana kiran Abba ba, aka bude kofa Sudais ya shigo parlon da sauri shi ma daga masallacin yake, Bude baki yyi yana kallon kakar tasa, tace "Kai ka ji ubanka da wani magana Sudess, daga taimako fa xai min rashin kunya, ita kuma yar banxan magani fa nake shafa mata...." Sudais yace "Toh kaka ba ke kika sa ta wanke wanken ba, ai sai bari har lkcn da kafar yyi niyyar warkewa ya warke da kansa, ynxu hakan da kike mata idan kika sake ji mata wani ciwon fa?" Kaka ta tura Heedayah a fusace tace "Ni dai Allah ya isa wllh, ya xa a dinga cewa ni na sa ta wanke wanke, ga yarinya dai da bakinta ko bata da ido ai sai ku tambayeta ta fadi gaskiya mana, kawai kawai an mayar da ni karamar mutum a gidan nan sbda ana bani abinci a kwano.... Ban da xalunci me xai sa in sa makauniya wanke wanke idan ba ita ta bukaci yin hakan ba da kanta??" Juyawa Baffa yyi ya fita daga parlon, Sudais ya jira har ya rufe kofar sannan yana nunata yace "Ke dai kawai baki son gaskiya, ki yarda kawai kin kusa karya yar mutane kin sa ta wanke wanken da kika tara an kwana biyar...." Kaka ta fashe da matsanancin kuka tana jawo dankwalinta xata yi hankici da shi, Sudais ya daga Heedayah suka fita parlon ya kulle mata kofarta yana murmushi, Heedayah dake dingishi tashin hankali a fuskarta tace "Plss ka wuce da ni wajen Abba kar ka dawo da ni nan" kallonta yake bai ce komai ba har ya isa stairs, daukarta yyi ya wuce sama, dai dai xai ajiyeta sai ga Ummarsa ta fito daga part dinta, tsaye tayi tana kallonsa da mamaki fuskarta, yace "Sannu da gida Umma..." Bata amsa ba tace "Ka sameni a parlona yanxun nan" daga haka tayi wucewar ta, bangaren Aunty ya shiga yana rike da Heedayah, Aunty dake xaune saman darduma ta idar da sllh tace "Ta ya kaka ta yrda ka fito da ita, daxu da rana kiri kiri taki yarda in fita da ita, wai ba ruwanta yar amana..." Sudais yyi dariya yace "Ae tana can na barota tana kuka" Aunty tace "Kai dai baka gudun abun magana koh Aliyu?" Ya xaunar da Heedayah saman kujera yace "Danneta fa tayi tana ta ihu wai magani take shafa mata a kafar" Dariya Aunty tayi ya juya yace "Ina xuwa Umma na kirana..." Tace "Amma xaka dawo ai" yace "Ehh xan dawo" daga haka ya fita, Dawowar da bai yi ba kenan har sha biyun dare yyi, Heedayah har ta gaji da tambayar Aunty ko ya dawo, Aunty ta kai ta bathroom dinta tayi fitsari sannan ta kwantar da ita saman gadonta nan da nan bacci ya dauketa, yaranta kuma suna dakinsu dama... Aunty na kwance har ta fara bacci ta ji ana kwankwasa kofar bedroom dinta, ta mike ta kunna wutan dakin tana kallon agogo ta isa kofar ta bude, Baffa ta gani tsaye kafin ta ce komai yace "Yarinyar nan na nan ne?" Da mamaki Aunty tace "Tana nan har tayi...." Hango kaka da tayi tsaye bakin kofar parlor tayi kicin kicin da fuska ya sa tayi shiru, Baffa yace "to fito da ita" Aunty bata ce komai ba ta juya ta koma dakin, sai a sannan ta girgixa kai ta shiga tada Heedayah, tana rike da hannunta har sannan tana magagin bacci suka fito parlon, Kaka tace "A bani amana sbda ance maku ban san girman amana ba xa ku cuceni ku dauketa, to uban me xata maki a nan din banda gulma Hauwa? wllh Umaru kasa bacci nayi, gani nake kawai Allah na fushi da ni, idan Amadu ya ji wnn me ku ke son ya daukeni? To ba ruwana a maido min da abata...." Baffa dai bai ce komai ba, Kaka ta warce hannun Heedayah a na Aunty ta fice daga parlon Heedayah da har baccin ya fice a idonta jin muryar kaka ta dinga bin ta kamar xata yi kuka, Baffa ya girgixa kai yana kallon Aunty yace "Toh Allah ya kyauta" dariya tayi tace "Halan har ka fara bacci" yace "Nayi bacci mana dama" daga haka yyi mata sai da safe ya fita. Kaka na shiga bangarenta ta kulle kofar tace "Gantalallen yaro kawai in sake ganinsa a parlona idan ban ja Allah ya isa ba" furan da ta rage ma Heedayah ta dauko mata ta ajiye gabanta tace "Gashi nan baxan shanye ban baki ba kar Allah ya tambayeni, duk da mugun halin ki" Heedayah ta ta6a cup din a hankali ta kai baki ta fara shan furan kamar xata yi kuka. Washegari juma'ah da safe Mami ta xo tafiya da Heedayah, Kaka ta kwaso kayanta da ta wanke ta linke su fesss tace "Sai kin sa ido sosai kan yar nan, shegen son jiki ne da ita kamar mage, baxa a fake da makanta ba a cuceta...." Mami tace "Toh mama" Kaka tace "Toh har yanxu baki saka ranan tarewar bane ke kuma? Ba a fa wasa da igiyar aure" Mami tace "Yanxu haka can gidan xa mu wuce gaba daya" Kaka tace "Toh alhmdllh, kin dai ji duk nasihar da na maki ranan ai ko, yanxu haka matar na can ta dawo, bbu ke bbu ita" Mami tayi murmushi tace "In sha Allah" sai kusan sha daya suka bar part din Kaka tare da Heedayah..... Horn Mami tayi dai dai gate din gidan Barrister Ahmad, mai gadi ya bude gate din ta ja motar xuwa cikin gidan tayi Parking a space din yin hakan, Da taimakon ta Heedayah ta fito a motar, tana rike da hannunta suka nufi entrance din shiga main parlor, Shuraim ne xaune balcony din da system a gabansa, tun daga nisa da ya kallesu ya dauke kai ya ci gaba da abinda yake a laptop har suka iso balcony din, Mami bata kallesa ba tace "Take off ur shoes Heedayah" Heedayah ta fara cire takalmin kafarta, Mami ta ajiye su gefe, ita kam dama bata cire nata ba da shi ta shiga tana bude jakarta don fiddo wayarta dake ring, ta daga ta kai kunne, Hajiya Amina mahaifiyar Sudais ce parlon da Mumy sai Hajiya Sadiya da Hajiya kyauta, kallo daya Mami tayi masu ta cikin siririn glasses din idonta still holding Heedayah's hand ta nufi bangarenta tana cewa "Ai court ma baxata bada bail dinsu ba, their case is different, baxai yiwu ba ma, so kar ku ji komai, pls hold on I will call you later" tana fadin haka ta katse wayar ta fiddo makullinta don bude bangarenta wanda aminiyarta da sister dinta suka xo tun jiya suka yi gyare gyaren da ya kamata, tana shiga ciki rike da Heedayah ta kulle kofar. a hankali Hajiya Sadiya tace "Tabdijam, lallai kina da aiki babba a gabanki Maryam, idan baki yi hankali ba wnn farar matar dai kwace maki gida ta shigo yi, ke kin ji wani kamshi da take xubawa kuwa, kalli fa ko kallon arxiki bata mana ba sai xancen kotu da bail take, da takalmi ma ta shigo parlon don rainin wayo..." Hajiya Maryam da taji kamar xuciyarta xai fashe don kishi bata dai ce komai ba nan ko naxari iri iri take yi a xuciyarta tana tunanin ta ina kenan xata fara....

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull