Kenza eBookz

Idan kaya ya gaji book 3 - Chapter 16

Idan kaya ya gaji book 3 - Chapter 16

Idan kaya ya gaji book 3 Chapter 16: Idan kaya ya gaji book 3 Chapter 16. Babangida:. Tunda dai ya sallami abokanshi, ya sallami Amarya da danginta da su…

4,456 words

Babangida:. Tunda dai ya sallami abokanshi, ya sallami Amarya da danginta da su tsire da lemukan kwalba. Sai ya nufi ɗakin Sabuwa.yana tura ƙofar ya shiga kanshi ya juya mishi sosai ganin babu ko tsinke a ɗakin sai bargo da yaran suke kwance dukkansu kawai. Duk sunyi bacci yaran banda Mardiyya da idanunta biyu idanuwanta sunyi jawut halamun taci kuka irin na fitar hayyaciinnan. Tsugunnawa yayi a kusa dasu ya rasa abinda zaice yayi shiru na tsawon lokaci masu yawan gaske. Ga wayarta Sauban yanata kira biyayya irin nata taƙi ɗaga wayar, da idanu Babangida ya kalli wayar kawai. Sai can yace da Mardiyya. "Sabuwa da kanta tazo ta ɗebe kayanta shine ta kasa bar muku katifa?" Ajjiyar zuchiya na tashin hankali ya sauke ya sake ja ya sauke. "Ba ita tazo ta kwashe kaya ba su Maigogul ne suka zo dasu Gaza" Ƙur yabi Mardiyya da idanunshi tausayinta ya kamashi sabida itace babba yanzu hankalinshi ya dawo kanta ne baki ɗaya burinshi ya kawar da'ita a gabanshi kawai amman rayuwa mai kyau da inganci yake nema mata ba Auren Sauban da Sa'a zata ta cusguna mata ba. "Shikenan kuyi haƙuri ku kwana a hakan gobe in Allah ya kaimu zan siyo muku gado da katifa. Mardiyya kece babba ki kula da ƙannenki kinji? Sannan kada ki ɗaga wayar Sauban na riga dana rabaku, akwai abinda nake so in zaunar dake mu tattauna ɗiyata. Akwai abinda kuke so ne?" Miƙewa zaune tayi ta gyara zamanta da kyau. "E Baba mu dai so muke zan dinga mana girkinmu daban ba sai mun jira kowa ba dan Allah Baba" Wallahi Babangida sai yaji hawaye na zubo mishi tsabaragen rauni. "Bayan wannan kuma me kike so Mardiyya dan Allah kiyi gaggawar sanar dani zan sama muku shi" Ya ambata a ƙagauce cikin zabarin son jin me take so kuma. "Shikenan Baba, kuma muna so duk juma'a tunda babu islamiyya mu dinga zuwa wajen Ummi muna dubata. Baba ba daɗewa zamu yi ba. Inma kaine zaka dinga kaimu ka jiramu duk babu damuwa" "To shikenan zan duba in gani. Bawai bana son kuje inda Umminku take bane, gidanne kawai bana son kuna yawan zuwa. Amman zan ƙoƙarta ko sau ɗaya a watane zan dinga kaiku." Da wannan matsayar suka tsaya. A ɗakin Ramatu yaje ya kwanta, amman tunanin Cus da baƙin rashin kunyarta wanda a yanzu yake jin dama zata dawo tazo tai ta yi mishi fitsarar idanu zai zuba yaita kallonta tana ƙara burgeshi ya hanashi bacci Washegari gida ya kaure da yinin biki, shi kuma ya tsallake gidan ya siyo ma su Mardiyya gado da katifa, sai katifa tasu Adda'u. A wajen Mustapha ya amshi kuɗin bashi, duk da Mustapha ya sanar mishi babu bashi tsakaninsu amman shi ya kafe kan saiya dawo mishi dashi. Yana isowa yaga Sauban da Mardiyya a ƙofar gida Sa'a tana dukan Sauban tana zaginshi daidai isowar Babangida. Ranshi ya kai iyakar sosuwa murmushi mai ciwo yayi kawai ya sakko a gaban motar kaya. Sa'a na ganinshi ta shige gida Babangida ya ƙaraso ya dafa kafaɗar Sauban. Mardiyya dake kuka ya kalla. "Ki shiga gida Mardiyya kada ki sake kuka" "To Baba" Juyawa tayi ta shige, Babangida yabi takun yarinyar da kallo har saida ta kule ya dubi Sauban. "Sauban kayi haƙuri Mardiyya Ɗiyata ce, kai kuma Sa'a ce mahaifiyarka. Tunda dai ta nace bata sonka da Mardiyya kayi haƙuri Allah zai ɓullo mata da wanda zai sota a yadda taken wani bare can. Yarinya bai kamata a hukuntata da laifin iyayenta ba. Shin Sa'a ta taɓa faɗa maka wani abunne dangane da dalilin da yasa za'a haɗa Auren naku?" "A_a Kawu na sha tambayarta ma dalili amman bata faɗa mun. Amman Kawu ni koma menene inason in auri Mardiyya kuma mahaifina ma ya amince. Kawu dan girman Allah kada ka rabamu. Jiya yadda naga rana haka naga dare, yanzu haka zazzaɓine a jikina, a duba lamarinnan kawu" Murmushin gefen baki Babangida yayi. "Sauban kenan. Kayi haƙuri dai wannan auren bazai yiwu ba. Ina mai baka umarnin kada ka sake zuwa wajen Mardiyya kuma kada ka sake nemanta a waya ka barta zuchiyarta ta warke, ka yarda ta manta dakai, kaima ka daure ka mance da'ita kada akan ku ku biyu zumunci ya ruguje" Hannunshi ya sauke a kafaɗar Sauban ɗin. Da haka Sauban ya ɗauke ƙafa a rayuwar Mardiyya sai dai fa ya ƙudurce a ranshi shi da aure har abada bazai yi ba in dai ba Mardiyya aka aura mishi ba. Haka yaita jinya a tsaitsaye yaro duk ya zauce ya fita kamanninshi fa. Ango Babangida dai haka ya kwana a ɗakin amarya ga ɗansu a falo Amir abun dai babu armashi amman ya riga daya rungumi ƙaddararshi kawai. Kuma yaji canji akan da sosai. Ko da su Sa'a suka ga Amir tabbas sunce kamarshi sak da mardiyya kamar kwabo da kwabo. Amman tunaninsu bai basu cewar Ɗan na Babangida bane. Sabida sun san wannan kamar ana iya samunta ko da ba'a ma taɓa ganin juna ba. Magungunan mata da Sumy tai ta dibga sunyu aiki sosai a jikinta. Washegari ya haɗa kan matanshi a ɗakin Ƴar Shuwa tunda itace babba. Tayi farin cikin girman data samu amman tana kishi da Sumy sosai musamman yadda taga Babangida na wani kallonta. Gata Ƴar duma duma da'ita fatarta akwai kyau da gani zata yi laushi sosai. Baki ta taɓe daya faɗa musu ɗanta zai zauna a hannunta. Haka dai ya tsara yadda za'a dinga girki da karɓa_karɓan kwana a tsakaninsu. Rayuwar dai taita shurawa aiyuka sukaima Babangida yawa sosai dan yana koyarwa a makarantu fin uku. Kuɗi yake tarawa yana so in Allah ya dafa mishi zai koma sana'ar Baban bola irin na unguwa da ake kawo musu suke siya, in sun tara kamfani tazo ta kwashe. Tsakanin Ƴar Shuwa da Sumy kuma ana buga kishi da kirsa na ƙin ƙarawa sosai Sumy suke zaman gugar jigida da Yar Shuwa abin duniya yabi ya damu Ƴar Shuwa sosai. Ramatu kuwa tana gefe dan wannan faɗa yafi ƙarfinta nesa ba kusa ba, basa ma ta tata sam. Duk juma'ar ƙarshen wata yana kwasar yara ya kai gidansu Sabuwa. Amman gudun fitina sai dai ya jira su Mardiyya a bakin layin su Sabuwa ya basu awa ɗaya suje a gaggaisa sai su fito ya maidasu gida Allah baisa ya taɓa ganin Sabuwa ba tunda dai ta bar gidanshi. Adama ko Labbai dai su suke rako yaran wajenshi. Gaga_gaga haka rayuwa taita garawa har zuwa tsawon wani lokaci. Yana tsaye a bakin mudubi yana gyara tsayuwar hularshi Ƴar Shuwa ta shigo ta sameshi ya buga shadda mai ruwan toka. Wani ƙududun baƙin kishine ya turniƙeta ta tsani juma'ar ƙarshen wata kamar yadda ta tsanii mutuwarta sabida tasan Babangida sabida Sabuwa yake son zuwan. Amman in ba haka ba ai yaran sun san hanyar zuwa gidan ya barsu su tafi da kansu mana. A duk lokacin da zaije kaisu kwalkiya ta musamman yake yi. Duk da ta baza ƙannenta suna mata c i d kuma sun tabbatar mata Babangida baya haurowa layin shine ma ta ɗan samu sassauci amman fa ba sosai ba tunda tasan gurbin Sabuwa yananan. Kuma wani faɗa da suka yi duk kishinta sai da ta roƙeshi ya cikace mata huɗu ya kulle ƙofa ita zata fi samun nutsuwa. A wannan faɗanne yace da'ita har gaba da abada gurbin Sabuwa zaici gaba da kasancewa dan bai cire ranshi da dawowarta ɗakinta ba. "Lafiya wannan irin kallo kamar zaki hadiyeni. Tunanin me kike yi haka inata magana shiru?" Cewar Babangida dake magana da yar Shuwa yana fesa turare. "Hmm naga sai sake gyara zaman hula kake ta faman yi tun tuni sabida zaka je gidansu tsohuwar matarka. Ai na riga dana bugo jirginka duk wannan kwalliyar sabida ita kake yi. Wai ni Babangida zawarcin Sabuwa kake yi ne ko?" Murmushin cusa haushin daya saba shi ɗin dai ya kuma yi kafin tace. "Me kika gani?" Yayi tambayarne sabida yaji abinda zata ce. Yana mamakin yadda tafi kishin Sabuwa fiye da sauran kishiyoyinta. "Sabida naga yadda kake ɗaukar wanka da aro motar abokai in zaka je wajenta abun yayi yawa. Sannan tunda dai Sabuwa taso rabuwa dakai ta makaka a kotu ka dena baccin kirki kullum kana Sallah. Da alƙali ya saketa sai ka sake ƙaimi wajen sallarka ta dare ni shine na kasa gane maka. Wai dama Sabuwa kana sonta duk abinda kaita mata a rayuwa har saida ka kaita maƙura?" Murmushi yayi kafin yace. "Ina mamakin yadda kika tsani aminiyarki sabida ni. Da gaske na ɗauka ni'imar da ƙawarki take ciki kaɗai kika biyo. Sai daga baya na fahimci da wata manufar taki ta daban kika shigo ni tsanine kawai. Kina bani mamaki in kina kishi da Sabuwa. Sabuwa da kike gani mun rabu ne bamu rabuba wallahi. Zauna kina nan zaki ji ana guɗar shigo da'ita cikin gidannan a karo na biyu. Dan tuni ciniki ya faɗa" Yayi hakanbe danya haɗa zuchiyarta da aiki na wuni guda, tunda yasan shi sakine mara kome itace jahila bata sani ba. Ficewa yayi daga uwarɗakin zuwa falo. A guje ta sha gabanshi a kiɗime. "Wai dan Allah Sabuwa zaka sake kwaso mana duk rashin tarbiyyar dake tattare a gidansu?" Ranshi ya sosu da abinda tace akan Sabuwa har fara'ar da yake yi saida ta ɗauke. "Da gidansu Sabuwa da gidanki duk ɗaya nake kallonsu. Ki ƙaddara gidanku yafi nasu tarbiyya amman ai kema tarbiyya Maigogul ne tunda a cikin gidan kikai rayuwarki. Ashe ke butulu ce Yar Shuwa har haka. Waime Sabuwa ta tsare miki ne haka? Wallahi Sabuwa ko yanzu tayi miki fintinkau, ta tafi data tashi tafiya saita warce zuchiyata tayi tafiyarta dashi. Aisha babu komai a ƙirjina Sabuwa ta tafi da komai, kuma bazan iya karɓowa ba. " Yana isada maganarshi ya ajjiye kuɗin cefane akan kujera. "Sakwara da miyar kifi za'aci yau a gidan. Sannan kada ki cika ma doyar ruwa sakwara in ba Sabuwa ce tayi ba bana gane kanta duk saita sake. Ko ita zaki kira a waya ta taimaka ta faɗa miki yadda take yi ne?" Ya ƙarashe zancan yana dariya ya barta a wajen zuchiyarta kamar zata toye dan ƙuna. Su Mardiyya kuma Babansu na fitowa suma suka fito ko wanne cikinsu zuchiyarshi cike da murna. Mota suka shiga Babangida ya ja motarshi fu. Wayarshi ce tayi ruri Sumy ke kiranshi amman bai ɗaga ba dan tun da dai ta fahimci Babangida ta ƙare mishi bashi da komai saita buɗe faifayin rashin mutuncinta gashi tazo a lokacin da rashin Sabuwa ya ladabtar dashi da kuma alƙawarin daya ɗaukarma kanshi in ba dai da wani ya kama matarshi ba, ko kuma tayi yinƙurin kasheshi ba. To babu batun saki haka su ukunnan zasu ci gaba da zama har mai rabawa ta raba su. Suna isowa bakin layin ya hango motar Khalid a ƙofar gidan. Tabbas ya shaida motar sarai. A madadin ya tsaya saiya kunna kan motarshi zuwa cikin layin. Kafin ya ƙaraso ya hango Sabuwa ta shige motar Khalid. Wani yawu mai ɗaci ya haɗiye take jijiyoyin kanshi sukai raɗa_raɗa. A bayan motar yayi parking. Yana ta ambaton Allah dan har wani duhu_ duhu idanunshi suke yi. "Mardiyya ku shiga gidan ku gaisa da kowa ku fito mu wuce" Yadda yayi maganar kaɗai yasa kowa ya shiga taitayinshi kawai. "To Baba" Kaɗai Mardiyya ta iya cewa ta tusa ƙannenta a gaba. Yana yinƙurin fitowane ya hango mahaifiyar Ƴar Shuwa ta leƙo tana waige_waige ga waya a manne a kunnenta. Jikinshi ne ya bashi Ƴar Shuwa ce duk yadda akayi tasa a leƙoshi a gani..zuchiyarshi na tafasa Allah _Allah yake yi ya fito yaje ya samu Khalid ya fesar musu da maganganun da suka daɗe a zuchiyarshi. Bai jira komawar Maman Ƴar Shuwa ba ya fito ya tunkari motar tasu.

SABUWA:. Ƙur mukaima juna ni da Khalid. Wallahi har ga Allah har kuma a cikin raina inason Khalid. Sai dai matsala guda biyu. Na farko rayuwar da muka gudanar a baya. Na biyu rayuwar da muke gudanarwa a yanzu tun da aurena a kaina. Inna Auri Khalid banyi ma kaina adalci ba. Kuma duk bala'in sona da yake yi bazai hanashi zargina ba. Kuma zai iya fin Babangida rashin ganin darajata da kimata. Zan iya komawa gidan da yafi na jiya. Ai ina ganin zai fi mun sauƙi in Auri mutumin da wani abun bai taɓa shiga tsakaninmu ba. Duk da wannan shine abu mai wuya duk wani ɗan mutunci bazai zo neman aurenmu yazo ɗaya biyu ƴan unguwarnan su barshi yazo na uku ba. Ina tunanin irin su Khalid sune daidai da irin rayuwarmu. Ya Allah ka kawo mun ɗauki amman dai irin rayuwar da nayi a baya har abada bazan koma ba, ya Allah kayi riƙo da hannayena. Hannuna da Khalid ya riƙe gam ne yasa na buɗe idanuna muka ƙurama juna idanu. "Sabuwa naga kinyi ƙiba kin sake yin haske. Da ganin yanayinki kamar kin samu ƴar nutsuwa. Na buɗe baki zan yi magana tare da yinƙurin fisge hannuna kenan saina ga Babangida ya zuro kanshi cikin motar ta ɓangaren da Khalid yake. Da sauri Khalid ya waiga jin hucin mutum a gefenshi. Idanu suka haɗa da Babangida idanunshi sunyi jawur jijiyoyi duk sun tattaso a fuskarshi. Da sauri Khalid ya saki hannuna ya haɗe ranshi shima. "Kai a tunaninka kaci nasara ka rabani da Sabuwa ko? Hmmm ka sani duk wanda yayi guga da nufin zai ɗebi duniya ko ya jawo bazai ga komai ba. Ka neme ta da aurena a kanta ma balle yanzu da saura kwana uku ta gama idda. Ke kuma kin kyauta dama halinki ne. Abu ɗaya nake son sanar muku wallahi _wallahi wannan mitsiyacin bai isa ya aureki ba. Yadda na rasa shima sai dai ya rasa. Sannan in dai irin hannun wannan ƙazamin kike son komawa ai kinyi gwari kuma kinci baya. Mutumin daya nemeki yake kwanciya dake, ya kai ki hotel_hotel shine harda yo miki tsarabar rigar mama da ɗan kamfai, da sigari da aure a kanki shine kike tunanin gidanshi zaki koma kuma ki samu nutsuwa, shi kike tunanin ki aura Sabuwa?" Murmushi yayi mun idanunshi tamkar zasu zubo da ruwan hawayen da suka taru yace. "Kinyi gwari Cus kinyi gwari Cus. Ajjiyeki zaiyi a gida yaita zarginki, kuma ba zaki taɓa burgeshiba neman matanshi zaici gaba dayi ya lalata miki rayuwarki a banza daga ƙarshe hawan jinin dana ɗaura miki ya kasheki a banza. Dake ke jahila ce ai lissafinki bazai kawo mik..." Ya isheka nace Babangida ka sani kai ba ubana bane. Kuma na yarda na gamsu zam auri Khalid ko dan in ƙunsa maka baƙin cikin da zai yi ajalinka ko yayo maka sanadin kamuwa da cuta marar warkewa kamar dai yadda ka haddasa mun hawan jini. Yaya kuke so in saka kainane" "Rufa mun baki ko in bubbuge bakin naki wallahi " Ya ɗaga hannu Khalid ya cabke. "Sanda take gidanka ma..." Fisge hannunshi Babangida yayi ya shaƙe wuyan Khalid da mugun ƙarfin da Khalid ya kasa ƙwatar kanshi. Fitowar yaran da Maigogul ne yasa ya sake wuyan Khalid. Da sauri na fito a motar yaran suka nufo ni. Maigogul kuma ya nufo wajen Khalid har jikinshi na rawa. Sororo Babangida yayi yana kallon yadda Maigogul yake ɓare_ɓaren son karasawa wajen Khalid har yatsu Maigogul ya take mishi. "Ummi ashe kina waje. Ina wuni?" Cewar Mardiyya da take kallona cike da fara'a. Ina nan ai banga shigowarku bane shi yasa. To ya karatun? Aminu, Yaya Aɗɗa'u yaya rashin ji? Malama yaya rashin son magani." Babangida yace. "Ku dallah ku tawo muje ni na gaji" Jin yadda yayi maganar da zafine yasa yaran sukai saurin juyawa. Da harara ya bini kawai ya tusasu a gaba suka wuce. Maigogul yana wajen Khalid yana zubar da mutunci. "Ke Lolo tawo mana me kike yi a tsaye da yara ki barsu su tafiyarsu" Yana juyowa yaga ni kaɗaice a tsaye. "Au ashe sunma tafi ai dai yafi. Kinyi baƙo maimakon kiyi ciki dashi a_a sale_salin ƴan unguwa su ganku aje a tareshi ai mishi munafurci. Ki kaishi can gidanku " Wani ƙududun baƙin cikine yasa nace. Ai mun gama Maigogul." Ina faɗin haka nayi shigewata ciki na barshi da Khalid ɗin. Ya suka ƙare oho ya dai shigo ya nemi gefen gado ya zauna yana dandalan yawu yana ƙirga kuɗi. Rakiya sai harara take zabga mishi. "Wai Sabuwa shi wannan ɗin da dai batun aure yazi dai ko? Naga akwai gari a hannunshi ni dai na shaida mishi nanda kwana huɗu ma ya turo magabatanshi" A_a Maigogul wallahi ni ba aurenshi zanyi ba. Gaskiya karma ka karbi kuɗinsu Rakiya ki saka baki fa a wannan karon ba yadda zanyi ba wallahi. Yaushe ma na gama warkewa akan ciwon baƙin cikin Babangida " Takalmi ya jefo mun nayi maza na rufe fuskata. "Mara kunyar kawai ni zaki ma baƙin ciki dan abu ta kazan...." Miƙewa nayi da sauri zan gudu yako yi nasara ya tare ƙofa. "Yau ga tsiya da wasali ƙasa. Wai meye haka ne Maigogul karyata zaka yi ne ko me?" Yana huci ga takalmi a hannunshi yace. "Kinga wata shirgegiyar mota ce fa tazo wajenta Rakiya baki ga wanda yake cikin motar ba yaro matashi mai tsabta. Ga kuɗi yanzu wannan kuɗin da kika ga ina kirgawa duk shi ya dunƙulo ya bani har jikinshi fa yana rawa. Dama meye dalilin da yasa muka nace ta zauna a gidan wancan fitsararren tambaɗaɗɗen yaron ba sabida arzikin da take ciki bane? To kuma yanzu Allah ya aiko mata da wani shine zata ce bataso. Ga yayyenta da ƙannenta babu ma mai shinshinarsu in banda Adama da gobe za'a ɗaura aurenta. Tana gani nine kwana a buzu ina buga ƙasa hakan baiyi ba har saida muka bi ƴan tsubbu kafin auren ya kusan tabbata zamu ce. Shine wannan yarinyar zata mun haka? Rakiya ƙyaleni da'ita nace" Tare suka haɗu sukaita zagina Rakiya ta rufeni da duka Hauwa ce tazo ta fincikeni. "Ke Hauwa babu ruwanki ki bari Rakiya ta ladabtar mana da'ita kaga ƴar baƙin ciki"? Ficewa nayi a gidan ina haki na koma can gidanmu. Ina shiga Khalid ya kira wayata a zaure na tsaya na amsa wayarshi. "Sabuwa ashe aurenki ya mutu shine kika kasa sanar dani, ko dai kina sha'awar komawa gidan mijinki ne ni ina can ina haukana a kanki?" Ajjiyar zuchiya na sauke. Na samu damar saisaita kaina dan na fahimci in banyi ma Khalid dabara ba wallahi sai dai inji labarin an ɗaura mana aure. Harga Allah bana fatan sake faɗawa matsala. Maganganun Babangida sun sake farkar dani ainun. Ba haka bane. Dama ni niyyata shine inna kammala iddata sai in neme ka." Murmushi yayi mun yace. "Burinmu ashe ya kusan ciki Sabuwa. Ɓarayinki yananan a rufe madam ɗina ma tuni na faɗa mata aure zanyi in saka matar a wannan wajen". Murmushi nima nayi mishi tare da cewa. Amman ai ina buƙatar lokaci. Maigogul ya shigo yake sanar mana cewar ya faɗa maka nan da kwana huɗu ka turo. To a zahirin gaskiya ina buƙatar kamar wata biyu masu kyau ko babu komai ai ya kamata in gyara jikina. Kuma yanzu haka gobe za'ayi bikin Yayata, ni kuma goben ma tafiya zamu yi da Uzairu Zuchiyata." "Uzairu zuchiyarki fa kika ce?" Dariya nayi nace. Au kishi ya motsa kenan? Yayanane uwa ɗaya uba ɗaya. Kano zamu je gobe dashi akwai abinda zamu yi ne" Bamu gama wayar ba saida na tabbatar Khalid ya janye da batun turo magabatanshi nan da kwana huɗu an ɗage sai zuwa wata biyu masu zuwa. Har a cikin raina bana jin zan iya aurenshi ko da maza sun ƙare. Amman ina tsoron yin saki na dafe. Naso batun bikin Adama ayi komai dani ko cikin abokan ango zamu dace duk da ko wacce cikinmu roƙonta shine ta dace wani abokin ango ya ƙillota yace yana so. Da tunanuka ratata na wuni. Dik da dai muna ta hira ana yima Adama tsiya sunje sun siyo kayayyakin bacci harda wanduna shine su Aisha da yaranta da suka zo zamu kwana tare suke ta mata dariya. Sai naji ina kewar nawa yaran da yanzu suna gefena. Amman inna tuno Babangida ya tafi da tulin buhunhunan ɓacin rai da kishi sai inji wani sanyi a zuchiyata. Tabb yau babu zaman lafiya duk wacce take da girki yau zata gane kurenta in tayi wani wargi." Washegari sassafe dan masifa muka wuce tasha ni da Uzairu Zuchiyata yaci uban gaye ya ƙwama gogul yayi kyau sai kamanninshi ya sake fitowa sak da Maigogul. Maigogul har tasha ya raka mu bai baro tashar ba ƙarewarta har saida motarmu ta tashi. Ƙarfe taran safiya a Kano tayi mana. Uzairu zuchiyata ya kira wani abokinshi ko ina suka san juna oho sai gashi anzo har tasha an ɗaukemu a ƙatuwar mota, ni dai ina bayan mota nayi zuru." Mrs BUKHARI ce taku

Babangida :. [8/24, 10:16 AM] BADA'AT IBRAHIM: https://chat.whatsapp.com/IUKFTeul76p2VaAvQ5nk0U?mode=ems_copy_c

IDAN KAYA YA GAJI... GAMMO MA YA GAJI LITTAFI NA UKU SHAFI NA GOMA SHA BAKWAI

BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI

BABANGIDA:.

Tuƙin cikin rashin nutsuwa yake yi. Babu nutsuwa tattare dashi ƙwaƙwalwarshi sai hasko mishi fuskar Sabuwa da Khalid take yi. "Yanzu kana ji kana gani zai rabaka da matarka ya kuma aureta kai kana kallo?" Zuchiyarshi ce ta shiga tunzurashi. Tsaki ya saki kawai ya girgiza kai. "Ina wallahi bazan taɓa bari haka ta faru ba. Sai dai ni dashi mu rungumi juna mu mutu amman ba dai ya auri Sabuwa ba." Wawan burki yaja a daidai bakin layinsu. "Ku sauka kuje akwai inda zanje" Yayi musu maganar a kausashe. Babu shiri suka sakko yaja motarshi fuu sai majalisa dama acan suka yi da Mustapha zasu haɗu ya karɓi motarshi mashin ɗinshi ma yana majalisar. Ko daya ajjiye motar bai zauna ba cewa yayi dasu yana zuwa. Kai tsaye ya nufi gida Baba Malam yana zaune a kujera cikin almajirai yana karɓan karatu Babangida ya shiga da sallama. Ita data zame mishi wajibi ita ya amsa amman durƙuso da gaisubar Babangida basa gaban Baba Malam. "Baba Malam dan Allah kaimun aikin gafara kaimun izini in dawo da Sabuwa ɗakina tunda har yanzu iddarta bata cika ba. Wallahi tunda muka rabu ban sake samun kwanciyar hankali bane. Kuma a yanzu wallahi na tuba na dena duk abinda nake yi. Nayi maka alƙawarin bazan sake sakin ko wacce mace ba ba kuma zan sake jajiɓo Aure ba" Ƙur Baba Malam yayi yana kallonshi yama rasa me zaice dashi. Domin dashi da shi ai sun san saki ne da babu kome a tsakaninsu. Haƙiƙa yaga ɗimuwa da gushewar tunani tattare da Babangidan. Yau ga ranar da yake yawan tunatar da Sabuwa zuwanta tazo. Murmushi yayi yace. "Bakin alƙalami ya riga daya bushe. Hala baka san ƙarfi da zafin shari'a bane ko? To ka sani in ma sabida uwarka kake yi Babba ta bar gidana kenan har abada. Kasan har saida na rabu da'ita na samu nutsuwa kuwa? Kai yaro tashi ka kama gabanka kada ka sake zuwanmun da irin waɗannan yashasshun zantukan. Inma turoka akayi ga amsa ka samar in kayi wasa ƴar gaisuwar taka da nake amsawa sai in dena nan ba wajen wasa ko wajen gwaji bane" Da sauri Babangida ya miƙe har yana tuntuɓe ya fice a makarantar ya nufi gidan Malama Babba. Acan ya tadda Kawu Manga a tsakar gida sunata tattaunawa duk akanshi ne. Waje ya samu kusa da Kawu Manga ya zauna jiki a mace ya gaishesu dukkansu kana ya ɗauki tagumi. "Toh kin dai ji abunda ake ciki. Nayi nayi ya amince yaronnan yaci gaba da koyarwa a makarantar Wallahi yaƙi fur. Dana matsa ma sai ya dena magana. Nifa Babba bana ganin lefin Yaya sabida a tsari na tafiyar rayuwar Yaya shi yadda da amincewa ɗaya ne tak. Daga ranar daka ci amanarshi ko ka aikata abinda zatonshi bai zata ba shikenan kai dashi yadda har abada" Malama Babba tace. "Toh shikenan babu komai tunda haka Malam ya zaɓa ai. Babangida nayi nayi dashi ya ɗebi kadarorina yayi amfani dasu tunda yana da ido a harkar baban bola amman yaƙi. Filina sukutum na mallaka mishi ya samu ya gina ya zuba matanshi a ciki yaƙi amsa, nice zanyi mishi ginin yaronnan wallahi yaƙi. Ni ba daɗin wannan faɗi tashin da yake yi nake ji ba. Nace to ya sai da filin ya samu mota ya ɗan dinga hawa yana sana'a da'ita duk dai abinda aka kawo Babana yaƙi yadda." Babangida yace.. "Baƙin amsa nayi ba. Ke Malama ce kina da saninki kada sona ya rufe miki idanunki. Ba daidai bane ki ɗauki wani shashe na dukiyarki ki bani ni ni kaɗai ba tare da kinba sauran yaran naki ba. Inma lallai akwai buƙatar hakan dole saida amincewarsu ɗari bisa ɗari da saka hannu kan takaddar yarjejeniyar cewar an bani abu kaza da amincewarsu bakuma ya cikin gado, ko hakan akayi an tauyesu. Malama in kowa ya yarda Kudidi da Sa'a ba zasu taɓa yadda ba. Ayi haƙuri kawai ina kan nema da izinin Allah komai zai wuce. Ni da magana nazo Kawu inason in mayar da Sabuwa ɗakinta gaskiya " Idanu Malama Babba ta zare kawai sai ta saki kuka kawai. Kan Babangida ya sake cajuwa shi kaɗai yasan irin azabtuwar da zuchiyarshi take yi. Ga wani irin masifaffen kishin Sabuwa da yake ta danne mishi numfashinshi. "Kul ka kuma zuwa mana da wannan maganar. Ni dai ko bayan raina kada ka sake gayyato mana Sabuwa cikin haularmu, sannan ai kasan aurenku ya ƙare har sai in Sabuwa ta yi wani auren ta fito ko? Ya kake son sake saka mahaifiyarka a cikin mawuyacin hali alhalin kasan a cikin halin jinya take." Miƙewa yayi har wani jiri na dibarshi. "Kuyi haƙuri bazan sake wannan zancan ba in sha ALLAH wannan shine jarabawata son Sabuwa shine ƙaddarata." Fita yayi a gidan yana haɗa hanya. Sai da akayi magriba ya shiga majalisarsu daidai ana cin abinci. Lokali ya zara ya dinfa cunkusa abincin bama tare da yasan me yake yi ba. "Maza wai lafiya ko kuwa Sumy ce ta zaburar dakai ne haka? Hmmm kasan Allah da ace nasan haka matan yaren ibra suke da irin wannan masifar babu abinda zaisa in taimaki yarinyarnan Allah nake faɗa maka. Yarinya tabi duk ta fitini kowa ni kaina bata ƙyale ni ba kai Adeiza masifa ce" Murmushi Babangida yayi kawai tare da girgiza kanshi. Amman ya kasa cewa uffan, yayi hankali bazai taɓa sake fitar da maganar iyalinshi ba. Lokalin ya ajjiye ya zuba zoɓo ya sha ya idasa cika cikinshi. Kafin ya miƙe. "Kunga bari in samu in rarrafa anayin isha ina da ɗalibai yau sai mun haɗu gobe." A hanya ya tsaya ya siya kayan tea leda biyu ɗaya nasu ɗaya nasu Mardiyya. A gurguje ya shiga gidan ya ajjiye mashin ɗinshi da ledojin biredin ya fice.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull