Idon nera by mamuhgee Complete - Chapter 11
Idon nera by mamuhgee Complete Chapter 11: Idon nera by mamuhgee Complete Chapter 11. Girgiza Kai tayi ahankali tana Dan sake lafewa jikin momyn tana…
4,494 words
Girgiza Kai tayi ahankali tana Dan sake lafewa jikin momyn tana lumshe fararen idanuwanta sbd rashin son doguwar motsin dazaita Jin babu Dadi.
Siddi dake dayan gefen nata cikin kulawa ta taba wuyan Amal din tana cewa,
"Sweetie jikinki akwai dumi,zankira Dr tayo gaskia gwara ko pain relief ne yazo ya Baki kada jikin yayi tsanani.
Sake lumshe idanuwanta tayi tana Dan bude idanuwanta zatayi magana saiga uncle Lulu yayi knocking kofar dakin tareda shigowa Kai tsaye Fareedah na bayansa tareda Fahat idanuwansa akan AMAL din yace,
"Baby jikin ne??? Fahat ya daga Mana hankali yace Antinsa batada lafiya tanada kuka da amai.
Anty Fareedah ce ta qarasa gefen Amal din itama cikin kulawa ta taba wuyanta tace,
"Jikin da zafi, Sweetie ki ragewa kanki wahalan karatu karki takura qwaqwalanki da yawa fa, Idan karatun kinji ya Miki nauyi inaga ki aje sai a canja ki tafi wata qasan kiyi acan..
Cikin kulawa dukkaninsu suka zuba Mata ido suga yanda ta amsa zancen na Fareedah Dan idan tayi raayin hakan babu Wanda zai hanata acikinsu sai inda takeso zataje.
Ahankali ta bude baki cikin Dan rashin son magana tace,
"Babu damuwar karatu Menstrual pain ne kawai Kamar yanda kuka sani Koda akwai damuwar karatun kadan ne shima kaida kawo ne damuwar.
Shiru sukai dukkaninsu cikin damuwar yanayinta duk da koyaushe tana hakan Amma sbd kaunar dake tsakanin familyn sun kasa sabawa duk tashiga wannan halin Haka suke tarairayarta cikin kulawa.
Bacci tasamu ya Dan dauketa tukuna aka barta tasamu baccin cikin nutsuwa.
Sai yamma sosai ta farka ta sake yin wani wankan ta saka doguwar Riga Mara hannu da nauyi tafito sanyeda slippers qamshinta na Turaren Cartier carat na tashi jikinta a hankali.
Palon momynsu ta nufa acan ta tadda siddi tareda momyn suna magana akan likitan da siddi zata gani a India Jan matsalar rashin haihuwarta.
Zama tayi suna binta da kallo da tambayar ya jikinta.
Da Kai ta amsa Dan Daman kusan halinta ne daya zama dabiarta komai Bata Masa karauniya saidai duk rashin hayaniyarta magana a bakinta Bata wuya kowace irice Dan Haka ake ganinta Yar Kai tsaye Bata rufa rufa Bata bin bashin magana Koda waye.
Kallonta Haj Zainab tayi tace,
Sweetie ko zamu tafi dake ne kema kiga likita sbd wannan ciwon matar taki yayi yawa gashi yawanci sai anyi aure ake denawa ke Kuma kince aure ba yanxu ba,inaga gwara kiga likita may be da abinda zai iyayi akan hakan.
Kallon siddi tayi tana cewa,
"Baby fada Mata auren baida duk wani damuwar datake tunanin akwai ko takura ga karatunta.
Mommy tasani ai tunda gashinan tana gani nida nayi babu damuwar danake ciki.. Bare ita yanda SSG ya gama mutuwa akanta babu abinda zata takura dashi a aurensa bayan matarsa wadda itama zata gaji da haukanta ne ta Dena tunda dai aure kam ba fashi.
Wani kallo Amal din ta jefa Siddi dashi tana cewa,
"Kece Zaki auramun Hayat din kenan?
Nice Zan aura Miki shi, Aure fa nakeson kiyi AMAL tayaya zan zauna Ina kallonki damammakin auren nata wuceki??? Kinfi kowa sanin ba karatunki kawaiba babu abinda zai sauya ko takura a rayuwarki Dan kinyi auren saima sake samun kwanciyar hankali da nutsuwa zakiyi a gidanki....
Mommy please""AMAL ta katse mommyn batason zancen kwata kwata musamman idan Ana maganar SSG Hayat Wanda tasan shine zaa aura Mata Koda cewa Tai auren zatayi sbd yagama samarwa kansa guri a zuciyar kaf ahalin nata Dan Haka kowa a gida shi yakeyi duk da akwai masu son auren nata dake sakarwa Haj Zainab da Lulu Nera Kamar Basu San zafinta suma Amma dai SSG Hayat yafi shiga ransu sbd shine matashin babba Bai Kai shekarun sauranba.
Amal kuwa babban abinda yasa Bata kaunar auren babban mutum shine ta tsani zaman kishi, Batada hakuri, Bata daukan reni, Bata iya qyalewa Dan Haka ta tsani auren duk Wanda yakeda Mata Dan tasan Koda ba guri daya sukeba Mijin ko waya yayi da matar a gabanta sai sunyi rigima ba Qarama ba uwa uba ta tsani auren mijinda wata ta Gama dashi shekara da shekaru ta bar mata Dan Haka ta zabi raayin auren saurayi Wanda Koda auren yayi a gaba itace dai tagama morarsa kafin wata din ta mora.
Daga mommy har siddi damunta sukai da zancen SSG Hayat duk sukaita korantasa tana saurarensu kawai saiga Anty Fareedah wadda itama takeyi SSG din take ta shiga suka ringa fadar qualities dinsa Amma Sam takasa jinsa cikin ranta.
Kamar jikinta ya lafa sai gashi da daddare ya dawo Mata sosai Wanda yasa Dole ko bayan zuwan Dr tayo Saida suka nufa asibiti da ita Acikin daren..
Acan suka kwana Ana qara Mata ruwa tareda allurai tasamu tayi bacci Mai nauyi Bata farka ba sai guraren 10 na safe.
Wanka tayi da ruwan dumi a toilet din dake Amenity room din dasuke ta saka free Riga da wando Tasha tea Mara sugar tana gamawa kenan saiga shigowar SSG Hayat dakin tareda uncle Lulu sai PA din Hayat din..
Qamshin tsadadden turarensa ne ya Dan gauraya dakin Mayun idanuwansa gabaki daya akan AMAL din wadda tayi fresh da ita komai nata da class din dayake kashe maza takeyinsa batareda tasan illar da hakan ke musu ba.
Haj Zainab ce ta shigo dakin itama tareda Fahat da sbd Siddi da Fareedah ne suka kwana da AMAL din ita kanta Haj Zainab din sai tsakar dare sosai ta koma itada uncle Lulu.
Ganin Haj Zainab yasa SSG takaita kallonsa akan AMAL da itama kallo daya tayi Masa duk yabi Yana neman rasa nutsuwarsa. Gashi batason doguwar magana Dole dasu Siddi da Fareedah da uncle suke fira cikin sakewa da wayeba babu ruwansu.
Shogowar Haj Zainab yagaidata cikin girmama a sake babu wani noke noken kunya sbd akwai sabo da wayewa so a sake suke dukkaninsu sunata fira Amma idanuwansa akai akai suna kan Classy Amal dinsa Dan kayan jikinta sun qara Mata kyau da aji harma da bayyanuwar sabon jini ce ita.
Ya Jima sosai a asibitin kafin ya baro tareda driver dinsa da securities dinsa da PA dinsa,
Koda ya Isa office dinsa kusan duka meetings dinsa na ranar kansilesu akayi sbd baida lokaci ko nutsuwar yinsu Yau Amal da rashin lafiyarta ce kawai a Ransa Ko gida daya dawo gabaki daya Hana kowa zuwa gurinsa yayi bayason damuwa Kansa na ciwo..
Da daddare a gidan IDON NERA Res yayi dinner sbd an sallamo AMAL din sun dawo gida Kuma sun saba sosai Dama Kuma duk ranar da SSG yazo gidan Nera ce zayi kuka Dan sake musu yake.
Ko aranar wasu irin siyayyar dimauta akayo aka kawosu Kaya guda na dukkanin abinda AMAL keso da buqata ne.
A main palour na gidan sukai dinner a makeken dining dinsu Anata fira cikin sakewa da kulawa har aka Gama suka koma palon Baqinsu na musamman shida AMAL din wadda taketa fizgar nutsuwarsa da Basarwarta da komai nata dayake sanyi.
Duk da Bata jinsa cikin ranta Bata wulaqanta sa saidai Kuma baya samun surunta sosai soyayyar sanyi da basarwa take Dan Yi Masa.
Sai after 10 yabar Gidan ya tafi bayan yayi musu abinda ya Saba wato barin Nera.
Bayan tafiyarsa Kai tsaye Bata tsaya komaiba tayi Shirin bacci ta kwanta.
Bayan isarsa gida Saida ya kirata yasake Jin jikin nata tareda Dan jimawa Yana tarairayarta a wayar tana basarwa sbd bacci datake ji.
Washe gari tafara samun sauki Amma SSG Bai samu nutsuwa ba Haka ya ringa yawon gidan duk da tarin schedules dinsa Amma Haka yake watsi dasu idan lokacin zuwa dubo AMAL dinsa yayi.
Ganin yanda SSG din duk yaqara mutuwa akan AMAL yasa familynta suka sake nacewa akan aurenta dashi duk da Bata sonsa Amma tanason abinda familynta ke so Dan Haka ta da fara saukowa akan maganar auren nasa Amma da sharadin duk abinda zaisa ta hadu da matarsa yayansa zai kiyaye bataso.
Familynta tsayawa sukai akan raayinta Suma sbd basuda niya ko nufin takurata tako Ina..
Shima SSG din babu musu ya amince sbd Daman yariga yasan raayi da halin Amal din Kuma shima matarsa yasan bazataso haduwa ko ganin Amal din ba.
****Maganar aurensa da Amal ta Amince Yana Isa kunnen matarsa hankalinta yayi mummunan tashi sbd Mijinta na auren AMAL tasan tagama yawo ita Dan Haka wlh bazata taba yardaba. ##MAMUH# #HOTLOVE/AMAL/MARRIAGE #IDON NERA
*_ZAFAFA BIYAR_*
*RUMBUN K'AYA*🔥 Hafsat Rano
*DAUDAR GORA*🔥 Billyn Abdul
*IDON NERA*🔥 Mamuhgee
*A RUBUCE TAKE*🔥 Safiya huguma
*KI KULANI*🔥 Miss xoxo
Littafi daya---400 Biyu---600 Uku----800 Hudu-----1k Biyar din duka----1200
ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN
0022419171 Maryam sani Access bank
Shedarka ta 09033181070
MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN
09166221261
🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪 *Ina yan uwa 'yan nijer?* *Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*
+22799643131
Littafi daya---450CFA biyu---650CFA uku----850CFA hudu----1050 CFA Biyar----1250CFA
*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!* *Thanks for choosing us*🔥
*_Arewabooks@Mamuhgee_* 23 Babbar 'yar SSG Yar kimanin shekaru goma Sha bakwai ce tashigo bedroom din mahaifiyarta riqeda wayarta a hannunta da alama kome nene yakawota dakin mahaifiyarta a Acikin wayar yake sbd yanda ranta yake bace.
Nafeesat dake zaune tana waya da babbar aminyarta Kuma Yar uwarta Bilkees wadda duka duka batafi wata ukuba zuwa hudu da dawowa kasar da Mijinta da yarta sai uwar Mijinta...
Dagowa tayi tana kallon 'Yar tata batareda ta Gama wayar datakeyiba tace,
"Amrah lafiya? Menene ranki yake a bace haka?
Miqa Mata wayar hannunta dake daukeda kyakkyawan hoton AMAL da kyanta ke bayyanuwa sosai kamar wadda ta hada jini Arab.,tace,
Mummy duba kigani maganar auren daddy da wannan karuwar dangin karuwai da Yan daudu ya tabbata sai yadawa akeyi a social media School ma kusan koina zancen suke tunda ansan AMAL din da zafin Kai da ajin banza tana familyn karuwai.
Zubawa screen din wayar idanuwanta tayi zuciyrta na bugawa da qarfi, Kyakkyawar fuskar Amal ta zubawa idanuwanta dake Neman qanqancewa da tashin hankali da baqin ciki tareda tafasar zuciya.
Ko tana so ko bataso kamai Hassada da baqin cikinta Akan Amal tasan kyakkyawace Wanda hakan yake qara mata baqin ciki da tsanarta harma da tashin hankali tunda tasan yanda mijinta ya gama Mutuwa akan kyan bayako duba da qazantar karuwanci dake tattareda zuriarsu
Jin shirun nafeesat din yasa bilkes da itama taji abinda Amrah ta fada ta cikin wayar, A dan hasale tace,
“Nafee meyesa wai kinaji kina gani da ranki da lafiyarki zaki bar Mijinki ya auri karuwa? Karuwar ma wadda tayi Gadon abinta ta uwa da uba da dangin uwa Dana uba tunda kince yayan uwarta ma Dan daudu ne na musamman mai zaman Kansa.,
Wace masifa ce wannan Zaki zauna kina kallo ta shiga rayuwarki?
Kinkuwa San babbar masifar dakika shiga wasa ce idan har wannan Idon Nera da ake fada tashigo gidanki??
Gaskia nafee kinada sake a komai,
Ni Aminyarki karkiji yanda zuciyata ke shiga tashin hankali da tisishi tareda daukan zafi idan na kwantanta halinda kike ciki ma kawai,
Gaskia Nafee banbaki shawarar barin SSG ya auro Yar IDON NERA ba kamar yanda naji sunan koina aka fadesa dai shedar daya ce.
Cikin Jin zafi da qunci Mai tsuma nafee tace,
"Inda ma ace irin karuwan Nan ne qanana marasa galihu da suka tuba zaa rufa musu asiri a aura sai suzo suyita yimaka biyayya......
A qule Aminiyar tata ta katseta da cewa,
"Ba tubabbiyar karuwa ba ko Tubabbiyar malama ce Karki yadda a auro Miki Dan babu gwara fa a kishiya,
Nafee kinji abinda nakeji kuwa ko sunan kishiya aka ambatarwa wani bare ke da kike Taredani, Nidai gaskia banaji Miki alkhairi a wannan lamarin gwara musan abinyi tunda har barazanar rabuwa dashi kinyi ko gwada yaqi fasawa.
Hawayen baqin ciki da radadin zuciya me suka gangarowa Nafee tana kasa riqesu tace,
"Bilkees Hayat fa ya Gama shallake duk wani tunanina, Yariga yayi Nisan da sai Allah Amma na tabbatarda Idon Nera Basu barsa Haka ba Dole akwai abinda sukai Masa, Qarin abin baqin cikin da takaici basa zaman auren fa, Tana shigowa zata mallaki fiyeda Rabin arzikinsa ta rabu da auren taje ta auri wani Wanda ya fisa a kudi takuma aura, Auren uwarta Dana 'yar uwarta baya kirguwa fa, yanzu gashi zaa hada da nawa Mijin gurin qirgan auren muguwar zuriar tasu.
Wani zazzafan numfashi Bilkees ta sauke tana sake jinjina lamarin,
Innalillahi wainna ilayhi rajiun,ita Kam duk ranarda nata Mijin yace zaiyi aure Kila bugawa zatayi uwa uba aure irin wannan na SSG din da dangin da kaf babu Mai kunya bare kawaici bariki sai wadda suka manta.....
Inaaaa,Astagfirllh, Astagfirllh, Allah yaci gaba da barmin mijina da kamewarsa da nisancinsa da Mata.
Hawayen Nafee dasuka koma sheshekan kuka yasa Dole suka katse wayar hankalin Bilkees a matuqar tashe da wannan masifar data fara isarta akan wannan Idon Nera din.
Ajiye wayarta tayi tana kokarin tunanin yanda zasu bullowa lamarin, Dan tsananin kishinta akan nata mijin yasa ko Wanda tasani taji kishiya akansa ta ringa zullumi da damuwa kenan bare Aminyarta guda Kuma Yar uwarta uwanta zaayiwa wannan babban lamarin.
Hameeda dake gefenta zaune tana duba waya ta dakata da duba wayar ta kalli mamar tata cikin Jinjina lamarin itama tace,
"Umme idan Kikaga AMAL IDON NERA din sai hankalinki yafi tashi fa, Gaskia mummyn dasu Amrah na cikin babban tashin hankalinda su kadaine zasu iya fadar abinda sukeji,
Hameeda bana buqatan ko ganin hotonta wlh, Idan bana son Abu to ko inda Zan gansa bana zuwa, Karki nunan hotonta Dan ko ahakan karkiji tsana da qyanqyamin danake musu bare Nafee da zaa aurowa, Tana zaman zamanta a kwaso musu jaraba da cutittika da komaima, Tazo karshe ta haihu yayan Nafee sun hada jini da yayan gidan karuwai fa kenan...ya Salam,wlh Nafee na cikin mummunan Hali,.ya Allah ka lalata wannan auren ka hanasa ka wargaza zancen can taje ta samu wani ta aura badai SSG dinba.
Amin umme fatar kenan, Can tasamu Wanda zai aureta..
Adduoin fashin auren da gaggawa suka ringa jerowa cikeda tsana Mai tsanani ga sunan IDON NERA din gabaki daya..
Dan kusan kamar sunfi su tsanar lamarin gabaki daya sukeji... musamman Bilkees Jin takeyi kamar ta zama uwar SSG ta tsine Masa idan ya yarda yayi auren.
Ita Kuma mufeeda takaici da tsanar AMAL din tafi ji sbd irin Yanda ake kuranta kyau da ajinta tareda Basarwarta ga maza tana tinkahon Arzkin da suke dashi Wanda yake na qazantama...
Ta gogewa Allah takuma ta gode Masa da yasa daddy dinta kwata kwata baya sabgar da zata hadasa ko huldan business ko aiki da masu irin wannan qazantacciyar rayuwar mai abin qyama sbd batasan Yaya zatayi da rayuwartaba idan akace itace daddynta zai aura AMAL din wadda so daya ta taba ganinta Amma taji Sam Bata kaunarta sbd ta tarwatsa gidan uncle SSG dinsu.
*****AMAL tunda ta aminta da auren na SSG duk da ba lokacin zaayiba Amma tini momynsu tafara gyaranta ahankali ahankali shikuwa yasake bude musu kofar aljihunsa..
Har alokacin Amal Bata wani doguwar soyayya dashi Amma ba kamar dah ba yanzu Yana Dan samun kanta.
Siddi kuwa yafe komawa Abuja tayi Kiri Kiri saidai Sweetheart din nata yakoma shine yake zuwa akai akai sbd shima ba qaramar mutuwa yayi akan Yar babyn tasa ba bare Daman Acikin mugayen shaidar da akaiwa IDON NERA shin duk Wanda ya aura 'yayanta saidai iyalansa su yafesa.
Tako Ina gyara da tsimin yarta takeyi Haj Zainab sbd Koda lokacin auren zaizo basa buqatan wani dogon gyara Koba komai tsimin ahankali ahankali yafi shigar mace maimakon na sai gabanin auren Sam wannan baya wani aikin dazai dauki lokaci mai Nisan tsayi ajiki.
Kasancewar AMAL din bamai son wainnan abubuwanba sai suka taqaita aka rage Amma dai still kullum sake rikida takeyi tana qara Kyau da kyan fata,
Dama AMAL komai nata Mai aji ne Koba yanzu ba fatarta lafiyayya ce sbd hutu da tsadaddun natural body products datake amfani dasu.
******Ta bangaren familyn SSG kuwa komai ya qarasa rikicewa matarsa da Aminiyarta Yar uwarta Bilkees wadda kusan ta fita shiga tashin hankali da damuwar wannan halin datake ciki,
Auren sai qara tabbata yakeyi sbd kudin auren da ake Shirin Kaiwa miliyoyan kudi uncle Lulu da baya qasar kawai ake jiran dawowarsa akawo kudin.
Tashin hankali akayi sosai tsakanin Nafee da SSG akan kudin dataji zaa kai na tambaya.
Da farko da Kansa ya Bata zabin kota zauna ta hakura kokuma ta tafiyarta Idan bazata iyaba yabata Dama.
Wannan kalmar tasa ta kawo mummunan tashin hankali a tsakaninsu sabo harta tattara kayanta da 'yayanta uku ta tafiyarta gidan iyayenta.
Hankali tashe Bilkees ya sameta gidan jikinta a mace.
Kamar zaman makoki ta tadda gidan sunayi sbd mahaifin Nafee din baya Nan yayi tafiya mahaifiyarta Kuma lamarin yafi karfinta sbd tasan bazasu taba iya Hana Hayat aureba to Amma Kuma abin baikai ya Koro nafeesat din gida ba.
Amrah kuwa tayi kuka sosai har idanuwanta sun kumbura sbd bazata taba kaunar iyayenta su rabu ba har abada,
AMAL IDON NERA ta zamar musu masifa da balain da zai tarwatsa gidansu su rabe tun iyayenta sunada sauran kuruciya a auren nasu.
Cikin tashin hankali da firgici Bilkees tace,
"Wannan balain tun Bata shigoba kenan, Idan sun shigo sai Yaya kenan? Ki dubi yanda ta rabo yara da gidan ubansu tana neman raba musu uwa da uba Ji Amrah yanda duk ta fice hayyacinta sbd kukan baqin ciki.
Anya kuwa DR SHAYKH yasan wannan danyan hukuncin na SSG kuwa??
"Umme gaskia banajin Daddy ya sani da bazai Bari komai yayi nisa hakaba ki fada Masa Dan Allah yayi wani abin cikin gaggawa nidai wlh banason uncle din ya auri wannan AMAL din Sam Sam rayuwarsu babu abinda yake ciki sai qazanta da datti.
Nafee ce ta Hana a sanarwa Babban Aminin Hayat din wato DR SHAYKH mijin Bilkees sbd Bama zai iya shiga zancen wainnan qazaman karuwanba..
Ita kanta Bilkees Dama fadane kawai tayi Amma bazata taba barin ko sunan IDON NERA yashiga kunnensaba Mai tsafta bare ya saka bakinsa harma ya iya ambatar sunan.
Har kusan dare a gidan kafin su balkees suka tafi gida sbd Nafee na cikin mummunan halinda yasa duka jikinsu yayi sanyi Matika.
Bayan isarsu gida tsaban basa cikin dadin zuciya daga ita har Yar tata mufeeda babu Wanda ya iya shiga gurin umma ya gaidata Kai tsaye part dinsu suka nufa zuciya da Rai a cunkushe.
Washe gari hakama kota bangaren umman Basu bi ba suka fice gidan zuwa gidansu Nafee sbd Amrah data kwana da zazzabi Mai karfi hardasu amai so Acikin daren suka nufa asibiti fa ita.
Ayanda ta tadda Nafee da Amrah sun jangwame a asibiti kamar wainda sukayo hijira sbd damuwar dake zukatansu take Bilkees ta kwatanto hakan akanta da mafeeda take tafara jero istigfar tana girgiza kai da sauri tana cewa ba akainaba"cikin ranta.
Mufeeda ma Jin tayi Ina bazata iya dauka ba...
SSG din shima tunda safen ya iso asibitin cikeda kulawa da damuwa da Yana tsananin so da kaunar yayansa harma da ita kanta Nafee din Amma dai son Amal IDON NERA Yana Ransa daram guri na musamman.
Ya Jima a asibitin kafin yatafi sbd babu fuska ko kadan daga Nafee din, Itama Bilkees kasa sake Masa tayi Kamar dah sbd harga Allah mutuncinsa ya zube Mata kwata kwata mutiqar ya auri wannan IDON NERA din.
Bayan tafiyarsa aka sallamesu suna kokarin shiga mota saiga motar gidan SSG din tashigo asibitin.
Shine da Kansa ya dawo asibitin batareda driver ba da Kansa yake Jan motar babu Wasa a fuskarsa yace Amrah ta shigo su tafi.
Cikowa idanuwan Amrah din sukayi da hawaye ta kalli mahaifiyarta zatayi magana Dad din ya sake cewa tashigo motar cikin Dan babban sauti Mai girma.
Motar ta nufa ta shiga jiki a mace tana hawaye Dan kamar rabata da mahaifiyarta ne zaayi tunda tasan gida zai tafi da ita.
Suna kallo ya dauki yarsa yabar asibitin yabarsu tsaye cikin zallar mamaki da sanyin jikin komai na sake daukan dumi kenan.
Gidansu Nafee suka Isa suka tadda acan dinma ya Aika driver ya dauki qannan Amrah din an tafi dasu gida..
Ta tabbata kenan auren Nafee da SSG rawa yakeyi a karo na biyu duk akan wannan lamarin.
Yau Kam ita kanta Bilkees din da wuri suka tafi sbd Nafeen dake cikin mummunan yanayi ayau din na 'yayanta da SSG ya karbe kenan baida niyar janyewa. ##MAMUH#
*_ZAFAFA BIYAR_*
*RUMBUN K'AYA*🔥 Hafsat Rano
*DAUDAR GORA*🔥 Billyn Abdul
*IDON NERA*🔥 Mamuhgee
*A RUBUCE TAKE*🔥 Safiya huguma
*KI KULANI*🔥 Miss xoxo
Littafi daya---400 Biyu---600 Uku----800 Hudu-----1k Biyar din duka----1200
ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN
0022419171 Maryam sani Access bank
Shedarka ta 09033181070
MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN
09166221261
🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪 *Ina yan uwa 'yan nijer?* *Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*
+22799643131
Littafi daya---450CFA biyu---650CFA uku----850CFA hudu----1050 CFA Biyar----1250CFA
*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!* *Thanks for choosing us*🔥
*_Arewabooks@Mamuhgee_* 24 Su balkees duk yanda suke tunanin lamarin SSG Hayat ya wuce Nan akan maganar aurensa a ahalin IDON NERA, Da fari bayan yakarbi yayansa ya Dan sauko sbd yanda yaran suka damu da rashin dawowar mahaifiyarsu Dan Haka ya Dan ringa lallabata tadawo Amma ta nuna bazata dawoba idan Bai fasa auren Amal Idon Nera ba, Ta yarda ya aura duk wadda yakeso Amma Banda Amal..
Bilkees dayasan kusancinsu yaso yiwa magana sai itama ya lura da tsanarta akan lamarin Dan Haka saiya fasa ya tattarasu ya watsar yaci gaba da harkokin gabansa idan taga anyi auren zata hakura ta yarda har ita har yan uwanta dasu bilkees harma da Amrah wadda cikin 'yayan ita kadaice takeda girman datasan wani taya uwarta kishi.
****Ta dayan bangaren kuwa Haka su balkees da 'yarta suka ara suka yafawa kansu tsanar wannan auren na SSG sbd tsakanin Nafee da balkees Aminci da kaunar Yan uwantaka ce tun yarinta sai gashi Allah yasa suka auri Aminai duk da ita Bilkees aurenta da nata Mijin kamar na Hadi ne.,
Aurenta da Mijinta DR SHAYKH AQEEL ASAD Hadi ne daga mahaifiyarsa Haj Maryamah sbd yanda yaqi auren kwata kwata duk iliminsa da addininsa harma da wayewarsa da arzikinsa sai Allah ya cire Masa shaawar aure da wuri Wanda ta rasa gane ko meyasa hakan,
Ummansa tayi tayi Amma zuciyarsa a wannan bangaren kamar ta mutu ne gashi tako Ina samun tayin aure yake daga 'yayan manya Dana malamai amma Bai taba karba ba,
Rayuwarsa wata irin baudaddiyar rayuwace yakeyi Mara hayaniya da son takura Kansa ko wani,
Ummansa itace rayuwar kadaicinsa take damunta ta nema Masa auren Bilkees wadda take ganin tanada ilimin addini sosai Kuma Dama hakan shine raayinta.
Da farko baiyi naam da zancen aurenba sbd bayason duk wani Abu dazai takurasa kokuma shi ya takura koma wacece zai aura da halayensa na rashin ko inkula da yawan rashin zamansa Amma Haka umman ta Dage sbd tanason ya dawo qasarsa dayaqi dawowa tun bayan zuwansa daya daya koma Bai Kuma dawowaba acan yake ayyukansa da rayuwarsa,
A yanda ummansa ta sansa da magana daya akan Abu yasa tasan bazai dawo dinba tunda yace bazai dawo ba Rashin dawowarsa Kuma tasan zai iya qin yin auren har abada tunda baida lokacin Kansa ya tattara rayuwarsa akan aikinsa da Kuma karatun addinin da Bai denaba har lokacin sai qara zufafa yakeyi.
Tana tsananin buqata da kaunar 'danta a tareda ita kusada da ita Dan Haka Dole ta nemar masa auren Bilkees Wanda ya aminta daqyar akai auren saidai Kuma ko bayan auren komawa yayi da matarsa UAE saidai ita umman sbd kadaicin rayuwa da rashin kowa sbd ga arzikin sun Tara Kuma kullum sai habbaka yakeyi Yana qaruwa Amma Bata cikin dadin rayuwa sbd rashin 'danta hakan yasa dole ta tattara ta bisa acan suka koma rayuwarsu gabaki daya.
Bilkees batayi wani dogon karatun Boko ba iyakacinta secondary Saida taga zata auri Cikikken namiji Mai aji da ilimi yasa ta fara diploma Amma dai batama gamaba akai auren ta watsar tabi Mijinta Wanda tagama mutuwa akansa dan kuwa ko kallon DR AQEEL ASAD tayi Jin takeyi kaman zata shide sbd tsananin son datakeyi Masa sbd saa ce ta aure ta samu ummansa ta yaba da ilimin addininta badan hakan ba tasan tako Ina AQEEL ASAD yafi qarfinta,babu Ma inda zai ganta yace yanaso sbd baya zuwa Cameroon gurin kakarsa wadda itace tasake kurarata agun umman har aka aurota.
Bilkees ba mummuna bace itama tanada nata kyan na fuska Dana jiki babu laifi, Tanada zafi da tsananin kishi duk da iliminta na addini kuwa, Kusan ma aka kishin Mijin nata data Gama macewa akansa mantawa takeyi da ilimin nata saidai takanyi kokarin danne halinta agaban umman sbd kada kada ta fice ran umman tunda AQEEL ASAD baya tsallake maganar umman ita Kuma umman na yinta dari bisa dari.
Bilkees din Bata taba Koda Bari ba Wanda hakan yafara Dan damun umma Amma Kuma batai yunqurin cewa komaiba sbd sanin Allah ne Mai badawa saidai Kuma harga Allah tana son haihuwar sbd idan ta biye AQEEL ASAD din bazai taba magana ba bare damuwaba tunda rayuwarsa yake ayanda tazo Masa ba cusawa Kai wahala.
Ita kanta Bilkees hankalinta fara tashi yayi da rashin haihuwar Ko Bari tanason tayi Amma babu damar.
Daga umma har ita tun suna dannewa har hankalinsu ya kasa kwanciya Dole da roko da kukan Bilkees da dagewar umman suka tafi asibiti sukaga likita..
Kai tsaye dubawar farko aka tabbatarda Bilkees din ce da matsalar rashin haihuwar.
Kusan qaramar hauka Bilkees tayi cikin tashin hankali da mummunan yanayin datashiga na wannan mugun labarin.
Basu fadawa umman ba sbd irin kukan da Bilkees keyi cikeda damuwa.
Yanda ta sakawa ranta qunci da damuwa yasa AQEEL ASAD din kaita wata qasar suka sake ganin likita saidai acan dinma result din dayane Dan Haka Dole ta dauki qaddara.
Ko bayan dawowarsu Basu sanar da umman komaiba Dan Haka har lokacin umman kesa Rai a samun haihuwarsu..
Wani ciwo umman Cameroon tayi sosai Wanda yasa umman AQEEL ASAD din tafiya Cameroon kusa tsawon shekara biyu Bata dawoba Wanda ya bawa Bilkees damar adopting mufeeda itada AQEEL din acan qasar sbd mahaifiyarta data rasu a qasar batareda ansan danginta ba kasancewarta Yar Nigeria yasa aka bawa Aqeel din ita Kuma yasan mahaifiyar tata sosai tun kafin yayi aure lokacinda tayi auren ne Bai saniba bare Mijin data samu cikin dashi Dan Haka Bai musaba da Bilkees ta nace akan tanason babyn.
Ta karba babyn ne sbd kare matsayinta agun umma kada tasan Bata haihuwa shikuma ya amintarwa Bilkees karba babyn ne sbd tallafa rayuwar yarinyar kodan Allah yasa sakamakon hakan shima Allah ya basa wadda zai tallafi tasa 'yar uwar da Maminsa aduk inda suke duk da yasan tini Maryamah tayi girma yanzu.
Babban kuskuren dasukayi shine rashin sanar da umma ba Bilkees ce ta haifi mufeeda ba, Shi yayi hakan ne sbd idan umman tasa daukota sukayi bazata taba barin su riqetaba sbd hakan kawai yayi shiru akan sune suka Haifa mufeeda Dan Haka a duniya bayan shi da Bilkees babu Wanda yasan basune asalin iyayen mufeeda ba har ita mufeedan wadda ta taso cikin gata da kulawa tareda daular arziki tana yanda takeso duk da kasancewar daddyn nata Mai zurfi a addininsa.