Idon nera by mamuhgee Complete - Chapter 19
Idon nera by mamuhgee Complete Chapter 19: Idon nera by mamuhgee Complete Chapter 19. Wayar AQEEL datai blocking ta fara sakawa Kira Amma shima baya dauka.
4,492 words
Wayar AQEEL datai blocking ta fara sakawa Kira Amma shima baya dauka.
Innalillahi wainna ilayhi rajiun
Innalillahi wainna ilayhi rajiun""take maimaitawa hankali tashe Babu inda baya rawa jikinta ta fita ko gabanta Bata gani ta nufi motarta.
Anty Fareedah ce data fito zuwa sashen taganta tayi saurin tareta cikin tsoron ganin halinda take ciki.
Haj Zainab din Bata iya mgn ba sai key data miqewa Fareedah din tana cewa,
"Just drive.
Fadawa sukai motar tana cewa,
" A ASADULLAH MOSQUE to sauri Fareedah kafin balain da bazai taru ba ya afku.
Agogo take kalla Wanda ya nuna karfe goma harda mintina ashirin saura.
Wani mugun gudu Fareedah ta qarawa motar suna qara Hawa titi.
***Qarfe goma da rabi da mintina Tara motarsu Haj Maryamah ta Isa kofar babba gate din gidan karatunsa wadda suka tadda Babu mutane sai daidaiku wainda ke neman wucewa Suma.
A rikice suka fito motar daidai isowar Haj Zainab da Fareedah dasuma suka fito motar a rikice
Babu Wanda ya tsaya bi takan Dan uwansa acikinsu sbd Babu Wanda hankinsa da nutsuwarsa suke ajikinsa
Rige rigen shiga gate din sukai Kai tsaye suka tinkari inda suka hangosa Yana tsaye tareda uncle Lulu da Al-Amin.
Wani irin kwarjininsa da kyansa dake cika idanuwan mutane haskawa duk da fuskarsa a Dan kame take magana zaiyi da uncle Lulu Amma saiya Gama sauraron Al-Amin dayake bayanin manyan Baqinsu dasuke Gama wucew...
Babu tsammani dukkaninsu sukaga su haj Maryamah din da Haj Zainab a gabansu Babu wadda ke hayyacinta sbd tsabar tashin hankali..
Bakin umma ne dayafi kowa qaiqayi da rawa a rikice tace,
"AQEELU kaida ubanwa aka daura maka auren?????
Haj Maryamah ce ta katsesu cikin matsanancin tashin hankali da cewa,
"An daura???
Al-Amin ne ya bude Baki yace,
"AN DAURA AUREN UMMA.
Wani Abu ne ya soki zuciyar haj Maryamah da Haj Zainab harma da umman take dukkaninsu suka yanke jiki suka Fadi a gurin.
##MAMUH#
#HOTLOVE#ROMANCE#AQEEL ASAD
AMUN UZURI PLEASE SHORT CHAPTER NE INADA UZURI.
SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!
Makarantar Lafiya dake garin Kazaure (Kazaure school of health technology) tana farincikin sanardaku cewa ta Kawo wani sabon tsarin karatu a saukake na part-time Degree da Diploma a wasu kwasakwasai domin ma'aikata masuson karin karatu da 'yan Kasuwa wanda basu da isasshen lokaci.
Kwasakwasan kamar haka:
DIPLOMA
1.Dental surgery Technician
2.Medical X-ray Technician
3.Health Information Technician
4.National Diploma in Biomedical Engineering
5.Public Health Technician
6. Community Health Extension Worker (Re-trainee)
7.Junior community Health Extension Worker (JCHEW)
DEGREE
1. Health Information Management
2.Public Health
3.English Language
4.Public Administration
5.Business Administration
6. Economics
7. Accounting
8.Computer Science
9.Mass Communication
10.Agricultural Economics
Domin karin bayani a tuntubi wannan Lambobin:08035298851, 07066542055 ko Azo haraban makaranta dake No 3 Emir's Palace road off Kano-Daura road Kazaure a jihar Jigawan Nijeriya
*_ZAFAFA BIYAR_*
*RUMBUN K'AYA*🔥
Hafsat Rano
*DAUDAR GORA*🔥
Billyn Abdul
*IDON NERA*🔥
Mamuhgee
*A RUBUCE TAKE*🔥
Safiya huguma
*KI KULANI*🔥
Miss xoxo
Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200
ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN
0022419171
Maryam sani
Access bank
Shedarka ta 09033181070
MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN
09166221261
🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*
+22799643131
Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA
*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*Thanks for choosing us*🔥
39
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
39
Al-Amin da Uncle Lulu ne sukai saurin Yi kansu cikin mamaki da tashin hankali suna ambatar sunayensu a rikice,
Uncle Lulu da Anty Fareedah Haj Zainab suka Kama suna Kiran sunanta cikin matsanancin tashin hankali,
Al-Amin kuwa Haj Maryamah da umma ya nufa Yana rasa wadda zai kama.
AQEEL ASAD daya rasa me zaiyi musu rintse idanuwansa yayi Yana budewa Akan Al-Amin da duk ya rude sbd baisan meyake faruwaba.
Securities yasa suka rufe gate da sauri sbd Yan Media dasuka fara dauka.
Uncle Lulu ya kalla yace,
"Ku dauko Mamin muje asibiti,
Qarasowa yayi Bai tsaya komaiba ya sunkuya ya dauko ummansa gabaki dayanta ya nufi motarsa da malam Rabiu yayi gaggawar budewa.
Al-Amin Dole shine ya dauki umma uncle Lulu da Fareedah suka dauki Haj Zainab zuwa motarsu shikuma Al-Amin motarda su haj Maryamah din suka zo da ita ya nufa da umman suka jero motocin a guje suka fito harabar babban gidan sbd kada ma Yan Media dake neman Jin zancen su samu daukan hotunansu.
Kai private hospital dinda familynsa ke zuwa ya nufa dasu.
Su Uncle Lulu ma can din suka nufa Dan Haka suna Isa aka karbesu duka Yana mamakin wannan jeran kumbo da akayo dasu a some ris.
Ana Shiga dasu uncle Lulu ya kalli Anty Fareedah yace,
"Amal kada tasan abinda yake faruwa Dan idan tasani tazo asibitin zata iya sanin maganar aurenta anan din Wanda abin bazaiyi dadiba gwara tasani a gida....
Kiran Amal dinne ya shigo wayarsa ya katse Masa zancen nasa.
Ajiyar zuciya ya sauke tareda bayyannan numfashi kafin ya dauki wayar.
Hello Uncle mommy ta fitane?
Nazo naduba ban gantaba ga wayarta Yana ringing Bata daukaba..
Wani numfashin Yakuma saukewa kafin yace,
"Eh ta fito tazo wani Dan aikin gaggawa ne damukeson kashewa
Amma ba wani babban Abu bane
Zamu dawo anjima kadan.
Ok"tace ahankali tareda kashe wayar.
Wayar Anty Fareedah ta saka Kira sbd motarta na Nan gashi Bilkisu tace ta fita,
A saninta Anty Fareedah Bata fita da motar kowa sai nata Dan Haka take mamakin ina ta tafi itama.
Anty ena dauka first abinda yafara shiga kunnen Amal shine muryar Uncle dayake waya a kusa da ita Yana fadawa Barr Salahudeen Wanda ya sallami nasu bakin dasuka samu halartar daurin auren suna asibiti da IDON NERA.
Shiru Amal tayi Dan kuwa kunnenta yaji dakyau Babu maganar batawa Kai lokacin sake tambaya da Haka Kai tsaye tace,
"Anty Fareedah wane asibitin ne??
Meya samu mommy?
Kallon uncle Lulu Anty Fareedah tayi da Ido ta nuna Masa Amal ta jisa Kuma tana tambayar wane asibitin ne..
Rintse idanuwansa yayi yana dafa Kansa dake sarawa Dan shima tun jiya yake cikin wannan pressure da tashin hankalin na wannan masifar dayayi gudun faruwa.
Karban wayar yayi yana kokarin kashewa Anty Fareedah ta girgiza Masa Kai tana cewa,
"Hankalinta zai matuqar tashi fa idan ba zuwa tayiba tinda kasan yanda mommyn take Acikin ranta.
Still hanata fadawa Amal din yayi Dole suka kashe wayar saiga shigowar sakon Amal a wayarta tata.
Satar kallon uncle Lulu Anty Fareedah tayi tayiwa Amal reply da sunan asibitin.
AMAL dake tsaye text din na shigowa tayi saurin zuwa dakinta da sauri ta dauko key din motarta ko kayan jikinta Bata sauyaba ta fito ta wuce Kai tsaye.
Mintina qalilan ne suka kawota asibitin tanayin parking ta fito Kai tsaye ta nufi inda Anty Fareedah tace suke.
Tun daga nesa Al-Amin dake tsaye gefen AQEEL ASAD dake zaune office din Dr Abdul ya hangota.
Kallonta yakeyi dakyau Dan tabbatarda idan ita dince da suka daura aurenta a yau din da Mai gidansa..
Riga da wandon Fendi ne ajikinta farare gabaki daya sai silk scarf dake kanta da slippers,
Duk da kayan bamasu Kama jiki bane kyan jikinta yafito sosai acikinsu musamman dayake fresh fuskarta ta safiya ce batada komai sai asalin ita dinta.
Dan sunkuyar da Kai yai ya saci kallon AQEEL ASAD da gabaki daya iyayen nasa suka Gama shallake mamakinsa dan Bai dauka qiyayyar tasu takai su iya somewa lokaci daya akan hada sabuwar alaqarba.
Sake kallonsa kofa Al-Amin yayi Yana mamakin kodai ba itace AMAL Idon Nera daya saniba Dan Koba igiyar auren AQEEL ASAD ta hau kantaba koma wani ne daban da baiyi sunaba bazata fito ahakanba ranarda aka daura Mata auren.
Kasa rike tinaninsa yayi Dan bazai iya shiruba ahankali yai Dan gyaran murya yace,
"Sir ga Ms Amal Idon Nera ta qaraso inaga.
Dakatawa daga taba wayarsa yayi Jin abinda Al-Amin din yace batareda ya dagoba ko kallon kofar.
Uncle Lulu dayaji shikuma Anty Fareedah ya kalla da sauri Yana matse fuska da cewa,
"Me kikayi?
Sorry" tace Masa ahankali cikin narke fuska.
Isowar Amal kofar office din da shigowarta yayi daidai da dagowar AQEEL ASAD sbd kamshinta Mai sanyi daya Gama kame jikinta da duka kayanta.
Kallo daya tayi Masa ta dauke Kai tareda qarasawa gurin Anty Fareedah da uncle Lulu tana cewa,
"Meya samu mommy?
Meyake faruwa ne Naga harda wasu duk anan.
AQEEL ASAD Anty Fareedah da uncle Lulu suka kalla sbd sunsan shi take nufi da wasu din datace.
Ahankali uncle yace,
"Ba wani abun bane Yar hatsaniya aka samu wadda tasaka Zainab din somewa Amma zamu koma gida bada jimawaba.
Daga goshinta tayi da dogayen faranta farare tas tana mamakin menene zai saka mommynta suma,
Koma meyene tasan yanada alaqa da AQEEL ASAD ko familynsa tunda sune masifar rayuwar mommynta.
Sanyayyan qamshin victorious carbon ne yagama cike office din Wanda yasata Jin maqoshinta na tashewa sbd duk wani abu daya dangancesa da ahalinsa Bata buqatansa a gabanta ko rayuwarta Dan Haka duk sanyi da dadin qamshin jinsa take kamar Yana yagar hancinta musamman dayake kusan tana kusa dashi Amma ta juya Masa baya tana fuskantarsu Uncle Bata buqatan ganin ko fuskarsa bare ta Tina yana gurin.
AQEEL ASAD ma Bai juyo ya sake kallon inda take din ba saima miqewa yayi ya fice office din Dan batareda ya waiwayo gefenba,
Al-Amin da gulmar duniya tagama cikasa yanason ganin AQEEL ko Amal din sun nuna su din ma'auratane da aka daurawa aure yau Amma yaga ko kallo Babu Wanda ya bi wani dashi sai shi AQEEL din da farkon shigowarta ya watsa Mata fararen idanuwansa masu cikeda kwarjininsa Amma zafin kan Amal Idon Nera din ya hanata nuna girgizarta da dafin idanuwansa da Babu Wanda baya girgiza suka kallesa Kamar hakan.
Bin bayan maigidan nasa yayi Yana satar kallon Amal da shigarta datafi komai basa mamaki duk da yasan agurinta da irin rayuwar gidansu wannan shigar ba komai bace tasaba fita da abarta Amma ai yau din auren DR SHAYKH AQEEL ASAD guda ne akanta.... gaskia Dole Haj Maryamah da umma su samu somewa Dan kuwa koshi sumar ne kawai baiyiba a jiyan da AQEEL ASAD ya sanar Masa AMAL Idon Nera zai aura ayau din gashi Kuma an daura din dai Dagaske shi din sirikin Idon Nera ne.
Yana fitowa aka sanar dashi farfadowar dukkaninsu gabaki daya Wanda Daman dukansu tsabar shock ne yasasu somewa.
Umma tinda ta farfadoba bayan ajiyar zuciya Babu abinda takeyi sbd bakinta wani abune Mai nauyin gaske ya toshesa ya danne Dan Haka takasa sai ajiyar zuci da kallon AQEEL din takeyi.
Haj Maryamah ma kuwa jininta yaqi sauka Dole aka mata allurai tareda wasu dubarun bacci ya dauketa na Dole Wanda acikinsa sai ajiyar numfashin takeyi itama..
Haj Zainab kuwa tunda ta farfado Bata iya cewa komaiba itama sbd ganin Amal agurin Dan Haka tace ita gida zata koma bazata zauna asibitin ba.
Sallamarta akai suka fito dukkaninsu harda AQEEL ASAD yasa Al-Amin ya wuce gida da umma shikuma a motarsa zai tafi da Maminsa yakaita gida tunda ummansa ita ba yanzu ba tana asibitin.
Amal Kai tsaye ta nuna itace zata tafi da mommyn Amma ko ta kan zancenta AQEEL ASAD Baima bi ba sbd lura da zafin datake ciki.
Uncle da Anty Fareedah suka lallabata baya AQEEL din ya wuce da mommynta yabarta agurin tsaye.
Uncle Lulu da Anty Fareedah ne sukabi bayansu mommy itakuma airport ta wuce sbd siddi datai Mata wayar ta iso.
Tana Isa airport din sun sauka already Dan Haka daukota kawai tayi suka nufo gida ranta har lokacin a bace yake da ikonda wani zai nuna Mata Akan mahaifiyarta bayan mommyn ta yanke duka wata alqarta dashi.
Har suka iso gida fuskarta a daure take ita kanta siddi hankalinta yayi mummunan tashi dajin mommynsu ba lafiya har a asibiti.
Suna shigowa parking kawai Amal tayi suka shigo ciki atare da siddi
Siddin ce a gaba AMAL tana bayanta taba kokarin duba wayarta da sakonni suka shigo Mata a jere Wanda ake tayaya murnar aurenta da AQEEL A....kasa qarasa karantawa tayi ta nufa palon mommynsu Kai tsaye a sama inda ta tadda siddi tsaye takasa qarasawa sbd abinda mommyn ke fadawa AQEEL da uncle Lulu.
Hawayene kwance kan fuskarta cikin matsanancin tashin hankali da fita hayyaci take kallon AQEEL ASAD Wanda yake tsaye gabanta ta riqe hannuwansa duka biyu tana cewa,
"AQEEL wallahi na yarda duk Wanda zaka aurawa Amal ka aura Mata kanada cikakken iko akai Amma Dan Allah ka warware aurenka da ita,
AQEEL bazan taba hanaka iko Akan Amal ba Amma Dan Allah ka warware aurenka dake kanta na rokeka........
Kallonta yakeyi da dukkanin idanuwansa masu kyau da Isa,
Baida niyar magana sbd Babu abinda zai iya Yi akan abubuwan datake fada,
Warware aure take magana nasa da MARYAMAH,.
Me zaice Mata?
Daga ita harsu ummansa ya shirya sakawa borinsu Ido kawai batareda tankawaba Dan kuwa sunyi nisanda basa gane komai idan ba na rabuwar ba.
Kallonsa uncle Lulu yayi Amma kwarjininsa ya hanasa yayi Masa magnar dayake son fada din.
Ahankali ya zare hannuwansa daga na Mamin Yana kallon fuskarta dake firgice gabaki daya ta fice hayyacinta.
Ahankali ya girgiza Mata Kai cikin nutsuwa da kamewa da muryarsa Mai aji acikinta yace,
Mami Babu saki ko warwara a wannan auren kinfi Kuma kowa sanin tsayuwata Akan zancen daya....
Siddi datai mutuwar tsaye ce da Jin abinda yake faruwa da matsanancin mamaki tajuyo tana kallon Amal wadda itama Tai mutuwar tsayen tana sauraron abinda yake faruwar tace,
"Wace Amal din ce aka daurawa aure dashi Mommy??
Haj Zainab da uncle Lulu ne suka waiwayo kofar a tare cikin firgici,
AQEEL ASAD din kuwa Babu wani damuwar data shigesa kai tsaye ya juyo ahankali ya zuba Mata idanuwansa dasuka saka gama rudar da Siddi da tsananin kwarjininsu.
#MAMUH#
#HOTLOVE#MARRIAGE#AQEEL ASAD.
SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!
Makarantar Lafiya dake garin Kazaure (Kazaure school of health technology) tana farincikin sanardaku cewa ta Kawo wani sabon tsarin karatu a saukake na part-time Degree da Diploma a wasu kwasakwasai domin ma'aikata masuson karin karatu da 'yan Kasuwa wanda basu da isasshen lokaci.
Kwasakwasan kamar haka:
DIPLOMA
1.Dental surgery Technician
2.Medical X-ray Technician
3.Health Information Technician
4.National Diploma in Biomedical Engineering
5.Public Health Technician
6. Community Health Extension Worker (Re-trainee)
7.Junior community Health Extension Worker (JCHEW)
DEGREE
1. Health Information Management
2.Public Health
3.English Language
4.Public Administration
5.Business Administration
6. Economics
7. Accounting
8.Computer Science
9.Mass Communication
10.Agricultural Economics
Domin karin bayani a tuntubi wannan Lambobin:08035298851, 07066542055 ko Azo haraban makaranta dake No 3 Emir's Palace road off Kano-Daura road Kazaure a jihar Jigawan Nijeriya
*_ZAFAFA BIYAR_*
*RUMBUN K'AYA*🔥
Hafsat Rano
*DAUDAR GORA*🔥
Billyn Abdul
*IDON NERA*🔥
Mamuhgee
*A RUBUCE TAKE*🔥
Safiya huguma
*KI KULANI*🔥
Miss xoxo
Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200
ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN
0022419171
Maryam sani
Access bank
Shedarka ta 09033181070
MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN
09166221261
🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*
+22799643131
Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA
*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*Thanks for choosing us*🔥
40
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
40
SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!
Makarantar Lafiya dake garin Kazaure (Kazaure school of health technology) tana farincikin sanardaku cewa ta Kawo wani sabon tsarin karatu a saukake na part-time Degree da Diploma a wasu kwasakwasai domin ma'aikata masuson karin karatu da 'yan Kasuwa wanda basu da isasshen lokaci.
Kwasakwasan kamar haka:
DIPLOMA
1.Dental surgery Technician
2.Medical X-ray Technician
3.Health Information Technician
4.National Diploma in Biomedical Engineering
5.Public Health Technician
6. Community Health Extension Worker (Re-trainee)
7.Junior community Health Extension Worker (JCHEW)
DEGREE
1. Health Information Management
2.Public Health
3.English Language
4.Public Administration
5.Business Administration
6. Economics
7. Accounting
8.Computer Science
9.Mass Communication
10.Agricultural Economics
Domin karin bayani a tuntubi wannan Lambobin:08035298851, 07066542055 ko Azo haraban makaranta dake No 3 Emir's Palace road off Kano-Daura road Kazaure a jihar Jigawan Nijeriya
****************
Da mamaki Amal ke kallon mommynta da Uncle Lulu dasuma ita din suke kalla,
Zancen Bai razanata sosaiba sbd tasan bamai yiyuwa bane abinda take tunanin taji din?
Ba ita Amal din ba sbd abune da bazai taba yiyuwaba mommyn su aurar da ita bada sanintaba Kuma aurenma na Dole da Wanda sukasan kota Yaya bazata yarda ta taba aurensaba.
Qin kallonsa tayi ta qaraso ahankali gabansu mommyn tana sake kallonta da kyau kafin ta bude Baki tace,
Mommy wace Amal ake magana akai?
Wane auren Kuma aka daura?
Dakuma waye aka daura auren??
Siddi ma cikin mamakin ta qaraso tana kallon Mommyn tasu Amsarta suke jiran ji Dan itama tashiga rudani da mamaki Mai girma idan har Amal dinsu ake nufi,
Mezai hada Amal da auren bazata, auren Dole, auren rashin sani??
Rintse idanuwa Haj Zainab tayi hawayen dake ciki suka Kuma gangarowa kan fuskarta datake ta jiqewa da hawaye tunda suka dawo din.
Kasa kallon Amal tayi sbd tasan baa kyauta Mata Dan Koda zaayi Mata auren bazata da dolen yakamata a sanar Mata
To Amma ya zatayi AQEEL itama yasha gabanta ya zartar da wannan danyan hukuncin da batasan ya zatayi ba bare Amal,
Girman kaunarda takewa AQEEL wata halittace da Allah ya halitta Mata cikin ranta da bazata taba iya cirewaba ko fincikewa,
Tasan kaman yanda yafada tafi kowa saninsa a duniyarsa baya magana ya janye tun Bai kawo yanzu dinba bare yanzu daya sake zama mutum tsayayye,
Wlh tasan bazai saki wannan aurenba a yanzu gashi tayi rokon harta galabaita Babu alamar Wasa ko sauyin raayi a tattarre dashi,
Me zata cewa Amal?
Tayaya zata kalleta tace Mata aurenta aka daura ayau batareda saninta ko Jin raayinta ba.
Innalillahi wainna ilayhi rajiun"
Kan daya daga kujerun palon ta zube dabas tana dafe kanta hawayenta na tsananta gudu..
Siddi ce ta qaraso kusada ita da sauri ta zauna tana sake shiga mamaki da firgici Dan kuwa alamun sun nuna dai kila Amal dinsu ake magana akai..
Dafata tayi cikin kulawa Mai tsanani da damuwar ganin halinda take ciki sanyaye tace,
"Mommy Dan Allah ki kwantar da hankalinki ki dawo daidai bamason ganinki hakan
Koma menene matsalar zata wuce zamu fuskanceta mu maganceta kaman yanda muka Saba tsayawa da juna,Amma Kuma mommy wace Amal din aka daurawa auren ayau??
Dago jajayen idanuwanta tayi ta kalli inda Amal ke tsaye tana jiran amsar da zataji tabawa Siddin.
Ahankali ta iya bude Baki murya a shaqe tace,
"Amal wannan da muke da ita guda daya gatanan.....
Kaman siddi batasan wacece Amal din ba ta waiwayo cikeda dinbin mamaki ta kalli Amal din zatayi magana Amal ta katseta da cewa,
"Aure fa kuke magana Mommy¿
As in aure aure irin na kowa da ake Masa???
Maida kallonta kan uncle Lulu tayi cikeda mamaki tana sake kasa gasgata abinda aka fada din tace,
"Uncle meyasa kayi magana Dan Allah Mana.
AQEEL ASAD daga inda yake Bai waiwayo ba ya nufi kofa hankalinsa kwance ya fice yabarsu sbd bayajin akwai sauran bayanin da Bata ganeba idanma Bata gane dinba zasu Mata bayanin dazaisa ta gane din.
Bayansa uncle Lulu yabi da kallo fuska a Dan yamutse da tunanin Yaya Kuma zai tafi ya barsu da bayani baya shine yayi Aika aikar gabaki daya.
Dawo da kallonsa yayi kan Amal Yana Dan Jin tausayin abinda zai fada Matan, cikeda kulawa da tausasa harshe yace,
"Baby Aurenki AQEEL ASAD yayi ayau,
Kudin aljihunsa ya cire tareda kamo hannunta zai Dora Mata ta zame tana kallonsa da idanuwanta dake cikowa da hawayen tashin hankali,mamaki da baqin ciki tareda firgita.
"Wannan shine sadakinki Amal" uncle Lulu yafada Yana kallon idanuwanta dake kokarin cika da hawayen baqin ciki da zafi zai tsanani,
"Sweetie kiyi hakuri....
Uncle aure fa kace?
Auren Dole kukai mun?
Kallon Mommy tayi sai kawai takasa cewa komai ta juya ta fice dakin da sbd zuciyarta harbawa takeyi da qarfi da ciwo..
Kai tsaye dakinta ta nufa tana kokarin rufewa mommynta ta tare kofar tareda shigowa idanuwanta cikeda rauni da tausayin 'yarta takasa magana sai rungumeta datayi Tana cewa,
"Kiyi hakuri Amal,
Bada niya ko cutatarwa akai Miki hakan ba Nima fin qarfina akai Akan hakan Amma ban taba tunanin yimiki auren Dole ba ko irin wannan na rashin tsammanin, I'm so sorry sweetie....
Kasa rike kukan dayake cin zuciyarta Amal tayi sbd duk yanda taso daurewa sbd takasa yarda da abinda suke fada din takasa daurewa, zuciyarta takasa riqewa Dan Haka ta saki wani irin silent kuka ajikin mommyn tana girgiza kai alamar bazata iyaba,bazata iya karban wannan abinda suke fada din ba.
Tausayintane yasake cika zuciyar mahaifiyarta ta sake rungumeta zuciya a karye tana cewa,
"Kiyi hakuri Amal Dina Zaki iya,
Zaki iya insha Allah,
Allah zai kawo mafita sbd Shi kadaine yasan dalilin hakan,
Shine ya qaddara hakan,
Please sweetie karkiyi irin wannan kukan Zaki sake karyamun zuciya.
Amal bazata iya magana ba sbd kuka takeyi sosai Wanda takeson abinda ya danne maqoshi da zuciyarta ya fada tukuna tasamu damar borewa wannan auren dasuke magana Dan bazata taba iyawaba,
Bazata Yi wannan aurenba dasuke magana,
Bazata taba son aurenba bare wainda suke cikin rayuwar auren,
AQEEL ASAD fa suke magana,
Mata ne dashi harda budurwar 'ya,
Mutuminda mahaifiyarsa tayiwa tata mahaifiyar tsanarda ko kafiri batawa irinta.
Kokarin tsayar da kukan dayaci qarfinta takeyi ta dago da idanuwanta dasukai jajir harma da fuskarta ta kalli mommyn muryarta a shaqe tace,
"Mommy wallahi bazan iyaba,
Kisaka ya sakeni batareda min wahalarda juna dukanmuba,
Bazan iyaba Mommy,
Wannan ba aure bane fitinace aka hada kawai,
Wlh bana sonsa ko kadan nidai ko kallonsa bazan iyayiba a matsayin mijina sbd ban taba fatan auren me mataba kinsani bare shi da mahaifiyarsa bazata taba karbanaba kaman yanda bazan karba dantaba.
Mommy kisa ya sakeni banason auren indai dashine..
Rintse idanuwa Haj Zainab tayi tana girgiza kai ahankali murya a sanyaye tace,
"Kiyi hakuri Amal bazan iyaba,
AQEEL nada iko fiyeda yanda kike tunani akanki,
AQEEL shine Wanda ya daukeki a duniya ya rada Miki asalin sunanki,.shine Wanda yakesonki fiyeda yanda kowa yakesonki a duniya bayan Ni Dana haifeki,
Bazan iya tirsasaba sbd yayi iko akanki,
Ya zartar da wannan hukuncin ne sbd ya tabbatarda Babu Wanda zai iya yin hakan akanki bayan shi,
I'm sorry my princess Amma Nima duk yanda nake qin wannan auren nasan bazan sauya komaiba tunda yariga ya rataya Miki igiyoyin aurensa akanki.
Hakuri zakiyi mu rungumi wannan sabuwar qaddarar muga inda zata kaimu tukuna kafin Allah yakawo Mana mafitarta..
Sake fashewa da wani sabon kuka Mai tsananin qona Rai da zafin zuci datake Jin kamar zuciyarta zata Kama da wuta.
Kallonta Haj Zainab takeyi idanuwanta na kokarin tsayar da nata hawayen ta sake kamota zatayi magana AMAL din ta girgiza kai ahankali tana kokarin tsayar da nata hawayen itama tace,
"Mommy bazaki iya Bata Masa ba ko quntata Masa shiyasa bazaki iya cewa ya sakar Miki 'yarkiba??
Wane matsayi ne yakedashi Acikin zuciyarki Wanda yafi na ni 'yarki da Kika Haifa,
Shi din fa 'dan maqiyanki ne wainda Basu taba sonki ba bare kaunarki....
Cikin tsawa da Hana bayyanarda zafin maganar tata ta katseta da cewa,
"Shut up Amal,
Hankalinki zai Bata ne sbd auren Dole yafara akanki ne?
Bakece farkoba bakuma Zaki zama qarsheba,
AQEEL ya aureki ne sbd ya Isa dake,
Koni dana haifekin bazan iya hanasa ba bare ke da aka Haifa din,
Idan inada ikon warware auren zakima San anyi ne?da tun lokacinda aka daura Zan sa a warware din,
Karki Bari bacin rai yasa Naga laifinki sweetie kiyi hakuri nasan tako Ina Babu inda aka kyauta Miki Amma AQEEL nada matsayi da girma a rayuwata da zuciyata da ba ke ba koni ya aurar wa wani bazan iya bijirewa duk tsanata kuwa da abin bare ke,
Nace Miki komai zai daidaita
Zan samo Mana mafita Akan lamarin Amma ba irin wannan da kike tunani ba...
Sassauta muryarta tayi cikin sanyi da kulawa tareda kauna da soyayyar 'yarta tana kallon yanda Amal din ke kallonta kamar yau tafara ganinta cikeda mamaki da tsoron irin kaunar AQEEL ASAD Mai tsananin girma datake hangowa Acikin idanuwa da kalaman mahaifiyarta,
Wace irin kaunace wannan Mai tattareda mamaki da tsoro da baqin ciki tareda kishi take ganin mahaifiyarta nawa 'dan matarda tasan a duniya tafi kaunar masifa da hasara akan Zainab din.
Kasa cewa komai tayi sbd sanyi da jikinta yayi na ganin abinda yake neman shallake tunaninta,
Ahankali ta saka bayan hannunta ta share hawayenta dake gudu sun kasa tsayawa ta bude Baki a hankali tace,
"Mommy meyasa kike sonsa da yawa Haka?
Rufe Ido tayi ta bude tareda miqewa ta nufi kofa ta fice sbd tasan Amal bazata taba yarda da komaiba cikin sauki bare su nutsu su samo ganin inda hanyar bullewa take garesu da wannan auren Kamar yanda tasan mutuwarta dolece tasan umma da umman AQEEL din Koda zasu rasa lafiyarsu bazasu yarda da wannan aurenba bare har ayi tinanin mafita a natse,
Masiface kwance a qasa tasani,
Zasu tashi tsaye da kyau su tabbatarda wannan auren Bai 'daga daga inda yakeba,
Koda zasu rasa komai bazasu taba karban 'yarta amatsayin matar AQEEL ASAD ba,
They can go to Any length to Make sure Amal Idon Nera tabar rayuwar AQEEL ASAD a wulaqance Wanda itama Koda zata rasa komai da kowa bazata yarda su lalata rayuwar 'yarta ba kamar yanda suka tabbatarda tata tagama lalacewa tako wane bangare har Saida taqare a titi gidan karuwai Acikin karuwai da prison cikin masu manyan laifukanda ko labari Bata taba ji ba,
Idan har bazai warware aurenba to itama bazata yarda 'yarta tabar gabanta ba taje koinaba sai taga yanda iyayensa suka tarba auren tukuna,
Saita Gama ganin kalar haukar data shigesu akan auren sbd suna taba Mata yarinya wannan karon rigimar da ake neman magancewarce zata Gama girmama ta zama wani abin Kuma,
Ita Bata da damuwar duk yanda duniya zataji sunanta ya lalace sbd Daman qaurin sunan ne da ita
AQEEL ASAD din kawai takeji kada duniyarsa takoma abar bugawa a jarida Koda yaushe Amma tunda kusan hakan kowa ya zaba bazata quntata rayuwarta ta quntata ta 'yartaba
Aure dai an daura to zata zuba Ido taga abinda zai biyo baya daga garesu.
Ficewa tai dakin tabar Amal wadda itama kukanta ya tsaya sbd abinda ya tsaya ya danne Mata zuciya akan yanda mommyn ta zabi kasa baqanta ran AQEEL ASAD akan nata,
Bazata sake maganar komai Akan aurenba tunda batama yarda da aurenba Dan Haka suda suka daura Saji da maganar Amma Babu Wani aure da zata dorawa kanta.
Bayan fitar mommyn kasa taurin ran tayi wani sabon kukan ya yunquro Mata ahankali sbd anrigda anyi Mata wata irin cuta da illa a rayuwa Koda an warware sbd har abadanta AQEEL ASAD shine Wanda akasan yafara aurenta.
Kuka takeyi ahankali jikinta koina Yana daukan zafi da mutuwar jikin.
Mommy na fita Kai tsaye Palo ta sama uncle Lulu daketa amsa wayoyin Taya murna Babu qaqqautawa daga mutanenda duk sai daga baya suke samun labarin daurin auren Wanda Babu Wanda ya taba Tunanin zasu iya samun Saar mutum irin AQEEL ASAD ba ya shigo cikin ahalinsu ya zama sirikinsu ba sbd Shi din dasu Kamar doya da manja ne rayuwarsu tayi hannun Riga data juna nesa ba kusaba.