Kenza eBookz

Idon nera by mamuhgee Complete - Chapter 30

Idon nera by mamuhgee Complete - Chapter 30

Idon nera by mamuhgee Complete Chapter 30: Idon nera by mamuhgee Complete Chapter 30. •Abu na farko daya sake biyowa bayan zazzabinta shine yawan baccinta,…

4,455 words

•Abu na farko daya sake biyowa bayan zazzabinta shine yawan baccinta, Ga zazzabi koyaushe Mai karfi ga yawan baccin saikuma Dan ciwon marar gashi period din yaqi zuwa, Hankalin Haj Zainab fara tashi yayi akan ciwon duk da hankali ko tinaninta Bai taba zuwa kan wani tunanin wani Abu Mai Kama da wani abinba Amal zata iya alkatawa. Ita kanta Amal din gain lamarin na neman ja Mata attention din mommyn sosai sbd abinda tafara magana shine meyasa wanna Karon Babu wannan ciwon marar kwata kwata sbd Dan wannan datakeyi bama ciwo bane akan Wanda ta Saba. Tashin hankali tashiga sbd sanin meyasa batai ciwon marar ba kaman vanda vafada Mata ai bazata garaba ayanzu sbd….....kasa qarasa tunanin tayi sai ta aro qarfin halin gaske ta dorawa kanta qarfin danne ciwon.Asibiti mommy tace zasuje a washe gari Dan Haka cikin mummunan yanayin tsoro da tashin hankali da kunar suie asibitin ace any wani abin da itane shiyasa ta Dena ciwon Mara. Da wane Ido zata kalli mommynta da familynta musamman idan sukaji Wanda yayi wani abun da ita. Kasa daukanta bacci yayi duk yanda kuwa take da tsananin bacci a kwanakin. Da kanta ya cake cikin tashin hankali da fargabar wayewar gari kuka ta fashe dashi tana rufe idanuwanta Dan Bata taba tunanin akwai dalili akusaba Wanda zaisa a iya ganewa., •Fatanta Allah yakawo dalilin dazai hanasu zuwa asibiti har aje aji wani abin tayi idanma ance tabbas zatayi denying Kai tsaye sbd bazata yarda da wanna zancenba. Sai guraren asuba bacci ya dauketa da ciwon kai Mai Dan tsanani. Batafi awa biyu tana baccinba ta farka tana duba agogo taga 8 saura Dan Haka ta tashi ta sauko gadon kanta na sake tsananta Mata ciwo ta nufi toilet. Brush da wanka tayo tana fitowa ta shirya cikin doguwar Abaya blue da simple gyaran data saba ta fito wayarta da hanbag dinta a hannunta ta fice gidan kowama Bai tashiba Daman takira Ahmed tana fitowa Suka wuce makaranta sbd tunda Suka kammala exam har aka guntun hutun aka dawo batajeba tana fama da kanta. Yanzune aka dawo Dan Haka ba waima angama dawowa hutun bane gabaki daya Dan Haka Babu Wani karutu sosai ko mutane sosai Sosai dasuka dawo ita kanta Bata fara zuwa da wuri Idan aka dawo Amma yanzu ba yanda ta ivane tana cikin tsananin Hali na damuwa da tashin hankalin mommy da zasu asibiti a yau din shiyasa ta gudo. A mota tayi zamanta tunda Suka iso makarantar ahakan bacci ya dauketa Ahmed saiya fita motar yabar Mata ita a kunne sbd AC Tasha baccinta tsawon lokaci kafin Kiran mommy ya farkar da ita dakuma yunwa da zazzabi Mai garfi daya sake sauko Mata, Cikin fada sosai mommy ke tambayarta tana inane? Dan daidaita muryarta tayi ta sanar Mata tana school kiranta akai akan akwai lecture din da zasuyi Mai mahummanci da safen. Rasa abin fada Mommyn tayi sbd takaici sai kawai ta kashe wayar tana cewa,"Neman lafiyar takima sai an ringa binki Ana rarrashi. Ajiyar zuciya Amal ta sake jikinta na sanyi sbd duk abinda mommynta tace tayi shi takeyi Basa tsallake maganarta duk freedom da rayuwar yancin dasukeyi ba takura ba saka Ido to sunada tarbiyar data Basu shine basada rashin kunya ko gadara tareda reni ga wainda sukasan manyansu ne musamman ita datake mahaifiyarsi, Amma ita yau gata a tsaka me wuya na wanna yanayi daya sameta, WIh batasan tayaya zata iya kallo ko Shiga gidansuba idan akasan me tai ta Dena ciwon Mara din., Me ma zatace Akan AQEEL ASAD din Wanda ko gaisawa baa San sunayiba bare kalion juna har irin wannan abin yashiga,WIh musawa zatayi duk likata ta bada tabbacin cewa tagano kila tayi sex ne ta dena. Fitowa makaranta sukai tace suje talindo steak house. Suna zuwa shine ya Shiga yayo Mata order na abincinsu da AQEEL ASAD ya koya Mataci sbd acan kawai ake siyo musu abinci. Brown spaghetti sauce dinsu takeso sosai kaman maita kusan duk suna tare sai ansiyo Mata duk da Bata taba fadaba Amma yanda take cinta yanayinta Yana nuna yanda takejin dadin cin nata yasa ya fahimci tana tsananin sonta Dan Haka duk zaa kawo musu abinci sai anhado da ita Kuma Idan so nawa zataji saita lumshe Ido cikin Jin dadinta. Suna barowa Kai tsaye school Suka koma acan taci abincin ko gamawa batayiba vau din sai amai ya biyo baya sbd ba ahaka ta Saba cintaba,Yawanci a zaune kan gafafunsa yake zaunar da ita a dining ya ringa Bata abaki tanaci atmosphere din bama daya Dana makaranta ba aikuwa take cikinta yakasa amsa ta ringa amai Mai qarfi da galabaitarwa. Hankalin Ahmed tashi yay ya rasa ya zaiyi Kuma waye zai Kira gashi ba Daman tabata, Bottle water guda uku ya siyo Mata masu Dan sanyi yakawo ta karba da gyar ta iya wanke fuskarta da bakinta wani mummunan jiri na dibanta ta dawo mota tana shiga jikinta ya ringa kakkarwa. Sake shiga damuwa Ahmed yay Yana Tunanin kaita gida Amma Kuma ya lura kaman yau tsoron zuwa gidan takeyi baisan meyake faruwaba kada yakaita ya lalata Mata shiri ko wani abinda takeda niyar Yi Dan Haka saiya sake shiga damuwa. Wayar AQEEL ASAD yafara Kira Amma sam baya dauka bd tana silent Yana meeting da mutane Kuma tana kife ne a gefensa so bazaiga ko hasken kiranba. Kira kusan biyar yay masa Bai dagaba Dan Haka ya lalubo numbern Al-Amin ya saka kiransa. Na farko Bai dagaba shima bd meeting din Amma ganin Ahmed ya sake Kiran yasan maganace data shafi Amal da ogansa tunda Shi duk kiransa Akan abinda ya shafa Amal ne bd Dan ita kawai aka daukesa aikin. Ahankali Al-Amin din ya miqe ya fito daga office na meeting din ya Dan Yi gaba kadan kafin ya daga Yana cewa, "Yes, Ahmed lafiya dai ko?? Ajiyar zuciya Ahmed ya sauke cikin damuwa Mai tsananin gaske ya sanar dashi Ms Amal ce batada lafiya sosai. Dan juyawa Al-Amin yayi ya kalli kofar daya fito kafin mamaki da kulawa yace, "Baa kaita asibiti bane? Tana inane? Bayani yayi Masa a tagaice cewan kaman batasan zuwa gida Kuma ga ciwon sosai Yana damunta shi baisan ya zeyi bane shiyasa yakira Sir AQEEL yafada Masa sai ya sanarda yanda zaayi idan ya kaita gidane kokuma asibiti. Sake Shiga mamaki da Dan abinda zaayi din Dan shima anan din Kam baisan mezaice ba sbd maganar ivalin AQEEL ASAD din ake magana Kuma ko Dan tsakanin Nan yanzu yafi kowa sanin Amal ba garamin matsayi take dashiba a zuciyar Sir AQEEL din Dan Haka shima bazai zage ya Fadi komai Dan Haka sai Sake Shiga mamaki da Dan abinda zaayi din Dan shima anan din Kam baisan mezaice ba sbd maganar ivalin AQEEL ASAD din ake magana Kuma ko Dan tsakanin Nan yanzu yafi kowa sanin Amal ba garamin matsayi take dashiba a zuciar Sir AQEEL din Dan Haka shima bazai zage ya Fadi komai Dan Haka sai kawai yace Ahmed din yakaita gidan karatun zaa turo likita yanzu idan ya fadawa AQEEL ASAD din. Ciki ya dawo ya qaraso gurin AQEEL ahankali tareda Dan ranqwafowa cikin tausasa murya qasa gasa yace, "Sir Ms Amal ce ba lafiya sosai inji Ahmed, Nace yakaita gidan Karatu Dr tayo na zuwa insha Allah. Shiru yayi ya dauke wuta gaba daya kaman Wanda Bai fahimta hausar ba kafin ya juyo ahankali ya kalli Al-Amin din Yana zuba Masa idanuwansa ya bude Baki yace, "MARYAMAH?? gyada Kai Al-Amin yayi ahankali Yana saka Kiran Dr tayo ya juya ya fice cikin gaggawa yace taje ta duba Amal din. Yana dawowa Kai tsaye AQEEL yace ya siya musu tickets zasubi jirgin yamma idan akwai. Amal kuwa gidan Karatu suka Isa suna Isa ta fito ta lallaba tashiga ciki sbd itama bazaso zuwa gidaba a wanna yanayin zai sake dagawa mommy hankali da zuwansu asibiti. Kai tsaye bedroom dinsa ta nufa ta shiga ta zube gasa ta kwanta tana maida wani irin numfashi Mai Dan wahala Tun tana juye juye hartasamu bacci Mai garfi ya dauketa cikeda azabar zafin ciwon zazzabi. Tana grin tana bacci saiga Dr tayo wadda da Bata gantaba a koina ta iso dakin tayi knocking daqyar Amal din ta farka ta jita ta rarrafo tazo tabude kofar ko tsayuwa Bata iya yi. Kamata Dr tayo tayi Suka koma dayan bedroom din sbd Nan master bedroom dinsane ko wancan lokacin sbd yanayin jikin natane yasa Suka shigo. Zaunar da ita tayi bakin gadon dayan bedroom din tana kallon yanayinta gabaki daya ta rasa karfin jikinta da kuzari. Fara taba jikinta tayi taji zafinsa ta kwantar da ita tareda duba plse dinta take tagane tanada ciki ajikinta saidai tana bugatan sake tabbatarwa Amma kafin Nan abubuwa ta rubutawa Ahmed yaje asibitin ta yakarbo Mata a pharmacy yana kawowa drip tafara daura Mata ta zauna tana jiran yaqare jikinta ya Dan sake suje asibiti a can akwai abinda take buqatan dubawa. Sai guraren 3 drip din yaqare Kuma tasamu karfin jikinta Sosai harma da isashen bacci Wanka tayi jikinta ya sake sakewa tayi sallah Tasha yoghurt Mai sanyi sosai a fridge. Har lokacin Dr tayo ce take tareda ita sbd AQEEL din daya bugaci hakan ita batama San yasan meyake faruwaba. Fitowa sukayi tareda Dr tayo Suka nufi asibitin Dan itama tanason sanin matsalar Bata Saba ciwo Mai kashe jiki irin wannan dinba. A motar Dr tayo din Suka tafi tabar Ahmed anan akan daga can Dr zata ajiyeta gida ta yanda mommy zatasan taje asibiti bama sai takaitaba any wani bude buden zance.Isarsu asibitin Kai tsaye dr tayo scanning Tai Mata Dan tafison tagani Kai tsaye din. Dr tayo na cewa scanning zatayi Mata taji gabanta yayi wani faduwanda yasata dakatawa daga Hawa gadon scanning din ta kalleta da idanuwanta dasukai ciki tsaban firgita ahankali tace, "Scanning name zaayi?? Qarasa zaunar da ita akai Dr tayo tayi tana cewa, "Naga alaman kinda ciki ne inason tabbatarwa. Shiru tayi tana kokarin fahimatar zancen dakyau a bude bd qwaqwalwanta daya kasa daukan zancan lokaci daya, "Ciki as in ciki na haihuwan baby?? Gyada Mata Kai Dr tayi tana Dan kallonta da mamaki tace, "Kina mamaki ne? Qasa riqeta gafafunta sukai ta silale zata zame Dr tayo tayi saurin rigota tana cewa, "Ki kula fa karki illata kanki da babynki. Tunda mommynta ta haifeta tayi wayo tasan kanta tun tana Yar Qarama harta kawo yanzu Bata taba kukan wayyo ita Allah ba sai alokacin. Ihun kuka Mai garfi ta fashe dashi tana Hawa gadon dukkanin jikinta na rawa tace a duba din idan da da akwaisa Amma dai fatarta Allah ubangiji yasa Babu cikin Dan kuwa batajin a rayuwarta zata shiga masifar datafi ace cikine a jikinta. Innalillahi wanna ilayhi rajiun" ta ringa maimaitawa dukkanin jikinta na rawa gabaki daya ciwon zazzabinta bacewa yay take tajita Ras sbd tsananin tashin hankali da firgici. Yanda tashiga tashin hankali da firgici yasa Dr tayo Jin firgicin itama tana mamakin meyene abin daga hankali a ciki musamman irin wanna da zaace AQEEL ASAD ne ubansa ita sai take ganin kaman sa'ar IDON NERA's dinne atlast dai zasu hada jini da AQEEL ASAD irin masu kudin dasukeso ace sunada alaga dasu, Kuma garshe dai gashi sun samu jikan da suketa so daga Siddi Dan ko ita tayita duba siddin akan nema haihuwa.

##MAMUH## *_Arewabooks@Mamuhgee_* 64 Dr tayo shiru tayi tana sake dubawa alokacinda ta tabbatarda cikine ajikin Amal din na sati biyar., Dagowa tayi ta kalli Fuskar Amal dake kallon screen din Amma Bata gane komai dake jiki ta sauke numfashi ahankali tana share Mata cikinta da tissue tace "Cikin sati biyar ne da kwanaki inaga shiyasa gananun sickness din sukai yawa Amma daya gota hakan zuwa 4mnth ko fiyema Zaki iya denawa….... "Ciki na haihuwa na sati bivar" takuma maimaita zancen cikin kanta tana Jin wani mummunan nauyi da tashin hankali mafi girma Yana rufeta,Hawayenta ne suka tsananta gudu ta sauko gadon ahankali tareda saka Kiran Ahmed hannuwanta na rawa tace yazo va dauketa sbd bazata iya nufar gidansuba a yanzu. Duk sauran bayanin Dr tayo daya biyo baya na yanda zata kula da cikin da kanta batai da batamasan me take cewaba tadaiga bakinta na motsawa sbd Nisan datayi ciki tinani Mai zurfi da tashin hankali. Ringing din wayarta ya fargar da ita tana ganin Ahmed ne ta mige tana Jan gafafunta ta fito batareda ta daukaba kokuma yiwa Dr tayo din godiya. Tana Isa motar ya bude Mata dasauri ta Shiga suna fitowa asibitin ya tambayeta Ina Suka nufa Amma ba amsa sbd Bata hayyacinta tayi nisa shiru Acikin tunanin ya zatayi da rayuwarta a daidai wannan gabar da abinda Bata taba kawo tinaninsa akantaba ko a mafarki yahau kanta, Innalillahi me zatayi? Ya zatayi? Me zatace? Ko yanda ake cire ciki da inda ake zuwa acre din Bata taba saniba tayaya zata fara fuskantar wannan tashin hankalin daya girmi tinaninta. Tafiya sukeyi batareda Ahmed yasan Ina suka nufaba sai yawon gari da bulayi yakeyi dasu. Wani masifaffen nauyi kanta ya dauka tareda zafi ta rasa Ina zata saka kanta, Wayarta taciro a karo na farko data Nemo numbernsa dakanta batareda Tama saniba ta saka kiransa cikin sa'a a daidai lokacin suke fitowa daga airport malam Rabiu ya daukosa tareda Al-Amin. Ganin Kiran nata shima a wavarsa a karo na farko yasashi sauke numfashi Mai sanyi sd vasan Dole akwai wani babban abin ne.Daukan wayar yayi tareda dorawa kunnensa kafin yayi magana ta sakar Masa wani kasalallan kuka tana rintse idanuwanta dasukai jajir ta. Ahmed na Jin hakan ya nema guri Mai kyau yayi parking ya bude motar yafito yabata guri. AQEEL najin sautin kukanta ya sake sauke wani nannauyan numfashin Kansa na daukan dumi ya kalli Al-Amin da Idanuwansa dasuka Dan sauya take ahankali yace, "Kira Ahmed kaji inda suke muje can yanzun Nan. "Okay Sir" yace Yana Nemo numbern Ahmed cikin rashin Bata lokaci ya saka kiransa,Ahmed dake wajen motar daga can gefe Yana ganin Kiran Al-Amin ya dauka da sauri cikin girmamawa kafima yayi magana A -Amin ya katsesa da jeho Masa tambayar inda suke, Shima Ahmed din cikin rashin Bata lokacin yafada ta guraren dasuke malam Rabiu na Jin inda Ahmed ya fada ya sake taka motar yana qara Mata speed. Har Suka iso gurin bayan tafiya Mai Dan tsayi ba sosai ba Bai kashe wayartaba tana kunnensa Yana sauraran kukan datakeyi Masa ahankali takasa cewa komai itama. Suna parking Al-Amin ya fito daga gaban motar zai bude Masa Bai tsaya jiransaba harya bude ya fito ahankali cikin nutsuwa bazaka iya gane abinda zuciyarsa da Ransa suke cikiba na yanayinda yashiga jin kukanta.Ahmed ma da sauri ya garasa motar ya bude Masa bayan motar inda take zaune daga dayan bangaren Yana Masa barka da dawowa amma Bai sakaran Yama jisa ba. Yana shiga Ahmed ya rufe Al-Amin ya kalli malam Rabiu yace sutafi ya ajesa gida yaje ya maida motar. Yana Shiga motar ta dago jajayen idanuwanta ta kallesa tana sake fashe Masa da kuka Mara garfi ahankali ya janyota jikinsa ya rungume Yana kokarin Hana Kansa rikicewar gangar jiki gabaki daya Dan yariga yashiga rikicewar zuci da ruhi daga lokacinda •vail kukanta vasauka cikin kunnensa ta wavar Kuka take Masa sosai ahankali harda shesheka Baice komaiba sai sake shigar da ita jikinsa yay Yana shata bayanta bugun zuciyarsa na wani irin tsananta sauya bugawa sbd ita din.Kiran Ahmed yayi yazo ya jata motar Suka nufa hanyar gidan karatunsa Yana kallon time sai alokacin 5 na yamma tayl. Har suka Isa Bata Dena kukanba harta gaji jikinta yayi sanyi hawaye kawai takeyi. Daukota yayi da Kansa daga motar ya kawota har Palo ya ajiye ya zauna tareda janyota ya zaunar gefensa tareda rigo hannayenta duka biyun cikin nasa Yana kallon idanuwanta dasuka sauya sod kukan ya sauke Ajiyar zuciya da numfashi a lokaci daya ya Ciro handkerchief dinsa Mai gamshi ya fara share Mata hawayen ya sake kallonta cikin wata irin kasalalliyar murya data Gama kashe Masa jiki da halinda ya ganta aciki yace, "Kuka va lsa Haka, Tell me meya faru? Menene kikewa wannan kuka?Jikin naki ne? Dr tayo Bata zo bane. Girgiza Kai tayi ahankali hawayenta na sake saukowa cikin qunci Mai tsanani da damuwa. "Mami ta gano kina kwana watara baa gidan bane?? Was hawaven masu zafine Suka Kuma gangaro Mata ta rintse Ido tana Jin Ya zatayi da rayuwarta. Sake sarke hannayenta Acikin nasa yay yana kallonta cikeda kulawa yace, "Menene? Hakan ne? Mami ce??? Uncle ne ko su Anty Fareedah? Waye ya gano? Meyasa Zaki damu idanma hakan ne a gurin Mijinki kike kwana waye baisan me ake nufiba da matsayin mili da aure acikinsu?? Girgiza Masa Kai tayi tana Nemo kuzari da qarfin halin dazata iya sanar dashi abinda yake faruwa din amma bazatama iya furta kalman ciki ne ajikintaba. Shirunta yasashi yin shirun shima sai kawai yaci gaba da rarrashinta Yana taba goshinta zuwa wuyanta yaji temperature dinta is normal sbd masifar data kunno Mata ta warke zazzabinta take. Qarfe 6 ta nace akan gida zata ta fito da Kansa yakaita har gate saidai ta hanasa shiga sbd mommy na gida ta hango motarta a harabar gidan. Bayason bata ranta musamman yanzu datake cikin wannan halin Dan Haka sai kawai ya juya din ya tafi bayan ta shige. Yana juyawa Kai tsaye Al-Amin yakira ya tambayesa Dr tayo batazo ta duba Amal din bane? Tazo" ya basa amsa Kai tsaye Yana sake basa tabbacin zuwanta sbd tace saisunie asibiti da Amal din ma amma batace komaiba Bayan hakan. Kashe wayarsa yayi ya ajiye tareda taka motar da speed Mai Dan garfi ya dauki hanyar asibitin sbd bazai iva Bata lokacin nemanta a wayaba zai sameta yaji abinda ya samu matarsa. Itama tana shiga ba kowa a gasa suna sama acan dinma tana hawowa ta samu duk suna Palo kowannensu zuba Mata idanuwa sukai sbd yanayinta daya nuna Batada lafiya da Kuma Jan da idanuwanta sukal. Mommy kafeta da idanuwa tayi sbd takasa gane kan Amal din gabaki daya kwanakin, Komai nata ya sauya yanzu Kuma ciwo yaqi ci yagi cinyewa ga jan Ido Kuma yau.Kiranta mommyn tayi tareda cewa tazo. Dakatawa tayi daga inda take tsaye tana kasa hada Ido da mommyn ahankali tace, "Mommy daga asibiti nake banajin Dadi sosai please abari na Dan nutsu sai nazo Dan Allah Mommy." Qarasa zancen tayi idanuwanta na cikowa da hawayen data kasa riqewa. Tashi hankalin Hai Zainab da siddi yay ta taso ta nufota tana rigo hannuwanta tace, "Meyake damunki ne Amal? Meyasa kikaje asibitin ke kadai ai nace nice Zan kaiki sod musan Meye wanna sabuwar matsalar data bullo, Me akace a asibitin to?Me aka gano Yana damunki??? Hawayen dake ciko idanuwanta ne suka gangaro takasa cewa komai sai kawai tace, "Ciwon maratane ya taso shiyasa naje, Yanzuma ciwo nakeji sosai mommy inason na kwanta. Kallon Hai Zainab siddi tayi cikin kulawa da tausayawa tace, "Mommy abarta ta huta da alama tanajin jikin please, Idan ta tashi ta huta ciwon ya Dan fada anima sai kiyi maganar da ita. Kyaleta Haj Zainab din tayi ta wuce dakinta ganin da gaske din da alamar Jin jiki atareda ita.Tana Shiga dakinta zubewa bakin gadonta tayi tareda sake sabon kuka Mara sauti tana rinse idanuwanta dake radadin kukan datasha. A dakin sai data Jima tana kukanta kafin ta tashi tashiga toilet tasake wanka tayo alwala tayi sallar magrib tayi karatun Qur'an kadan tasamu zuciyarta ta Dan sake tasamu qwarin gwiwar fitowa tana Dan nuna dauriyar samun sakewa Acikin familynta. Abinci sukaci Banda ita da fruits kawai Tasha ganin Mommy na kallonta sai ta Dan sakura abincin tana basarwa. Fira sukai a Palo dukkaninsu kaman yanda Suka Saba Amma ita tana gefe kwance tareda Fahat suna firarsu kaman vanda Suka Saba Amma shine Mai surutun yau sauraronsa kawai takeyi. Suna zaune suna firar saishi Bilkisu ta bude Masa kofar dayayi knocking Yana shigowa dukkaninsu Suka gaidasa Banda Amal datake neman rikicewa bd idanuwansa daya kafe akanta batareda damuwa da Maminsa da sauran jamaar gidan nagurin ba. Jin idanuwansa har lokacin akanta yasata dago nata da Basu koma daidaiba har lokacin ta Dan saci kallonsa sai gashi idanuwansu yashiga cikin na juna ta janye nata tana kallonsu Anty Fareedah da hankalinsu ke kan zancen dasukeyi na wani kayan da zasu siya a waya. Gurin mommy da uncle ta maida kallonta sukuma magana sukeyi dashi bilhaqqi batareda sun lura da idanuwansa na kanta ba. Sake kallonsa tayi ganin kallon nasa kusan ya banbanta dana koyaushe..Wani tunani ne yashigeta na ko Dr tayo tayi magana dashi take gabanta yay wani irin mummunan faduwa jikinta ya dauki rawa a boye tasake kallonsa taga irin kallon dayake binta dashi idan Bata bar gurinba zai iya tasowa ya dawo gurinta agaban kowa Dan Haka ta janye Fahat daga jikinta ahankali tareda miqewa tsaye tana gin sake kallon gefensa ta daga gafafu a sanyaye cikin toro da fargaba ta nufi stairs zata Haye.. "MARYAMAH" ya ambaci sunanta cikin wata irin nutsuwa hankali kwance Wanda fadan sunan yasa dukkaninsu kowa ya juvo Yana kallonsa sbd Babu Wanda ya taba kiranta da sunan sun ma manta da ance sunan nata na asali MARYAMAH ne Dan har lokacin Hai Zainab Bata fadar sunan a bakinta Koda na wanine daban ta yafe fadarsa. Ita kanta cak ta tsaya bugun zuciyarta na wata irin tsananta take idanuwanta suka ciko hawaye matugar ya bude Baki yayi maganar data danganci abinda take boyewa to zata iya yanke jiki agurin tsabar tashin hankali da mummunar kunyar duniya.Fatanta da adduarta a lokacin shine ya kasance baiyi magana da Dr tayo ba Dan kuwa tsabar tashin hankalin data Shiga yasa ta manta Bata fadawa Dr tayo din karta sanar da kowaba. •Ha Zainab kallonsa tayi lokacinda ya dawo da fararen idanuwansa dasukai wani irin sanyi akanta Yana kallonta Kai tsaye yace, "Amal zataje gain likitan da nay alqawarin zataje akan matsalarta, Ta shirya gobe da safe zamu wuce Zan kaita da kaina... Daga Hai Zainab harsu siddi da Anty Fareedah da uncle Lulu kallonsa sukai Ita kanta Amal din juyowa tayi ta kallesa cikin yanayi biyu sod tariga ta saddakar maganar cikin jikinta zaiyi saikuma taji wanna zancen Wanda shima ta tabbatarda idan akaje duk likitan da zata gani take zai tabbatar da cewa akwai ciki ajikinta.•Hai Zainab kuwa Dadi da akasinsa ne tareda mamakin Yaya Amal zataje taga likita Babu kowa atareda ita saishi Kuma bawani sabo ko magana sukeyi da junaba babu yanda tafiyar zata yiyu a hakan Dole saidai idan ta shirya ta bisu kokuma Fareedah ko Siddi. Magana zatayi uncle ya dakatar da ita da cewa, "Amal dawo zo. •juyowa tayi ahankali jikinta na sake mutuwa da wannan abubuwan wani bayan wani datake shiga, Shikuma uncle ko ya taba ganinsu ne kila shiyasa shima yace tadawo. Innalillahi wanna ilayhi rajiun" tafada cikin ranta hannuwanta na rawa ta saci kallon AQEEL dayake kallonta Kansa tsaye da alamar yariga yagama magana takuma sani tafiyar Nan sai Allah idan baayita ba Amma itama batason zuwa koina yanzu ta cikin jikinta take tukuna. ##MAMUH# * ZAFAFA BIYAR *

*_Arewabooks@Mamuhgee_* 65 Kasa qarasowa sosai tayi tsakiyar palon ta tsaya daga gefenda su Anty Fareedah suke tana Dan sauke kanta qasa,abinda yasake bawa kowa mamaki kenan ganin kanta a qasa Abinda Basu taba ganiba kenan,

Haj Zainab AQEEL ta maida idanuwanta akansa ta kalla sbd Shiga mamakin wannan halin na Amal datake tunanin da ace sunada kusancin da juna da tabbas zatace akwai saka hannunsa a sauyin da aka samu na wannan dabiar da zaa iya sakawa cikin kyawawan dabiu saukar da Kai gaban manya.

Shi kansa uncle Lulu hakan datayi sai yasashi manta ma mezai fada cikin Dan mamaki yace,

"Amal Yaya dai? Akwai matsalane??

Dagowa tayi jikinta na sanyi da tambayarsa ta kasa kallonsa shima tace, "lafiya kalau"

Shirun da AQEEL ASAD yayi musu tareda zuba musu Ido Yana jiran abinda sukeson fada suke zagaye zagaye yasa dukkaninsu Dan rudewa da rashin sanin yanda zasu Masa bayanin yabari zuwa ko qarshen watan Nan ne sai Amal din tareda Siddi mommyn tasake kaisu.

Haj Zainab dince tayi karfin halin kallonsa Kai tsaye tana cewa,

"Qarshen watan Nan zamu koma da siddi insha Allah inaga abari lokacin yayi mutafi taren kawai.

Cikin sanyi da nutsuwa tareda girmamawa harma da kulawa yace,

"Ai Mami ba likita daya zasu ganiba, Wanda MARYAMAH din zata gani daban ne so inaga ba amfanin jiran ta shirya goben insha Allah.

Ajiyar zuciya Haj Zainab ta sake sbd har cikin ranta batason zuwan yanzu sbd wancan likita taso Amal din tagani musamman yanzu da period din ya canja yayi latti da wuri takeson sanin menene wannan sabuwar sauyin da aka samu duk da ba dabiarta bace daddigin yaranta Dan ta yarda da abinta kawai dai ita kanta yagama juyewa yanzu Bata gane komai sosai.

Kan Amal dataqi sake kallon gefensa yayi cikin nutsuwa da kulawa yace,

"Ki Gama shirinki kafin 10....

Kallonsa ta juyo tayi tareda Dan juyawa ta kalli su Anty Fareedah harma da mommyn dake jiran ta watsar da zancensa a gurin ta wucewarta kaman yanda ta Saba har umman na fargaban yanda Amal zata karbi zancen Dan Daman ita harda sanin Amal din bazata yardaba yasata kame Kamen yabar tafiyar su saisu tafi da ita sbd abune Mai wuya Amal ta Amince tafiya dashi din tunda haryanxu taqi kallonsa a matsayin Mijinta.

Kallon mommynta tayi da Uncle Lulu ta bude Baki cikin Dan matse fuska tace bata buqatan zuwa koina yanzu abarta kawai.

Tanajin idanuwansa akanta lokacinda tayi maganar.

Jin wannan maganar yasashi miqewa batareda yasake cewa komaiba akan maganar yayiwa Maminsa da itama takeson ya tsaya ayi maganar dalla dalla asan abinda zai yiyu acikinta Dan tafi kowa sanin rigimar Amal din, Saida safe yamasu tareda uncle ya fice daga palon Yana Hana Kansa janyo matarsa a gurin ya rungumeta ko zai dawo cikakkiya nutsuwarsa daya rasa na Abinda Dr tayo ta sanar Masa.

Yana ficewa Haj Zainab ta kalli Amal data Gama kasheta da mamaki tace,

"Kinji abinda ya fada ai, Ki bude Baki kiyi magana ki roka yabari sai lokacinda zamu din kiga wancan likitan Amma kin tsaya wani Sumi Sumi,Wai Ni mema ya sameki ne da wannan dabiar?? Meya samu duka Baki da kuzarin naki be Wai?

Siddi data kasa rike nata mamakinta Kai tsaye tace,

"Mommy shakkarsa takeyi fa, Kina ganin AQEEL ASAD dinnan bafa Wasa ko fuskar Wasa a lamuransa, Gashinan karfi da yaji yaso hanata karutu Allah yasa ya sassauto yanzu gashi tsakanin gaskia da gaskia ya hanata driving da kanta saidai driver duk inda zata kaman tsohuwar mace,

Mami kema fa kina Dan shakkar wannan fuskewar ta 'dan ki bare mu, Nidai gaskia karma asani tafiya binsu bazan iya binsa ba Kinga ko kallon Mata bayayi itama datake matarsa Baga Yana kallonta bare,

Saidai ko Anty Fareedah zataje Ni Abuja ma zankoma satin Nan.

Readers Also Read