Idon nera by mamuhgee Complete - Chapter 35
Idon nera by mamuhgee Complete Chapter 35: Idon nera by mamuhgee Complete Chapter 35. Har Suka Isa gida idanuwansa rabi a hanya rabi akan Matarsa dake…
4,490 words
Har Suka Isa gida idanuwansa rabi a hanya rabi akan Matarsa dake gefensa ita kanta Amal din duk tabi ta narke sai rikitasa da idanuwanta takeyi.
Umma daqyar taga sun Isa gida karsu saka zuciyar 'yarta ta qara bugawa,
Yana parking harabar gidan Suka fito motar umma ce da Haj Maryamah din sukai gaba zuwa sashensu shima hannunta ya riqo jikinta na sanyi da zuwanta gidan Dan bazata iya Masa rigima bane sbd ummansa da Babu lafiya.
Kai tsaye bayansu umman sukabi har lokacin Yana riqeda hannunta sbd yasan tana cikin wani Dan yanayi na zuwanta cikin ahalinsa.
Suna qarasowa palon su umma harsun zauna Jamila da habiba Masu aikinsu harsun fito sunawa su Haj Maryamah sannu da jiki dakuma dawowa gida.
Shigowarsa yasa Suka bar palon bayan sun Masa barka da shigowa suna satar kallon Amal da hannunta yake cikin nasa batareda taji komaiba a gaban iyayensa.
Zaunawa sukai har lokacin tana gefensa Dan harga Allah Bata sakeba
Batasan mezatayiba a gidan.
Mufeeda ce tayi sallama tashigo jikinta da murya a matuqar sanyaye.
Kallonta umma tayi lokacinda ta qaraso cikin palon tazo gefen AQEEL tana satar kallonsa da Amal dake gefensa wadda ko juyowa batayiba ta kalleta.
Cikin sanyin murya tace,
"Daddy barka da dawowa.
Dagowa yayi ya kalleta a natse kafin ya amsa Kai tareda tambayarta dalilinta na qin zuwa school ranar.
Shiru tayi Dan batasan me zataceba Amma Kuma bazata iya fita taje school ba cikin qawayenta dasuka Gama saninta da dagawa amatsayin 'yar daddynta qwalli daya Yar gatan gidansu tako Ina Amma yanzu lokaci daya kowa yaji ita Yar tsintuwa zatace koma yar da aka samo da inda baada masaniyar iyayenta.
Tabbas Shigowar Idon Neras rayuwarsu wata babbar mummunan jarabawace da masifa,.
Rana daya lokaci daya sun shigo rayuwarsu sun lalata musu komai,
Sun tarwatsasu,
Sun raba umminta da Mijinta da duk abinda tayi tayine akansa,
Sun tona Mata asirin asalinta da batasaniba Kuma badan shigowarsu rayuwarsu ba da wannan sirrin ta tabbatarda bazai bayyanaba zata cigaba da zama jinin Mahaifinta da mahaifiyarta batareda kowa yasaniba.
Gashi yanzu sun rabasu da komai sun karbewa kansu.
Shirunta yasa umma kallonta tace,
"Ko kin hakura da karatun ne.
Shiru tasake Yi.
Haj Maryamah da Bata saka musu bakiba juyowa tayi ta zubawa mufeeda din Ido tana juya girman son datayiwa mufeeda din tsawon shekarun Nan sbd tinanin ita din jinintace,
Shin baqin halinta ake ganine akan tace tanason su haihu shine sukai Mata hakan?
Sun hadata da aikin wahalar dawainiya da son wadda ba jinintaba Bata hada komai da itaba,
Mufeeda kuwa ganin Haj Maryamah na kallonta tana tinani yasa jikinta sake sanyi sbd tasan a yanzu matsayinta dake zukatansu ya canja harshi daddyn Wanda ayanzu yakeda jininsa na gaske daga wadda yake ganin yafi kowa sonta a duniya.
Miqewa Haj Maryamah tayi ta nufi hanyar bedroom dinta tashige tabarsu a palon itama umma miqewa tayi ta nufi nata dakin duk da taso tambayar ko Amal din ta tare ne basuda labari Amma Kuma ganin yanda Amal din take zaune a gefensa bako space yasa takama bakinta ta shige.
Mufeeda kuwa so takeyi ta bawa daddynta hakuri akan laifinta Amma Sam har lokacin baibata Fuskar hakanba tunda abin yafaru fushi Mai tsanani yakeyi da ita duk da bawai baya amsa gaisuwarta ko wani abin ne dabanba.
Kallonsa Amal tayi tareda dan maraice fuska ahankali tace yakaita gida.
Kasancewar mufeeda na gurin yasa Bai taba fuskartaba sbd duk abinsa tarbiyar dayakeson 'yarsa tazamo akai daban take tintini Amma Ashe Bilkees tagama Bata Masa tarbiyarta,
Miqewa yayi Suka bar palon ya nufi mota suka shiga suka bar gidan.
IDON NERA Rs suka nufa suna zuwa ta sauke ajiyar zuciya a boye sbd batasan tayaya zata iya dadewa a can gidan ba jinta ta ringayi a takure sbd ba sabo ba kusanci a tsakaninsu danma yanzu ansamu Ana haduwa batareda anyi tashin hankali da masifu ba a tsakaninsu.
Bai shigaba yana ajiyeta ya juya yace zaidawo anjima su tafi.
Batareda tagane abinda yake nufiba sukai sallama tashigo ciki ya wuce.
Haj Zainab datake tunanin yanda zata tambayi AQEEL idan yatafi da Amal din kenan kokuma zai Basu ita sai a danyi Shirin tarewar,
Tana wannan tinanin Amal tashigo Suka bita da kallo mommyn na sake Fuska tareda sauke ajiyan zuciya Dan gaskia zataso yabari ayi Shirin tarewan kobabu bikin komai Dan Daman Kam ta hakura da maganar wani biki Dan bazataso Ayi wani taron komaiba Amarya na yawo da ciki agabanta.
Siddi ce ta kalleta lokacinda take zama tana cewa Bilkisu ta kawo Mata drink me sanyi tace,
"Amal na dauka yatafi dake shikenan Saida muzo kawo kayan Amarya daga baya.
Drink din da Bilkisu ta kawo Mata tafara karba ta bude Tasha sosai kafin ta ajiye tana kallon Siddin tace,
"Wane kayan?
"Kayan Amaryar AQEEL ASAD mana." Siddi tabata amsa tana juyowa.
"Mommy kice ta Dena Banaso fa"
"To ai gaskia tafada Amal dan Nima na dauka saidai na biyoki da kayan jeranki.
Bata fuska tayi tana yin shiru tunda mommy ma tashiga zancen Kuma ai shikenan.
Miqewa tayi ta wuce bedroom dinta tayo alwala tazo tayi sallah ta sauko sukaci abincin Rana Takoma sama ta tube ta hau gado tafara bacci cikin kwanciyar hankali.
Bata farkaba sai yamma lokacin ba kowa a gidan sun fita Dan Haka wanka tayi jikinta ya Dan sake tayi sallar laasar tasauko taci abinci tana chatting sama sama da wata course mate dinta dake Mata maganar karatu fa yayi nisa sosai yakatama tafara zuwa.
Ajiya zuciya ta sauke kawai sbd karatun neman zame Mata wahala yakeyi sbd cikin Amma dai Haka zata daure ta qarasa tunda suna final semester dinsu.
Sai Bayan magrib su mommy suka dawo salloli sukai Suka hadu cin abincinsu su dukan.
Ko farawa basuyiba hancinta ya shaqo Mata qamshin Mijinta a kusa
Tana dago Idanuwanta suka sauka cikin nasa Yana qarasowa idanuwansa akanta shima hutawa yaje gidansa yayi yasamu ishashe lafiyayyan bacci sai yamma ya farka sai Kuma yanzu daga masallaci yayo Nan cikin fararen Door sweatshirt da wando.
Yana qarasowa yaja kujewa kusada ita ahankali ya zauna yana gaida Maminsa da uncle Lulu.
Siddi ma gaidasa tayi tareda Anty Fareedah sai Fahat daya dawo gurinsa Yana gaidasa.
Amsawa yayi duka idanuwansa akanta
Ta Dan dauke idanuwanta daga Kansa sbd su Mommy dake gurin.
Qasa qasa tace Masa" welcome"
Amsawa yayi Yana kallon abincin gabanta data zuba kadan yace,
Kinci abincin yamma ne?
Girgiza Masa Kai tayi ahankali tana Dan neman narkewa Amma kallon daya Mata yasata fasa narkewar Dan zai iya Kai hannunsa gareta ko yayane a gaban mutanen.
Zuba Masa abinci tayi daidai yanda tasan zai ishesa kafin ta sake zaunawa maimakon yaci abincin saiya zuba Mata idanuwansa kawai Yana kallon yanda take tsakurar nata abincin alaman bawani yada takeson cinsa bane kawai ci takeyi.
Uncle Lulu ne yafara barin gurin ganin abinda yake faruwa
Yana miqewa Mamin ta miqe Dan AQEEL yafara nema sakata kunyarsa.
Siddi da Anty Fareedah ne Suka zauna ganin kwaf harsaida ya gaji ya karbe spoon din hannunta ya ajiye Yana cewa,
"Ki barshi haka jeki ki shirya kizo muje kici abinci.
Kallonsa tayi zatayi magana ya Dora yatsansa a bakinta Yana cewa,
"Just go get ready.
Miqewa yayi yabar gurin batareda yaci komaiba.
Gurin Maminsa ya dawo ya kalleta ya kalli uncle Lulu yafada musu kai tsaye Amal zata tare yau gidansa.
Shiru sukayi suna kallonsa uncle Lulu yace,
"Abar maganar tarewa yau abari asaka time sbd Basu Daman shiryawa da dai sauransu.
Itama Haj Zainab abinda uncle Lulu din yace tace AQEEL din ya duba sbd suna buqatan Mata shiri gaskia,
Kuma suna buqatan yabasu Daman gyaramata inda zata tare din.
Shiru yayi na minti daya kafin ya dago ya kallesu su duka yace baya buqatan komai na wani kayan tarewa Amma tunda suna buqatan time zasu iya Kai Mata komai nata gidan karatunsa zuwa next week idan masu sauya komai na gidan sun Gama sauyawa angama tsara komai sabo a gidan.
Dadi Haj Zainab taji harda saka Masa albarka da Kansa da fira har tsawon lokaci anan ma yayi sallar ishai tareda uncle a waje suna dawowa ya fidda wayarsa yakira Amal yace ta sauko su tafi.
Shiru Haj Zainab da uncle Lulu sukai suna kallonsa Haj Zainab sake da Baki sbd Bata Gama fahimtar me yake nufiba.
Ita kanta Amal kasa saukowa tayi sbd bazata iya tsallake su Uncle da mommyn ba ta bisa su fice gidanba bayan tasan ba lallai ya dawo da itaba a yau din kila sai gobe.
Firar dasuke yaci gaba da yimusu Amma Haj Zainab bakinta ya mutu uncle Lulu ne keda karfin halin cigaba da firar har time yasake ja ya kalli Maminsa yace Mata zai tafi.
Miqewa tsaye yayi Yana kallon Time yasake Kiran Amal din wadda takasa dauka tana kokarin kashe wayar mommyn tashigo dakinta ko kallonta bataiba tace taje AQEEL na kiranta zai bata sako wai.
Ficewa tayi Bata tsaya jiran amsar Amal dinba.
A sanyaye Amal din ta fito ta sauko kasa uncle ne kawai da AQEEL din shima Yana ganin saukowarta yayi wa AQEEL din Saida safe ya wuce.
Tana tahowa cikin sanyi sanyeda doguwar Riga da doguwar hijab har qasa ta sallarta data Gama Bata cireba tun dazun datayi.
Dan dauke idanuwansa yayi daga kanta yana riqe murmushinsa Dan yanda take tafiyar a cikin sanyima kashesa takeyi.
Tana isowa ko magana batayiba ya Kama hannunta Suka fice Yana cewa yunwa yakeji.
Mota Suka Shiga Dan itama yunwar cin abinci taredashi takeji Dan Haka Kai tsaye Al-Amin yakira yace ayi musu ordern abinci.
Can gidansu umma Suka fara zuwa Kai tsaye sashensu umman Suka nufa tana riqeda hannunsa Dan takasa sabawa da yanayin datakeji idan zata fuskanci su ummansa.
Suna shiga palon su umma dukansu suna zaune harda mufeeda datake kwana anan tunda Bilkees ta bar gidan sbd acan sashen daga ita sai masu aikin Bilkees din da already an sallami daya saura daya.
Akan hannunsa da Amal take riqe dashi Haj Maryamah ta sauke idanuwanta tana kasa cewa komai zuciyarta na harbawa Amma dai ta danne ta dauke idonta.
Umman Cameroon kuwa kallon Amal din tafara Yi bayan taga hannuwansu a riqe taga ba alaman Jin komai a tareda ita sai ta hadiye zancenta itama.
##MAMUH#
*_ZAFAFA BIYAR_*
*RUMBUN K'AYA*🔥
Hafsat Rano
*DAUDAR GORA*🔥
Billyn Abdul
*IDON NERA*🔥
Mamuhgee
*A RUBUCE TAKE*🔥
Safiya huguma
*KI KULANI*🔥
Miss xoxo
Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200
ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN
0022419171
Maryam sani
Access bank
Shedarka ta 09033181070
MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN
09166221261
🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*
+22799643131
Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA
*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*Thanks for choosing us*🔥
75
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
75
Qarasowa sukayi shine yafara gaida su umman tareda tambayar jikin nata kafin ya kalli Amal data koma kaman me koyan magana yayi Mata alama da Ido Akan ta gaidasu umman.
Ahankali ta bude Baki cikin nutsuwa da sanyinta ta gaidasu tareda tambayar jikin ummansa kaman yanda taji ya tambaya din.
Shiru umman tayi batareda ta amsa ba,
Ta kalli umman Cameroon itama Kai tsaye cikin nutsuwa ta gaidata tana kallon AQEEL din alaman gaisuwar nata yayi.
Gyada Mata Kai ahankali Yana Dan sake Mata murmushin Jin Dadin hakan.
Umma quri tayi tana kallon AQEEL da yau gabaki daya mamakin abubuwansa takeyi Dan su ba Haka Suka sansaba,
Kamili natsatse Suka Sansa da alkunya Amma yanzu wasu abubuwan take gani a taredashi kaman wadda ya tashi a Dan iska ga Amal datake maqale a gefensa kamar me tsoron mutane ko gudunsu Dan kuwa Sam taqi matsawa daga gefensa.
Mufeeda miqewa tayi ta shige ciki kaman wata munafuka sbd Idan tana ganin Amal da daddynta Jin takeyi kaman zuciyarta na daukan sabon ciwo.
Zama sukayi sama sama yasake Jin umman kafin suka miqe yayi musu Saida safe zasu wuce ya sake kallon Amal cikin kulawa yace,
"Say goodnight to them.
Juyowa tayi tasake musu Saida safe itama kafin suka juya Suka fice.
Suna fita umman Cameroon data kasa rufe Baki da mamaki ta juyo ta kalli Haj Maryamah data Gama shiga yanayi na abinda yafi karfin mamaki,
Cikin mamaki Mai girma umma tace,
"Wace sabuwar rayuwar Kuma zamu fara gani yanzu?
Me nake gani yarinya kaman cingum ta manne jikinsa kaman mune Bilkees data tashi kasheta.
Haj Maryamah da batada ta cewa sbd karfin tunaninta da lamarin neman yi numfashi kawai ta sauke tana cewa,
"Ki shirya ganin fiyeda wannan ma umma tunda 'yaya sun taso a hannun 'dan daudu da Idon Nera.
Su Amal kuwa suna fitowa mota suka nufa Suka fice daga gidan ya nufi gidan karatunsa.
Koda suka Isa Al-Amin yakawo abincinsu harya jera ya tafiyarsa.
Hijabinta Suka fara cirewa Suka ajiye ya rakata tayi fitsari Suka dawo
Kitchen Suka fara zuwa ya wanke musu hannayensu shi da ita Suka fito.
Zama yayi ta zauna da kanta kan qafafunsa tareda sauke ajiyar zuciya tana kallonsa shima ita yake Kallo Yana murmushi qasa qasa yace,
"Idan kinyi missing kafafun Mijinki meyasa danaje dazu gidan Mami Baki hau kansu kin zaunaba kinci abincinki.
Gyara zamanta tayi akansa da Yar sakaltacciyar murya tace,
"Kaine baka janyoni ka doraba akai ai.
Wani silent murmushi yasake yana Dan bude idonsa akanta ya matsota jikinsa Yana Mata wani mayen kallonsa dayake tayarda tsikan jikinta yace,
"Kika fada Haka??
"Ki shirya abinda zai faru idan cin abinci ya sameni a gidan kina taredani...
Manna Masa kirjinta dake kusan kashesa tayi tana marairaice fuska tace,
"Aa ban fadaba karkayi komai please.
Wani kallo yayiwa kirjinta data manna Masa da gangan Yana Jin kaman tana zare Masa notikan Kai ya shaqi qamshinta tareda rintse Ido ya bude Yana sauke ajiyar zuciya.
Ganin yanayinda yashiga yasa ta Dan motsa jikinta ahankali cikin wani irin salo tana sake goga Masa kirjinta dake neman zautar dashi
Ya bude idanuwansa yana kallonta Yana rasa wane irin kiss zai Mata kafin ta zautar dashi.
Itama shi take kallo ganin yanayinsa yasa ta janye kirjin nata tana murmushi tafara kokarin miqewa daga jikinsa ya riqota tareda zagayeta da hannayensa Yana hanata miqewa da wata fitinanniyar murya datai qasa sosai yace,
"Me kikayi?
Kallon cikin idonsa tayi tareda cire idonta daga cikinsu ahankali murya qasa qasa itama tace,
"Me nayi??
Kirjinta ya gangara idanuwansa ya kalla ya dawo da kallon cikin idonta ya sauke wani kasalallan numfashi yace,
"Kinsan Abinda Kika aikata kuwa?
Uhmmmnn??
Girgiza Kai tayi tana lumshe Ido sbd shafar dayake wa wuyanta zuwa cikin rigarta Yana zira dayan hannunsa cikin rigarta.
Numfashi ya sauke Mata a fuska a hankali kafin ya bude idanuwansa dake lumshewa ya kalleta kafin ya maida kallonsa kan abincin dake jere a dining din.
Hannunsa daya yakai a kan babbar robar Mick and Kay greek yoghurt din da kusan shine abinda takeso sosai take Kuma sha ya dauko tareda budewa ya saka spoon ahankali ya debo yafara Bata abaki Yana Jin jikinsa na macewa da yanda take bude Baki cikin wani irin sanyi tana karba.
Ita kanta yanda yake Mata wani mayen kallo yasata yin sanyi tana bude bakin a narke tana Dan dauke idonta daga kallonsa sbd kaifin idonsa dake sakata Jin kaman zata kasa ko bude bakin.
Wani spoon Yakuma debowa yakai bakinta tana budewa ya fasa saka mata ya saka bakinsa ahankali cikin bakin nata cikin sanyi ya ringa tsotsan zaqi da sanyin da bakinta yayi na Greek yogurt din yanajin jikinsa na sake mutuwa.
Ahankali ta zare bakinta tana kallonsa shima ita yake Kallo.
Spoon din ta karba ya debo takai bakinsa ya bude Mata ahankali ta saka Masa ya lumshe Ido saidai Bai shanyeba ya hade bakinsu Yana hadawa da bakinta da harshenta da yogurt din Yana tsotsewa Idanuwansa a lumshe.
Sake debo wani tayi tasaka Masa abaki shima yasake hadawa da bakinta ya tsotse Yana sake qarawa abin Dadi da yawun bakinsu.
Tuna taba iya debowa harta jikinta ya mutu ta kasa..
A jikinta yaqarasa lashewa ya zarce da zare rigar jikinta tana Zane kan qafafunsa daga ita sai black transparent lace wire bra datake bayyanar Masa da hasken fatar kirjinta dasuke cikin bra din.
Wani mayen yawu ya hadiye a makoshinsa kafin yafara Bata abinci tanaci yana binta Yana lashewa da shafawa harta koshi shima ta tayasa ci suna gamawa brush Suka fara Yi kafin wanka Wanda tun a toilet ya Gama galabaitar da ita da romances dinsa masu sanyi kafin suka fito yaqarasa aikinsa Yana rabata da towel din jikinta a tsakiyar gadonsa ya yai Mata wani irin lafiyayyan aikin dayasata bacci a take Yana gamawa.
Saida ya dawo daidai shima kafin ya dauketa da Kansa yayo musu wanka Suka fito rigarsa kawai ta zira ta kwanta bacci ya dauketa Mai nauyi da dadi ta manta da maganar komarta gida.
Rufeta yai da abun rufa tareda komawa Palo ya zauna Yana amsa wasu Yan wayoyinsa kafin yaje yayi alwala yayi sallolinsa na dare kafin yaje ya kwanta tareda Shigewa jikinta ya rungume cikinta yayi musu addua bacci ya daukansa shima.
Washe gari bayan sunyi asuba sun koma Basu farkaba sai after 10.
Batayi wankaba Saida tafito Palo ta nufi dining taci abincin da aka kawo musu tana gamawa tayi wanka lokacin shima yafito wanka.
Bayan ya shirya yafito Saida ya sake Bata abinci kadan taci suka fito tare.
Gurin ummansa Suka fara zuwa yabarta acan ya wuce office kaman zatayi kuka Suma su umman kaman zasuta Rusa ihun hakama mufeeda.
Zugum tayi a Palo tana rasa abinyi duk bayan mintina saiya kirata yaji yanda take
Rikice Masa takeson Yi duk yakira Amma saiya lallabata ya kashe
Ahaka har lokacin sallah yayi dole aka kaita dakin ummansa acan tayi alwala tayi sallah tana idarwa ta Kirasa cikin sanyin murya da kasala tace Masa yunwa takeji.
Suna Gama wayar yakira ummansa yace Amal na Jin yunwa abata abincin Kuma kartasha ruwan sanyi sosai sbd Dr tayo ta hana.
Haj Maryamah shiru tayi zuciyarta na nauyi jikinta kuma na sanyi.
Saidatayi mintina ahakan kafin ta samu ta sauke ajiyar zuciya tareda juyowa takalli inda Amal din take zaune kan dadduman sallah har lokacin tana waya da mommynta ahankali wadda itama Jin Amal din na gurinsu umma yasata sauke numfashi kawai badan taji tsoro ko shakkar komaiba Dan tasan Babu abinda zai faru tinda shine da Kansa ya barta agurinsu Yana sane.
Qwarin gwiwa kawai mommynta tabata kafin suka kashe wayar suna mantawa da kunyar bama gida Amal din ta kwanaba
Abinci aka Kai Mata a dining aka jera umman batareda ta kalletaba tace taje ga abinci can a dining.
Babu musu ta miqe ta fice daga dakin sbd Daman ba a sake takeba zamanta a dakin daga ita sai umman.
Tana fitowa mufeeda na fitowa daga kitchen daukeda cup da fura aciki tanasha.
Wucewa tayi batareda ta kalli Amal dinba itama Amal din ko kanta batabi ba ta wuce habiba na gaba ta kaita har dining.
Tana zama ta kalli abincin dasuke gurin take taji ta koshi sbd qamshin tafarnuwa dake tashi sosai a abincin.
Miqewa tayi da sauri tana kokarin barin gurin sbd zuciyarta daya fara tashi sosai abinda Bata taba yiba tun samun cikinta wato su amai.
Habiba da Bata fahimta ba bude Mata abincin tafarayi take amai Mai qarfi ya yunquro Mata da gudu tabar gurin ta rasa gurin zuwa da gudu tayi dakin datayi sallah tana shiga ta nufi toilet da sauri tafara zuba amai Mai qarfi.
Habiba bayanta ta biyo ta tsaya kofar bedroom din Haj Maryamah tana jiran taji idan lamarin da sauki.
Umma dataji Ana kakarin amai da qarfi
Fitowa tayi ta shigo dakin Haj Maryamah tana tambayar lafiya.
Amai sosai Amal din keyi Dama tunda Suka taho take a yanayi sbd qamshin girkin dayake Dan fitowa daga hanyar kitchen Sama sama Dan Haka take Aman sosai qarfin jikinta na qarewa.
Jin lamarin yafara wuce tinani yasa umman Cameroon nufar toilet din tana cewa,
"Me kikaci ne?
Amal dai Bata iya magana idanuwanta sunyi laushi sunyi ja.
Kamata umman tayi ta kunna Mata ruwa ta wanke fuskarta da bakinta Suka fito gabaki daya qarfinta yayi qasa.
Zaunar da ita tayi a sofa tana Kiran habiba tace taje takawo Mata ruwa.
Da sauri habiba taje takawo Mata ruwan sanyi umma ta karba ta miqa Mata Haj Maryamah ganin sanyin ruwan Yana nunawa har a cup ta Tina da maganar AQEEL Dole ta bude Baki tace,
"Yace Kar abata Abu me sanyi.
Juyowa umma tayi ta kalli umman cikin mamaki tace,
"To fa,
To kawo kafin yazo yana mana ciki ciki da Ido.
Karban ruwan tayi aka kawo Mara sanyi ko kadan aka Bata tasha jikinta na sake sanyi.
Shiru dakin yayi Bayan habiba ta wuce sbd Babu Mai Abun fada Dan Haka itama saita Kama kanta tayi shiru a zaune jikinta na qarasa sanyi sbd yunwa Dama zazzabin dataji kaman zai taso Mata.
Zaman jigum jigum sukayi tsawon lokaci zazzabin na sake shigarta da mutuwar jiki har yamma Bai dawoba ahakan ta zame a gurin ta kwantar da kanta take baccin wahala ya dauketa.
Sai yamma ya baro office Kai tsaye gidan ya taho Yana shigowa ya samu su umman duka a Palo ya gaisa dasu Kai tsaye ya tambayi Amal din da Ido umman Cameroon ta nuna Masa dakin mahaifiyarsa tana cewa,
"Amai tayi dazu inaga bacci ya dauketa koma kila ta farka.
Kallonsu yayi yaga kowa ya fuske Dan Haka ya nufi kofar dakin Kai tsaye yashiga.
Cikin bacci taji qamshinsa a kusa da ita ta bude idanuwanta ahankali ta gansa gabanta durqushe Yana kallon fuskarta data Dan fada kadan wuni daya kawai.
Numfashi ya sauke tareda tayar da ita zaune Yana zaunawa gefenta ta kwanta jikinsa ahankali tareda sauke ajiyan zuciya itama tana qarasa bude idanuwanta
Fuskarta ya shafa ahankali yace,
"Kinci abinci?
Girgiza Masa Kai tayi tana jikinsa kwance.
Wuyanta ya taba zuwa goshinta yaji zazzabine ajikinta Dan haka ya Ciro wayarsa Kai tsaye wayar Dr tayo yafara Kira suna Gama magana yakira Al-Amin ya kashe.
Tayar da ita yayi yakaita kofar toilet tashiga yadawo ya zauna.
Bata jimaba ta fito ya saka Mata hijab din da aka Bata tayi sallah tayi sallar laasar da batayiba.
Tana idarwa ya cire Mata hijabin ya Kama hannunta Suka fito Palo.
Suna fitowa su umma dukkaninsu Suka bisu da Ido ya kawota gefen ummansa ya zaunar Yana zama shima wayar Al-Amin na shigowa.
Dauka yayi yace Masa ya samesa sashen umma.
Abincin datafi so ne aka kawo Mata mufeeda yasa ta karba takai dining ta jera jiki amace.
Da Kansa yakaita dining suka zauna tare dayake baa ganinsu da Kansa ya Bata batareda ya dorata a cinyarsa ba kaman yanda Suka saba.
#MAMUH#
*_ZAFAFA BIYAR_*
*RUMBUN K'AYA*🔥
Hafsat Rano
*DAUDAR GORA*🔥
Billyn Abdul
*IDON NERA*🔥
Mamuhgee
*A RUBUCE TAKE*🔥
Safiya huguma
*KI KULANI*🔥
Miss xoxo
Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200
ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN
0022419171
Maryam sani
Access bank
Shedarka ta 09033181070
MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN
09166221261
🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*
+22799643131
Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA
*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*Thanks for choosing us*🔥
76
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
76
Su Haj Maryamah dai Shiru sukayi ba magana sai Ido sbd ita yanzu tattala zuciyarta takeyi karta buga a banza indai akan Zainab ko ahanlinta ne ta Dena sakawa kanta azaba ta mace a banza ta barwa su Zainab 'dan Dan Haka tunda ba dayar 'yar da Zainab din ta Haifa a bariki bane to da sauki suje ahakan sbd shine yaji yagani ya zabeta.
Bata wani ci abincinba sosai sbd gabaki daya jikinta ya mutu gidan takeson Bari Takoma gidansu kokuma gidan karatunsa Amma anan din Sam batada sakewa bare walwala.
Zuwan Dr tayo yasa suka baro dining din suka dawo palo Dr tayo ta kalleta taga jikinta duk a mace tace,
"Mrs AQEEL ASAD Yaya dai?
Meye problem din?
Muji jikin?
Taba jikinta tayi ta kalli AQEEL daya tadota tana murmushi tace,
"Wannan babyn yana sani yawo fa.
Kallon Haj Maryamah umma tayi
Haj Maryamah din ta miqe tabar palon gabaki daya.
Umma kuwa tana zaune a palon har Dr tayo tagama tatafi.
Kallonta yayi cikin kulawa yace tazo suje bangarensa.
Bata fuska tayi Ahankali tace bazataba.
Yanayinta yasa ya fahimci sbd Bilkees datayi zama a bangaren yasa tace bazatajeba.
Hannunta ya Kama ya Dan rarrasheta akan su tafi din Amma tadage taqi.
Numfashi ya sauke tareda barinta a sashen badan yaso ba ya nufi bangarensa Dan yin wanka yafito sallar Magrib da ake Kira.
Itama dakin ummansa takoma tunda batada zabi acan tayi sallah tana idarwa ta fito tadawo Palo ta zauna tana jiransa gida takeson su tafi duk da bataga alaman hakan daga garesaba.
Aikuwa Bai dawo bangarenba sai after 10 bayan har bacci ya dauketa a palon zaune Yana shigowa ya ganta zaune tana bacci umman Cameroon na gefenta zaune hakan ummansa na daga nesa dasu tana amsa waya cikin nutsuwa.
Kallonta yayi Kai tsaye yace musu anan zata kwana...
Daga ummansa har umman Cameroon kallonsa sukayi Haj Maryamah tace,
"Sbd me?
Numfashi ya sauke ahankali yace,
Umma can gidan karatu zata zauna Amma anfara aikin gyaransa yau hakama Ni gobe insha Allah tafiya zanyi tariga ta baro gida zata zauna anan kafin nadawo.
"Sai ka kaita bangarenka.
"Kallon umman tasa yayi jikinsa na sanyi da yanayinta nako yaushe da Bata sakin komai da sauki.
Nutsuwa yai ya kalleta yafara Mata nasihunsa kaman yanda ya Saba yayi Mata sosai kafin yace Amal tace batason can bangaren Kuma bazai iya tilasta Mata ba Dan Haka ta zauna a gurinsu Ga amanarta Nan kafin ya dawo.
Suna kallo ya dauketa yakaita dakin ummansa ya kwantar ya fito ya fice.
Ita kanta Yana shiga da ita dakin ta farka tanaji tana gani ya fice yabarta.
Haj Maryamah raba dare tayi a Palo sbd batasan ya zatayi takwana daki daya da Amal dinba,
Shikuma Daman Yana sake ya yanke shawarar barinta a hannunsu kafin ya dawo ta tare gidanta sbd su fara sabawa da junansu Dan Dole.
Daga Haj Maryamah din har Amal Babu Wanda yayi wani baccin arziki Ana asuba dukkansu Suka miqe.
Bayan sallar asuba Amal tasamu tayi bacci Bayan umma tabar Mata dakin Takoma Palo tana karance karancenta.
Bata farkaba sai kusan 10 tana tashi brush tayi da wanka ta fito sanyeda doguwar Riga cikin kayan da akai Mata order tunda safen kafin ya wuce.
Batama San wucewarsaba saidai text dinsa data samu.
Abincin da habiba tayi duka batasonsu Dan Haka tace tayi Mata white Noodles da kwai kawai.
Tana Gama breakfast din saiga su Siddi da Anty Fareedah kaman zatayi kuka sbd murnar ganinsu
Suma kasa hakuri sukai Suka taho Jin ita kadai ya Bari a gurinsu umman.
Dakin Haj Maryamah Suka shige tana ji tana gani batada abin cewa.
Harda wasu kayanta Suka kawo Mata na sakawa datake buqata sai mommy data kirata tace ta sake sosai karta takura kanta ko sawa kanta damuwa sbd juna biyun jikinta.