Idon nera by mamuhgee Complete - Chapter 4
Idon nera by mamuhgee Complete Chapter 4: Idon nera by mamuhgee Complete Chapter 4. Zainab ganin lamarin ya girmama yasata tashi da gudu ta dauko ruwa a…
4,499 words
Zainab ganin lamarin ya girmama yasata tashi da gudu ta dauko ruwa a fridge tadawo Tana tsoro da shakkar zubawa Antyn tata Amma Kuma batada zabi sbd Maryamah din kamar bama wani sauran Rai a jikinta Dan haka jiki na rawa ta zuba Mata ruwan.
Wani tunani ne ya haska cikin kan Zainab na cewa ko Umma ne aka bugo waya ta rasu? Mummanan faɗuwa kirjinta yayi take ta sake shiga firgicin dayafi na farko sbd idan umma ta rasu ita shikenan batada Wanda zai tsaya Mata a rayuwa Koda kuwa Babu so Babu kulawa kamar umma.
Ba shiri ta sakewa Maryamah ragowar ruwan da ke hannunta Tana kallonta hannuwanta na rawa batama San tafara tambayar Maryamah din waye ya rasu ba.
Babban masifar data sake rikita Zainab shine rashin farfadowar maryamah Dan haka suka kwasheta hankali tashe sai asibiti.
A asibitinma saida suka dauki lokaci kafin ta farfado cikin tsananin kuka da tashiin hankali Mai ban tausayi,
Zainab sai alokacin tasan waye ya rasu take itama jikinta ya sake daukan rawa da firgici sbd Bata kawo mutuwar a kansaba....
Innalillahi Wainnah IlayhirRaju'un..."
Shine abinda tahau maimaitawa tanajin tashin hankalinta na qaruwa da tausayin Aqeel daya zama maraya kamar ita duk da shi yanada sauran gatansa sosai.
Washe gari har aka gama haɗa gawar MUHAMMAD ASADULLAH bisa jagorancin ƴan uwansa da suka samu isowa tare da abokan arziƙinsa Maryamah na can gadon asibiti ita da umma data taso tun jiya ta iso gabanin asubar yau Zainab Kuma Dole Takoma gida sbd gidan a hannunta yake matuqar masu gidan basa Nan gakuma Aqeel da zazzabinsa ya dawo Wanda kowa ya tabbatarda na rashin mahaifinsa ne da yayi.
An Gama komai maryamah da ake jira suka dawo daga asibiti ko tafiya da kanta Bata iyayi riqe ake da ita sbd mummanan jiri dake dibarta ga wata irin firgicewa datai a kwana dayan Dan kuwa bakinta Kansa ya bushe ko yawu daqyar take iya nemowa a bakinta ta hadiye.
Dawowarta kuka ya dawo sabo acikin gidan dake cike sosai da mutane Yan uwan Asadullah din na nesa da kusa duk sun halarto cikin baqin ciki da alhinin wannan mummanan rashin daya samesu.
An yi masa sallah an kuma kaisa gidansa na gaskiya ya samu ɗinbin mutane da kyakkyawar sheda daga gurin mutane musamman malaman addini sunata yabonsa sbd mutum ne Mai tsananin son Addininsa.
Maryamah kuwa dai tana cikin matsanancin hali na ɗimuwa da firgicin babban rashin nagartaccen miji kuma uban ɗanta ƙwaya ɗaya jal
Addu'a kawai ake mata tana sha ana tofa mata sbd lamarin ya tabata sosai Dan kuwa daga baya har asibiti ake tunanin fara kaita idan ba harda kanta rasuwar ta taba ba.
Zainab kuwa wani babban al'amarine ya risketa na zaman karban gaisuwar Dan kuwa kusan a tsaitsaye tagama figewa tas Takoma kamar Yar qaramar fatalwa sbd wahala da nata tashin hankalin na rasuwar Wanda shine takewa kallon gatanta a gaba Amma shima ta rasashi Dan haka kukanma kasawa tayi sbd nauyi da dacin da zuciyarta take dabaibaye dashi koina,
Abincin datake dafawa na zaman yafi qarfin duk wani kokari da iya wahalarta Dan kuwa duk masu taimakawa gurin aikin ba wani aikin arziki sukeyiba kusan duk itace qarfin aikin aikuwa take cikin kwanaki qalilan ta fice hayyacinta Ga kula da Aqeel Wanda shima jikin yakeji Kuma yaqi aminta da kowa ya kula dashi sai ita Dan haka duk tabi ta qarasa haukacewa gwanin tausayi.
Haka aka gama kwanakin zaman karban gaisuwar har rasuwar tayi sati biyar kusan koyaushe basa rasa Yan zuwa gaisuwar.
Kwanakin da suka biyo bayan rasuwar Alh Asad sun kasance kwanaki mafiya ƙunci da soya zuciya a wajen Maryamah da ma duk wani me ƙaunarta don ta yi kwanakin ne cikin tsananin ruɗani da ficewar hayyaci sabida bada wasa ba soyayyar mijinta ta gama rarike zuciyarta baki ɗaya gashi Aqeel danta datake kallon Asad acikin Sam yakasa rabarta kokuma kaunarta yanda yake kaunar wadda renonsa kawai takeyi duk sai tasake susucewa Takoma kamar wata bebiya ko yawan magana bataso kullum shiru take batason hayaniya.
*********
A hankali kwanaki sukai ta shurawa suna bada watanni cikin aminci da yardar Ubangiji Maryamah ta gama takaba A hankali aka fara tattara duk wasu kadarori da marigayin ya mallaka kama daga kan kamfanoni da gidaje zuwa zunzurutun kuɗaɗe da ya tara aka raba gadonsa Wanda kusan 'dansa Aqeel shine da mafi yawan gadonsa sai mahaifiyar Alh Asad din da matarsa maryamah sai ya kasance kusan komai na tarin dukiyarsa Mai yawa a hannun maryamah yaje Dan kuwa itama sai dataji tsoron dukiyar da 'dan ya gada harma da nata Jason
Hakan ya sanya wasu daga cikin ƴan uwansa suka fara jin haushin Maryamah din musammam dasuka nuna zasu karba Aqeel din su rikesa Tunda ita Cameroon zata koma gurin mahaifiyarta...
Babban rikici tayi da Yan uwan nasa akan 'danta Aqeel Wanda qarshe ta yanke shawarar Babu inda zata tafi zata zauna ta tarbiyantar da 'dan takuma kula da dukiyarsa.
Da wannan aka kashe zancen Wanda kusan har kotu ake Dan kawai suna son karbe yaron.
Sun saka Mata ido sosai tareda sharadin idan ta almubanzarar da dukiyarsa da tarbiyarsa zasu karbesa har abada bazasu Bata Shiba.
Wannan rigimar itace babban qalubalen daya fara samun rayuwar maryamah Wanda kusan tashin hankalinta sabo yadawo Dan kuwa tasan badan Allah sukeson karban Aqeel dinba su rabata dashi sai Dan kawai su cinye dukiyar da mijinta yayi wahalar Tarawa iyalinsa karshe 'danta yayi wulaqantacciyar rayuwa.
Wannan qalubalen shine yafara juya rayuwar maryamah datayi alqawari tareda sadaukar da kanta gurin tsare haqqinta Dana 'danta Dan kuwa bazata Bari 'danta yayi wulaqantacciyar rayuwaba indai har Allah yabarta da ranta da lafiyarta da ikonsa insha Allah zatayi yaqi ta kare haqqinsu.
*****Ahankali Maryamah tafara yawon duk garuruwa da inda dukiyarsu take Tana duddubawa da kanta sai personal assistant dinta da aka kawo Mata Dan kuwa dukiya ake magana a manyan gurare...
Tun lamarin na zuwar Mata da sauki har kanta yafara neman bugawa sbd Takoma ko sati hudu Bata iyayi a gidanta kullum Tana hanya a mota ko a jirgi musamman Lagos Wanda kusan can cibiyar kasuwancin Alh Asad din yake sbd acan yayi karatu Kuma yayi rayuwa.
Duk yanda take tsananin so da kaunar 'danta Aqeel haka tanaji Tana gani ta hakura tabarwa Zainab shi Dan kuwa Shi Kansa Bata ganin kaunarta a idonsa irin yanda yakewa Zainab...
Zainab itace tasan ciwonsa,. Itace tasan lafiyarsa, Itace tasan damuwa da quncinsa, Itace tasan wankansa da kashinsa da fitsari tun Yana jaririnsa har zuwa lokacin,
Dararraku marasa adadi Zainab ce take kwana zaune Tana fama da kukansa da ciwonsa,
Tunda aka haifesa Zainab ta rasa barcinta na dare da lokacinta sai nasa,
Batayi aureba bare tasan Yaya daukar cikin yake Amma takai stage dinda zata daki kirji ta sanar cewa daukar cikin da haihuwa ne kawai bataiba Amma Babu abinda kowace uwa zata nuna Mata akan rainon 'da tun Yana zaninsa har girmansa.
Tayi bautar mahaifiyar maryamah, Tayi ta maryamah da mijinta Yanzuma gashi tanayin ta 'danta Wanda shi tasa bautar ta yarda ta sadaukar da rayuwarta agurin wahalta Masa har tsufanta sbd tsananin son datakewa Aqeel din jinsa takeyi tamkar 'dan data Haifa jininta.
Ba Aqeel kawai maryamah tabarwa Zainab ba hatta gidanta Dan kuwa kusan komai a hannun Zainab yake na kula da komai Amma a fannin wahala sbd kusan wani nauyi ne dayafi qarfinta aka Dora Mata.
Bata taba saurayi ko wani Wanda zai ganta yayi shaawar aurenta ko soyayya da ita sbd Bata wani fita tamkar a prison take Idan ta fita ko dai wani aikin wahalar aka aiketa taje tayi.
Aqeel karatunsa yafara nisa Dan kuwa yagama primary js 1 zaije,
Zainab kuwa tuni tafara wuce tsarin 'yan Mata budurwai sbd shekarunta dasuke gaba da baya ba Amma Babu wani cigaban dayazo Mata koda na barin bautane saima abubuwan dake sake cabewa rayuwarta Dan yanzu maryamah Sam Bata zama tayi dedicating rayuwarta itama gurin aikinta Dan kuwa yanzu tazama babbar mace Haj MARYAMAH ADAM ASADULLAH.
Aqeel bai taba Jin kaunar Mamin tasa (Zainab) ta ragu a ransaba duk girman dayakeyi.
Kullum shaquwa da kaunarta yake qatawa tareda dibbin tausayinta,
Tun baiyi girmaba lokuta da Dama idan yaga yada take figewa Tana fita hayyacinta agurin aikin wahalar gidan kullum alqawarinsa akanta shine"
"Mami idan na girma nayi Miki Alqawarin zan daukeki daga Nan na Gina Miki babban gida da mota da komaima da kikeso"
Murmushi kawai takeyi Mai ciwo aduk lokacinda ya fada Mata Hakan sbd batasan me kaddararsu ta tanadar musu a gaba ba Amma Zataso hakan ace Aqeel dinta ya girma suna tare,taga aurensa da 'yayansa Dan ba lallai ita tanada nata rabon 'yayanba da zataga nasu auren da yayan.
Haj maryamah Bata taba zaunawa ta duba wautar datakewa kanta da rayuwarsu itada 'danta ba,
Takasa zaunawa taja yaronta ajiki, Ta kaunacesa, Ta rungumesa tayi fira dashi, Taji Yaya rayuwarsa take..
Shin meyasa ba shaquwa da kauna tsakaninsa da ita tabarwa Zainab komai nasa Wanda hakan yasa Zainab tamaye gurbin uwa agaresa batareda dukkaninsu sun Ankara da hakan ba.
Kwata kwata Hankalinta a kwance ya ke akan ɗan ta AQEEL din don zuwa yanzu ta gama yarda cewa duk duniya Babu Wanda zai iya so da kaunarsa da kulawa dashi sai Zainab Wanda su Zainab da 'danta Aqeel din har mantawa sukeyi da Bayan junansu sunada wasu 'yan uwan ko mahaifiyar. ##MAMUH# #FAMILY#SISTERS#LOVE#ROMANCE #AMAL IDON NERA# HAJ ZAINAB IDON NERA.
*_ZAFAFA BIYAR_*
*RUMBUN K'AYA*🔥 Hafsat Rano
*DAUDAR GORA*🔥 Billyn Abdul
*IDON NERA*🔥 Mamuhgee
*A RUBUCE TAKE*🔥 Safiya huguma
*KI KULANI*🔥 Miss xoxo
Littafi daya---400 Biyu---600 Uku----800 Hudu-----1k Biyar din duka----1200
ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN
0022419171 Maryam sani Access bank
Shedarka ta 09033181070
MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN
09166221261
🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪 *Ina yan uwa 'yan nijer?* *Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*
+22799643131
Littafi daya---450CFA biyu---650CFA uku----850CFA hudu----1050 CFA Biyar----1250CFA
*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!* *Thanks for choosing us*🔥
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
7
_ASSALAMU ALAIKUM JAMA’AR KWARAI.. JAMA’AR AMANA… JAMA’AR ZAFAFA… MASOYA KUMA MABIYA MASU ALHERIN SAYAN ZAFAFA A KODA YAUSHE BA GAJIYAWA…GODIA MAI TARIN DIMBIN ALBARKA DA FATAN ALKHAIRI AGARE KU.._
_KUNSAN DUK INDA ABUBUWAN ARZUKA SUKE MUNA SHIGA MU KURDA MU NEMO MUKU SU DOMIN JIN DADIN KU..🥰💕SABODA KU DIN NA GABAN GOSHINAN MU NE._
_TAMKAR KO DA YAUSHE.. YAU MA MUNZO MUKU DA WATA TSARABAR.. TSARABAR DUNIYAR KAYAN KITCHEN, DECORATIONS DA SAURAN SU… KU MARMATSO KU JI…_
*_MAAB LUXURY HOME_* *_MAAB LUXURY HOME_* *_MAAB LUXURY HOME_*
_KUN GANI KO? TO INA AMAREN? INA UWAYEN GIDAH INA YAMMATAN DA KE SHIRYE SHIRYEN SHIGA DAGA CIKI? INDA ZAKU JE KU KANKARO MUTUNCI KU DANDALO ARZIKI NA KECE RAINI.. INDA ZAKU WUCE RENI DA GANIN KASKANCI..INA MAZAN DA KE BURIN FARANTAWA MATAN SU DA ‘YAYAN SU DA KANNEN SU? _
_MAAB LUXURY HOME: RIGIJI GABJIN KENAN! WOHOHO WANI KAYA SAI AMALE KAN DAUKA.. MAAB LUXURY HOME : ALJANNAR KAYAN KITCHEN KENAN, INDE AKACE KAT TOH KARSHEN MAGANA TA KARE KENAN.. MAAB LUXURY HOME ; A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY KITCHEN UTENSILS, HOME DECORATIONS AND MUCH MORE_
_ADIRESHIN MU: MUNA KAN TITIN AHMADU BELLO WAY, KANO STATE. ZAKUGA TAMBARIN DA MAAB LUXURY HOME.._
_DAN SAUKAKA MAKU FITA ZUWA SHAGON MU. ZAKU IYA ORDER AKAWO MUKU DUKKANIN INDA KUKE A FADIN NIJERIYA DA KETARE. _
_INSTAGRAM: @maabluxuryhome._
_FACEBOOK: @maabluxuryhome._
_KO KU NEME MU TA LAMBAR TARHON MU: 08034631010_
_KYAU! INGANCI! RAHUSA! ADADE ANA AMFANI DA SHI SAI KAYAN: MAAB LUXURY HOME_
_100% TESTED AND TRUSTED😍☑️_ ______
******** Tun Haj maryamah na tafiyenta da basa wuce kwanaki zuwa satittika yanzu wasu lokutan takanyi doguwar tafiya qasashe Wanda suna share wata daya,biyu,uku,har fiye Basu gantaba,.
Ana cikin hakan Wani aminin Alh Asad dayake babban Justice dake Abuja ya fito neman auren,
Da farko Bata aminta ba Amma ummanta da hajiyar su Alh Asad suka tilastata tareda nasihu tukuna ta amince akai auren Amma shi Yana can Abuja da iyalinsa itama yabata ware Mata nata gidan Amma Bata wani zama sai can can idan taje abujar ta Dan zauna tayi kwana biyu kokuma idan shi yazo Mata Haka dai aure yake kamar Wadda akaiwa Dole a auren Shima Justice Ayub Nasir din bai wani damuba sbd sanin uzurirrikanta da Kuma dama shima baya wani som zama.
Ita Kuma Zainab Hakan yasa ta sake dagewa sosai gurin tarbiyantar da Aqeel Wanda yaketa qara girma Yana cigaba da karatunsa Tunda yazama dai itace tamkar uwa Kuma ubansa.
Aqeel Kyakykyawar Yaro ne Mai nutsuwa da rashin son shiga cikin mutane sosai bare Wasa cikin yara 'yan uwansa,
Kasancewar yanayin yanda rayuwar tasa ta taso yasa yake shiru shiru mara son hayaniya, Baida mahaifin dazai tsaya masa ya zama jagorarsa,
Wadda itace ta haifesa Sam batada lokacinsa bare nuna Masa kauna da shakuwa,
Wadda yakewa kallon uwa Kuma mahaifiya agaresa Tana cikin wani irin qunci da rashin yancin Kai dazasu sake suyi rayuwarsu,
Duk gata da daular da ake kashewa gidan kamar baasan zafin nemansuba bai saka Aqeel din ya taso cikin Jin cewar ba Maminsa ce mahaifiyarsa ba shiyasa maimakon yayi rayuwar Jin dadi saima yake rayuwar kadaici kaman Maminsa suna rayuwarsu da Jin basa buqatar komai Ita Zainab batada wani buri ko kwadayi bare shaawar wata rayuwar, Ko Aqeel dinta aka Barta dashi baa rabasuba batada doguwar damuwa.
Dukkanin wahalar da ta sha tun yana ƙarami har kawo yanzu da ya fara zama babba bata taɓa jin daidai da rana ɗaya ta gaza ko ta gaji da hidimarsa ba,
Shi AQEEL Yaro ne me tsananin son a kula dashi tareda lallabasa, Hakan wata dabi'arsa ce data lura ta fahimta tun Yana qanqani shiyasa tafi basa mahimmanci da kulawa fiyeda komai a gidan.
Duk masu aikin da ake kawowa gidan basa wani zama tafiyarsu sukeyi sbd dagasu sai Zainab Aikin kawai akeyi Babu Mai gidar gashi duk da batanan aikin Babu Wanda aka Dena saima qaruwa Dan kuwa har kullum baa Dena karatu a gidanba saima qaruwa da jamaa sukai kusan duk manya Yan anguwar dake karatun da 'yayansu manya a gidan Malam Sanda ke basu karatun kullum tsakanin magriba zuwa ishai,
Hakama dangin Alh Asad maza kusan dukkaninsu anan gidan ake karatun dasu kullum Wanda sbd sakawa rayuwar gidan ido yasa suka maida sallar magriba dinsu zuwa ishai anan suma suna qaruwa da karatun.
Duka wannan lamarin dayake faruwa a rayuwar gidan har tsawon wannan lokacin babu Wanda yasan Zainab jinin Haj maryamah dince
A matsayin me Aiki suka santa tun kuruciya har kawo yanzu data girma zama mace shiyasa Babu Wanda yake ganin girma ko wani mutuncinta saima mayyar kwadayayya dasuke kallonta Dan uwar wahalar datakesha suna ganin kwadayi kawai zaisa ka zauna irin wannan rayuwar.
Shi Kansa Aqeel baisan qanwar mahaifiyarsa bace, A taqaice baisan sun hada jini da itaba saninsa Mai aikin gidance Shikuma uwace agaresa.
Qarin abinda yasa wasu masu aikin da Dama dasuke tafiyarsu shine duk wahala da biyayyar Zainab Haj maryama Bata yabawa bare nuna wani Jin dadi sai jikinsu na mutuwa da tsoron Hakan, Wasu Babbar sata suke zubawa su gudu wasu Kuma salin alin suke tafiyarsu Dan Zainab dasuke karkashinta meta zama duk shekarun bare suda abin duniya suka fito nema ba Wai zaman bautar banza ba.
Babban abinda yaqara saka Haj maryamah yiwa Zainab tsanani akan rashin barinta fita shine gudun tasamu mijin aure a lokacin tayi aure tabar Aqeel Wanda tasan bazai taba zamaba Zainab ta tafi tabarsa Tasani Sarai bin Zainab din zaiyi Koda zata hauka ne akan bataso tasan saiyabi Zainab Itakuma bazata iya Bari danta yayi rayuwa a qazamtaccen guriba.
Sabuwar dabia Mai karfi data shigeta shine tsanar duk wani Abu daya shafi gwagwarmaya da mutanen daba nagartattuba...
Ta tsani zuwa ko irin guraren dasuka shafi irin Hakan shiyasa ma gidanta yasake samun tsaro da dokoki Ko masu aikin da ake kawowa batason wadda Alama ta nuna tagama lalacewa da sanin maza, Sam Bata kaunar irinsu Qyanqyaminsu takeyi tareda musu fatar shiriya daga nesa shiyasa duk tsanani idan Tana gida batacin abincin kowa saina Zainab itama sbd tanada tabbacin tsarkinta da tsaftar rayuwarta da Bata gurbata tako Ina.
Rayuwarsu tafara sauyawa ne lokacinda haj Maryamah ta nemawa Aqeel wata tsadaddiyar makarantar boarding Amma Kai tsaye yaqi yarda da makarantar bakuma sbd kowa yaqi makarantarba sai Dan Maminsa wadda yasan wanu gata da sanyin datake ji duk sbd shine Dan haka akai akai Amma yaqi yarda.
Kiran Zainab Haj maryamah din tayi tai fada sosai tareda cewa lallai saita rarrashesa tasa ya amince ya tafi makarantar Dan tariga ta kashe maqudan kudi sosai akan karatun nasa.
Da farko Zainab rarrashinsa tayi tareda nasihu da Jan hankali iri iri Amma Sam yaqi yarda
Duk da bai fadaba itama tasan sbd itane Qarshe dabai yardaba hakura tayi ta qyalesa Dan Bata son takura Masa Tunda baya gardama da duk abinda ta sakasa sai wannan karon Dan haka bazata takurasaba Dan Jin take kamar tace a qyalesa karsu takura Masa Amma Kuma ba Dama Tunda uwar data haifesa ce take magana akansa.
Issue din makarantar yasa ran haj Maryamah baci sosai qarshe ta dorawa Zainab din lefin Bata basa tarbiya Mai kyauba tunda har zai iya qin abinda tace ita data haifesa.
Fada da bacin rai sosai akai akan maganar makarantar tasa Wanda dukanin laifin akan Zainab aka dorasa karshe kukan datake dadewa bataiba sbd bushewar da idanuwanta da zuciyarta sukayi Amma wannan karon saida ta kwana Tana kukan bacin ran da lamarin ya kawo Dan kuwa ko umma ta Kira wayarta Babu kalar fada da gorin da baayi Mata ba Hakan ta Basu hakuri Dan batada komai na fada.
Aqeel kuwa abinda sukaiwa Mamin yasa yace bazai taba zuwa makarantar ba Dan farko harya fara sauka akan zaije din ganin Maminsa nata lallabasa.
Tunda akai wannan tashin hankalin sai haj Maryamah tafara Jin buqatar raba danta da Zainab tun kafin lokaci ya qure Mata Dan kuwa da Alama 'danta tanaji Tana gani zai bijire Mata Wato dai kamar Zainab ta haifawa Dan kenan.
Ita kanta Zainab sake kame kanta tayi tareda shiga taka tsan tsan sbd ganin ran su umman da Haj maryamah ya baci sosai.
Aqeel baije boarding school dinba Amma Hakan daya faru yasa Haj maryamah yanke shawarar daukesa daga qasar kwata kwata zuwa wata qasar yayi karatunsa acan sbd da gaske take buqatar rabasa da Zainab yanzu sbd zuwa yanzuma tsoron irin kaunar dayakewa Zainab din takeyi Dan kuwa yafara maganar abawa Zainab qananun abubuwa zuwa gaba yayi girmanda zai karba dukiyarsa ta tabbatarda zai iya mallakawa Zainab komai nasa data Gama yawo da wahalar kular Masa da kare Masa.
Ta bangare daya malam Sanda ne ya zama malami na musamman ga Aqeel tareda cusa Masa akidu na so da kaunar karatun addnini sosai sbd harda shi acikin burikan mahaifinsa akansa,
Mahaifinsa yanada tsananin shaawa da buqatan 'dan nasa yasan Addininsa sosai yayi zurfi acikinsa Dan haka ahankali sai shima Aqeel din Hakan ya shigesa yafara zama Mai tsananin son addini da karatunsa sosai.
Yana karatun bokonsa Kuma Yana na addinin sosai,
Kokarinsa da nutsuwarsa akan Hakan yasa malam Sanda maida hankali gabaki daya akan Aqeel din Dan cika burin Alh Asad dakuma Dan samun qarin Wanda addnini zai qaru dashi.
Ahankali shaquwarsa da malam Sanda tayi zurfi sosai har yake Masa kallon mahaifi sbd shima ya manyanta yazama dattijo mai nutsuwa sbd ilimin addini daya ratsasa,
Sam baya tsallake maganar malam Sanda sbd ba qaramin girmansa yake ganiba musammam daya kasance ta wani bangaren kamar shi kadaine Bayan Maminsa Wanda yake fahimtarsa.
Yazama matashi Mai cikakkiyar nutsuwa da kamun Kai Kuma har lokacin Babu Abu daya rage na shaquwa da girman kaunarsa da Maminsa saima abinda yayi gaba,
MUHAMMAD AQEEL ASADULLAH yazama wani irin saurayi da kallo daya zakai Masa kasan 'dan gatane daya taso cikin gata da nitsatsiyar rayuwa,
Kyakkyawane Wanda ya dauko kamannin mahaifiyarsa sak wacce itama kyakkyawar tun asalinta.
Zainab Kuma zuwa wannan lokacin sosai ta fita a sahun matasa masu 'yan shekaru Dan kuwa tazama mace sosai gashi har Haj Maryamah data girmeta nesa sosai ta fita kyan gani da jikin kuruciya sbd Hutu da Jin dadi Itakuma wahala duk ta sauyata tasa manyancin zuwar Mata da wuri.
Har wannan lokaci Babu wani Wanda yataba sanin matsayin Zainab agun Haj maryamah acikin gidan
Shi Kansa Aqeel Asad har lokacin Baisan alaqartaba agurin mahaifiyarsa wadda yanzu Yana girmamata sosai sbd girma da hankali dayayi tareda sanin matsayin uwa data wuce kowace irin Wasa da reni.
A fadin duniyarsu shi kadai ne matum daya dayasan Maminsa ciki da bai, Shi kadai ne yasan menene abinda ranta bayaso da Wanda ranta yakeso duk da Sam batada wani raayi ko buqatar kanta sai tasu Amma ahakan yasan kowane yanayinta abinda yake nufi Dan haka yafara tsayuwa sosai akan duk wani lamarinta Dan kuwa ankai bagirenda shine da Kansa yasa aka kawo masu Aiki a gidan har uku yakuma daukewa Mamin tasa Aiki ko daya na gidan.
Zainab taji dadin Hakan Amma duk da Hakan tasaba da ayyukan wasu aikin Dole itace takeyi dakanta
Kamar lura da tsaftar babban bangaren mahaifinsa da aka maida sabon guri tareda zuba komai sabo na Jin dadi rayuwa na masu arziki yanzu shine aciki duk da bayaso Yana Mata fadan yin aikin Amma takasa barwa kowa aikin kulawa da duk abinda ya shafesa sbd tasan rikakken halinsa daya gado gun mahaifiyarsa na kyankyami da rashin son takura Dan kusan yafi mahaifiyar tasa qyanqyami da tsandar abubuwa nesa ba kusa ba.
Hakama tsaftar bangaren Haj maryamah har kullum itace da wannan sbd Haj maryamah din nada tsananin qyanqyami da tsanda,
Abincinsa Dana Haj maryamah shima har Koda yaushe nata kawai suke ci Dan haka dai kusan anyi baayi bane.
Tunda ya kammala secondary School aka fara yimasa shirye shiryen tafiya karatu UK Kuma bai musaba sbd shi Kansa yana buqatar zuwan duk da Maminsa na cikin ransa ta yadda zai tafi yabarta baa qarqashin kulawar kowaba. ##MAMUH# #LOVE/AQEEL ASAD/ #IDON NERA #ROMANCE #AMAL.
*_ZAFAFA BIYAR_*
*RUMBUN K'AYA*🔥 Hafsat Rano
*DAUDAR GORA*🔥 Billyn Abdul
*IDON NERA*🔥 Mamuhgee
*A RUBUCE TAKE*🔥 Safiya huguma
*KI KULANI*🔥 Miss xoxo
Littafi daya---400 Biyu---600 Uku----800 Hudu-----1k Biyar din duka----1200
ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN
0022419171 Maryam sani Access bank
Shedarka ta 09033181070
MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN
09166221261
🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪 *Ina yan uwa 'yan nijer?* *Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*
+22799643131
Littafi daya---450CFA biyu---650CFA uku----850CFA hudu----1050 CFA Biyar----1250CFA
*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!* *Thanks for choosing us*🔥
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
8 Da farko Jin tafiyarsa Zainab tashiga damuwa sosai saidai kuma Tunda karatu ne zaije, Qaruwarsa ce hakama duk cigabansa tanaso Dan haka sai ta danne damuwarta kawai ta boye a ranta Tunda kafin zuwansa duniya cikin kadaici take rayuwarta batareda kowa Dan haka yanzu dinma zata iya idan Allah ya yarda.
Dayake Yana karantar yanayinta Kai tsaye kwana biyu duk yanda take dannewa ya gane Tana cikin damuwa da kadaicinsa tin yanzu Dan haka sai shima yaji damuwar barin nata ita kadai din.
Kwana biyu yafara tunani da neman yanda zaiyi da lamarin Dan kuwa bazai taba iya tafiya yabar Mamin cikin damuwa da kadaiciba Kuma Hakanan zuciyarsa takasa nutsuwa da barin nata...
Ficewa tafiyar tafara yi daga ransa sbd ita, Jin yake zai iya hakura da tafiya wata qasar ya zauna yayi karatunsa anan sbd ita Amma Tunda Haj maryamah tafara fahimtar abinda yake Shirin faruwa na sauyin raayinsa dayake Shirin Yi take Hankalinta ya tashi sosai Kuma ranta yayi mummanan baci Dan kuwa wannan karon batajin zata sassautawa Aqeel din bare Zainab idai akan tafiyarsa ne.
Farko Kai tsaye ta tarasu a babban palonta da Aqeel da Zainab din wadda take zaune a kujera jiki amace
Ita kanta zaman kujerar sbd Aqeel Yana gurin ne take zaune akai Dan tuni yayi Hani da Zamanta a qasa Dan bazai iya yarda Yana ganinta zaune a qasa ba shi Yana kan kujera Haka Haj maryamah tanaji Tana gani ta dauki wannan dokar tasa ta barin zaman Zainab din a kujera a palonta idan suna tare sbd kaucewa bacin ransa.
A yau din ranta bace yake sosai Wanda kusan su dukansu sun shaida Hakan Dan haka palon yayi tsit suna jiran abinda zata fada musamman Zainab data Gama sanyi akan ko wane irin laifine tariga tasan itace zaace ta aikata Tunda akai kiranta.
Take jikinta ya sake mutuwa Dama kwanakin sai ahankali Tunda maganar tafiyar 'dan nata ta tabbata takasa gane kanta Dan Jin takeyi idan ya tafi kamar sun rabu kenan...
Kai tsaye Zainab Haj maryamah ta kalla kafin ta maida kallonta akan Aqeel Wanda ya kalla Maminsa yaga yanda duk tayi sanyi take zuciyarsa tayi Dan nauyi Dan haka ya dauke kallonsa daga gefenta ya gyara zamansa tareda hade dogayen fararen yatsun hannuwansa guri daya Yana Dan lumshe fararen idanuwansa cikin Yar damuwa da rashin Jin dadi.
"Aqeel maganar tafiyarka UK nakeson nasake Jin raayinka Dan kasan yanzu Kai ba yaro bane da zan zauna muna Abu daya koyaushe akan tafiyarka karatu, As you can see manyanci yariga yaxomin Dan haka Dole zaka maida hankali kan karatu Dan is dakemun wannan nauyin na Aiki da kula da komai Nima nasamu na huta na fuskanci gyaran gobe na.. so me kace gameda tafiyar???
Ahankali ya sauke idanuwansa akanta tareda Dan sauke idanuwansa qasa Dan girmamawarsa ga manyansa itace Sam baya iya kallon idanuwansu ko tsaida kallonsa akan fuskarsu Dan haka Bayan ya kalleta kadan saiya sauke idanuwansa..
Muryarsa data fara zama budaddiya irin na mazan dasuka amsa sunansu maza yace"
Umma inaga zanyi karatun anan hankalina zaifi kwanciya....
Katsesa Haj maryamah din tayi da cewa"
Sbd Zainab kake ganin karatun naka anan zaifi??
Baya qarya kwata kwata sbd ilimin addinin daya ratsasa yasan illarta barema ba halayyarsa bace Dan tarbiyar da Zainab tayi Masa Sam Babu gurbatacciya a cikinta Dan haka ka tsaye yace"
Eh harda ita a dalilin.....
Ajiyar zuciya Haj maryamah ta sauke zuciyarta na wani irin nauyi da 'daci tareda mutuwar jiki
Bata iya cewa komaiba ta juya ta kalli Zainab cikin sanyin murya tace"
Kinji da kunnenki ko?
Haka kikeson rayuwar tasa ta qare batareda karatun dazai Gina Kansa ba dama mu gabaki daya.. Haka kikeso ko Zainab??
Kasa magana Zainab tayi saidai AQEEL dinne ya duba umman cikin nutsuwarsa yace"
Umma Mami batasan da wannan tunanin nawa Dana yanke ba...
Cikin qosawa da halayensu Haj maryamah ta katsesa da cewa"
Tashi kaje nagama maganata dakai.
Miqewa yayi ba musu ya fice a natse Yana Dan rufe idon wasu halayen na iyaye Dole sai kana musu uzuri da kuwa sun wuce ka tsaya gardama ko sainsa da su.
Bayan fitarsa ahankali Zainab ta dago cikin sanyi ta Dan kalli Haj maryamah tace"
Anty wallahi bansan da wannan tunanin nasaba, Koda nasani Anty wlh kinsan bazan taba barin ya zaba abinda zai daqile cigaban rayuwarsa ba....
Kasa magana Haj maryamah tayi sai data dafa goshinta dake sarawa Yana saka kanta wani matsanin ciwo Dama gashi rayuwarta gabaki daya tagama juyawa Tunda tazama itace komai hatta hawan jini na wahalar Aiki da tunanin duniya duk ya kamata gashi acikin gidanma Aqeel da Zainab na neman sake Dora mata wani hawan jinin akan Wanda take fama dashi.