Kenza eBookz

Idon nera by mamuhgee Complete - Chapter 7

Idon nera by mamuhgee Complete - Chapter 7

Idon nera by mamuhgee Complete Chapter 7: Idon nera by mamuhgee Complete Chapter 7. Umma dataga zasuyi biyu babu sai gata ta iso ba shiri gashi da a ranar…

4,472 words

Umma dataga zasuyi biyu babu sai gata ta iso ba shiri gashi da a ranar zai wuce Abuja Gobe su wuce UK din.

Hankalinsa sosai yatashi ganin Halinda mahaifiyarsa tashiga akan lamarin dan haka sai jikinsa yayi sanyi ya zauna tareda ita yana nuna mata kulawa da kauna qarshe umma na ganin irin tsananin son dayakewa mahaifiyar tasa itama sai sukayi magana da maryamah sukai shawara.

Shawararsu suka sanarwa Aqeel din akan haj maryamah din zata karbi zainab da 'yarta su zauna a gurinta insha Allah.

Da farko hakan bai kwanta masaba dan kuwa hankalinsa yafi kwanciya da kulawar zainab din a hannun dangin mahaifinsa amma kuma duba da yanayin unman tasa data shiga damuwar tafiya sai kawai ya amince ahakan jikinsa duk yayi sanyi.

Yanason zuwa gurin maminsa amma itama Ummansa duk takasa barinsa sbd yanayin jikin nata Haka ya hakura.

Washe gari tunda safe ya shirya tsaf batareda lokacin wucewar yayiba ya tafi asibiti tareda umma gurin zainab. Batayi wani mamaki ko damuwar rashin dawowarsa a jiyan ba sbd tariga tasan zuwan nasama Allah kawai yasan irin fitinar da akeyi a gidansu akan hakan.

Ganin umma ya sata jin sanyin jiki dan kuwa tasan dole sai wani abu yafaru umman ke zuwa dan haka tasan akwai wata rigimar.

Gaida umman tayi cikeda girmamawa Umman ta amsa tareda Yimata gaisuwar mijinta da Barkan haihuwarta duk lokaci daya.

Aqeel ne da Kansa jiki a mace cikin kulawa yayi mata bayanin tafiyarsa a yau din tareda sanar da ita daga asibiti gidansu zata koma da zama komai ya wuce tsakanunta dasu ummansa sun karbeta ita da little MARYAMAH.

Shiru tayi zuciyarta na shiga tunanin lamarin Shiyasa umman tazo kenan dai akwai rigimar da akeyi din Wadda tasa suka aminta zasu amsheta Amma dai kuma a yanzu datakeda 'ya batajin zamanta gidan haj maryamah din zai yiyu sbd Dalilai da dama,

Haj maryamah bazata taba son Maryamah qarama ba sbd tun asali batason masu aiki dake da qananun yara Bare ita datakeda jinjirar 'ya,

Tayaya zata iya watsi da yarta tayita aikin bautarda ko yar tasan baa kaunaci ganiba,

Bayan haka Tayaya zata koma kurkukun da Allah yasa ta fito da qyar da 'yar marainiyar 'yarta suje itama rayuwarta ta mutu kamar Tata tun kuruciya har tsufa dan kafin Aqeel yadawo ya zama Gatan maryamah din tuni ta rasa abubuwa da dama.

Ganin yanda tayi shiru yasa umma kallonta a shagube tace,

"Ko kinfi karfin zama gidan ne tunda yanzu kema kin zama uwa babu Wanda ya isa dake.

Shiru Zainab tayi batace komaiba.

Cikin dan fada umman tace,

"Da tsufana amma kullum Ina hanyar tafiya mai shegen nisa sbd ke zainab, Duk zuwana babu na lafiya sbd rikicin halinki ne Dana yar uwarki,

Yanzu Ana fatar yaron nan ya tafi karatun nan angama komai rana tsaka sbd ke yasake cewa bazashiba Yanzu an samu ya aminta Zaije tunda ya shiryaki da mahaifiyarsa kin tsaya tunanin ta yanda zaki sake hargitsa lissafinsa ya fasa tafiyar ko zainab?????

Mun koma ga wadda ta Haifi 'dan ga wadda muke rarrashi akansa sbd isa da ikonsa da Allah yabaki..

Jin hakan yasa zainab taqaita fitinar da cewa ta amince zata koma can din karya damu ya wuce karatunsa kawai Allah yabasa saa da nasara.

Batason fitina da tashin hankali da gorinsu umma dan haka ya yanke zancen da hakan dan a samu ya tafi Suma su umman dan asamu ya wuce din yasa sukace sun shirya da zainab din komai ya wuce duk da kusan umma ce take kidan kuma take rawar Ita haj maryamah dai taqi saka baki sbd jikinta da zuciyarta dasuka kasa sakewa idan ba ganin tayi Aqeel din ya tafi ba dan kuwa da gaskiarsa magana daya tak yake tsayawa akai ba tafiyar zaiyiba idan ba zainab da 'yarta yaga yabarsu a cikin kulawaba.

Yaje ganin little MARYAMAH amma basu bashi damar daukantaba saidai yaganta daga cikin kwalban Dan haka yayi mata addua sosai da fatar tsarin Allah gareta yafito.

Zainab duk inda zuciyarta take tayi rauni sosai na rabuwa dashi din amma ta boye ta danne a ranta sbd kaucewa laifi gun umma kokuma hanasa tafiyar... Addua tayi masa sosai tareda fatan samun dibbin nasara da cigaba a rayuwarsa.

Harya baro asibitin kasa hada ido yayi da maminsa sbd yana iya hango damuwa da tashin hankalinta harma da firgicin tafiyarsa ya barsu itada little amma kuma tunda yasan gida yabarsu to tasa damuwar ta dan ragu yanada nutsuwar tafiya yanzu. #MAMUH# #MARYAMAH AMAL IDON NERA #DR AQEEL ASAD #HAJ ZAINAB IDON NERA #life#love#hotlove#marriage#

*_ZAFAFA BIYAR_*

*RUMBUN K'AYA*🔥 Hafsat Rano

*DAUDAR GORA*🔥 Billyn Abdul

*IDON NERA*🔥 Mamuhgee

*A RUBUCE TAKE*🔥 Safiya huguma

*KI KULANI*🔥 Miss xoxo

Littafi daya---400 Biyu---600 Uku----800 Hudu-----1k Biyar din duka----1200

ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN

0022419171 Maryam sani Access bank

Shedarka ta 09033181070

MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪 *Ina yan uwa 'yan nijer?* *Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA biyu---650CFA uku----850CFA hudu----1050 CFA Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!* *Thanks for choosing us*🔥

_*Arewabooks@Mamuhgee*_ 14 Yana barin asibitin ta zainab ta sauke wani kasalallen numfashi tareda sauke kanta qasa sbd idanuwanta dake kadawa jajir..

Fatan samun nasara da albarkar ubangiji tayi Masa a duk dinta yake sbd Allah ne kawai yasan ranar dawowarsa yasamesu ko wane yanayi Kuma sai yanda Allah yasa.

Zamewa tayi ahankali ta kwanta kan gadon datake tana rufe idanuwanta duk tasan ba baccin zatayiba.

Aqeel kuwa Yana Isa gida breakfast yayi batareda Bata lokaciba yagama aka fiddo da luggages dinsa suka fito hannunsa cikin na mahaifiyarsa dakejin kamar ta goyasa Dan dadi da farin ciki, Ta matsu taga ya wuce kafin zainab ta bugo tace 'yarta ta mutu yafasa tafiyar Kuma.

Dashi da uncle dinsa alh Yusuf suka wuce Har airport haj maryamah din ta rakasa sukabi jirgin Abuja Wanda a Daren ranar jirginsa zai tashi shima daga Abujan.

Tana dawowa wata irin lafiyayyar hamdala tayi tada tabbatarda jirginsu ya daga At last dai tasamu 'danta yatafi Yayi nesa da zainab Yanzu tasamu damar da zata ringa ziyartarsa shaquwa da kaunar dayakewa zainab duk zai maido kanta ya ragewa zainab din.

Wuni sukai a gidan cikin nutsuwa da farin ciki daga ita har umma.

Saida yamma tafito a shirye Dan zuwa asibiti ganin likitanta dazai sake duba dp din nata.

Tareda umma suka tafi asibitin Suna baya driver na jansu cikin daya daga cikin lafiyayyun motacin gidan.

Umma ma ciwon baya da qafafun datake fama dashi aka dubata akai suka fito zasu nufi mota umman tace suje haj maryamah ta dubo zainab tunda tana asibitin itama.

Da mamaki haj maryamah takalli umman sbd sanin asibitin ta kudine sosai Dan basuda ko irin dogayen dakunan ward haka Duka dakunansu daddaya ne Amenity rooms dai Kai tsaye.

Cikin basarwa umman tace"

Atoh, ai danki ne ya kawota Allah ne kawai yasan uban kudin daya kashe daga haihuwarta zuwa yanzu, Ko kudin haihuwar ba qananu bane gana jinyar 'yar Kuma acan wani dakin daban..,ai wlh maryamah kinyi sake sosai,.

Ace 'danki da Kika Haifa Yana hada kainarki data wata Duk laifinki ne Dan kece Kika barwa zainab 'dan gashinan yanzu bake kadaiba munata fama dashi Ga shegiyar kafiyar tsiya agunsa Shi ala dole yasan Allah baya qarya baya magana biyu.

Numfashi haj maryamah ta sauke tana kasa cewa komai sbd tarasa abin fada.

Dakin da zainab din take suka nufa tunda umma tasan dakin dasukazo tareda aqeel kafin wucewar tasa.

Koda sukaje tana kwance idanuwanta a rufe tana tunanin mijinta da 'yarta datazo ta zauna tsakiyar ranta,

Sam Bata qarar da hakan da yake zaunuwa Aran mahaifiyarsa ba sai yanzu data sake qararwa duk da har lokacin kaunar aqeel mai girma tana cikeda ran nata sai takejinsu su biyun sun cike mata zuciya tako Ina.

A tsawon shekarun datayi tana wankin wasu daga cikin kayan haj maryamah da gyaran dakinta tareda wankin toilet dinsa to tariga ta haddace qamshinta ras acikin hancinta Dan haka suna shogowa dakin tun kafin ta bude ido hancinta ya tabbatar mata da 'yar uwartace ta shigo.

Ahankali ta bude idanuwanta dasukai jajir a kumbure ta kallesu tareda sauke Kai tana sake gaida umma kafin ta gaida haj maryamah din.

Dukkaninsu kusan atare suka amsa gaisuwar sai haj maryamah data gyara tsayuwarta tana kallonta tayi mata gaisuwar rasuwar Mijinta kafin daga baya ta tambaya baby.

Amsawa zainab tayi tareda cewa ta gode Allah yabada ladan gaisuwar malam din.

Shiru sukai dukkaninsu saidai umma ce tafara maganar zainab din idan ansallameta taje gidanta tafara tattara kayanta tasan yanda zatayi dasu tukuna saita wuce can gidan haj maryamah din.

Gyada kai tayi kawai batareda ta iya bude Baki tai maganaba Dan batajin zata iya.

Basu wani jimaba suka tafi bayan haj maryamah din ta Ciro 10k daga handbag dinta ta ajiye mata a gefe na dubiyane ko sadaka ne tabata oho.

Bayan tafiyarsu tashi tayi ta nufi toilet din dakin tasake Dan kamo ruwa ta fito Takoma ta zauna tana zubawa 10k din da itace alkhairin farko dazatace Yar uwarta tayi mata na kudi dai.

Da daddare Saida aka Kuma zuwa aka matsa nononta still har lokacin ba komai dayake Acikin siyayyar da aka rubutawa Aqeel ya siyo harda Madara Kuma kaman yasani ya siyo musu da yawa.

Washe gari da yamma tayi tunanin Kiran aqeel din sbd tasan Kila ya Isa a time din, Tunaninta tsayawa yayi data tuno da batada waya yanzu tun rasuwar malam ta rasa wayar da rikicinta dasu umma.

Wani nannauyan numfashi ta sauke sbd shima Aqeel ya manta da batada wayar saiya nemeta yajita babu.

Sanyi jikinta Yakuma Yi sai kawai ta cire ran jinsa sai Randa Allah yabada iko.

****Cikin kwanaki hudu ita kam ta warke sumul batada ciwo ko damuwar komai a jikinta Dan haka hankalinta gabaki daya nakan 'yarta MARYAMAH da itama tana Dan samun kuzari da kulawa sosai Dan kuwa Aqeel babu abinda bai tanadarba ya biya kafin ya wuce din.

Baa kawo mata abinci daga gida Dan haka itace take siyan abincinta taci anan duk da nata jegon dakuma damuwar rashin miji duk yasa cikinta a bushe yake batason cin abincin, Wanda ma take nace tana siya tanaci sbd tanason tasamu Nononta ya taru MARYAMAH tasamu nono.

Wasu daga cikin maqotanta sunzo har asibitin sun dubata da yarta duk da baa bada babyn Kuma dazasuzo kusan duka sun kawo mata abici wasu kudi harda kunun haihuwa mai kyau suka kawo mata Tasha kuma taji dadinsa sbd ya taimaka mata gurin samun nonon Dan ajiyewa tai tana shansa kwana biyu kafin yaqare dayake dakin akwai fridge harma da heater ta ruwan zafi.

Samun ruwan Nononta yasa babynta tafara samun kuzari da lafiya sosai Dan haka takesan nono sosai gashi Daman ba laifi babyn tanada Dan girma kadan ba irin sosai takeda rashin girman Nan ba ko kadan.

Acan gidan haj maryamah kuwa umma sati daya tayi ta komawarta bayan tasake zuwa asibitin so daya kafin ta wuce.

Aqeel kuwa ya Isa lfy yanata kokarin fara karatunsa Amma yakasa samun Maminsa Yayiwa ummansa magana ta sanar dashi baa sallamosuba tukuna dole ya hakura harsu dawo gidan yasamu ko ummansa zata hadasa da mamin tasa a waya.

Haj maryamah kuwa tini ta tattara ta wuce Abuja itama kafin tawuce tazo asibitin ta sake dubata so daya taqara Bata wasu 10k din ta wucewarta bataredama zainab din tasan gari zata Bari ba.

Ahankali ahankali Saida zainab ta share kusan sati uku a asibitin kafin aka sallameta ta nufi gidanta da 'yarta.

Gidan yayi datti sosai dayake lokacin iska ne Dan haka dole ta goya Maryamah tafara aikin gyaran gidan.

Saidata gyare koina ta share ta wanke kafin ta fito ta samu yaro ya siyo gawayi ta Dora ruwan zafi tayi wanka tayiwa maryamah da aka koyo mata yanda zatayi mata daga asibitin.

Ruwan zafin Tasha da Lipton ta kwanta suka Dan samu bacci tana tashi maqotanta Wanda Basu samu zuwa asibitinba suka shigo sunatayi mata barka da qarin gaisuwar malam.

Da daddare Dole ta dafa shinkafa dayake akwai sauran abinci dasuke dashi.

Da manja taci shinkafar tasake Shan ruwan Lipton tagama sauran ayyukanta ta kwanta.

Washe gari ma haka ta wuni ita kadai a gidanta daga ita sai 'yarta dare yayi suka kwanta abinsu.

Haka ta runguma rayuwarta data 'yarta data zama sanyin idaniyarta Kuma sanyin zuciyarta, A yanzu duniyarta 'yarta itace babban abinda yake gabanta, Batada buri ko buqatan daya wuce inganta rayuwar yarta data warware abinta tayi mulmul sbd nono mai kyau da sauran madarar datake Bata wadda har lokacin sunada sauran kusan gwanwani biyu da Basu fasaba.

Aduk lokacinda tayi sallah iyayenta da Malam da Aqeel sune farko a adduarta da 'yarta kafin kanta,

Ayanxu wata rayuwa take gudanarwa ta kadaici da rashin kowa,

Batada wani farin ciki ko jin dadi 'yarta kawai take kalla taji qwarin gwiwa da farin cikin rayuwa,

Ba laifi tana hulfar arziki da maqotanta duk da babu Wanda ya taba zuwa yabata taimako ko tallafi daga cikin mutanen malam harna Aqeel Dan haka taci gaba da lallaba abubuwan datake dasu Shi abincinta tuni ya qare dole kayayyakin gidan ta tattara ta Saida tabar katifar kwanciyarsu kawai da kayan kitchen.

'yar sanaar Saida gawayi da kayan Miya tafara Amma mutane sun maida komai bashi take suke kwashe komai data kawo Amma bashi Qarshe Kuma wasu da yawa basa biya haka zataita yawon bin bashin kudin Amma basa bayarwa koyaushe da qaryar da zasu fada.

Babu inda sanaar taje komai ya karye aka rasa kudin gabaki daya Takoma tana kame kame.

Watanta uku da dawowa hayarsu ta qare masu gidan suka Bata notice dole tafara tunanin barin gidan.

Batada gurin zuwa, Batasan Ina zata da jinjirar 'ya ba gashi bazaso 'yarta tayi tashin garari ba.

Har notice yacika batada gurin zuwa,

Ana hakan ne Daren wata asabar wani mummunan tsautsayi ya sameta na shogowar qato gidanta Allah bai basa ikon yimata komaiba saidai fuskarta ta kumbura da irin Marin daya ringa zabga mata sbd taqi yarda yayi Mata komai Qarshe haka ya gudu bai samu damar lalata mutuncintaba haka itama Bata samu taga fuskarsaba.

Tunda take hankalinta bai taba tashi da tsoroba irin hakan Dan haka gari na wayewa takai maganar gurin Mai anguwa Amma qarshe dai haka mutuncinta ya zube babu wani takamaimai sheda ko tabbacin abinda ta fada din sbd kusan duka anguwar ansan juna Basuda samari duka dattijai ne da tsofi To tayaya take tunanin zasu yarda kowa da mutuncinsa zai shiga yayi irin hakan.

Qarshe hakuri aka Bata akan saidai daga wata anguwar aka shigo aka Mata hakan.

Wannan lamarin ya sake firgita tsayuwarta ta rasa inda zata saka kanta da 'yarta, Tsoron gidan da anguwar ma takeji kwata kwata Dan kuwa duka rayuwarta ko yanda ake fyade Bata saniba sai yanzu da hakan yaso faruwa da ita,

Ba kanta takejiba MARYAMAH dinta takeji tunda fyaden yanzu har yara qanana Ana yiwa,

Wannan tunanin ya toshe dukkanin wata basirarta da tunanin,...

Tunaninta kan rayuwarta na baya yakoma, Da wani abun yasamu 'yarta gwara taje tayita bauta har tsufa acan din.

Batada zabi, batada dabara, batada mafita tunda ko abin kanta batada dolenta ta juya ta fuskantar bayanta.

Littafan addini da Alqur'anan malam masallacin anguwarsu ta bada aka aje Dan masu karatu hakama siturunsa badawa tayi akaiwa dattijan anguwar kyauta Sauran kayan tarkacenta na kitchen saidawa tayi wasu Kuma ta bada sbd duk ba wasu kayan kirki bane.

Koda ta iso babban tsohuwar kurkukunta wato gidan haj maryamah Adam Asad babu kowa gidan sai masu gadin gidan biyu.

Dukkaninsu sun santa Dan haka babu Wanda ya hanata shiga saidai Basu bari ta qarasa cikiba dan koina a rufe yake Saida aka Kira Haj maryamah din tace abarta tashiga tukuna suka bata mukullan gidan.

Kai tsaye bayan ta bude koina inda tasan kanta a dah can takuma Kai kanta goye da 'yarta.

Babu inda baiyi wata irin quraba da datti a gidan,

Kallon kanta tayi taji hawayen baqin ciki na gangaro mata Dan kuwa tasan rayuwar data Bari ce tadawo Amma Kuma zata iya kowace irin wahalace akan MARYAMAH dinta tasamu rayuwa a natsatsen guri da rayuwa Mai kyau.

Babban aikinta na farko data fara komawa shine aikin shara..

Goya MARYAMAH tayi ta rufeta sbd qura tafara aikin shara da gyaran koina.

Har harabar gidan sai data share ta gyare koina tas tadawo ta gyara Mata dakin ta wanke toilet tukuna ta sauke Maryamah sukayi wanka tazo tayi sallah ta kwanta daqyar tana rintse idanuwanta sbd ciwon baya Dana kwankwaso mai qarfi daya taso Mata. ##MAMUH# #MARYAMAH AMAL IDON NERA #MARRIAGE/HOTLOVE #ZAINAB IDON NERA

*_ZAFAFA BIYAR_*

*RUMBUN K'AYA*🔥 Hafsat Rano

*DAUDAR GORA*🔥 Billyn Abdul

*IDON NERA*🔥 Mamuhgee

*A RUBUCE TAKE*🔥 Safiya huguma

*KI KULANI*🔥 Miss xoxo

Littafi daya---400 Biyu---600 Uku----800 Hudu-----1k Biyar din duka----1200

ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN

0022419171 Maryam sani Access bank

Shedarka ta 09033181070

MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪 *Ina yan uwa 'yan nijer?* *Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA biyu---650CFA uku----850CFA hudu----1050 CFA Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!* *Thanks for choosing us*🔥 *_Arewabooks@Mamuhgee_* 15 Babu komai na abinci a gidan tunda ba kowa Dan haka sai data fita ta siyo bread da lemu tasha takwanta ita kadai a qaton gidan Kamar mayya.

Kusan ko anan dinma a tsorace take, Tunda wancan lamarin ya faru da ita kowane dare a firgice take kwana rungume da MARYAMAH dinta.

Washe gari haka ta wuni zaune shiru Kamar hoto Sai yamma sosai saiga drivern gidan shafi'u yazo da kayan abinci masu yawa an zuba a store.

Koda aka kawo abincin harya kwana biyu Bata tababa sbd babu gas Kuma batason tabawa tunda ba cewa akaiba nata ne.

Kullum bread da lemu ko garinta take siyowa Tasha tayi renon yarta dare yayi su kwanta.

Sai datai sati biyu ahakan saiga haj maryamah din tadawo da masu aikinta har biyu, daya yarinya dayar Kuma dattijuwa.

Zuwansu yasa akayo refilling duka cylinders na gidan da gas aka kawo dole itace ta Dora girkin tunda sun iso a gajiye Kuma su din Basu taba zuwa Nan ba acan Abujan aka Samar Mata su dan haka a gidan Basu San koinaba da komai.

Dayake bata taba tsallake inda takeba taje bangaren Haj Maryamah sai ya zama bangaren nata yana buqatan gyara sosai.

Masu aikin nata ne sukai aikin gyara Mata koina a sashen nata suka wanke komai tareda gogewa suka kunna AC Ac dasu fridge da sauran kayan dayake aiki da wuta.

Abincin Haj Maryamah din data Gama ta Basu suka jera Mata a dining ita sai daga baya bayan ta tabbatarda tagama cin abinci da hutawa taje ta gaidata tana rungume da MARYAMAH dataqi bacci tanata rigima sbd aikin girkin dasukai sunsha zafi.

Kallon zainab Haj Maryamah din tayi dakyau kafin ta maida kallonta kan yarinyar daketa Kika duk ta ruda palon.

Kasa magana tayi sai kawai ta amsa gaisuwarta tareda sallamarta Dan kukan gabaki daya ya rudasu su dukan.

Zainab na fitowa daki ta nufa tayiwa MARYAMAH din wanka ta canja Mata kaya cikin kayanta dasuka fara Mata kadan sbd bayan kayanda Aqeel ya siya Mata batada wasu kayan gashi tanata girma.

Baya tayi Mata wanka bacci tayi sai kawai ta kwantar da ita ta fito taje ta gyare kitchen din data Gama aiki ta tattara komai tadawo daki itama tai wanka tayi sallah ta zauna tana kallon MARYAMAH dake bacci cikin nutsuwa da kwanciyar hankalin irin na yara.

Da daddare kasa nutsuwa da gyaran da shafa Mai aikinta tayi Mata Haj Maryamah tayi sbd akwai qura sosai Sam aikin baiyiba.

Fada sosai tayiwa shafa'atu din kafin qarshe tasa aka Kira zainab itace tayi Mata gyara Mai kyau dayasa hankalinta kwanciyar tasamu ta kwanta.

Washe gari zainab bata fitoba sbd batasan me zatayiba idan ta fito Babah ladi itace take aikin girkin gidan Shafa'atu Kuma tanata aikin shara da gyaran koina Dan haka saita Kama kanta a daki musamman dataga suna Mata kallon wulaqanci Dan daukarsu itama Mai aikince Gashi sunga an kushe gyaransu ansaka tayi sun dauka shiga tafisu samu agun hajiyar gidan basusan wulaqanta tafisuba.

Duk uban aikin dasuketa fama dashi kwana biyu babu Wanda Haj Maryamah ke yabawa sbd tsaurin raayinta da yai yawa,

Duk aikin dasuke Mata Dama acan Bata Jin dadinsa Kuma tana nunawa Koda yaushe Amma sbd su kadaine sai basa damuwa sunyi sabo da halinta shiyasa suka Dena damuwa, Amma anan duk aikin dasukai bayayi saita saka zainab tayi Mata wani sai hakan yasa sukejin daci da zafin zainab din a ransu,

Musamman babah ladi data fito fili ta bayyanarda rashin kaunar zainab din dake ranta, Ita shafa'atu tana Dan taqaitawa sbd MARYAMAH data shiga ranta Dan tana tsananin kaunar yara.

Girkin abincin gidan a hannun babah ladi yake Dan haka idan tagama kullum Dan kadan take bawa zainab haka zataci ko Bata koshiba zata Sha ruwa ta Kama kanta gashi tana shayarwa tana buqatan abinci sosoi gashi mukullin store a hannun babah din yake koyaushe da gayya take yawo dashi a jikinta duk inda zata.

Idan har tasamu taci abinci isashe yanda ya Kamata to itace tayiwa Haj Maryamah girki aranar dan bako yaushe haj maryamah din ke Jin Dadin abincin babah ba.

Shi gyaran bangarenta Kuma tuni yadawo kan zainab din da batason na shafa'atu Kuma tanada qarancin yarda shiyasa zainab kawai ke Mata gyaran daki taji hankalinta akwance da dukiyarta.

Bayan gyaran sashen Haj Maryamah harda abincinta yadawo kanta sai gashi kusan duka aikin gidan kadan ne basa kanta ga MARYAMAH da rigima sosai harma da qyuya Dan haka duk aikin dazatayi tana bayanta ko hannunta.

Ahakan suka fara Jan lokaci sosai suna wani irin mugun zama a gidan tsakaninta dasu babah..

'yarta MARYAMAH tayi wayo sosai harta iya zama da rarrafe Amma batasan kowaba bayan mahaifiyarta,

Bata sabu dasu babah ba Dan basa janta ajiki bare hajiyar gidan da iyakacinta da ita idone.

Aqeel kuwa yayi rokon, Yayi neman ummansa ta hadasa da mamin tasa Amma kullum uzuri take basa Har waya yace asiya abata Amma duk dai hakan bai samuba Amma tunda dai ta sanar dashi suna lafiya hakanma yasa hankalinsa ya kwanta.

Babbar matsalar da aka fara samu a gidan shine tsanar da ake nunawa 'yarta wadda ko sunanta basa Kira sbd sunan hajiyar gidan ne da hakan qarfi da yaji suke Kiran yarta da KE, kokuma 'YAR ZAINAB..wannan kalmar itace abinda yake sosa ran Zainba aduk lokacinda suka Kira MARYAMAH dinta da hakan,

Tana danne wannan lamarin ne matsala ta bullo tsakaninta da Haj Maryamah akan MARYAMAH din datake zuwa da ita gyaran bangarenta Dan yarinyar nata barna sosai.

Tun lamarin na dannuwa a ranta har abin yafara yimata yawa Dan kuwa kusan kowa a gidan kyarar Mata 'ya sukeyi.

Daga ita har yarta kamar wasu almajirai suke a gidan Dan kuwa kayansu na sakawa tuni suka mutu wasuma duk basa shigar MARYAMAH din Amma ahakn take saka Mata su tunda basuda wasu.

MARYAMAH sai datai kusan shekara biyu Ta yayeta sbd yarinyar itama yanayin rayuwar dasuke ciki yafara tabata, Sam yanzu batada walwala ko sakewa yarinyar, Duk da qarancinta tasan batada sakewa komai tayi na barna dukanta su babah da shafa'atu sukeyi tun zainab na kauda Kai har tayi magana sai abin ya zama fitina Dama babah mutuniyar banza ce gidan abinci a Tasha takeda Jin gida masu kudine zaa Kai yar aikin abinci ta rufe shagonta tazo ta karbi aikin shiyasa take tsula tsiyarta son ranta tunda Haj Maryamah din Bata wani zama ba ruwanta da Yan aiki gashi yanzu itace shugaban masu aikin gidan Dan haka take zuba tsiyarta son ranta.

Zainab rayuwa a gidan tafara yimata tsanani, Komai ya juye a rayuwar gidan ba kamar da ba, Idan zata sashen Haj Maryamah ta dena zuwa da MARYAMAH 'dinta sbd gudun fitinar dazata biyo baya idan tayi Mata wata barnar datafi fasa Mata laptop datayi ta aikinta.

Acan dinma idan tabarta kafin Takoma sai ta tadda bacin ran wani abun Duk tabi ta fige da masifar gidan da yanzu komai ya lalace mata,

MARYAMAH sbd tsangwama da kyarar datakesha yasa gabaki daya ta rasa walwala da kuzari tareda sakewa irinta yara, Idan har ba ajikin uwarta takeba Bata wani dogon motsi a gidan.

Wannan yasa itama zainab din ta tasa kuzarinta gabaki daya suka koma kamar Yan gudun hijirar gidan kullum suna daki kamar masu abin kunya.

Ana haka kwatsam Allah yayiwa mijin Haj Maryamah yace ta tattara tadawo Abuja gabaki daya.

Da farko shafa'atu aka fara sallama sbd idan Takoma Abuja Bata buqatar ya aiki da yawa sbd hutawa takeson Yi batason hayaniyarsu Dan can gidan baiyi girman wannan ba da bazakaji motsin masu aikinbama.

Ganin an sallami shafa'atu yasa hankalin babah tashi Dan ta fahimci zaiyi wuya a kori zainab duk da gata da 'ya da Bata barin tayi aiki dakyau.

Babban tashin hankalin farko data fara fuskanta akan tafiyar tasu Abuja shine Haj Maryamah data Kira umma akan zata Aika Mata da MARYAMAH Qarama acan Cameroon bazasu da ita Abujan ba.

Bugawar da zuciyar zainab tayi yasata dafa bango tana Dan bude idanuwanta dake Mata dishi dishi.

A gabanta umma da aka Kira Kai tsaye itama tace bazata iya riqon MARYAMAH dinba sbd tsufa yazo Mata Kuma dasuka riqe uwarta tun tana jinjira me ta saka musu dashi Banda butulci Dan haka ita ma wanna halin uwarta zatayi itakam bazata iyaba.

Haj Maryamah ma Kai tsaye ta nuna zainab bazataje da MARYAMAH dinba idan har umma bazata karbetaba to gwara zainab din ta nema dangin mahaifinta ta miqa musu ita.

Tunda zainab take Bata taba Jin daci da radadin zuciyaba akansu sai wannan karon,

'yarta ake ture turen inda zaa Kai kowa nacewa baya son saikace wani mugun abun, Me tayi musu da tsanar dasuke Mata zata shafa 'yarta hakan wadda batasan komaiba.

Tafiyar na matsowa umma ta Dage akan bazata karbi maryamah dinba,

Kukan da zainab tayi Saida takai idanuwanta ma basa gani sosai, Tayaya zata iya bada qanqanuwar marainiyar 'yarta har Cameroon itama taje ta taso Acikin qangi da wahala.

Kukan Rashi iyaye Dana Mijinta tayi tareda na Aqeel Wanda tuni ta cire Rai daga Kansa itada yarta.

Hada dukkanin tsumman kayanta tayi guri daya Dan tasan rigimarda zaayi idan tafada raayinta na bazata taba rabuwa da 'yartaba, Idan har Haj Maryamah zataje Abuja da ita to zataje da yarta,

Tasan hakan zai kawo rigima tunda ansaba takuma san ran kowa zai baci Amma bazata iya barin arabata da yartaba.

Rigimar kuwa akayi sosai tareda bacin rayika alokacinda ta sanarda Haj Maryamah bazata tafi bada MARYAMAH dintaba.

Umma ranta kusan yafi na Haj Maryamah din baci sbd mamaki da takaicin zainab take tafara jero Mata gorin irin rokon da Aqeel yayi musu akan su amsheta ta zauna gurinsa shine yanzu an zabar Mata rayuwar sauki da Jin Dadi zatace bazata rabu da yartaba, Ashe 'da yanada dadi shine ita ta raba haj Maryamah da nata Dan kullum cikin fada yake da mahaifiyarsa akanta.

Readers Also Read