Idon nera by mamuhgee Complete - Chapter 9
Idon nera by mamuhgee Complete Chapter 9: Idon nera by mamuhgee Complete Chapter 9. Lulu na cikin wannan Fadi tashin neman kudin Samar Mata gurin zama…
4,490 words
Lulu na cikin wannan Fadi tashin neman kudin Samar Mata gurin zama barayi suka shiga gidan DS suka kashe Mai gadinsa tareda yiwa 'yarsa daya fyade suka ko sata basuyuba suka gudu.
Babu tunanin komai akaiwa Lulu mummunan sharri akan da saka hannunsa a lamarin,
Ds da Kansa ya bada tabbacin Lulu ne kawai zai iya yimasa hakan Sbd fyaden kanwarsa yasa anyiwa shima tasa yar Kuma a ranar da abin zai faru kowa ya shaida fadan maigadin gidan DS da Lulu akan taron da Lulu yayi da jamaarsa har kofar gidan ds din mutanensa ne. ##MAMUH# #IDON NERA #AQEEL ASAD #LOVE/MARRIAGE
*_ZAFAFA BIYAR_*
*RUMBUN K'AYA*🔥 Hafsat Rano
*DAUDAR GORA*🔥 Billyn Abdul
*IDON NERA*🔥 Mamuhgee
*A RUBUCE TAKE*🔥 Safiya huguma
*KI KULANI*🔥 Miss xoxo
Littafi daya---400 Biyu---600 Uku----800 Hudu-----1k Biyar din duka----1200
ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN
0022419171 Maryam sani Access bank
Shedarka ta 09033181070
MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN
09166221261
🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪 *Ina yan uwa 'yan nijer?* *Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*
+22799643131
Littafi daya---450CFA biyu---650CFA uku----850CFA hudu----1050 CFA Biyar----1250CFA
*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!* *Thanks for choosing us*🔥
*_Arewabooks@Mamuhgee_* 18 Tunda Lulu yake baa taba Masa zargi ko sharri Mai girma da munin wannan ba, Kisa da fyade fa ake magana....
Innalillahi wainna ilayhi rajiun""" shine abinda zainab da siddi suke nanatawa cikin mafi girman tashin hankali lokacinda akayiwa Lulu mummunan kamu.
Gabaki daya jamaar anguwa kowa da abinda yake tofawa lamarin wasu alkhairi wasu sharri da mugun kalami.
Zainab ce da siddi suka fara yawon neman mafita Amma babu sai wahala da qara gurbacewa da lamarin keyi.
Tun lamarin na wasa harya girmama Dole suka nema lawyer da taimakon wani saurayin siddi..anan suka fara kashe kudi sbd case din babba ne sosai tunda kisa ake magana.
Zainab Bata ankaraba ta samu kanta dumu dumi a wani bangare na ruyuwa irin wannan ta kaida kawon cikin maza nagari da Bata gari,
Lulu shine Dan uwanta daya da bazata iya gani cikin wannan halin ba Dan haka itada siddi suka Dage dan ganin sun taimakesa alokacinda yakeda buqatan hakan.
Tun Ana iya ganin lulun har andena barinsu ganinsa,
Sannu ahankali komai da siddi ta mallaka yaqare Daman ita zainab batada komai sai nauyin restaurant din lulun daya dawo kanta sbd kallon uwa daya uba daya da ake musu ita dashi,
Tun suna iyawa harsunkai basa iyawa haka aka Saida restaurant dinsa da komai suka bada kudin Dan a fiddo lulun Amma babu sauki.
Komai na Lulu Saida aka Saida suka bada kudin Amma babu wani sauki sai agurin ubangiji.
Ds suka koma gurinsa roko da neman alfarmar akan case din.
Da farko kin kulasu yayi sbd tsanar dayayi a gansa da karuwai sbd tsoron abinda zai taba mutuncinsa da siyasarsa.
Daga baya Kuma dasuka ci gaba da roko da magiya akoda yaushe saiya nuna raayinsa akan zainab..
Kai tsaye ta sanar dashi ita din ba karuwa bace sbd kadama su batawa juna lokaci,
Siddi ce ta miqa Masa kanta a maimakon zainab din yayi abinda zaiyi da ita qarshe yaqi Yi musu abinda yace din saima kamasu daya saka Yan hisbah sukai akan suna bibiyarsa da mummunan dabiarsu akan ya asaki Dan uwansu...
Yayi musu hakan ne da a kamasu su ta yanda babu Mai sake kokarin tada maganar Lulu.
Hisbah ta kamasu tareda kaisu gidan gyara Hali na tsawon sati uku kafin aka sakosu,..zuwa wannan lokacin Lulu anriga an yanke Masa hukuncin zama gidan yari har ankaisa da hakan aka rufe case din.
Bayan fitowarsu wata muguwar qaddarar ta samesu ta bayyanar ciki a jikin siddi Wanda yake tabbas na DS ne,
Sun shiga tashin hankali da damuwa sbd siddi tai duk yanda zatayi cikin yaqi fita sai zainab tace ta hakura tabarshi tunda hakan Allah ya qaddaro.
Rayuwar zainab da sunanta sun Jima da lalacewa daga ranarda ta saka kafarta a anguwar,
Kowa da sunan karuwa yake kiranta Wanda ita masifar datake ciki Bata barinta Jin zafi ko takaicin sunan,
Babu ta yanda zata iya wanke kanta sbd ba yarda zaayiba, Wayema ya damu da mutuncinta da zata tsaya wanke kanta..
Rayuwarta data MARYAMAH ta sauya Babban burinta shine fitowar Lulu da saukar siddi data koma yau lafiya gobe ciwo,
A ayanxu da siddi Takoma cikin duk ya Gama lalatar da rayuwarta sbd tsananin ciwo da laulayi kala kala Zainab itace take dawainiyarsu,
Itace take karban kudin hayar kowane daki na gidan da karuwan ciki ke biya,
Itace take sanaar Saida kayan planning da siddi keyi a gidan harma da wasu abubuwa da karuwan gidan ke siya komai ya dawo kanta Duk tabi ta qara hargitsewa,
Siddi ta rayuwarta ta koma abin tausayi gabaki daya sbd cikin yazo da matsala sosai...
Zagi da zunde tareda bacin suna babu wanda baa musu akan ita ta Haifa shegiyar da baasan ubataba, Lulu ankamasa sbd yayi fyade da kisa, Siddi Kuma tayi shege lafiya ta gagareta.
Zainab dakejin irin wannan zagin da cin fuskar Bata damuwa sbd abinda yake gabansu yafi qarfin tsayawa biyewa zagin mutane.
Cikin siddi Yana fita wata takwas tafara zubar jini Tun Yana zuwa kadan kadan daga Baya yafara zuwa da yawa Hankalinsu ya tashi suka nufi asibiti.
Zuwansu asibiti yasa yanayin tsanananta nan hankalin Zainab ya tashi ta rasa was zata nema, Wa zata tinkara.
Jikin siddi tsanani yayi kuwa qarshe dai ta haifi 'ya mace itama saidai take ta rasu bayan haihuwar tata.
Rungume da 'ya cikin tashin hankali da firgici Mai tsanani zainab ta fito asibitin MARYAMAH na biyeda ita Cikin tsanani rikicewa take jefa qafafunta Bata ko gani sosai....
Innalillahi wainna ilayhi rajiun"" take furtawa a fili tana tafiya da jinjirar a hannu batamasan Ina ta nufaba tsabar tashin hankali.
Da magriba siddi din ta haihu kafin ishai ta rasu... Ga 'ya a hannunta yanzu inane makomarta da yara har biyu...
Bata ganin gabanta haka tabi hanya tana tafiya kamar mahaukaciya.
A daidai wani layi ta tsaya bayan tayi tafiya Mai tsayi ta durkusa a gurin tana neman kukan dake cikin zuciyarta ya fito Amma yakasa fitowa sai gurnani takeyi tana gunji...
Motar dazata shiga bakin gidan datake durqushene ta hasketa tareda danna Mata horn....
Shafi'u driver ne ya zubawa gurin idon cikin Dan mamaki yace,
"Haj Kamar Zainab ce a gabanmu.
Umma da Haj Maryamah dake bayan motar zaune suka dago lokaci daya suna kallonsa Umma ce ta iya cewa,
"Kace waye???
"Zainab dai ta Nan gida, matar marigayi malam sanda.
Tsit sukayi wuta ta dauke musu lokaci daya sbd zallan mamaki da firgicin abinda ya kawota gaban gidan kakannin mijin Haj Maryamah din,
Isowarsu garin kenan yau daga ita har umma sbd gaisuwar mahaifiyar Mijin Haj Maryamah din data rasu jiya.
Cikin sauri umma tace"
Shafi'u ka tabbatarda zainab ce kuwa?
Haj Maryamah datake tsananin kaunar mutuncinta da sunanta fiyeda komai Bata tsaya komaiba ta bude motar tafito dan bazata tsaya tambaya ba har wani ya fito yaga zainab din agurin asan sunada alaqa sunanta yabaci.
Turus ta tsaya batareda ta qarasaba tana kallon zainab din cikin shahararren mamaki da tsoro harma da wata irin qyama dake bayyane ganinta da sabon 'da a hannu dunkule Acikin zani.
Umma data fito motar tana tafiya ahankali sbd manyanci sosai daya kamata tsayawa tayi kallon abinda ke hannun Zainab din kafin a rude tace"
Ke,Meye haka? Daga Ina? Me kikeyi anan? Bibiyarta kikeyi ne? Meye wannan a hannunki? Wata haihuwar Kika sake Yi kenan?? Shi Dan daudun naki bai fada Miki baa haihuwa a bariki ba??? Me kikeso da kikazo Nan da wannan abin naki?
Me Maryamah tai Miki da kikeson Bata sunanta agun dangin Mijinta da mutanen dake ganin girmanta matuqa......
Haj Maryamah da baqin ciki Mai tsanani da tashin hankali sukai Mata yawa kasa magana tai ta dauke kallonta daga kallon Zainab din da yaranta biyu dake tareda ita,
Wace qaddarar ce wannan ace ubanta daya da karuwa Mai 'da Tabbacin ita Yar barikin ce kenan....
Muryarta kunshe da damuwa da zallan baqin ciki da damuwa tace"
Bayan kudin gadonki dake hannuna banajin akwai dalili ko alaqar dazata saka ki zo inda nake, Me kikeso? Kudin gadonki???
Mota ta juya ta dauko Jakarta tabude ta fiddo rafar 100k guda uku ta jefa Mata cikin tsananin bacin Rai da baqin cikin dake neman rufe zuciyarta tace"
Rayuwar da Kika zabarwa kanki da zuriarki kenan ko Zainab?? To kije kiyi rayuwar yanda kikeso saidai kada ki sake zuwa inda nake sbd har abada bazan taba iya kallon karuw.....
Kasa qarasa sunan tayi sbd baqin cikin fadarsa ma datakeyi...
Kije Zainab... Kije... Tashi kije....
Zainab data kasa dagowa ta kallesu sbd batasan ta ina suka diroba itama...
Sai alokacinda Haj Maryamah ta jefo Mata kudin ta dago ta kalleta idanuwanta na radadi da zafin kalaman 'yar uwarta.....
Magana zatayi umma ta katseta da cewa"
Idan kincika Yar halak dakiketa fada kotu to karki Kuma ambatar ko sunan Maryamah da 'danta bare zuwa inda suke sbd kin Riga kin lalata sunanki Dana zuriarki to karki lalata Mata nata....
Har abada babu abinda zai hada tsaftatacciyar rayuwarta da zuriarta da wainda suka qazanta rayuwarsu....... Zainab kin zama tamkar rubabbiyar rayuwa wadda zata lalata suna da mutuncin duk Wanda ya rabeta...
Allah yasa kada ki lalata rayuwar wainnan yayan naki Kamar yanda Kika lalata taki.......
Hawayen dataketa nema tsawon lokacin ne yau Allah yabasu ikon saukowa daga idanuwanta dasukai jajir...
Haj Maryamah take kallo da dukkanin Idanuwanta dake tsayayar hawaye sbd ayanxu tana ganin ita kadaice takeda alaqa da ita Dan itace jinin, Itace suka bada uba daya Amma umma batada alaqar komai da ita tunda Bata haifetaba Kamar yanda ta fada....
Hawaye sosai takeyi masu radadi daga zuciya, Kuka Mai qarfi ta fashe dashi agaban Haj Maryamah din wadda itama zuciyarta wani radadi da nauyin take Mata...
Share hawayenta tayi dukda sunkasa tsayawa ta dago takalli Yar uwarta Kuma yayarta Acikin wani irin sauti Mai bayyanarda tabbacin abinda zata fada tace,
"A yanda umma takira rayuwata da rubabbiyar rayuwar da zata lalata rayuwar Wanda ta raba Ayau Ina Miki alkawarin har abada bazaki sake ganin Zainab ba,.. Alaqar da kuka yanke Dani ayau Nima na yafe na yanke alaqa ta jini data zahiri dake, Kece jinina kece nakeda alaqa dake ba umma ba kema to ayau din na yanke kamar yanda Kika fada ba Ni bake har abada, Bani ba jininki, Bani ba zuriarki, Ayau har sunan mahaifinmu na yafe Miki daga yau ko sunan mahaifi daya bazaa sake kiranmu dashiba... Sunanki ma a bakina nayi alkawarin bazan sake fadarsaba har ranarda zan bar Miki duniyar na...
Wani mahaukacin Mari umma ta sakarwa Zainab din cikin tsananin fushi da takaici tareda bacin rai Mai tsanani tace,
"Basai kin nuna Mana cikarki Yar barikiba mun tabbatar tunda gashinan munga shaidar a hannunki,
Itace tafi kowa baqin ciki da takaicima idan kinkira sunanta ita da aka sakawa 'yarki sunanta........
Daga sakannin da nayi alqawarin yanke alaqar Nan a wannan lokacin na rufewa 'yata sunan..... Baniba ko Wanda bai sanniba bazai sake Kiran sunan 'yata wannan sunanba.......
Kudinsu dake qasa ta kalla kafin ta Kama hannun MARYAMAH tace,
"Kudin gado na Kuma na barwa Allah tintini.
Jan hannun yarta tayi suka bar gurin zuciyarta na wata irin zafi da tafarfasa.
Asibiti Takoma ta tadda gawar siddi na jiran Azo a dauka Dan Haka ta Kuma fitowa ta nufi gidansu tarasa was zata sanarwa haka tadawo asibitin ta sanar musu basuda kowa ayi janaizarta anan.
Gida tadawo tayi kwanan zaune, Zuciyarta zafi,qunci,radadi da hayaqi takeyi Mata.. Komai yasake juyawa Mata akaro na babu adadi..
Yaya zata fuskanci rayuwa da yara biyu bayan ita kanta haryanxu bata tsayarwa kantaba...
Washe gari acan asibitin akaiwa siddi komai aka Kai maqabarta saima data biya kudin mota dasu likafani.
Anan gidan take koina ya dauki labarin mutuwar siddi.
Madara ta siyo tana shayar da babyn wadda ta sakawa sunan mahaifiyarta wato siddiqa itama tana kiranta da siddi....
Sabuwar rayuwar jaruma Kuma tsayayyar mace ta budewa kanta sbd 'yayanta Wato MARYAMAH wadda ta sauyawa suna AMAL da Siddi..
Sanaoi da gwagwarmaya tafada gadan gadan Kuma Allah ya tallafa Mata sai gashi tanata tsayuwa da kanta.
Hausawa sukace zama da madaukin kwanwa..... Rayuwarta ta sauya sosai Dan kuwa ta tashi daga Zainab mai sanyin jiki Dana zuciya zuwa Zainab mai zafi da rashin daukan Reni.
Zama cikin karuwai da Yan bariki kala kala yasa idanuwanta budewa fiyeda su dinma Amma duk da hakan Bata taba aikata Zina ba.
Babban matakin nasarar data fara samu na taka Wanda ya takasu shine sonta da Ds ya fito ya nuna yanayi har lokacin baya Yana sane da mutuwar siddi sanadin haihuwar cikinda yasan shine yayi. ##MAMUH#
*_ZAFAFA BIYAR_*
*RUMBUN K'AYA*🔥 Hafsat Rano
*DAUDAR GORA*🔥 Billyn Abdul
*IDON NERA*🔥 Mamuhgee
*A RUBUCE TAKE*🔥 Safiya huguma
*KI KULANI*🔥 Miss xoxo
Littafi daya---400 Biyu---600 Uku----800 Hudu-----1k Biyar din duka----1200
ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN
0022419171 Maryam sani Access bank
Shedarka ta 09033181070
MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN
09166221261
🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪 *Ina yan uwa 'yan nijer?* *Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*
+22799643131
Littafi daya---450CFA biyu---650CFA uku----850CFA hudu----1050 CFA Biyar----1250CFA
*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!* *Thanks for choosing us*🔥
*_Arewabooks@Mamuhgee_* 19 Duk wata alamar kulawa Ds ya nunawa zainab sbd Zainab din yanzu daban take da zainab din dah kwata kwata,
Ta wanke tafito fes da ita duk da gwagwarmayar datakeyi Amma tana cikin rufin asiri sosai.,
AMAL da Siddi suna cikin lafiyayyar kulawa da kaunar mahaifiyar tasu,
Ta tsaya musu a komai babu abinda suka nema yafi karfinsu, Komai nasu iri daya take siya musu babu wani bambamci saidai babbancin kala sbd fatarsu ba daya ba, AMAL tafi siddi haske itakuma siddi tafita kaurin jiki..
Zuwa wannan lokacin kusan kowa ya manta da siddi ba zainab ce ta haifeta ba wainda ma basusan asalin waye mahaifiyar siddin ba sunfi yawa..
AMAL tana primary ita Kuma siddi tana nursery akai rikicin wata yarinya Qarama a anguwa da aka lalata abun babu Dadin ji da gani,
Zainab taji hankalinta yayi matuqar tashi akan yayanta,
A duniya yanzu data bude Ido tasan kanta da yanci to mutuncin 'yayanta shine abinda kawai yake Bata tsoro da girgizata, Bata kaunar ko sunan fyade taji sbd Su Amal dinta, Sbd sune taji zama acikin gidan da anguwar yane neman ficewa a ranta sbd tako Ina anguwar 'yan duniya da mutanen banza ne aciki uwa uba gidan nasu dasuke ciki duk da dokar Lulu na Nan Bata Bari ta lalaceba saima qarfi jajircewa datayi ta qarawa dokar karfi sbd 'yaya matane da ita.
Alhaji Bulama wani Dan kasuwa Kuma Dan siyasa shine ya nacewa buqatarta amma Sam taqi basa damar suyi lalata shiyasa yake sakar Mata kudi sosai Dan kawai ya samu sauya raayinta ta bashi Dama su huta..
A yanda ta Gama karance Shi tsaf ba sonta yakeyiba shaawarta yakeyi Mai tsanani itama Bata taba jin alamar zata so kowane namijin ba saidai shima tsabar nacinsa taqi yarda saiya bullo Mata da maganar aure...
Batayi mamaki ba hakama Bata Musawa aurenba Dan tana buqatan dauke 'yayanta daga gidan.
Auren akayi ta tare Dan babban gidansa dake kusada anguwar tasu take ta bude sabuwar rayuwa,
Bude hannuwanta tayi ta ringa qwaqwalar kudi a gurin alhaji Bulaman ba sassauci sbd tagama sani da gano auren shaawa yayi Mata Kuma Yana Gama cire shaawarsa sallamarta zaiyi Dan Haka itama ta rufe idonta ta ringa amsar kudade a hannunsa kafin tabari yai yanda yakeso da ita din.
Mugun zama sukayi na tsawon wata hudu kafin ya sakota,
Tasan zaayi hakan tunda ta gane manufar aurensa Dan Haka Bata damuba ta tattaro yayanta suka dawo gida bayan tasa anyiwa gidan babban gyara tareda fadada shi yakoma tamkar sabo Dan Haka kudin gidan ta qaru ga kowa.
Aurenta gidan Alhaji Bulama yasa idanuwanta suka sake budewa tas,
Tasake wankewa tas itama,
Daga ita har yayanta sun canja sunyi kyau da qarin lafiya abunsu,
Jikinta Mai kyau ne sbd batada qiba ko sakakken jiki Dan Haka saitayi fes fes abinta Kamar ba itace da yayan gabantab.
Ana cikin hakan babban tsautsayin Datafi tsoro a rayuwarta yaso afkawa siddinta Wato 'dan DS daya kusa lalata Mata ita,..
Maigadin gidan ne yaja siddin yakaiwa Suraj din sai gashi Allah yasa anga shigar siddin gidan akazo aka sanar Mata Hankali tashe jiki na rawa ta Isa.
Mummunan gani tayi alokacinda ta taradda siddinta tsaye gaban Suraj harya zare Mata wando....
Sumewa take neman Yi agurin saidai karfin da tafarfasar zuciyarta ya riqeta Jikinta na wani irin rawa ta qarasa da gudu ta fizgota daga gabansa Bata tsaya komaiba ta sauke Masa wasu irin mugayen marirrika guda biyar a jere kafin ta fidda wayarta ta dauki hotunansa..
Jikinta babu inda Baya rawa tace,
"Wannan shine karo na qarshe da wani daga zuriar DS ma zai Kuma kullon mace bare lalata, Alqawarine wannan nayi muku da yardar Allah.
Juyawa tai da yarta zata fito ya biyota da sauri shima jikinsa na rawa yafara rokonta akan zai Bata ko nawane kada zancen ya fita Ko mahaifinsa bayason yaji sbd zai iya komai idan yaji ya aikata abinda zai taba Masa mutuncinsa da muqaminsa...
Maigadin na ganin hakan yasan wasa ya 'baci Dan Haka ya miqe da sauri zai nufota A haukace tadauki sandarsa ta gora ta ringa dukansa ta koina tana musu ihu tana Kiran jamaa
Kafin kace me gidan yacika da mutane Ta rufe Ido tanata ihu da neman daukin sun lalata Mata yarinya...
Dayake DS ya Jima da barin gidan 'dan nasa ne kawai aciki Yana aikata Barnarsa kala kala da Yan Mata da shaye shaye Shikuma DS din da matarsa da sauran yaransa Mata da wancan Dan nasa daya da Lulu ya illata sun koma babban makeken gidansa dayafi wannan din so da Dama,
Kuma Daman sbd ya ringa lura dame basa barazana wato Lulu yasa ya zauna a anguwar To yanzu daya Gama da matsalar lulun saiya tashi daga anguwar Dama ba mutuncinsa bane zama anan din.
Wani irin mummunan duka zainab tayiwa maigadin dashi Kansa Suraj Wanda yasa Dole akai Kiran hukuma tazo ta kwashesu Itama tayi hakan ne Dan case din ya zama babba.
Ana zuwa gurin hukuma babu Bata lokaci yan anguwa suka bada shaidar abinda zainab ta fada Aka Kai yarinyar asibiti aka duba bai Kai ga yimata fyaden ba Amma dai hukunci yahau kansu dagashi har maigadi gashi dukansu suna asibitin sbd Shi maigadi har haqorinsa hudu ya rasa dan harda Yan anguwar aka taru aka rufar musu da shegen duka Mai muni.
Zance yanata yaduwa a duniya da social media take hankalin DS ya tashi yayi duk yanda zaiyi Amma zancen yariga ya yadu mutane idanma baayi adalciba zainab a shirye take da Kai zancen sama inda komai zai sake lalace masa..
Matar DS ta samu zainab har gidanta ta fada Mata maganganu masu daci da tozarci,
Takirata da karuwa, Mai 'yaya shegu Dan Haka kome akai musu ai ba fyade bane tunda sanaar uwarsu ce, Ta kirata da Mara asali Kuma zuriar Yan daudu...
Tayi kukan data manta Yaya akeyin kukan ma sai aranar, saidai Kuma aikine ya tashi Dan kuwa qudurinta akansu ma sauyawa yayi,
Ds yayita nemanta a sirrance akan tajanye case din taqi sai shima ya bullo Mata da maganar aure Dan yayi amfani da damar su janye case din sbd yazama babba lamarin.
Kamar yanda ko yanzu tasan cewan auren manufa ne zaiyi da ita itama saita sakawa ranta hukuntasu da manufar tasa.
Amincewa aurensa tayi sai gashi cikin qanqanin lokaci akayi auren Aka Kuma yada cewan sbd karamcinsa ya aure matarda 'dansa ya lalatawa 'ya shine abinda zaiyi ya kare mutuncin yarinyar da aka so lalatawar.
Hakan yasa mutuncinsa ya ringa qaruwa a idon mutane sai hakan ya ringa Masa Dadi musamman da zainab din ta fito ta nunawa duniya irin kulawa da kaunar dayake Mata itada 'yayanta...
Aikuwa hakan datake nunawa yasa DS sake mutuwa akanta da yayanta,
Matarsa Haj sadiya hankalinta mummunan tashi yayi ganin DS gabaki daya ya koma wani iri agun zainab, Ga Suraj din har lokacin Yana gidan yari zainab taqi ma yarda DS ya tasa zancen, Cikin salon daukar hankali ta nuna Masa abar Suraj din acan sai bayan zabe sai a fiddosa gudun yadawo ya lalata Masa komai tunda yanajin haushin an aureta din.
Aikuwa hakan akayi ds yabar maganar Suraj din akan sai angama zabe....
Sabuwar rayuwa zainab ta bude a gidan uban siddi batareda kowa yasan siddin DS ne ubantaba,
Kudi da Jin dadin rayuwa suke ja tako Ina hakama duk wani tattalin arzikinsa tanata janyewa tana tanadarwa 'yarta siddi Dan kuwa tayi alqawarin duk sai sunbiya abinda sukaiwa Lulu da marigayya siddi.
Koda aurenta da Ds yayi watanni Tara tagama tarwatsa gidansa Dan kuwa hatta matarsa Saida sukayi rabuwar kotu inda tun anan mutunsa yafara zubewa mutane,
Dan kuwa Haj sadiya cikin bacin Rai tonan asiri tai Masa Wanda zainab tayi amfani da hakan aka tada case din Lulu.
Tada case din Lulu yasa hankalin ds tashi haka zainab tasa ya ringa sakin kudi koina yanaso a sake rufe case din Amma baisaniba hakan yasake badashi da kuwa duka kudaden dayake badawa a banza suke tafiya....
Qanqanin lokaci rayuwarsa da iyalinsa tagama wargajewa Akai zaben Kuma bai ci aikuwa qaramar hauka ta taso Masa gadan gadan.....
Bai qarasa Aron haukaba sai ranarda zainab tayi winning case din Lulu akansa sai gashi Lulu ya fito.....
Qarar qarshe data kusan buga zuciyar DS itace qarar yayiwa siddi fyade hartasamu cikin yarta ta rasu gurin haihuwa.....
Binciken asibiti da kotu ta bayar ya tabbatarda siddi yarsa ce Dan Haka aka yanke Masa hukuncin bin dansa gidan yari shima.
Dukiya Mai tarin yawa tasamu daga da aurensa Dan Haka fitowar Lulu ta sauya musu rayuwa gabaki daya...
Lulu yai kukan ganinta tare dana mutuwar siddi,
Daga Shi har ita zaman anguwar data garin fita kansu yayi gabaki daya sbd a rayuwa bayan Rashi da baqin ciki Basu San komaiba....
Amma a yanzu dasuke da 'yaya gabansu bazasu sake barin quncin kowa ya illata rayuwarsu data 'yayansuba.
Qaton gidan DS dayake kusa dasu tuni ya mallaka Mata Shi da Ana zaman Dadi kafin ta fara tarwatsashi Dan Haka gidan Mahaifinta ya dawo Mata.
Da gidan da gidan Lulu suka hade tareda maidasa wani irin babban gida da shaguna a waje suka zuba yan haya....
Mutuwar aurenta da Ds babu abinda yaja Mata sa suna da farin jinin manya Dan Haka cikin qanqanin lokacin takuma wani auren sadai shima baifi watanni huduba suka rabu Wanda Shi yamafi ds din arzki Wanda ta aura daga bayan..
Yawan aurace auracenta yasa Ake Mata kirari da IDON NERA,
sunan yafara binta ne tun anan kafin suka tattara sukabar garin sanadiyar wani Mai kudin data aura ya kaita Lagos...
Zuwansu Lagos da wata shida shima auren ya lalace daganan sai Bata dawoba Lulu ya sameta acan suka bude babin wata baudaddiyar rayuwar zaman Kai da budewar ido....
Kamar yanda akace zaman gidan yari qarin course,,,to hakan ne ga Lulu sbd yanzu daya fitone yake asalin hamshaqin tantirin Kansa bare sun dawo Lagos sun sake zama fitsararru..
Gidan kansu ne dasu na masaukin duk wata Yar barikin data rasa gurin zama to suna tallafa Mata sbd sabo da zama da karuwai da sukai tun acan dasuma gararin dasukai anan karuwan ne suka karbesu da mutunci sai basa iya ganinsu Acikin garari....
Da farko Suma Lagos din sunsha tsananin wuya da garari kafin suka gane kanta suka fara gwagwarmaya da Fadi tashi Dan duk arzikinsu da zainab ta Tara Saida ya qare musu a yawon Haya da wahalhalu a garin kafin da Lulu yaga ta kwabe masu suna neman wulaqanta kudin cin abinci ma na neman gagarsu ya tsunduma harkar dillanci Mata da alhazai shine fa suka fara daidaita...
A wani babba gidan karuwai suke zaune wanda ya hada mutane sama da 40,
A gidan kowa karuwanci sukeyi shine sanaarsu, Ita Kuma zainab auren masu kudi shine nata, Suna nan suna karuwancin Basu Tara komaiba ita Kuma a aure biyu ta Tara wani irin arziki suka tattara suka koma sabon gidansu itada Lulu dasu Amal sai sabuwar Mai aikin datayi....
Sunan IDON NERA yayi sunane a aure auren manyan data ringa Yi a garin Wanda yaja Mata attention din mutane sbd zuwa lokacin manyan gaske take aura,
Asalinta da kowa ya sani shine karuwanci Wanda har lokacin Bata taba jin shaawa ko tunanin tsayawa ko so daya tace ita ba karuwar bace, Duk Wanda yaji ya fahimta ita karuwa ce to aje hakan Dan kuwa tai Nisan da saidai a fada a iya inda kake badai a fili ba.
Business sukeyi sosai Wanda shima ya karbu Kuma sunanta yasake habbaka sunan kasuwancin nasu,
Ta goge, Ta sauya, Takoma kamar ba uwar Yan Matan dasuka fara girma ba a gabanta,
Ta rufe idonta batajin komai Bata gane kowane yare saina NERA,
Shi kansa lulu baka ganesa Dan kuwa yakoma hamshaqin Dan daudunsa mai hulda da manya Dan kuwa shine asalin wanda yake kutsawa ya shiga ya fita ya samo Masu rumbun nerar da zainab ke aurewa.
Babbar kaunar dake tsakaninsu da karuwai baya sauyaba tana Nan dan haka gida garesu na musamman dasuke bawa karuwanda basuda mafita gurin zama wasu Kuma sune suke zama gatansu Ire iren wainda karuwancin bai Gama shigarsuba kenan... ##MAMUH# #HOTLOVE/AMAL IDON NERA #AQEEL ASAD
*_ZAFAFA BIYAR_*
*RUMBUN K'AYA*🔥 Hafsat Rano
*DAUDAR GORA*🔥 Billyn Abdul
*IDON NERA*🔥 Mamuhgee
*A RUBUCE TAKE*🔥 Safiya huguma
*KI KULANI*🔥 Miss xoxo
Littafi daya---400 Biyu---600 Uku----800 Hudu-----1k Biyar din duka----1200
ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN
0022419171 Maryam sani Access bank
Shedarka ta 09033181070
MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN
09166221261
🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪 *Ina yan uwa 'yan nijer?* *Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*
+22799643131
Littafi daya---450CFA biyu---650CFA uku----850CFA hudu----1050 CFA Biyar----1250CFA
*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!* *Thanks for choosing us*🔥
*_Arewabooks@Mamuhgee_* 20 Rayuwarsu a Lagos da gwagwarmaya da wahala suka Kai matsayinda suke a yanzu,
Mutane babu ruwansu da wahalarka,.da zufanka, da gwagwarmayarka, da dararrakun baqin cikinka Amma daga ranar da aka gano kuskure daya atareda Kai zaa fassaraka,zaa bika da zantukan gaskia da sabaninsu,hakam zaa bika da tsinuwa da kalamai maka mantansu,....
Daga ranar da aka haifi siddi ta gano hakan Kuma taji hakan daga gurin 'yar uwarta, jininta Dan Haka duk abinda duniya zata kirata dashi kokuma ake kiranta dashi Bata damuba sbd ko tace aa babu me shedarta......
Kowa Yana aikata kalar nasa laifi ko sabo tsakaninsa da ubangijinsa ne Dan Haka itama wannan shine nata laifin,
Ta zabi aurarrakin datakeyi ne akan karuwanci Wanda mutane suka kasa rabasa da karuwancin sbd abinda takeyi din karuwan ma sunason samun damar Yi Amma Basu samu ba Dan basuda kamar hajiya Lulu Wanda shine sanin manyan gwamnati na gida Dana waje....
'yayanta tuni akai musu tambari da sunan shegu basuda uba Dan babu wadda akasan ubanta acikinsu,
Taji ta gani takuma dauka saidai Kuma nerarta na sake zaunuwa Ana mantawa da yayanta shegu ne kamar yanda ake fada...
Ta badawa yaranta gata da Jin dadin da duk wani Mai uwa da uba zai nema,.