Kenza eBookz

Inaaya completed by mamuhgee - Chapter 1

Inaaya completed by mamuhgee - Chapter 1

Inaaya completed by mamuhgee Chapter 1: Inaaya completed by mamuhgee Chapter 1. S

4,489 words

S

*_ZAFAFA BIYAR_*

*_INAYAH_* _Mamuhgee_

*_GURBIN IDO_* _Huguma_

*_SANADIN LABARINA_* _Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_* _(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_* _Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_ *_Littafi biyu 400_* *_Littafi uku 500_* *_Littafi hudu 700_* *_Littafi biyar 1k_*

ZENITH BANK HAFSAT UMAR KABIR 2270637070

Shedar biya👇 07040727902

MTN card👇 09134848107 [10/26, 8:45 PM] Sweet sis: *_30_* *_Arewabooks@Mamuhgee_* Kusan da yawan jama'ar gurin Basu fahimci wane ABDULMAJEED din ake nufiba sai Amin kawai suke amsawa da ita suna qarawa da adduar zaman lafiya da albarkar aure sbd sunan Abdul din da aka ambata cikin sunan basu wani bambamceba tunda dai kowa yasan sunan Ango Abdul.

Iyayen Abdulsamad Wakilansa sune suka saki Ido da Baki cikin zallar mamaki da firgici Jin andaura da wani Abdul din daba nasuba Dan Babu Wanda ya tsaya kawo wani rubabben tunanin AA MAJEED mahaifinta ake nufi.

Shi kansa Abdulsamad kasa tantance meyake faruwa yayi saiyafara tunanin ko matsalar fadan sunan aka samu Mai fadar be kila ya rude ya fada sunan mahaifin Inayah a matsayin uba Kuma yadawo ya fada amatsayin Miki Wanda aka daura auren dashi.

Jin zuciyarsa dai takasa yarda sai tsinkewa data farayi yasashi kokarin baro Inda yake Dan zuwa gaban wakilan daurin auren yaji wane rudadden ne Mai sanarwar dazai saka kansa kuncewa da zancensa.

Kusan dai jama'a tsakani da Allah duk Basu ganeba idan ba wainda suke Yan uwan Abdulsamad ba sbd suka Sarai sunji ba sunan angonsu aka fadaba Sauran jama'a da Basu ganeba tunda ba hankali mutane ke badawa sosaiba gurin daurin aure sai an daura zu amsa da Amin da fatan Alkhairi su tafi Dan haka aka ringa gaggaisawa ana Allah sanya Alkhairi ana neman fara watsewa.

Ciki mamaki Mai tsanani da kokarin danne bacin Rai yayan Marigayi salisu ya kalli CM da Alhaji babbah kafin ya maida kallonsa kan AA yace"

Alhaji MAJEED mufa bamu gane abinda yake faruwaba anan, Auren da zaa daura biyu ne Daman kokuwa dai Wanda zamu daura dinne aka daura da wani 'dan ba namuba? Dan idan naji daidai sunan yarinyar dai shine wadda zaa daurawa danmu da ita.

Duk Inda damuwa da 'dacin Rai Dana zuciya suke sune a dabaibaye da A MAJEED, Bai taba samun kansa a yanayi Mai 'daci da qaqa nikayiba irin wannan Rana, Ko a wancan lokacin daya hadu da qaddarar samun Inayah baishiga damuwa da quncin dayake cikiba yanzu.

Me zaiyi da auren 'yarsa ta kansa? Wace mummunar masifa Hadiza ta sakasa daya qare qarshe a auren Inayah 'yarsa??

Innalillahi wainnan ilaihrrjiun, Yau shima yahadu da qaddarar Sharrin shedan Dana zafi da yanke hukunci cikin fushi.

Duniyama idan taji shine ya aura 'yarsa zai anyi Allah wadai da tunaninsa.

Gashi garin yanke hukunci kada Hadiza ta ra'bi Inayah har Inayah tasan bashine mahaifinta ba yaje cikin fushi da bacin Rai yayi abinda ba iya Inayah kadaiba da bayason ta taba sanin bashine ya haifetaba duniyama kowa zai sani yanzu Wanda harga Allah yaso riqeta amatsayin ya har abada batareda kowane Dan Adam yasan bashine ya haifetaba sbd daga lokacinda mahaifiyarsa datafi kowa saninsa da tarbiyarsa ta tuhumesa tareda yarda da zai iya aikata Zina harma ya Haihu a hanyar Zina yasaka a ransa ya karbi Inayah amatsayin 'ya dabazai taba barin wani yasan bashine ya haifetaba ciki kuwa harda mahaifiyarsa saigashi Rana tsaka Hadiza ta sakasa a mummunan tarko.

Hadiza itace masifar rayuwarsa yau ya tabbatarda hakan sbd akaro na biyu takuma sakasa masifar da kusan tafi ta baya yaqare da rataya igiyoyinsa na aure a wuyan 'yarsa baisan wane mummunan Al'amarin Zata Kuma kawo masaba a gaba Dan yasa zaifi wainnan zauta Kai da qwaqwalwa.

CM ne yayi saurin kallonsu Alhaji buhari ganin ransu yafara baci sosai sunason Jin bayanin abinda yake faruwa Dan haryanzu sunkasa yarda da auren matar 'dansu aka daura da wani sbd har lokacin Babu Wanda yakawo da AA MAJEED aka daura auren tunda ba abune Mai yiyuwaba uba ya aura 'yarsa Dan hakan kaf gurin Babu Wanda yakawo ABDULMAJEED mahaifinta ake nufi suma su CM da Alhaji babbah sunqi barinma agane wane ABDULMAJEED Dadi da qari kusan duniya da AA MAJEED tasansa bada cikakken sunansaba ABDULMAJEED ABDALLAH.

Cikin qarfin hali Abbin yataso Yana sallama da mutanensa dake wucewa suna Masa Allah ya sanyawa auren 'yarsa albarka Yana amsawa da amin.

Kaurewa da gurin yayi da jiniyar motocin 'yan sanda da civil defense ga yawan jama'a kowa nata kokarin miqa barkarsa ya wuce shiya taimakawa su CM gurin Jan su Alhaji buhari zuwa cikin gida palon Alhaji babbah Wanda shine da kansa ya iya fara tankwafarsu sbd fadan tozarci dasukagani qarara dasuka fara yi.

Alhaji buhari ne mai iya dan danne tsananin bacin ran dasuke ciki su Alhaji kabiru 'yan Nan Hadiza kuwa kasa dannewa sukai suka fara zuba masifar tashin hankali Dan duk Inda ake wulaqantawa an wulaqantasu ankuma tozartasu sun debo jiki tun daga adamawa sunzo Lagos daurin aure ace suna zaune suna kallo kaman wasu gumaka andaurawa amaryar aure da wani koma Dan uban waye ai Basu cancanta wannan tozarcinba.

Abdulsamad a rikice cikin tashin hankalin daya zaburo Masa tako Ina ya ringa kutsa jama'a Yana neman iyayensa maza dasune wakilan Amma Bai gansuba Dan haka ba Shiri ya zare hular kansa Yana Jin akwai gagarumar matsala Mai tsananin girman gaske kuwa.

Saida mutane suka rake sosai aka fara Ankara da abinda yafaru ganin rudewa da tashin hankali da Abdulsamad yake ciki da yawa wainda suka dauka sune basuji sunan daidaiba suka fahimci cewan daidai sukaji Ashe auren ne dai bada Dr Abdulsamad aka dauraba.

Take kurar hayaniya tafara kaurewa daga gurin Ganin Abdulsamad na Neman zarewa yasa Abbi daya Gama sallamar baqinsa ya Kama hannunsa sukai cikin babban gidan na Alhaji babbah.

Qanin CM Professor Ibrahim shine ya tsaya yaqarasa sallamar sauran jama'ar aka watse wasu nata sake sawa auren albarka wasu Kuma na shiga mamaki da son Jin yanda wannan mugun Al'amarin yafaru hakama wasu take suka ringa maimaitawa wainda basujiba cewan sunan fa AA MAJEED ne aka daura dashi. Mamaki da firgici wasu suka Kuma shiga Jin sunan Wanda aka daura dashi din aikuwa take tun anan suka fara shigar da gulmar Internet.

An watse tsaf ba kowa Dan hakan Alhaji babbah ya kalli su Alhaji buhari dake cikin mummunan yanayi na bacin Rai da fushi.

Cikin sanyi da taushin murya ga Wanda baa kyautawaba yace"

Alhaji buhari kuyi hakuri nasan baa kyauta mukuba tako Ina Musamman da baa sanar daku komaiba ko fahimtar daku komaiba Saida kukazo cikin baynar jama'a hakan tafaru.

Dr Abdulsamad dake tsiyayar wasu ruwan zufan tashin hankali da fita hayyaci ya kalla duk saiyaji jikinsa yayi sanyi da tausayin Abdulsamad din sbd duk Wanda ya kallesa yasan yana tsananin son Inayah so Mai tsanani,

Tayaya Za'a kallesa ace Masa uwarsu daya, Uban ne kawai Basu saniba ko dayane tunda A MAJEED cewa yayi uwar kawai yasani itama a bisaga qaddara.

Shi kansa Dr Abdul idanuwansa duka da hankalinsa suna kan Alhaji babbah sbd ya fahimci agurinsa zasuji abinda suke buqatan ji Wanda zuciyarsa ayau harbawar datake yasan ta wuce kowane irin tsari da akeson zuciyar Dan Adam ta buga.

Babu wani yaren dazai gane ayanzu idanba na maganar aurensa da Inayah bane.

Dan jinjina maganar dake bakinsa Alhaji babbah yiyi tareda dauke idanuwansa daga Abdul ya maida kan su Alhaji buhari dasuke manya zasu fahimtarsa a natse yace"

Ita wannan yarinya Inayah wadda mahaifiyar Abdulsamad ke Kira da Ayshatouh 'yar mahaifiyar Abdulsamad ce wadda ta jima da Bata tun jarinta Wanda A jiyan bayan haduwar mahaifin Inayah Wanda yanzu zance mijinta da ita mahaifiyar tasa suka tabbatarda Dr Abdulsamad da Inayah uwa dayace ta haifesu,

Dr Abdulsamad da Inayah uwarsu daya Kuma kaman yanda duk muka sani Babu aure tsakaninsu,

Sauyin Wanda aka daura dashi Kuma wannan nine Nan na tayasa yanke wannan hukuncin sbd kaman barazana da ita mahaifiyar yarinyar takeson tayiwa MAJEED Dan hakan muka yanke hukuncin ya aureta.

Dan haka a taqaice ABDULMAJEED shine ya aura AYSHATOUH INAYAH, Shine mijinta ayanzu, Sauran bayanin Inda ita mahaifiyar Dr ta samo yarinyar har suka Zama uwa daya da Dr wannan saidai aji daga gareta.

Wani mummunan shock da matsiyacin zufane ya fesowa Alhaji kabiru zuciyarsa na harbawa da mamaki ya juya ya kalli malam Umar Dan uwansa Wanda harya fisa jiqewa jagab da zufa.

Alhaji buhari daya Gama samun qullewar Kai da mamaki da Yar rudewa yace'

Inayah kuma Yar Hadiza? Tayaya? Garin Yaya? Yaushe?

Shaqewa muryar Alhaji kabiru tayi a Rikice murya na yankewa yace"

Inayah itace AYSHATOUH???? 'yar da Hadiza ta Haifa ranarda mahaifiyarmu ta rasu??

Da tashin hankali malam Umar ya karba da cewa"

Innalillahi wainnan ilaihrrjiun Tabbas Hadiza ta haifi 'ya takuma saka Mata Ayshatouh., Idan har ya tabbatarda Hadiza ce dimun wadda tabar Masa 'ya to tabbas kuwa wannan 'yar ta Hadiza ce halak malak sbd ranarda ta haifeta ranar tabar gida.

Sai alokacin zufa ta karyowa Alhaji buhari Jin dai ta tabbata Hadiza haihuwa tayi ba aure bayan rasuwar salisu.

Da sauri malam Umar daya fahimci tunanin dake zuciyar Alhaji buharin yace"

'yar Hadiza 'yar halak ce 'yar sunna Dan kuwa cikinda salisu yabarta dashine muma sai daga baya muka Ankara da hakan Dan haka 'ya 'yar halak ce Uwarsu daya ubansu daya da Abdulsamad gashinan zaun....." Ya qarasa fada Yana waiwayawa Inda Abdulsamad ke zaune sai kawai sukagansa zube baya numfashi da alama ya jima da sumewa Basu saniba sbd tashin hankalin da kowa yake ciki.

Arikice Alhaji buhari yayi kansa shida malam Umar suna Kiran sunansa Amma da alama ba sumar kadai yayiba kaman harda attack yasamu.

Innalillahi wainnan ilaihrrjiun""Alhaji buhari yake fada Yana kamo Abdulsamad din da qarfinsa Ba arziki Dole zaman bayanin yaqare sukai asibiti dashi hankali tashe.

Bayan fitarsu kallon Abbi Alhaji babbah yayi yana nazarin halin tsananin damuwar dayake ciki da rashin ta Ina zai Kama wannan rakitaccen Al'amarin.

Tausayinsa ne Dana Abdulsamad ma dayafi kowa tausayi yanzu Dan yasan Al'amarin zai daki yaron sosai sudai dama saukinsu da hamdalar dasuke shine da baa daura aurenba da komai yafi lalacewa uwa daya uba daya.

Bayason qarawa MAJEED damuwa da wasu zantukan Dan haka ya taqaita da cemasa,

"MAJEED kaje gida kasamu ka nutsa kanka ya sake kafin shima Abdulsamad asamu lafiyarsa saiku zauna duka kuyi taron fahimtar juna,

Itama yarinyar kada kace zaka kasa karban wannan qaddarar sbd ko ahakan Allah ikonsa ne ya nuna, Haisawa sukace matar mutum kabarinsa Allah yayi itace matarka shiyasa Bai baka ikon aureba tun kuruciya har gashi manyanci nason zuwa hakama rabon zamtowarta matarka ya hadaka da mahaifiyarta harta dawo hannunka dan ka tarbiyantar da matarka da kanka Dan haka shi Allah Babu ruwansa idan ya jarabta mutum to akwai tanadin dayayiwa wannan bawan idan har yayi tawakkali yacinye wannan jarabawar.

Allah yasa mudace, Allah Kuma yabaku zaman lafiya yasawa wannan auren albarka.

"Amin" CM ya amsa adduar ta Alhaji babbah Yana cewa"

Allah yaqara girma.

A natse MAJEED shima yayiwa Alhaji babban godia kafin suka fito.

Dayake da lafiyayyar Lexus din CM sukazo Dole shine ya maidasa gida.

Suna Isa gidan Yana ajiyesa harabar gidan yakira matansa yace kowaccensu ta fito su koma gida sbd yasan ba qaramar rigima zaayiba idan zancen auren ya Isa cikin gidan tunda duk matane bare ita kanta Inayah din Gwara idan zatai Rigimar ya Zama ba kowa a gidan. ##MAMUH# #LOVE/MARRIAGE/ROMANCE#

2270637070

Shedar biya👇 07040727902

MTN card👇 09134848107*_49_* *_Arewabooks@Mamuhgee_* Bai dauki wasu mintinaba ya Gama shima ya goge bakinsa da tissue tareda miqewa yabar dining din A natse cikin sautin Mara qarfi yace"

Saina dawo umma.

Umma yaganah ya dan kalla itama yace"

Saina dawo.

Kusan atare sukai Masa adduar adawo lfy.

Zaune Inayah take tana chatting sama sama da Neesah dake son Jin labari daga gareta tana ganin ya nufota tafara kokarin saka wayar cikin aljihun skinny jeans din dake jikinta da farar doguwar Riga Mara nauyi wadda gefenta yake yanke daga qasa har gurin qugunta.

Cinyoyinta da wandon ya lafewa ya Dan kalla Yana dauke kai kafin ya dakata daga shiga motar ya juyo cikin fada yace"

Kije kisa native wear.

Kallonsa tayi da sauri tana kallon kayan jikinta....

Me Kuma kayanta yayi?

Sake dagowa tayi ta kallesa taga harya shige motar Yana zaune Batace komaiba ta juya Takoma cikin gida ta sauya kayanta zuwa Riga da skirt na atampa dark green da qaramin medium chantley veil ta fito riqeda qaramar Chanel handbag.

Gaban motar ta bude tashiga suka wuce.

Suna fara tafiya ahankali ta juyo ta kallesa tareda marairaice fuska ta dafa dayan hannunsa dake gefen datake cikin wata sanyayyar muryar shagwabar data Saba yimasa tace"

Abbi idan nayi lefi Dan Allah kayi hakuri bazan sakeba.

Dan juyowa yayi ahankali ya kalleta da idanuwansa dake sake Jin hawayen shagwaba, Tace please Abbi Dan Allah bazan sakeba.

Hannunta ta qarasa dorawa kan hannunsa Ya Dan sake kallonta

Tana ganin ya kalleta ta gangaro da hawayen data Tara a Ido tana qara marairaice Masa.

Rintse idanuwa yayi ya bude ahankali Yana dauke kai daga kallonta....

Besan yaushe Inayah ta iya wainnan abubuwanba na saurin kuka yanzu Musamman idan tanason Abu daga garesa sbd tasan kukanta shine abu na karshe dazai so a duniya.

Ahankali ya sauke boyayyan numfashi cikin kulawa da sanyin lafazinsa yace"

Meyasa kike Wasa da abinci? Kina aikin lfy kice bakisan ciwo da dama suna shigaba ta hanyar yunwa?

Karna kumajin zaaci abinci kinbada different story daga yau. Okay?

Gyada Masa Kai tayi tana sake riqe hannunsa cikin nata.

Zare hannun zaiyi tasake riqewa tana cewa"

Nacefa bazan sakeba Abbi, Ahaka zamu qarasa ai ni matarkace yanzu Ab....

Wani mummunan burki yaja dasu akan hanya Saura kiris motar bayansu ta dakesu.

Kallonsa takeyi da mamaki batareda ta damu da abinda tafadaba cikin kulawa tace"

Are you okay Abbi?

Juyowa kadan yayi Yana zuba Mata manyan fararen idanuwansa dasuka sata Jin gabanta faduwa a Karo na farko sbd Abbin nata Bai taba zuba Mata idoba sosai Yana kallonta.

Koyaushe kallonsa akanta taqaitaccene duk da tsananin kaunar da son dayake Mata amatsayin ubanta.

Sunkuyar da kanta tayi ahankali Jin kallon yayi Mata nauyi da karfi ahankali tace"

Sorry Abbi.

Hannunsa dake cikin nata ya janye ahankali batareda yace komaiba ya ja motar suka wuce.

Shiru bakinta yayi sbd tasan ta zaro zancen da umma ke cewa idan batada abin fada ta ringa yin shiru Dan haka tayi shiru Amma Kuma ai Dagaske shi mijintane kodai Abbinta baya Sonta kenan da auren???

Innalillahi wainnan ilaihrrjiun" ta furta a fili tareda dagowa ta kallesa tana Jin kaman hankalinta zai tashi da wannan tunanin.

Har suka Isa asibitin Babu Wanda yasake magana Yana parking motar Dr Abdul na shigowa harabar asibitin.

Fitowa Inayah tayi tana kallon motar Dr Abdul din kafin tadawo da kallonta kan Abbinta.

Bai lurada Hadiza ba dake cikin motar ya sauke glass din motarsa Yana amsa gaisuwar Dr Abdul daya iso cikin girmamawa kaman da can Yana gaidasa.

Ba tsammani sai ganin hadiza yayi tana qarasowa gurinsa.

Inayah ya juya ya kalla itama shi take kallo batareda ta kalli Inda Hadiza ke tahowaba.

Hadiza na isowa cikin Jin kunya da nauyinsa Mai tsanani ta Dan kallesa a sanyaye tace"

Ina kwana Abbin Inayah.

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_* _MamuhGee_

*_GURBIN IDO_* _Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_* _Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_* _(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_* _Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_ *_Littafi biyu 400_* *_Littafi uku 500_* *_Littafi hudu 700_* *_Littafi biyar 1k_*

ZENITH BANK HAFSAT UMAR KABIR 2270637070

Shedar biya👇 07040727902

MTN card👇 09134848107[11/8, 9:55 AM] Sweet sis: *_ ashiru badamasi

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_* _MamuhGee_

*_GURBIN IDO_* _Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_* _Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_* _(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_* _Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_ *_Littafi biyu 400_* *_Littafi uku 500_* *_Littafi hudu 700_* *_Littafi biyar 1k_*

ZENITH BANK HAFSAT UMAR KABIR 2270637070

Shedar biya👇 07040727902

MTN card👇 09134848107 [11/8, 9:55 AM] Sweet sis: *_51_* *_Arewabooks@Mamuhgee_* Qin wucewa tayi bedroom dinta tabi bayan Abbi Wanda baisan tana bayansa ba Saida yashiga palonsa taji mutum a bayansa Yana juyowa suka hade Saura kadan ta Fadi ya tarota ta dawo jininsa.

Shiru tayi tana kallon kyakkyawar fuskarsa dayake kokarin hanawa karban kowane yanayi.

Cikin nutsuwa ya zareta Yana cewa"

Meyake damunki ne kwanakin Nan Inayah?

Murmushi tasake tana kamo hannunsa bayan ya zauna itama ta zauna gefensa tareda shige Masa sosai tana cewa"

Abbi Ni bansaniba ko nayi lefi yanzu ka daina ji Dani kaman da,.

Ko Dan Haj umma Bata Sona ne?....

Wani kallo ya juyo yayi Mata da idanuwansa dasuka Dan sauya cikin Dan fada yace"

Karki Kuma cewa haka, Ki Dena hada matsayinki Dana ummana kowa matsayinsa daban...karna sake Jin hakan a bakinki.

Ahankali tace"

Sorry Abbi na dena Amma Abbi ai zaka barni a matsayin matarka ko?????.....

Rintse idanuwansa yayi da wani irin yanayi na mamaki da fara kosawa da zancen Yaushe Inayah ta Zama haka akan aurene Bai saniba? Bude idanuwan yayi tareda juyowa ya zuba Mata su gabaki daya Yana kallon bakinta da yayi maganar zuwa kirjinta dake harbawa da sama sbd fargabar zancenta Mara control daya sake fitowa bakinta ba Shiri.

Farare idanuwanta dake kallonsa cikeda kauna Mai girma ya maida NASA idanuwan Yana kalla....

Hannunsa dake cikin nata takuma kamawa tana kallonsa a sanyaye.

Kasa cewa komai yayi Yana kokawa da tunanika dake yawo akansa Yana kokarin kwantarda kansa.

Ahankali ta furta sunansa cikin wata kasalalliyar murya wadda ta sanya tsigar jikinsa tashi sbd numfashi Mai dumi data furzo a fuskarsa bayan Kiran sunan nasa.

Ganin har lokacin baice komaiba sai idanuwansa Daya dauke ahankali daga kanta Yana maidawa kan tv Dake kunne.

Ahankali cikin seta murya yace"

Haryanzu maganar aure Bata fita bakinkiba Inayah.

Yanda yayi magana da wata shaqaqqiyar murya yasa jikinta mutuwa itama ta kwantar da kanta a kan hannunsa tana cewa"

Abbi Ni naka auren kawai nakeso yanzu ai.

Sake danne numfashinsa yayi Yana basarwa.

Sosai tayita yimasa fira wadda duka yawanci shagwabane ta ringa zuba Masa wadda tagama take neman lalata kamewarsa da wuce tunaninsa akan yanda Inayah din take abubuwan dabaisan a Ina tasaniba.

Tana tafiya dakinta ya miqe ya nufi toilet din bedroom dinsa Kai tsaye ya sakarwa kansa ruwan dumi Yana lumshe idanuwansa dasuka sauya Yana sake riqe kansa da kamewa.

Ita Kam tana komawa daki sallar ishai tayi zuciyarta cikeda farin cikin yau tayi fira da Abbinta kaman da Tayi Shirin bacci ta haye gado tayi kwanciyarta tana jin yanayi Mai qarfi fa girma a zuciyarta gameda Abbinta Wanda takejin yanafin na dah.

Washe gari fes ta shirya cikin haricca long knitted skirt and blouse milk sai vincci loafers ta fito ta wuce aiki Bayan taje ta gaida Haj umma Umma yaganah Kuma tare sukai breakfast Abbinta Kuma Bai fitoba da alama Bai tashiba.

Agurin aiki yau ma umma Hadiza tazo sunyi fira sosai kafin tadawo gida.

Tun a harabar gidan tasan anty Hafsat tazo sbd taga motar CM daya.

Batai tsammanin samun harda dr farhataba a gidan Dan haka duk fitarta da Anty Hafsat Basu wani samu sinyiba gashi Haj umma ta cika kowa da kulawarta akan Dr farhat wadda itama sosai take nuna Jin dadin hakan Dan tasan tagama samun guri a gun AA MAJEED.

Har dare Basu samu sunyi maganaba yanda ya kamata saidai sama sama anty Hafsat din tasake nanata Mata akan itace Zata gyara aurenta yazama kaman kowanne aure da kanta.

Bayan tafiyar anty Hafsat da Dr farhat rasa abin kamawa tayi saidai ta shiririce gurin waya da Neesah wadda suka qarasa shiriricewa akan firarrakinsu na Yan Mata yanda suka Saba.

Sallar ishai tayi ta fito zuwa dakin umma yaganah sbd sunci abinci already tun dazu taredasu Anty Hafsat.

Tana Shiga dakin zubbi tace"

Abincin Sir yazama ready zaa aje a dining ne kokuma zaa kai Masa dakin Haj umma? Ko a palonsa zaa Kai?

Kallon Inayah umma yaganah tayi daga zaune tace"

Kije ki Kai Masa palonsa basai an jera a dining ba.

Fitowa tayi tareda zubbi batareda taje dakinta ta sauya kayaba ta dauki qaramin tray din da tea ne akai sai faten dankali dayaSha kayan ciki da curry.

Kai tsaye palonsa ta nufa da tray din tana shakkar kada abbin yayi Mata fadan kayan jikinsa sbd akwai sanyi gashi Riga da wandon baccine ajikinta masu santsi Kuma wandon ba har qasa bane ko bra Babu ajikinta.

Tana shiga palon sanyin AC daya Gama gauraya da turarensa ta shaqa tareda nufan table ta ajiye tray din tana dagowa Yana fitowa daga bedroom dinsa sanyeda pyjamas shima fuskarsa tayi fresh kaman baya Shiga Rana.

Akan kayan jikinta idanuwansa suka fara sauka ya dauke Kai Yana qarasowa ya zauna.

Zama tayi gabansa tana daukar tea din ta miqa Masa tana cewa"

Abbi barka da da fitowa.

Numfashi yafara saukewa ahankali kafin ya dago ya kalleta tareda sakin taqaitaccen murmushi yace"

Barka Dr Inayah majeed.

Dadi taji sosai ta taso daga gabansa ta dawo gefensa kusa dashi sosai tareda dafa cinyarsa Saura kadan ya qware da tea din dake bakinsa tayi saurin janye hannunta tana kallonsa Dan itama batasan a cinyarsa ta Dora hannunba.

Daqyar ya hadiye Wanda ya kurba a bakinsa tareda juyowa ya kalleta idanuwansa na gangarawa ga bakinta dake motsi tanason yin magana Amma takasa sbd idanuwansa dake Neman rudar da ita.

Qamshinta ya shaqa ahankali tareda Dan rufe Ido ya bude Yana ajiye cup din hannunsa ya juyo gabaki daya Yana kallonta Magana yakeson yin Amma qamshinta yayi Masa yawanda yake kokawa da nutsuwarsa ya hadiye numfashi ahankali zai bude Baki yace ta tafi tayi saurin Kai hannunta kan bakinsa ta rufe sbd tasan korata zaiyi....

Saukar tafin hannunta Mai taushi akan bakinsa yasashi rufe idanuwansa dasuka sauya ya bude ya watsa Mata idon numfashinta na shiga hancinsa tareda qamshinta Kai tsaye Wanda yasa numfashinsa Dan sauyawa.

Janye hannunta yayi Kai tsaye Yana fuskewa tareda daukan cup dinsa yakai bakinsa Yana kurba a natse yace"

Kije ki saka kayan sanyi ki kwanta akwai sanyi yau.

Zuciyarta dake bugawa da qarfi ta dafa da sauri tareda kallon gurin tana Jin yanda bugun zuciyarta ke qaruwa.

Juyowa yayi ahankali ya kalleta Jin Bata motsaba Yaga hannunta kan kirjinta dayaketa kaucewa kalla sbd yanayin datake ciki....

Sosai tsatsayyun kirjinta suka nuna basa batareda bra sbd yanda suke motsawa kadan cikin santsin rigarta.

Kaman Mara lafiya ya dauke Ido daga kanta yakasa tambayarta lafiyarta data dafe kirji sai kawai a hankali yace"

Kije ki sauya kafin sanyi ya kamaki.

Bata musaba ta miqe ta nufi kofa ta fice sbd bugawar da kirjinta yakeyi yasata Shiga fargaba da tunanin itakuma.

Tana fitowa Palo suka hadu da Haj umma data fito daga dakin umma yaganah dubota da ciwon kan datace tana Dan ji tun yamma.

Da boyayyan mamaki take kallon Inayah wadda ke tafiya a sanyaye hankalinta baya ma kan Haj umma din Dan Bata lura da itaba.

Kai tsaye dakinta ta wuce tareda fadawa kan gado tana shigewa bargo ta lumshe ido tanajin sabon feeling Mai qarfi akan Abbinta.

Daqyar tayi bacci da daren Dan haka tayi lattin tashi...

Shima Abbi ranar baisamu wani bacci ba Dan haka tunda safe ya shirya ya fice sbd zuciyarsa dake buqatan iskan da Babu Qamshin Turaren 'yarsa ko kansa zai sake.

Da wuri Inayah ta dawo Dan kawai tasamu fira da Abbinta Amma Bai dawo da wuri ba Qarshema ranar sai dare yadawo Bayan sunyita jiransa itada Haj umma Amma sai kusan 10 yadawo Kuma Kai tsaye yayi musu Saida safe ya shige sbd Yana tareda gajiya.

Haka Inayah taqi tafiya daki saida ta dafa tea takai Masa tareda cake Mara zaqi sosai sbd Sam bayason zaqi ko kadan.

Haj umma na kallo Inayah taje palon nasa Kuma ta dauki mintuna sosai kafin ta fito Wanda itakuma tsayawa tayi yafito daga bedroom Amma tayita jira Bai fitoba Dan haka ta tahowarta ta wuce daki jikinta a sanyaye.

Washe gari haka abbin yakuma fitar safe Bai tsaya breakfast ba Kuma Bai dawoba sai dare yauma.

Washe gari ma hakance takuma faruwa tun abin na Wasa saigashi Abbi ya rage zaman gida Sam Baya Zama he's always busy Sam yaqi bawa kowannensu time sbd Haj umma tafara tunkararsa da maganar Dr farhat Wanda Inayah Bata saniba batada labari Umma yaganah ce kawai tasani Kuma taqi barin Inayah taji zancen sbd rigimarta.

Hankalin Inayah tashi yayi fiyeda komai, Rashin lokacinsu daga Abbinta yasata sukukucewa ta daga hankalinta sbd tsoron ko tayi wani lefin ne tunda itama tasan bataji.

Haj umma ma tashi hankalinta yayi tashiga damuwa tareda Dora lefin akan Inayah tayi masa lefi ne shiyasa yake cikin damuwa Dan kuwa damuwa ta nuna sosai akan fuskarsa.

Jin Abbinta na cikin damuwa yasa hankalinta ninkuwa atashi Dena fita aiki sosai tana Neman hanyar zaunawa da Abbin tabasa hakuri.

A bangare Daya pressure din da Haj umma ke basa akan ya aura Dr farhat yasa ciwon Kai Mai tsanani kamasa qarshe ya Dena fita sbd Yana buqatan kansa ya sake sosai.

Ga Inayah duk yanda taso ta kusantoshi bayaso yanzu sbd matsalar da hakan ke basa Itakuma ganin hakan saita rikice da damuwa sbd bayason tana zuwa gurinsa sosai.

Dr farhat ce tazo daga gidansu ta dubasa sbd ciwon kan ya tsananta Masa.

Rashin bacci ne da damuwa yake damunsa abinda yafadawa Haj umma.

Hakan kuwa yasa Haj umma yanke shawaran aurawa majeed din Dr farhat Kai tsaye sbd yasamu Mai kulawa dashi,

'danta yana buqatan kulawar mace Wadda Zata sakasa farin ciki tabasa kwanciyar hankali Kuma bataga hakan atareda Inayah ba wadda bayan shagwaba datake zuba Masa Babu abinda Zata iya Dan haka bazata zuba Ido 'danta ya mutu abanzaba ko jikiki Bata samuba.

Anty juwairiyyah takira tanayiwa wannan bayanin akan harta Kira qanin abbansu MAJEED din zaa saka lokaci a je Neman auren.

Umma yaganah damuwa da nata tashin hankalin tashiga Jin hukuncin Haj umma din Wanda Kuma Babu Mai iya takesa tunda itace uwar MAJEED Bayan shi Babu Mai iya tsallake wannan zartarwar.

Hafsat takira a waya tace tazo tana nemanta sbd Dole sufara shawarar yanda Inayah zataji wannan mugun labarin.

Abinda Bata saniba shine MAJEED din ya amince kokuwa? sbd batai maganar dashiba Kuma shima baizo yamataba.

Inayah na asibiti anty Hafsat tazo cikeda damuwa sbd umman tafara Mata bayani a waya shiyasa batazoba Saida ta tabbarda Inayah na asibiti.

Tagumi suka rafka dukkaninsu biyun cikin dakin umma Bayan umma yaganah tagama yimata bayanin abinda yake faruwa ta Dora da cewa"

Hafsat ki kokarta ki sake nutsar da ita tasan abinda takeyi Dan kuwa kishiya da qananun shekarun Nan nata da sangantar datake basune zasu fiddataba Duk kuwa da tsananin son da MAJEED ke Mata idan ya auri wata macen yasamu nutsuwa a gurinta bazata sake gane komaiba.

Numfashi anty Hafsat ta sauke cikin takaici da damuwar maganar tace"

Umma Inshallah Inayah bazata taba wulaqanta a hannun AA ba saidai Zan dage na sake lurar da ita abinda yake gabanta..Amma dai yanzu inaga kada abari tasan Abbin aure zaiyi kusa.......

Inayah dake bakin kofar shigowa dasuka Bari a bude Zata shigo A Rikice qafafunta na rawa tace"

Aure Kuma?

##MAMUH# #HOT/LOVE/ROMANCE #MAJEED& INAYAH

_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_* _MamuhGee_

*_GURBIN IDO_* _Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_* _Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_* _(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_* _Billyn Abdul_

Readers Also Read