Ja'jirtacce complete - Chapter 9
Ja'jirtacce complete Chapter 9: Ja'jirtacce complete Chapter 9. Ganin hakan yasa Momy juyowa ga Amar wanda yake a sandare cikin wani yanayi. "Amar ina…
4,430 words
Ganin hakan yasa Momy juyowa ga Amar wanda yake a sandare cikin wani yanayi. "Amar ina hankalinka yake da har zaka bar Safeenah ta ɗauko mota bayan ka tabbatar bata kware ba, yanzu da ace a hanya ne wani mummunan hatsari ya auku ya zamu yi?" ya rasa taya zai fara yiwa Momy bayani domin shi kan shi bai san dalilinta na yin hakan ba. "wlh Momy ban sani ba, ni kaina sai neman ta nayi na rasa shi yasa na dawo gida hankali tashe." ya juya gareta yana shirin janyo ta jikinsa yana faɗin "me yasa kika yi haka kanwata, waya ta6a min ke?"
Da karfi ta kwace jikinta ta koma cikin jikin Momy tareda tsananta kukanta. Iya da Momy sai rarrashin ta suke Amar kuwa wani sabon tashin hankalin ne ya same shi domin tunda yake Safeenah bata ta6a yi masa kwatankwacin hakan ba. "Ace da kansa yana junta tana kwarewa?" Momy ma dai mamakin ne ya kamata domin ganin sabon lamarin da bata ta6a gani ba. Ta kalli Iya tace "iya ki je gurin Dr. Kice ya zo yarinya ta farka." dattijuwar ta amsa da "to" ta tashi ta fita. A hankali Momy ta ɗaga Feena a jikinta ta gyara mata zamanta tana kallon ta sai Kuka take taki tayi shuru haka Amar ma ganin ya yi ta yi mata magana ta kyale shi, ga kuma fisgewar da take idan ya rikota kawai sai shima ya fashe da kuka.
Momy Yusra hankalinka ya tashi ta rasa wa zata rarrasa a cikin su duk wanda ta yiwa magana ba ya shiru sai Kuka suke kamar wasu kananan yara.
*Nasmat* ✍ [12/16/2017, 11:19 AM] Yar'mutan Arkilla ✍: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
........... *JA'JIRTACCE*....... *43*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _____________________________________ We are here to educate motivate and entertain our readers. _____________________________________
© Yar'mutan Arkilla✍ ____________
"Wai meye haka ne?" ta faɗa a tsawace cikin ɗaga murya da nuna 6acin rai. Sannan ta ci gaba da magana "haukata ni kuke so kuyi, akan me zaku saka ni gaba Kuna kuka y, me aka yi muku." ganin 6acin ran Momy yasa duk suka yi tsit! Shiru ne ya ratsa ɗakin na wasu dakiku babu wanda yayi yunkurin yin magana a cikin su kowa da abinda yake sakawa a ransa. Suna cikin wannan halin likita ya shigo tareda Iya da Dady wanda zuwansa kenan. Sun yi mamakin ganin sa tunda ba gaya masa suka yi ba, shine ya gaya mata ai da dawowar shi Mudi ya gaya masa, yayi takaitacciyar maganar ne idonshi akan Feena. "sannu Safeenah" da kai ta amsa masa domin yadda take ji ba zata iya magana ba, likitan ya duba ta tareda yi mata yan'tambayoyi shima dai bai sami amsar ko ɗaya ba. Momy ta bashi hakuri ta gaya masa fushin Amar ne ya shafe shi domin ta lura shine ya ta6a Feena." likita yayi murmushi bayan yan gajerun rubuce-rubuce ya bawa Dady takardar yana cewa "magungunan da zata bukata ne, a saya mata su Allah ya baki lafiya Feena." ya karkare yana mata murmushi yayi musu sallama ya fita.
"Dady ya ce to ai sai ku tashi mu tafi." ganin yanayin Amar yasa Momy tace bata yarda tayi tuki ba sai dai driver ya kai mishi motar gida sannan shima ya dawo ya ɗauki tashi motar. Su kuma zasu tafi a motar Dady. Nan fa aka shiga wata sabuwar drama, domin Feena karuwa tayi kai da fata ba zata shiga mota ɗaya da Amar ba. Tun Iyayen na ɗaukar abin wasa har suka tabbata da gaske take, tun Dady na rarrashin ta har ya dawo ya 6ata rai ya tubure mata da faɗa abinda bai ta6a yi mata ba, ita kuwa sai kara fashewa da kuku tayi tana buga kafarta da kasa bisa dole ta buɗe bayan motar ta shiga inda ta tarar da Amar yana ta kuka domin shi tuni ya daɗe da shiga.
Dady ya zaga ya shiga mazaunin driver bayan ya buɗewa Momy gidan gaba ta shiga. Ya tashi motar ranshi a 6ace suka kama hanyar gida. Ba Amar ba ba Feena ba duk sun cika motar da koke-koke ba daɗin ji sai tashin hankali. Basu koma ce musu komai ba suka dukkan su suka kyale su.
Da isar su gidan kamar jira take da tsayar motar ta falle kofar ta fita da gudu ta shige gidan kai tsaye ɗakinta ta nufa ta faɗa bisa gadonta ta koma rushewa da wani sabon kukan
Har ga Allah kukan da taga Yayanta yana yi ciwo yake mata sai dai bazata iya saurarar shi ba tunda har yafi son wata a kanta, bayan da ita kaɗai yake kula da ita.
Amar kuwa dakyar ya fito daga motar yana matsar kwalla ya wuce ciki kaman baya son ɗaga kafarsa. Iyayen suka bishi da kallon tausayi, sannan suma suka rufa masa baya da shigar shi ɗakinsa ya nufa, shima dai kwanciyar yayi yana mai cigaba da kuka tareda zurfafa tunanin neman dalili ko laifin da yayiwa Feena da har bata son ganin sa.
Nan da nan zazza6i ya rufe shi kafin kace me jikinsa ya fara makyarkyata, dakyar ya iya jan blanket ya rufe jikinsa da yake jin saukar sanyi kamar wanda ake zubawa ruwan sanyi a jiki. Kamar mintuna goma da kwanciyar sa Momy ta turo kofar ɗakin ta shigo da sallama. Sam baya iya amsa mata domin yana nan rufe da mayafin jikinsa sai kyarma yake yana karkarwa. Gabanta yayi mummunar faɗuwa da sauri-sauri gudu-gudu ta isa gare shi tana kiran sunansa "Amar! Amar! Me ya same ka?" cikin in-ina da rawar murya yace "Banida lafiya Momy, Feena ta tsane ni sam bata son ganina bata bukatar zama kusa da ni, karshena ne kawai yazo Momy na san mutuwa zan yi." da sauri ta rufe bakinsa da tafin hannunta ta fashe da kuka sannan ta juya da gudu ta fice daga ɗakin.
Amar yaja numfashi dakyar ya furzar muryarshi na rawa yake sambatu "kar ki yi min haka kanwata, zan mutu koda ba kiyi kewata ba ni zanyi kewar ki koda ba kiyi kukan rashi na ba ni zan yi kukan rashin ki. Ina kaunar ki Safeenah kin riga kin zama gudun jini na idan babu Ke jinin zai daina gudana, dan Allah ki zo gareni zo amanar Ummata." yana cikin wannan halin ne suka shigo ɗakin Momy da Dady harma da Safeenar wadda Momy taje ta gaya mata ga Yayanta can zai mutu saboda rashin kula shin da tayi. Da gudu ta faɗa jikin sa tana kuka "Yaya dan Allah ka tashi, idan ka tafi nima zan bika ka tashi Yayana wlh na bari bazan koma ba." zumbur ya mike jin wadda ke magana kuma take kan shi. Bai jira komai ba ya yakice bargon ya rungume ta.
Suka kankame juna suna maida numfashi domin kowannen su yaji a jikinsa, sun tabbatar wa kansu cewa ɗaya ba zai iya rayuwa babu ɗaya ba. Kuka take sosai tana ta6a kumatunsa "Yaya zazza6i ne ya kama ka? Momy dan Allah ki bashi maganin zazza6i."
Dady ya girgiza kai ya juya yana faɗin idan yasha maganin ke da shi Ku same ni ɗaki ina son ganin ku." Momy kuwa juyawa tayi ta fita dan ɗauko masa magani har zuwa lokacin suna nan rungume da junan su sun kasa rabewa ji suke kamar in suka rabu ba zasu koma haɗuwa ba.
Cikin hakan nan yake raɗa mata "dan Allah kar ki koma gudana kinji kanwata." "bazan koma ba yaya, wlh bazan koma ba bana so wani abu ya same ka."
"Dakin kyautawa kanki, ɗaga shi yasha magani." Momy ce mai maganar cikin murmushi...
*Nasmat* ✍ [1/7, 8:05 PM] Yar'mutan Arkilla ✍: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
........... *JA'JIRTACCE*....... *44*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _____________________________________ Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร. _____________________________________
© Yar'mutan Arkilla✍ ____________
📚 Zaku iya samun littafan mu a Facebook 👇🏽 Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION
📩 Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu 👇🏽 Zamaniwriterassociation@gmail.com
A hankali Feena ta sake shi suka dai-daita zamansu bisa gadon, ta kar6i maganin daga hannun Momy ta ba shi. Ba musu ya kar6a ya sha, dama maganin a 6alle yake.
"Sannu yaya." ta faɗa tana kallon fuskarshi. Murmushi yayi mata sannan ya mike yana karasa yaye mayafin da ya rufu da shi, ya kama hannunta itama ya mikar da ita bayan ya sauko daga kan gadon yana faɗin "muje muji kiran Dady ko?" Momy ta riga su ficewa daga ɗakin itan ma ɗakin Dady ta nufa suka rufa mata baya.
Zaune yake yana nazari akan wannan sabon lamarin da basu ta6a gani ba, tunda yaran suke basu ta6a samun sa6ani makamancin wannan ba, kome ya haddasa hakan?. Dai-dai nan yaji sallamar matarshi Yusra ya amsa sallamar tareda ɗago kansa. Ganin yaran a bayanta yasa ya 6oye murmushinsa, ya ɗan haɗa fuska tareda juyar da kansa gefe. Abinda yasa yaran suka kara shan jinin jikinsu kenan, domin tunda suke basu ta6a ganin wannan sauyin a tattare da shi ba.
Haka suka karasa jiki a sanyaye suka zauna gefen shi akan carpet, kawunan su sunkuye a kasa. Momy kuwa a kujerar dake gefen daman shi ta zauna.
Amar ne yayi karfin halin cewa "Dady gamu mun zo." yayi maganar ne dan ganin Dadyn yayi kamar bai san da shigowar tasu ba. Ya gyaɗa kai yana faɗin "na ganku" ya tattara kallonsa ya mayar kan Feena babu wasa ko alamar ta ya ce "ina son sanin dalilin da yasa kika baro Amar kika ɗauko mota ke kaɗai kuma cikin tashin hankali me ya faru, me aka yo miki?" Safeenah tai narai-narai da ido sai hawaye ta riga tasan Dady ta kuma san yadda ya tsani a mishi karya kanta na sunkuye a kasa ta fara share kwalla "kayi hakuri Dady bazan sake ba." idonsa a kanta yace "amsar tambayar da nayi miki kenan?" "a'a Dady" "to tambayar ce batada amsa kika maye gurbin ta da wannan?" tayi shiru shima bai koma cewa komai ba sai ido da ya tsare ta da su. Amar ma ita yake kallo domin har yanzu baisan dalilin da yasa ta aikata hakan ba bai kuma san dalilinta na yin fushi da shi ba, tabbas yaji daɗin wannan tambayar kuma shima yana so yaji amsar da zata bayar.
Momy ma ita take kallo cikin ina-ina ta fara magana "dama..dama shine..."
Nan ta kwashe duk abinda ya sanyata fushin ta gaya musu. Dady da Momy kamar zasu yi dariya musamman a kalmar ta ta karshe inda take cewa "tun daga ranar idan aka fito baya kula ni sosai sai dai su ke6e shida Jidda su yi ta hira ni kuma su bar ni ni kaɗai."
Dady ya kalle ta dariya kunshe a bakinsa yace "wannan shine dalilin da kika tashi kashe kanki a kan sa?" ta gyaɗa kai tana share kwalla. Dady yau shiru yana nazarin halin kurciya irin na Safeenah. Shi kuwa Amar tuni ya shiga wata sabuwar damuwar zullumi da tsoro suka baibaye shi, cewa yake a zuciyarshi "kar fa in zamo sila na tarwatsa 'amanar Ummana', babu shakka ban kyauta ba." a fili kuwa hawaye ne sharkaf a kan fuskar shi ya tashi daga zaunen da yake ya tsuguna a gabanta suna kallon juna. Ganin yadda take Kuka ya kara razana shi sai yaji gaba ɗaya ya tsani Jidda a lokaci ɗaya ta fita rayuwarshi.
Yasa hannayensa ya tallabo kumatunta ta ɗago kanta tana kallon shi sannan ya fara magana "ki yi hakuri Feena tabbas nayi kuskure sam ban kyauta miki ba, amma dan Allah ki yafe min kanwata. Idan nayi miki laifi ki yi mini kowane irin hukunci amma pls kar ki koma yunkurin hallaka kanki, koda duka na zaki yi ki dake ni ke ki min komai ma amma dan Allah karki yi abinda zai shafi rayuwarki. Feena ke amana ta ce dan Allah kar ki koma cutar da kan ki a kaina Umma bazata ji daɗi ba kin ji Feena na." yana maganar hawaye na bin kuncin sa "daga wannan ranar na bar Jidda har abada babu ni babu ita, zan ci gaba da baki kulawa kin ji kanwata." kalaman Amar suka sun ratsa zuciyarta tausayinshi ya lullu6e ta ta fashe da kuka ta rungume shi tana faɗin "na gode yayana, nasan ba zaka koma yin nisa da ni ba."
Momy ce ta gyara zama cike da mamakin wannan kuruciyar wato shi ɗin ma yarantar bata gama fitar sa ba. Ta kalli Dady wanda shima mamaki ne fall zuciyarshi. "Wannan wane irin hauka kenan Amar?, yanzu saboda bata so kayi nisa da ita yasa zaka bar budurwar taka? Me hakan yake nufi?."
Amar ya ɗago da jajayen idonsa yace "ba haka bane Momy Jidda tana da laifi sosai kusan ma ince kamar da gan-gan take saka ni yin wasu abubuwa dan kanwata taji haushi. Sau tari sai ta nuna tana jin haushin yadda nake kula da Feena wanda nikam bazan ɗauka ba."
"kenan bazaka koma son wata mace ba?" Dady ne ya wurgo masa wannan tambayar. "yai murmushi zan so mana Dady, sai dai bazan koma amincewa da wata macen ba har sai ta amince da Feena a matsayin kanwa ta kuma so ta kamar yadda nake son ta, taso abinda take so ta kuma guji abinda bata so. Wannan shi ne doka akan duk wata macen da zan koma so nan gaba."
Yana kaiwa nan a zancensa ya muke tsaye hannunsa rike da na kanwarsa suka fice. Dady da Momy kam kasa magana suka yi ko shakka babu sun san abinda ya faɗa shi yake nufi kuma zai aikata.
*Nasmat* ✍ [1/10, 1:57 PM] Yar'mutan Arkilla ✍: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
........... *JA'JIRTACCE*....... *45*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _____________________________________ Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร. _____________________________________
© Yar'mutan Arkilla✍ ____________
📚 Zaku iya samun littafan mu a Facebook 👇🏽 Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION
📩 Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu 👇🏽 Zamaniwriterassociation@gmail.com
"Amar!" aka dakatar da shi a ɗan tsawa ce. Jin muryar Dady yasa ya juyo tareda dawowa ya tsuguna a gabansa Feena ma hakan tayi kasancewar hannunta na rike a nashi. Dukkan su shiru suka yi suna sauraren abinda zai fito daga bakinsa. "Abinda kake shirin aikatawa kuskure ne, ko ba dan kai ba saboda ita. Shin baka san daga yanzu zuwa kowane lokaci ba wani zai aure ta?, taya kake tunanin zata zauna da shi a inda babu kai in har tun yanzu baka koyar da ita ba?. Kai yaro ne Amar Safeenah da kake gani bakuwa ce a gidan wani zata rayu ba zamu dauwama da ita ba. Ko kuma kai a tunanin ka da akwai wata macen da zata amince maka da waɗannan sharuɗɗan daka gindaya akan kanwarka?."
Amar yayi shiru jikinsa yayi sanyi kalau musamman da ya ji maganar wata rana za'a aurar da Feena wanda tabbas ya san haka ne. Hawaye suka fara bin kuncisa "na sani Dady na san zata za'a aurar da ita kuma in Allah ya yarda zata zauna musamman idan muka aurar da ita ga wanda take so. Da sauri ta ɗago kai ganin yayanta na kuka itama sai ta fara kukan "a'a Dady ni ba zan yi aure ba, anan zan ci gaba da zama da ku da kuma yayana zan rika taya Momy da matar yaya aikin gida."
Momy ce ta kalle su ta girgiza kai kafin tace ku tashi ku tafi. Suka mike suka fice kowannen su na sharar kwalla.
Hjiy Yusra ta kalli mijinta tace "habibi wlh ni tunda nake ban ta6a ganin yan'uwan da suke son junan su kamar Amar da Feena ba. Rayuwarsu tana burge ni amma yanzu sun fara bani tausayi." Alhj ya kalle ta da mamaki "tausayi kuma?" ya tambaya "eh" ta bashi amsa a takaice tana share kwalla a idonta. "babu wanda yasan sirrin yaran nan sama da ni, nice na rene su ni nasan komai game da su, ko shakka babu lokaci yayi da dukakkanin su zasu sha bakar wahala."
Dady ya kalle ta da sauri "wannan wace irin magana ce Yusra?" "maganar gaskiya ce Alhj sai dai kawai mu taya su da addu'a amma muddin aka aurar da ɗayan su za'a sha fama musamman ita Feena da take mace ɗaukar ta za'a yi a kai ta wani guri."
Alhj ya sauke numfashi domin ya gano inda maganar matar tasa ta nufa abinda ta faɗa gaskiya ne sai dai su dage da addu'ar neman sauki daga Allah.
Amar da Feena kam suna fita garden suka nufa a can suka baje suna ja'jantawa juna abinda ya faru, yana bata hakuri tana bashi yana mata alkawura itama tana mishi wanda duk dai akan kula da ita ne da kuma yin duk abinda take so.
Haka rayuwarsu ta ci gaba da gudana. Kamar yada ya kudurta a ransa tun daga ranar ya bar Jidda da shirginta tayi waya tayi aike tayi zuwa da kanta duk a banza. Karshen ta ma har gurin Momy ta zo kamun kafa amma ba'a dace ba Momyn kanta hakuri ta bata dan bata san yadda zata yi ta tilasta Amar ya so ta ba.
Bisa dole ta bar shi ba dan ranta na so ba.
Tun daga lokacin ya fara gwagwarmaya da rayuwa, ga karatu ga takurar da Dady yake masa akan lallai ya fito da mata ya masa aure domin su a ganin su kasancewar shi da Safeenah a koda yaushe shi ne ya hana ita ma ta samu saurayi ko mijin aure. Sai dai abinda basu sani ba shi ne ko a school masoyanta ba zasu kirgu ba. Ita ɗin ce dai bata basu fuska balle su sami damar furta mata abinda ke ran su. Hujjarta kuwa ita ce bata son aure tunda ta ji ance idan aka aurar da ita ɗaukar ta za'a yi a kai ta gidan wani har ma ana cewa zata rabu da kowa harda yayanta wannan kenan.
Duk wata budurwar da ya fara nema da zarar ya je da Feena ya gabatar da ita da kuma dokokinsa akan ta sai lamarin ya lallace, wasu yan'matan har bakaken maganganu suke ya6a masa. Haka zaka gansu kullum indai aka je da Feena gun budurwa to da Kuka take dawowa. Abin yana damun ta sosai ganin yayan nata ya gagara samun macen da zata so shi ta so kanwarsa.
Momy kam nata ido ne, domin bata san wani abin yi da wuce addu'a ba.
(ni kuwa Nasmat cewa nayi "kuruci dangin hauka" lolz)
*************************************
Yau gidan Alhj Tijjani Wakkala an tashi cikin farin ciki da kuma jimami domin safiyar yau ta kama ranar zagayowar shekarar haihuwar 6atacciyar yar su wato (Baby). Bikin da basu ta6a tsallake shekara ba'a yi shi ba. Sai Shirye-shirye suke an gama gyare gidan tsab. Momy da Dady su tafi ɗauko Ummy da yan rakiyar ta airport. Amar kuwa yana can da masu decoration suna karasa gyara ɗakin na Baby inda ake gudanar da birthdayn. Feena kuwa tuni ta gama shirin ta cikin haɗaɗɗiyar gwon ɗinta red color gashi nan yasha gyara an tufke shi guri ɗaya an ɗaure shi da wani tafkeken band shima red ne haka takalmin dake kafarta da pos dinta ma red color ne. Budurwar ta fito shar da ita, a hankali ta taka zuwa gaban mudubi kai kace ɗanyen fure ne ke rausayawa. Tsayuwa tayi tana karewa kanta kallo kafin daga bisani ta saki wani lallausan murmushi, ita kanta ta San ta haɗu.
Cikin zumuɗi ta juya ta nufi ɗakin yayanta, ta shiga da sanɗa tana waige-waige kamar 6arauniya ta buɗe wardrobe ɗinsa sannan ta tsuguna can kasa ta lalubo ɗaurin sarka nan da yace Umma ta bata ita.
Wani irin daɗi da farin ciki ne suka lullu6e ta a lokacin da idonta suka yi arba da rantsatstsiyar sarkar zinarin, mai tsananin haske da sheki. Hannunta har rawa yake gurin sakawa tun kan yayanta ya gani tana tsoro kar ya hana ta sakawa. Sai da ta gama saka sarkar sannan ta matsa gaban madubinsa ta kalli kanta, duk da cewa sarkar ta ɗan matse wuyanta hakan bai hana bayyanar kyawun da sarkar tayi mata ba. Ta zauna ɗas! Sai taji tunda take saka sarka ma bata ta6a saka wadda ta ka6e ta kamar wannan ba. Ta ɗora hannunta bisa sarkar tareda lumshe idonta, a fili ta shiga kwararowa Ummanta addu'ar neman rahmar Allah da jin kansa.
"Ameen ya Allahu" ta ji an amsa addu'arta a bayan ta. Da sauri ta buɗe idonta. Karf! Ta sauke su a nashi, Amar ne jingine da kofar ɗakin ya harɗe hannayensa fuskarsa ɗauke da murmushi. "Kin yi kyau kanwata." ya faɗa a sanyaye. Murmushin ta mayar masa tana kallon sarkar tace "kayi hakuri Yayana naga kamar baka so in saka kyautar Umma." da sauri ya girgiza kai "ni na isa?, wannan fa ba kyauta Umma ta baki ba, taki ce ta kanki inji Umma." ta kalle shi cikin rashin fahimta. Da sauri ya dawo hayyacinsa ya kuma fahimci su6ul da bakan da yayi. Sai yayi hanzarin kawar da maganar da cewa "zan shiga wanka, fiddo min kayan da zan saka." ya shige bayin da sauri.
*Nasmat* ✍ [1/10, 5:30 PM] Yar'mutan Arkilla ✍: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
........... *JA'JIRTACCE*....... *46*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* _____________________________________ Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร. _____________________________________
© Yar'mutan Arkilla✍ ____________
📚 Zaku iya samun littafan mu a Facebook 👇🏽 Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION
📩 Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu 👇🏽 Zamaniwriterassociation@gmail.com
Murmushi tayi tana kallon kofar toilet ɗin kafin ta girgiza kai ta nufi wardrobe. Kayan da zai saka yau sababbi ne na musamman suka siyo kamar yadda suke yi a kowace shekara. Tana cikin fesawa kayan turare ne taji tsayuwar motoci a harabar gidan na su, hakan ne ya tabbatar mata da isowar bakinsu. Wato Ummy da tawagarta. Da gudu ta fice daga ɗakin ta nufi harabar gidan tana tsalle da ihun murna zataga yar tsohuwa Ummy kamar yadda take kiran ta, dattijuwar da take ji da kaunarta har cikin ranta.
Ummy ma ta kagu taga Safeenarta hakan yasa ta saki fara'a a lokacin da ta hango ta ta nufo inda suke da murna. Ummy ta saki hannun jikinta Sagir ta rungume Feena cike da farin cikin ganin ta. "Oh wannan yar' haka kika kara nauyi? To sake ni kar ki yadda ni." inji Ummy cikin raha da wasa. Feena tayi dariya tana ko'karin raba jikinta da na Ummy tana faɗin "naci beta ne, kin san fa Momy da Dady ba karamin daɗi suke bani ba..." ciwon da taji a wuyanta ne ya hana ta karasa maganar cikin daɗi, sai ta karashe da faɗin "...wash!" tana rike wuyanta. Ummy tayi gaggawar rike ta a jikinta dan kar ta ji ciwo saboda sarkar wuyanta ce ta makale a jikin babban mayafin na Ummy. A hankali ta fara ko'karin cire sarkar Safeenah na aikin wash! Wash! sai dai cikin rashin sa'a sarkar ta tsinke kat!
"Innalillahi! Wa inna ilaihiraji'un." Feena ta faɗa da karfi cikin kwalalo ido waje, kafin ta ɗora hannu aka ta fashe da kuka. Abinda ta bawa su Dady matukar mamaki. Ta tsuguna ta ɗauki rabin sarkar da ya faɗi kasa ta fara ko'karin haɗa su tana sharar kwalla tana faɗin "shikenan sarkar da Umma ta bani, yau na fara sakawa gashi ta tsinke." Momy ta sauke numfashi tana faɗin Allah ya shirye ki Feena wlh kin tsorata ni wacce irin sarka ce wannan?" a sanyaye ta Mike tana nuna musu sarkar da yadda ta zama. Tana sharar hawayen tana cigaba da cewa "ban ta6a sakawa ba sai yau tunda nake"
Ummy da Momy suka kaiwa sarkar cafka a lokaci ɗaya ko waccen su ta zari rabin suka kura mata ido suna nazarin sarkar da abinda suke so su gano game da ita.
Kamar haɗin baki tare suka ɗago kai idanunsu kan Feena, gaba ɗaya jikinsu rawa yake yana karkarwa bakunansu na motsi amma duk sun gagara furta komai. Al'amarinda ya jefa Dady da Feena da matar yayan Mommyn cikin ruɗani. Dady ya matsa kusa da su ganin hawaye sun wanke fuskokin uwa da yar', yace Ummy lafiya kuwa me ya faru ne?" Ummy ta kasa magana tamkar wadda aka zukewa jini haka ta silale zata zube kasa sarakuwarta tayi gaggawar riko ta tana faɗin "subhanallahi Ummy" Alhj ya kara ruɗewa yace ta shiga ciki da ita. Momy Yusra ta fashe da kuka ta kara kankame ragowar sarkar dake hannunta ta fuskanci Safeenah bakinta na rawa hannayenta na karkarwa ta buɗi bakin dakyar tana faɗin "Feena! A ina kika samu sarkar nan, wacce ce Umman da ta baki wannan sarkar?" tsoro da firgici suka kara kama Safeenah ga tashin hankali da ta ga iyayen nasu sun shiga. Ta gagara magana ita kanta jikinta kyarma yake. Momy duk ta ruɗe ta fita hayyacinta ta koma baya ta cakumo rigar Dady tana girgiza shi "habibi sarkar Baby ce, sarkar da Ummy ta sa aka buga mata a lokacin haihuwarta." Dady ya zamo ido yana kallon Yusra cike da tantama bakinsa ya kasa furta komai. "wlh ita ce habibi, dan Allah ka tambayi Feena ta gaya mana inda ta samu." Wani sabon kuka ya su6uce mata.
Dady ya nufi Feena dake gefe ta zubawa sarautar Allah ido. Ya kama hannayenta duka biyu ya rike a nashi "ya'ta Safeenah ki taimake mu ki gaya mana ina kika sami wannan sarkar?" ganin hawayen Dady ya kara tashin hankalinta. Haka sauran manyan malaman nan biyu suma hawayen suke ganin halinda Yusra da Alhj suka shiga suka isa gaban Feena babban ne ya fara mata magana "haba yar nan ki yi magana mana, ki taimaka ki gaya musu inda kika same ta sarkar tasu ce ta yar'su ce data 6ata."
Tirkashi! Nan fa ɗimuwa da kiɗima suka kara kama ta. Ta fara ja da baya tana girgiza kai, zasu sa zuciyarta ta buga akan abinda batada masaniya a kai. Kanta har wani juyi yake ta juya da gudu ta koma cikin gidan tana kwalla wa yayanta kira. A falo suka yi kici6is da shi yana tsaye a kan Ummy dake kuka kamar ranta zai fita tana rokon shi ya gaya mata inda suka sami sarkar nan da ke wuyan Safeenah.
Tana zuwa ta rungume shi cikin tsananin kuka ta fara magana "yaya dan Allah ka gaya musu sarka ta ce da Umma ta bani, suna nunawa kamar sun San sarkar har suna cewa sarkar Baby ce yaya pls ka yiwa Dady da Momy bayani." dai-dai nan su Dady da suka biyo bayan Feena suka shigo, fuskar kowannen su sharkaf da hawaye. Suka saka Amar gaba wanda hankalinshi ya gama tashi zuciyarshi ta shiga kai komo. Bakinsa na son magana amma ya rasa me zai furta, su Dady suna son sanin gaskiya game da sarkar ta yaya zai iya furtawa a gaban Feena ya gaya musu cewa ita ɗin yar'tsintuwa ce?