Kanwar matata complete - Chapter 12
Kanwar matata complete Chapter 12: Kanwar matata complete Chapter 12. *👭GARKUWAR MATA* *Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa…
4,397 words
*👭GARKUWAR MATA* *Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci* *GA* *Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa* Rage tumbi💯 Nono💯 Sanyi💯 Karin kiba💯 girmar hips💯 Ni'ima💯 Sabulai💯 Humra💯 Turarukan wuta💯 Matsi💯 Miski💯 Dilka💯 Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI *08089965176* *07084653262*
Paid book 08128755583
*_MATAR SAYYADEE_* [9/29, 12:59 PM] AMINA KABIR CAPS: 🦜 *KANWAR MATATA* 🦜
*PAGE 16*
A zafafe Uncle Ameeru ya mik'e tare da fad'in, "Na rantse da Allah ba zan tab'a bari ayi auren nan ba. Dole ne muje gidan can yanzu mu saka su a gaba muje mu kwaso duk abunda muka kai gidan. Mun janye maganar auren." Wani murmushi uncle Ridwan yayi tare da fad'in, "Gaskiya baka da hankali Ameeru!" "Rabu dashi mana, ni ai kallon wawa nake masa daga nan zaune. Ko ka manta cewa yayi ba zai auri y'armu ba saboda ta lalace? A gaban idanunmu gaba d'aya babu kunya ya fad'a mana wannan maganar. Har yanzu maganar tana sukar zuciyata. Ai ni wannan abu ba dad'i yayi min wallahi. Naji dad'i sosai da ya zam yarinyar gantalalliya ce. Kun ga kenan mun samu hanya mafi sauk'i da zamu cimma burinmu. Kawai had'a kai za muyi da yarinyar mu kashe d'an iska da ransa, musamman ma Bilkisu da ta hana mu rawar gaban hantsi. Shegiya duk hukumomi ta haifo, daga soja, sai d'an sandar farin kaya da kuma d'an iskan nan Barrister da ya gaji ubansa." Fad'in uncle Zayyanu. Uncle Shamsu kuwa cewa tayi, "Ni wallahi duk cikin y'ay'an Bilkisu nafi tsanar d'an iskan yaron nan _Khalil_ da wansa Abdullah. Kun ga da ace yaron nan soja a Kadunan nan yake, wallahi watarana sojoji zai saka su b'alla k'afafuwanmu. Bakwa ganin yanda yake nuna isa yana wani fankama kawai don ya kasance soja. Ni dama a kashe d'an iska acan wallahi." "Shegu taurin rai garesu kamar ubansu. Wani irin farmaki ne bamu kaiwa Nura ba, amma yana nan kamar kainuwa har sai da lokacinsa yayi. Mun sha wuya wallahi." Fad'in uncle Ameeru. Uncle Shamsu yace, "To yanzu dai mu tsayar da mafita. Mai kuke ganin za muyi? Ta yaya zamu b'ullowa ita yarinyar da zai aura?." Uncle Ridwan ya fad'i. "Ku bar min duk wannan a hannuna." Fad'in uncle Ameeru. "Yauwa Ameeru. Na sanka indai ta wannan fannin ne. Da ace yarinyar nan da ta turo sak'o ta bar wani makama da za mu bibiyeta, da ta cab'a don ta hanyarta zamu samu bayanai masu dama. Don ga dukkan alamu bak'in ciki take yi shiyasa ta tona asirin wancen, watak'ila kuma k'awa ce. Duk da hakan dai kuma za mu bincike gaskiyan labarin da ta bamu a kan gidan sabida mu san ta yanda zamu b'ullowa abun." "Yauwa nima abunda nake so in fad'a kenan." Uncle Zayyanu ya fad'i. Hajiya babu abunda take yi sai shirye-shirye. Gaba d'aya ta gama kiran dangi na kusa da na nesa na shaida masu auren _Khalil_ da za ayi nan da sati biyu. Aunty Maryam kuwa har ta gaji da zuwa kasuwa ita da aunty Khairat, don tun da aka saka bikin Aunty Khairat tazo don tuni har sun koma Kano, sai dai can ta baro Barrister shi sai ana saura 2days biki zai zo sabida aikinsa. Duk da kayan lefen kusan gaba ki d'aya a Dubai suka sayo har da akwatin, don private jet suka bi suka yo sayayyar kasancewar duka bangarori hud'un sun saki kud'i, Yaya Abdullah 5million ya bada, ya Barrister kuma ya bada 3million, ya Abdul-Hakeem ya bada 2.5million, shi kuma mai gayya 10.million ya bada. Hajiya kuma ita ta saya akwati set d'aya mai guda goma sha biyu. Gaba d'aya jimillar kud'in suka kama 20.5million. Dasu gaba d'aya su aunty Maryam, aunty Khairat da wata autar su Hajiya suka tafi Dubai. Sai da suka sayo akwatina set uku, na hajiya dozen, sauran biyun kuma mai guda six-six sai dai masu d'an karan tsada kuma gaba d'aya sai da aka cika su da mahaukan kaya masu tsada, don lesses d'in da aka saka babu na k'asa da 200k, kaya dai kamar za'a bud'e shago. Bayan sun dawo gida Nigeria kuwa, haka suka dunga yawon kasuwa suna k'aro wasu abubuwa don sai da suka dawo Hajiya tayi ta fad'a ganin babu kayan uwa da uba. Ana Nigeria suka k'ara had'o set d'in akwatuna guda uku irin mai biyu d'innan da kit. D'aya shaddojine da takalmar maza da turare da huluna masu tsada wanda ya kasance na Baba, sai d'ayan set d'in kuma aka zuba atamfofi da lesses da manya-manyan mayafai da takalma da turare. Shi kuma na Lami, sai d'ayan set d'in akai wa y'an uwan Sarah komai kala biyar-biyar, lesses kowa ta samu biyu, haka shadda da atamfa, sai takalma uku-uku da jakunkunarsu har da sark'a da y'an kunne. Gaba d'aya a parlourn Hajiya aka zube kayan. Sosai Hajiya taji dad'i don gaba d'aya babu k'arya. Yawan kayan ya saka ba komai Hajiya ta iya gani ba daga cikin kayan Sarah don akwatuna har set uku, wanda gaba d'aya jimillar akwatunanta kawai sun kama 24. _Khalil_ kuwa sai dad'a gyara b'angarensa yake yi wanda ya kasance four bedroom a k'asa da wawakeken parlour guda biyu mai d'auke da, dinning sai kitchen da store wanda girmansa da tsaruwarsa ma kawai abun kallo ne. Sama kuma two bedroom da parlour d'aya. Can gidansu Sarah kuwa, Lami da Aina'u ne kawai basa farin ciki da wannan aure da za ayi, gwara ma Lami ita gani kawai take yi idan akai auren shikenan za'a daina kawo mata abun arziki, yayin da Aina'u ita tsabar hassada ce da mugun hali. Babu kuwa kullum bakinsa bai rufuwa sabida farin ciki, sai shirye-shirye yake yi. Don yanzu Alhamdulillah har waje yana iya fita ba tare da sandar ba. Yana zuwa wajen abokansa suna ta shirye-shirye don Baba yace har walima sai yayi. Sarah kuwa babu wacce ke fad'o mata a rai irin K'awarta Muniba, duk duniya ita kad'ai ce k'awarta, gashi kuma tuni iyaye sun raba tsakaninsu. Kamar Baba ya san halin da take ciki, har gida yaje ya samu liman (Mahaifin Muniba) ya bashi katin gayyata sannan kuma ya rok'eshi alfarmar ya bar Muniba tazo wajen Sarah suyi shirye-shiryen biki don duniya bata da wata k'awa sai Muniba. Mahaifin Muniba yaji dad'i sosai jin Sarah za tayi aure kuma yace wa Baba in Sha Allah Muniba zata zo. Sarah na zaune tana sak'awa da warwarewa, don basu jima da waya da _Khalil_ ba yake shaida mata zuwa anjima zai zo suyi maganar shirye-shiryen da za tayi na auren tunda gaba d'aya bikin yanzu ya rage saura kwana bakwai don har anci sati d'aya daga cikin ranakun auren da aka saka. "Assalamu alaikum!" Da mugun gudu Sarah ta fito jin kamar muryan Muniba. "Munibaaaaaaaaaa!" Ta fad'i sunanta da k'arfi cike da farin ciki ta rungumeta tana fad'in, "Wayyooooo Allah na, Muniba kece? Zo mu shiga daga ciki." Ta kama hannunta suka shiga cikin d'aki. Sakin labule Aina'u tayi, don tun jin sallamar Muniban ta d'aga labulen d'akin Lami tana kallon su. Dogon tsaki taja tare da fad'in, "Duk ku gama zumud'inku, wallahi wannan aure ba mai yuwuwa bane. Bamu y'an iska marasa sanin darajar kai irin y'an uwan mahaifin _Khalil_ d'in ma, ace a tura maku irin wannan sak'o amma baza ku tashi kuyi bincike tare da d'aukar mataki ba. Y'an iska kawai!" Duk a zuciya tayi maganar tare da shigewa tana mai yin kwafa tare da fad'in, "Ina da shiri a k'asa mai zafi, duk sai kunci ubanku." "Ke kuma dawa kike kwafa?" Fad'in Lami. A zafafe tace, "Babu ruwanki dani. Tom!" Tana gama fad'in haka ta zari gyale tare da ficewa daga gidan. "K'awata nayi kewarki. Ya aka yi su Baba suka bari kika zo gidan nan?" Sarah ta fad'i bayan ta bud'e d'an k'aramin fridge d'in dake d'akin ta d'auko mata ruwan sanyi da exotic. "Masha Allah! Haka kuka yi gyara a gidan? Wuri yayi kyau. Wannan irin makeken gado haka!" Ta fad'i hakan tare da hawa kan gadon tana shafawa. "It's a long story Munee, naji dad'i da Baba yaje yayiwa babanku magana don wallahi ke kad'ai ce k'awata a duniya gashi kuma d'azu muka gama waya dashi akan zai zo ya sallami k'awayen amarya." Saukowa Munee tayi tare da fad'in, "K'awata wa kika kamo haka? Kwanaki nake ta jin rumours wai kin yi cikin Shege Farouq ya fasa auranki. Ni ina jin maganar ta shiga kunnan hagu ta fita ta dama. Kuma kin san wake fad'awa mutane? Aina'u fa!" Tab'e baki Sarah tayi tare da fad'in, "Uhm, kyaleta. Kin san su suna goyon bayan Lami ne, basu son inyi aure. Ni kuwa zaman mai zan yi a gidan. Ai gwara na tafi nawa gidan nayi bautar ubangiji." Hannu Munee ta bawa Sarah suka kashe sannan tace, "K'awata kenan! To shi angon naki a ina yake." Gyara zama Sarah tayi ta d'an bata labarin in brief saboda ciki ba don abinci kawai aka yisa ba, duk da kuwa ta yarda da Muneeban. "K'awata na taya ki murna wallahi. Allah ubangiji ya sa mijinki ne ya kuma baku zaman lafiya mai d'orewa." "Ameen k'awar arziki." Daga nan suka fad'a hirar yaushe gamo har har lokacin da _Khalil_ yayi kiran Sarah a waya ya shaida mata yana waje. Tare suka fita da Muneeba zuwa wajen _Khalil_ d'in. Lokacin da Muneeba tayi arba da _Khalil_ rud'ewa tayi don b'ata tab'a hasaso haka yake ba. "Wannan itace k'awar tamu?" Fad'in _Khalil_ yana murmushi don tsabar rud'ewa Muneeba ta kasa gaishe shi har sai da Sarah ta d'an tsunguleta a cinya sannan ta dawo hayyacinta. "Kamar mai asibitin _Khalilullah specialist hospital_ ko? Ka tab'a duba ni sau d'aya a asibitin ka." Dariya yayi tare da fad'in, "K'aninsa ne, ba shi bane." Ya k'arisa maganar yana mai kashewa Sarah idanu. Dariya Sarah tayi tana kallon Muneeba dake masa anya kuwa. "Gaskiya kamannin sun b'aci. Kai ne mijin k'awar tawa kenan?" "In Sha Allah!" _Khalil_ yayi saurin fad'in. "Ma sha Allah! To bud'e kunnuwanka da kyau zan baka amana." Hannu biyu _Khalil_ ya saka ya rik'e kunnuwan nasa tare da fad'in, "Ina jinki k'anwarmu." Dariya Sarah ta kwashe dashi ganin yanda yayi tare da bada full attention d'insa wa Muneeba. "Wannan k'awata ce kuma aminiyata. A yau karo ba farko ina mai damk'a amanarta a hannunka, kar inji ko a cikin mafarkina tana kuka, idan ma za tayi, to ya kasance na farin ciki. Sannan a rik'a lallab'ata kamar kwai. Baka da matsala in dai aka zo fannin biyayya, don k'awata akwai biyayya kuma na tabbata za tayi maka biyayya. Yi, nayi, bari, na bari. Duk zata kiyaye su. Kai ne babba, key na controlling gidanka yana hannunka, Sarah kamar motarka ce, duk inda ka nufa da ita, nan zata bi. Saboda haka, dan girman Allah, kar inji Sarah tayi kuka da kai." Sosai _Khalil_ yaji Munee ta kwanta masa a rai. Murmushi yayi tare da fad'in, "An gama aunty Muneeba. Hud'ubarki ta shiga sosai." Juyawa tayi ta kalli Sarah tare da fad'in, "K'awata na dawo kanki, kin ga, wallahi kiyi masa biyayya domin aljannarki na k'ark'ashin k'afarsa. Idan ya take, sunanki sorry, don haka kema kar inji yayi kuka dake. Irin tarairayan duk ki rik'a masa. Kamar irinsu, Gwandi, zaka sha gwanda, honey zaka sha Honey, Sweety zaka sha swee....." Kamun ta k'arisa cewa sweet d'in daga _Khalil_ har Sarah suka fashe da dariya. Ita kanta Muneebar dariyar take yi. "Gaskiya k'awar mu naji dad'in wannan hud'uba naki. Mun gode Allah ya saka da alkhairi kuma mun d'auka." Murmushi a fuskanta tana mai taya k'awarta farin cikin samun miji kamar _Khalil_ tace, "To ma Sha Allah. Haka nake so ai." Gyara tsayuwa _Khalil_ yayi tare da fad'in, "To yanzu wani shirye-shirye kuka tsara ta wajenku?" Kallon Sarah Munee tayi sai kuma ta kalli _Khalil_ tare da fad'in, "Gaskiya ta wajen mu, walima kawai za muyi da k'awayen mu na makaranta da kuma mutanan anguwa. Ko ya kika ce k'awata?" Ta k'arisa maganar tana kallon Sarah. Gyad'a mata kai Sarah tayi tare da fad'in, "Eh hakane." "To ustazai. Ni dai abokaina sun had'a min dinner. Don haka bayan an d'aura aure akwai dinner sai ku kasance cikin shiri. Allah yasa k'awar tamu tana da account?" Ya k'arisa maganar yana kallon Munee. "Eh ina da shi." Fad'in Munee. Fiddo wayarsa yayi tare da fad'in, "Fad'a min account number d'in." Bayan ta fad'a masa da sunan bank d'in, a take yayi mata transfer d'in 500k. Waro idanu Munee tayi lokacin da tayi arba da kud'in da ya turo don har sai da ta murza idanu. Tun da take kud'i dubu ashirin ma basu tab'a zama cikin account d'inta ba ko da mistake, sai ga dubu d'ari biyar sun shigo yau. "Wad'annan kud'in fa? Wallahi sun yi yawa. Duk na minene haka." "Duk na walimar ce." Ya fad'a kai tsaye. "Dan Allah sunyi yawa wallahi." With serious face yace, "Basu yi ba. Kuma kar ki sake magana. Kuje kuyi duk wani hidimar da za kuyi dasu. And in Sha Allah two days before the wedding za'a kawo maku raguna guda uku da drinks. Yanzu haka ma idan kun koma gida kuyi list d'in duk wani abubuwan da zaku buk'ata sai ku turo min." Gaba d'aya Muneeba is speechless. Sai gyad'a kai kawai take yi. B'ata tab'a yin y'an matan amare ba, amma ta sha gani da ji, wani lokacin ma da fad'a ake k'arewa da abokan angon domin wasu dakyar suke fitar goma zuwa sha biyar. "Bari na baku waje, sai kin shigo k'awata." Fad'in Muneeba. "To k'awarmu, mun gode sai ta shigo tunda ni baza amin sallamar ba." Dariya Muneeba tayi tare da fad'in, "Sai da safe asha soyayya lafiya." Tana gama fad'in haka ta shige gida tana dariya. Sun jima a waje suna hirar su ta soyayya, sai da zai wuce yake fad'a mata ta fad'a a gida gobe za'a kawo akwati. Tana shigowa gida ta nufi d'akin Baba kai tsaye ta fad'a masa sak'on _Khalil_ shi kuma ya cire dubu hamsin a cikin kud'in da _Khalil_ ke basa idan yazo gaishe sa yace taje gidan su Muneeba ta kaiwa mahaifiyarta ayi y'an soye-soyen fulawa da kuma kaji. Sannan ya ware wasu kud'i ya ajiye wanda idan y'an kawo kaya sunzo a basu tukwuici. Da Muneeba zata wuce gida tare suka tafi wajen mahaifiyarta tayi mata bayanin sak'on da Baba ya turo ta ta fad'i. Hannu biyu Mama ta karb'a har ta bada sautu saboda a sayo komai da wuri kasancewar gobe bak'in za suzo. Anan ne kuma Sarah da Muneeba suka fad'a mata yanda suka yi da _Khalil_ game da walimar da za suyi da kuma kud'in da ya turo. Ita kanta mama tayi mamakin kud'in, amma da taji anan mahaifin _Khalil_, sai mamakin ya sake ta don ta san irin kud'in da suke dashi. Mama tambayar Sarah tayi shin akwai wani gyara ne da ake mata na jiki a gida, sai Sarah ta fad'a mata babu abunda ake mata. A take mama ta kira waya aka turo mata number d'in wata kwararriyar mai gyaran jiki da yake tana home service. Cikin awa d'aya ta iso da duka kayan gyaran jiki. A cikin kud'in _Khalil_ da ya turo aka tura mata 200k domin soma fara yiwa Sarah gyaran jiki daga yau da daddare. Ai kuwa na dare d'aya tal sai da Sarah ta tabbatar an soma gyara jikinta. Baba da kansa yaje har d'akin Lami ya shaida mata y'an kawo akwati za su zo, sai da tayi masa kallon sama da k'asa tukun sannan tace, "To wata uwar zan yi masu da kazo ka tsaya min a kai?" Murmushi kawai baba yayi tare da juyawa ya koma d'aki don dama yaji a jikinsa babu wani abu da Lami za tayi shi yasa ma ya tura Sarah can gidan su Muneeba. Na'ima ce ta kalli Lami tare da fad'in, "Gaskiya Lami ba haka ake yi ba. Idan fa za'a kawo akwati, dangin amaryar sha tara na arziki suke yiwa dangin ango kamar irin su soye-soyen kaji, su meatpie, samosa, spring rolls da sauraransu har da tukwuicin kud'i. Kuma ni ina ji a jikina ba k'aramin kaya za'a kawo wa Sarah ba." Harara Aina'u ta makawa Na'ima tare da fad'in, "Munafuki annamimiya!" A cikin zuciyarta. Amma a zahiri sai cewa tayi, "Wallahi Lami kar kiyi komai. Kin san halin masu kud'in nan da shegen raini da d'aga kai kamar dan su Allah yayi duniyar." Da sauri Na'ima tace "Ke dai Aina'u annamimiya ce. Idan baza ki kashe wuta ba, to kar ma ki soma hurawa. Shegiya gwara dai ki fito da naki nashinshinin bar yiwa wata hassada. Ko sau d'aya bam tab'a jin wani yazo yana sallama dake ba." A fusace Lami tace, "Wannan wani irin maganar banza ce haka Na'ima? Ban so! Kar ki kuma yi mata irin wannan maganar. Ni kaf y'ay'ana babu wanda bai da farin jini. Farin jini a nono na kuka tsotsa." A fusace Aina'u tace, "Ni ko mai zan yiwa Hassana a jikin wannan banzan da zata aure! Allah ya kiyaye in auri wanda zan zama baiwarsa. Ai duk wata shegiyar da tayi aure ta san inda ta kai kanta. Daga wanke min kayana, dafa min abinci sai goge min takalmi. Sannan idan dare yayi ya kwashi romon albarkan jikin banza a banza ya tashi ya kakkab'e jikinsa kuma ba shi zai hana gobe yayi maki muzurai ba. Watak'ila ma naira d'ari biyu sai kinyi kamar za kiyi kuka ka mun ya cire ya baki. Allah ya sawake nayi aure! Ita ma da kuka ga ina nuna kamar ina jin haushi, sabida y'ar uwata ce ina hango mata wahala musamman da zata shiga gidan masu arziki. Kun ga sun samu y'ar aiki a sama wacce bata da salary." "Nace ba, da kike wannan hak'ik'icewar, ina naki tsayayyan kwarton?" Fad'in Na'ima tana harararta. Aina'u za tayi magana kenan Luckyboy ya fad'o d'akin tare da fad'in, "Ke Aina'u, gasu can a waje suna jiranki." Kwafa Aina'u tayi tare da mik'ewa babu ko gyale ta fice daga d'akin. "Kina ji ko Lami, dan Allah kar kibi shawarar Aina'u, kiyi amfani da kud'inki kiyi masu sha tara ta arziki, sannan gayya fa ake yi. Dole sai kin kira k'awayenki domin su zasu karb'i kayan ba ke ba." Fad'in Na'ima. "Wai maganar me kuke yi haka? Ni sallame ni kawai Lami in ware. Kuma eh, naga anyi eh ya ne a cikin gidan nan, amma ba'a bani rabona ba. Ke nan ni ba d'an gidan bane?" "Ungo wannan, tafi ni ka ishe ni." Fad'in Lami tare da mik'a masa dubu talatin. Da idanu Na'ima tabi kud'in sannan ta juyo ta kalli Lami bayan fitar Luckyboy tare da fad'in, "Lallai ma Lami! Dama duk uban kud'in da muke baki, da wanda _Khalil_ yake baki Lucky kike tattarawa kike ba yana tafiya shi da abokai suna shaye-shaye." Lami ko taro bata yi ba sai zurawa plasma TV tayi tana kallon arewa kamar bata san mai Na'imar ke cewa ba. Washa gari wajajen k'arfe biyu sai ga dirar motoci masu kawo lefe sun zo. Dama kuma Munee na gidan, da sauri ta fiddo waya ta kira mahaifiyarta ta shaida mata sun zo don ita ce tace su fad'a mata a waya idan sun k'ariso. Cikin k'ank'anin lokaci sai ga mama da tawagarta su k'ariso gidan hannunsu nik'i-nik'i da manyan kuloli. A nan tsakar gidan aka shimfid'a masu k'atoton tabarma. Su suka yi insisting sabida d'akin ba d'aukar su zai yi musamman da irin kayan da suka zo dashi. Aunty Maryam, aunty Khairat, kanwar Hajiya, matan uncles da matar ya Abdullah ne suka kawo kayan. Su suka fara shigowa, sai da suka gama gaisawa da mahaifiyar Munee da mutananta da ta gayyato. Na'ima kuwa hana Lami fitowa tayi don cewa tayi sai tayiwa Baba da mahaifiyar Munee tujara akan abunda suka yi mata. Sai zage-zage take tana fad'in akwai wani banzan alak'a tsakanin Baba da mahaifiyar Munee. Allah yaso babu wanda yaji abunda take fad'i sai Na'ima da take ta faman bata baki a d'aki. Kuma ta kulle d'akin ta ciki duk da kuwa tana so ita ma taje taga kayan da ta hanga ta window driver na wucewa dasu yana ajiyewa a nan tsakar gidan. Sai da ya kawo duka sannan aka soma bubbud'ewa. Babu abunda ke tashi sai kabbara da gud'an mata. Tun mata na irge har suka hak'ura don b'ata lissafi suke yi. Mata sai uban santi suke yi da gud'a. Gaba d'aya gidan ya cika da mutanen dake ganin kayan Sarah. Aina'u kuwa zawonta uku a cikin wando ganin mahaukatan kayan da aka zubawa Saran. Bayan an gama gani, mama ta ware na Baba, Lami da kuma wanda aka ce na k'annai da yayyin amarya ne ta ajiye a gefe, sauran kuma aka bar su nan tsakar gida. Dubu d'ari uku Baba ya bada matsayin tukwuicin duk da kuwa bai san adadin kayan da zasu kawo ba. Y'an kawo akwati sun mik'e zasu wuce kenan sai ga tawagar matan zumunta sun shigo gidan da wani irin mahaukacin gud'a suna tafi tare da yin wak'ok'in coci. Gaba d'aya sai kallo ya koma sama. "Elizabeth kina ina? Ashe aurar da yarinyarki za kiyi amma shine baza ki gayyaci mutanan coch ba. Baki kyauta ba sam. Pasto William yayi fushi dake kuma yace idan baki kai Sera (Sarah) ya saka mata albarka ba, auren ba zai yi albarka ba. Yace ya baki kwana biyu ki kaita ayi mata wankan zunubi kamun ta shiga gidan miji. Da k'arfi aunty Rose Merry take maganar duk da kuwa bata ga Lami a tsakar gidan ba. Aunty Maryam da aunty Khairat da kanwar Hajiya, sai wannan ta kalli wancen, sai wancen ta kalli wannan. Da suka ga abun ba na k'arewa bane, sai suka yi salama suka tafi domin sosai dai aunty Rose Merry da tawagarta suka baje suna wak'ok'in suna kiran sunan yesu almasihu. Idan suka buga wani ihu har hanjin mutum sai ya kad'a. Baba dake d'aki kuka kawai ya fashe dashi. Don bai tab'a kawowa Lami zata iya yin wannan iskancin ba. Lami dake d'aki ita ma mamaki ne ya kamata don ko da wasa bata tab'a fad'awa mutanen coch d'insu zata aurar da y'a ba. Ko aunty Rose Merry da take k'awarta bata fad'a mata ba. "Na'ima wallahi bani na gayyace su ba, kuma ban san wanda ya kira su ba." Na'ima kuwa kallon mahaifiyarta take yi cike da tuhuma tare da fad'in, "Lami dama kina zuwa coch? Wa za ayiwa wankan zunubin?" Lami bata ba ta amsa ba, sai wucewa da tayi ta bud'e k'ofar ta fita ta samu ce aunty Rose Merry dake ta kwasar ihu da kiran yesu suna d'ad'd'aga kayan akwatin Sarah. "Hajiya kina bacci ne aka kwaso maki dangin arna matsayin surukarki?"
*👭GARKUWAR MATA* *Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci* *GA* *Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa* Rage tumbi💯 Nono💯 Sanyi💯 Karin kiba💯 girmar hips💯 Ni'ima💯 Sabulai💯 Humra💯 Turarukan wuta💯 Matsi💯 Miski💯 Dilka💯 Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI *08089965176* *07084653262*
*_K'ANWAR MATATA ISN'T FREE, PAY #500 VIA THIS ACCOUNT NUMBER 0592412800 ZULFAU SAID GTBANK AND SEND YOUR EVIDENCE OF PAYMENT THROUGH THIS NUMBER 08128755583_*
*_MATAR SAYYADEE_* [9/29, 12:59 PM] AMINA KABIR CAPS: 🦜*KANWAR MATATA*🦜
*PAGE 17*