Kanwar matata complete - Chapter 14
Kanwar matata complete Chapter 14: Kanwar matata complete Chapter 14. "Ke, bana son hauka! Kaza ce ita da zata b'ata? Ba ke kika kira wayarta ba? Kamun na…
5,004 words
"Ke, bana son hauka! Kaza ce ita da zata b'ata? Ba ke kika kira wayarta ba? Kamun na juyo yanzu ki nemo min matata a duk inda take idan ba haka ba a kaf zuri'arku bana tunanin akwai wanda zan iya kyalewa ko jaririne." Yana gama fad'in haka ya katse wayar tare da yin reverse ya fizgi motar da gudu don har yayi nisa da layin. Muneeba kuwa jikinta ne ya soma wani kakkarwar tsoro zufa na yanko mata. Wayarta ta haska ta soma bin hanya tana kwala kiran "Sarah" ko Allah zai saka ta amsa. "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!" Fad'in Munee tare da saurin d'ukawa ta d'auki takalmi da kuma ledar da _Khalil_ ya ba Saran. Kuka Munee ta fashe dashi tare da fad'in, "Inna lillahi wa'inna ilaihir, Allahumma arji'ini fi musibati. Saratu kina ina? Mun shiga uku, wayyo Allah, Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un." Haka ta dunga yin gaba tana dawo baya tare da ambatan sunan Allah. _Khalil_ nayin parking ya nufi hanyar da Sarah tabi a gaban idanunsa, kicib'is suka yi da Muneeba dake kuka tana kiran sunan Allah. "Ke!" Ya daka mata wani irin tsawa tare da fad'in, "Ki bar wannan haukan kukan ki fad'a min ina matata take." Gaba d'aya sai Muneeba ta sake rikicewa saboda yanda yake daka mata tsawar. Takalmin Sarah da ledan hannunta kawai ta mik'a masa jikinta na rawa. Hannu ya kai ya amsa yana kallon ledar da kuma takalmin. Tabbas ledar da ya bata ne kuma takalmin ma nata ne. Ransa ne ya k'ara b'aci, bai iya yi mata wani magana ba sai wayarsa da ya fiddo ya danna number d'in ya Abdullah-Hakeem. Ringing uku ya d'auka yana fad'in, "Ango kasha k'amshi." Shi kuwa _Khalil_ cewa yayi, "Yaya motocin mutanan ku uku nake so yanzu. An sace Sarah. So nake gaba d'aya daga farkon Jos road har zuwa k'arshe a zuba mutanan ku, duk wanda aka yayi kala da rashin gaskiya a kama shi." Tashi zaune ya Abdul-Hakeem yayi tare da fad'in, "An sace Saratu? Wannan ma k'arya ne. Ka kwantar da hankalinka yarinyar nan in Sha Allah baza ta kwana ba. Yanzu zan kira yaya Abdullah domin ya turo mana da sojoji, kuma zan kira abokina ACP Lawal Yakubu domin a bamu police guda talatin. Gamu nan zuwa yanzu. Koma wanene yayi wannan aikin zai san ya tab'o jinin Chief Justice Nurudden Muhammad Ibrahim." Yana gama fad'in haka ya katse wayar tare da soma kiran yaya Abdullah. Yaya Abdullah ya fisa ma d'aukar zafi don kamar zai fito ta wayar. Kuma take yayi waya bariki aka turo motar sojoji har biyar. Tun daga Katsina round about mutanan dake Jos road suke jin jiniyar y'an sanda da sojoji. Matasa gaba d'aya hankalinsu ya tashi. Mutane sai firfitowa suke daga gidajansu suna kallo, wasu kuma suna dannawa nasu gidan sakata. Y'an daba da y'an shaye-shaye kuma sai nemar mab'oya suka soma yi. Tun daga farkon Jos road y'an sanda da sojoji suka samu position suka tsaya fuska babu rahama ko kad'an har k'arshe layin. Su Hajiya Lami kuwa cewa tayi, "Yanzu haka saboda d'aurin auren da za ayi gobe ne aka turo so domin su bamu tsaro." Na'ima tace, "Babu shakka kam!" Baba dake d'aki kuwa hakanan yaji hankalinsa bai kwanta ba. Aina'u kuwa gaba d'aya ta kasa sukuni sai lek'e take yi tana kiraye-kirayen waya. Muneeba kuwa sai kuka take yi a gaban _Khalil_ tana mashi rantsuwar ba da ita aka had'a baki ba kuma wallahi bata san inda Sarah take ba, bata san ko wa ya sace ta ba. Shikuwa _Khalil_ kwakkwarar motsi ya hanata don cewa yayi bai yarda da ita ba. K'aran jiniyar motocin sojoji da y'an sandan da suka iso inda suke ne ya k'ara hargitsa mata tunani ta saki wani marayan kuka tana k'an'k'ame jikinta. "Ke!" Wani soja ya buga mata uban tsawa sai gata a zube a k'asa ta sume dai-dai lokacin da ya Abdul-Hakeem ya iso wajen. Shi da kansa ya zira hannu ta cikin motar _Khalil_ ya d'auko ruwa tare da yayyafawa Muneeba. A firgice ta farfad'o tana fad'in, "Wallahi bani bace, ban sa wanda ya sace ta ba, kuma wallahi bani na kirata a waya ba." Hannu ya Abdul-Hakeem ya saka a baki tare da fad'in, "Shssh! Kwantar da hankalinki babu abunda za ayi maki a nan wajen. Yi min bayani mai ya faru." Ajiyar zuciya Muneeba ta sauke tare da fad'in, "Sarah tu a gidan mu take kwana tun saura kwana biyar bakinta. Kuma mama ta hana mu fita kuma ta cewa _Khalil_ ya hak'ura da zuwa tad'i har sai an kawo masa ita gida sabida ana mata gyaran jiki. To kullum sai suyi ta damuna su biyu suna cewa suna kewar juna. Shine jiya muka yi waya da shi _Khalil_ akan in taimaka masa in fito masa da Sarah suga juna ko mintuna biyar ne, shine na fito da ita ba tare da sanin mama ba na kawo ta wajensa sai na koma gida domin basu waje suyi magana. To K'anwar Sarah tazo gidan mu tana neman ita Sarah har mama taji shine ta tambaye ni ina Sarah, sai nayi mata karyar tana ban d'aki shine nayi sauri na fito domin in kira ta mu koma gida. To da nazo nan d'in sai naga babu motar _Khalil_ sai nayi ta kiran number d'in Sarah amma ba'a d'agawa, daga k'arshe ma aka kashe. Shine na kira shi _Khalil_ d'in ina tambayarsa Saratu, sai ya fara min ihu wai ai nice na kira ta har ta tsora tace wata k'ila an gane bata gidan ne sai suka yi sallama ta tafi. Kuma ni wallahi, tallahi ban kira ta ba." Haushi ne ya kama _Khalil_ jin rantsuwar da tayi akan bata kira Sarah ba, bai san lokacin da ya d'aga hannu zai wanke fuskanta da mari ba, da sauri Abdul-Hakeem ya tare hannunsa tare da fad'in, "Baka da hankali ne? Ko in barka kayi binciken ne da kanka? Ashe babu amfanin kiran mu da kayi kenan?" Matsawa baya _Khalil_ yayi tare da fad'in "I'm sorry." Kallon Muneeba yaya Abdul-Hakeem d'in yayi tare da fad'in, "Ina wayarki?" Da sauri ta mik'a masa wayar hannunta na rawa shi kuma ya mik'a wani dake gefensa. Cike da ladabi ya amshi wayar sannan ya sara masa tare da koma cikin mota ya kunna computer ya soma danne-danne cikin sauri da kwarewa. Muneeba kuwa da mararta ke cike da fitsari, ihu d'aya za'a kuma buga mata ta saki fitsari. Mintuna biyar sai ga wannan da aka ba waya ya dawo tare da fad'in, "An kira number d'in sau bakwai mintuna goma sha bakwai baya amma ba'a d'aga ba kuma daga baya aka kashe wayar. Lokacin da ake kiran wayar ba'a d'aga ba, nabi diddigin layin, makwamusan suna dai-dai round about d'in stadium, kuma an kashe wayar ne a dai-dai wajen tare da jefar da waya. Don har yanzu diddigin layin na wajen. Sannan kuma an kira wayar k'arfe bakwai da mintuna arba'in da uku, sai dai har ya gama ringing ba'a d'auka ba." Da sauri _Khalil_ yace "Lokacin muna tare, kuma a wannan ne Sarah hankalinta ya tashi ta wuce gida." Abdul-Hakeem ya kalli Muneeba tare da fad'in, "Kin ce baki kira Sarah ba, kuma gashi bincike ya nuna kin kira da misalin 7:43." Kuka Munee ta saka tare da soma rantsuwa tana fad'in, "Na rantse da ubangijin da ya halicceni ban kira taba, bani na kira ta ba." "To idan baki kira taba, waye ya kira ta? Kin ba wata wayar ne a wannan lokacin?" Shuru Muneeba tayi tana tunanin wa ta ba wayar a wannan lokacin? Kallon Abdul-Hakeem tayi tare da girgiza kai tace, "Ban ba kowa wayata ba a wannan lokacin. Kuma wallahi ban kira ba." "Oga wannan yarinyar fa baza tayi magana ba har sai mun tafi da ita." Fad'in wani police. Tuni Muneeba ta soma sakin fitsarin da ya dad'e da cika mata mara tare da durk'usawa a k'asa tace, "Na rantse da girman Ubangiji da ya halicceni ban sace Saratu ba. Wallahi bani bace. Dan Allah kar ku tafi dani." Yaya Abdul-Hakeem tun kallon farko da yayi wa Muneeba ya san cewar bata da hannu a cikin sace Sarah da aka yi, sai dai tabbas duk wanda yayi hakan yana tare da ita amma ita bata san hakan ba. "Wa kika ce tazo neman Sarah har mamanki taso ta fahimci bata gidan?" Da sauri Muneeba tace, "Aina'u!" Wani harara _Khalil_ ya watsawa Muneeba tare da fad'in, "Aina'un ce za ta sace Sarah?" Girgiza kai Muneeba tayi tare da fad'in, "Ba haka nake nufi ba." yaya Abdul-Hakeem kuwa cewa yayi "Aina'u tayi amfani da wayarki ne lokacin da tazo?" Da sauri Muneeba ta girgiza kai tare da fad'in, "Bata yi ba. Cewa kawai tayi ina Sarah. Ni kuma nayi saurin janta gefe nace tayi shuru kar mama taji don ta hana mu fita ni kuma na saci hanya na kai Sarah wajen _Khalil_. Ita kuma sai ta mik'o min kayan Sarah tace in bata baza ta iya jiran Sara ta dawo ba, don itama jiranta ake yi saurayinta yazo." "Wani irin kaya ta kawo mata, kuma dama Sarah ce tace ta kawo mata kayan?" Fad'in ya Abdul-Hakeem. "Eh ita ce tace ta kawo mata doguwar rigar baccinta da kuma hula." Jinjina kai Ya Abdul-Hakeem tare da fad'in "Jeki gida, zan neme ki idan buk'atar hakan ta taso." Da sauri Muneeba ta juya har da had'awa da gudu ta bar wajen. Shi kuma _Khalil_ a fusace ya kalli ya Abdul-Hakeem tare da fad'in, "Ya ka barta ta tafi? Ita ce suspect d'in fa." Ko kallonsa ya Abdul-Hakeem bai yi ba, sai daga ma d'aga kiran da aka yi masa yayi tare da sakawa a kunne. "Ok kar ku tab'a komai gamu nan zuwa." Yana gama fad'in haka ya yanke wayar tare da kallon _Khalil_ yace, "Shiga mota ka biyo bayan mu." Shi kuma ya nufi motar da ya shigo bayan ya bawa sauran y'an sandan umarni akan kar ku yarda su bar wajen har zuwa gobe shi kuma ya shiga motar da ta kawo sa suka nufi Barnawa inda wanda ya kira yanzu ya fad'a masa. Kasancewar gudu suke yi kuma ga shi dare ne babu mototi akan titi sosai, cikin k'ank'anin lokaci suka isa. Wasu cincirundo y'an sanda ne a zagaye da wata mota k'irar golf, sai wasu matasa su shidda an fito dasu sun yi kneeling a k'asa fuskokinsu a kumbure. Abdul-Hakeem na isowa wajen ya fiddo pistol tare da kicking ya d'aura akan goshin d'aya daga cikin su, zawo ne ya soma zubowa daga jikinsa na tsoro tare da fad'in, "Kar ka kashe ni dan Allah. Wallahi ba muyi mata komai ba. Tana cikin buhu a bayan mota." Da jin haka haka ya Abdul-Hakeem nufi bayan motar bayan ya saka hand gloves sannan ya bud'e tare da warware saman buhun. Da mugun gudu _Khalil_ ya iso wajen zai kai hannu ya d'auko Sarah da bata da maraba da gawa amma ya Abdul-Hakeem ya tare sa tare da fad'in, "Wait a minute!" _Khalil_ bai saurari ya Abdul-Hakeem ba ya ciccib'o buhun ya fito dashi tare da fiddo Sarah da gaba d'aya jikinta a sake yake ya nufi motarsa da ita ya bud'e back seat da d'ayan hannunsa ya shimfid'ar da ita tare da soma ceto ranta don ya duba pulse d'inta yaga akwai rai a jikinta. Tsabar wahala kawai tasha da kuma abunda suka shak'a mata. Numfashi ya soma bata ta bakinsa yana hura mata. Sai da ta d'au tsayin lokaci kamun ta ja wani irin dogon numfashi tare da rirrik'e damatsen _Khalil_ d'in da k'arfi. Wani irin ajiyar zuciya ya saki tare da d'agota ya had'a da jikinsa ya rungume k'am-k'am. Yana jin yanda bugun zuciyarta ke tafiya da k'arfi. A can waje kuwa, wani irin mahaukacin duka sojoji hud'u suka rufe su dashi. Sai da suka karya k'afafun su da hannaye sannan suka jefa su cikin mota. Yaya Abdul-Hakeem kuma k'arisowa yayi ya kwankwasa motar _Khalil_ sai a sannan ya saki Sarah dake kuka a hankali ya fito daga motar. "Ka mayar da yarinyar gidan iyayenta. Sojoji da y'an sanda zasu cigaba da bata tsaro har sai an d'aura aure gobe an kawo ta gida tukun zasu bar layin." _Khalil_ yace, "To yaya. Amma ya akai aka gano su?" Murmushi ya Abdul-Hakeem yayi tare da fad'in, "Tun da muka gama waya da kai na kira wani daga wajen aikinmu, kwararren masanin na'ura na tura masa number d'inka. Na number d'inka yabi diddigin layin Sarah. Ko da nake wa yarinyar nan tambayoyi, wasu na can tuntuni sun bi bayansu har Allah yasa suka damk'o su. Sai dai kuma koma wanene wanda ya saka aka sace Sarah, ba k'aramin wayau gare shi ba, don bai yarda ya bar wani makama ba, ko su wanda muka kwamushe yanzu, basu san ko wanene ya basu aikin ba. Kuma da boyayyiyar number ake basu umarni. Kuma sun ce muryan namiji ne ke basu umarnin." Da mamaki _Khalil_ yace, "To wanene wannan yake son ganin baya na ta hanyar raba ni da Sarah?" Kai tsaye ya Abdul-Hakeem yace "Makiyi!" "Allah ya shiga tsakanin mu da koma wanene. Kuma in Sha Allah aure babu fashi. Gobe za'a d'aura aure." Fad'in _Khalil_. "In Sha Allah. Ma mai masu yarinya gida dare nayi." "To yaya sai na dawo gidan. Don Allah kar ka fad'awa Hajiya ka santa nan da nan hankalinta ke tashi" Sai da ya hararesa sannan yace, "To yaya _Khalil_, ai ka san dama bani da hankali." Dariya _Khalil_ yayi tare da bud'e gidan baya inda Sarah take ciki ya shiga. "Stop crying my baby. Gani a kusa dake. Bazan k'ara bari haka ya faru dake ba. I'll always protect you my wife. Kiyi hak'uri laifina ne. Da ban zo ba, hakan ba zai faru ba." Share hawaye Saratu tayi tare da fad'in, "Ko kazo, ko baka zo ba, haka sai ya faru tunda rubutaccen al'amari ne." Hannu ya kai ya share mata hawayen da suka gangaro tare da fad'in, "Gobe, by this hours, kina kwance a k'irjina, ba zan bari ko sauro ya hau kan jikinki ba bare kuma d'an Adam." Hannu sara ta saka ta rufe fuskanta tare da fad'in, "Ni dai ka bari. Mu tafi gida dare nayi." Dariya yayi tare da fita daga motar ya koma mazaunin drive ya kunna tare da barin wajen ya hau hanya. Sarah ganin basu yi hanyar gidansu Muneeba ba, sai tace, "Gidan su Muneeba zaka kai ni fa." Sai da ya juyo sannan yace, "Babu gidan wata Muneeba da zaki k'ara kwana. Gida zan kai ki. Ni ban yarda da Muneeba d'in nan ba. Ina zargin har da saka hannunta a sace kin da aka yi. Don tana ta rantsuwa wai ita bata kira ki ba lokacin da muna tare dake." Waro idanu Sarah tayi tare da fad'in, "Dan Allah kar kace haka. Wallahi Muneeba baza ta tab'a cutar dani ba. Babu hannunta wallahi." Kallon titi yayi tare da fad'in, "love, mugu bashi da kama. Ki bar wannan maganar. Gida zaki kwana." Kuka Sarah ta saka tana fad'in, "Wallahi Muneeba ba muguwa bace." Banza yayi da ita har yayi parking a k'ofar gidansu. Uban dandazon sojojin da ya ta gani a k'ofar gidansu sai da ta tsorata. Ganin da sauri sojoji kusan hud'u sun nufo su tare da bud'e gidan baya ina take, baya san lokacin da ta kwala ihu ba sai da _Khalil_ ya tsorata tare da fitowa da sauri ya ture wani soja yana fad'in, "Baby lafiya?" Da hannu tayi masa nuni da, sojan dake tsaye k'ik'am kamar an dasa shi. "Malam matsa mana. Baka ganin tsoranka take ji." Da sauri sojan ya matsa, shi kuma ga kamo hannunta ya fito da ita. Har tsakar gidansu ya raka ta dai-dai lokacin da Baba ya fito daga d'aki yana fad'in, "Wanene nan wajen?" Amma ganin _Khalil_ da Sarah tsaye sai hakan ya bashi mamaki don ga san Sarah a gidan Liman Muhammadu take kwana. "Ibrahim lafiya? Wani abun ya faru ne? Shiyasa naji jiniyan sojoji ko ta ina kenan d'azu?" Baba ya jero tambayoyi gabansa na fad'uwa. Jin muryan baba sai gaba d'aya mutanan gidan suka fito. Aina'u kuwa har da cin tuntub'e tana waro idanu ganin Sarah a tsaye. "Baba wani tsautsayine ya d'an afku, amma Alhamdulillah yanzu." Daga nan ya kwashe komai ya sanar da baban. Salati Baba da su Na'ima suka d'auka. Lami kuwa wani uwar yare mai tsawo ta dire tare da fad'in, "Yesu almasihu kana ganin komai. Mak'iya sun fara bina don sun ga y'ata zata auri babban mutun d'an gidan manyan mutane." _Khalil_ kuwa kunnansa ne suka yi masa wani duum jin Lami tace _Yesu almasihu_. Bai gama dawowa daga duniyar mamaki ba, Lami ta kuma cewa, "Ya Uba mai-iko duka, mai-yawan jinkai, mun rantse, mun bache daga tafarkokinka kaman batattun tumaki. Mun cika bin dabarun zukatanmu da muradinsu. Mun sab'a dokokinka masu-tsarki. Abin da ya wajabba garemu, mun bari: Abin da ya wajaba mu bari, shi muke yi; Babu lafiya garemu. Amma, Ya Ubangiji, ka yi mana jinkai, mu masu-sab'o abin tausai. Ya Allah ka yafi masu fad'in laifinsu, Masu tuba kwa ka amshe su: bissa alkawalin da ka furta ma yan Adam. Almasihu Isa Ubangijinmu, Uba kuma mai-yawan jinkai, ka sa duk mai neman mu da sharri ya koma masa, kada kayi duba da laifinmu a gare ka. Ya Almasihu mai-tsarki ka amsa addu'armu Amin." Ba _Khalil_ kad'ai hatta su Nuratu sun firgita da jin maganganun mahaifiyarsu. Marfu'a kuwa kallon Lami tayi tare da fad'in, "Lami dama ki koma addinin kiristancinki? Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Gaskiya Lami baki kyauta ba. Shikenan baki da rabo a lahira." Aina'u tayi caraf tace, "Tunda kece da aljannar sai ki hanata ai. Ai gwara ita an san cewa kirista ce, ke kuma fa? Kina amsa sunan musulma amma ban tab'a ganin kin aje goshinki a k'asa ba. To Menene marabarku kenan? Kowa dai yasan bambamcin musulmi da kirista shine Sallah." A fusace Marfu'a tace, "Dan uwarki dake nake magana? Alhamdulillah tunda da na furta kalma La'ilaha illallah Muhammadur Rasulillah. Kuma dai ai ance duk wanda ya furta Kalmar bai dauwama a wuta." _Khalil_ gaba d'aya ji yayi kamar ana zare nasa wani abu a jiki, yayi dana sanin shigowa cikin gidan. Sai yaji dama a k'ofar gida ya tsaya har Sarah ta shige ciki. "Ke, ba kowa bane yake da rabon shiga addinin kiristancin. Addini na shine addinin gaskiya. Kuma ni tun farko ban tab'a yin wani addini bayan addinina ba. Addinin ku ya cika tsauri da yawa, mutum yayi da dungure sau biyar a rana, wata d'aya ana azumi, ba'a sata, ba'a k'arya ba'a saduwa, ba'a shan burkutu. Abubuwa da yawa addininku sun hana. Addininku addinin takura ne." Sai a lokacin Baba ya bud'e baki tare da fad'in, "Ke Lami! Ki kiyaye harshenki. Addinin Musulmi addinine na gaskiya kuma addini ne mai bawa kowa y'anci. Duk abunda kika lissafo addinin da kike ik'irararin shi kike yi, shima yayi hani akai. Babu wani Bible d'in da ya halasta duk abunda kika lissafo. Idan kinga dama ki zama mara addini gaba d'aya, wannan ruwanki ne. A gaban sirikinki kike wad'annan maganganun sabida baki da hankali da tunani." Da sauri _Khalil_ yace "Baba sai da safe, sai da safe Sarah." Yana fad'in haka ya juya. Aina'u kuwa wani farin ciki taji ya ziyarci zuciyarta ganin reaction d'in _Khalil_. Tana ji a jikinta auren Sarah dashi ba zai yuwu ba gobe. Baba juyawa yayi tare da shiga d'aki Sarah ta bishi a baya. Su Nuratu ma suka shige d'aki. Aina'u kuwa, hanyar toilet ta nufa. Tana shiga ta rufo k'ofar tare da kiran wata number bayan ta shiga magic voice ta mayar dashi na tsofaffi sannan ta b'oye number. Ringing uku aka d'aga wayar tare da fad'in, "Zance ya b'aci, su Arowa suna state CID yanzu haka. Sai dai sunana bai fito ba, don kamar yanda ake b'oye number ana canza muryoyi ana kirana, nima haka nake musu. Ni dai koma wanene nake magana dashi yanzu haka, bamu da matsala domin babu wanda ya san mu." Aina'u wani murmushin jin dad'i tayi duk da tasan ko ta fashe babu wanda zai kamata don bata bada k'ofar da za'a ganeta ba. "Yayi kyau! Zan kira ka idan wani aikin ya kuma b'ullowa." Tana gama fad'in haka ta yanke kiran ta fito daga bayin ta koma d'aki." "Baba wallahi ban san ko su wanene suka min haka ba. Amma ga dukkan alamu anso ayi garkuwa dani domin kud'i. Tunda kaga da zan ba'a yi hakan ba sai da aure na ya kusa kuma da d'an Chief Justice Nurudden Muhammad." Ajiyar zuciya Baba yayi tare da fad'in, "Ubangiji Allah ya kare ki daga sharrin mutum da aljan. Wannan aure kuma, idan ma anyi hakan ne domin a fasa,in sha Allah an riga an d'aura a sama, shaidar duniya kawai ake jira. Tashi kije ki kwanta, in Sha Allah da safe zan je can gidan liman Muhammadu inyi masa bayani komai. Ni kai na ban ji a jikina Muneeba zata had'a baki da wasu domin a sace ki. Amma zan je gidan gobe da safe." "To Baba Allah ya kai mu." Sarah ta fad'i tare da ficewa daga d'akin ta koma nasu. "Sarah kin tab'a karanta littafin hausa mai suna _Ayi dai mu gani_?" Fad'in Aina'u tana mai danna wayarta. Kallon Sarah tayi tare da fad'in, "Kin fara karatun novels ne na hausa?" Sarah ta fad'i tana mai kallonta. Ba tare da Aina'u ta kalleta ba tace, "Eh, yau kwana uku da na fara da wani littafi mai suna _Iska na wahalar da mai kayan kara_, yanzu kuma _Ayi dai mu gani_ nake karantawa." Girgiza kai Sarah tayi tare da fad'in, "Gaskiya ban karanta ba. Ban ga kinyi lalle ba, kuma har nan na turo mai lalli d'azu da safe. Su Na'ima duk anyi masu ja da b'aki." Tab'e baki Aina'u tayi tare da fad'in, "Ni kinsan lalli bai dame ni ba. Kuma da safe bani nan naje kitso. Za kuyi wani program ne?" Zama Sarah tayi a bak'in gadon tare da nannad'o gashin ganta ta tura cikin hula ta k'eya tare da jawo hulan har zuwa goshinta saboda kar gyaran kan da akai mata ya lalace. Tace, "Eh, naga duk su Na'ima ma sunyi kitson ai. Ni ko da da nake saka attachment, ba zan iya yin wannan uban k'ananan kitson ba. Na'ima muga naki, kamar yafi na Aina'u k'anana ko?" Sarah ta fad'i maganar tana kallon kan Na'ima wacce taja hulan kanta baya. "Wai! Gaskiya kitson yayi k'ana. Sauk'in ta ma a can inda kukai kitson ake tsefe maku." Nuratu tace, "Ni ko kinga nawa bai kai nasu k'anana ba. Ghana weaving akai min manya." Ta fad'i maganar tana mai jan hular kanta. "Ni da Hassana fixing kawai akai mata. Don wallahi naji bazan iya zaman kitson ba. Basir!" Fad'in Marfu'a tana mai zame Fadwa da ta gama shayar da ita daga jikinta ta kwantar. "Amma dai ba anan zata kwana ba ko? Don na tsani kukan daren nan da take yi. Duk ta hana mutum bacci." fad'in Aina'u. "To nan zata kwana. Ni ban san wani uban gulmar ce ta dawo dake kwana anan d'akin ba, ai da a d'akin Lami kike kwana." Cike da rashin kunya Aina'u tace, "To nan d'in naga damar dawowa da kwana. Ai gidan ubana ne." Ficewa daga d'akin Sarah tayi ganin zasu fara raba halin nasu da suka saba. D'akin Baba tayi sallama ta shiga. Zaune ta same shi a kan gado yana kallon Sunna Tv. "Baba dan Allah wayarka zaka ara min." Ba tare da yace komai ba ya d'auko wayar a gefensa ya mik'a mata ita kuma ta amsa tare da ficewa. Number d'in _Khalil_ tayi dialing, ringing biyu yayi sai yayi rejecting tare da biyo kiran. Sarah na d'agawa yace, "Assalamu alaikum Baba." Sarah sai ta canza murya tare da fad'in, "Wa'alaikassalam d'ana." A tare suka saki dariya, _Khalil_ yace, "Ke nine d'an naki? Za kiyi bayani gobe a irin wannan lokacin." Hararar wayar Sarah tayi tare da fad'in, "Bayanin mai zan yi? Ni babu wani bayani da zan yi." Dariya _Khalil_ yayi tare da fad'in, "Kuma kin san na mance y'an iskan da suka d'auke min ke sun yar da wayarki, wallahi na kira yafi sau shurin masak'i, dole ma gobe da sassafe in kawo maki waya. Ba zan juri rashin jin muryanki ba." "To bayan gobe zamu kasance tare har abada." Sarah ta fad'i a kunyace. "Na'am, maimaita dan Allah love." K'it ta kashe wayar tare da mayarwa Baba wayarsa. Daga can kuwa _Khalil_ kamar ya fasa ihu, yana tsoron kira yaji wayar a hannun Baba. Washa gari da sassafe kamar yanda _Khalil_ ya fad'i, sai gashi da sabuwar waya k'irar LG mai tsananin kyau da tsada, wani tsohon MTN sim d'insa ya saka mata a ciki ya kawo mata. Na'ima ta fito zata shago ta gansu a tsaye suna magana. Wani irin kyau suka mata, sai taga kamar anyi su don juna ne don ba k'aramin dacewa suka yi ba. "K'anina ayi hak'uri haka, anjima kad'an zamu kawo maka ita." Murmushi kawai _Khalil_ yayi ita kuma ta wuce. Dai-dai nan Muneeba ta iso wajen, tana ganin _Khalil_ ta juya da sauri. Shima _Khalil_ da sauri yabi bayanta yana kiran sunanta don jiyan sunyi magana sosai da ya Abdul-Hakeem ya fahimtar dashi Muneeba bata da hannu a ciki. "K'awarmu dan Allah kiyi hak'uri da abunda ya faru jiya. Tashin hankali ne ta saka nayi abunda nayi. Koma wanene a matsayina abunda nayi shi zai yi. Kiyi hak'uri kinga ma na kama kunnena. Kar ki manta ke kika ce min in kula da k'awarki sosai kada tayi kuka. To hud'ubarne ya shiga kunnena." Kuka Munee ta fashe dashi tare da fad'in, "Naji tsoro jiya, banyi bacci ba. Mama kwana tayi tana mun fad'a. Sai da baban Sarah yazo gidan mu yayi mana bayanin anga Sarah sannan hankalinmu ya kwanta. Wallahi ko a cikin mafarkina bai tab'a zuwarmin in cutar da Saratu ba." "Naji na yarda dake Muniba. Dan Allah kiyi hak'uri." Fad'in _Khalil_. Sai da ta murgud'a baki sannan tace, "Na hak'ura dan ba halinka ba." Sai ta juya ta kalli Sarah data k'ariso ta rungumeta tare da fad'in, "Alhamdulillah k'awata. Duk wanda yayi maki wannan abun Allah ya tona asirinsa." Da Ameen Sarah ta amsa tare da jan hannunta bayan ta d'agawa _Khalil_ hannu. Baki _Khalil_ ya bud'e tare da fad'in, "Har munyi sallama." Muneeba tace, "Anjima zamu kawo maka ita sai kaga dama ka barta tazo wajen mu." _Khalil_ kuwa cikin zuciyarsa cewa yayi, "Kamar kuwa kin sani. Don ina raba Sarah da wannan gidan, ko zata zo to tabbas ina jiranta a waje, tana gama gaishe da Baba zata fito mu wuce." Kan kace me, gaba d'aya gidan su Sarah ya cika da mutane har da y'an unguwa da basu tab'a shigowa ba. Don Na'ima gida-gida tabi ta kai masu chewing gum. Bamu abunda ke tashi sai k'amshin soye-soyen nama sa, rago da kaji. Don shanu k'osassu biyu aka yanka, raguna hud'u kaji d'ari da hamsin. Y'an matan zumunta kuwa sun fi hamsin sunyi ankon wani koriyar atamfa sai hada-hada suke yi baki na motsi. Sarah kuwa komawa gidansu Munee tayi don acan suke sitting. Mai make-up tazo ta tsan-tsara mata kamar ka sace ka gudu. K'arfe d'aya da mintuna sha biyu wasu uban jiniya mai tafe da convoy na ya Abdullah suka shigo layin kasancewar k'arfe d'aya da rabi za'a d'aura auren anan masallacin layinsu. Sai ga tawagar manya-manyan mutane da abokan mahaifinsu. Jos road kamar zata tsage sabida mutane. Muneeba hannun Sarah ta kama suka koma can d'akin Baba mahaifin Muneeban sabida kiran wayarta da _Khalil_ d'in yake ta yi don wayar Sarah na hannunta. Kuma nan gidan ma a cike yake da k'awayensu na islamiya da poly. Don duk sai da Na'ima ta gayyace su. Bayan ta bata wayar ta fita. Sarah na picking ta jiyo zazzak'ar muryan _Khalil_ na mata wak'a, If you make me clean I will be clean. If you make me whole I will be whole. If you make me yours I will be yours And I won't run anymore. If I seek you, will I find you there. If I call your name will you still hear Is it too late or can I start again Can I begin again Oh. Don't ever let me go Oh... Don't ever let me go Oh... Don't ever let me go Don't ever let me go Can you drown it in the deepest sea. Can you cast it far as west from east Can you raise me up to live again So I can live again Oh... Don't ever let me go Oh... Don't ever let me go Oh... Don't ever let me go Don't ever let me go I'm surrendering my will You are crumbling all the walls I've built My defence is coming down Down I can't deny you I am broken open wide Now you can come inside My defences have come down Down I can't deny you I'm surrendering my will You are crumbling all the walls I've built My defence is coming down Down I can't deny you I am broken open wide Now you can come inside My defences have come down Down I can't deny you Oh... Don't ever let me go Oh... Don't ever let me go Oh... Don't ever let me go Don't ever let me go Oh... Don't ever let me go Oh... Don't ever let me go Oh... Don't ever let me go Don't ever let me go Don't ever let me go Don't ever let me go. "I will never let you go. Never, ever!" Fad'in Sarah. "And I'll always be there for you my love. Sai mun had'u anjima." Yana gama fad'in haka ya katse wayar. Aina'u na tsaye a tsakar gida abun duniya duk ya isheta ta jiyo shalar da ya tsayar da bugun numfashin ta zube a k'asa sume. "An d'aura auren _Ibrahim Khalil Muhammad Nurudden_ da amaryarsa _Saratu Nuhu_ akan sadaki naira na gugan nera har dubu d'ari biyar, lakadan ba ajalan ba."