Kanwar matata complete - Chapter 2
Kanwar matata complete Chapter 2: Kanwar matata complete Chapter 2. *_Chart me up 08128755583_* [09/09, 10:03 A [9/29, 12:59 PM] AMINA KABIR CAPS: _K'ANWAR…
4,863 words
*_Chart me up 08128755583_* [09/09, 10:03 A [9/29, 12:59 PM] AMINA KABIR CAPS: _K'ANWAR MATATA_*🦜
_Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_
☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️
Page 3
Hannu Sarah ta d'aura a kanta tare da fad'in, "Haba Lami wannan wani irin magana kike yi haka? Mai yasa a kullum burin ki, ki zubar min da mutunci a idanun Farouq? So kike kiyi ta danka mu a cikin gidan babu aure?" Sarah ta fad'i tana kuka sosai. Shi kuwa Farouq da idanu kawai yake bin Sarah da mahaifiyarta kamar wawa. Don sam bai son gasgata abunda kunnuwansa suke ji. "Bak'ar munafuka! To sai nayi magana. Wato baki so nima na samu rabo na ko? To wallahi komai dani za ayi shi. Juyo nan ka bani amsar tambayata, shin kai ne uban cikin dake jikinta?" Wani irin b'acin rai ne yake tasowa tun daga can k'asan zuciyar Farouq, bai iya magana ba sai kallon fuskan Sarah yake yi yana son jin wani k'arin bayani ko kuma ta k'aryata zancen da mahaifiyar nata take yi. Amma maimakon haka, Sarah sai girgiza kanta kawai take yi hawaye na zubowa daga idanunta. "Wai ba da kai nake yi bane Umar da kayi min banza kamar wata sa'ar ka!" Lami ta fad'i a zafafe. Gyara tsayuwa Farouq d'in yayi tare da kallon Lami k'asa-k'asa sannan yace, "Ban san maganar da kike yi akai ba! Kwata-kwata ma ban fahimci mai kike cewa ba Mama." Dak'uwa Lami tayi masa tare da fad'in, "Uwarka nace kaji? Ai nasan ka fahimci wannan ko! To ni menene ma na tsayawa sai naji ko kai ne kayi cikin ko ba kai bane. Bayan na san kai d'in fak'iri ne ba wani abun kirki zan samu daga gare ka ba. Amma sai dai ka sani, daga yau ban k'ara bata ko loma d'aya daga cikin abincin gidana, don sai taci ne abun cikinta zai ci, kuma ni da in ciyar da jinin ka, gwara na ciyar da karuwai goma babu lada." K'asa-k'asa Farouq yace, "Ai yanzu ma karuwan kike ciyarwa a cikin gidan." Kallonsa Lami tayi tare da matso da kunnanta tace, "Kace me?" Kau da kai Farouq yayi tare da fad'in, "No babu abunda nace!" Dogon tsaki taja sannan ta juya ta shige cikin gidan har da bugo masu k'ofa. Kicib'is suka ci da Na'ima taci uban kwalliya ta tsuke cikin k'ananan kaya kamar d'iyar arna, "Y'ar albarka har zaki wuce?" Yamutsa fuska tayi tare da fad'in, "Eh! Idan kun ji shuru ku rufe gidan kawai, don ba lallai na dawo gida na kwana ba." "To Allah ya tsare." Fad'in Lami har da d'aga mata hannu. Duk abunda Na'ima da Lami suke cewa, tsaf a kunnan Sarah da Farouq. Fitowa Na'ima tayi daga cikin gida tare da gallawa Farouq harara ta saki tsaki tare da tsirtar da yawu. Har tayi gaba, sai kuma ta dawo dai-dai inda Farouq d'in yake a tsaye tare da sauke glasses d'in fuskanta k'asa kad'an sannan tace, "Ina fatan masoyiyar taka ta fad'a maka tana d'auke da ciki har na tsawon sati biyu." Ta k'arisa maganar tana daga yatsunta biyu a fuskan Farouq d'in. Wani banzan kallo Farouq ya bita dashi mai cike da tsana. Sarah kuwa ji tayi dama tana da layar b'ata ta danna kawai ta ganta a cikin gida saboda tsananin kunya mai had'e da tsoro da take ji. Farouq yana kallo Na'imar ta bud'e gaban motar wani mutum wanda a haife ta haife ta, yaja motar suka bar layin. Juyowa yayi tare da kallon Sarah wacce kanta ke k'asa, ya jima yana kallonta tare da had'iye wani miyau mai d'aci da ya tokare masa mak'oshinsa sannan yayi k'arfin halin fad'in, "Sarah mai nake ji haka daga bakin mahaifiyarki da y'ar uwarki?" Kuka kawai Sarah ta fashe dashi do ita kanta abun jinsa take yi kamar hauka ko rainin hankali ta bud'e baki tace bata san ta yanda aka yi ciki ya shiga jikinta ba. D'agowa tayi ta kallesa tare da fad'in, "Ni wallahi tallahi....." D'aga mata hannu yayi tare da fad'in, "Na fahimta, basa son alak'ata dake ne shiyasa suke son raba mu da wannan zancen na su. Ni kuma idan har ba canza hali za kiyi ba Sarah, babu mai raba mu idan ba mutuwa ba. Ni dai alfarma d'aya nake rok'o a wajen ki Saratu, dan girman Allah ko sau d'aya kada rayuwar da y'an uwanki suke yi ya burge ki. Idan kika mun haka, ni kuma zan cigaba da tsaya miki duk rintsi, kunnuwata zasu kasance a toshe, haka babu wani suka naki ko kuma laifin y'an uwanki da za ayi amfani dashi wajen nuna min bak'inki har yayi tasiri a waje na." Kuka Sarah take yi har da shasshek'a, ita kad'ai tasan mai take ji a cikin zuciyarta. "To wai kukan na miye ne haka? Idan har ba b'acin rai na kike son gani ba, ki share wad'annan hawayen naki." Bayan hannu Sarah ta saka ta share hawayen fuskanta tare da k'irk'iran murmushin babu babu inda ya tsaya sai iya lab'b'anta. "Yauwa ko ke fa! Sannan abu na gaba, ban ji dad'in yanda ba ganki d'azu ba, na d'auka tuntuni mun riga mun gaba magana akan irin shigar da kike yi. Kin san fa da shigar jikin mutum kad'ai akan iya gane wanene shi. Dan girman Allah ki daina saka wannan zaro-zaron gashin idanu nan da wannan k'umbar dake hannunki. Ni wallahi kyama yake bani. Wanda Allah yayi maki ma ya ishe ki Sarah." Hawaye na zuba a idanunta ta furta, "In sha Allah daga yau ba zan k'ara saka d'aya daga cikin abunda ka lissafo ba." Ajiyar zuciya Farouq yayi tare da fad'in, "Allah ya miki albarka amaryata ta sati hud'u masu zuwa. Ki shiga gida hadari ne sosai a gari. Sai mun yi waya." Bata iya cewa komai ba sai murmushin da tayi tare da yi masa bye-bye ta shige cikin gidan. Tana turo k'ofa ta jingina da k'ofar tare da dafe k'irjinta da hannu d'aya sannan ta toshe bakinta da d'ayan hannun tana kuka sosai. Juyawa tayi ta lek'a ta wani d'an rami a jikin k'ofar, ga mamakinta sai ganin Farouq tayi tsaye a wajen amma ba k'ofar gidan yake kallo ba, wani wajen yake kallo daban. Can kuma ya saki ajiyar zuciya tare da tsallake kwatar dake gaban gidan ya wuce. Sai a sannan Sarah ta zame k'asa ta fashe da wani irin kuka mai tafasa zuciya. Ta jima a wajen tana kuka kamun ta mik'e ta nufi cikin gidan. D'akin su ta shiga ta cire hijjab d'in jikinta ta ninke tare da rataye sa a hannun wardrobe sannan ta cire suwaitan jikinta ta mak'ale a abun rataye jaka sannan ta kashe wutar d'akin don babu kowa a ciki, sauran y'an uwanta suna d'akin Lami kamun masu zuwa fita dasu su k'araso. Hawa kan gadon tayi ta kwanta rigingine tana sak'awa da warwarewa akan cikin dake jikinta. Sosai tayi zurfi a tunanin ta yanda aka yi ta samu ciki, sai dai duk iya zurfin tunaninta, bata gano bakin zaren ba, don zata iya dafa Qur'ani tayi rantsuwa bata tab'a sanin wani d'a namiji ba a duk tsayin rayuwarta. Daren ranar bacci b'arawo ne ya kwasheta. Kiran sallar asubahi kuwa, a kunnanta ladani ya kwad'a shi. Saukowa tayi daga kan gadon tare da kunna wutan d'akin haske ya kawo, babu kowa a d'akin, hakan ne ya tabbatar mata da ita kad'ai ta kwana a d'akin. Don da ace y'an uwanta sun dawo daga yawon banzan su jiya, babu abunda zai saka su kyale ta ta kwanta a kan gado ba tare da sun turo ta k'asa ba. Kai tsaye d'akin mahaifinta ta nufa, kamar yanda tayi tsammani hakan ce ta faru. Zaune ta samu mahaifin nata ya fuskanci gabas yana sallah a zaune. Don ciwon k'afar nasa bai barin sa yayi sallah a tsaye. Tun kusan shekaru biyar baya sallah dare ta zame masa tamkar jinin jikinsa. K'arfe uku kamar a kunnansa take bugawa saboda sabo da tashi. Bai kuma komawa bacci sai gari yayi tarwai tukun. Sarah d'aukar roban pentin da yake yin bowali tayi ta fitar dashi tare da zubar dashi a makewayi sannan ta dawo dashi ta ajiye sannan ta fita ta koma bayin ta kamo ruwa sannan ta fito ta d'auro alwala. Kamar zata wuce, sai kuma wani zuciyar ta jata ta nufi d'akin Lami. Tun daga bakin k'ofar take jin wani wawan munshari mara dad'in sauraro kamar an danne rago. Hannu ta d'an d'aura akan k'ofar ta tura, sai taji k'ofar a bud'e. Tura kai tayi ta shiga d'akin tare da lalubar bango ta kunna globe d'in dake d'akin. Lami ta hango tayi wani irin washarere a kan gadon kamar gawa, babu riga a jikinta daga ita sai d'aurin k'irji, shi kansa zanin yayi gefe, mamukanta kuwa d'aya ya kalli arewa, d'aya ya kalli kudu. Gata Ma sha Allah irin jibga-jibgan matan nan ne. Hatta bakinta a bud'e yake. Kau da kai Sarah tayi ta kalli d'ayan gefen da autarsu y'ar shekaru goma sha bakwai da watanni take. Ita ma dai bacci take yi cike da rashin tsari domin bacci ne irin wanda ba'a son musulmi ya rik'a yi wato ruf da ciki. Hannu Sarah ta kai ta d'aka mata duka cinyarta ta baya da yake a kwaye. Da sauri Aina'u ta kai hannu wajen ta Sosa ba tare da ta yanke baccin da take yi ba. Wani dukan Sarah ta kuma kai mata, wannan karan a furgice ta mik'e tana mitsitsitsike idanu tare da sakin wani irin hamma kamar d'iyar arna. Sai da ta ware rass sannan ta k'arewa Sarah kallo wutar balbalin bala'i na taruwa a kwayar idanunta. Don Aina'u irin fitsararrun yaran nan ne wad'anda duk girman mutum ko da kuwa jikinsa kaf furfurace bata raga masa. Y'an unguwanmu sun ce ita ce tayo sak halin Lami, wasu sun ce tafi Lami d'in ma. Tun tana k'ank'anuwarta makirar yarinya ce ta bugawa a jarida. Ga salo kamar wata uwar mata. "Uwar me zan maki cikin daren nan da zaki zo ki katse min bacci na!" Fad'in Aina'u kamar harcenta zai zazzago, don ta kasance irin matan nan masu harshe. Duk yanda tayi magana a hankali, ji za kayi kamar a kwar gida take magana. Da dare da rana basu da bambamci a wajenta. Yanzu haka da tayi magana kasancewar dare mai d'aukar sauti, har sai da mahaifinsu dake d'akinsa ya jiyo sautin muryanta. Hatta Lami mai bacci kamar gawa sai da ta farka a firgice tana sambatu. "Sallah nazo tashin ki kiyi. Don gashi can shirin tada sallar ake yi a masallaci. Ace duk k'arar speaker d'in masallacin can ba zai iya tada ku kuyi sallah ba!" Fad'in Sarah tana mai k'ok'arin juyawa ta bar d'akin duk da kuwa ta san cewa ba sallar za suyi ba. "Dan ubanki baza muyi sallar ba. Idan mun d'aga k'afa zamu shiga aljanna sai ki dawo damu baya saboda ta ubanki ce! Fita ki bar d'akin nan tsohuwar annamimiya!" Fad'in Lami tana mai nuna mata hanyar k'ofa. Komai Sarah bata ce ba, sai ma ficewa da tayi daga d'akin ta koma nata d'akin ta shimfida darduma ta tada salla. Tana nan zaune ko da ta idar da sallar har sai da gari ya waye tass, lokacin k'arfe bakwai sannan ta soma jin bacci a idanunta, amma kuma bata son yin baccin. Burinta ta shirya ta kuma fita domin yawon bin asibitoci ko za tayi dace da asibitin da scanning machine d'insu zai k'aryata cikin da wasu asibitocin da suke cewa tana dashi. Ta yunk'ura zata tashi daga kan sallayar taji muryoyin mata na tashi a tsakar gidan su. Gabanta ne ya buga da k'arfi sai tayi saurin d'aga labule kad'an ta lek'a waje. Da sauri ta saki labulen tana mai dafe k'irjinta da zuciyarta ke barazanar fasowa ta fito saboda arba da tayi da yayyin Farouq mata uku da kuma aunties d'insa guda biyu, gaba d'aya fuskokinsu a turbud'e..............
_Ko mai zai faru a gaba?🤔_
*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE* _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ [09/09, 10:03 AM] Matar Sayyadee: 🦜 [9/29, 12:59 PM] AMINA KABIR CAPS: _K'ANWAR MATATA_*🦜
_Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_
☀️ *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION*☀️
Page 4
"Ah'aaa! Yaya haka, menene haka kuma zuwa da sassafen na sai kace karb'an kud'in bashi? Ni fa bani son irin wannan naci tun ba'a je ko'ina ba." Fad'in Lami wacce fitowarta kenan daga d'aki baki duk miyan bacci. Bayanta kuma Aina'u ce ke mik'a tare da hamma babu addu'a sai wani "umm'iyyyyyyy!" Take fad'i kamar k'atuwar rago ko kuma bijimin sa. D'aya daga cikin matan wacce sai jijjiga take yi, ga dukkan alamu tafi kowa a cikin su hassala tace, "To dama uban me zai kawo mu wannan wulak'antaccen gidan wanda babu albarka cikinsa in ba tsautsayi ba. Banda fitina da jawowa kai jidali irinta Umar Farouq, menene abun so a cikin y'ay'an gidan nan wanda gaba d'aya kowa ya gama sanin karuwan gida ne su." D'ayar siririyar cikin sy tayi saurin cafe zancen wajen fad'in, "Aunty Bilkisu ai gansama-gansaman zaurawar gidan nan sun wuce karuwan gida, don ni kam ba zan Kira su da y'an mata tunda tun daga kan babbar har k'aramar babu wacce bata san dad'in d'a namiji ba." Saurin cafe zancen k'aramar cikin su tayi tare da fad'in, "Yo aunty Halima ai ga zahiri tunda kina ganin shegu ta kowani lungu na gidan an ajiye. Kai Allah yai wadaran naka ya lalace. Wallahi ko wucewa ta kwar gidan nan ban k'aunar yi balle har in tako k'afata cikin gidan nan." Lami kuwa dake tsaye suke fad'in duk abunda yazo bakinsu, wani shewa tayi tare da nuna wacce aka kira da aunty Halima tace, "Alhamdulillah, ko yau na fad'i na mutu za'a nuna abunda na bari ace Allah sarki ga y'ay'an wance da ta bari. Ke kuwa fa? Ko b'ari kin tab'a yi ne? Idan fitsari banza ne, kaza tayi ma. Kuma y'ay'ana Kainuwa ne, babu yanda aka iya dasu. Duk wani munafurcin ku da k'ananun maganganunku, kanku zai koma." Aunty Halima wani tsalle ta daka kamar za tayi wasar y'ar gala-gala sannan ta bugi k'irji kare da fad'in, "Haihuwa idan har irin taki ce Lami, kada Allah ya bawa ruwan maniyy d'in mijina isa ga mahaifata. Ai da Haihuwa irin y'ay'anki wallahi gwara b'arinsu. Lami haihuwa irin taki ko, na gwammaci har in koma zuwa ga ubangijina ban ajiye ko kwai d'aya a duniya ba. Kuma ki bud'e kunnuwanki dakyau kiji, idan har ni k'anwar mahaifiyar Umar Farouq ce, to wallahi auren sa da Sarah sai dai bayan raina. Domin Na'ima har gida taje ta samu mahaifiyar Umar ta fad'a mata y'arki da ake son mak'alawa d'ana, tana d'auke da ciki. Dama kuma banda hauka da rashin hankali, mai Farouq zai ci da d'iyar karuwa, tubabbiya wacce sana'ar danginsu kenan karuwanci! Mun bar maku duk wani abu da aka kawo gidan nan da sunan naiman auren y'arku, sai dai amma ki sani, babu aure tsakanin zuri'arki da namu zuri'ar." Wani irin rushewa da kuka Sarah tayi jin abubuwa da Aunty Halima take fad'i A bayyyane ta soma fad'in, "Shikenan, Farouq d'in ma ya sub'uce min. Dama na sani ba zan tab'a aure ba a rayuwata." Ta fad'i hakane tana mai kaiwa cikinta duka da duka hannunta biyu. Lami kuwa kitchen d'in dake tsakar gidan ta nufa tare da d'auko katoton tab'aryarta mai nauyi da tsayi tayo kan su Aunty Halima don har cikin ranta taji zafin maganganun da aunty Haliman tayi mata. "Aunty Halima, aunty Halima!" Siririyar mai suna Najma ta kwad'a kiran sunan aunty Halimar tare da fizgo hannun aunty Bilkisu ta janye ta baya saboda kawo tab'aryar da Lami tayi. "Barta, barta ta jawowa kanta bala'i Najma. Wallahi ba zan gudu ba, karyar hauka take yi, idan ta isa ta buga min taga abunda zai faru da ita yau d'in nan." Fad'in aunty Halima amma deep down tana jin tsoran kar Lami ta buga mata zabgegiyar tab'aryar dake hannunta. Lami kuwa k'ara yowa kansu tayi da tab'aryar ta d'aga sama zata kwad'awa aunty Halima da tayi k'arfin hali tak'i guduwa. Caraf taji an rik'e tab'aryar ta baya, a fusace ta juya suka yi idu hud'u da Sarah wacce idanunta suka kad'a suka yi jazur alamar tayi kuka. "Cika min tab'aryana ko inci ubanki cikin gidan nan!" Lami ta fad'i da k'arfi tana mai zarowa Sarah idanun. "Dan girman Allah Lami kar ki tab'a su, ki kyale su. Yanzu idan kika bugawa d'aya daga cikin su, RAI kuma yazo yayi halinsa, ya za kiyi?" Fizge tab'aryar tayi tare da fad'in, "To idan na kashe sai me? Ko kotu aka je babu wanda za tuhume ne don sune suka biyo ni har cikin gidana. Duba kiga cikin zuri'ar da kike son shiga, su kansu tun daga yanayin shigarsu zaki fahimci babu abun arziki a gidan. Daga ganin kayan jikin wannan shanyayyiyar matan (Tai nuni da aunty Bilkisu) kayan jikinta kwance ne. To a nan wajen mai na sama yaci balle ya baiwa na k'asa. Shashasha! Ni Allah ya yiwa Na'ima albarka da har taje gidan su Farouq d'in ta fad'awa mahaifiyarsa kina d'auke da juna biyu. Dama kuma nayi rantsuwa idan har ni y'ar Samuel da Debora ce ba zan tab'a bari kiyi aure da d'an iskan yaron nan ba. Sai gashi Allah ga kawo hanya mafi sauk'i. Ke bama shi ba, babu ke babu aure da kowani namiji a duniya nan." Salati gaba d'aya su Aunty Halima suka d'auka suna tafi. "Eh lallai! Yau na tabbatar da ke d'in cikakkiyar arniya kuma bakatafiya ce ke. Kin fi k'aunar suyi ta gantali a titi suna yawon hotel-hotel suna kawo maki kud'i kina musu goyon shegu ko? Tirr! Shiyasa aka ce idan za kayi aure ka auri uwa ta gari domin ta haifo maka y'a'yana nagari. To kema kan ki ba tarbiyar gare ki ba balle ki bawa y'ay'anki tarbiyan." Kamun Lami tayi magana, sai ga Na'ima da Nuratu sun shigo gidan a tare ko wacce hannunta rik'e da manya-manyan ledoji. Washe baki Lami tayi tare da fad'in, "Ka ga y'ay'an albarka wanda aka haife su tsiya na barci!" Baki sake su Aunty Halima suke kallon su Na'imar da sai wani yatsine-yatsine suke yi. "Lami akwai ruwan wanka kuwa a gidan nan? Don ni wallahi a mugun gajiye na dawo. Mutun hud'u suka yi ciniki na." Amshe maganar Nuratu tayi tare da fad'in, "Wallahi nima a gajiyan nake tib'is. Ni mutum d'aya ne ma ya d'auke ni muka tafi _Asa pyramid_, wallahi ko runtsawa banyi ba. Ruwan zafi nake buk'ata sosai in galgasa jikina." Washe baki Lami tayi tare da fad'in, "Y'ay'an albarka, y'ay'an gwal kenan. Babu ruwan zafi amma yanzu nan zan had'a wuta na d'aura maku, ku shiga daga ciki naga alama babu k'arfi a jikin ku gaba d'aya duk kun yi laushi." Su aunty Halima kuwa, wannan ta kalli wannan, sai wannan ta kalli wannan, haka su kayi tayi tsakanin su suna mamakin hali irin na Lami. "Way'annan kuma mi suke yi a nan gidan?" Fad'in Nuratu tana kallon su d'ai-d'ai. Sai da Lami ta balla masu harara sannan tace, "Wai zuwa suka yi su fad'a mana sun janye auren da suke nema na Sarah. Baki ganni da tab'arya a hannu ba, ai tahowa nayi in sheme y'an iska." Gaba d'aya daga Nuratun har Na'ima kallon Aina'u suka yi tare da fad'in, "Ke dan ubanki tsayuwar mi kike yi da baku tare ke da Lamin kun kakkarya k'ashin bayansu ba!" Aina'u tayi wani tafi tare da fad'in, "Ai ni jira kawai nake yi Lami ta fara kai hannu kiga suga yanda ake yi a cikin gidan nan, don billahil lazi babu wacce zata fita da kaya a jikinta. Sai na tabbatar mun yi masu tsirara sannan mu hankad'a su waje." Cire siririn gyalenta Na'ima tayi sannan taci d'ammara dashi tare da kallon Nuratu tace, "Maza je rufo mana k'ofar gida saboda kar su samu damar fecewa." Da gudu Nuratun ta nufi k'ofa ta saka lock tare da sakata sannan ta dawo. Wani dogo sanda wanda aka ajiye a barandar d'akin mahaifinsu Nuratu ta d'auko, Na'ima kuma ta d'auko muciya, ita kuma Aina'u ta koma d'aki ta d'auko wata murd'ad'd'iyar bulala. "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Nasiba sai da nace maku kar muzo gidan nan. Mu kira kawai a waya ya wadatar. Yanzu kinga d'aya daga cikin jahilci da rashin hankalin nasu ko." Fad'in aunty Lubabatu wacce bata cika fitana ba, asalima ita taso abi komai a hankali amma Mama ta matsa su tafi su fad'a masu sun janye neman auren. "Wai nan tsoro kike ji? Ai wallahi sarkin yawa yafi sarkin k'arfi, mu biyar ne fa!" Fad'in Rahima wacce ita ma tunda aka fara fad'an bata ce komai ba sai yanzu. "Baki da hankali hala? Gidansu fa muka iske su. Wallahi mune a ciki ko kotu aka je!" Ko kamun wani ya fara magana a cikin su, Nuratu ta shak'o wuyar aunty Halima ta baya ta kaita k'asa. Ganin haka ya saka gaba d'ayan su suka hau Nuratu da duka domin ceton aunty Halimar don tana kaita k'asa ta hau dukanta da sandar da ta d'auko. Suma su Lami na ganin haka, sai suka hau kansu da duka. Aina'u sai zabgawa ko waccen su zambad'ed'iyar bulalan hannunta take yi, Na'ima kuma tana maka masu muciyar hannunta. Kan kace kwabo, kasancewa su Nuratun da makami a hannunsu, tuni jini ya fara sharara a goshin aunty Luba, Aunty Halima da Najma. Don sun fi kowa buguwa. Ga shaidan bulala ta ko'ina a jikinsu. Sarah kuwa gefe ta koma tayi ta rusa kuka don ita kanta ta samu nata rabon wajen ceton su aunty Halimar. Baba ne ya samu ya fito da kyar don k'afar na matsa masa da ciwo sosai. Yana fitowa tsakar gidan ya tsaya turus, don tun shigowar su aunty Halimar yake sauraran komai daga ciki yana share hawayen bak'in ciki. Babu wacce yake tausayi banda Saratu don ya san ba k'aramin damuwa zata shiga ba na fasa auren nan nata da ake shirin yi. "Ke! Nuratu, Na'ima, Lami, Aina'u, wallahi kamun na iso wajen nan ku rabu da mutanan nan. Ku wasu irin yara ne kamar dabbobi. Kai ko dabba baza tayi abunda kuke yi ba. Babu wawuya mara hankali a cikin su kamar ke Lami. Wallahi kuka yi kisa a cikin gidan nan, nine nan zan bada shaida duk a tafi a rataye ku." D'agowa Lami tayi tana haki tare da fad'in, "To sai me idan mun kashe sun? Ai dama ni na jima da sanin ba k'aunar mu kake ba ni da y'ay'ana. Kana d'aka kana jin duk maganganun da matan nan suke fad'a min, amma baka iya fitowa ba, sai da kaji muna d'aukar mataki tukun zaka fito kana wani maganar banza da wofi, yara, ku cigaba da d'umamun su!" Ko rufe baki bata yi ba, su Nuratu suka cigaba da dukansu aunty Halima. Tsabar azaba aunty Luba kuka take yi tana basu hak'ura amma basu saurara ba. Baba kuwa dogaro sandar shi yayi tare da isowa inda suke ya d'aga sandar ya makawa Lami, sannan ya kuma d'agawa ya bugawa Nuratu da Aina'u, ya d'aga zai bugawa Na'ima, tayi caraf ta rike sandar tare da tura shi baya sai da ya kai k'asa k'afarsa ta markwad'e, Aina'u kuwa d'aga k'afa tayi dagangan ta take yatsun k'afarsa har da murzawa. Wani irin salati Baba ya saki tare da fashewa da kuka yana mai kai hannu kan k'afarsa da Aina'un ta mitstsike. Nuratu kuwa hannu ta saka ta dungure masa kai tare da fad'in, "Wallahi kar ka kuma ka kai hannunka jikina." Da mugun gudu Sarah ta iso wajen ta d'auke Aina'u da gigitaccen mari, sannan ta kuma d'aga hannu ta zabgawa Nuratu da Na'ima mari, sannan ta kuma d'auke Aina'u da mari don a idanunta ta mitstsike k'afar mahaifinsun. "Dan uwarki ni kika mara?" Fad'in Na'ima tana mai nuna kanta, Nuratu kuwa muciyar dake k'asa ta d'auka ta bari Sarah dashi a fuska, nan da nan fuskan ya tashi, bakinta kuma ya kumbura ya soma fidda jini don har ta wajen bakinta dukan ya samu. "Allah ya isa shegiya y'ar iska! Kuma wallahi nima sai na rama!" Fad'in Aina'u tare da yin hanyar pamfo da gudu ta d'auko bokitin da aka cika ruwa aka ajiye tayo kan Sarah wacce ke tsugunne dafe da kuncinta da Nuratu ta buga mata muciya. Sai ji tayi shaaaaa an antayo mata ruwan sanyi tun daga tsakar kanta har cikin pant d'inta. Saurin kallon gefenta tayi inda Baba yake saboda jin wani ajiyar zuciya da ya sauke, sai tayi arba dashi a jik'e shataf, don ba ita kad'ai Aina'un ta jik'a ba har da baban. Baba kuwa kallon Aina'u da Na'ima yayi yana fad'in, "Ni! Ni ko? Ina mahaifinku zaku saka hannu ku ture ni har sai da ba kai k'asa ko? Aina'u ni kika kwarawa ruwan sanyi a jiki har mitstsike min k'afa ko!" Sai kuma ya kalli Nuratu ya ce, "Nuratu ni kike saka hannu kina dungurewa kai kamar d'anki ko?" Ya fad'i hakan yana nuna kansa wasu zafafan hawaye na biyo kuncinsa. "Kuje! Duniya zata koya maku hankali." Ya fad'i yana mai fashewa da kuka tare da k'ok'arin mik'ewa. Sarah kuka take yi sosai ganin yanda jikin mahaifinsu ke wani irin rawa kuma yana kuka sosai. "Lami dan ubanki kizo ki bani abinci yunwa nake ji!" Fad'in Safwan d'an Na'ima. Saurin kallon Lami Na'imar tayi tare da fad'in, "Yanzu Lami dama yaran nan basu karya ba? Haba Lami! Haba!! Wannan wani irin wulak'anci ne. Nafa bar komai na abincin yaran nan." Marairaicewa Lami tayi tare da fad'in, "Yi hak'ura Na'ima, dama fitowa ta kenan domin in d'aura masu abincin sai ga wad'annan fitinannun mutanan sun shigo." Kallon su Na'imar tayi tare da fad'in, "Zaku fita ku bar gidan nan ne ko kuwa sai kun sake ji a jikinku?" Babu wanda yayi magana cikinsu sai ma kama junansu da suka yi suka nufi k'ofar gida. "Sake ni Saratu kije ki bud'e masu kwar gidan ki basu hak'uri ki dawo." Fad'in Baba yana mai share hawayen da suka kasa tsayuwa a idanunsa. Sarah bata sake shi ba sai da ta kai shi wajen barandarsa sannan ta nufi k'ofar gida da gudu, nan tayi arba dasu suna ta kiciniyar bud'e gidan. Hannu Sarah ta kai bayan sun bata hanya ta bud'e masu gidan tare da saurin kai guiwowinta k'asa ta shiga fad'in, "Aunty dan girman Allah kuyi hak'uri da abunda y'an uwana suka yi maku. Ku......" Katseta aunty Bilkisu tayi tare da fad'in, "Matsa mana a hanya mu wuce tun kamun nayi ball dake a nan wajen." Aunty Luba kuwa saurin cewa tayi, "Mai ya kawo maganar Ball kuma! Ke jeki gida mun ji mun yi hak'uri. Bamu hanya mu wuce tun kamun shan ruwan mu a duniya ya k'are. Wannan da muka sha ma, ya ishe mu ishara!" Ta fad'i hakan tana mai bud'e gidan. Karaf gaba d'ayan su suka yi ido hud'u da Farouq dake k'ofar gidan. Da sauri Sarah ta mik'e tana kallonsa, kallon irin na bankwana. Najma kuwa tana arba dashi ta fashe da kuka tare da soma labarta masa abunda ya faru. Wani irin yunk'uri Farouq yayi zai fad'a cikin gidan ganin yanda jini ya b'ata gaba d'aya gaban rigar aunties d'insa da k'annan nasa. Saurin rik'osa aunty Luba tayi tare da fad'in, "Bada yawuna ba wallahi ka shiga cikin gidan na, yaran da har mahaifinsu duka suke yi, to uban waye baza su daka ba a cikin fad'in duniyar nan. Farouq dama inda kake nai man aure kenan? Wallahi, tallahi ko da ace yarinyar nan ba ciki bane a jikinta, kai da ita sai dai a lahira idan da rabon auren a can. Sam wannan gidan ba gidan had'a zuri'a dasu bane." Sarah kuwa da sauri ta fito daga cikin gidan ta zube a gaban Farouq, ko kamun ta bud'e baki ya d'aga hannu ya wanke fuskanta da gigitaccen mari tare da nuna ta da hannu yace............