Kanwar matata complete - Chapter 22
Kanwar matata complete Chapter 22: Kanwar matata complete Chapter 22. "To sannu ɗan masu gida! Wai kai Khalilullah mai yasa baka da kawaici ne a rayuwarka?…
4,263 words
"To sannu ɗan masu gida! Wai kai Khalilullah mai yasa baka da kawaici ne a rayuwarka? Ƙanwar matarka ce fa! Ai ko don uwata ka raga mata. Gaskiya ka ɗauki hakki, kuma ka bata haƙuri." Faɗin Hajiya rai a ɓace. Nuna Aina'u dake riƙe da kunci yayi da hannu tare da faɗin, "Wannan ɗin zan bawa haƙuri? Kiyi haƙuri Hajiya, ban taɓa tsallake umarninki ba, amma yau kam bazan iya abunda kika umarceni da nayi ba. Hajiya hayaƙi ma ba sonsa kike yi na sani, Laure ko ina da tabbacin bata ma taɓa ganin wiwi ba bare ta kai bakinta, yarinyar dake fama da kanta ma ina taga lokacin shan wiwi! Nayi imani da Allah Aina'u ce tasha wiwin nan, kuma a yau ɗin nan kuma ba yanzu ba, sai ta bar gidan nan wallahi!" Da ƙarfi Hajiya tace, "To kuwa za kayi kaffara don Aina'u babu inda za taje wallahi! Wiwi dai ni nasha gama sauranta nan." Faɗin Hajiya ta hau waige-waigen inda zata hango saurin da Aina'u ta har a parlourn, da sauri tace, "Yauwa gashi nan!" A tare suka kai jiki, ita ta kai hannu, shi kuma ya kai ƙafa ya take sauran guntun wiwin don kada Hajiya ta kai hannu ta ɗauka. "Ai Hajiya da sauri kika yi kika rigasa ɗauka, kin ga idan kika kunna kika yi zuƙa ɗaya a gabansa wata ƙila yafi gasgata maganarki." Wani irin shaƙa Khalil ya kai mata tare da faɗin, "Hajiya zan kashe yarinyar nan sai dai nima a kashe ni." Da sauri Hajiya ta taso ta hau kiciniyar kwace hannun Khalil a wuyan Aina'un da har idanunta sun soma firfitowa, "Wallahi idan baka saki wuyar yarinyar nan ba zan tsine maka Ibrahim." Wani irin wurgi da ita yayi sai da kanta ya bugu da Centre table ɗin dake ɗakin ji kake tatsatsatsatsa ya fashe, take jini ya hau tsartuwa a kan Aina'u wacce tuni ta sulale ta sume, hannu Hajiya ta ɗaura a kai tare da faɗin, "La'ilaha illalah, Muhammadur Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallam, Khalilullah!" Da sauri Khalil ya bar ɗakin a zuciye, don shi ko a jikinsa duk da uban jinin da yaga Aina'un na zubarwa. Daga nan fita yayi daga gidan gaba ɗaya domin cuku-cukun passport ɗin Sarah. Hajiya kuwa gaba ɗaya ta ruɗe sai kiran sunan Khalil da ya jima da barin gidan take yi, Laure dake zaune itama ko motsi bata yi ba, addu'a kawai take yi a zuciya Allah yasa daga suman da tayi ta wuce barzahu kowa ya huta. Ruwa fridge Hajiya ta ɗauko ta fasa a fuskan Aina'un, a gigice ta farfaɗo tana zazzaro idanu, can kuma ta tashi da sauri jini na ɗiga ta wuce ɗakin dake mallakinta ta rufo ƙofa, bata damu da ciwon jikinta ba ta matsa tafin hannunta da ƙarfi sai ga Khalil ya bayyana a immigration office suna magana da wani, wani irin zaro idanu tayi tare da faɗin, "Barin ƙasar? To ai sai kuyi tafiyar in gani duk da kuwa na san idan asibitocin duniyar zaku zaga, Sarah baza ta taɓa samun lafiya ba." Tafin hannun ta kuma matsawa, sai ga wannan mummunar halittar ya bayyana fuska a ɗaure tare da faɗin, "To uwar ƴan ƙorafi, menene kuma yanzu?" Kallon gefe tayi tare da kai hannu ta ɗauki kwalbar turaren dake kan mirror ta fasa sannan yanki hannunta na dama tare da tsiyaya jinin a fuskan wannan mummunar halittar sannan ta ɗuka akan guiwowinta tare da faɗin, "Dan tsarkin tsafin _Hell Ofulafu_ ka taimakeni kamar yanda Khalil ya zubar min da jini, ina so shima ya ɗanɗana ɗacin da naji wajen yin kuka da idanunsa, ina son a yau ayi kukan mutuwa a cikin gidan nan, sannan a hana Khalil fita daga ƙasar nan da matarsa, bama ƙasar nan ba, a kasar masa da tunanin nemawa matarsa magani ko da a wajen Kaduna ne!" Ta ƙarisa maganar ne tare da tara kanta dake tsiyayar jini a tafin hannunta, yayin da mummunar halittar nan ya saka harshe yana lashe duk wani jini dake ɗiga a jikinta. Sai da ya gama lashewa sannan ya shiga ɓaɓɓaka mahaukacin dariya tare da turo hannu ya dafa kanta sannan ya ɓace. Lumshe idanu tayi tare da faɗawa bayi don ta san ɓacewar yana nufin buƙatarta zai biya. Khalil yana tsaye yaji kamar an kwaɗa masa guduma akai yayi saurin dafe kan tare da tsugunawa. "Lafiya Khalilullah?" Abokinsa yayi saurin ɗukawa tare da faɗin haka. Bai ce komai ba, amma ya daɗe yana jin wani irin wuuuu a cikin kansa kamun ya miƙe ba tare da yace komai ba ya nufi wajen motarsa, "Ibrahim! Ibrahim!!" Abokinsa yayi kiransa yana bin bayansa, amma ko sauraran bai yi ba ya buɗe motarsa tare da shiga yaja ya bar wajen, sai da yayi nisa da immigration office ɗin sannan ya soma jin wasai a cikin kansa. Aina'u kuwa canza kaya tayi tare da yiwa kanta dressing sannan ta kunna wiwi tasha tare codine saboda zuciyarta da yayi zafi, sai da ta zuƙi wiwi ta fesar sannan tace, "Na rantse da girman Yesu Almasihu, ba don tsananin son da nake maka ba, da wannan marin da fasa kan da kamin ba zai tafi a banza. Da sai na kashe ka a yau ɗin nan, amma duk da haka, You'll pay for it!" Nafeesa na kitchen tana dafa pasta, Qasim na parlour yana kallon Tv kwance akan resting chair dake parlourn yana jiranta ta kawo abuncin, don tun da suka tashi basu ci komai ba, "Honey kin kusa?" Ya faɗi da ƙarfi ta yanda Nafeesan zata ji daga kitchen ɗin, "Soon in Sha Allah!" Faɗin Nafeesa tana mai saka carot da ta gama wankewa, a gigice ta saki ludayin dake hannuta tare da buɗe baki za tayi ihu, cak bakin ya tsaya a buɗe ba tare da ihun ya fito ba, jininta babu inda baya rawa ga fitsarin tsoro dake zirarowo daga jikinta ganin halitta mafi muni a gabanta, harce ya fiddo kamar na maciji ya caki wuyanta ya shiga tsotse jinin jikinta, sai da ya tsotse kaf sannan ta faɗi ƙasa yaraf, shi kuma ya kai hannu ya cire pipe ɗin gas ɗin tare da haɗa gobara a kitchen ɗin sannan ya ɓace ɓat. Da mugun gudu Qasim ya fito daga parlourn jin wani irin warin gas na bala'i, yana tura ƙofar kitchen gas yayi wani irin uban tsalle ya bugi fuskansa, kan kace kwabo gaba ɗaya gidan ya kama da wuta, gas ɗin nan kuwa haka ya dunga tsalle yana faɗawa gidan maƙota. Kasancewar layine na masu kuɗi, tuni har a kira ƴan kwana-kwana na Private, kuma cikin ƙanƙanin lokaci suka iso suka fara aikinsu. Sai da aka fara cire wutan unguwar gaba ɗaya sannan aka shiga kashe wutan, mutane goma sha shida ne suka yi mummunar ƙonewa, daga ciki har da Qasim mijin Nafeesa, gaba ɗaya tun daga kai har tafin ƙafa ya ƙone, ana taɓa jikinsa fata ke biyowa, Nafeesa kuwa tattare dagwargwajajen namanta aka yi, don wasu ma dun manne a jikin tiles da wuƙa aka kankaro, babu abunda ke tashi unguwar sai koke-koken mutane. Ƴan uwan Qasim kamar zasu haukace, wasu suka nufi asibitin da aka kai shi, wasu kuma suna tare da dagwargwajajen naman Nafeesa, ya LTG Abdullah suka kira, sai dai number ɗinsa bai shiga don jiya ya bar ƙasan zuwa China. Mayar da aƙalan kiran suka yi zuwa ya Abdul-Hakeem, shikuma ya kashe wayarsa gaba ɗaya saboda tashin hankalin da yake ciki, Khalilullah da driving zai dawo gida wayarsa ta hau ringing, sai da yayi parking saboda bai ɗaga kira idan yana driving sannan yayi picking, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!" Shine abunda ya dunga maimaitawa har ya sauke wayar a kunnansa, haɗa kai da steri yayi wasu zafafan hawaye na zubo masa daga idanunsa, ya jima yana hawaye kamun yayiwa motar key ya nufi can gidan Qasim ɗin. Tun daga nesa da layin yake hango hayaƙi da ƙauri duk da an samu nasarar kashe wutan, parking yayi ya nufi inda ƴan uwan Qasim suke, maza huɗu ne da mata biyu, matan sai rusa kuka suke yi, mazan kuma sunyi jigum-jigum suna kallon naman Nafeesa. Kai tsaye wajen dagwargwajajen naman yayi tare da duƙawa yana kallo wasu maƙudan hawaye na zirarowa daga idanunsa, jikinsa har rawa yake yi tsabar tashin hankali, "Allah ya jiƙanki Nafeesa, Allah yasa kina cikin rahamarsa, Annabi yasan da zuwanki." Yana kawowa nan ya fashe da kuka tare da saka tafin hannunsa ya rufe fuskansa. Sai da Mukhtar wan Qasim ya ɗagosa tare da janyesa gefe yana bubbuga kafaɗunsa alamar rarrashi. Haɗa kai da bango Khalil yayi, hawaye sun kasa tsayuwa daga idanunsa, dakyar ya iya controlling kansa ya fiddo wayarsa daga aljihu tare da dialing number ya Abdullah, wayar bai shiga, sai ya kira layin ya Abdul-Hakeem, shi kuma switchoff, sai ya mayar da akalar kiran zuwa layin uncle Ameeru, bigu biyu ya ɗaga tare da faɗin, "Tunda naga kiranka nasan ba alkhairi zaka faɗa min ba, don haka nan baka kira ka gaishe mu, balle kuma yanzu da kayi aure kana ganin kanmu ɗaya!" "Allah yayiwa Nafeesa rasuwa ta hanyar gobara, yanzu haka ina can gidanta!" Shine abunda Khalil ya faɗi tare da yanke kiran ba tare da ya bari uncle Ameeru ya dire salatin da ya ɗauko ba. Uncle Ameeru a gigice ya kira sauran ƴan uwansa a waya ya shaida masu, nan da nan suka haɗu suka yo gida wajen Hajiya maimakon su wuce can gidan Nafeesan kai tsaye, Hajiya najin sautikan muryansu yayin tahowarsu taji gabanta ya faɗi don ta san zuwansu ba alkhairi bane, ɗayan biyu ne, ko sun zo neman kuɗi ko kuma tijarar da suka saba yi mata. Babu sallama suka faɗa ɗakin kasancewar ƙofar buɗe take don Hajiya bata kulle ƙofa idan dai ba dare bane. "Bilkisu ashe abunda ya faru kenan? Allah ya jiƙan Nafeesa, oh! Yaushe-yaushe ƴarta ta koma, ashe itama tana tafe." Da sauri Hajiya ta miƙe tana faɗin, "Ban gane ba mai kuke faɗi ba. Nafeesar ce ta mutu? Nafeesa tawa?" Kallon-kallo aka shiga yi tsakanin su uncle Ameeru, don sun ɗauka ta san da mutuwar, Uncle Shamsu yace, "Kenan baki sani ba, ɗazun nan Khalil ya kira Ameeru yake faɗa masa gobara ta kama a gidan duk sun mutu har da mijin." Hannu Hajiya ta ɗaura akai tare da faɗin, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!" Sau uku sannan ta faɗi ƙasa sumamma. Laure a sittin ta fita ta nufi side ɗin aunty Maryam ta shiga bugawa da ƙarfi, ya Abdul-Hakeem na fitowa ta kamo hannunsa ta dunga jansa har ɗakin Hajiya, da sauri ya nufi Hajiya yana jijjigata tare da tambayar mai ya faru da ita, uncle Ameeru ne ya shaida masa abunda ke faruwa, a gigice ya soma karanto Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un, can kuma ya cicciɓi Hajiyar zuwa mota ya fita daga gidan zuwa asibiti shi da Laure, su uncle Ameeru kuma suka wuce gidan Nafeesan. A can Asibiti kuwa, jinin Hajiya yayi mugun hawa, ya Abdul-Hakeem bai bar asibitin ba sai da Hajiya ta farfaɗo aka saka mata drip da kuma alluran bacci, bai samu sallar gawa ba, domin yayyafawa naman ruwa kawai aka yi saboda yanda tayi dagwargwaje, Khalil ne yace ba sai Hajiya ta ganta ba, don ganin naman Nafeesa zai iya jefata cikin mummunar hali, ko shi da yake namiji kuma doctor ba ƙaramin tashin hankali yake ciki ba. Suna dawowa daga maƙabarta da ya halartu mutane da yawa, don maza da matan unguwan kowa sai bada shaidar alkhairin Nafeesa yake yi. Sosai ta samu shaida mai kyau daga ƴan unguwa da dangin mijinta, don surukarta har yanzu bata cikin hayyacinta, wani mugun tashin hankalin suka kuma taraswa, gawar Qasim mijin Nafeesa aka dawo da ita shima ya amsa kiran Ubangiji domin ba ƙaramin ƙuna yayi ba, ya riga ya dahu sosai. Khalil dai ba ƙaramin tashin hankali suka gani ba a ranar, yayi wani irin zuru-zuru kamar wanda ya shekara yana ciwo. Haka suka kuma yiwa Qasim sallah bayan an yayyafa masa ruwa, don shima namar jikinsa sai zagwanyewa yake yi, bayan sun kai shi makwancinsa sun dawo, sai suka shiga gidansu Qasim ɗin aka yiwa juna gaisuwar mutuwa sannan shi da Laure da ya Abdul-Hakeem suka wuce asibiti wajen Hajiya duk da ƙanwarta Aunty ya Gana da Aunty Yaana suna tare da ita. Gaba ɗaya duk wanda ka kalla tsakanin ya Abdul-Hakeem da Khalil ba wanda bai zama abun tausayi ba. Hajiya kuwa ta farfaɗo amma ko iya ɗago idanu bata yi, harshenta ma har so yayi ya soma karyewa! Khalil kallo ɗaya yayiwa Hajiyar yaji hawaye sun taru a idanunsa, da sauri yaju ya bar ɗakin. Aunty Yaana da yare tayi wa Laure magana akan ta zauna ta tsaya a tsaye kamar sanda. Zama tayi tana kallon Hajiya hawaye na zuba a idanunta. Hannuta Hajiya ta kamo tare da faɗin, "Laure da gaske Nafeesa ta mutu? Da gaske babu auta Laure?" Sunkuyar da kai Laure tayi tana hawaye, Aunty Yagana tace, "Haba ya Bilki, kullu nafsin za'ikatul maut! Ki daina saka damuwa aranki, Allah ya fiki son Nafeesa, na san abun da zafi, amma daurewa za kiyi, addu'ar ki kawai Nafeesa take bukata matsayin ki na uwa. Bp ɗinki ya hau sosai, idan kina wannan kukan da damuwa ba zai taɓa sauka ba. Dan Allah ya Bilki, kiyi haƙuri ki sakawa zuciyarki haƙurin rashi." Duk cikin yaren Kanuri tayi mata maganar. Sai kuma ta kalli Laure tare da faɗin, "Je kira Khalil yazo yayi mata allurar bacci!" Da sauri Hajiya ta ɗaga hannu alamar bata so tare da danƙe hannun Laure da ɗayan hannunta. Sarah ba ƙaramin wahala taci ba, ga yunwar dake nuƙurƙusan cikinta amma ko motsi ta kasa, ji take kamar ana hura wuta a jikinta saboda wani irin azabar zafi da take ji, ta kai gudun ac ɗin ɗakin gaba ɗaya amma bata daina jin zafin ba, ta haɗa da warware fanka zuwa number ɗin ƙarshe nan ma kamar ƙara hura wutar jikinta ake yi. Ta cire kayan jikinta gaba ɗaya ya rage daga ita sai bra da pampers ɗin da Khalil ya saka mata nan ma dai bata ji wani salama ba, daga ƙarshe sai da ta cire komai na jikinta ta kwanta flat a ƙasan tiles amma still babu wani salama sai ma ƙaruwa da zafin yake yi ga kuma fitsarin da ya zama mara control yana zubo mata, don bata sanin lokacin da take jinsa, zubowarsa kawai take ji, tsutsotsin nan kuwa sun yi faca-faca a tsakar ɗakin. Da kyar ta rarrafa ta faɗa bayi ta dunga kwarawa kanta ruwa a jiki, amma da ruwan ya sauka a jikinta sai taji kamar tafasasshen ruwan zafi ta kwarawa jikinta. Fitowa tayi daga bayin ta zauna daɓar a ƙasa tare da fashewa da kuka tana sosa jikinta saboda wani mahaukacin ƙaiƙayi da ta soma ji kamar an watsa mata karara. Khalil bashi ya shigo gidan ba sai gab magrib gabansa na faɗuwa saboda bai ƙaunar yaga Sarah cikin wani hali gashi ya barta ita kaɗai kuma ya san mahaukaciyar ƙanwarta ba zuwa dubata za tayi ba. Ɗauke numfashi yayi jin wani uban ƙarni, zarni, hamami, ɗoyi da warin da saman gaba ɗaya ya ɗauka. Haka ya daure ya ƙarisa don yasan shi ɗinne dai, idan bashi ba babu mai iya jurewa, yana tura ƙofar ɗakin Sarah na sakin wani mahaukacin gyatsa mai tafe da lafiyayyar tusa mai warin fitar hayyaci, tuni ɗakin yayi wani irin duum akan wanda yake yi. Cikin sauri ya nufeta ganinta tsirara kuma kwance a ƙasa tana susan jiki, "Mine Lafiya, mai ya faru dake!" Da hannu bibbiyu ta soma turesa tana faɗin, "Ka bar nan wajen, wari kake yi, warin jikinka zai kashe ni, ka tashi ka fita nace!" Da mamaki Khalil ya hau shinshina jikinsa yana kallon Sarah, sai kuma yace, "Ɗakin ne ke wari, bari na gyara miki jikinki na gyara ɗakin zaki daina ji." Faɗin Khalil, Aina'u daka ɗakin Hajiya tana kallon komai cikin tafin hannunta ta ɗaura ƙafa ɗaya akan ɗaya tana ɓaɓɓaka mahaukacin dariya. Sarah kuwa duka ta shiga kai masa ta ko ina a jikinsa tana faɗin, "Ka fita nace, wari kake yi, kai abun kyama ne. Ka fita kabar ɗakin nan." Hannunta ya riƙo biyu tare da faɗin, "Naji zan fita, amma bari na gyara maki ɗakin tukun da jikinki." Ta jin haka sai tayi wuf ta miƙe ta shiga jifansa da duk abunda taci karo dashi a ɗakin har tayi sanadin fashe masa goshi. Fita yayi daga ɗakin yana mai matsanaicin jin tausayinta, ya bar gaba ɗaya abunda tayi masa yanzu matsayin depression ne ya kamata saboda halin da take ciki shi yasa take acting haka. Ɗakinsa ya koma yayiwa kansa dressing a goshi lokacin ana kwaɗa kiran sallah sai yayi alwala tare da wucewa masallaci. Sarah kuwa tun sanda aka soma kwaɗa kiran sallah sai taji gaba ɗaya zafin da take ji a jikinta ya kau, sai wani nannauyen bacci yayi gaba da ita. Lokacin da Khalil ya dawo daga masallaci, haka kawai ya yaji yana buƙatar jin karatun Alkur'ani, sai ya kunna ƙira'ar minshawi ya saka wayar a gaban aljihusa, kai tsaye ɗakin Sarah ya nufa, kwance ya sameta a ƙasa, a hankali ya tura ƙofar ya shiga, bai taɓa ta ba sai da ya gyara ɗakin tsaf sannan ya ajiye wayarsa da har a lokacin tana karatun ya cicciɓi Sarah yayi bayi da ita, daga can ɗakin hajiya kuwa, tun da Khalil ya kunna karatun nan ta daina ganinsa a tafin hannunta. Sarah na jinta a hannun Khalil ta buɗe idanunta da sauri tare da zabura, sai kuma ta mayar da idanu ta rufe, wanka yayi mata sannan ya saka ta ɗaura alwala sannan suka fito ya taimaka mata wajen saka pampers ya fiddo mata da kaya marasa nauyi ta saka ya bata hijjab ta tada sallah. Bata ƙara jin warin da Khalil ke yi mata ba saboda karatun da ya kunna, shima kuma bai ji mahaukacin warin ba, sai ya ɗauka saboda ya gyara ɗakin ne. Shi ya dafa masu indomie da kwai, sai da yaga ta ƙoshi tukun ya daina bata, sai taga ya jingina da gado yayi shuru, rai babu daɗi ta kallesa tare da faɗin, "Happiness, mai ke damunka?" Murmushin yaƙe yayi mata don bai ji zai iya faɗa mata Nafeesa ta rasu kuma Hajiya na kwance a asibiti ba, "Ina tunanin ki ne, Mine. Allah ya baki lafiya kinji!" Ya ƙarisa maganar yana kallonsa. Kallon indomie ɗin da tashi ta rage tayi tare da ƙarisowa wajensa ta saka hannu cikin plate ɗin ta dunga ɗebowa tana saka mashi a baki, ba daɗin indomie ɗin yake ji ba ko kaɗan, amma saboda bai son sosa mata rai sai yayi ta amsa har ya cinye. Kwanciya tayi a jikinsa tare da faɗin, "In Sha Allah zan warke" Ga mamakinta sai taji saukar hawayensa akan kafaɗanta, da sauri ta kallesa daidai lokacin da wayarsa ya hau ringing ɗin wakar _I miss You like crazy_, wani irin mahaukacin ihuu Sarah ta saki tare da toshe hancinta tana nuna masa waje alamar ya fita, da ɗumbin mamaki yake kallonta ita kuwa sai turashi take yi tana faɗin, "Fita nace! Fita daga ɗakin nan wari kake yi Ibrahim!!" Miƙewa yayi itama ta miƙe ta dunga turashi har waje sannan ta jawo ƙofar ɗakin ta rufe tare da zamewa jikin ƙofar ta soma wani irin kukan fitar hayyaci, har cikin zuciyarta bata jin daɗin abunda take masa, amma bata san mai yasa take jin wannan warin da ko ta ƙudurtawa zuciyarta zata jure sai ta kasa. Khalil ya jima a ƙofar yana mamaki, can kuma ya juya ya koma ɗakinsa. Wani irin tsallen murna Aina'u tayi daga ɗaki don tana ganin komai tun lokacin da karatun nan ya tsaya. Haka suka kwashi kwana goma suna yi, da ya shiga ɗakin domin gyarata zata hau ihu tana faɗin ya fita wari yake yi, tana kuma turashi da ƙarfi. Wani lokacin ƙarfi yake saka mata ya gyara mata jikinta da ɗakin sai ya ajiye mata abinci ya fita. Wani lokacin kuma sai ya bari sai tayi bacci sai ya shigo ya gyara ko ina don tana iya gyara jikinta ta canza pampers, zarnin fitsari da ƙarni da warin tsutsotsin naso ya kashe ɗakin don bata bari Khalil ɗin yayi abunda ya kamata. Kwanan Hajiya ashirin da uku aka sallamota, tunda suke asibitin ko sau ɗaya Laure bata taɓa sha'awar dawowa gidan ba, haka Aina'u bata taɓa taka ƙafarta taje asibitin ba. Ɓangaren Sarah sai abunda yayi gaba wajen kyaran Khalil, shi kuwa ko afuska bai taɓa nuna ɓarin rai ko ƙosawa da ita ba, sai ma wani irin nunkular kulawa da ya ƙara bata don duk tunaninsa depression ke damunta. Kamar daga sama sai ga Muneeba a gidan Sarah, sosai Khalil yayi murnar ganinta, har bedroom ɗin Sarah ya kaita, kuma a gaban idanun Muneeban ta yiwa Khalil ɗin koran kare, bayan fitarsa Muneeba ta hau Sarah da faɗa kamar ta ari baki, sai kawai Sarah ta fashe da kuka tare da faɗin, "To ni ya zanyi Muneeba, ina zan saka kaina! Ciwo duk yabi ya dame ni, tsutsotsi a gabana, wari da ƙarni gami da hamami a ɗakina. Mijina kuma duk lokacin da ya kusanto ni, wani irin ƙarni da hamami yake min!" Da idanu kawai Muneeba take bin Sarah, can kuma sai tace, "Sarah! Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!! Wani irin abu nake ji haka? Shin baba da Lami sun san wannan zancen kuwa? Ai wannan ba cutar da za ayi shuru da baki bane, dole iyaye suji don cutarki bai yi kala da cutar asibiti ba. Bari ki gani ina zuwa.." Tana gama faɗin haka ta mike tare da ɗaukar jakarta domin zuwa gida ta faɗawa mahaifiyarta abunda ake ciki domin tayiwa babanta magana ayi mata treatment na Islamic. Sai dai miƙewarta yayi dai-dai da miƙewar Aina'u da sauri tare da fitowa ta tsaya bakin gate, Muneeba na fito ta soma tafiya da sauri, sai kawai ji tayi an juyo da ita da auri tare da taɓa goshinta, "Ki kalli gabas kiyi ta tafiya kar ki ƙara waiwayar nan gidan!" Gyaɗa kai Muneeba tayi tare da kallon gabas ta hau tafiya ba tare da sanin inda ta nufa ba. Wani irin dariya Aina'u ta sheƙe dashi tare da faɗin, "Babu mai ja dani ya zauna lafiya, Khalil nawa ne ni ɗaya, don ni aka halicce shi, duk wacce tayi ƙoƙarin rabani dashi sai na ɗanɗana mata azaba, haka duk wacce tayi ƙoƙarin ceton Sarah sai na wulaƙanta rayuwarta!" Tana gama faɗin haka ta juyo ta dawo cikin gida. Cikin Sarah ya shiga na wata bakwai, still babu abunda ya canza, haka kuma Khalil shima bai taɓa canza mata ba. Aina'u ta kai maƙurar ɓacin rai ganin babu wani canji daga Khalil, sai kawai ta hau shirin tafiya Abia domin samun _Hell Ofulafu_ gaba da gaba domin tayi mai kankat.. Ranar wata asabar ta tafi, wannan karan ma Ugo ne yayi mata jagora bayan sun gama watsewarsu. Ba ƙaramin tsafi Hell yayi mata ba wannan karan, sannan sai da tayi masa alƙawarin jinin mutane goma, biyar jarirai, biyar kuma waɗanda suka soma tadawa ƴan shekaru uku zuwa goma. Sannan ya bata wani kwaɗo ƙarami yace ta haɗiye, idan har ta haɗiye duk wanda ta kalla tace yayi wani abu babu musu sai yayi, sannan kuma idan har tana son asirin da za ayiwa Khalil ya kama shi, sai ta kwanta da mahaifinta. "Idan har buƙatata zata biya ko Sarkin maka kace na kwanta dashi zan kwanta dashi." Shine abunda Aina'u tace. Kwananta uku a Abia ta juyo ta dawo Kaduna, bata sauka a ko ina ba sai gida lokacin ƙarfe biyu na dare. Banƙare ƙofar gidan tayi sannan ta shiga, ɗakin baba ta nufa kai tsaye tare da tura ƙofar ta shiga don shi bai saka sakata a ɗaki. A Zaune ta samu baban don tun lokacin da ta tura ƙofar gida ya farka, hannu ta kai ta kunna switch ɗin ɗakin tare da yin wani irin tsayuwan karuwai tana mitsi-mitsin da idanu, shi kuwa baba sai yaga gama ɗaya suffarta ta koma ta Lami sak lokacin da take amarya. Wani irin mugun sha'awa ce ta shiga fuzgar baba har bai san lokacin da ya miƙa mata hannu tare da faɗin, " _Elizabeth_" ba. Aina'u kuwa wani murmushi ta saki tare da kashe wutan ta nufe shi gadan-gadan. Cike da rashin imani Aina'u ta bari mahaifin da yayi sanadin kawota duniya ya kusanceta. Sai bayan komai ya nutsa baba ya sauko daga kan gadon a gigice ya kunna wuta, arba yayi da fuskar ƴarsa kuma autarsu tana saka brezia, hannu ya kai ya dafe saitin ƙirjinsa tare da soma nunata da hannu yana son yin magana amma bakinsa ya karkace. Take ya yanke jiki ya faɗi ƙasa rabin jikinsa gaba ɗaya ya mutu. Aina'u kuwa tana gama saka kaya ta tsallakesa ta bar ɗakin ta koma ɗakinsu. Da sassafe kamun kowa ya tashi ta bar gidan ta nufi gidansu Khalil. Sarah kuwa tun asuba ta soma jin wani irin mahaukacin ciwon mara wanda bai misaltuwa don naƙuda ta soma yi gadan-gadan duk da kuwa lokacin haihuwarta bai yi ba don cikin watansa bakwai, itace har safiya tana abu ɗaya, idan ta kai hannu gabanta tana jin gashi, amma haihuwa taƙi zuwa sai nuƙurƙusan azaba take yi. Aina'u na fitowa daga gida ta shafa tafin hannunta sai ga Sarah ta bayyana cikin halin naƙuda. Wani irin nishine ya taho mata, cikin sauri Aina'u ta haɗe yatsanta biyu ta kame gam, sai Sarah taji kamar an saka igiya an shaƙe wuyarta ga kuma kan ɗa daya soma turowa............
( _Anya Aina'u ƴar Adam ce kuwa_? 😭)