Kanwar matata complete - Chapter 24
Kanwar matata complete Chapter 24: Kanwar matata complete Chapter 24. Tsaye take a tsakiyar ɗakin tana wani irin dariya mai tafe da hawaye baƙin ciki da…
3,930 words
Tsaye take a tsakiyar ɗakin tana wani irin dariya mai tafe da hawaye baƙin ciki da kuma farin ciki lokaci guda, domin bayan tsawon shekara ɗaya har da wata uku, jiya da daddare _Hell Ofulafu_ ya dawo mata da makamanta, yanzu tana iya ganin komai ta tsakiyar tafin hannunta, sannan tana iya magana da _Hell_ da wannan mummunar halittar duk ta tafin hannun nata. Tsafinta ya ninku yanzu ta yanda tana iya ganin mutum idan taso har a jikin bango, sannan ta jikin bangon zata iya yi masa duk abunda taga dama, yanzu haka ma, tana kallon Sam'an da Sauban dake tsere a parlour, pampers ne kawai a jikinsu, tuntuni Sarah ke so tayi masu wanka amma da wannan yayi can, sai wancen ya zille yayi can, Khalil na zaune kan kujera sai dariya yake yi mata kuma yaƙi tashi ya taimaka ya kamo mata su, shekaransu ɗaya da wata uku cif, amma wayansu ya zarce tunanin mai karatu, ga magana a bakinsu kamar uwar aku. Idan Sarah ko Khalil suna so su tantancesu, sai su kira suna, misali sai suce Sam'an! To Sam'an ɗin ne zai juyo Sauban kuma harkan gabansa zai cigaba dayi kasancewar ko ita kanta Sarah sai tayi dagaske take bambance su, daga baya kamar sun gane, idan aka ce Sauban ko Sam'an, sai gaba ɗaya su juyo. Khalil ruɗewa yake yi sai ya shiga tambayar Sarah, "Dan Allah wanene Sam'an, wanene Sauban a cikinsu?" Taɓe baki take yi tare da faɗin, "Ka gano da kanka ai kai babansu ne, idan a waje aka tambaye ka yaya za kayi?" Sai Khalil yace, "To ai shiyasa nake son ki bambance min tunda ke kina gane su gudun kar inji kunya watarana!" Idan ya faɗi hakan sai ta nuna su ɗaya bayan ɗaya, ita kanta tana ganesu ne da ɗabi'unsu, Sauban yana da faram-faram kuma yana da dogon fuska, Sam'an kuma bai cika faram-faram ba, kuma fuskansa bata kai ta Sauban ɗin tsayi ba duk da shima dogon fuskan garesa, babu abunda suka ɗauko na Sarah idan ka cire dimple, amma bayan haka kaf kamannin Khalil suka yo. Wani kalan murtuke fuska Aina'u tayi ganin yanda Sarah da Khalil suke wasa suna zagaye parlourn su da ƴan biyun nasu. "Wannan shine ƙarshe farin cikinki a cikin gidan nan, ni Aina'u sai na baƙanta maki fiye da yanda kika baƙanta min, sai na wulaƙanta rayuwarki, sai na saka ki hawayen jini, sai na ruguza zuciyarki, sai na ɓalɓalta rayuwarki dana ƴaƴanki, sai na kashe ki da baƙin ciki, sai nayi kwanciyar aure da mijinki a gaban idanunki, sai na zama kishiyarki, na kuma ƙasƙantar dake. Babu aure tsakanina da mijinki, amma na rantse da Ubangijin mu Yesu Almasihu mai ceto, sai nayi tarayya da mijinki kuma a cikin gidan nan a gaban uban kowa, kuma duk wanda yace zai kawo mi shamaƙi ko shishshigi, sai na kashe shi!" Tana gama faɗin haka ta ɗauko wani icce wanda aka ɗaɗɗaure shi kamar ƴar tsana sannan ta jawo wani tulu daga ƙasan gado mai ɗauke da wani irin baƙin ruwa mai kauri sannan ta ambaci sunan Khalil sau uku sannan ta tsunduma iccen nan har sai da guiwar hannunta ya shige ciki sannan ta fiddo hannun, wani mugun murmushi ta saki tare da saka ɗayan hannunta ta fizgi gashin kanta sannan ta tura a cikin ramin idanun wannan iccen da ya koma ƴar tsana amma bana itace ba, sannan ta tsaki saitin zuciyar ƴar tsanar nan har sai da hannunta ya lume tare da ambatan sunanta sau uku sannan ta saki ƴar tsanan cikin tulun ya bata sautin 'tsumbul', sai ta mayar da tulun ƙarkashin gado tare da duƙawa ƙasan guiwowinta ta leƙa ƙarƙashin gadon ta jawo wasu ƴan tsanar guda biyar, ɗaya bayan ɗaya ta riƙa tsaka wani abu mai tsini a ƙahon zuciyarsu sannan ta jefa cikin tulun nan ta miƙe tana jin wani irin matsanaicin farin ciki ganin gaba ɗaya ɗakin ya turniƙe da hayaƙi da kuma wani irin duhu, can kuma bayan mintuna talatin komai ya washe, kuma dama _Hell_ yace idan har hakan ta faru bayan kammala aikinta, to hakan na nufin aikinta yayi! Khalil ya kai hannu zai cafki Sarah dake ƙoƙarin kama Sam'an yaji wani irin abu kamar mashi ya soki zuciyarsa da ƙarfi, wani irin baya yayi zai faɗi Sarah ta kai hannu ta riƙosa amma duk da haka sai da suka kai ƙasa saboda gaba ɗaya jikinsa ne ya saki. A ruɗe ta shiga kiran sunansa tana jijjigasa har hawaye ya wanke fuskanta, ƴan biyu kamar sun san abinda ke faruwa sai suma suka zagaye Khalil ɗin suna jijjiga cikinsa, shi kuwa duk yana jinsu, amma sai ya rasa shin a wani duniya yake, a hankali yaji zafin zuciyar na raguwa, can kuma sai ya soma jin wani baƙon al'amari na shiga zuciyarsa, kuma ya rasa shin farin ciki yake yi ko akasin haka. Zuwa can sai ya miƙe da sauri yana mai riƙe kansa, "Happy lafiya? Mai ke damunka?" Sarah ta faɗi tana mai kai hannu goshinsa, twins ma da gwarancinsu suka haɗa baki suka ce, "apy yafila? (Happy lafiya?)" Murmushi Khalil yayi tare da dungure masu kai yana faɗin, "Dan gidanku, daddy ba apy ba." Murmushi ƙarfin hali Sarah tayi don gaba ɗaya hankalinta bai jikinta, duniya bata ƙaunar Khalil yayi ciwo don bai iya ciwo ba. Kamun yayi yana jimawa, amma kuma idan ya tashi yi, kamar ba zai yi raiba haka yake. Tashi yayi tare da faɗin, "Kaina ne ya ɗan sara min, amma nasan ina shan magani zai tafi, bari naje na ɗan huta kamun lokacin sallah yayi." Gyaɗa masa kai kawai Sarah tayi jiki duk sake. Kumatunta ya kama tare da faɗin, "Smile now! Ba mutuwa zanyi ba, muna nan tare mutuwar ma baza ta raba mu ba, tare zata ɗauke mu." Duk da haka yaƙe kawai tayi, shi kuma ya hau sama ya barsu nan parlour. Jiki a sanyaye Sarah ta wuni, aikin ma dai kawai yinsa take yi. Shi kuwa Khalil, koda ya koma ɗakinsa, bai iya baccin ba, tunani kawai ya riƙa yi, can kuma ya sauko don haka nan yaji yana son zuwa side ɗin Hajiya. Saukowa yayi lokacin Sarah na ɗaya parlourn ita da yara, ba tare da ya neme su ba ya fice abunda bai taɓa yi ba. Ita kuwa Sarah bata san da fitarsa ba, ta ɗauka har a wannan lokacin yana sama a ɗakinsa. Aina'u kuma tana fitowa daga ɗakita, kai tsaye ɗakin Hajiya tayi hannunta riƙe da wani baƙin padlock, ba tare da knocking ba ta murɗa handle ɗin ƙofar da ƙarfi tare da faɗin, "Hajiya!" A razane kasancewar ita nata sihirin _Hell_ yace sai ta firgita tukun zai kamata. A razane Hajiyar ta juyo, cikin sauri Aina'u ta ɗaga padlock ɗin tare da datse shi tana dariyar samun nasara. "Aina'u kina buƙatar wani abu ne?" Hajiyan ta samu kanta da faɗin haka. Aina'u kuwa domin tabbatarwa sai cewa tayi, "Buɗe bakinki ki tsaya a haka." Nan take Hajiyar tayi kamar yanda Aina'un tace. Wani irin dariya Aina'u ta saki tare da faɗin, "To rufe bakin." Tuf Hajiya ta rufe tana mai bin Aina'u da idanu. Zaro mata idanu Aina'u tayi tare da faɗin, "Bar kallo na!" Da sauri Hajiya ta sunkuyar da kai ita kuma Aina'u ta maka mata harara tare da faɗin, "Da ace lokacin da na kira ki a waya domin ki dakatar da ɗanki ga auren yayata, kin dakatar, da yanzu kina zaune cikin lumana babu tashin hankali, amma tunda baki yi hakan ba, yanzu aka soma wasan!" Tana gama faɗin haka ta fice daga ɗakin tare da fitowa parlour dai-dai lokacin da Khalil ya turo ƙofa ya shigo, idanu huɗu suka yi da juna, wani irin ajiyar zuciya Khalil ya sauke tare da sakarwa Aina'u wani irin murmushi wanda ya kusa sumar da ita. "Aina'u!" Ya kira sunansa cikin wani irin salo, "Na'am Khalilullah mijin Saratu!" Ajiyar zuciya ya kuma saki for the second time sannan ya zauna tare da faɗin, "Zauna mana Ai'n." Yanda ya gajerta sunanta sai taji kamar duk duniya babu wanda ya iya kiran sunan kamarsa, zama tayi daf dashi kasancewar a 2sitter ya zauna, fuskantar yayi tare da faɗin, "Oh, Ai'n kamar ba cikin gidan nan kike ba, ko zuwa wajen ƴar uwarki bakya yi balle a haɗu a gaisa." Wani farrrrr da idanu tayi tare da faɗin, "To ai ku ɗinne love bird, sam baku buƙatar irin mu masu hana ruwa gudu kusa daku, kullum kafi son ganinka naniƙe jikin matarka." Kau da maganar yayi tare da faɗin, "To yanzu dai muna gayyatarki shashinmu domin taya mu hira." "As you wish, your excellency!" Dariya Khalil yayi tare da faɗin, "Sai kace wani gomna. Mu dai muna jiranki, na miƙa maki katin gayyata kullum da daddare kike zuwa kina taya mu hira!" Faɗin Khalil. "An gama ranka ya daɗe." Faɗin Aina'u. Daga nan Aina'u ta riƙa jansa da hira, sai ga Khalil har da kyakyatawa. Kamar yanda Khalil ya buƙata, da daddare sai ga Aina'u cikin wani irin mahaukacin kwalliyar ɗaukar hankali, gaba ɗaya suka kan dinning suna cin abinci ta murɗa handle ta shigo, Khalil ne ya fara juyawa fuskansa ɗauke da murmushi yana mai faɗin, "Ƙariso nan Aina'u ayi dinner ɗin dake. Sauban na riƙe a wajensa, jin muryan Aina'u duk sai ya rikice yana neman guduwa wajen uwarsa, Sam'an dake wajenta riƙe hannunta yayi gaam jikinsa na rawa. Sarah kuwa murmushi tayi tare da faɗin, "Aina'u kenan, kamar ba gida ɗaya muke ba! Ko kin koma gida ne?" Taɓe baki Aina'un tayi tare da faɗin, "Baki so gani na bane kawai." Ta faɗi hakane tare da jawo kujeran kusa da Khalil ta zauna a kai tare da kallon Khalil ɗin tare da narke fuska. tana mai faɗin, "To ayi serving ɗina mana, ko da kaina zanyi." Cikin sauri Khalil ya miƙe tare da ajiye Sauban, shi kuwa dama abunda yake jira kenan da gudu ya nufi gun mamarsa yana kuka, ita kuwa Sarah wani irin maɗaukakin mamaki ne ya rufeta ganin yanda jikin Khalil yake rawa don kawai zai zubawa Aina'u da basu taɓa ga macijiba abinci. Sai kawai ta zuba idanu tana kallon ikon Allah. "Ai'n ga couscous, ga jellof rice, wanne za'a zuba maki?" Ɗaga idanu sama tayi tare da faɗin, "Wanda kake ci shi zaka zuba min." Jellof rice ɗin ya zuba mata tare da kaza sannan ya ki plate ɗin har gabanta tare da faɗin, "Gashi _Ƙanwar matata_" wani irin ƙululun baƙin cikine ya mamaye zuciyar Aina'u jin sunan da ya kira ta dashi wai _Ƙanwar matata_! "Nafi gaban haka wallahi!" Aina'u ta faɗi cikin zuciya, amma a zahiri sai tayi wani irin murmushi tare da kallon yanayin Sarah ta gefen idanu, abun yayi wa Aina'u daɗi ganin confusion a idanun Saran. Spoon ta saka ta ɗebo abincin tare da sakawa a baki, lunshe idanu tayi jin wani daɗi da ya mamaye kunnuwanta don Sarah gwana ce wajen iya girki duk da ba yi suke yi a gida ba. Aina'u na cin abinci a lokaci guda kuma tana jan Khalil da hira, shi kuma kamar wani wawa ya saki baki sai ɓaɓɓaka dariya yake yi. Sarah miƙewa tayi ta bar wajen zuciyarta na susa, duk da tasan babu aure tsakanin Aina'un da Khalil ɗin idan dai har ba mutuwa tayi ba, sai taji wani irin matsanaicin kishi da damuwa yanda Khalil ɗin ya manta tana wajen, da dane, Aina'u bata ma isa ta ƙariso inda suke ba balle har ta zauna kusa dashi, da bata jin daɗin yanda Khalil ɗin yake ɗaurewa Aina'un fuska ganin su Na'ima yanzu har wani respect yake basu matsayin yayyin matansa, amma kuma ya kasa sabawa da Aina'u, sai ta bar hakan matsayin rashin haɗuwar jini, amma yanzu lokaci guda da taga wannan sauyin duk sai taji matsanaicin damuwa ya kamata. Bayan ta hau sama sai ta canzawa twins pampers tare da saka masu kayan baccinsu sannan ta sayar dasu har bacci ya ɗauke su lokacin ƙarfe tara da mintuna biyar amma har yanzu Khalil bai dawo ba, kwanciya tayi tare da rufe idanu amma sai taji gaba ɗaya baccin yaƙi zuwa, tashi tayi ta sauka a kan gadon tare da fitowa ta tsaya daga nan sama tana hangen Khalil kusa da Aina'u kamar zasu shigewa juna yana nuna mata abu a waya suna dariya. Da sauri ta juya ta bar wajen saboda bata son kawo zargi a zaman aurenta dashi. Ko da ta koma ɗaki, sam bacci ya kasa zuwan mata sai juyi take yi tana saƙe-saƙe a zuciya tare da duba agogo a wayarta, sai da agogo ya buga ƙarfe ɗaya sannan taji buɗe ƙofar Khalil ya shigo ɗakin, tana jinsa ya shiga toilet yayi wanka kasancewar kullum zai kwanta sai yayi wanka, kayan bacci ya saka sannan ya hayo gadon tare da gyarawa twins kwanciya ya mayar dasu ƙarshen gadon ahankali gudun kar su tashi sannan ya jawo Sarah jikinsa ya rungume, duk tana jinsa sai tayi kamar bacci take yi har ta soma jin saukar numfashinsa alamar baccin ya ɗaukesa. Ajiyar zuciya ta sauke domin ta rasa wani irin tunani za tayi, sai wajajen ukun dare bacci yayi gaba da ita. Washa gari da sassafe bata nuna masa komai ba ta haɗa masa breakfast da duk abunda zai buƙata, haka kayan da zai saka bayan ya fito daga wanka. Ita ta taimaka masa ya saka kayan sannan yayiwa twins kiss a kumatu kasancewar basu farka ba sannan suka sauko ƙasa tayi serving ɗinsa ya karya. Sun rabu kamar kullum bayan yayi hugging ɗinta tare da yi mata kiss ita kuma tayi masa addu'ar Allah ya tsare sannan ya tafi. Da sauri Aina'u dake kallon komai a bangon ɗakinta dake shashin Hajiya ta fito cikin uban kwalliya tare da isa inda yake yana ƙoƙarin buɗe mota, "Manyan gari kenan, har za'a fita ba tare da an ganni ba!" Da sauri Khalil ya kalleta tare da faɗin, "I'm so sorry Ai'n, na kusa nayi latti ne shine nake sauri, kin san jiya mun sha hira, abunda ya makarar dani kenan." "Kar inzo yau kenan?" Faɗin Aina'u tana wani kashe idanu. Waro idanu Khalil yayi tare da faɗin, "Wa! Ai ko da har ɗakin Hajiya zan biyo ki, baki san yanda hira dake yake matuƙar sani nishaɗi ba ko? Kar ma ki fara min wannan wasan." Wani shu'umin dariya Aina'u tayi tare da faɗin, "Hakane! To mu fita tare ka ɗan rage min hanya nima dama fitan zan yi." Da sauri ya buɗe mata gaban mota sannan ya zagaya ya shiga mazaunin driver yaja motar suka bar gidan. Sakin labule Sarah tayi tare da jinginar da bayanta jikin window ɗin tana faɗin, "Ya Allah ka tausaya min kasa ba abunda nake tunani bane akan mijina da ƙanwata. Wunin ranar sukuku tayi sa, ƙarfe shida Khalilullah ya dawo kamar yanda ya saba, sai dai kuma tare suka dawo da Aina'u kamar yanda suka fita tare, kasancewar Sarah na ɗakinsa tana fesa airfreshner, sai tayi saurin ɗaga labulan window jin ƙarar motarsa, gabanta ne ya buga da ƙarfi ganin Aina'u ta fito daga motar hannunta ɗauke da wata ƙatuwar leda bakinnan kamar zai yage tsabar washesa da take yi. Sakin labulan tayi tare da saukowa ƙasa sauri, buɗe ƙofar Khalil yayi ya shigo fuska ɗauke da fara'a, ganin yanayin matar tata duk sai jikinsa yayi sanyi, gashi tayi bala'in kyau cikin wani Indian material da tayi ɗinkin straight gown dashi, gashin kanta kuma ta kama shi in a middle ponytail, jelar gar dokin wuyanta, fuskanta yaci makeup mai ɗaukar idanu, "Wife, lafiya naga fuskanki haka?" Maimakon ta bashi amsar tambayarsa, sai cewa tayi, "Ina kuka je kai da Aina'u? You left this house together and you also came back together." Murmushi yayi tare da faɗin, "Wai Aina'u? Rage mata hanya nayi wai zata wajen ƙawarta, luckily kuma sai muka sake haɗuwa shiyasa muka dawo tare." Sarah bata iya cewa komai ba sai kallonsa da ta riƙa yi, "Come on, smile!" Ya faɗi yana mai bata side hug. Yau ma dai irin na jiya aka kuma, Aina'u ta kuma zuwa kuma still sai 1am Khalil ya dawo ɗakin, abun na matuƙar damun Sarah a zuciya, sam bata samun kulawar Khalil yanzu, ya kai yanzu ko kwalliya tayi bai kallo bare ya yaba, girki kuma Aina'u ta koma yi masa, idan Sarah ta zuba masa abinci, sai yace mata Aina'u zata kawo masa, tun Sarah na daurewa kusan sati Uku, har ta zuciya wata rana taje har side ɗin Hajiya ta samu Aina'u a ɗaki bayan Khalil ya wuce asibiti, zaune take tana kallon tafin hannunta, ba kowa bane a ciki sai Khalil dake zaune yana duba petient, bata san da zuwan Sarah ba kasancewar ba ita take kallo ba a wannan lokacin, turo ƙofar da Sarah tayi ne ya dawo da ita cikin hayyacinta tayi saurin kallon ƙofar don tasan Hajiya da Laure ko giyan wake suka sha baza su shigo mata ɗaki ba, wani kallon banza ta watsawa Sarah da taga itace a ƙofar ɗakin, a zuciye Sarah ta ƙarisa ɗakin tare da ɗauke Aina'u da mari sannan ta nunata da yatsa tare da faɗin, "Dan ubanki ki tattara kayanki ki bar gidan nan, idan ba haka ba, sai na kakkaryaki, shegiya ƴar iska, na gama gane take-taken ki, so kike ki ɗauke min hankalin miji ko? Don baki da kunya mijina kike so? To wallahi ahir ɗinki! In the first place ma na kasa gane uban da kike yi cikin gidan nan tunda ba gidan ubanki bane, to ki saurareni da kyau, ki tattara ki bar gidan nan tun kan inyi maki watsi da kayanki wallahi. Wawuya shashasha!" Tun da Sarah ta fara magana har ta dire Aina'u ko tari bata yi ba sai ma wani murmushi da take yi, amma deep down ita kaɗai tasan mai take shiryawa cikin zuciyarta. Sarah kuwa fita tayi tare da banging ƙofar. Har akai kwana uku Sarah bata kuma ganin Aina'u ba, sai tayi tunanin ko taji abinda ta faɗa mata ne ta bar gidan, sai dai kuma gaba ɗaya ta kasa gane kan Khalil, don wani lokacin har mancewa yake yi idan zai kirata sai yace, "Aina'u." Sarah gaba ɗaya hankalinta ya tashi ta soma tunanin mai Aina'u tayiwa Khalil haka. A ran kwana na huɗu, kawai sai ganin Khalil tayi ɗauke da akwatin kaya, Aina'u a bayansa shikuma ransa a mugun ɓace, a nan gaban Aina'u ya hau Sarah da faɗa abunda bai taɓa yi ba, "Wannan wani irin haukane da jahilci! Ƙanwar taki kika kora a gidan nan saboda selfishness ɗinkin? Kin bani mamaki Saratu! To yanzu na dawo da ita da kaina, she will stay here with us." Yana gama faɗin haka ya ɗauki akwatin tare da kallon Aina'u yace, "Ai'n, follow me." Da sauri Sarah tasha gabansa tare da faɗin, "Aina'u bata da ɗaki a sama." "Let go of my way Sarah Nuhu! Kar ki ja inyi maki abunda ban taɓa yi maki shi ba a daran nan." Baki sake Sarah ke kallonsa, yayin da Aina'u ke wani irin shu'umin murmushi. A gaban idanunta Aina'u ta bi bayan Khalil suka haura sama. Da daddare bayan Khalil ya dawo ɗakin Sara, don yau sun kai kusan 2am suna hira da Ai'n kamun ya dawo ɗakin Sarah. Sai da ya gama komai ya hawo kan gadon sannan Sarah ta miƙe ta zauna tare da kunna bedside lamp tare da faɗin, "Ka tashi za muyi magana Please!" A raunane tayi maganar yanda zai ji tausayinta, amma ko juyowa bai yi ba don juya mata baya yayi abunda bai taɓa faruwa ba tunda suka yi aure. Ƙara maimaita abunda tace tayi a karo na biyu, a fusace ya juyo tare da faɗin, "Baccin baza ki bari inyi cikin salama ba? Wato kin ɗauko wani hali da ba naki ba kin ɗaurawa kanki ba? Saboda tsabar kishi da rashin sanin ya kamata, shine za ki riƙa kishi da ƙanwarki ciki ɗaya, Aina'u fa ƙanwarki ce, _Ƙanwar matata!_ kin taɓa jin inda miji ya auri ƙanwar matarsa uwa ɗaya uba ɗaya kuma ba mutuwa tayi ba? Ni dalla malama kin isheni!" Yana gama faɗin haka ya fita daga ɗakin tare da bugo mata ƙofar da ƙarfi sai da twins suka firgita tare da tsala ihu. Aina'u kuwa daga ɗakinsa tana kallon komai, daga ita sai wata ƴar iskan rigar bacci da babu komai a ciki ta fito ta tsaya a bakin ƙofa, Khalil na zuwa wajen ta jawo hannunsa tare da shigo dashi ɗakin sannan ta murza key. Narai-narai tayi da fuska tare da shafa fuskansa zuwa ƙirjinsa ta shiga faɗin, "Kayi haƙuri ta hanaka bacci ko? Kar ka damu idan ita bata sonka, Ni ina sonka kuma zan kula da kai." Wani irin babu daɗi Khalil ya dunga ji amma bai san mai yasa ba ya kasa hanata abunda take yi, hannunsa ta kamo ta zaunar dashi a bakin gado tare da zama akan cinyarsa ta kamo ƙeyarsa tare da haɗe bakinsu waje ɗaya. Da sauri Khalil ya rufe idanu gabansa na faɗuwa da ƙarfi, can kuma ta ɗaga shi tare da turasa ya kwanta flat sannan ta hau kanshi ta shiga kissing ɗinsa, shi kuwa Khalil bai son lokacin da ya biye mata ba..........
_Na san yau zan sha caccaka, wallahi har gabana faɗuwa yake wajen rubuta page ɗin nan saboda nasan akwai wanda zasu tsine min tabbas, amma don Allah abunda nake so daku, kar ku kalli wannan page ɗin a wani mahanga ta daban, wallahi ko Khalil da Sarah + Hajiya suna addu'a da sauke Qur'ani kullum, abunda Allah ya rubuta sai ya faru, mutum bai taɓa wuce ƙaddararsa, Fiyayyan mahalicci ma asiri ya kamasa balle wani kashi Khalil_
*👭GARKUWAR MATA* *Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci* *GA* *Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa* Rage tumbi💯 Nono💯 Sanyi💯 Karin kiba💯 girmar hips💯 Ni'ima💯 Sabulai💯 Humra💯 Turarukan wuta💯 Matsi💯 Miski💯 Dilka💯 Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI *08089965176* *07084653262*
*_MATAR SAYYADEE_*
*Paid book 08128755583*
🦜 *KANWAR MATATA* 🦜
*32*