Kanwar maza 1 and 2 Complete - Chapter 5
Kanwar maza 1 and 2 Complete Chapter 5: Kanwar maza 1 and 2 Complete Chapter 5. Yasir ya ce "Wallahi mama hakan ma ta gode sosai Allah ya saka da alkhairi,…
3,307 words
Yasir ya ce "Wallahi mama hakan ma ta gode sosai Allah ya saka da alkhairi, ya ƙara buɗi, ai kin yi ƙoƙari, ke Ruma wannan rigar idan ki ka sakata ai ba sai kin ɗaura zanin ba, kaɗan ya rage ta zama doguwar riga, idan kuwa zaki ɗaura zanin sai ki ɗaura shi a kam rigar, ki yi ɗaurin barmana coge wallahi kyau zaki yi" Gaba daya ta fuskanci Yasir rashin mutunci kawai yake yi mata, kamar zata fashe haka ta tattare kayan ta kai ɗaki ta zubewa Mama a kan kujera, ta barwa ranta cewa gara tayi zamanta a gida da salla, da ta saka wannan zulumbuwar rigar a matsayin kayanta na salla ta fita ayi mata dariya.
Mama ta fita yin barka a maƙwabta, hakan ya bawa Yasir damar zama ya sanya Ruma a gaba ya dinga tuntsira mata dariya, duk wanda ya shigo sai ya ɗauko masa kayan ya nuna masa, daga atamfar har ɗinkin irin na zamanin su Mama ne. Huzaifa ya fi kowa ƙyaƙyatawa, ya ce "Lallai mama ta iya punishment, ai ni ta biyani da aka miki wannan ɗinki, kamar yadda Yasir ya faɗa, idan ki ka saka kayan nan, ki ka kafa ɗauri irin na barmana mu samo ƙorrai, da sallar nan mu baza kiɗan ƙwarya a cikin unguwa, wallahi kuɗi zamu samu, dan dama mutane duk sun watsar da al'ada". Abdallah har da yi mata magiya a kan ta gwada kayan yanzu, ya ga yadda za su yi mata. Tayi musu banza ta koma gefe ta ci magani. Yaya Usman ne ya zare mata ido, wai sai ta gwada kayan sun ga yadda za suyi mata, kasancewar tana shakkarsa shima, haka ta je ta saka kayan ta fito tana danne kukan da yake ƙoƙarin ƙwace mata. Tana fitowa tsakar gidan Huazaifa ya bushe da dariya ya ce "Waya ga babba da jaka".
Abdallah ya ce "Allah ya bar mana Delun mu, wallahi dama delun aka saka miki, kin yi kyau".
Usman Ya ce "Abdallah, yi mata ɗaurin barmana cogen, mu gani, zan mata video" Duk yadda ta so haɗiye kukan sai ta kasa, sun kewayeta sai dariya suke kamar sun ga mahaukaciya, ga Usman yana yi mata video da wayarsa suna dariya. Huzaifa sai kifawa yake, kamar wanda ya zare, yana cewa Usman"Ka yi mata hoton da Black and white mu ce ga kakar su Mama 1940" Babu tsammani Umar ya shigo, ya tarar da Rumaisa a tsaye kamar an dasa ta, ga uban ɗauri a ka, ta ɗaura zani a kan riga, tana tsaye tana kuka su kuma sun kewayeta suna dariya.
"Meye haka?" Yayi maganar a kausashe.
Usman ya ce "kayan sallarata ne, aka kawo take ta rashin mutunci wai bata son kayan, shine nake punishing ɗinta, nan gaba ta koyi godiya ga Allah a kan duk abin da ya bata, sannan ta godewa wanda ya batan". Shi kansa Yaya Umar ji yayi kamar ya yi dariya, saboda yadda Ruman tayi a kayan, kai da gani ka san sun yi mata yawa, sai tayi kamar wadda ta kawo tallan kalwa birni. Gimtse dariyarsa yayi ya wuce ɗakinsu, suka gama yi mata rashin mutunci sannan suka sallameta.
Da ta koma ɗakin ma, sai da ta sha uban kukanta, ta cire kayan ta ajiye tana jin yadda ranta yayi mugun ɓaci a kan abinda suka yi mata.
Kasancewar yau ba tuwo mama tayi da daddare ba, ya sanya ruma zaman cin abincin dare ba tare da mita ko ƙunƙuni ba, ga kuma uwa uba a ƙule take da rashin mutuncin da su Yaya Abdallah suka yi mata. Tana ta lissafa yadda zata rama abin da suka yi matan ta huce. Duk da yadda yau tayi shiru, babu wanda ya kula da shirun nata, dama mama na jin haushin tayi mata abu ta kushe, mama ta mayar da hankalinta kan 'yan mazanta suna ta hira.
"Mama ina da tambaya" duk suka waiwayo suka kalleta.
mama ta ce "To ina jinki, Allah ya sa na sani"
"Wallahi na san ƙarshenta banzayen tambayoyinta ne marasa kan gado, dan Allah mama kar ki saurareta" Huzaifa yayi maganar yana kallon Ruma.
Cikin tsiwa ta ce "Ban kasa da kai ba, dan haka babu ruwanka da ni".
Mama ta ce "Yi tambayarki ina jin ki"
"Yauwa, dan Allah kar na tambayeki kuma kice mini sai an kwana biyu, menene Janaba, kuma meye fyaɗe!!!"
Ayshercool 08081012143
Kar a manta ayi subscribing YouTube channel ɗina domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
[20/06, 6:52 pm] JAKADIYAR AREWA: ƘANWAR MAZA
Na Aisha Adam (Ayshercool)
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Ku yi subscribing YouTube channel ɗin @Cool Hausa Novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro. Ku yi following ɗina a arewabooks a kan account ɗina na ayshercool7724 Ko watpad Ayshercool7724 kowanne a cikin manhajojin za ku iya samun litattaiafaina da na yi a baya, da wanda nake yi a yanzu na gode.
P5
Sak suka yi gaba ɗayansu, lomar da Yaya umar ya haɗiya ya ji taƙi wucewa tana kai komo a wuyansa kamar zata dawo. Amma ya basar kamar bai san me suke faɗa ba.
Huzaifa kuwa tsam ya miƙe yana faɗin "Ai sai da na ce kar ki saurareta ki ka ƙi, sai ku san abin da zaku gaya mata" yana maganar ya bar tsakar gidan. Mama ta rasa mai zata cewa Ruma da hankalinta zai ɗauka, sam yarinyar bata tunani dai-dai da shekarunta.
"Wai ya na ji kin yi shiru? Me kuma nayi?" Ta yi maganar cikin taɓara.
Cikin ƙarfin hali mama ta ce "Ke a ina ki ka ji wannan kalmomin da ki ka tambayeni?"
"Mama ya kuma ki ke tambayata bayan nima tambayarki nayi"
"Ki amsa mini dan ubanki" mama tayi maganar a hasale.
Ta ɗan cuna baki sannan ta ce "Ba wani ne ya gaya mini ba, kece ki ke jin radiyo ranar, na ji ana cewa ayi wankan janaba idan aka yi ko me? Oho na manta shi ne nake son na san meye janaban, kuma meye wankan. Shi kuma fayɗe idan aka faɗa a radiyo sai na ga hankalinki ya tashi kina girgiza kai kina Allah ya tsare zuriyar musulmi baki ɗaya, shine nake son na san menene?"
"Tirƙashi, aiki ga mai ƙareka mama Allah ya bamu alkhairi " Yaya Aliyu ya faɗa yana ƙoƙarin shigewa ɗaki.
Yaya Usman ya ce "Kuma duk abin da ake faɗa a radion babu wanda ki ka riƙe sai wannan?"
Ruma ta ce "To ai akwai wasu ma, mantawa nake yi ne sai yanzu na tuna"
Mama tayi ajiyar zuciya ta ce "Kina jina ko Ruma?"
"Eh ina jinki"
"Yauwwa, zan gaya miki zan miki bayani, amma ba yanzu ba sai an kwana biyu, yanzu ko na yi miki bayani ba zaki gane ba, kuma nan gaba ko ba a gaya miki ba ma, zaki gane da kan ki".
Cike da yarinta ta ce "Nan da kwana biyu ranar asabar kenan, in Allah ya yarda zan tuna miki ki gaya mini"
"Ba wanna kwana biyun nake nufi ba hansai, sai kin ƙara girma da hankali"
Cikin mamaki Ruma ta ce "Yaushe kuma zan ƙara girman da hankali, wancan karon ma fa na taɓa tambayarki menene MATA MAZA, ki ka ce mini sai na girma, na tambayeki menene haila ki ka ce mini ba yanzu ba, amma da zan yi wani abun sai ki ce ina girma amma bana hankali wane irin girma ki ke son nayi to?"
"Ke tashi ki wuce ki kwanta dan uwarki, kawai kin saka mutane a gaba da tambayoyinki na shirme, ko a gidan uban wa ki ke jiyo wannan manyan maganganun oho miki, wuce kan na karya ki biyu, ba zaki tambayi abu daidai da hankalinki ba sai wanda ya fi ƙarfin kanki" sai da ta kalli in da Yake zaune yana bata umarni, bayan da fari yayi kamar bai san me suke yi ba.
A hankali ta tashi ta nufi ɗaki, tana tunanin menene aibun tambayarta?.
Tafiya ta yi ɗaki, ta gyara shimfiɗarta ta kwanta, tana tunanin meyasa kullum tayi tambaya sai ace mata ba yanzu ba sai an kwana biyu, ko ace wai tana tambayoyin da suka fi ƙarfin ƙwaƙwalwarta me hakan yake nufi kenan?. Da wannan tunane-tunanen bacci yayi awon gaba da ita.
Da safe tana kwance tana baccinta, duk samarin gidan sun gama komai, har abin karyawa, Kasancewar Asabar ce Ruma tana ta baccin asara, ba aikin fari balle na baƙi, har ƙasan ranta tana matuƙar jin daɗin rashin zuwa makarantar allo da ba ta yi, saboda tana samun isasshen lokacin bacci. Ji take ina ma ace bokon ma ta daina zuwa, idan tayi baccinta ta ƙoshi da yamma ta kfa suyar wainar fulawa a ƙofar gida ta tara 'yan kuɗaɗenta. Baccin yayi mata daɗi, tayi nisa sosai a duniyar mafarkai kala-kala, ta ji kamar daga sama ana taka mata ƙafa. Buɗe ido tayi a hankali, amma taƙi motsawa, tana son ta tabbatar da a zahiri ne ko duk cikin mafarkin ne. Ji tayi an kuma zungurarta da ƙafa, ba tare da ta waiwayo ba ta ce "Wallahi Huzaifa zan maka rashin mutuncin da baka taɓa tunani ba, kar ka sake takani" Bai ji kashedin ba, ya sake haurinta da ƙafa, "Allah ya isa wallahi, kuma ba zan tashi ba" tayi maganar tana sake dunƙulewa a wuri guda.
Ƙashin bayanta ya kuma daka da ƙafarsa, ta yinƙuro a matuƙar zafafe, da nufin ta kafa masa haƙora ko a ina ne, amma me tayi tozali da Umar a tsaye a kanta. Jikinta ne ya hau tsuma, ta ma rasa me za ta yi, ko ta ce. Shiru yayi yana nazartarta, daga bisani ya ce "Ki tashi ki je ki ki yi wanka ki karya ina jiranki, kuma idan ki ka ɓata mini lokaci kin san sauran"
Saroro tayi tana kallonsa, da ba ta gama fahimtar me yake nufi ba.
"Za ki tashi ko sai na yi ball dake?" Cikin hanzari ta tashi, ta ɗauke katifarta ta nufi banɗaki tana mamakin to ina zasu je, kar dai boarding ɗin zai kaita kamar yadda ya ce. Gabanta ne ya faɗi ta fara tunanin ko ta gudu. Kai tsaye ta nufi banɗaki, tana shiga ta tarrar da an haɗa ruwan wanka, ba tayi tunanin ko ruwan waye ba, ta rufe ƙofa ta hau wanka da shi.
Yasir ne ya nufo banɗakin da sauri, wuyansa ɗauke da soson wankansa, zai shiga banɗaki saboda ya kai ruwan wankansa, amma yana zuwa ya ga ƙofar a rufe. Iya ƙarfinsa ya hau dukan ƙofar yana faɗin "wani ɗan rainin hankalin ne ya shiga bayan na kai ruwa?"
Gyran murya tayi masa, tsaki ya ja ya ce "Ki hanzarta zan yi wanka na fita na kusa makara. Tun yana saka ran zata fito har ya tashi ya fara zaginta yana bugun ƙofar. Ba ta da tabbacin wankan da tayi ta fita, ta buɗe ƙofar banɗakin, zagi ya dinga surfa mata, bai kai ga rufe baki ba, idonsa ya sauke a kan bokitin da ya haɗa ruwa, Ruma ta zubar da komai.
A hasale ya zura hannu ya janyota tsakar gida ya ce "Wallahi yau mai ƙwatarki sai Allah, na zuba ruwa na kai zan fita makaranta kina can kina bacci, amma ki zubar mini". Babu alamar nadama ta tsuke fuska ta ce "To ba Yaya Umar ne ya ce nayi wanka ba"
Wani ranƙwashi ya yi mata a tsakiyar ka, da azabar zafinsa ya sanya ta durƙusa a kan gwiwoyinta, tana sakin wani irin kuka mai sauti.
Yaya Umar ya ɗaga labulen taga ya leƙo ya ce "Ƙyaleta tun da ka daketa" ba ƙaramin ɓaci ran Yasir yayi ba, dan niyyarsa sai ya yiwa Ruma dukan da duk taurin kanta sai ta bashi haƙuri.
Kasa karyawa tayi saboda kuka, tana tsaye tana duru-durunta, Umar ya shigo hannunsa riƙe da leda ya miƙa mata ya ce "Maza ki shirya ki wuce mu tafi"
Karɓar ledar tayi tana duddubawa, uniform ne na islamiyyar su Huzaifa, makarantar da ta ce ko aljanna ake rabawa a cikinta ba zata yi ta ba, saboda azabar tsaurinsu, asabar da lahadi tun tara sai biyar ake tashi, ba a fashi balle makara, ga haddar Alqur'ani ake yi da gaske ba wasa ba. Saroro tayi tana kallon Yaya Umar, cike da rashin fahimta amma ta kasa yi masa Magana.
Wata uwar harara da ya yi mata ne, ya sanya ta shiga ɗakin Mama, ta saka uniform ɗin jikinta sai tsuma yake yi, ita ta san har ga Allah ba zata iya zaman makarantar nan ba. Mama dai ba ta ce musu kanzil ba, ya tasa ta a gaba suka tafi.
A zuciyarta tana ta addur Allah ya sa makarantar suce ba zasu karɓeta ba, bata tunanin ko su Huzaifa sun san za a sakata a makarantar su, dan da sun sani cewa zasu yi basu yadda ba.
Tun da suka shiga makarantar, tashin karatun Alqur'ani kawai ka ke ji, daga kowacce kusurwa, kuma da alama ɗaliban makarantar a nutse suke. A ofishin shugaban makarantar aka titsiye Ruma ana yi mata interview, amma ba abin da ta iya, izifi biyun da aka yi mata tambayoyi da ƙyar ta kai.
Umar ya shiga tunanin tsawon lokacin da Ruma ta shafe tana zuwa makarantar allon nan, me take yi da ta kasa izifi biyu.
Ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, ya hau ta da faɗa a gaban mutane.
Cikin kuka ta ce "Wallahi yaya na iya karatu"
"To uwar me ki ka iya, kin kasa izifi biyu"
Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Eh na iya, amma ba a allona na rubuta na iya ba, na allon wani almajirin malam babba ne, idan aka ƙara masa nake iyawa, ni kuma sai na kasa nawa" Murmushi malamin yayi ya ce to biya mu ji "Tiryan-tiryan da ƙira'ar warsh, take karanta suratul Yusuf, ko tuntuɓe babu"
Shugaban makarantar yayi mata kabbara ya ce "Ahh gaskiya 'yar baiwa ce, zamu san a in da yakamata mu sanyata, daga islamiyyar har tahfiz ɗin, zaku ga sauyi in sha Allah zata yi karatu"
Yaya Umar ya ce "To masha Allah, haka muke so" aka saka wani malami ya kai Rumaisa aji. Tare suka fito da Yaya Umar, ya dubi Ruma ya ce "Ga makaranta nan na kawo ki, idan kin ga dama kiyi karatu, idan baki ga dama ba nan ma ki yi musu halin naki, kiga abin da zai biyo baya" ta sunkuyar da kai kamar ta Allah, yayi faɗansa ya gama ya tafi.
Gaba ɗaya ba tayi murna da zuwa makarantar nan ba, haka aka kai ta aji ta nemi wuri ta zauna. Gaba ɗaya ɗaliban sun mayar da hankali, suna ta zuba karatu, Ruma kuwa sanyin fanka ne ke nema ya sanyata bacci.
"Ke ya ba kya karatun?" Cewar malamin da yake kula da karatun nasu.
Kallonsa ruma tayi, shima uniform ne a jikinsa na ɗalibai, amma ya tsaya zai yi mata iyayi.
"Sabuwar zuwa ce ni, ban iya wurin ba" ta bashi amsa kanta tsaye. Bai kuma saurararta ba, ya cigaba da tilawar tare da sauran ɗaliban.
Ta dubi wata ɗaliba ta ce "Ke, dan Allah nan aji nawa ne?" Ɗalibar ta kalli Ruma sannan ta ce "Aji ɗaya ne"
"Kutmar, ban gane aji ɗaya ba, kina nufin aji ɗaya aka kawo ni?"
"Eh mana" yarinyar ta bata amsa.
Ruma ta jinjina kai ta ce "Lallai ma an raina mini hankali, wallahi ba zan zauna a aji ɗaya ba".
Ɗaliban suna ta tilawarsu, yayin da malamin yake jin haddar wasu, amma Ruma hankalinta na kan yadda zata fita daga ajin, dan zaman ajin ya isheta. Daga bisani ta koma gefe ta hau gyangyaɗi. Lokacin da aka fita break, yunwa ta saka Ruma a gaba, dan ba ta karya ba Yaya Umar ya taso ta a gaba. Ɗalibai ne masu yawa sosai a makarantar, dan makarantar sananniya ce sosai a unguwar, dan kusan babu ta biyunta. Daga yanayin mayar da hankalin su Huzaifa da yadda suke bayar da labarin tsananin makarantar ya sanya ta ji ba ta son makarantar sam. Tun da aka fita break da salla, wuri ɗaya ta samu tayi zamanta tana bin ko ina da kallo, sai da ta gaji ta tashi ta fara dubawa ko zata ga Yasir ko Huzaifa amma babu wanda ta gani a cikinsu. Haka aka koma aji ba tare da ta samu komai ta saka a cikinta ba.
Aka dawo aji aka ɗora da karatu babu ƙaƙƙautawa, gaba ɗaya Ruma ta gaji da zaman makarantar. Malamin ajinsu ya fara yi musu ƙari, ta buɗe Alqur'anin ta ajiye, ta cigaba da gyangyaɗinta.
Tun da Ruma ta shigo ajin ɗazu yake kallonta, sam ya lura babu alamar son karatun a tare da Ruma, daga hamma sai bacci take yi. Ƙarshe ta haɗa jakarta ta cewa malamin fitsari take ji, ya ce taje tayi, ta ɗau jakarta ta bar ajin. Zagayawa take tana lelleƙa azuzuwa ko Allah zai sa taga mutum ɗaya a tsakanin yayyenta, dan har wani irin jiri take ji, dan a duniya ba ta wuce ƙarfe ɗaya ba ta ci abincin rana ba, yau sai ga ta har azahar babu ko karin kumallo.
Ajinsu yayi tsit, sun tattara hankalinsu a kan ƙarin karatun da ake yi musu, kamar daga sama ya jiyo muryarta "Huzaifa, dama nan ne ajinki tun ɗazu nake neman ku" gaba ɗaya ajin aka waiwaya don ganin waye yake wannan wautar.
Kallon da ake yi mata bai sanya ta nutsu ta daina maganar ba "ka ganni a makarantar ku ko? Hmm ɗan zo ka ji wata magana mana".
"Ke wacece haka, baki ga karatu muke yi ba?" Malamin yayi maganar yana kallon tagar da Ruma ke tsaye.
"Yunwa nake ji, shiyasa nake nemansa" ta faɗa tana sake leƙo cikin ajin.
Shi Huzaifa mamaki ne ya cika shi, yaushe aka saka Ruma a makarantar nan bai sani ba?. Ganin babu komai a kan Ruma sai wauta ya sanya malamin ya kalli Huzaifa ya ce "Je ka ka sallameta"
Cike da jin kunya ya tashi ya fita, yana fitowa ta tare shi da murmushi, shi kuma ya haɗe rai ya ce "Uban waye ya kawo ki makarantar mu?"
Kallonsa tayi ta kalli harabar da suke ta ce "Sai ka ce wata makarantar arziki, nima ban ce a kawoni ba, wayewar garin Allah kawai mai sunan Baba ya bani uniform ya kawoni, ni wallahi gara na koma na bawa malam babba haƙuri, in koma makarantar allon mu ba zan iya wannan jidalin ba".
"Ke dalla rufewa mutane baki, daga zuwanki kin fara nuna hali, kawai ki zo ta window kina kirana saboda hauka, maimakon ki yi sallama ki tambayi malamin, ke Allah sai kin bar makarantar nan, dan ba zaki zubar mana da mutunci ba".
"Saboda gani annoba ko?" Tayi maganar tana hararasa.
"To ba gara annoba ba, idan aka samo maganin ta shikenan ba, ke kuma maganinki sai Allah, yanzu uban me zan miki?"
Ta yatsuna fuska ta ce "Ni yunwa nake ji, kuma wallahi sonake na tafi gida" Huzaifa ya ce "Lallai baki da hankali, to ke da gida sai ƙarfe biyar, wuce muje ajin su Yasir gara mu raba abin, da ki dinga yi mini ni kaɗai"tura baki tayi, ta rungume jakarta, Huzaifa ya sanyata a gaba yana mita suka nufi ajinsu Yasir. Ita kuma sai mita take, a kan daga yau ba zata sake zuwa wannan makarantar ba da ake uzzurawa mutane.
Yasir kansa salati ya dinga yi da salallami "Dan girman Allah meyasa mai sunan Baba zai yi mana haka, ya saka yarinyar nan a makarantar nan ba a shawarce mu ba, wallahi mun kaɗe"
"Oho muku, ku kwantar da hankalin ku, ni ba kuma zuwa zan yi ba, kawai ku bani Abinci" Yasir ya dungure mata kai ya ce "Shegen ci kamar kazar hausa" suka sakata a tsakiya suna tafe suna zaginta, suka saya mata awara da ruwa ta cinye tsaf, sannan suka korata aji.
Ko da ta isa aji, tuni an gama karatun Alqur'ani, ana jiran wani malamin ya shigo.