Kanwar maza 1&2 complete - Chapter 3
Kanwar maza 1&2 complete Chapter 3: Kanwar maza 1&2 complete Chapter 3. A soro suka yi karo da Yaya Usman zai fita, ya tsaya yana kallonta, har zata wuce…
4,465 words
A soro suka yi karo da Yaya Usman zai fita, ya tsaya yana kallonta, har zata wuce ya ce "Wai me kika dawo yi ne gidan nan yanzu, ina Makarantar kuma?"
Ta tura baki ta ce "Kashi nake ji shine na dawo gida"
Tsaki yayi ya ce "Haka dai kika iya, wannan uban cin da kike yi, ba dole kullum ki kasance cikin zawo ba, baki da aiki sai kashi da tusar tsiya" banza tayi masa ta raɓe shi ta wuce tana murguɗa masa baki, ba tare da ya sani ba.
Ta shiga cikin gidan tana ciccin magani, ihuu tayi, tare da tsalle ta nufi in da wani dogon matashi ke zaune, mai tsananin kama da Yaya Umar, sai dai banbancinsu, Yaya Umar fari ne shi kuma bai kai shi haske ba, sannan shi wannan fuskarsa ɗauke take da murmushi saɓanin fuskar Yaya Umar.
Babu tunanin komai, ta faɗa jikinsa tana murmushi. Shima rungumeta yayi yana murmushi ya ce "Autar Mama, tun ɗazu zaman jiran dawowarki nake yi".
"Babban Yaya, yaushe ka dawo?"
"Tun ɗazu na dawo, nace kina ina aka ce kin tafi makarantar allo".
"Wayyo daɗi, yaushe rabon da na ganka, gaba ɗaya gidan babu daɗi, kowa ya tsane ni, har da cewa na ishesu wai kamar su murɗe mini kai su huta".
Waro ido yayi ya ce "Wane mara ta idon ne yayi wannan iƙrarin a gidan nan?" Ta waiwaya sannan a hankali cikin raɗa ta ce "Waye banda ƙaninka, ya tsaneni wallahi".
Yayi murmushi ya ce "Ai ba wanda ya isa ya taɓa mini auta ina raye, ai gani a gidan na dawo".
Wani matashin ne ya sake fitowa, yana faɗin "Iya rigima, ya halinki?"
Sake waro ido ta yi ta ce "Yaya Abdallah".
Ya amsa da "Na'am uwar rikici".
"Haɗa baki kuka yi duk kuka dawo yau kenan?"
Abdallah ya ce "Eh haka ne, su Baba Atine suna ta gaisheki, sun ce ke ba kya zumunci"
Ta taɓe baki ta ce "Waye zai barni na je garin, ai ni ina son zumunci kai ni ne ba ayi" Gaba ɗaya sai ta manta da damuwarta, ta shantake suna hira. Sai da aka jima sannan ta shiga ɗaki ta ajiye allonta.
Sabgoginta ta shiga yi, ta zage ta ce ita zata yi wa su Babban Yaya girki, abincinta zasu ci. Aikuwa faɗa ya kaure, Huzaifa ya ce ba zasu ci jagwalgwalonta ba su zasu yi girkinsu, ƙarshe Yaya Sadik ya ce na Rumaisa zai ci.
Zuwa Azahar gida ya ɗinke kowa ya hallara a falon Mama suna cin Abincin rana, Sadik sai jinjinawa ƙoƙarin Rumaisa yake ta yadda ta iya girki mai yawa haka, Huzaifa da Yasir kuwa sai kushewa suke yi.
Zaratan maza ne su bakwai sai Rumaisa, Mama a hankali take binsu ɗaya bayan ɗaya da kallo, tana tuna baya.
Hadiza shine sunan Mama na gaskiya, haifaffiyar garin Kano ce, unguwar mandawari. A nan ta taso tayi karatun boko da islamiyya, sai dai tana aji uku na Sakandire, ta haɗu da mahaifinsu Rumaisa, Muhammad Aminu a nan unguwar sabon sara, amma asalinsa ɗan garin Katsina ne, yana zuwa gidan wan mahaifinsa ne a Kano yana koyan harkar kasuwanci, a nan suka haɗu suka yi aure, kan Hadiza ta gama makarantar sakandare.
Haihuwar fari Mama ta haifi tagwaye Abubakar Sadik da Umar faruk sune 'ya'yanta na fari, Sai ta kuma haihuwar Usman, sai Aliyu, Abdallah da Huzaifa, Yasir ne kawai ba ɗan ta ba, ɗan ƙanwar mahaifinsu Rumaisa ne, ta haife shi da kwana kaɗan Allah ya yi mata rasuwa, a lokacin Mama tana shayar da Huzaifa sai ta haɗa su ta shayar da su tare, ba zaka taɓa cewa ba 'yan biyu bane ba, ko ba ita ce ta haifesu ba. Mama gaba ɗaya tayi tunanin ta daina haihuwa, saboda galibi bai fin shekara biyu uku a tsakanin yaran take haihuwa, amma bayan haihuwar Huzaifa sai da ya shekara takwas, kawai ta daina ganin al'ada, sai ga cikin Rumaisa. Tun da Allah ya sa ta haifi Rumaisa, kowa ya ɗauki soyayya ya ɗora mata, kasancewarta kallabi a tsakanin rawuna, kowa babban burinsa ya faranta mata. Mahaifinsu Rumaisa, mutum ne mai matuƙar kulawa da son iyalinsa, kasancewar Ruma ce kaɗai 'yar sa mace yafi kowa ji da ita, ba shi da magana sai ta Rumaisa, Akwai tsananin ƙauna da shaƙuwa a tsakanin Ruma da mahaifinsu, dan kusan tafi son sa a kan Mama, saboda Mama akwai faɗa, Abba kuwa lallaɓata yake. kwatsam Allah ya yi masa rasuwa tana da shekaru uku kacal a duniya, bayan yayi gajeriyar rashin lafiya. Bayan rasuwar sa sai da Rumaisa tayi cuta kamar ba zata rayu ba, saboda alhini. Dangin mahaifin su Rumaisa suna da zumunci sosai, sun so a rarraba musu yaran su riƙe su, amma Mama ta ce ba ta son a raba nata kan yaranta, dan haka ta ce su ƙyale mata su. Haka tayi ta ɗawainiya, 'yan uwa da abokan arziki suna taimaka mata da abin da zasu iya Tasowar Rumaisa a cikin 'yan mazan nan, wannan ya ɗauka wannan ya sauke ya sanya ta taso tamkar namijin ita ma. Ba ta jin magana ga rashin tsoro, ga tsiwa da ɗan karen surutu da iyayi, gashi lokacin da take tasowa girma ya fara kama Mama duk tayi sanyi, dan haka ta mayar da Mama kamar wata kakarta ba uwa ba. Mutum ɗaya take tsoro shi ne Baban Mama, Yaya umar mai sunan baban Mama, Allah yayi masa kwarjini shi ko irin wasan nan na yarinta baya yi, ba shi da abokai, ga tsare gida ba shi da fara'a ko walwala baya son shiga mutane sam, idan kaga an taka masa burki kai tsaye to Yaya Sadik ne. Mama tana matukar girmama shi saboda sunan mahaifinta da yake da shi. Yanzu Rumaisa tana aji huɗu na Firamare, Abubakar yana Dutse yana karatu, babu wanda yake da cikakken ƙarfin ɗaukar ɗawainiyar gidan gaba ɗaya, amma kowa babban burinsa ya nemo ya kai gida, komai suka samu mahaifiyarsu da ƙanwarsu kawai suke tunani.
"Hajiya Mama, ya naga kina ta kallonmu ne kamar da baƙo a cikinmu".
Mama tayi murmushi ta ce "Allah nake yiwa godiya, da ya sanya duk ku ɗin nan nawa ne, Allah ya dafa muku ya ƙara haɗa mini kanku"
Suka amsa da "Amin" Yasir ya ce "Mamanmu, maganin kukanmu Allah ya ƙara hore mana, mu gantataki fiye da kowace irin uwa a duniya"
Huzaifa ya ce "Hmm kamar gaske, nan fa kake zuwa da abin duniyarka ka hanata, ka hana kowa ka bawa waccan yarinyar mai kama da Akushin"
Murguɗa baki tayi tana fari da ido ta ce "Tubarkallah zuƙul-zuƙul maye ya ci kansa da kansa, wallahi ni bana kama da Akushi, son kowa ƙin wanda ya rasa"
"Ke dalla ware, meye son kowa ƙin wanda ya rasa, aba Kamar gurguwar akuya" Yasir yayi maganar yana dariya.
Haushi ne ya kamata ta buɗe baki za tayi rashin mutunci, ta sanya idonta a cikin na Umar, ta haɗa maganar da zata yi, da lomar abincin ta haɗiye.
Suka gama cin abincin, Yasir ya kwashe kwanuka, ya fara ƙoƙarin wankewa, Huzaifa ya shigo da tsintsiya zai share ɗakin, Umar ya ce ya ajiye tsintsiyar ya bawa Rumaisa ta share. Haushi ne Yakamata ta lura tun da aka kawo ƙararta ya tsaneta, dama can ba wani shiga shirginta yake yi ba. Bayan ta kammala sharar ta nemi wuri za ta kwanta Mama ta kalli kan Rumaisa, da ta fara tsifa, tayi rabi ta bar rabi ta ce "Fita ki bar mini ɗaki, karki sake shigowa sai kin gama wannan tsifar.
Fitowa ta yi ta na tura baki, tana nema ta yi kuka. "Autar Mama, meya ɓata miki rai ne?" Cewar Yaya Abubakar da yake ƙoƙarin shiga ɗaki. Dama ƙiris ta ke jira, dan haka ta fara kuka "Ba mama ce ta koreni daga ɗakinta ba, wai sai na gama tsefe kaina ba, ni mama ta tsaneni".
Girgiza kai ya yi ya ce "Yi haƙuri ki daina kukan, bari na zo na tayaki tsifar" Haka suka zauna ya samu kibiya ya tsefe mata kan tsaf, suka wanke gashin, ya ce da safe zai bata kuɗin kitso. Mama ta na kallonsu ba ta kula su ba, ta cigaba da sabgoginta.
Abdallah yana ta dube-dube a kitchen, ya ci karo da allon Rumaisa, duk gefensa ya karye, ga rubutun jiki yayi baƙi ƙirin, ba ta sake wani ba. Ya fito da allon a hannunsa ya ce "Ruma, wannan allon naki yaushe zaki yi wani rubutun?" Ta haɗe rai ta ce "To ban iya ba, sai na iya zan wanke".
"Haka dai, ba kya ja a ko ina, daga arabin har bokon, Allah ya sa su zaneki idan ki ka je sati mai zuwa, baki wanke allon kin yi wani rubutun ba, gandamemiya da ke amma haryanzu a izifi biyu ki ke" Sai da yayi wannan maganar ta tuna yadda malam Babba ya dinga ƙwala mata kira amma ta gudo gida, yanzu sati mai zuwa ta yaya zata je makarantar allon? Kuma muddin abin da ta yiwa malam ya zo gidan nan, ta san ta kaɗe".
"Astagfrillah, ni 'ya su meyasa haka ne, garin in gujewa wani hukuncin sai na faɗa wani tarkon, ya zan yi da raina?.
Ayshercool 08081012143
Kar a manta ayi subscribing YouTube channel ɗina na Cool hausa tv [18/06, 2:35 pm] JAKADIYAR AREWA: ƘANWAR MAZA
BY AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
Ku yi subscribing YouTube channel ɗin mu, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro. https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels Arewabooks @ ayshercool7724 Watpad@ ayshercool7724
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION
p 4
Ko da sati ya zagayo, Mama tana sa ran ta ga Ruma ta shirya ta tafi makarantar allo, amma ta ga bata da niyyar yin hakan. Sai ma aiki take a tsakar gida, wanda ba ta saba ba, tana naɗe yayyenta je komai. Aliyu ne ya fito daga banɗaki, hannunsa riƙe da buta ya kalli Ruma ya ce "Ke ina makarantar allon?" Ta ɗan ɓata fuska ta ce "Ni na cire kaina na daina zuwa".
"Saboda ke ki ka saka kanki, shine sama ta ka ki ka cire kan ki ko? Da alama baki da gaskiya"
Mama ta fito tsakar gida ta ce "Ali ajiye butar nan ka je mini makarantar allon ka ji me ta aikata, dan ban yadda da ita ba" dan jikinta ya bata Ruma wani laifin tayi.
"Wallahi Mama ba abin da na yi, ba sai ya je makarantar ba, idan ya je ma sharri za su yi mini, ba sa sona malaman"
Mama ta ce "Au malaman ne suke miki ƙarya Rumaisa, ai ko me za ace mini kin aikata ba zan musa ba"
Huzaifa daga cikin ɗaki ya ce "Dama saboda ƙawayenta ya sa ta ce ita ma a sakata a makarantar, ba dan Allah take zuwa makarantar ba ".
Aliyu ya saka jallabiyarsa ya tafi makarantar allon.
Bayan fitarsa rantse-rantse take ta yiwa Mama, akan ita fa ba abin da ta aikata a makarantar nan, amma Mama ta shareta.
"Ruma!"
"Na'am Yaya Sadik "
"Zo ki sayo mana ƙwai ki soya mana mu karya" Kasancewar Ruma akwai kwaɗayi, ya sanya ta daina fargabar zuwan Aliyu makarantar su, ta karɓi kuɗi ta tafi aiken da Abubakar ya yi mata.
**********
A kashingiɗe take a kan kujera, ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, ta tattara dukkan wata nutsuwarta a kan ƙatuwar wayar hannunta, da alama ko me take kallo mai muhimmanci ne. "Samha me ki ke wa wannan kallon ƙurillar ne?"
Wadda aka kira da Samhan ba ta motsa ba, balle ta daina abin da take yi.
Hannu ɗayar ta saka, ta zare wayar daga hannun Samhan, tana dubawa. Har a wannan karon, Samha ba ta yi motsi ba, balle ta karɓi wayarta ta ba.
"Samha kina da hankali kuwa? Wai dan Allah da gaske ki ke dama?"
Samha ta ja ajiyar zuciya ta ce "Nusaiba, ke da kin ɗauka da wasa nake yi dama?"
Nusaiba ta jinjina kai ta ce "Eh, ni ban san abin da ki ke faɗa har zuciyarki ba"
Samha ta gyara zamanta ta kalli Nusaiba, cike da son tabattar mata abin da take faɗa ta ce "Nusaiba, ban fara dan na daina ba, ko zan tafi tsirara zan mallaki abin da zuciyata take muradi"
Nusaiba ta ɗan jinjina kai ta ce "Amma ya batun alaƙa fa, ko kin manta?".
"Alaƙa bata gabana, na san a yadda zan yi wasana. Kar ki manta anjima akwai walima a gidan Shamaki"
"Hmmm Allah ya kaimu, Allah ya sa ba wani banzan abun zaki yi ba".
Wani ɗan guntun murmushi Samha tayi, ta ce "Koma dai menene, we should see"
********
Ko da Runaisa ta dawo gida daga aiken Yaya Sadik, tana daga tsakar 6 tarar da Yaya Aliyu a falo yana wassafawa Mama abin da aka gaya masa a makarantar allonsu, ga Yaya Umar a zaune.
"Wallahi mama ba ki ji yadda ake complain a kan yarinyar nan ba, malaminsu ya ce dama ko ta dawo korarta za su yi, ba karatun take yi ba, sai tsokana da fitsara, da damben da yaran mutane, wai sam ba ta da nutsuwa da ɗa'a, malam Babba ya tara su zai hukunta su sun yi laifi ta ɗau allonta ta gudu, yana kiranta amma tayi masa banza".
Cike da fushi Umar ya ce "Ba kune kuke goya mata baya take wani rashin mutuncin ba, tun da ta san ko me ta ɗauko zaku tare mata ba, ku bari ta tsokano waɗanda zasu nakasata yadda gobe ba zata ƙara ba. Babu wanda yake faɗar alkhairi a kan ta sai sharri" ya ƙarasa maganar yana fitowa tsakar gida cike da fushi.suna yin ido huɗu da Rumaisa ta saki ƙwan hannunta a ƙasa ta na ja da baya, saboda tsoro da fargaba.
Taku biyu ya yi ya danƙota, ya sanya hannunsa ya riƙe kunnenta ɗaya da ƙarfi. Wani irin ihu ta kurma tana riƙe hannunsa, saboda ji tayi kamar zata ɗaga kai ta ga kunnen a hannunsa, saboda azabar zafi.
"Dan ubanki idan har ba zaki canza hali ba, makarantar kwana zan kai ki, tunda ba ki in da yake miki ciwo ba, ko mu mayar da ke can ƙauye, su miki aure" Usman ya ce 'Ai Rumaisa sai ka ce wadda ta sha nonon aljana, hatsabibancin ta yayi yawa, ba ta jin magana sam"
Abubakar ne ya fito daga ɗakinsu a fusace, ya ƙaraso ya riƙe hannun Rumaisa, ya kalli Yaya Umar ya ce "Sakar mata kunne" Umar ya ɗan yi turus yana kallon Sadik.
"Baka ji bane?"
Sadik ya maimaita masa. Yaya Faruk ya saki kunnen Rumaisa, da idanunta tuni suka yi ja saboda kuka.
Ya janyota ya zaunar da ita a kan tabarma, ya dinga share mata hawayen fuskarta.
Cikin ɓacin rai ya ce "Yakamata ku dinga yiwa kan ku adalci a kan yarinyar nan, ita kaɗai ta tashi a cikinmu mace, tayaya zaku ce sai kun tanƙwarata yadda ku ke so? Tayi laifi kowa yayo kanta, ba mai yi mata nasiha, daga mai ce mata munafuka sai me ce mata aljana haka ake rayuwa?"
Yasir ya ce "Wallahi Yaya Sadik, duk ranar da yarinyar nan ta kwaikwaya maka rashin mutuncin da take aikatawa zaka gane ba tsanarta aka yi ba"
"Koma dai yane, a dinga barin yarinya ta huta a daina takura mata haka "
Guntun tsaki Umar ya ja, ya fice daga gidan gaba daya, suna zaman zamansu Mama ta haifo wannan 'yar kalen hanjin da ta gallabi rayuwarsu.
Yau cikin dare, Mama ta tashi tana ibada, kamar yadda ta saba domin a cewarta wanda duk ya tara zuriya yake neman kuma dacewa, bai ga ta bacci ba. Fitilar ɗakinta ta kunna, haske ya gauraye ko ina, Rumaisa tayi rashe-rashe a kan katifa, zaninta daban ita daban daga ita sai wando, kanta ko ɗan kwali babu. Mama ta girgiza kai, ta janyo zanin ta ɗaura mata, ta saka mata hula ta lulluɓeta, sannan ta fice ta ɗauro alwala ta zo ta tayar da salla. Sai dai sam Ruma ba ta san an yi bama, tana ta fama da bacci.
Can Mama ta kuma juyawa, amma ta ga Rumisa ta kuma yada zanin, ƙafafuwanta duk suna ƙasan katifar, ta kuma tumɓur tana bacci. Haushi ne ya kama Mama, ta ƙarasa in da take, ta ɗala mata duka a cinya. Amma maimakon ta tashi, sai ta sake dunƙulewa tana bacci. "Ke Ruma, ba zaki tashi ba sai na saka miki bulala?" Da ƙyar ta tashi tana murza ido tana kalle-kalle.
'tashi ki ɗauki rigarki ki saka, ki ɗaure kanki ki je ki yo alwala ki salla".
"Wai har asubar ta yi ne?"
Mama ta ce "Wato ke idan ba sallar farilla ba, baki san ki yi nafila ba, sai dai ki saki leɓe kina bacci. Ki je kiyi alwala ki zo ki yi salla ki roƙi Allah ya yaye miki wannan wautar da rashin hankali da kike fama da shi" kafin Mama ta gama maganar, Rumaisa ta sake ɓingirewa ta kwanta. Aikuwa mama ta ƙule, ta janyo mafici ta shiga rafka mata a cinyoyinta, a razane ta miƙe tana sosh-soshe. Mama ta bata riga da ɗan kwali ta ɗaura, ta korata tayo alwala.
Mama ta koma kan tata sallayar ta cigaba da salla. Kusan mintuna arba'in, Mama ta manta ta tura Rumaisa tayi alwala, ta kalli shimfiɗarta taga bata wurin. Da sauri ta tashi ta fita tsakar gida tana dubawa, sai dai babu Rumaisa babu dalilinta. Lelleƙawa Mama ta hau yi, tana nemanta a cikin gidan amma bata nan.
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ina yarinyar nan ta shiga ne haka?" Tayi maganar lokacin da ta ƙarasa soro tana haska fitila, amma taga ƙofar gidan a rufe.
Ƙofar ɗakin samarin gidan ta tsaya tana bubbugawa da ɗan ƙarfi. Usman ne ya taso cikin yanayi ya bacci, ya kalli Mama ya ce 'Mama lafiya kuwa?".
Cikin tashin hankali ta ce "Ruma na tasa tayi sallar dare, daga ta fito tayi alwala, na nemeta na rasa".
Ƙwalalo ido waje yayi, ya ce "Ruman? To ina ta tafi?"
Mama ta girgiza kai ta ce "Ban sani ba, na duba ƙofar gida tana rufe da sakata ba a buɗe ba"
Mamaki duk ya cika Usman ya ce "To in ta shiga a tsohon daren nan, bari na sako rigata a buɗe gidan a dudduba".
Ya shiga cikin ɗakin, ya kunna wutar lantarkin ɗakinsu, sai ga Ruma a tsakiyar su Yasir tana bacci.
Kunna fitilar ne ya sanya Huzaifa ƙoƙarin yin juyi, amma ya ji mutum a kusa da shi, yayi zaton Yasir ne, dan haka ya dage ya hankaɗa Rumaisa, ta kifa kan Yasir amma ba ta farka ba.
Usman Ya ce "mama leƙo kiga" Jiki na rawa mama ta shiga ɗakin, daidai lokacin da Yasir ya ji nauyi a kansa shi ma ya dage ya hankaɗata gefe guda. Mama ta shiga tafa hannuwa tana salati, a irin magagin bacci, da shirme na Rumaisa tsaf za a saceta tana wannan baccin na asara. A ƙufule Huzaifa ya tashi yana zage-zage ya zata Yasir ne yake damne shi, amma ya ga Ruma a tsakiyar su, ga su Mama a tsaye.
"Ke uban me ki ke yi a ɗakinmu, mama meyafaru?"
Jin hayaniya ya sanya Sadik ma farkawa, ya dinga kallonsu ɗaya bayan ɗaya 'mama lafiya kuwa'.
'lafiya lau, kai Huzaifa taso mini ita' Abubakar ya kalli in da Rumaisa ke ta more laushin katifa tana barci. "Wai me ya kawo yarinyar nan ɗakin nan?"
Usman yayu masa bayani kamar yadda Mama tayi masa.
Sadik ya ce "Kai Huzaifa, kai da Yasir ku sauko ku bar mata katifar dan Allah, wannan ba tashi zata yi ba" Yasir ya ce "Kaii, Yaya haryanzu fa yarinyar nan tana fitsarin kwance, kawai a tasheta ta fita, kar ta tsula mana fitsari dan katifar nan wuyar bushewa za ta yi".
Yaya Umar kuwa tun shigowar Rumaisa yana kallonta, lokacin bai daɗe da kwanciya ba, ya ganta ta shigo tana tangal tangal, ta nemi wuri ta kwanta, tun da ta shigo yana kallonta.
Mama ta ce "Ba zata kwana a nan ba, taso mini ita ta wuce mu tafi".
Yasir ya daddaki Rumaisa a kafaɗa, amma ta hau surutai da irin faɗace-faɗacen da suke yi da yara a makaranta.
Ƙarshe haushi ya ƙule, Umar ya tashi danƙo Ruma ya hankaɗowa Mama ita tsakar gida, ya rufe musu ƙofa. Mama har mamakin wannan magagi da kuma suratan baccin da Rumaisa take yi, ita duk wani da mutane suke yi, nata ya zarta ƙa'ida. Har mama ta kama hannunta zuwa ɗaki, magagin bacci take yi.
****** Sassanyar iskar da bishiyoyin ke bayarwa ne ya haɗu da ƙamshin furanni, tare da samar wani kyakkyawan yanayi mai sanyawa zukata nutsuwa da annashuwa.
Duk da wannan tarin ni'ima, gaba ɗaya Samha ba ta jin dadin yanayin sam. Wayar hannunta ce ta fara ringing, wadda ta katse mata dogon tunanin da take yi, ɗagawa tayi ta kara wayar a kunneta ba tare da ta ce komai ba. "Ki fito mu tafi, ina haraba".
"Ok, ya maganar mu? Kun yi magana da ita, zasu zo ne". Nusaiba ta ce "Hmm, Samha kenan ke meya hana ki tambayeta?"
"Nusaiba bana son wasa, am serious about it".
Nusaiba ta ɗan taɓe baki ta ce "Eh, za su zo" Ta sauke wayar daga kunnenta, ta nufi hanyar fita daga lambun.
*** Mama tana yawan yin istigfari da nemawa Rumaisa shiriya, musamman yadda bakin mutane yayi yawa a kanta, duk wani rashin ji irin na ɗa namiji shi take yi, bama irin na mata sa'aninta ba, duk sa'aninta ta kere su a rashin ji. Babu yadda Mama ba tayi ba a kan aje a bawa malaman makarantar allon su haƙuri, ta koma amma mirsisi Yaya Umar ya ce sai dai a sauya mata makaranta, in da zata fi mayar da hankali, amma a ƙasan zuciyarsa zafin maganganun da malaman suka yi a kan Rumaisa ne ya fi ɓata masa rai har ya sanya ya ce ba zata koma ba.
Ita kuwa Rumaisa ganin Yaya Umar ya hana a mayar da ita makarantar allon Malam Babba, tayi ta murna a ganinta ta huta da zuwa makarantar nan mai cike da takurar tsiya, Allah ya sa makarantar bokon ma a cireta, ta dawo gida Mama ta bata jari ta dinga sayar da wainar fulawa a ƙofar gida. Murmushi ta yi bayan wannan tunanin ya zo ranta.
Ta dubi Abdallah da yake ninke kayan da ya wanke ta ce "Yaya Abdallah, dan zaka gayawa abokananka zan fara sayar da wainar fulawa, naga kai ne me abokai masu kuɗi, ka talatta musu su zo su dinga saya, ba irin abokan su Huzaifa ba gayyar ƙolawa da tsamaye ba" Saroro ya kalleta ya ce "wace irin wainar fulawa kuma?"
"Eh tun da na daina zuwa makarantar allon, sai Mama ta bani jari na diga sayar da wainar fulawa a ƙofar gida".
Huzaifa ya ce "Eh dama kin yi kalar sayar da wainar fulawar ai, ai ni da kai na zan din ga yi miki ciniki, ai suyar wainar ce ta dace da le delu"
Murguɗa baki tayi ta ce "Da dai ban san halinka bane, ci ka tsere ka rusa mini jari, kama kar ka sake ce mini wata deluna gaya maka. Ta mayar da hankalinta kan Abdallah ta ce "Dan Allah Yaya Abdallah ka yi magana mana".
"To ai Ruma na rasa me zance miki ne, wace irin wainar fulawa ana zaman lafiya".
"To Yaya ba gara ace ina sana'a ba, kuma ku huta ba, ana ta shelar mata su kama sana'a, Mama ai zaki bani jari ki saka mini albarka ko?"
Mama ta ce "kada Allah ya nuna mini wannan rana, kuma kar ki sake sakoni a cikin shirmenki, idan kuma ki ka sake sai na ci ubanki ke da soya wainar fulawa a ƙofar gidan, tun da ke dai Allah bai sa an raba hankali kin samu ba" ɓata fuska tayi a ranta ta ce 'sai na tambayi Yaya Abubakar, na san shi ba zai hana ni ba ai, tun tuni ake cewa mata su kama sana'a ni kuma zan yi ana hanani'.
Umar yana ɗaki yana jin shirmen da Ruma take, ji yake kamar ya ɗauketa ya kai ta boarding kowa ya huta, amma ya san Mama ba zata taɓa amincewa ba.
Wayewar garin Allah, wurin ƙarfe sha ɗaya na safe, mama na shirin fita, telar da take yiwa Mama ɗinki ta aiko da ɗinkin da Mama ta kai mata, bayan mama ta karɓi ɗinkin ta sallami yaron, ta kalli Ruma ta miƙa mata ledar ta ce "gashi nan kayanki ne".
Da murna ta karɓi ledar ta buɗe, cike da son ganin menene a ciki. Tana buɗewa tayi karo da wata atamfa koriya da yellow, ta kalli Mama ta kalli atamfar sannan ta ce "Wallahi Mama wannan Salamatu mai kayan ba ta kyauta mini ba, sai da nace ba na son atamfar nan, amma dan taga ba na nan shine ta liƙa miki, ki ka saya amma shikenan na gode, amma dai ba dan an ɗinka ba sai na mayar mata" ba ta gama rufe baki ba, ta buɗe kayan taga riga da zani jaka a tsaye, da wata uwar bunjumemiyar riga kamar zata tashi sama.
"Ta kalli mama ta ce "Mama wai wannan kayan nawa ne ko kuma naki?" Ruma tayi maganar a rikice.
Mama ta ce "Ni ce zan saka wannan kayan? Naki ne mana"
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, yanzu mama wannan ne kayan salla na, dan Allah kalli rigar tsaf sai an saka irina sittin a ciki, mama ko gwada ni fa ba ayi ba aka ɗinka kayan"
A fusace Mama ta ce "Naji na gode, ki ajiye mini kayana tunda ba ayi miki gwaninta".
Yasir ne ya dubi Ruma ya ce "Amma Ruma baki da kirki, yanzu mama ta sai miki kaya ta bayar a ɗinka miki, amma ƙiri-ƙiri ki nuna ba kya so".
Mama ta ce "Rabu da ita, ta je ta ƙarata".
"Mama kiyi haƙuri, ba cewa nayi bana so ba, amma dan Allah kalli rigar nan, ni ba tattabara ba ina zani da wannan rigar kalli hannun kamar fuka fukai, ba irin wannan rigar na gani a jikinku a wannan tsohon hoton naku ba?" Yasir ya karɓi rigar yana dubawa, ƙunshe dariyarsa yayi ya ce "To dan ubanki maje gaba aka yi miki, tun kina yarinyarki da ke, wato kin fi son matsatsun kaya ko, to baki isa ba, wannan rigar da ita zaki yi wankan idi mu je masallaci, maje gaba ce " Haushi ne ya gama cika Ruma, ta tura baki tana jin kamar ta yi ihu.
"Wace irin maje gaba, ai sai a bari nayi gaban tukuna, sai a ɗin ka mini daidai ni, idan ban je gaban ba fa?"
Mama ta ce "Rabu da ita, ta gama rashin mutuncinta tun da abin nata haka ne, daga wannan ba zan ɗinka mata wasu ba, da su zata yi sallar, dama ba jin maganata take yi ba, nima an zo wurin da zan fanshe, bana ba kayan salla sai kala ɗaya".