Kenza eBookz

Kanwar maza 1&2 complete - Chapter 32

Kanwar maza 1&2 complete - Chapter 32

Kanwar maza 1&2 complete Chapter 32: Kanwar maza 1&2 complete Chapter 32. *** Ammi ta fito babban falo, ta dubi ɗaya daga cikin barorinta ta ce "Maza je ki…

4,453 words

*** Ammi ta fito babban falo, ta dubi ɗaya daga cikin barorinta ta ce "Maza je ki korawo mini iman" ta amsa mata cikin girmamawa, ta tafi.

Bai fi mintuna bakwai ba, sai ga Iman "Ammi gani, Allah ya sa ba laifi na yi ba?".

"Ai laifin ki ka yi, na gaji da zaman ɗakin nan da ki ke yi, jikinki ai da sauƙi yanzu, ki shirya zamu je gidan Jamil, an ce matarsa tayi ɓari" ɗan ɓata fuska iman tayi kamar zata yi kuka.

"Menene ko ba zaki ba?" Ammi tayi maganar tana tsare iman da ido.

"A'a zan je, bana son na je na tarar da Anty samha ne" tayi maganar kamar ta rushe da ihu.

Ammi ta kalleta a tsanake ta ce "Meye tsakaninki da Samhan da ba kya son haɗuwa da ita?" Sai kuma ta sha jinin jikinta jin abun da ammin ta ce.

"Bakomai Ammi, bana son fita ne"

"Aikuwa sai kin fita, maza muje in shiryaki, kar ma ki ɓata mini lokaci" Nusaiba kuwa sai dariya take yi, ganin ammi ta saka iman a gaba wai ita zata shiryata. Hakan kuwa aka yi, Ammi na tsaye iman ta shirya cikin baƙar abaya, da ta karɓi kyakywar farar fatarta, sai ɗaukar ido take yi, ta ɗora mayafin a kan ta, sai dai kwantaccen gashinta sai da ya bayyana. Tare suka fito da Ammi, tana janyo hannunta, ita kuma kamar ta fashe da kuka, sai tura baki take yi. Haka suka jera da Nusaiba da iman da ammi. Nusaiba ta ce "Allah ammi kin shagwaɓa yarinyar nan da yawa, ji wata taɓara da take yi".

Ammi ta ce "Bar ni da ita, sai na zaneta tukuna" haka suka fito harabar gidan a tare.

Tun daga nesa yake kallonsu, ya tattara nutsuwartsa a kan Iman, tamkar ba bugun Nigeria ba haka take.

"Ruky wannan ma 'yar gidanku ce?"

Ruƙayya ta waiwaya ta hango su Ammi, a fusace ta dube shi ta ce "To ba 'yar gidan nan ba ce, tsintota aka yi aka riƙeta a gidan nan, babu wanda ya san danginta ma, wataƙila ma ba ta da uba" Maimakon ya fusata sai ya ce "Wow, amma dai a ƙasashen Larabawa kuka tsinto ta ko? Ko irin Afrika ta gabas ɗin nan". "A'a africa ta sama, aka tsinto ta aikin banza " ta tashi fuu ta shiga ciki.

Tashi yayi yana kiran sunanta, amma bata ko sake waiwayo wa ba ta tafi.

"Wallahi na gaji, ni da gidan ubana saboda bala'i ban fiye zama ba, ko na kawo baƙina ba, da gayya idan bar zan yi baƙo mu zauna a harabar gidan nan, sai wannan banzar yarinyar ta fito, ita kuma ammi ta wani sako su a gaba riii kamar shanu, duk yadda na ƙallafa rai a kan gayen nan, yana ganinta ya hau wani surutu, ji nake kamar na zuba mata wuta a fuska uban kowa ya huta".

Mummy da take jin ta tayi shiru ba ta yi mata magana ba, ta ƙaraci bala'inta ta gama, amma Mummy ta fara hasala, duk yadda suka kai ga ɓata iman, ba ya wani tasiri sam. Kamar ba zata yi magana ba sai kuma ta ce "daga yau idan kin yi baƙi, ku din ga shigowa falon waje, kuna zama, ku bsrni da ita, zamanta a gidan nan ya kusa expire " haka ruƙayya ta zauna tana cigaba da huci.

*** Yasir da Abdallah basu saki jikinsu ba, sai bayan ganin kyakywar tarbar da Bashir yayi musu, ya kai su wani katafaren office, har da sanyawa a kawo musu ruwa da lemo. Abdallah ya ce "Ranka ya daɗe mai ɗan uwana yayi ake nemansa ne? Hankalinmu ya kasa kwanciya, kar wani abu ne ya faru, mahaifiyar mu babu lafiya, ba wanda muka sanarwa ma a gida"

Bashir ya yi murmushi ya ce "Ɗan sanda ai abokin kowa ne, ba abun tashin hankali bane, ni na so mu zo har gida amma wani aiki nake yi wa uban gidana. Shekaranjiya aiki ya kaini jihar katsina, na kwana ɗaya a can, a kwana na biyu na kamo hanyar baro garin, na tsinci wata yarinya da jariri a gefen hanya, wani mutum yana tambayarta, so nayi amfani da id card ɗina, muka kaita asibiti da yaron, amma yarinyar ta kasa bamu haɗin kai saboda jaririn nan, so a jiyan muka taho kano, aka kwantar da ita a asibiti ita da yaron, ta ce mini dai ɗanta ne, na yi reporting wa abokan aikina, shine ta bani lambar wayar Yasir ta ce mini yayanta ne, suananta Rumaisa.

Miƙewa tsaye suka yi tsaye gaba ɗayansu, suna kallon Bashir, amma suka kasa magana. Bashir ya miƙe ya ce lafiya kuwa?"

Tuni hawaye ya wanke fuskar Yasir ya ce "Yallaɓai ina ruma take, ƙanwarmu ce aka saceta a katsina, tafi wata biyu kusan watanta uku a hannun 'yan bindiga, dan Allah tana ina"

Bashir ya dafa kafaɗar Yasir ya zaunar da shi ya ce "Calm down, tana nan ana kula da lafiyar ta, ku godewa Allah, duk da ba ta gaya mini meyafaru ba, amma dai gaskiya a galabaice take, ikon Allah ne ya fitar da ita, tana nan asibitin koyarwa na kano, zaku bamu bayanin yadda aka yi ta ɓata da komai da komai ". Daga Yasir har Abdalla aka rasa mai magana, dan Abdallah durƙusawa yayi yana kuka dan tuni suka fara fitar da rai. Nan Bashir da abokan aikinsa, suka din ga rarrashin su, suka gaya musu iya abun da suka sani, daga tafiyar su ita da Aliyu zuwa yanzu, aka kuma duk wasu cike-cike da za ayi, aka ce zasu tafi Asibitin wurin rumaisa.

Abdallah ya gige hawaye ya ce "Yallaɓai zamu iya kiran gida mu sanar musu, mahaifiyarmu na nan ba yadda take saboda azabar tunani da damuwa"

"Eh ku kirata ku sanar musu".

Yasir ya ce "Mai sunan baba zaka gayawa, shi zai san yadda zai ya sanar mata, kar ta gigice jininta ya kuma hawa".

Haka kuwa aka yi, sai dai Umar bai ɗaga wayar ba, sai Aliyu aka samu, gaba ɗaya ya rikice da jin maganar, amma yayi iya ƙoƙarinsa ya saita kansa, mama ba ta gane ba, ya sanarwa Usman da Mai sunan baba.

Mai sunan ya ce su yi gaba, zai taho da mama, ba tare da ya bari ta gane wani abu ba, su fara zuwa su duba idan da gaske ruman ce.

Tun da rumaisa ta ɗan farka, Yayar bashir ke fama da ita ta ci abinci, amma ta gardame ta ƙi ci, sai surutai kawai take marasa kan gado, tana kukan ita fa a kawo mata jaririnta. Sai da nurses suka ɗauko shi, an saka masa kaya, sai dai ya ɗan yi dama dama, an sanya masa robar hanci, ta nan ake ɗura masa madara.

Rumaisa ta zubawa jaririn ido a hannun Asiya, tana bashi madara ta sirinji, sai ta ga ta koma mata suffar Aisha.

"Anty Aisha, kin ga amanarki? Ashe nan suka kawo ki suka barmu a can?".

Asiya ta ce "Asiya dai, sunana kenana ba Aisha ba" sai da ta yi magana, sannan rumaisa ta ga ta koma Asiyan.

Ita kanta ruman a yanzu bata iya banbance wacece ita, da kuma rayuwar da take yi.

Ƙofar ɗakin aka buɗe, rumaisa ta ɗaga kai, bashir ne a farko da wasu 'yan sanda, Yasir ya ture su, ya rugo da gudu ya zo ya rungume rumaisa yana kuka. Rumaisa ta kwantar da kanta sosai a jikinsa ta ce "Yasir, idan ka zo mafarkina ka daina tafiya, ka barni tsoro nake ji". Bai san me ma take faɗa ba, Abdallah ma ya garzayo ya rungumesu gaba ɗaya, sai dai ruma ba ta da ƙwarin da zata iya rungumesu ita ma. Dan ita gaba ɗaya ta riga ta yadda da cewa mafarki take yi.

Abdallah ya kalleta, 'yar da mama ke ta tattalawa tana kula da tsaftar ta da jikinta, sai gata duƙun-duƙun kamar ta warke daga ciwon hauka, koma dai wadda take cikin haukan tuburan

Su Usman ne suma suka banko ɗakin, suna addu'ar Allah ya sanya rumaisan ce. Suna ganinta suma suke kewayeta suna kuka, kallo ɗaya zaka yi mata ka san ta sha azaba ta wahala.

"Dan Allah duk kar ku tafi ku barni, mu yi ta zama a cikin mafarkina" tayi maganar tana fashewa da kuka. Babu wanda ya rarrashe su, kai da ganin yadda zaratan samarin ke kuka, ka san sun shiga ɗimuwa da ɓatan 'yar tahalikar.

Mai sunan Baba da ƙyar ya lallaɓo mama a kan zai kai ta ganin likita wani asibitin daban, ta ce ba zata ba, wani abun suke ɓoye mata kawai, sai da suka kai ruwa rana sannan ta yadda.

Ko da suka isa ɗakin da ruma take, kasancewar Usman ya tura masa message na sun ganta rumaisa ce, ya sanar masa ɗakin da take.

Ko da mama tayi ido huɗu da rumaisa ƙamewa tayi, sai ruwan hawaye.

Ruma ta hau miƙa mata hannu tana hawayen ita ma ta ce "Mama dan Allah ki zo in taɓaki kar na tashi daga baccin na ga kin tafi" Mama ta ƙarasa ta ƙanƙame rumaisa kamar ta mayar da ita ciki.

"Dan Allah mama kar ku tafi, kullum sai kun zo a mafarki na ganku, amma sai ku tafi ku barni a wannan dajin mukaɗai, dan Allah mama ki zauna da ni, Allah ya sa kar na tashi daga baccin nan, mamana tsoro nake ji kar ki bari na farka"

"Ruma nima ji nake kamar mafarkin ne, ina ta gaya musu kin dawo kina waje amma basu yadda ba, Allah Alhamdilillah" tayi maganar tana sake rungume rumaisa.

Wata nurse ta shigo da tray na magunguna ta ce "Gaskiya bayin Allah kun yi yawa a ɗakin nan ku ragu zan yi mata allurai, bacci muke son tayi ƙaaƙwalwarta ta huta" ta yi maganar tana ƙarasawa gaban gadon rumaisa.

Bashir ya ce "ki bi a hankali, watanni uku ba sa tare an saceta, ki bari ta ga ahalinta"

Nurse na ƙoƙarin ɗaga hannun ruma daga jikin mama ta yi mata allura, a zuciye rumaisa ta yi jifa da trayn "So ki ke dole na tashi daga baccin? Bana so ki ƙyaleni" ruma tayi maganar kamar mai shirin tayar da aljanu.

Sai a yanzu mai sunan baba ya ƙarasa, ya zauna a gefen gadon, ya ɗago rumaisa daga jikin mama, ya rungumeta a jikinsa, ya ɗago hannunta ya riƙe ya ce "Yi mata abun da ya kamata"

Ta yi lamo a jikinsa, sai kuma ta ce "Mai sunan baba".

Ya ce "Na'am"

"Yau a mafarkin nawa ba zaka sakani kama kunne ba? Kullum idan ka zo sai ka sakani kamun kunne, amma ko zaka sakani kamun kunnen, ka zauna a mafarkina, tsoro nake ji bana son duhun nan" tayi maganar tana shirin fara fizge-fizge amma ya danneta a jikinsa ana gama allurar ta cigaba da bacci.

Bayan baccin ya ɗan ɗauketa, mama ta share hawayenta ta ce "Aliyu, ku je gida ku zo da ruwan zafi, ayi mata wanka, kan mutane su ji su fara zuwa"

Bashir ya ce "No, kar a taɓata tukuna sai zuwa dare, muna jiran result ɗin likita tukuna, sai ayi mata wankan, sannan akwai jariri da na tsince su tare, ta ce mini ɗanta ne, duk da ni ban ga alamar hakan a tare da ita ba".

Mama ta ce "Jariri kuma?"

Asiya dake gefe ta miƙa musu jaririn ta ce "Gashi, bayan tafiyarka ta sanya rigima sai da aka ɗauko shi".

Mama ta karɓi jaririn tana ƙare masa kallo, Bashir ya ce "Ikon Allah, ban yi zaton yaron nan zai rayu ba, amma cikin ikon Allah kun gan shi, har da sauran ƙazantar haihuwa a jikinsa na gansu".

Usman ya ce "to a ina ta samu jariri?"

Aliyu ya ce "Oho, tubarkallah gashi ƙato mai kyau.

Ruma tana baccin nan, aka juyata ana wanke mata raunin da yake ƙeyarta, gashin kanta har da kwarkwata, ban da tarin datti da dauɗa.

Mama ta din ga yi wa Bashir godiya, rumaisa ba ta daɗe ba allurar ta saketa, sai dai ta kasa yadda ba mafarki take yi ba. Kamar kullum Bashir ya din ga lallaɓata ta gaya masa, ina ta samu jariri, amma ta ce "Na gaya maka ɗana ne".

Mama ta ce "Rumaisa, ki gaya mana ko hankalinmu zai kwanta, ina uwar ɗan take" rumaisa ta yi shiru tana tunani.

"Ba kya ji ne?" Mai sunan baba yayi maganar yana kallonta.

"Ɗan wata mata ne" ta basu amsa.

Nan ta gaya musu iya abun da ta sani, ta ɓoye musu wani abun.

Bashir na gama jin bayanin ruma, ya ce asibiti za a canza mata.

Suka shiga tambayarsa dalili, amma ya ce likita ne ya bada shawarar hakan.

Daf da magariba Bashir ya isa gidansu takawa, bayan yayi ta kiran lambarsa amma yaƙi ɗagawa. A harabar gidan suka yi kiciɓis, Bashir ya tattara nutsuwartsa ya ce "Allah ya baka yawan rai, ina ta kiran lambarka ka ƙi ɗagawa". Ƙoƙarin tureshi Adam yake ya wuce, amma Bashir yaƙi matsawa ya ce "Tuba nake, amma ka tsaya ka saurareni, wallahi babban uzuri ne ya sameni, na gaya maka yarinya na tsinta, ta kuɓuto daga hannun 'yan bindiga"

A fusace Adam ya ce "Ka je ka yi abun da kake so mana, ai ban yi maka magana ba, ambulance sarkin taimako ka je ka yi ta yi mana, tun da ni tawa buƙatar ba buƙata bace".

Bashir ya ce "Dan Allah Adam ka saurareni ka ji"

"Ba zan ji ba, bana son ji" yayi maganar a fusace zai wuce.

"What if yarinyar tana da alaƙa da aikin da ka bani? Ka rage zafin zuciya ka dinga cin ribar rayuwa, ka zo mu je zuwanka ka ganta yana da muhimmanci, za a iya samun muhimman bayanai a tare da ita, yanzu haka Ammi na asibitin". Cak Adam ya tsaya yana kallon Bashir.

"Ka zo mu je, ina tabattar maka da cewa, yarinyar nan za ta iya zama ita ce makarin abun da muke nema, ka yi haƙuri ka yadda mu je".

"Amma meya kawo ammi cikin zancen nan".

"Dole ce, dole ce ta shigo Ammi cikin lamarin nan, kuma har zuwa yaushe zamu cigaba da wannan ɓoye-ɓoyen? Ka zo mu je" Adam bai kuma cewa komai ba, ya bi Bashir motarsa.

Wani katafaren asibitin kuɗi Bashir ya sanya aka mayar da rumaisa, sai dai ba ta iya taka ƙafafuwanta, saboda raunukan da suke jiki, mama tana yi mata wanka tana kuka, haƙoranta sun yi yellow, gashi nan a cukurkuɗe, fatar rumaisa duk cizon ƙwari, haka zalika cikin kayanta duk ƙwari, Mama ta sanya almakashi ta ragewa rumaisa gashinta, saboda tana da cukurkuɗaɗɗen gashi mai tsayi.

Mama ta tsorata da ta ga uban gwal ɗin da yake cikin ɗan kwalin da yake ƙugun rumaisa, ko da mama ta matsa mata da tambaya, sai ta hau kuka. Abinci ma da ƙyar ta ci kaɗan, ta kwanta ta cigaba da aikin bacci.

A hankali take motsawa, tana buɗe idonta da kaɗan-kaɗan, tana tsoron kar ta buɗe idonta ta ganta a duhun dajin nan, ko wurin su sule. Ganinta ta yi a wani wuri na daban, dan har aka canza mata Asibiti mama tayi mata wanka, ba a hayyacinta take ba, ko ina farin tiles da farin ƙwai, ga sanyin ac da yake ratsata, a hankali ta fara shaƙar wani irin daddaɗan ƙamshin turare, ta din ga kallon mutanen ɗakin ɗaya bayan ɗaya, wata babbar mace ta gani a zaune tayi mata kama da wanda ta sani. A hankali ta ga su Aliyu da Usman a wurin, ga wasu dogarai masu kaya kalar na bayi da mama ta ce mata.

Gabanta ne ya faɗi da ta yi tozali da Adam a kan gwiwoyinsa, rungume da jariri hawaye na zuba daga idonsa.

Cikin ihu ta ce "Wayyo Allah mama, kina ganinsa ko ni kaɗai nake ganinsa?"

Mama ta ce "Waye?"

"Wannan mugun mutumin" tayi maganar tana nuna Adam.

A rikice mama ta ce "Me yayi miki?"

Bashir ya ce "Rumaisa, ki kwantar da hankalinki, ba mugu bane ba, kwatancen da matar nan ta baki, shi na yi tracking, mutanen da ta gaya miki gidan sirikanta ne kuma iyayenta, Adam abokina kuma shi ne baban jaririnki, shi ne mijinta".

(Danƙari!🥺) Ayshercool.

₦500 ne via 0009450228 Aishs Adam Jaiz bank Sai a turo shaidar biya ta 08081012143

*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?* *TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI* *SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*

*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*

👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*

*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*

*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*

*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*

*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*

*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*

*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*

*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*

*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*

*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*

*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*

*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton* *14. Supplement na whitening/glowing skin*

*15. Supplement for Acne, dark spots remover*

*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*

*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*

*ƘANWAR ₦500 ne, via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143*

Kamar sokuwa haka ruma ta bi bashir da kallo, daga bisani ta ja wani uban tsaki ta ce "Dan Allah ka daina raina mini hankali, wai komai nawa sai wannan mutumin ya shigo ciki, to wallahi ba shi bane ba, ɗana ne ba shi ne babansa ba". Ko cikin gushewar hankali takawa ba zai manta wannan muryar me shegen karaɗi da tsiwar tsiya ba. Shi kansa mamaki yake yadda aka yi rumaisa take shigowa cikin rayuwarsa a bazata. Ya ɗaga jajayen idanunsa ya na ƙare mata kallo.

Usman ya ce "Rumaisa, kin ga ki nutsu kin ji, shi a ina ki ka san shi?"

Ta kalli Bashir, sannan ta ɗan kalli takawa, ta girgiza kai ta ce "Ni ban san shi ba, ku karɓo ɗana ku bani, ba shine babansa ba, ni ba shi ta ce mini ba".

Bashir shima ya ƙarasa gaban rumaisa ya ce "Rumaisa, ba cewa ki ka yi tace miki ita 'yar turakin kano ba ce? Ta ce miki giwar Galadima ce sirikarta ba, to ai ga giwar Galadima nan, Adam kuma ɗanta ne" ruma ta yi shiru ta tafi tunanin abun da ya faru ita da Aisha.

Lokacin da ta kammala bawa Aisha labarin abun da ya faru a tsakaninta da Adam, ta din ga yi mata dariya ta ce "Kamar na san mutumin nan da kike bani labari".

Rumaisa ta ce "Taɓ, aikuwa idan ɗan uwanku ne sai dai ki yi haƙuri dan ba shi da mutunci, bama ki san shi ba anty aisha".

Aisha ta kalli ruma ta ce "Ɗan gidan marigayi Galadiman Kano ki ka ce ko?"

"Oho masa, amma dai kamsr haka aka ce"

"Amma da ƙarfin hali kike ruma, dan ƙarfin hali babban mutum ki yi masa wannan rashin kunyar?"

Ruma ta taɓe baki ta ce "Ai ni Allah kaɗai nake tsoro"

Aisha ta yi murmushi ta ce "To ki yafe masa mana my baby rumaisa" ruma ta daki ƙasa ta ce "Ai ko shine zai zo gabana ya ce na yafe masa ba zan yafe masa ba, kin ga rashin muntucin da yayi mini, har da ce mini 'yar talakawa, yanzu da ciki ya fito mini da ya taɓa mini nono fa, ina zan saka kaina?"

Tayi dariya ta ce "Ai bai fito ɗin ba, kuma gaskiya kar ki yi masa sharri dan kin tsane shi, you are still a baby, ina wani nono a nan banda sharrinki ruma? Ko kwatan nawa ba su kai ba fa, ko ganinsu ba ayi"

Rumaisa ta ce "Wallahi sun fara fitowa, mama ta ce duk wanda ya taɓa ciki zai fito mini, kuma korata za su yi daga gidan su, yanzu da ya sa an koreni fa, ni fa bana son ma su fito, idan ba haka ba mama zata hanani yawo ba riga, yanzu ma hanani take yi"

Aisha ta yi dariya ta ce. "gaskiya ki daina zaginsa tun da dai ba a korekin ba, kin yi masa sharri, ina wani abun taɓawa a nan" tayi maganar tana sake tuntsirewa ruma da dariya.

Ruma ta ce "Wallahi ya taɓa, kuma idan Allah ya sa na bar nan idona idonsa zai gane bashi da wayo, ana i gobe zan zo katsina, yayi mini wanka da kwata a tsakiyar layi, wai har da cewa na yi masa sharri da nace ya taɓani, wai zuwa yayi ya duba ya ga ko akwai wani abu a ƙirjina ki ji ɗan iska fa"

Aisha ta dafe ƙirji ta ce "Wayyo zuciyata, haba baby rumaisa sunan mijina adam, kar ki sa kishina ya tashi. Amma ni nawa Adam ɗin shima yana da zafin zuciya, baya son raini ga miskilanci, amma idan ki ka fahimce shi, mutumin kirki ne, mai son kulawaga iya soyayya, sai dai...." ta ɗan yi shiru sai kuma ta ce "Ruma zaki auri Adam?"

Ruma ta waro ido ta ce "wane Adam ɗin? Ni da ban yi tsawo na girma ba za ayi mini aure?".

"Adam da kuke faɗa, ki yafe masa ko dan albarkacin yana da sunan mijina"

Ruma ta turɓuna fuska ta ce "Ai wallahi ko yayanki ne ba zan yafe masa ba, da in auri Wannan gara na mutu ba aure, kuma ni miji kyakkyawa nake so, kuma mai kuɗi"

"In dai kuɗi ne akwai su ruma, kuma ai kyakykyawa ne"

Rumaisa ta dubeta ta ce "Ba fa mijinki ba, wannan da muke faɗa nake gaya miki, mai suffar mugwaye da wata banzar motarsa in sha Allah sai an sace motar ma".

"In an saceta ma zai sai wata, kuma ya sai miki kema, banda faɗan rashin gaskiya ke fa ki ka fara zaginsa a social media, amma tsabar rigimarki kina ta zaginsa, kin ci sa'a da bai ɗaureki ba, ko ya sa a zaneki ba".

"Oho ni dai ban yafe ba"

Tayi ajiyar zuciya ta ce "I love your confidence my dear, you can face the challenges. Jikina na bani wani abu game da ke, zaki iya ruma" tayi maganar tana jan kunatun rumaisa ta ce "Kamar haka mijina yake wasa da kumatuna".

"Anty Aisha, yake taɓaki? Ba a wasa da maza fa" ba ta bawa ruma amsa ba, sai dariya da take yi mata, tana fatan Allah ya tabbatar da abun da take ji game da ruma.

Ranar da zata rasu bayan ta haihu, ta riƙe hannun rumaisa ta ce "Baby rumaisa, idan Allah ya sa kin kuɓuta, ni 'yar gidan turakin kano ce, amma kar a nemi mahaifina kai tsaye a nemi sirikata, idan ba zaki iya riƙe jaririn nan ba, ki danƙa mata shi, Hajiya Binta giwar Galadima, uwar gidan galadiman kano, sirikata ce ita zaki danƙawa jaririn nan, ɗan ta shine mijina" a lokacin gaba ɗaya ruma ta manta da wani adam balle ta kawo shi a lissafi da aisha ta yi zancen galadima.

Ko da ruma ta zo nan a tunaninta sai ta tambayi kanta 'Kenan da gaske shi ne mijinta?' a zahiri kuwa ta fashe da kuka ta ce "Wallahi ba shi ne babansa ba, ni ba shi ta ce mini ba" a bata iya tafiya ta fara ƙoƙarin dirowa daga kan gadon tana miƙa hannu ta ce "Ni ku bani jaririna, ba ɗansa bane ba, ni ba ta ce mini in bawa kowa ba, ku bani ɗana" mama tayi shiru ta zubawa sarautar Allah ido.

Bashir ya miƙawa Adam hannu ya ce "Ka ga Adam, kawo yaron nan, gaba ɗaya a ruɗe take, kamar ba ta hayyacinta ne ma, kawo a bata shi kan muga yadda hali zai yi".

"Bashir ka haukace ne? Taya ka ke cewa in baka ɗana ka bawa wani?".

"Wallahi ba ɗansa bane ba, ku bani ɗana" ruma tayi maganar tana kuka.

Bashir ya karɓe yaron, ya miƙawa rumaisa, ta rungumeshi tana fashewa da kuka ta ce "Cewa ta yi idan ba zan iya riƙe shi ba, in bawa giwar Galadima ni ban santa ba ma, ban san a in da take ba, amma ni dai zan iya riƙe yarona, ai cewa ta yi ta bar mini shi har abada nice mamansa". Gaba daya ɗakin aka zubawa sarautar Allah ido.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull