Kanwar maza 3 and 4 complete - Chapter 18
Kanwar maza 3 and 4 complete Chapter 18: Kanwar maza 3 and 4 complete Chapter 18. "Ban san ya zan yi ba, jinina kar ya ƙare ka mayar da ni asibitin".
4,500 words
"Ban san ya zan yi ba, jinina kar ya ƙare ka mayar da ni asibitin".
Guntun tsaki ya ja, ya wuce banɗakinta, ruwa ya haɗa mata, ya fito ya ce "Shiga" ba musu ta taka a hankali ta wuce banɗakin.
Ya nuna mata yadda za ta yi, ta wanke jikinta, ya fita daga banɗakin, ya janyo akwatin lefenta, ya ɗauko mata pad, kasancewar lokacin da aka haɗa lefen har da ita a ciki. Ya ɗauke bedsheet ɗin daga kan gadon.
Ta fito sanye da doguwar rigar da ta shiga da ita banɗakin, tana ta raɓe-raɓe.
Ya kalleta ya ce "ƙazamar ina ce ke? Ba ta ɓaci da jini ba ki ka kuma sakawa?".
"To ba kaya zan fito?" Ta yi maganar tana kawar da kanta gefe.
Ajiye mata pad ɗin yayi, ya ɗauki bedsheet ɗin ya fice.
Ya je ya dawo, ya tarar da ita ta canza kaya, amma pad ɗin na in da ya ajiyeta.
"Ba zaki saka bane?".
"Ban iya sakawa ba, waccan ma su yaya ne suka saka suka bani"
Kallonta yayi, kuma da gaske take maganar, ba wai wasa take ba.
Ya nuna mata yadda za ta yi amfani da ita, ya sanar da ita, duk awa biyar zuwa takwas, ta yi wanka, ta cire pad ɗin ta ɗaure a leda, ta canza phant ta canza wata. Ta jinjina masa kai, ya fita ya bar mata ɗakin.
Ba tare da ya rintsa ba, haka ya shirya fita aiki, ko karyawa bai yi ba ya sauka domin tafiya, ya cewa baba uwani, idan rumaisa ta tashi a tabattar ta ci abinci, sannan akwai bedsheet a washing machine, a wanke a shanya, a haɗa da kayanta da ta cire suna banɗakinta.
Ta amsa masa da za ayi, sannan ya fice.
Ko da baba uwani ta ciro bedsheet ɗin, ta shanya, kallonsa ta din ga yi, da in da jini ya shata, ta yi shiru da ta tuna a yadda ya tafi Ruma asibiti jiya.
"Anya ba wani abun ne ya faru a tsakanin su ba, babu ko tantama ya haikewa yarinyar nan, amma dai wannan akwai jarababbe wannan ƴar tatsitsiyar ƴar? Wannan ba labarin da zan gaya wa Samha ba ne, ko Hajiya Jamila ƙarshenta ma na sha zagi".
Babban abun da ya yi wa rumaisa daɗi, bai wuce da ta tashi ta tarar da iman ba, ta ce "Anty Iman, meyasa baki tasheni ba?"
Iman ta ce "Ni na isa? Yaya ne ya ce lallai in zo, in tayaki zama ba kya jin daɗi, karatu nake yi an kusa yi mana screening na sauka".
Rumaisa ta ce "Ni dama ki dawo gidan da zama, ina jin daɗin ganinki a gidan nan, tun da aka kawoni fa, ban ga mama ba, ranar da ki ka zo, su mai sunan baba su ka zo, ko zama ba su yi ba, suka tafi"
"Eyya, kar ki yi kuka, baba uwani ta ce baki karya ba, ki karya sai na baki wayata, ki kira maman".
Haka kuwa aka yi, rumaisa ta karya, ta karɓi wayar Iman dan kiran mama a waya, amma ba ta shiga, sai ta saka lambar mai sunan baba ta kira shi a waya.
Tun a lokacin da ta yi masa kira na farko, tana neman rumaisa, ya gane lambar, kuma lambar take cikin kansa, ko da bai ɗaga ba ya san lambar iman ce, yana kallon wayar ta ƙaraci ringing ɗin ta, ta kaste yaƙi ɗagawa.
Lambar Usman ta yi trying, shi ma sai da ta kusa katsewa, sannan ya ɗaga yayi sallama.
"Saboda tsabar kun tsaneni, kun kawo ni, kun ajiye ni, ba wanda yake nemana mama ma taƙi zuwa ta gannu, kuma bani da lafiya ma"
"Iyee, ko amsa sallamar ma ba zaki yi ba, sai wassafo mini ƙorafi?".
"Mama taƙi ta zo ta ganni, ni na gaji da zaman gidan nan, dan Allah ku zo ku tafi da ni, gida nake so, kuma bani da lafiya".
Usman ya ce "Ke ban son shirme, a hakan zamu zo gidan naki, ki na yi wa mutane kuka? Meya sameki?".
"Fitsarin jinin da nake ne na kuma yi, a asibiti fa na kwana, cikina ya din ga ciwo, jini sai zuba yake mutuwa zan yi idan baku zo ba".
Maimakon usman ya tausaya mata, sai ya ƙyaƙyace da dariya, ya ce "Kin ci kai, Allah sarki girma ya zo".
Cikin kuka ta ce "Yaya usy da gaske nake, a asibiti na kwana wallahi"
Sai kuma ya daina dariyar ya ce "Ahha haba dai?".
"Tun da baka yadda ba, bani mama mu gaisa".
Usman ya ce "Maganar gaskiya mama ta tafi cikin gari, yi wa mutane bangajiya, amma idan ta dawo sai a kiraki".
"To ai ba wayata ba ce ba".
"Aliyu yana da lambar mijinki, zamu zo ma in sha Allah, Allah ya ƙara lafiya uwar gida sarautar mata" yayi maganar cikin zolaya. Ganin ba shi da niyyar ɗaukar maganar ta ta serious ya sanya ta katse wayar.
*** "Ya ake ciki da maganar yaron nan ne, kwana biyu na jika shiru, babu wani update a kan moves ɗin sa ne?".
"Ranka ya daɗe, ai babu wani sabon abu, ka san yayi aure kwanan nan, kuma kamar ma hankalinsa ba ya kan aikin a kanka yanzu, ko cikin Abujanma, ya fi watanni rabonsa da zuwa".
"A'a fa, ka san yaron nan da wayon tsiya, kar in je lumbu-lumbu yake yi mini, yana wani binciken ta ƙarƙashin ƙasa, ko shirya wani abu da ban sani ba".
"Babu abun da yake aiwatarwa, ba tare da na san motsinsa ba, a yanzu dai haka babu ranka ya dade".
Ya juya ya kalli wakili ya ce "Khalifa, kai wurinka babu wani update ɗin".
Khalifa ya ɗan sauke numfashi ya ce "Babu Daddy, sai dai ina nan ina ta bin diddigin sa fiye da yadda ka ke tsammani, babu wani abu da yake yi s kanmu, sai dai wani ƙishin-ƙishin da nake ji, wai yarinyar da ya aura, ita ta tserato da ɗan sa daga wurin masu garkuwa da mutane, amma bani da tabbas, an ce in jira a samu tabbacin hakan". Senator wakili ya jinjina kai ya ce "Duk yadda ake ciki ka sanar mini, idan har ita ɗin ce, ka samo mini tabbacin hakan, a kan lokaci".
"To shikenan, In sha Allah daddy"
*** A duk lokacin da rumaisa ta je canza pad, cikin ƙyanƙyami take yi, kuma a tsorace take da tunanin jininta zai ƙare, har sai da iman ta fuskanci wani abu, amms ba ta takura mata da son sanin menene ba, tun da ba ta gaya mata ba. Mai sunan baba kuwa wuni yayi yana kallon missed call ɗin, iman a wayarsa, yana tunanin me za ta ce masa haka, da har ta yi masa 3missed calls, ko tana nufin ta ce Haryanzu ba ta san wayarsa ba ce ba?. Gashi dai yana sane yayi ignoring kiran, amma yana son sanin dalilin kiran.
Yau sai da takawa ya dawo, sannan iman ta fara shirin tafiya gida, rumaisa ta din ga yi mata magiya a kan ta kwana, amma ta ce ba ta gaya wa ammi ba, direba ya zo ya ɗauketa ya mayar da ita.
Takawa ya dubi ruma da ta haɗe rai saboda Iman ta tafi ya ce "Ya jikin naki?".
"Da sauƙi"
"Kin sha magungunan ko kuwa?".
"Na sha" ta amsa masa a taƙaice, bai sake kulata ba ya ƙyaleta, dan yanayin fuskarta ya nuna masa a fusace take, idan ya biye mata rashin kunya za ta yi masa.
Mai sunan baba kuwa, missed calls ɗin nan a ransa ya wani, zuciyarsa na ta raya masa ya bi kiran nan, ko ya manta ya cigaba da sabgoginsa, sai ya tuna, yayi iya ƙoƙarinsa ya manta, amma ya kasa, yana ta tunanin menene haka mai muhimmanci da ya sanya ta yi masa missed calls har uku.
Babban abun da ya ɓatawa iman rai, bai wuce yadda ta koma gida ta tarar da Jabir ba, ya kasa ya tsare a falo, suna hira da Ammi, yana ganinta ya hau rawa jiki, ya fara yi mata hira. Iya ƙoƙarin ta take yi, kar ammi ta fuskanci wani abu, dan haka ta ke amsa masa hirar.
Ammi ta tashi ta bar musu falon, ta tafi ɗakinta, iman na shirin tashi ita ma, wayarta ta fara ringing, ba ta duba ba ta ɗaga ta saka a kunnenta, tare da yin sallama. Shiru yayi bai amsa ba, sai wani numfashi da yake saukewa a hankali, yana jin yadda murayar ta ta, ta daki zuciyarsa.
"Hello, ba a jina ne, Assalamu alaikum" ta yi maganar cikin ɗabi'arta ta iyayi.
"Missed calls na gani" yayi maganar cikin dakakkiyar muryarsa da take razanata.
Sai da ta ɗan ruɗe, amma ta yi iya yin ta, ta haɗa nutsuwar ta wuri guda ta ce "Yaya Umar ina wuni?".
"Lafiya ƙalau".
"Dama Anty Rumaisa ce ta karɓi aron wayata ta kiraka, kuma ba ka ɗaga ba, ba intentionally na kira ka ba, ai ka gaya mini na daina kiran wayar ba tata ba ce, ka yi haƙuri dan Allah" ta ƙarasa maganar kamar za ta saka masa kuka.
Ji yayi jikinsa har wani rawa yake yi, dan shi a rayuwarsa, idan ba mama da rumaisa ba, babu wata ƴa da yake keɓewa yayi wata doguwar magana da ita, ko ita rumaisan ba shiga shirgin ta yake yi ba, amma ya tsinci kansa da jin daɗin sauran muryarta.
Amma da yake namiji namiji ne, cikin basarwa ya ce "Ina rumaisan take?".
"Ɗazu ne na je gidanta, ba ta jin daɗi shi ne ta karɓi wayata, ta kira ka, amma ta ji sauƙi".
"Shikenan" ya katse wayar.
Wata irin ajiyar zuciya ta sauke, duk da muryarsa na razanata, amma ta tsinci kanta da jin daɗin kasancewa da shi ta waya. Wani guntun murmushi ta yi, tana ɗaga kai ta ga Jabir da Nusaiba duk ita suke kallo.
"Iman da wa ki ke waya?" Jabir yayi maganar a hasale.
"Kamar yaya? Yayan Anty rumaisa ne".
"To meye alaƙarki da shi" ya sake yin maganar yana tsareta da ido.
Tashi ta yi tsaye ta ce "Yayan matar wa na ce, kuma ni babu wani abu tsakani na da shi, ta ari wayata ta kira shi ne kawai".
"Ina fa lura da yadda ya din ga bin ki da kallo lokacin bikin nan, idan ya ganni tare da ke ya din ga hararata".
Ta girgiza kai ta ce "Gaskiya kai ne ka ga haka, amma ba hakan bane" ta wuce ta nufi ɗakinta.
Jabir zai kuma magana, Nusaiba ta ce "Uncle J, ka bi ta a hankali, fushi da tashin hankali ba naka bane ba, ba abun da yake tsakaninta da mutumin nan, na riga na baka shawara, ka je wurin ammi kawai, ko ka gaya wa turaki, na san komai zai zo da sauƙi" sauke numfashi ya yi, ya tashi ya fice.
*** Tun da Adam ya fara hawo wa step ɗin bene, yake jin ƙauri, yana hawa falon saman, ya tarar da ya turnuƙe da hayaƙi, kuma hayaƙin daga kitchen yake fitowa. A sukwane ya nufi kitchen ɗin, ya na zuwa ya tarar da rumaisa tana suyar wainar fulawa tana tari, Saboda ƙaurin manja.
"Ke meye haka? Me ki ke yi?"
Ta waiwaya ta ce "Girki nake yi"
Da sauri ya ƙarasa yana ƙoƙarin kashe gas ɗin, dan tuni suka haɗa baki da iman, direbanta ya ɗuro mata.
Tarewa ta yi ta ce "Girki fa nake yi na iya"
"Matsa, ban ce kar ki kuskura ki ce zaki yi girki ba?" Buɗe masa flask ta yi ta ce "Ka ga fa, na iya" wainar fulawa ce ta yi saƙa mai kyau, sai ƙamshin attaruhu take. Ba ƙaramin mamaki ta bashi ba, amma a fili ya ce "Idan ki ka yi mini gobara a gida, sai na casaki".
Ta ce "Eh na yadda" ya gyaɗa kai ya fice.
Kusan awa guda, ya ma manta da batun rumaisa ya tuna kar ta yi wata aika-aikar, ya leƙa falo, ya hangota tana ta suɗar baki tana cin yaji.
Ganin tana lafiya, ba wani abu da ya faru, ya sanya ya nemi wuri ya kwanta, dan a gajiye yake sosai.
Sai dai bacci ya gagare shi, tunani daban-daban ya addabi kwanyarsa, ya rungume pillown sa, ya rintse idanunsa, ba ya son tuna yana da tarin matsalolin da ya kasa soloving ɗin su. Ga wani abu da yake bijiro masa ba gaira babu dalili.
Tashi ya yi ya kunna fitilar ɗakinsa, ya tafi kitchen, sai dai ya tarar da rumaisa ba ta yi bacci ba, tana ta gyara abubuwan da ta ɓata, tana tsaye a gaban sink tana wanke-wanke.
Bai ce mata uffan ba, ya ɗauki heater, ya zuba ruwa ya jona, ita ma ba ta kula shi ba, ta cigaba da aikinta.
A ransa yake yabawa mahaifiyar rumaisa da yayyenta, dan a ƴan kwanakin da suka yi, ya fuskanci tana da ƙoƙarin tsafta.
Tea yake son haɗawa, ga ruwa ya tafasa amma sai duru-duru yake yi.
Ta kalleshi ta ce "Rumaisa, dan Allah tun da na ga kin iya girki, dafa mini tea, zan sha. Shi ne abu mai wahala a wurin ka, bari dai na taimaka maka, ai tun da na ga ka ɗauko kofi na san shayi zaka sha, a gida ma kusan kullum sai su Yaya Aliyu sun sha shayi da daddare".
Ta taka kujera, ta buɗe wata drower, ta ɗauko Lipton, da kayan shayi, wanda bai san a in da ta same su ba.
Ta zuba a cikin ruwan zafin, ta sake tafasawa, ta ɗauki ƙaramin flask ta juye masa, ta haɗa masa da kofi a kan tray, sannan ta ce "Gashi nan, kar ka damu ba sai ka yi mini godiya ba, dan na san ba za ka yi ba, muna da irinka a gidanmu. Idan ka gama shan shayin, ga omo da soso, ka wanke kofunan, kar ka bar mini kwanuka wani abun ya bi".
Kamar soko haka yake kallonta, ta ɗauki wani ɗan bowl, ta zuba uban cabin da madara da sugar, ta fice.
Washegari ta tashi da safe, tana aikace-aikacen ta, barira ɗaya daga cikin hadimanta, ta kawo abinci ta ce na takawa ne. Ta karɓa ta ajiye masa, dan da baba uwani ta gaya masa rumaisa ta ce a daina kawo abinci, cewa yayi su ƙyaleta su cigaba da kaiwa.
Ɗakinsa ta shiga da kayan mopping, ta tarar yana banɗaki yana wanka, ta karkaɗe masa gadon, ta gyara ta kalli gadon bai gyaru sosai yadda yakamata ba, ta ce "Oho, ni a gidanmu babu gado sai katifa, hakan ma na yi ƙoƙari ai".
Idonta ne ya sauka a kan side bed, in da ya sha shayin, nan ya bar kwanukan, "Kam bala'i, Wa ya bar wa kwanukan nan a nan?" Ja ta yi ta tsaya tana jiran fitowarsa.
Rigar wanka ce a jikinsa, sai dai gaban rigar a buɗe yake, gashin ƙirjinsa ya kwanta saboda ruwa, da sauri ta kawar da kanta gefe.
"Ya aka yi?".
Ba ta kalleshi ba ta ce "Eh kwanukan da na ce idan ka gama shan shayin ka wanke na gani a nan".
Ya ce "Eh, idan kin gama ki fita da su ki wanke"
"Ni na sha maka da zan fita da su in wanke?"
Ya kalleta ya ce "Me ki ka ce?" Ta girgiza kai ta ce 'Bakomai".
"Oya kwashe su ki fita da su, ki je ki wanke, sannan kan na gama karyawa, ki shirya, zamu je gidan turaki".
Ta ji daɗi za su fita, amma babban abun da ya bata haushi, bai wuce sakata fita da kwanukan da shi ya mora ba ita ba.
Wata turkey abaya ta saka, blueblack fuskar nan fayau babu ko kwalli, ta yi ta shafa turare, dan akwaisu available a kan mudubinta, dan ko a gida ta saba, dan Abdallah har ɓarauniyar turare yake ce mata.
Suna tafe a hanya, tana kallon titi, tana son gane hanya, dan so take wataran ta ɓalle ta tafi gida.
A gidan turaki suka tarar da Jabir, da shi da Jamil ga kuma Zainab da Mummy, Samha ce ba ta nan.
Rumaisa ta gaishe su, sai dai ba wanda ya amsa mata da mutunci sai Zainab.
Adam ya ce "Zainab nema mana iso wurin mai girma turaki" ba musu Zainab ta tashi.
Rumaisa da sun haɗa ido da Jabir take galla masa harara, haka Jamil da yake ta kallonta a wulaƙance.
Aka yi musu izinin shiga wurin turaki, turaki yana ganin rumaisa ya fara murmushi.
Ita ma Murmushin ta yi ta ce "Barka da wannan lokaci ranka ya daɗe".
"Barkanmu dai ƴar albarka, ya gidan ya ƙoƙari?"
Ta amsa da "Alhamdilillah"
Adam har leƙa fuskarta yake, ya ga ko ita ce ta nutsu haka.
Shi ma suka gaisa da Adam, Adam ya ce masa sun zo su yi godiya ne, tare da yi musu bangajiya na hidima da aka yi.
Turaki ya yi musu nasiha sosai, mussaman ma Adam, a nasihar rumisa ba komai take fahimta ba, mussaman da ta ga da Adam ake.
Bayan turaki ya gama, yayi musu addu'a sosai, Adam yayi ta godiya, ya ce masa za su je wani wurin daga nan.
Rumaisa ta ce "Babana, yaushe zaka zo gidanmu, na iya abinci in dafa maka duk abun da ka ke so?" Yayi murmushi ya ce "Za a zo ne in sha Allah".
Gudun kar ta fara sakin layi kamar yadda ta saba, ya sanya adam sakata a gaba suka fita, sai dai a wannan karon sai suka fita ta ƙofar da zasu fita haraba kai tsaye, ba tare da bi ta falon gidan ba, sai dai suna fita suka yi kiciɓis da Samha!
Ayshercool. 08081012143 *Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Susbcribe my YouTube channel please 🙏
Adam yayi ta maza ya ce "Au dama kina nan? Mun wuce su mama a falo ban ganki ba ai".
Cikin matsanancin takaici ta ce "Meye na borin kunya kuma? Ai ba ka so ka ganni ɗin ba ne? Tun da har ka shiga ta falo, ka biyo ta nan za ka tafi".
Rumaisa ba ta kula Samha ba, dan ba zata manta fuskar ta ba, ta mayar da hankali wurin tsinkar furanni da ke wurin, sai dai tana jin duk abun da suke faɗa.
"Yanzu da ma adam a kan wannan abar ka wulaƙanta ni, ka ƙi ka aureni? Yanzu wannan abar wani abu ta fi ni da shi, yarinyar da ba ta kai a kirata mace ba ma, an ya ka yi mini adalci kenan? Soyayyar da na nuna maka tsawon shekaru shikenan ba ni da wata makoma?"
"To ni idan ba mace ba mace ba ce, namiji ce ni?" Rumaisa ta yi maganar tana riƙe ƙugunta.
Adam ya kalli rumaisa ya ce "Wuce ki je mota ki jirani"
"To saman motar zan hau ko ƙarƙashin tayoyi? Tun da a rufe take".
"Duk in da ya yi miki" kallon banza ta yi wa samha ta wuce.
Samha tana ta tunanin a ina ta san fuskar rumaisa ma, ta kasa tunawa, ta ma fi cika ido a hotunan bikinsu, a zahiri kuwa ƙwaila ce ta gaske.
"Yanzu abun da ki ka yi kin kyauta Samha? Da auren wuri aka yi miki, ko baki haifeta ba kin kusa, wannan ai salon ki janyo wa kanki raini ne".
"Ban damu ba adam, ba raini ne a gabana ko akasin haka ba, ni batun soyayyaya ta ce a gabana, wallahi ka cutar da ni Adam".
Adam ya ɗan yi shiru, sannan ya ce "Ban cutar da ke ba Samha, abun da nake son ki gane shi ne, komai muƙadarri ne na Allah. Daga haɗuwata da rumaisa, zuwa lokacin da na aureta, da zan gaya miki zaki gane aurena da ita ƙaddarar Allah ce".
"Ba ka son ta kenan?"
"Ba zan ce eh ba, kuma ba zan ce a'a ba, ki yi haƙuri ki cigaba da addu'a, idan da rabo sai in aureki, idan kuma babu ko yi haƙuri, ki auri wani, kar ki ce zaki cigaba da zaman jirana samha".
Rumaisa kuwa ranta a ɓace, ta ƙarasa in da motarsu take, tana zuwa ta ga Jamil da Jabir a tsaye a wurin suna magana, ba ta kula su ba ta tsaya, tana hura hanci.
Jamil ya ƙarewa rumaisa kallo ya ce "Lallai, Adam sai ka ce makaho, dan Allah ina mamora a tare da wannan yarinyar? Me wanna za ta tsinana masa a zaman aure? Yanzu wannan ya zaɓa ya bar Samha? Saboda wannan abar?".
Jabir ya ce "Kai ba ka san komai ba ai, ba ta da kunya ne yarinyar nake gaya maka, kai ka ga wahalar da ta din ga bashi, ka san ita ta dawo da jaririn fulani, kan ta faɗi fulanin ma ta rasu, sai da aka kai ruwa rana, ba ta da kunya"
Zabura Jamil ya yi ya ce "Kana nufin da gaske wannan yarinyar ce, ta dawo da yaron wurin aisha?".
Jabir ya ce "Tambayeta ka ji"
Juya musu ƙeya rumaisa ta yi, tana wasa da ƙasa da ƙafarta.
"Ke, da gaske kin ga fulani, kin ganta a hannun ƴan bindiga, suwaye? Ya aka yi suka kasheta?" Yayi maganar cikin rikicewa yana kallon rumaisa,ya na jin tamkar yanzu A'isha ta rasu.
Ɗaga kai Rumaisa ta yi ta kalleshi, ta yi guntun tsaki.
"Magana nake yi miki, aisha ƙanwata ce, jami'in tsaro ne ni, ki gaya mini abun da ya faru, ko kuma ƙarya ne kawai haɗin baki ne?" Yayi maganar kamar zai kaiwa rumaisa duka.
Sheƙeƙe rumaisa ta ce "To mijinta ma shi Adam ɗin ban gaya masa komai ba, balle wani kai, ba ruwanka da ni kuma, wallahi ka sake ce mini wannan abar, sai na yi maka rashin mutunci, mai na yi muku, ni na ce kar ya auretan? Wannan masifaffiyar matar na na ɗauka ma babar wasu ce".
Daga nesa da ya tunkaro su, ya hangi rumaisa tana zazzaga masifa, Jabir ya riƙe hannun Jamil, ya ce kar ya yi magana.
Adam ya ƙaraso ya ce "Lafiya kuwa?"
Rumaisa ta ce "Ce mini yayi wai wannan abar, ni na ce kar ka auri waccan matar, da za su din ga ce mini wai wannan abar, shi kuma wannan har da ce mini mara kunya, me na yi masa na rashin kunya".
Adam ya buɗe motar, ya ce wa rumaisa "Shiga ki jirani"
Buɗe motar ta yi ta shiga ta zauna, tana cigaba da tura baki.
Adam ya kalli Jamil ya ce "Sannu Jamil, kirkin ka har ya yi yawa, shikenan ita rayuwa ba za a karɓi ƙaddara ba, ka ƙi halartar ɗaurin aurena, kuma ka ƙi yi mini Allah ya sanya alkhairi".
"Allah sanya alkhairi saboda ka auri wannan abar?" Yayi maganar yana nuna motar adam.
Adam ya sauke hannun Jamil ya ce "Ko dan albarkacina, yakamata ka tausasa harshe a kan ta, matata ce, kuma bana son zumuncinmu ya samu matsala saboda son zukatanmu".
Jamil ya ce "Adam ka na da ƙwarin gwiwar yin wannan maganar? Dama yarinyar nan ita ce ta zo da jaririn aisha, ka ce aisha a hannun 'yan bindiga ta mutu, ya aka yi ita ta kuɓuta, wani mataki ka ɗauka, na san dole ba za a rasa wani information daga bakinta ba, menene dalilinka na ɓoye mana?".
Nan da nan Adam ya hasala ya ce "Kai ma kana zargin ni na kashe fulani na yi tsafi da gawarta ko? To na yi, idan wani bayani ka ke da buƙatar ji daga bakinta, ka je ka tambayi mai girma turaki".
Cikin sauri Jabir ya ce "Jamil, bai kamata ka faɗi irin wannan maganganun ba, da na san haka abun zai zama, da ban gaya maka ba, takawa dan Allah ka yi haƙuri"
Bai ko tsaya ba, ya wuce mota, ya buɗe ya shiga, zuciyarsa na yi masa wani irin zafi.
Sai da suka ɗan yi nisa sannan ya cewa rumaisa me suka ce miki?.
"Su wa?" Kallonta yayi, ta ga alamar babu wasa a idonsa, ta ce "Tambayata yayi, wai ya aka yi na san anty aisha, ni kuma na ce ban sani ba"
Jinjina kai kawai ya yi, ya cigaba da tuƙinsa.
Wani store yayi parking, ya ce ta fito su shiga. Ta fita ta bishi tana kallon wurin.
Suka je ɓangaren jakunkuna ya ce ta zaɓi jakar makaranta. Haushi ne ya kamata, dan ko zancen makaranta ba ta so.
Ya sai mata kayan karatu da rubutu, da takalma, jakar ma uku ya saya mata, sannan ya sakata a mota suka tafi.
Gidajen ƴan uwansu ya din ga zagayawa da ita, suna gaishe su, sai dai rumaisa ta ƙule da yadda wasu suke karɓarta, tare da nuna ita yarinya ce, ta yi masa ƙarama da aure. Babu wanda ya sake ƙona mata rai, kamar hajiya Lubabatu, wato mahaifiyar Jabir, matar Galadima mai ci a yanzu.
Ban da tana ganin girman matar, ta yi sa'ar mama, da babu abun da zai hana ta zageta, dan ma Adam yana ta kareta, amma matar ta ci zarafinta, duk da bakomai take fahimta ba.
"Ragowar ƴan bindiga aka kawo mini kenan, lallai takawa, ka yi jihadi sai fatan Allah ya biya ka".
Adam ya ce "Ba ragowa ba ce ba, kuma aurenta ba ni na yi jihadi ba, ita ta yi, tun da kun san waye ɗanku, amma ta amince da aurensa".
Hajiya Lubabatu ta yi dariya ta ce "Yo ba dole ba, ai ko a turu kake ɗan mu yana da arziki da sarautar da za a aure shi domin sa, kuma a zauna da shi, kwaɗayin abun duniya ne kawai". Ba dan Ammi ta matsa, lallai ya zagaya da rumaisa, ya nuna mata familynsa ba, ya kuma yi musu bangajiya ba, da babu abun da zai sanya ya zo gidansu Jabir, wurin mahaifiyarsa.
Adam ya ce "To Hajiya, ina ga bari mu koma, akwai in da zamu je".
"Ahh haba dai, na saka a ɗora muku girki ai".
"A'a Alhamdilillah, a ƙoshe muke".
Hajiya Lubabatu ta ce "Gaskiya ban ji daɗin wannan zuwan ba, yakamata a kawo mana ita ta wuni, da haka tana shiga cikinmu, za ta san yadda matan sarakai suke rayuwa, dan na san ba sani ta yi ba".
Adam ya ce "Bakomai ana koya mata"
Wata hadimar Hajiya Lubabatu ta ƙaraso, ta bawa hajiyar wata leda. Ta karɓa ta miƙawa rumaisa ta ce "Amarya ga wannan ba yawa, kya sai tsintsiya, sai na sake kawo ziyara, tun da rabona da gidan, tun washegarin kai ki, mun ce a bamu ƙyalle mu tabattar da abun da aka auro mana, an yi mana wala wala".
Rumaisa ta sha kunu, ta ƙi karɓar ledar.
"Ki karɓa mana" rumaisa ta girgiza kai ta ce "A'a"
Hajiya Lubabatu ta ce "Takawa, ba ka gaya mata, masarauta ba ma kyauta ace a'a ba, rayuwar masarauta, ba kamar ta sauran gama garin mutane ba ce".