Kenza eBookz

Kanwar maza 3 and 4 complete - Chapter 20

Kanwar maza 3 and 4 complete - Chapter 20

Kanwar maza 3 and 4 complete Chapter 20: Kanwar maza 3 and 4 complete Chapter 20. Ya ganta tana hawowa sama, bai san me ta je yi ƙasa ba, ya ce "Ki shirya,…

4,497 words

Ya ganta tana hawowa sama, bai san me ta je yi ƙasa ba, ya ce "Ki shirya, gobe in Allah ya kaimu da safe, zan kai ki makaranta"

Ɓata fuska ta yi, dan sam ko zancen makaranta ba ta so. Ya juya ya koma ɗakinsa.

Da asuba ta yi wanka, ta yi salla, tana tantama dai-dai ma ta yi wankan, ko ba daidai ba, dan ba za ta iya tunawa complete yadda mama ta koya mata ba, kuma ita ba za ta tambayi takawa ba.

Haryanzu rumaisa tana ɗokin sababbin kayan kitchen, dan haka haryanzu ba ta gaji da shiga kitchen ta yi girki ba.

Ta dafa tea, ta fito da biscuit, ta nufo falo, takawa ta gani a kan dining, ga kayan karyawarsa a kan dining, baba uwani kuma durƙushe a gabansa, ba ta san me take ce masa ba.

Kai tsaye ta nufi dining ɗin, ba ta kula su ba, ta je ta hau saman dining table abun ta, ta fara ƙoƙarin haɗa tea.

Baba uwani ta yi shiru, ta daina maganar da take yi.

"Barka da safiya ranki ya daɗe".

Rumaisa ta ce "Yauwwa sannu".

"Meye haka, zaki hau saman dining?".

"Idan na zauna a kan kujera, bana jin daɗin zama a kan tebur ɗin, gara na hau sama, ya fi daɗi, ka san babu a house".

Ya girgiza kai ya ce wa baba uwani, "Je ki kawai, ma ƙarasa maganar".

Tunani rumaisa take yi, me baba uwani take gaya masa, da ba za a faɗa a gabanta ba.

"Haɗa mini tea zan karya, ki je ki ɗauki jakarki mu tafi"

"Ni na kawo maka da zan haɗa maka, ita wadda ta kawo makan ta haɗa maka mana"

Hannu ya saka ya janyo ta ta baya, ya jawota ta ƙeya tana kallo fuskarsa.

Ya ce "Da ni ki ke?".

"A'a da kaina nake" ya hankaɗata ta tashi zaune, tana ƙiƙƙifta id.

Ta janyo kayan tean, ta fara haɗa masa, tana yi tana tura baki ta miƙa masa.

Ita kuma ta yi ƙerere a kan table, tana karyawa.

Ba ta gama na ta ciye-ciyen ba, ta ji ta ƙoshi, ta tashi ta kwashe kayan.

Sai wurin ƙarfe tara da rabi, sannan suka fita, ya tafi kaita makaranta.

Tsari da ginin makarantar, ba ƙaramin burge rumaisa ya yi ba, ta tabattar wa da kanta, akwai banbanci a tsakanin makarantarsu, da wannan, hatta ajinsu, basu da yawa, ga kujeru masu kyau, ga fankoki ko ina ga kayan wasa, ajinsu har da projector, da ake haska musu komai, duk wani abu na koyo da koyarwa akwai makarantar nan, makarantar ta burge rumaisa.

Kan takawa ya tafi, sai da aka kai shi har ajin su rumaisa, ya kalli ruma ya ce "Yau ga ki a makarantar ƴaƴan ɓarayi da suke sace muku kuɗi suna karatu. Sannan ba zan lamunci ina biyan kuɗin makaranta in tarar ba kya karatu ba, kullum zan din ga tambayarki me aka koya muku. Ban da surutun banza, da ciye-ciye. Na bayar da ordern abinci a wani restaurant, za su kawo miki abincin break, tun da kin ce ke ba za a dafa a gida ki ci ba".

"To, kai zaka zo ka ɗaukeni, ko gida zan tafi?".

"Dama ke ki ka kawo kanki?"

"Ahh na san hali ne, kar ka tafi ka barni, ka ga kayan wasa a makarantar nan, zan sha lilo, idan na din ga hawa ina sufa...."

"Ba shi na kawo ki yi ba, karatu zaki yi, wuce ki shiga aji"

Rumaisa ta shiga ajin, tana ƙarewa ajin na su kallo.

*** Takawa kuwa da ya tafi hanya, Bashir ya kira a waya, ya ce masa zai shiga bamfai su haɗu su yi magana.

Haka kuwa aka yi, ya haɗu da Bashir, sai dai bai shiga ciki ba, a shiya fito haraba, suka haɗu.

"Allah ya taimake ka, ya amarya yaushe za a gayyaceni cin abincin amarya ne?" Yayi maganar cikin zolaya.

Adam ya ce "Idan ma da wasa ka ke yi, to ta iya girki".

"Ahha haba dai?"

"Ka bari kawai bashir, yarinyar nan caza mini kai kawai take yi, Ammi ta bata masu aiki, amma ta ce kar su kuma dafa abinci su kai mata, wai kar ayi mata asiri. Jiya fa horon yunwa ta yi mini, mun samu saɓani da safe, na fita aiki ta hana ayi girki, wai ta dafa mai da yaji ta bani, na yi magana, wai ramawa ta yi. Wallahi haƙurina na daf da ƙarewa, duk maganar da ta zo bakinta, idan zan mutu haka za ta faɗa mini"

"Adam, sai ka yi haƙuri, ka san yadda yarinyar nan take tun farko, kuma ka san ba shiri ku ke yi ba, dole ka yi haƙuri da ita, idan ka nuna mata halin muzurai, ba zaka samu abun da ka ke so ba".

Adam ya yi ajiyar zuciya ya ce "Na gaji ne, gashi familynmu, sun fara yar mata da maganganu, ka san ba ta da kunya ba za ta yi shiru ba. Ga matar da take tare da ita tana yi mana aiki, baba Uwani na san zaka santa, ita ma sun fara faɗa, ita duk abun da yake dama to ita hagu za ta yi".

Bashir ya yi dariya ya ce "A dai ƙara haƙuri, zai wuce in sha Allah".

"To, Allah ya sa, gata can dai na kaita makaranta. Jabir ya gaya wa Jamil rumaisa ce yarinyar da ta tsinci sabir, ya kuma tayar da jijiyoyin wuya a kan, dan me na ɓoye masa yana jami'in tsaro kuma yayanta. Abun da nake so da kai shi ne, ko da zance zai zo, ya san tare da kai mu ke bincike, kar ka gaya masa komai".

Bashir ya ce "In sha Allah, ba zan bayar da wata ƙofa na kowane bayani ba, sai mun yi nasara in sha Allah".

"Allah ya amince, na gode sosai " suka yi sallama Adam ya tafi.

Da daddare bayan ta dawo, tana ta murna, ta sha lilo har ta gaji, sai dai ba ta gane turancin da ake yi, dan malamansu har da turawa.

Tana ɗakinta, ta baje textbooks ɗin aka bata tana kallon hotuna, Adam ya shigo hannunsa riƙe da wayarsa, rumaisa na ɗaga kai ta kalli takawa, ta yi sauri ta rufe idonta, da hannunta, saboda daga shi sai dogon wando babu ko riga a jikinsa.

"Gaskiya ka daina shigo mini ɗaki tsirara"

"Dalla karɓi" yayi maganar a kausashe, ta ɗan zame hannunta ɗaya ta karɓi wayar, ta duba ta ga kira ne, ta saka a kunnenta.

"Ƙanwar maza, ƙanwar maza".

"Yaya Aliyu, ashe baku manta da ni ba, tun ina kuka har na daina".

"Saboda kin samu duniya ko?".

Ruma ta ce "Ba wata duniya, ina mama? Ba za ta zo ba ko?".

"Mijinki sun yi waya da mama, ta ce kar a kawo ki"

"To Meyasa, bani ita".

Mama ta karɓi wayar ta yi sallama ta ce "Ƴar auta".

"Mama shi ne ki ka ƙi zuwa, kuma ki ka ce kar a kawoni".

Mama ta ce "Ke tafi can, ba gaki nan ba abun da ya same ki ba".

"Ni dai dan Allah ki zo, ko in ta yi masa kuka, tun da kin fi son sa"

Mama ta ce "Shi wa?".

"Mijina" ta bata amsa kai tsaye.

"Sannu mara kunya, ai dama ban ce nawa ba ne naki ne".

Ruma ta ce "Mama albishirinki".

"Goro"

"Kin ga haɗaɗiyar makarantar da ya kaini, kamar a turai, kin ga liluka kuwa? Ga fankoki har da malamai turawa, baki gani ba, baki taɓa zuwa gidana ba ma, gidana haɗaɗɗe, duk ya sai kayan daɗi ya zuba mini"

Mama ta ce "Sai ki je ki same shi, ki yi masa godiya, dan na san baki yi ba"

"Taɓ, mama yaushe zaki zo to?"

"A'a ni ba zan zo gidanki ba, amma dai idan ya kawo ki shikenan". Za ta yi wa mama taɓara, mama ta kashe wayar.

Rumasai ta share hawayenta, ta bishi ɗakinsa, ta tarar yana banɗakin, ta ajiye masa wayarsa ta fice.

Kwanci tashi asarar mai rai, yau juma'a rumaisa kwana biyar da fara zuwanta makaranta, kuma wata guda cif, da ɗaura mata aure.

Takawa ya ɗaukota daga makaranta, ta ga ya canza hanya, maimakon su tafi gida.

"Ina kuma zamu je?".

"Sayar da ke, na yi tsafi da ke, kamar yadda aka ce na yi da aisha" ya bata amsa.

"To ai dai bani na faɗa ba ko?"

Tana gane gidansu zai kaita ta ce "Yeee zan ga Ammi zan ga Sabir da Anty Iman".

Da haka suka ƙarasa, cikin murna ta riga shi shiga sashin Ammi.

"Oyoyo ga ruma"

"Ammi, kin ga na fara zuwa makaranta, kin ga jakata"

Ammi ta yi murmushi, ta ce "Masha Allah, Allah Ya sanya albarka"

Iman ta ce "Congratulations Anty rumaisa".

"Thank you anty iman"

Takawa ya shigo, ya tarar da rumaisa a kusa da ammi tana nuna mata litattafanta.

Wato rumaisa ko kumyar nan ta sirka ba ta da ita.

"Ammi ina Sabir?".

Ammi ta ce "Yayi bacci"

"To bari in gama nuna miki litattafaina, sai na je na ganshi".

Ammi ta dubi Adam ta ga yanayinsa, kamar mara lafiya, ta ce "Takawarka lafiya, ya aka yi ne? Na ga yanayin ka kamar akwai damuwa"

Ya ce "Bakomai" tare da kashingiɗa.

Ta kalli rumaisa ta ce "Rumaisa, ko akwai matsala ne?".

Ruma ta gyara zamanta ta ce "Eh, dama ƙararsa zan kawo miki tun rannan, dan dai bamu zo ba ne, na ce sai na gaya miki, kin ce duk abun da yayi mini na gaya miki".

Ammi ta ce "Subhanallah, meyafaru?"

Ya kalli rumaisa yana jiran ya ji me za ta ce "Wai cewa yayi zai ƙara aure, saboda ba ni da nono!!!"

Tirƙashi!.

Ayshercool

*Chat me on what's app, to subscribe yours 08081012143, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank* Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Susbcribe my YouTube channel please 🙏

Sai da falon yayi tsit na wucin gadi, Adam bai taɓa tunanin wautar rumaisa ta tsananta har haka ba. Ji yake tamkar yayi layar zana ya ɓace daga wurin.

Ta kuma cewa "Ammi, kuma yana yawo babu riga a cikin gidan nan, kuma alhalin ni ba muharammarsa ba ce, Yaya usy ya ce yayyena ne kawai muharramaina, amma yake yawo ba riga, ina kallonsa, ko kunya ba ya ji".

Wani kallo ya yi wa rumaisa, amma ta share shi ta ce "Ai dama na rantse sai na faɗa mata, ammi ta ce duk abun da ka yi mini na rashin kyautawa na gaya mata. Hmm ni ko za a shekara nawa idan aka yi abu bana mantawa, ina riƙe da shi a zuciyata, ina sane sai yau na ce bari na gaya wa ammi".

Ammi ta yi murmushi cike da dattaku ta ce "Haba dai, wace irin kishiya ana zaman lafiya, tsokanarki yake yi kawai, wanda yake da wannan zuƙeƙiyar yarinya, ina ruwansa da wani ƙara aure. Kuma in dai saboda wannan abun ne, rai dai an fille wa fara kai, muna zaune Allah zai kawo su".

"Ammi ai hijjabi zan koma sakawa, ya daina saka mini ido, dama na ce gara in gaya miki, ba zan gayawa mama ba, saboda na fuskanci yanzu mama ta fi son sa a kaina, cewa za ta yi ƙarya nake yi, kuma ita ta ce duk wanda ya gaya mini maganar banza, wadda ta saɓa da tarbiyyar da take yi mana, in je in gaya mata. Shiyasa nake gaya mata komai, amma na san a wannan karon da zan gaya mata abun da ya yi, ba zata yadda ba".

"Da gaskiyarki kam, mama ta yi iya ƙoƙarin ta a kan tarbiyyar ku, bai kamata ta rushe ba, Allah ya cigaba da dafa muku, bar mini litattafan naki na cigaba da gani, duba ɗakina, ko Sabir ɗin ya tashi, zamu yi wani sirri da ke".

Rumaisa ta tashi ta nufi ɗakin Ammi, ka sa haɗa ido Adam ya yi da ammi, ji yake kamar ya zama guguwa ya bar wurin, saboda takaici da kunya.

"Takawa" ya ɗan ɗaga kai amma bai kalli ammi ba.

"Ka din ga sanin me zaka gaya mata, tun da ta ce ko za a shekara nawa ba ta manta abu, na ga hakan a cikin idonta, a hankali zaka nusar da ita abun da ya shafi sirrin aurenku naku ne, ta daina faɗa, na san kana haƙuri amma ka ƙara nan gaba zaka ci ribar hakan in sha Allah". Ya jinjina wa Ammi kai ya tashi ya nufi ɗakin ammi, bin bayan rumaisa.

Ammi ta ce "Dan Allah kar ka yi mata wani abun, Allah ya taimake ka, daga ni sai ku ta faɗa, Iman ta riga ta tafi amsa waya, kar ka ce zaka yi mata wani abu".

"Babu abun da zan yi mata, Sabir kawai zan gani, a nan za ta wuni, a haɗa masa kayansa, da shi zamu tafi, zan kaita gidansu gobe in Allah ya kaimu za su wuni a can, ba ta taɓa zuwa gida ba".

Ammi ta ce "Masha Allah, babu laifi"

Rumaisa tana zaune a gaban sabir, da yayi ruf da ciki a kan gado, yake ta bacci, sai shafa sumar kansa take yi tana murmushi. Da hannu ɗaya ya ɗaga rumaisa ya juyota tana fuskantar sa.

"Me na yi maka?".

"Ban sani ba, ke wace irin yarinya ce sai ka ce na'ura mai ƙwaƙwalwa, kanki gaba ɗaya baya gaya miki abun da ya dace, iya abun da aka zuba miki shi ne yake aiki a kanki, ammi fa sirikarki ce, ya dace ki gaya mata wannan maganar?".

Ta kalleshi ta ce "Meye wani sirika kuma, ni ammi babata ce, haka mama ta gaya mini, ka ci sa'a da ba komai na gaya mata ba, har da cewa nonona bai fi girman wake ba, duk wannan rufa maka asirin da na yi ba ka gode ba, ga gingimen asirin da na daɗe ina rufa maka"

Adam ya dafe kai ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ba dai aure ba, zan ƙara aure ba zan zauna da ke ba kamar namiji ba, ba zan iya ba daga nan ki je ki cigaba da faɗa"

"Ni ba zan kula ka ba baban sabir, na san haushina ka ke ji saboda na faɗi abun da ka ke yi, ni da kai idan na ce zan yi maka nasiha, ba yadda za ka yi ba, amma yanzu na san idan ammi ta yi maka faɗa zaka yadda"

Rumaisa ta zubawa sabir ido, Ammi ta shigo, ta ce "Maman sabir, Haryanzu ba ki gama ganin sa ba?".

"Wallahi kuwa ammi, bana gajiya da kallonsa ni ai".

Ammi ta zauna a gefen gado ta ce "Zo ki zauna a kusa da ni mu yi sirri ƴar auta".

Rumaisa ta tashi ta zauna a kusa da Ammi, Ammi ta ce "Kin ga dai ba kya so ya yi miki kishiya ko?" Rumaisa ta ce "Eh".

"Meyasa ba kya so?".

"Kai, ammi duk mata kowa sai na ji ta ce ba ta son kishiya, shiyasa nima na ce ba na so".

"To ki saurareni ki ji, Abun da nake nufi da duk abun da ya yi miki na rashin kyautawa ki gaya mini, ba yana nufin ki din ga faɗar sirrin aurenku ba, ya ce mini da wasa yake yi miki, kin ga kin sa ya ji babu daɗi".

Ruma ta ce "Ammi, ba dan ya ji haushi na faɗa ba, kin ga tsoro nake ji kar na yi wani abu da idan mama ta ji, ba zata ji daɗi ba, ta ce na watsar da tarbiyyar da ta yi mini".

"Ba za ta ce haka ba, ai shi mijinki ne, sannan kar ki sake ki faɗi irin wannan a gaban wani kin ji?"

"To ammi, in Allah ya yarda".

Ammi ta dafa kafaɗarta ta ce "Yauwwa yarinyar kirki, Allah ya sa kin fara makaranta a sa'a, idan aka kwana biyu mai koya miki girki zan ɗauko, har gida ta din ga koya miki ".

"Ammi na iya girki fa, ki tambayi iman ki ji, har shi papa ya san na iya"

Ammi ta ce "Waye papa kuma?"

"Baban Sabir "

Ammi ta yi murmushi, ta ce "Masha Allah, Allah Ya albarkaci aurenku"

Rumaisa ta yi gum ba ta amsa ba, dan ita auren nan ya isheta.

Rumaisa ta dage ta bi Iman kitchen, har da ammi a yin girki, sai dai ammin ya jinjinawa basira irin ta rumaisa, da ka ga yadda take gudanar da girkin zaka san, ta horu.

Wuni ta yi tare da ammi, ga iman ga sabir, jin su take tamkar wani ɓangare na rayuwarta, da ganinsu kawai ke samar mata da nishaɗi.

Da yamma, rumaisa ta silale ta fita harabar gidan, ba tare da sun sani ba, ta din ga zagaya fulawoyin gidan, da manyan bishiyu. Wani zomo ta gani, fari tas da shi, yana tsalle-tsallen sa, ga sauran tsuntsye da suke kaiwa suna komowa. Da sauri ta bi zomon, tana son ta kama shi, sai dai ta ga ta ɓullo wani wuri.

Yana zaune a kan fararen kujeru, gabansa da litatafai, da system, ya tattara nutsuwarsa sosai a kan abun da yake yi.

Bayansa ta gano ta ce "Papa" a hankali ya waiwayo ya kalleta, ta ɗan tsura masa ido, sai kuma ta ce "Laa ashe ba papa ba ne kai ne, na gane ka, da ka taɓa sawa na shigo gidan nan" ta yi maganar tana ƙarasawa in da yake.

Ya ce "Wow, ashe zamu sake haɗuwa, sannunki, ya ki ke?"

"Lafiya ƙalau" ta ƙarasa maganar tana zama a kujerar da ke facing ɗin sa.

"Yau ya aka yi aka bari ki ka shigo, har ki ka zo nan?"

Da ɗan mamaki ta ce "Wa zai hanani shigowa, to shi ya kawoni"

Mahmud ya ce "Shi wa?"

"Baban Sabir, ba ka san yanzu mijina ne ba?"

Ya ɗan yi turus, sai yanzu ya gane zancen da Mummy suke yi ita da su Samha ɗazu, amma bai gane ba, kasancewar tun da ya dawo sai yau ma ya fito.

"Da gaske ke adam ya aura?".

Rumaisa ta ce "Hmmm, ya aka yi baka sani ba? Ba a gidan nan kake ba, ba ka zo bikinmu ba kenan?".

"Ina ƙasar waje ai, can makaranta, labarin bikin kawai na ji".

Cikin mamaki rumaisa ta ce "To ta yaya kuna gida ɗaya, amma ba ka sani ba, wai ku ba ƴan uwa ba ne?".

"Eh, kowa babarsa daban".

"To, ku ƴaƴan kishiyoyi ne?".

Yayi dariya, tambayarta ta yi yawa amma ya ce "Eh".

"Taɓ to ni wallahi ba za ayi mini kishiya ba, amma to dai meyasa ba ka zuwa wurin su, baka san yayi aure ba?".

"Ni ma ba ya zuwa wurinmu"

Ruma ta ce "Ai papa sai fatan Allah ya shirya shi".

"Ke ma yana yi miki halin na sa kenan, na rashin kirki?"

"Hmm, ai ba dan Sabir ba ko, ba zan aure shi ba, amma dai ya sakani a makaranta mai kyau na ji daɗi".

Mahmud ya tattara nutsuwarsa a kan ta ya ce "Da gaske dai, ke ki ka dawo da jaririn nan?"

"Wai meyasa ƴan dagin nan naku, suka damu da lamarin nan ne? Wato an rainani ko? To anty aisha da kanta ta bar mini jaririn nan, kuma har da zobunanta da ɗankwalinta, ta bani, ni fa bana damuwa da kowa sai ya yadda da ni a duniyar nan, malaminmu ya ce idan Allah ya yarda da kai, ka huta, shiyasa ni ban damu da kome za a ce a kaina ba".

Mahmud ya yi dariya ya ce "Wow, i like your confidence "

"Wai kai ya sunaka ne?".

"Mahmud" ya bata amsa, ɗan turus ta yi tana kallon sa, "Dan Allah da gaske?"

Ya ce "Eh"

Ta ce "Innalillahi, sunan babana, sunan ɗa na"

ya ce "Shikenan na yi ƴa, na zama daddynki"

Ta yi dariya ta ce "yauwwa to ka taɓa zuwa ka ga ɗa na? Ranar nan na ce ka je wurin ammi ka ganshi".

"Zan je wataran".

Rumaisa ta ce "A'a, yanzu dai mu je in ga mamanku, ita ce ban taɓa gani ba, kai ma sai mu je ka ga ɗa na, mai sunan ka".

Mahmud ya ce "mijinki ya huta kallon Tv, ke kaɗai kin isa ba shi dariya".

Ta ce "Taɓ, sai ka ce wata cartoon, mu je ka nuna mini ita" ya tashi tsaye, yayi gaba, ya jagoranci rumaisa har tsakiyar falon Mummy.

Ya ce "Mummy, ga amaryarku fa ta ce na kawota ta gaida babata"

Gaba ɗaya suka juya suna kallon rumaisa da ke bin su da kallo.

Samha ta fara ganewa a cikin su, ta kalli Fauziyya da ruƙayya, sai dai suna haɗa ido da Mummy, jikinta ya yi sanyi, gaban Mummy kuma ya yi mummunar faɗuwa.

Mummy ta ce "Wace wannan?"

Samha ta yi tsaki ta ce "Matar Adam ce, saboda asara, kalli abun da ya kwaso saboda ba ya gudun abun kunya".

Mahmud ya kalli Samha ya ce "Ba ruwanki, ba wurinki na kawota ba" ya kalli rumaisa ya ce "Daughter, ga mamana nan"

"To ya na ga ba ka kama da ita, kana kama da ammi?" Ji yayi wani irin gumi ya tsatstsafo masa ta kafar gashin jikinsa.

Mummy cikin jarumta da iya duniyanci ta ce "Ikon Allah, da ba a kawo mini ita mun gaisa ba, kai ka kawo mini ita, takawan ne ya ce ka kawo ta mu gaisa?"

Mahmoud ya ce "A'a, cewa ta yi zata zo ta gaida babata".

Fauziyya ta ce "Tirƙashi, ashe da muka ganta a wurin dinner ta fi cika ido, ni Wallahi ban gane ta ba ma"

Samha cikin ƙuluwa ta ce "Mummy wai meyasa ki ke wani sakar mata fuska, meye alaƙarta da ke, tun da ba ɗanki take aure ba, kuma ba ayi niyyar kawota ta gaishe ki ba?"

A fusace rumaisa ta ce "Baiwar Allah wai me na yi miki ne? Kullum ki ka ganni sai kin zageni, ba ruwanki da ni, ni ba wurinki na zo ba".

Mahmud ya ce "Samha ba ruwanki da ita please, ki ja girmanki, daughter ga mamana".

Rumaisa ta kalli mummy, ta risuna kamar yadda ta ga ana yi ta ce "Barka da wannan lokaci "

Mummy ta ce "Barkanmu dai, kuna lafiya?".

"Lafiya ƙalau"

"Ya mijin naki, ya Sabir? Ko da yake fushi nake yi da mijinki, ba ya zuwa in da nake, kuma ba ya kawo mini ɗan naki, Allah sarki fulani, ashe tare aka yi garkuwa da ku?".

Rumaisa ta yi shiru, ba ta ce komai ba.

Mummy ta ce "Ruƙayya, ki saka a kawo mata abinci".

"A'a na ƙoshi, yanzu muka gama cin abinci da ammi".

Cikin ƙarfin hali Mummy ke magana, domin wani irin bugu ƙirjinta yake yi, har hakan na neman bayyana a fuskarta.

"Ni ma ai babar takawa ce, ki zauna mu yi hira mana, da takawa, da aisha, duk ƴaƴanmu ne, haka muka ji rasuwar ta, mun shiga tashin hankali da ruɗani, babban abun takaicin yadda ta haihu a hannun 'yan bindiga, abun bai yi mana daɗi ba".

Maimaita rumaisa ta amsa mata, sai ta tashi ta ce wa Mahmud "Daddy mu tafi mu je ka cika mini naka alƙawarin" kallon rumaisa suke yi, da tunanin anya ma ba ta da taɓin hankali kuwa? Abun da ake tambayarta daban, abun da take yi daban.

Yayi murmushi ya ce "To mu tafi, tun da kin ga mamana, kin gaisheta".

Rumaisa ta ce "Eh, Mummy sai anjima " "To amarya, sai mun zo gidan naki kuma"

Allah ya kawo ku.

Mahmud ya nuna mata Fauziyya da ruƙayya ya ce "Wannan ƙannena, ga Fauziyya ga ruƙaiyya"

Kan ya ce wani abu a kan Samha ta ce "Ita kuma wannan na santa, mai zagina ta na ce mini ƴar aba, na santa a gidan baba farin rawani, mai girma turaki, baban anty aisha, shikaɗai ya yi mini mutunci a gidansu".

Yayi murmushi ya ce "To shikenan mu je" suka fita. Samha ta tashi zaune ta ce "Na shiga uku, na rasa me ma zan yi? Kaina ya gama kullewa".

"Jikina ya na bani akwai wani abu ɓoyayye a game da yarinyar nan, dole zan ganta a karo na biyu, kuma ya zama dole baba uwani ta sanya mini ido sosai a kan su"

Fauziyya ta ce "Ji munafuka kai, wai Mahmud ba ya kama da ke, kin ga idonta a tsaitsaye"

Mummy ta ce "Na gani" nan suka cigaba da tattaunawa a kan abun da yakamata su yi a kan rumaisa.

Ammi kuwa sai neman rumaisa suke yi, basu ma san in da ta yi ba, ammi har hankalinta ya ɗan fara ɗagawa.

Rumaisa kuwa da suka fito harabar gidan, sai surutu take yi wa Mahmud, kamar dama can sun saba, ya fi takawa sauƙin kai da sakin fuska, a wajejen harabar sashin ammi ya tsaya ya ce "To shikenan, ki gaishe mini da takwarana". Ta kalleshi ta ce "Haka muka yi da kai, ba na gaida mamanka ba, ni ma ka zo mu je ka gaida tawa"

Ya ɗan yi jimm yana kallon rumaisa, "Dan Allah haba daddy, ni fa a gidanmu ban san babana ba, sai yayyena su bakwai, komai nake so suna yi mini, dan Allah mu je ka ga Sabir".

"Ki shiga ki ɗauko shi, ki kawo shi na ganshi".

Ta noƙe kafaɗa, kawai ya tsinci kansa da bin rumaisa.

Ba Ammi ba, har iman sai da ta razana, ganin Mahmud a filin falonta, shi kansa tsayawa ya yi yana bin su da kallo, rabonsa da falon nan, kusan shekara da wani abu, da Ammi ta neme shi, ta nemi alfarmasa kai tsaye ya ce ba zai yi ba.

Ammi ta ƙure shi da ido, kamar yau ta fara ganinsa.

Kallo ɗaya ya yi wa ammin, ya sunkuyar da kansa, ƙasan zuciyarsa yana tuna abun da ya yi mata na ƙarshe da ya kasa mantawa.

"Ashe ka dawo, ya makarantar?"

Ba tare da ya ɗago kai ba ya ce "Lafiya lau"

Ruma ta ce "Ka zauna mana" ta nufi in da Sabir yake wasa da kayan wasansa, yana ta rarrafe yana ɓarna, ta ɗaukko shi ta kawo masa shi.

Ya karɓi sabir, ya zauna da shi a jikinsa, ta kalli sabir ta ce "Waye wannan?"

Sabir ya ƙura masa ido, Mahmud wani murmushi ya saki, ya shafa kan Sabir, wata irin ƙaunar yaron ta shiga ransa, da yake jin tamkar daga jikinsa ya fito. Har aka yi dambarwar nan aka gama, bai taɓa ganin Sabir ba.

Cikin murmushi ya ce "Na yi kama da babanka ko, nima babanka ne"

Su Nusaiba kamar tv, haka suke kallon Mahmud da rumaisa.

Ruma ta ce "Ba papa ba ne, uncle ne wannan"

Mahmud ya ce "A'a Daddy dai" ya miƙe da Sabir a hannunsa ya nufi hanyar waje yana faɗin "Allah ya bani ɗa ba mata"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull