Kenza eBookz

Kanwar maza 3 and 4 complete - Chapter 37

Kanwar maza 3 and 4 complete - Chapter 37

Kanwar maza 3 and 4 complete Chapter 37: Kanwar maza 3 and 4 complete Chapter 37. Sai dai da ta tafi ɗakin, ta kasa manta rungumar da yayi mata, haka ta…

4,498 words

Sai dai da ta tafi ɗakin, ta kasa manta rungumar da yayi mata, haka ta shirya ta kwanta bacci, tana sake ganinsu a tare a cikin idonta, yana magana yana yi mata dariya. Rungume pillown tayi, ta furta "papa a hankali"

Washegari da wuri ta tashi ta hau aikace-aikace, ta gyara ko ina duk da babu datti. Ta shiga kitchen ta haɗa abincin karin kumallo, ta leƙa ɗakin Adam.

Ya lulluɓe jikinsa da bargo, saura fuskarsa kawai a ya bari a waje, baccinsa yake yi hankali a kwance, kai da gani ka san a gajiye yake.

Ta kalli agogon ɗakin, tara da rabi na safe, a hankali ta ce 'Papa baka jin yunwa ne?'

Sai kuma ta tuna lecture malamarsu da ta laila, wai yadda ake tashin miji daga bacci.

Ta rife bakinta da hannunta ta ce "Ni, haka kurum in je in wani kama shafa shi, ina cewa ya tashi, kamar wani mage, ko ɗan jariri, ai gara in daki ƙofa da ƙarfi irin yadda mama take yi wataran a gida, idan haka ne abun, meyass a gida ba a haka ake tashin su Yaya usy ba? Kai anty laila bata da kunya, zaman turai duk ya canza ta'.

Ta gama soki burutsunta, ta koma kitchen tayi wanke-wanke.

Daga nan ta tafi ɗakinta, yin wanka.

Sai dai ko da ta fito daga wankan, bisa mamakinta adam har ya tashi, dan ya ma biyota ɗakin.

"Wai daga zuwana nayi wanke -wanke har ka tashi?" Tayi maganar a ɗan tsorace tana rufe jikinta.

Maimakon ya amsa, kawai ya hau dariya, ta tsaya cak ta ce "Menene?".

Purple ɗin brezia da ta bari a kan gado, ta shiga banɗaki, ya ɗaga mata ya ce "Meye wannan?"

Kame-kame ta fara tana son faɗar abun da zata kare kanta da shi.

Ya ce "Inyeee mutuniyar, ai kamata yayi a nuna mini, ni dama tun da nayu hugging ɗinki jiya, i feel it but i thought na scam you wanta scam me, ashe na gaske ne, come let me see inyeee".

Shan kunu tayi ta ce "Papa bana so"

"Meye ba kya so kuma? Ganin kawai"

Ƙarasowa tayi zata karɓi breziar, amma ya riƙeta yana dariya, ta saka hannu ta riƙe towel ɗin ta gam, tana ihu.

"Ni wallahi da baka nan, nafi sakewa"

"Abun har da sharri, kamar ba jiya ki ka gama kuka ba, saboda kin ganni. Anyway, shirya ki zo mu yi breakfast, zamu yi magana"

Sai da ya bar ɗakin sannan hankalinta ya kwanta, ta shirya, ta fito tana wani haɗe rai.

Shi kuma ya ƙureta da ido, har ta zauna.

Taƙi kula shi, tayi serving ɗin sa, ta ja nata ta fara ci, duk yadda ya so ya maze kasawa yayi, dan yana jin daɗin tsokanar rumaisa yaga ta haɗe rai.

"Papa dan Allah ka daina kallona kana dariya, Allah zan tashi".

"Allah da iko yake, abun ne da mamaki, six months back, a ƙwailarki na tafi na barki, amma in just six months ace lamari ya kankama haka, kuma kin ƙi yarda na tabattar kar in je acuci ake yi mini. Abunki ras da ke, ai ni yanzu kuma na daina takara da ke, na yarda yafi nawa nesa ba kusa ba, wane ni ma? Ai ni yanzu babu suaran jayayya, zaki iya rainon baby yanzu sosai, kai congratulations mimi, kamata yayi fa mu yi party, tare da celebration, mimi is no more ƙwaila, she's now a big girl, she can bear a baby, she even wore brezia size nawa ne ma ki ke sakawa, mu je mu sayo dozens of it" ƙarshen ƙuluwa rumaisa ta ƙule, ta jefa masa guntun ƙashin da yake hannunta, ta tashi za ta tafi. Ba dan ya iya shanye dariyarsa ba, ya riƙe ta yana cigaba da ƙyaƙyatawa.

Duk da tsiyatakun da yake tayi mata, ta kasa fushi da zuciya, watannin nan da yayi, ba ƙaramin missing ɗin sa tayi ba, amma dawowarsa ya sakata a gaba da tsokana kamar tayi kuka.

Ta tafi kitchen yin wanke-wanke ya bita, ba abun da yake tayata, ya sakata a gaba da tsokana. Ruma ta kalleshi, kamar ba shi ne idan ya kamile ya tsuke fuska, ko fara'ar kirki ba ya yi ba, yayi ta muzurai, mussman idan yana cikin shigarsa ta sarauta, amma yadda ya sakata a gaba sai ka ce yaya usy saboda tsokana.

Ya ƙaraci dariyarsa ya koma falo, ya cigaba da kallo, lokacin sallar azahar yayi, ya tashi ya fita masallaci.

Sai dai da ya dawo, har ta kammala girki, ta yi salla ta canza kaya, amma ta kima uban hijjabi, tana so ta ganshi sosai, amma tsiyar da yake mata duk ya takurata.

Ya ɗaga kai ya kalleta ya ce "Budurwar, meye haka kuma?".

"A ina?".

"Meye na wani saka hijjabi ana zaune ƙalau, wannan abu na farinciki da ya same mu, gaskiya ban yadda ba".

"Allah papa zan tafi ɗaki na daina fitowa"

Ya ce "Sorry, ke kin san yadda na yi kewarku kuwa, tsokanar da na daɗe ban yi miki ba nake fanshewa. Ya ƙarasa wurinta ya cire hijjabin, tana riƙewa amma ya cire shi.

Kasancewar ba a dining za su ci ba, suka zauna a ƙasan carfet.

Ta janyo kwanukan abinci, da plate biyu, ya ce mata "an daina raba plate, a ɗaya zamu ci" ta tuna anty laila ta ce mata cin abinci kwano ɗaya da miji, yana ƙara soyayya, amma ita ba wannan ya dameta ba, sai tambayarta da tayi, to ba zai yi mini kishiya ba, laila ta ce sai kin kula da abubuwan da na koya miki tukuna.

Ta zuba abinci ta ajiye masa spoon, ya kalleta ya ce "Ke ni fa tun farko a baki ake bani abinci, ba zaki ajiye mini cokali ki maza ba".

"Ni zan baka abinci a bakin?".

"Eh mana"

Ta ce "Taɓ papa, ko jajjage baka yi mini ba da ina girki, ko sannu sai ma tsokanata da ka yi tayi, na gama abincin kuma sai na baka a baki, in bawa sabir abinci a baki, in bawa babansa saboda jin daɗi".

Yayi dariya ya ce "To ki bari in baki, ai ni a wurina da ke da sabir, duk ɗaya, baku da wani banbanci dan abun da yake na shiririta kema yi ki ke" kan tayi magana ya ɗorata a cinyarsa, ya ɗebo abinci a cokali ya kai bakinta.

Rufe fuska tayi ta ce "Ayi haka? Kunya nake ji fa"

Sauke hannunta yayi, ya tura mata cokalin a baki, tun tana noƙewa ta saki jiki tana karɓa, ta ce "Da na san haka bawa mutum abinci yake a baki da daɗi, ai da na daina ci da kaina, idan na dafa sai ka bani a baki".

"Ni zaki saka aiki, yanzu ki ka gama cewa saboda jin daɗi zaki bani abinci a baki, amma yanzu kina gaya mini, in din ga baki abinci a baki. Mara kunya kawai baby mimi an zama lady mimi"

"Wallahi idan ka ce babyn nan kunya ka ke bani, ga abinci a baki ga baby, idan aka ga na koma yin rarrafe kai ne ka ja"

Dariya Adam yake yi, rumaisa ba za ta taɓa girma tayi hankali ba.

"Mimi, kin shiga kin fita kin hana auren jabir da iman, ki ka haɗa da yayanki, kin saka jabir gaba da ni, Jamil ma har na je na dawo bai yi mini magana ba, gaba ɗaya fushi suke yi da ni, duk saboda ke mimi"

"A'a nifa ban hana aurensu ba, kuma can suka ƙulla soyayyar su da mai sunan baba, ban sani ba ina gefe ni ƙarfafawa kawai nayi. Kuma papa kawai fa ban gaya maka bane ba, kar na zama munafuka kai baka san me jabir yayi wa ammi ba, wai saboda ba yi auren sa da iman ba, ka ja maganganun da ya din ga gaya mata? Wallahi sai da Mahmoud ya mare shi".

"Wane Mahmud ɗin?"

"Daddy" ta bashi amsa. Yayi shiru yana mamaki, ya san rumaisa ba za ta yi masa ƙarya ba, yanzu har jabir zai iya kallon ammi ya ci mutuncin ta, matar da duk da abubuwan da mahaifiyar sa take yi mata, bai hana ta ɗauke shi tamkar ɗa ba.

"Papa ni fa wasu lokutan ba haka kawai nake tsanar mutum ba, da jabir sonka yake tsakani da Allah, kome ammi za ta yi masa, ba zai wulaƙanta ta ba. Shi kuma jamil sake bina yayi, wai sai na gaya masa yadda aka yi anty aisha ta ɓata, da kuma in gaya masa abun da na sani a kan ta, na ce masa ban san komai ba, sai filin da gwamanti ta karɓa a hannun turaki, ake bashi percentage ya sanya anty aisha a matsayin magajiyarsa, shi ne hankalinsa ya kuma tashi, ya ce kaine ka gaya mini"

Adam ya saka hannu ya juyo da fuskar rumaisa tana fuskantar sa, ya ce "Rumaisa, meyasa ba zaki daina yi mini yawo da hankali ba? Yanzu magana ake ta shekara guda da watanni, da ɓatan aisha, ba zaki tausaya mini haka ba, ki daina yi mini ɓoye-ɓoye? Kin bani zane ya ɗaga mini hankali, kuma ban gane komai a ciki ba Please rumaisa" Yayi maganar jikinsa a sanyaye.

"Papa ba laifina bane, laifinka ne haryanzu, ka wuce duk wasu matakai da yakamata, kuma ina iya ƙoƙarina na tallafa maka, ɗaya ya rage haryanzu, nima ba son raina bane in ta wahalar da mijina ba, baban ɗa na"

"Wani mataki ne mimi?".

"Sauran ma ka tsallake su, ba tare da ka sani ba, wannan ma dan kan ka nake son ka yi surrender ka tsallake shi. Kullum ina yi maka Addu'a, duk wanda na yi wa abu yaji daɗi, sai in ce ya saka ka a addu'a, komai zai zo ƙarshe fa"

Jiki a sanyaye ya ce "Shikenan mimi, Allah ya yi mana jagora"

Ta ɗebo abincin ta kai bakinsa, amma ya girgiza kai ya ce "I loss my appetite, na ƙoshi".

"Dan Allah ka ci papa, zan yi kuka, kar ka saka na karaya na rigaka miƙa wuya, ba haka muka yi da anty aisha ba"

Cikin mamaki ya ce "You mean you set a deal with her a kaina?" Ta jinjina masa kai alamar eh.

"What was it?".

"This is not the right time to voice it out, i have to finish it first, but am sorry papa"

Idonsa fal hawaye ya ce "Shikenan miki, baki yi mini laifi ba"

Tuni hawaye ya gangaro mata, ta shafa fuskarsa ta ce "Dan Allah papa kar ka yi kuka".

"No mimi allow me, it really hurts me, ina jami'in tsaro na kasa bawa iyalina kulawa, har ta rasa ranta mutuwar wulaƙanci, ta haihu a dokar daji, what a mess".

Ruma da tuni ta fara sheshsheƙa ta ce "Daga baya na gane is not your fault, ka daina dan Allah".

Ya kwantar da rumaisa a ƙirjinsa, yana shafa bayanta da sigar rarrashi, amma hakan ya bashi damar, zubar da nasa hawayen silently.

A hankali ya ce "Ashe turanci ya fara zama Inyeee".

Ya zira hannu ya kamo hannun brziar ya ce "ina zamu je celebration ne? A buga cards, da congratulations on your newly developed... Bai ƙarasa ba ta gantsara masa cizo a hannunsa ta tashi.

Dariya yayi, atleast ta rage damuwar da ta shiga yanzu.

*** Yasir kuwa kai da fata ya dage, ya ɗauki lambar iman a wayar mama, kasancewar mama ta kira iman da kanta, tana mata ƙorafin, ta daina zuwa gidan gaba ɗaya, wanda ba iman ba ƙaramar kunya ta ji ba.

Yayi amfani da damar, ya ɗauki lambar, ya yi wa iman magana ta what's app, bayan sun gaisa yayi mata bayanin shi ne, ya tura mata akwatuna ya ce ta zaɓi wadda take so.

Iman ta ce "Yasir duk abun da yaya umar ya bani ina so, ba zan zaɓi komai ba dan Allah ku ce masa kar ya wahalar da kansa yayi mini iya abun da Allah ya hore masa".

Yasir ya ce "Amma dai bani ni ne zan gaya masa hakan ba ko? Ai wannan aikin sai ke ko hajiya mama, ni a suwa, dan Allah ki zaɓa amma kar ki gaya masa"

Iman ba ƙaramin burgeta suke yi ba, suna matuƙar son junansu, fiye da tunani.

Ƙin zaɓa tayi, ta ce kowacce aka yi ta gode.

Da yamma mai sunan baba ya dawo daga kasuwa, ana ta cigaba da gini, yana tara kayan lefe, kowa ya fita ya dawo, sai ya kawo wani abun na kayan lefe, kuma ƴan uwa basu gaza ba, da cigaba da kawowa mama gudunmuwa.

Turus yayi ganin wasu kyawawan akwatuna, guda shida da kid, haɗaɗɗu masu kyau.

Mai sunan baba bai tanka ba, sai da mama ta ce "Babana, mutuminka fa ya cika alƙawari ga akwatunanka nan".

"Meyasa Yasir ba ya jin magana ne? B jari yake tarawa ba, dan me zai kwashe kuɗinsa ya yi wannan hidimar, sonake na ga me zan samu a cika masa, amma ya kwashe kuɗinsa yayi wannan aiki, sai kuma da nace masa ya bari, yanzu kan ya mayar da kuɗin fa"

Yasir da yake tsakar gida, bai ji daɗin abun da mai sunan baba yayi ba, sai dai ko menene shi ya san yaya umar ha cancanci fiye da haka.

Mama ta yi ta yi wa mai sunan baba faɗa a kan bai kyauta ba.

Ko da ya fita tsakar gida, ya kalli fuskar yasir, fuskarsa ta nuna bai ji daɗin abun da mai sunan baba ya yi masa ba.

Har dare Yasir sabgoginsa kawai yake yi, ko ɗan shishshigin nan da suke yi wa mai sunan baba, yau bai yi masa ba. Sai dai da ya shiga ya fita, sai mama tayi ta saka masa albarka tana kwarara masa addu'a.

Har ƙarfe goma na dare, yasir bai shiga gida ba, mai sunan baba ya ɗau babur ya biya shagon yasir, ya tarar da shi yana ta aikin wayoyin mutane da system, shi da yaransa.

Horn ɗin da mai sunan baba yayi ne ya dawo da shi hayyacinsa, ya ajiye wayar hannunsa ya fito.

Mai sunan baba ya bashi galan ɗin man fetur, ya ce "Gashi nan ka zuba a injinka" Yasir ya karɓa ya ce "To na gode sosai"

"Ka rufe shagon nan mu tafi gida, dare yayi goma tayi"

Ya amsa masa da "To, bari na sallami yaran" ya wuce cikin shagon ya sallame su.

Shagon da Yasir yake harkar wayoyinsa da system, har ma da POs mai sunan baba ne ya kama masa shagon, ya saya masa system. Ya ce hauzaifa kuma ya iya ɗinki, shegiyar shirirtar sa ta hana mai sunan baba bashi jari.

Yasir ya rufe shagon, ya hau babur suka tafi gida, a ƙofar gida mai sunan baba ya ce "Yasir".

"Na'am"

"Ban yi maka faɗa a kan abun da kayi mini dan na ɓata maka rai ba? Kaga jari kake tarawa, bai kamata ace na mayar da kai baya ba".

"To waye ya bani jarin?".

"Duk da haka bai kamata dan na baka na dawo na cinye ba, anyway ka daina fushin na gode sosai Allah ya ƙara buɗi, ya sanya ku fi haka, ya sanya maka albarka a nemanka" yayi maganar yana musabaha da hannun yasir.

Yasir yayi murmushi ya ce "Muke da godiya mai sunan baba"

"Nima yakamata na gode, na san ka kashe kuɗi sosai, Allah ya mayar maka da ninkin abun da ka kashe"

Ya amsa da "Amin Yaya"

Suka shiga gida tare.

*** Kwanan Adam huɗu da dawowa, rumaisa ta tarar da shi a ɗakinsa, da travelling bag.

"Ya haka, me nake gani, wannan jakar fa? Ga breakfast can".

Ya ce "Kin tashi kenan?"

"Eh mana ina zaka?"

"Nemana ake a abuja, zan je na yi booking Flight"

"Daga dawowar taka za ka kuma tafiya?"

Takawa ya ce "Kiran gaggawa ne, suna buƙata ta, ba zan fi sati ɗaya ba"

Haushi ne ya kama rumaisa, kawai ta fice daga ɗakin, ta koma nata.

Bin bayanta yayi yana kiran sunanta, ya tarar da ita a falo, ta cika tayi fam.

Ya zauna kusa da ita ya ce "Wai mimi meyasa ki ke da matsala ne, harkar aiki ne, idan ban je ba ya zan din ga samo mana kuɗi, na biya miki kuɗin makaranta, na saya mana abubuwa"

"To daga dawowarka sai ka kuma tafiya, kullum baka nan ai shikenan"

"To yanzu ya ki ke so ayi?"

"Kawai ka fasa"

"Mimi zuwana yana da muhimmanci, ga kuma karatuna na kammala, akwai aikace-aikace a gabana sosai da sosai, kiyi haƙuri 5days kawai in sha Allah zan dawo".

"Ni sai dai ka tafi da ni, idan ba haka ba zan yadda ba".

"To shikenan, zan saka ayi mana booking Flight shikenan"

Ta waro ido ta ce "Dan Allah jirgi zan hau?"

"Ƴar ƙauye zata hau jirgi"

Ruma har da tsalle ta ce "Wayyo daɗi, bani waya na kira yaya usy, na gaya masa zan riga shi hawa jirgi".

Yayi murmushi ya ce "Sai mun sauka tukuna, Ki ɗaukko mana akwatinki guda ɗaya, ki haɗa mana kayanmu"

Tashi tayi da sauri ta tafi tana murna yau zata hau jirgin sama.

Ta waya ta sanar da mama zata raka takawa abuja, amma ba zasu fi kwana biyar ba zasu dawo. Aliyu ya ce "Yarinyar nan tana sararawa, taɓararta kawai take yi son ranta".

Rumaisa bakinta yaƙi rufuwa, da ta ganta a cikin jirgi, ta ce "Papa, yanzu idan nayi tsalle a jirgin nan, ya zai yi ƙasa zai yi".

"A'a sai dai idan yanzu zaki gwada tsallen".

Ta ce "Haba dai su rainani"

"Gaskiya dai, babbar yarinya kamar wannan mai abun arziki ai sai a rainaki"

"Zaka fara ko?"

Ya ce "Ban fara ba tukuna".

Ko da suka sauka taxi suka hau, suka nufi hotel ɗin da zasu sauka.

"Papa, to ina gidan shugaban ƙasa yake a nan?"

"Me zaki yi wa shugaban ƙasar?"

Rumaisa ta gyara zamanta ta ce "Zan ce masa dan Allah ya saka a daina sace mutane, wallahi wahala ake sha sosai"

Murmushi kawai yayi bai ce mata komai ba.

Hotel ɗin yayi wa rumaisa kyau, sai dai nanata masa take yi, ko sun koma gida kar su gayawa kowa hotel suka zo a abuja, kar ayi musu kallon mutanen kawai.

Da suka shiga bedroom ta ga ɗaki ɗaya tal, da toilet.

Ta ce "To ina banɗaki, da kuma kitchen da nawa ɗakin?"

"Babu kitchen, a nan zamu din ga kwana tare"

"Kai, ni da kai a ɗaki ɗaya, kuma ba kitchen to me zamu din ga ci?".

"Saya zamu din ga yi"

"To waye zai din ga kwana a kan gadon?"

"Ke dai kin san ba zan biya kuɗin ɗaki in kwana a ƙasa ba ko? Sai ki nemawa kanki mafita"

Ya ajiye akwatin, ya nemi wuri ya zauna, ya ɗauki wayarsa yana kiraye-kirayen wayarsa, ya ce a kawo masa mota.

Da daddare ya ɗauki ruma suka fita yawo, hakan ba ƙaramin daɗi ya yi wa ruma ba, duk da dare ne fitar tayi mata daɗi sosai.

Ta ɗauki wayarsa ta kira Huzaifa, tana ta bashi labarin yadda jirgi yake, da abubuwan da ya sai mata.

Usman ya karɓi wayar ya ce "Ke wayar nan a handsfree take?"

Ta ce "A'a"

"To ki ba ya fita dake yawo ba, har kin hau jirgi kina yashe baki, ga uwar tsaraba da ya yi miki da ya dawo, idan. Ki ka kuma kawo mini ƙarar kin yi masa wani shirmen, wallahi kina zaune zai auri wata ya din ga wannan yawon da ita, gara a din ga gaya miki gaskiya".

Shiru tayi daga baya ta ce sai anjima, ta kashe wayar tana tura baki.

Takawa bai san me suke cewa ba, kuma bai damu da ya tambaya ba.

Suka koma masaukinsu, sai nanatawa take ita fa tunda ta baro gida, ta saba da kwanan kan gado, dan haka ba zata kwana gado ɗaya da shi ba, kuma ba zata kwana a ƙasa ba.

Yayi mata shiru, ya ɗaukko system yana daddanawa.

Ta shiga banɗaki ta fito, ta zauna a gefen gadon tana kallo abun da yake rubutawa a system ɗin.

Ya tashi ya shiga banɗaki, hakan ya bata damar tashi ta buɗe akwati, ta fara canza kaya.

Ayshercool. 08081012143 **SHIN YAR UWA KIN SAN ILLAR DAKE TARE DA INFECTION KUWA?, TO BARI KI JI KAƊAN DAGA CIKIN ILLAR DA INFECTION YAKE DA SHI? KIN SAN CEWA INFECTION YANA HANA HAIHUWA?, YANA HANA MA'AURATA JINDADIN MU'AMALA, YA NA SAKA WARIN GABA KOWANE IRIN TURARE KI KA YI AMFANI KO GYARA KI KA YI, BA ZAI HANA WANNAN WARIN FITA DAGA JIKIN KI BA FITAR FARIN RUWA, TARE DA ƘURAJE. ƘAIƘAYIN GABA, TUSAR GABA, DUK SUNA DAGA CIKIN ILLAR DA INFECTION YAKE WA LAFIYARKI INA MASU FAMA DA ULCER, ASTHMA, SICKLA, INA MATAR DAKE FAMA DA MATSALAR FIBROID, MATSALAR RASHIN HAIHUWA KO BUSHEWAR JIKI DA FATA, KU GARZAYO KU GWADA MAGUNGUNANMU MA GHT SUPPLEMENT, KU GANI DA IKON ALLAH DA IZININ ALLAH, MAI BUƘATAR ƘARIN BAYANI YA NEMI WAMN 0703 527 5119* Ko ku danna wannan link ɗin, domin kasancewa da mu, ku ji yadda

https://chat.whatsapp.com/COM8NE7rDs8HAG0Oqfr9wm

*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?* *TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI* *SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*

*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*

👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*

*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*

*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*

*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*

*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*

*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*

*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*

*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*

*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*

*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*

*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*

*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton* *14. Supplement na whitening/glowing skin*

*15. Supplement for Acne, dark spots remover*

*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*

*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*

Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Susbcribe my YouTube channel please 🙏

*TALLA! TALLA!! TALLA!!! *ƊANƊANO DAGA LITTAFIN NAZEEFA SABO NASHE, MAI SUNA ƘUDURAR ALLAH*

Ta Yaya zai zama jinina alhali ni na san bayan matana ban tab'a kusantar wata mace ba?" Ya furta kai tsaye yana kallon likitan da sakamakon gwajin yake hannunsa. Likitan yana jinjina kai ya sake furta "Tabbas Jaheed jininka don gwajin k'wayar halittarku da komai ya tabbatar kai ne mahaifinsa kafin a kai ga haka ma ko Kamanninku da suka zamo kwabo da kwabo sun tabbatar da Hakan koda Ba'a yi gwajin ba."

Shiru na tsawon lokaci d'akin ya d'auka kowa da irin tunanin da yake a ransa ya kasa yarjewa zuciyarsa shine Mahaifin Jaheed duk da k'wararan shaidu. Abinda ya sani ko da wasa bayan matansa na aure na Sunna bai tab'a rik'ewa wata mace hannu ba, idan kuwa ya tabbata Jaheed d'ansa ne ta yaya ya samar da cikin nasa a jikin wacce aka kira mahaifiyarsa da ko a mafarki bai tab'a ganin mai kama da ita ba TABBAS AKWAI LAUJE CIKIN NAD'i. Mahaifiyar Jaheed ma Zata iya zama abar tuhuma da zargi. Kai tsaye zai iya cewa hakan zai iya zama K'UDIRAR ALLAH….

(*Ina ma'abota karance-karancen litatafan hausa, na san kun santa, Nazeefa sabo nashe, tsohuwar marubuciya, da ta saba nishaɗantar da ku, da ɗaɗan litatafan hausa masu ma'ana da ilimantarwa, ya kuke tunanin wannan turka-turka, DNA ɗin sa ya kasance daidai da na yaron da bai taɓa ganin mahaifiyarsa ba, haka zalika a iya saninsa tun daga ƙuruciya har girmansa, bai taɓa aikata zina ba? Ku kasance da Nazeefa sabo nashe, dan jin yadda zata warware wannan turka-turka a cikin littafin ƙudurar Allah. Masu buƙata kai tsaye za su iya tuntuɓar ta a kan lambar wayarta 08033748387*)

*Littafin kuɗi ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143*

Buɗe ƙofar banɗakin yayi ya fito, ta ƙwala ihu ta rufe jikinta, ko kallonta bai yi ba, ya maze kamar bai ganta ba, ya wuce ya kashe fitila ya kwanta.

Ajiyar zuciya tayi, ta saka kayanta, ta nufo gadon, sai dai ya babbake gadon, kuma ya ajiye system a kan gadon.

"To ka matsa mini in kwanta".

Ba tare da ya kalleta ba ya ce "Gado ɗaya zaki kwana da ƙaton?".

"To a ina zan kwanta?"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull