Kanwar maza 3 and 4 complete - Chapter 44
Kanwar maza 3 and 4 complete Chapter 44: Kanwar maza 3 and 4 complete Chapter 44. "Kuma ka sani ban ɓallo ruwa ba tukuna, dan wallahi abubuwan da zan faɗa…
4,446 words
"Kuma ka sani ban ɓallo ruwa ba tukuna, dan wallahi abubuwan da zan faɗa a gaban wamban nan da yawa, dan sai dai ka sake ni ko a kashe ni, dan Jamil shi ne mutumin da anty aisha ta gaya mini ta gayawa cewar ta zo kano, za ta je dubiya. Kuma lambar ƴan bindiga suka kira, suka sanar da cewa ta rasu, na haddace ta, Yasir yayi tracking ɗin ta, Jamil ne, kuma shi ne yake haɗa kai da wakili yake ko waliyyi oho muku dai. Kuma duk abun da na faɗa ina da cikakkiyar hujjata, kuma ba wanda ya isa ya hana ni magana"
A gigice cikin tsawa ya ce "Me ki ke nufi rumaisa? Me ki ke faɗa ne? Jamil fa ki ka ce"
"Malam sake ni, ba gaya maka nayi dan ka yarda ba, amma ko ka so ko ka ƙi, Jamil ne ya bayar da bayanan da aka sace anty aisha, kuma har da shi aka je aka ɗauki gawarta, duk da a cikin kaya yake ya rufe fuskarsa, amma na gane shi"
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Innalillahi wa Innalillahi raji'un " ya din ga maimaitawa jikinsa yana rawa.
Banza ruma tayi masa, ta fice daga ɗakin ta bar shi.
Wata irin rawa jikin Adam yake yi, yana fatan Allah ya sa abun da ruma ta faɗa ba gaskiya bane ba.
Jikinsa yana rawa, ya ɗaukko wayarsa da take vibrating, Sunan Bashir ya gani, ya ɗaga amma ya kasa magana.
"Adam, maganar madam fa ta zama gaskiya, Wakili su ne Smoke, kuma ba su kaɗai ba ne ba, manyan ƙusoshin ƙasar nan SMOKE! Sai dai magana mara daɗi, DSS fa na Kano sun je Abuja sun kama Jamil, an kama shi da laifin fitar da sirrin hukumar ga marasa gaskiya, yanzu haka yana tsare"
Ba tare da ya katse wayar ba, ya ajiyeta yana jin yadda kansa yake wata irin bugawa, zuciyarsa sai harbawa take yi da saurin gaske.
Ruma ta dawo ɗakin ta tarar da shi ya haɗa gumi, sai tsuma yake yi.
"Ka tashi ka bar mini ɗakina, ɗakin maƙaryaciya mai haddasa muku husuma a dangi, ka je ka bawa wadda ka ke so haƙuri, kuma ka kwashe wannan kayan tsubbun da aka binne mini, duk saboda kai".
Kallonta yake yana sake jinjina yadda abubuwa suke gudana, tashi yayi ya bar mata wayarsa da kayan tsubbun, ya fice ya bar ɗakin.
Ta kwashe kayan ta ɓoye, ta ɗauki wayar sa, ta buɗe pin ɗin, ta kira Iman.
Iman na ɗagawa ta ce "Kun tafi ne?"
"Eh, amma yanzu su mama suka shiga"
Ta ce "Ok".
Ta kira wayar mama, mama ta ɗaga "Mama ya jikin daddy, ya tashi kuwa?".
"Eh, a zaune muka tarar da shi, jikinsa da sauƙi sosai".
"Mama dan Allah ba shi wayar"
Mama ta miƙawa Mahmud, da yake zaune yana hira da su mama da Ammi.
"Hello daughter"
"Jikin ka da sauƙi daddy?"
Ya ce "Sosai Alhamdilillah"
"Get ready, an ce gobe in Allah ya kaimu za a kawo ƙarshen wannan lamarin, zamu haɗu a gaban wambai, kuma ba zamu yi magana ba sai a gaban ƴan sanda"
Ya ce "Am ready in sha Allah, ku yi magana da su Yasir, dama komai na sa ya zama ready, zai tafi Canada, next week"
"Shikenan daddy, na gode sosai".
Hankali kwance ruma ta sha baccinta yau, sai ƙarfe uku da rabi ta tashi, ta na sallar dare, tana roƙon Allah ya basu sa'a.
Shiru tayi tana tunani, lokacin da take mamakin yadda mama ke katse bacci tana sallar dare, yau sai ga abun ya zo kanta.
Takawa kuwa bacci ya gagari idonsa, yana sake nanata Kasancewar Jamil a cikin mummunan aikin nan, to idan rumaisa ƙarya take yi, binciken su Jamil da kama shi da aka yi fa?.
Ammi kuwa ta wani fannin a iya cewa, rashin lafiyar Mahmud gaba ta kaita, domin kuwa sun fi ƙarfe biyu suna hira. Ta yi iya ƙoƙarin mantawa da abubuwan da suka faru a baya, ya bata labarin makaranta, da yadda ya samu kansa a wurin aiki, amma a cikin hirar ya din ga haɗawa da abubuwan alkhairin Mummy.
Sai dai ga marasa gaskiya, ciki ya ɗuri ruwa, Samha ta din ga kiran wayar baba uwani, dan tabattar da abun da rumaisa ta faɗa a bakinta, amma wayarta ba ta shiga. Gashi ba tare da saninta ba, maman su, ta je ta sanarwa da turaki komai, cikin bala'i da tashin hankali, kuma ta kira wambai ta gaya masa, cewar takawa ya mari Samha, kuma ya ce a kan matarsa ba abun da ba zai yi ba, sai dai zumuncin ya watse. Ga gefe guda, Hajiya Lubabatu ta kai ƙarar Mahmud, wai Mummy ta saka shi, ya yi wa Jabir duka, ya saka an rufe shi, ba tare da ta san wani station ɗin aka kai shi ba.
Samha ta san muddin aka yi zaman nan, to fa kashin su ya bushe, domin wannan matar ta takawa, ba mutunci ne da ita ba.
Suna tsaka da wannan bala'in, maman ta lura da wuni guda, yau Jamil bai kira su ba, sun kira shi amma ba ta shiga, hakan ya ƙara dugunzuma hankalinsu.
Dan haka marasa gaskiya, bacci sai rabi da rabi.
*** Da safe ruma ko ta kan takawa ba ta bi ba, ta shiga sabgoginta, Asiya ta tayata gyara ɗaki, saboda yadda cikinta ya fara tsufa, duk da ba a gani, sai ta saka kaya ƙanana.
"Rumaisa" ta ji ya kira sunanta.
"Ba zamu Asibiti ba?"
"Sai ka dawo, kar na je na kuma ɓata muku zumunci"
"Kiyi haƙuri, na rasa yadda zan yi ne"
Ta ce "Ni ba zani ba"
"Dan Allah "
Ruma ta ce "Ba fa zani ba, idan an shirya zama a gaban Wamban, na je kuma ba zan yi magana ba, sai da ƴan sanda a wurin".
Juyin duniya ruma ta ce ba in da za ta je.
Ya ƙyaleta ya fita tafi.
Ya tarar da ammi, tana bawa Mahmud abinci a baki.
Takawa ya samu wuri ya zauna, yayi shiru bai ce komai ba.
Ammi ta ce "Takawa, ya dai?"
"Bakomai" zata sake magana Mummy ta shigo, Mahmud ya ce "Mummy sai yanzu ko?"
"Eh ai jiya korata aka yi, aka nuna bani na haifeka ba, ba dan kai ne ba ba abun da zai dawo da ni".
Ya ce "Allah ya baki haƙuri, a cewa likita ya zo ya sallame ni, saboda ayi ta ƙare a yau"
Mummy ba wanda ta kula sai mahmud, suma ba su kulata ba.
"Mahmud ina ka kai Jamil ne? Kana a wannan yanayin zaka je wani wuri? Ka sa matar nan ta tayar wa da mutane hankali, sai bala'i take yi. Ta shafa mini kashin kaji, wai ni na saka ka dake shi ka kulle shi. Ga wani zancen ma wai ko an kama Jamil gaske ne ko ƙarya oho"
Ammi ta ce "Kenan maganar ruma gaskiya ce"
"Ba da ke nake ba, da ɗana nake malama" Mummy ta yi maganar gatse-gatse ga giwa.
Ammi ta ce "Allah ya baki haƙuri"
*** Katafaren falon ya cika ga Wambai, ga turaki da wasu manya daga masarautar kano. Ammi ta hallara, ga Mahmud dan ko gama warwarewa bai yi ba. Aka jima sai ga rumaisa da takawa, Bashir jami'an tsaro da wasu daga cikin yayyen rumaisa, ga Samha a wurin da mahaifiyar ta, ga Hajiya Lubabatu da duk wanda yakamata su halarci zaman.
Gaban Samha sai dukan uku-uku yake yi, dan bata san mai rumaisan za ta kwatsa ba.
Wambai ya ce "Su kuma waɗan nan lafiya?" Yayi maganar yana nuna jami'an tsaro, da suka shigo da jabir, a wahale.
Bashir ya ce "Ranka ya daɗe, zuwanmu wannan zaman yana da matuƙar muhimmanci, zaka ji dalilin zuwanmu in sha Allah. Zuwanmu nan ayi tattaunawar da mu, sai ya fi sirri, saboda wasu abubuwan da za a bayyana, akwai kunya ace wasu laifukan daga gidan girma da daraja suka fito"
Adam ya ce "Allah ya taimake ka, wannan ita ce rumaisa matata kamar yadda ka sani, waɗan nan kuma ƴan uwanta ne, wannan kuma abokan aikina ne"
Wambai ya kalli rumaisa ya ce "Ke! Ke ce mai haddasa mana husuma da tashin hankali a cikin family ko? Kafin ki zo lafiya lau mu ke zaune, amma daga zuwanki kin hargitsa komai, ki ce wancan yana asiri, ki ce wannan baya son wannan saboda me?" Ya fara yi wa ruma faɗa, tayi shiru ta sunkuyar da kai.
Turaki ya ce "Ina ganin, a fara bari mu ji ta bakinta tukuna ranka ya daɗe, kar a yanke mata hukunci kai tsaye"
Wambai ya kalleta ya ce muna saurarenki.
Ruma ta ƙulu, basarwa kawai ta yi, ta haɗiye wani abu mai ɗaci sannan ta ce "Kafin na ce komai, zan fara da bawa babana haƙuri a kan abubuwan da zasu fito daga bakina, duk da ya san wasu, na san bai san wasu ba. Ina neman afuwarka babana mai girma turakin kano"
Turaki yayi murmushi mai ciwo, sannan ya ce "Kar ki damu yarinyar kirki, kamar yadda na riƙe miki alƙawari a baya, ina umartar ki da ki faɗi komai, dan fita daga zargi.
Ayshercool. 08081012143 08081012143
Rumaisa ta ja numfashi, sannan ta fito da wata waya, duk ta sha jiki, screen ɗin ma duk ya tsage, ta ce "Wannan wayar, ita ta fara haɗani da takawa, kafin ƙaddara ta sake haɗa mu a karo na biyu. Silar haɗuwarmu na farko wannan abu ne da ya shafi rayuwarmu ni da shi, bai shafi abubuwan da suke faruwa a yanzu ba"
Ta ɗan yi shiru sannan ta cigaba da cewa, "Kamar yadda wasu suka sani, yayyena maza ne, nice ƙarama da duk wanda ya sanni, aka yi mini shaidar rashin ji. Wannan wayar na ɗauke da wasu abubuwa da ka iya taimakawa jami'an tsaro, saboda a rashin ji na, bani da tsoro, kuma cikin ikon Allah ranar da mu ka tafi kai ziyara dangin mahaifina, muka haɗa mota da ƴan bindiga. A cikin wayar akwai hotunan wurare da abubuwa da na yi ta ɗauka, ciki har da jakar bullet mai ɗauke da wasu lambobi, da sunan SMOKE. A rashin ji na, na tattauna da ƴan bindigar, har shugaban su yake ce mini, ƙasa ta san da zaman su, dan kuwa akwai kason su, a kasafin kuɗi da ake duk shekara. Kasancewar a lokacin bakomai nake ganewa ba, amma na fuskanci wasu abubuwan.
Zuwana garin su babana, wanda ƴan bindiga kusan suke mulkar garin, nan ma nayi wata tattaunawar da wani dattijo da aka ƙona rigar su, sai shi kaɗai, wanda shima yana da alaƙa da ƴan ta'adda.
Daga nan har zuwa lokacin da aka yi garkuwa da ni, abubuwan dai tamkar a mafarki, duk yadda za a bawa mutum labarin yadda abun yake, sai ya je ya gani. Na sha baƙar wahala saboda ina da taurin kai da rashin jin magana, na daku kamar ba mutum ba, saboda ban daina rashin kunya ba.
Kwatsam! Aka kawo matar da silarta abubuwa da dama suka faru, mace da tsohon ciki, ta din ga magiyar a bari ta tafi, ko dan cikin jikinta, aka ce a kula wannan ajiyar wakili ce".
Ɗiff ɗakin yayi, Wambai ya ce "waye wakili, wane waikilin tukuna".
Turaki ya ce "A daina katse ta, mu bari ta kammala tukuna".
Rumaisa ta ɗora da cewa "Lokacin da ta zo ina tsaka da rashin lafiya, halin da take ciki bai dameta ba kamar ni, ta kula da ni sosai da sosai, sai dai wasu lokutan sai tayi ta kuka, idan na bata haƙuri sai ta ce; ba sace ta da aka yi ne dameta ba, mijinta, ba yadda bai yi da ita ta fasa tafiya ba amma taƙi, sai kuma sanya hannun ɗan uwanta a wurin saceta.
Ta bani labarin mijinta, iyayensa, yadda suke rayuwarsu, da kuma irin rayuwar da tayi a nasu gidan.
Ta gaya mini mahaifinta ya saka sunanta a kadararsa, kuma wasu kuɗinsa na shiga account ɗin ta, saboda ita bai taɓa mallaka mata wata kadara ba, saɓanin ƴan uwanta, da kowa yana da wani muhimmin abu da ya bashi.
Ta gaya mini matar mahaifin ta da yayyenta, sun uzzura mata sosai a kan hakan, kuma babu wanda ya san da zuwanta Nigeria, sai yayanta da ta gayawa, ta sanar masa ga ranar da zata je dubiya....
"Ƙarya ne, me ki ke nufi, Jamil ne ya sanya aka yi garkuwa da aisha, wallahi ƙarya ki ke yi, ni za a yi wa sharri, a cuci ɗa na a ɓata mana suna"
Wambai ya ɗagawa babar su Jamil hannu, ya dubi ruma ya ce "Wani tabbaci zaki bamu a kan haka, ta yaya zamu yarda da ke?".
"Na yi wa anty aisha alƙwarurruka, bayan ta ce mini ta bani amanar mijinta da ɗan ta, duk da ƙarancin shekaruna, na fahimci abubuwa da dama a labarin da ta gaya mini" rumaisa ta basu labarin komai, har kan mutuwar aisha.
Ta kalli Abdallah ta ce "Bismillah"
Abdallah ya dawo tsakiya, ya zauna da kayan zanensa.
Ruma ta ce "Wannan yayana ne, kuma ƙwararre ne wurin iya zana abubuwa, da shi nake koyi, ya sanya nima na iya zane-zane, amma kasancewata ƴar koyo, zan ba shi damar ya zana wani abu, kar ace na yi son zuciya ko sharri nake son yi wa wani, yana daga in da yake zaune, zan siffanta masa abun da zai zana ɗin, Abdallah ba ya nan aka sace ni, nikaɗai aka sace, dan haka you should be good in judgment"
Kowa yayi shiru ya zuba musu ido, sannu a hankali take siffanta masa abubuwa yana zanawa, bai ja lokaci ba ya kammala zanen ya miƙa musu takardar da yayi zanen a kan ta.
Ta siffanta masa Mutanen da suka je suka ɗauki gawar aisha ne, da motarsu, da yanayin da suka ɗauki gawar.
A yadda rumaisa ta suffanta masa ya zana, Jamil ne a gaba cikin kayan ppe, amma yanayin tsayuwar da sashin da aka iya gani na fuskar sa, zai tabbatar maka da shi ne, idan har ka san shi.
A lokacin takawa ya tuna a tsukin lokacin yayi ta fama da faɗuwar gaba, da fita hayyaci, kuma Jamil yayi balagro a lokacin.
Mahaifiyarsa ta cigaba da bala'i, da iƙirarin wannan shegantakar banza ce ba Jamil ba ne ba.
Mahmud ya ce "Allah ya baku yawan rai, muna da shaida ta gaba, ban sani ba kafin ni, ko ta gaya wa wani, amma ta same ni da maganar, kuma da ni da wasu daga cikin ƴan uwanta maza muka yi aikin nan. Akwai lambar waya da ta bani, lokacin tana magiyar a kai aisha asibiti kan ta rasu, ita ce lambar da aka kira, na bayar an yi tracking ɗin ta, haka zalika ɗan uwanta Yasir yayi tracking ɗin ta, an daina amfani da layin, amma Jamil ne yayi register da layin, Yasir na da tracking result ɗin sa, ni ma ina da nawa da police suka yi"
Wani daga cikin ƴan sandan ya ce "Amma wannan ai aikin police ne, mu yakamata ace mun yi shi, ko shi Adam tun da jami'in tsaro ne".
"Ban ji na yarda da kowa ba da zan iya ɗaukar shaidu, masu muhimmanci na bawa ƴan sanda ba, dan a lokacin na ji takaicin ace ƙasata da jami'an tsaro amma aka kasa kuɓutar da ni, daga hannun ƴan bindiga, kuma ƴan bindiga da kansu, suka tabbatar mana da kun san da kune ku ke sauƙaƙa musu aiki, ku jami'an tsaro. Takawa kuma ban gaya masa komai ba, saboda a wancan lokacin yana cikin damuwa da tashin hankali ne, da kuma fuskantar matsin lamba daga mutane, a yadda yake a zuciye zai iya ɓata komai a wannan lokacin.
Maganar ina ƙoƙarin ɓata zumunci ta hanyar haɗa husuma kuma, ina da shaida babu wanda na yi wa sharri, ranka ya daɗe wannan ledar ta gabana, cike take da kayan tsubbu da na sanya baba uwani tsohuwar hadimar ammi tonewa, kuma nayi amfani da wayar ɗaya daga cikin ma'aikatana, na naɗi duk abubuwan da aka saka ta yi mini, suma suna cikin wannan wayar na tura a ciki".
Adam ya tashi jiki a matuƙar sanyaye, ya ɗauki excuse ya fita amsa waya.
Tun da suka shiga ake kiran wayar, sai dai da ya duba ya ga private number na.
A yadda ruma suka tsara da Mahmud, shi ne zai faɗi abubuwan da suka shafi ɓangaren Mummy, kutungwilar da take shiryawa amma ya kasa.
Turaki ya sunkuyar da kai zuciyarsa na yi masa raɗaɗi, saboda abun duniya yana ciki ɗaya da aisha, ubansu ɗaya, ya sanya aka saceta, kuma yake ta ƙoƙarin sanyawa a ɗora zargi a kan Adam, Adam ɗin da ya kasance abokinsa ɗan uwansa da suka tashi tare.
Kuka matar turaki take yi, ta ce "Ita haryanzu ba ta yadda da cewa Jamil zai iya aikata mummunan abu irin haka ba sharri ake yi masa".
Bashir ya ce "Hajiya sai dai ki yi haƙuri, domin kuwa jami'anmu sun riga sun kama shi ma"
Mahmud kuwa ya dubi Jabir, sannan ya mayar da idonsa kan Hajiya Lubabatu ya ce "In faɗi me Jabir yayi, ko kuma in bari ku faɗa da kanku?"
Suka yi tsit babu wanda yayi magana, Mahmud ya ce "Dole ka cigaba da zama a hannun 'yan sanda su kammala bincike"
Wambai ya ce lallai a nemo masa baba uwani duk in da take, gaba ɗaya falon ya hargitse da hayaniya.
Rumaisa ta ce "Babban roƙon da zan yi muku shi ne, kar wanda yayi ƙoƙarin yin wani abu a kan wakili, saboda nikaɗai ce shaida a kansa, sai dai in Jamil ne ya yi magana a kan sa, idan ba haka ba".
Bashir ya ce "Haka ne, amma ban taɓa tsammanin wakili zai kai haka ba, saboda tsamar da ke tsakanin sa da Adam ba"
Adam ya ɗaga wayar tare da yin sallama "Na san ko ban yi magana ba, ka san da wanda ka ke magana, Senator mai wakili ne. Ina tayaka da ƴan team ɗin ka murnar gano suwaye SMOKE. Sai dai nikaɗai ka sani a SMOKE, amma ka sani gano smoke ba shi da wani amfani, saboda su kansu wanda ka ke tunanin zasu ɗaukar maka matakin suna cikin SMOKE. ministan man fetur ke da shiyyar satar mai, Ɓangaren tsaro suna da kamasho a kasafin da ake yi, da wasu manyan mutane a ƙasar nan. Talakawan da ka ke yi domin su, basu isa su yi maka komai ba, duk wata shaida da kake tunanin kana da ita a kanmu, akwai gaɓar da idan aka kai, kai ne zaka kwana a ciki, dan na san baka isa ka yi jayayya da shugabannin rundunar tsaro ba, ba ka da wata shaida a kan sa. Dan haka kai zaka kwana a ciki, duk yaranmu da ku ka samu ku ka kama, babu wanda ya san suwaye SMOKE, kai kaɗai ka yi nasarar gano suwaye, ɗan uwanka Jamil yaron Khalifa ne, tare da shi suka yi aiki, sai dai shima bai san mune SMOKE ba, mun yi amfani da sace matarka, wurin ɗauke hankalin ka daga kanmu, kuma cikin ikon Allah ta haihu ta rasa ranta. Abu ɗaya zuwa biyu nake son gaya maka. Ka bar al'amarin nan a iya haka, idan ba haka ba zaka yi ta ranka, ko kuma ran matarka da ɗanka, dan kuwa ita ce duk sanadin komai, dan kuwa duk motsin ku, da duk abun da take yi, muna samun labari ta ɓangaren Jamil. Dan haka sai ka zaɓi ɗaya, fito na fito da masu ƙasa, ko kuma ka rasa rayuwarka da na matarka, dan ka san ba abu ne mai wahala ba. Sai dai fa ka yi haƙuri, domin kuwa rayuwar matarka ta salwanta kamar ko wani karabutin ɗan ƙasa, duk da kasancewar ka mai kaki, kuma jinin babbar masarauta, ire-iren yaranmu ne kisan su baya tafiya a banza. Kuma duk wani abu da zai faru Jamil ba zai taɓa furta sunana ko na ɗa na ba. Dan haka gara ka watsar da duk wani yinƙurinka, ka tattala abun da yayi saura a rayuwarka, kan mu gama ɗiaɗaita ku" ya katse wayar.
Duk da hatsaniyar da ta kaure a falon, yanayin da takawa ya shigo, ya sanya kowa yin shiru, wani irin gumi yake yi, jikinsa yana tsuma, kuma aka rasa mai tambayarsa meyafaru, kowa ya zuba masa ido.
Ruma ce ta miƙe tsaye, ta ce "Papa lafiya kuwa?"
Gabanta ya ƙarasa, jiki a matuƙar sanyaye ya zube a kan gwiwoyinsa ya furta "Na gaza, dama kin gaya mini, na gaza rumaisa ba laifina bane, na yi iya yina, abun ya fi ƙarfin yadda nake tunani, na barwa Allah, tun da a cikin gidanmu ma aka kware mini baya, ba ni da saurin ƙwarin gwiwa. Da izzar da tawa da sarautar tawa da komai na zube su a kan gwiwoyina, na gode rumaisa, na gode. Ke alkhairi ce ga rayuwata da ahalina, wataƙila ba dan ke ba, ba zan gane bara gurbin da suke rayuwata ba" Hawaye yake zubarwa kamar ƙaramin yaro, cike da ƙunar zuciya. Lallai faɗa da aljani ba daɗi, shiya san bai isa cigaba da fito na fito da wannan mutanen ba, in dai a Nigeria ne, mutane sun san ta'addancin Smoke, sai dai basu san suwaye ba, kuma wani abun shaidar rumaisa kawai ba zata wadatar ba, hakazalika da rayuwar rumaisa ta salwanta gara ko menene ya haƙura da shi, yarinyar tayi sacrificing alot".
Rumaisa ta durƙusa ta ce "Papa dan Allah ka tashi, ka sakani a duhu, ni ban gane me ka ke nufi ba, ka tashi dan Allah, a gaban mutane ne fa"
Mahmud ne ya tashi ya kama Adam, ya miƙar da shi tsaye, ya ja hannunsa ya cewa rumaisa su tafi.
Ƴan sanda suka tattara duk wasu bayanai da suka kamata, wanda rumaisa ta bayar, da zanen Abdallah da aikin da Yasir yayi, Bashir ya karɓe ya ce sai sun kammala na su binciken tukuna, zasu gani idan da yiwuwar ba wa ƴan sanda.
Wambai kansa ya girgiza da jin lamarin, tausayin ɗan uwansa turaki ya kama shi.
Sosai babar Jamil ke kuka, tana cewa turaki ya saka baki, ya ƙaryata abun da suka faɗa, ya sanya a saki Jamil.
Wambai yayi mata tsawa, ya ce su tashi su tafi sai ya sake nemansu.
Mummy godiya ta yi wa Allah, da ba a faɗi komai a kanta ba, Hajiya Lubabatu ta zube tana yi wa wambai magiya ita ma a kan a taimaka a sanya baki, a saki Jabir.
Mummy ta ce "Wallahi ba ta isa ba, ba zai lalata mata ƴa ya ci bulus ba" jin abubuwa babu Allah a ciki, dagulewar lamuran yayi yawa, ya sanya wambai cewa su tafi su je su ƙarata a wurin ƴan sanda.
Sai da ya rage daga shi sai turaki, sannan turaki ya samu zubar da hawaye, ya daɗe matar nan tana citar da shi da Aisha, amma ba ya iya ɗaukar mataki, dama tun a farko rumaisa ta gaya masa komai, sai dai bai tabattar ba sai a yanzu. Wambai ya dafa kafaɗarsa ya ce "Ina neman afuwarka ɗan uwana, na rashin tsayawa in fuskance ka a abubuwa da dama. Dama na san biyayya ce ta sanya ka auri Sa'adatu, sai dai wannan abu ba kai kaɗai ya shafa ba, zan yi iya ƙoƙarin ganin cewa maganar nan ba ta fita ba"
"Kar ka yi haka, ko kayi hakan, ko ba kayi hakan ba, dole sai maganar ta fita, Allah ya jiƙan fulani da mahaifiyarta, rumaisa kuma Allah ya yi mata kyakykyawan tukuici da ita da iyayenta.
Mahmud kai tsaye har gida ya kai Adam da rumaisa.
Adam na kwance a jikin rumaisa kamar uwa da ɗa, sai aikin rarrashin sa take yi, tana bashi haƙuri.
"Rumaisa, ni wakili yake gayawa sai in dai in yi haƙuri, ran matata ya salwanta a banza, saboda wautata da rashin hankali, kuma wai ba wani abu da zan iya yi a kai"
"Ban gaya maka ba? Na ce zaka iya bincike ne kawai, amma in dai a ƙasar nan ne, kar ka yi tsammanin samun adalci, mu bar wa Allah papa, you try your best, Allah shaida ne"
Mahmud ya ce "Takawa dan Allah ka daina kukan nan haka, kar ka tayar mata da hankali, ga ciki tana fama da shi".
"Mahmud baka san me nake a zuciyata ba, ba zaka gane ba"
"Na sani mana, saboda sauƙaƙa maka raɗaɗin da ni da rumaisa muka yi aiki tare dan sauƙaƙa maka aiki. Ina mai baku haƙurin rashin exposing Mummy, amma ita ma very soon in sha Allah, ka yi haƙuri dan Allah"
Cikin kuka ya sake cewa "Jamil fa mahmud, a ɗakin Ammi muka yi wasa tare muka faɗi muka tashi, amma ni Jamil zai din ga yi wa wannan cin dunduniyar? Me nayi masa? An kashe mini mata kuma ya cigaba da bibiyata da ƙoƙarin ɗora mini sharri? Me nayi masa ne?"
"Baka yi masa komai ba Papa, hassadar ka fi shi komai ne kawai da kwaɗayin abun duniya ya sanya shi haɗa kai da maƙiyanka, gashi wanda ka ke yi wa kallon maƙiyin, shi ne ya taimake ka, duk lalacewar ɗan uwa naka ne papa".
"Na gode mimi na gode sosai"
"Dan Allah ka daina yi mini wannan godiyar, ni ba abun da na yi "
Mahmud ya miƙe ya ce "Daughter, ki kula mini da shi sosai dan Allah, zan je gida wurin ammi, na san tana cikin damuwa ita ma"
Ruma ta ce "Wait, wai ba daga gadon asibiti ka taso ba?"
"Rabu da ni na warware "
"Amma ka yadda maman jabir tayi maka wani abu?"
Ya ce "Na yarda, Kamar yadda muka saka Yasir bibiyar wayar Mummy, ya kunna mini wayar da Mummy tayi da Hajiya Lubabatu. Na karɓi duk wata shaida ta hannunsa, jibi in Allah ya kaimu zai tafi wurin Anty laila, kar ma a samu wata matsala saboda aikin da ya yi mana"
Ruma ta ce "When are you exposing her?"
"Soon in sha Allah"
"Idan ba zaka yi ba, allow me to do it"
"I will in sha Allah" ya juya ya fita.
Haka ruma tayi ta aikin rarrashin Adam, dan abun ya dake shi sosai da sosai, duk iya tunaninsa bai ga ta ina zai iya jayayya da SMOKE ba.
Kuma dolensa ya haƙura da cigaba da duk wani yinƙuri a kan garkuwa da aisha, saboda rayuwar rumaisa.
*** Kwanaki uku kenan, gidajen sarautar suka shiga ɗimbin tashin hankali, komai ya damalmale, ba kama hannun yaro, aka gaza samo bakin zaren abubuwan da suka riga suka dagule, Kodayake ba komai ne zai gyaru ba, kasancewar wata ɓarakar ta samo asali ne tun shekarun da suka gabata, ba tare da an mayar da hankali an gyara su ba. Kodaye rumaisa ta kawo gagarumin cigaba da kuma gyara wasu abubuwan.