Kenza eBookz

Kanwar maza 3 Complete - Chapter 48

Kanwar maza 3 Complete - Chapter 48

Kanwar maza 3 Complete Chapter 48: Kanwar maza 3 Complete Chapter 48. Tafiyarsa babu daɗewa, takawa ya kira iman, ya ce su fito ya mayar da su gida. A…

3,365 words

Tafiyarsa babu daɗewa, takawa ya kira iman, ya ce su fito ya mayar da su gida. A kayan da mai sunan baba ya kawo wa rumaisa, har da uban fura da nono, kaya guda da su mazarƙwaila, sai addu'oi a rubuce, da wasu saiwoyi da ba ta san ko na menene ba. Ga su ƙuli da man ja da fari, kayan kuka da kuɓewa har da su wake abun ka da mutanen karkara.

Haka ta keta kayan biyu, ta ce wa Iman ta kaiwa Ammi.

A lokacin da Adam ya dawo daga kai su iman gida, ya tarar tuni ruma ta yi bacci.

Ya ci abincinsa, da ya tarar a kan dining, dan yanzu idan ba makaranta ta tafi ba, shine su barira suke dafo abinci.

Ya leƙa ɗakinta, ya tarar tana kwance a ɗakinta da kayan baccinta, ɗan mini skirt, da riga vest, ga jigidar da ke ƙugunta tayi mata cif.

Ya taka ya ƙarasa ya tsaya a kanta, amma baccinta kawai take yi, ya zauna a kusa da ita, ya zubawa ƙafafuwanta ido, daga ƙasa dai ga ta da hips, amma sama kam, yanzu ne ma dai suka ɗan tasa. Murmushi yayi da ya tuna wasiƙar da ta aika masa, da ya yi ta yi wa Allah godiya babu wanda ya ga takardar ya karanta.

Ya kai hannunsa kan jigidar, yana ɗan ja a hankali, yana zancen zuci, abu kamar wasa ya koma shafa cinyoyinta.

Duk da nauyin baccinta, caraf ta riƙe hannunsa, ta buɗe ido "Meye haka?"

Ko a jikinsa ya ce "A ina?"

"Papa bana so" tayi maganar tana tura baki.

"Ni ina so ai" yayi maganar yana janyota ya haɗata da jikinsa yana kallon idonta.

Mutsu-mutsu take tana hararsa za ta ƙwace, amma ya saka hannunsa ya ɗaya ya ɗago haɓarta ya ce "Can we try it now?" Tayi masa ƙuri da ido tana kallonsa.

"Are you ready for it? I want kiss you mimi".

Girgiza masa kai ta yi ta ce "Dan Allah bana so" tayi maganar idonta na cikowa da hawaye.

Bai kuma ce mata uffan ba, yayi abun da rumaisa ko da wasan wasa, ba ta taɓa kawo hakan ba. Kissing ɗin ta yake yi sannu a hankali.

Ta rirriƙe jikinta, tare da jin abun wani banbarakwai a duniyar ta, abun da aka ginata a kan cewa abu ne da bai kamata ba, yau ta tsinci kanta dumu-dumu a cikin sa.

Ba ta tsinke da lamarin ba, sai da ta ji Adam yana ƙoƙarin yin wani abu daban da ya tayar mata da hankali. Ihu ta din ga yi, tana riƙe rigarta, har da kiran su baba uwani su zo su rabata da Adam, zai yi mata abun da bai dace ba.

Ba ihun rumaisa ne ya tayar masa da hankali ba, illa jin sa da yake yi kamar ba shi ba, kamar an canza shi.

'Me hakan yake nufi?' ya tambayi kansa a ɗan tsorace.

Jikinsa ne yayi sanyi sosai da sosai, ga rumaisa a hannunsa na ta ƙoƙarin ƙwacewa.

Kwantar da kanta yayi a ƙirjinsa, ya ɗora kansa a nata, a ransa yana maimaita Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wace irin masifa ce kuma wannan ya sake tsintar kansa a ciki?

Yana jin yadda rumaisa ke ta zubar da hawaye, tana alwashin sai ta gaya wa kowa na duniyar nan, ya saka mata hannu a riga.

"Yi mini shiru, ni ki ke yi wa wannan ihun ko?".

"To waye ya ce ka yi mini abun da ka yi mini, bayan ni a gidanmu an ce mini ba kyau. Wasan banza fa kenan, kuma saboda a daina ce mini ƴar iska na ƙara yadda muka yi aure".

Halin da yake ciki bai hana shi yin murmushi ba, ya ce "Duk wani mai aure ɗan iska ne ai, wannan sirrinmu ne, ba a faɗa"

Rumaisa ta tashi zaune ta ce "Sai na faɗa, kuma kowa na duniyar nan, duk wanda na sani sai na gaya masa"

"Idan ki ka faɗa, cewa zan yi ke ki ka ce ayi, gara ma ki yi shiru".

Share hawaye take ta ce "Wallahi ni ba ƴar iska ba ce, bani na ce ayi ba".

Takawa ya ce "Oho dai, idan ki ka faɗa abun da zan ce kenan, yarinya ki adana hawayenki ma, ba yanzu yakamata ki yi kuka ba. Sai an zo making baby"

Ba ta gane me yake nufi ba, ta cigaba da kuka.

"Gobe in Allah ya kaimu zan fara shirin tafiya, in dai Mummy ta janye maganar ta, ina son zuwa wurin mai girma turaki ma"

"Kai ta tafiya, ni ba sake shiga harkar zan yi ba, kuma sai na tambayi mama, in dai duk mai aure kallon ɗan iska ake yi masa, sai na koma gida"

"To ki tambayo, idan kin tambayo sai ki bani amsa. Banda tsiwa ina abun yake, meye a rigar da ki ke mini wannan bankaɗar, da kururwar, abun da bai fi murfin jarkar faro ba"

Banza tayi masa tana sake kawar da kanta gefe.

Ya tashi tsaye, ya bar ɗakin.

Duk son baccin rumaisa sai ɓarawo ne ya ɗauketa, tana jin tsoron ta rufe ƙofa, kuma tana tsoron takawa ya sake dawowa.

Adam kuwa hankalinsa a tashe ya koma ɗakinsa yana safa da marwa, yana tunanin wa zai tunkara da wannan matsalar, matsala ce ba ƙarama ba, da take buƙatar ya samu mafita, kan rumaisa ta gama fahimtar menene aure, kar ya cutar da ita.

Iman kuwa bayan ta koma gida, ammi kallonta kawai take tana son nazartar ta, za ta fita, ta ganta a damuwa, ta dawo ta ganta cikin annashuwa, ba tare da ta san menene ya sanya ta cikin farin cikin ba.

Sai da ta je kwanciya sannan ta janyo wayarta, ta shiga what's app, cikin fargaba ta turawa mai sunan baba saƙo "Yaya umar ya ka je gida?"

Kallon message ɗin ya din ga yi, yana shafa kan message ɗin amma yaƙi reply.

Kusan mintuna talatin, tana ganinsa online, amma bai reply ba.

Tunani tayi meyasa ma ta tura saƙon, sai ta yi sauri ta goge.

Ta na gogewa ya yi replying da 'Me ki ka goge?'

"Bakomai" ta bashi amsa.

"Send it again"

Tsuru-tsuru tayi kamar tana gabansa, sannan ta sake rubuta masa ya ka je gida.

"Wayata yakamata ki kira, idan kin damu ki ji ya na je"

Ta yi masa replying da "Yi haƙuri"

"Kin yi laifi ne ki ke bayar da haƙuri?"

"A'a na ga kamar ka ji haushi ne"

"Ba haka nake ba, masifaffe kamar yadda waccan yarinyar take baki labari ba".

Iman ta ce "Eyya ba haka ta ce mini ba wallahi"

"Umar ba masifafe bane, na dawo lafiya ƙalau, na gode sosai" tashi zaune iman ta yi tana yarfe hannu cikin murna.

Offline mai sunan baba shi ma yayi, ya na murmushin da bai san dalilinsa ba.

Yau juma'a akwai makaranta, amma ruma ta ƙi shiryawa, ta sha baccinta.

Takawa ma bai takura mata ba, bai ce sai ta je ba.

Sai sha ƙarfe goma na safe, sannan runaisa ta fito, ta shiga kitchen ta haɗa abinci ta dawo falo ta zauna.

Ta zauna ba jimawa, sai ga shi ya shigo, ashe ma ba ya gidan ba ta sani ba.

Ta wani sake tsuke fuska, ya ƙarasa ya zauna a kusa da ita ya ce "Ba gaisuwa yau?" Ta matsa daga kusa da shi. Ya sake matsawa ya ce "Mun yi faɗa ne?".

"Gaskiya papa bana so, Allah ka taɓa ni sai na yi ihu da ƙarfi"

"Me zan taɓa?" Yayi maganar yana kallon ta.

"Oho ai ka san me kayi mini".

"Ba wannan ba, tun da yau kin ƙi zuwa makaranta, zan je na ɗan yi bacci ne, an jima zaki tayani haɗa kaya, gobe in Allah ya kaimu zan tafi"

Da sauri ta ce "Haba dai?"

"Ba kya so na tafi ne? Ai gara na tafi, na je na yi aure, tun da ihu ki ke yi mini. And turaki ya ce mini Mummy ta samu mai girma wambai ya ce magana ta wuce, Weldon little Mimi, aikinki yayi kyau"

Kallo ta bi shi da shi, har ya shiga ɗakinsa.

Ta kalmashe ta kunna Tv, tana kallo, ta ji sallamar wata mata, wani irin ƙamshi ya daki hancinta.

Ta ɗaga kai ta kalli matar, matar fara sol kamar ka taɓa jini ya fito, wata ƴat gayu, ta sha baƙin glass, da English wears.

Ta nemi wuri ta zauna, ta kalli rumaisa ta ce "Hey, ina mutanen gidan?"

Rumaisa ta kalleta, tare da jinjina rainin wayo irin na matar, ta ce "Mutan gida kamar wa kenan?".

Matar ta ce "Matar gidan, da kuma takawa"

Cikin rainin hankali ruma ta ce "Matar gida ni ce, takawa kuma is not available"

Ayshercool. 08081012143 [12/12, 7:33 PM] rahama Jos: Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Susbcribe my YouTube channel please 🙏 Rumaisa na nan tsaye tana kuka, tawagar ta tashi, suka yi gaba.

Ammi sai rarrashin rumaisa take yi, laila ta ce "Wai ke ba kya jin kunya ne, wa ki ka fi iya soyayya, soyayyar da ko iya ta baki yi ba, ko Kunyar ammi ba kya ji".

Ammi ta ce "Babu ruwanki, mu ba ma wata kunyar sirikai".

Su Jamil suka ƙaraso, suka gaida Ammi, sai dai ammi ba ta san, meke faruwa ta takawa da su Jamil ba, dan haka normally ta amsa musu, kamar yadda suka saba.

Jabir ya dubi iman ya ce "Iman ko zaki zo in mayar da ke a mota ta?"

Ammi ta ce "Kar ka damu, kwa haɗu a gida, laila mu shiga ciki mu gaisa da mutanen gidan, tun da matafiya sun tafi"

Suka shiga wurin mama, sai wani cika take tana batsewa, sai dai duk da haka, ta shiga taitayinta ganin ammi tare da laila, dan kar ta san kar.

Ta dubi laila ta ce "Ashe kin zo garin?"

Cikin taƙama laila ta ce "Yeah, almost 2days"

"Yayi sannu da zuwa, wannan kamar matar takawa ko? Meya sameta take kuka?".

Laila ta ce "Abun mata da miji sai Allah, ga yarinta a kan ta, dole tayi kuka".

Mama ta ce "Mhmmm Allah sarki Aisha, har ta kai adam ya manta da ita, ya cigaba da rayuwarsa?"

Laila sarai ta gane magana matar turaki take nema, dan haka ta ce "Aka rasa iyaye ma a dangana, a cigaba da rayuwa ayi musu addu'a, rasuwar fulani ai mu aka yi wa, kuma babu yadda za ayi mu manta da ita, kuma takawa yana nan yana aiki tuƙuru a kan neman hakkinta. Kuma dan ya rasata baya nufin ba zai sake farinciki a rayuwarsa, da ya rasa soyayyar mahaifi ma bai mutu ba, dan haka dan Allah a daina kawo wannan maganar"

Laila ta miƙe ta ce "Ammi mu tafi"

Babu wanda ya kuma magana har suka fice.

Zee da tana falon aka yi komai a gabanta, shiru ta yi, dan kaɗan da aikin laila ka yi mata rashin kunya, ta kwaɗeka, saboda masifarta.

Takawa suna airport, ya kira iman, ya ce ta haɗa shi da rumaisa, ta miƙawa ruma wayar, sai dai ta yi shiru.

"Hello, mimi"

"Na'am"

"Ki yi mini Addu'a, nan da mintuna talatin jirginmu zai tashi"

"To Allah ya kai ku lafiya"

"Amma dai kin daina kukan ko?"

Murya can ƙasa ta ce "Na daina"

"Yauwwa buruwar mijinta, da kun koma gida, ki samu ki ɗan yi bacci, jiya bamu samu isasshen bacci ba. Sannan a gida akwai key ɗin wardrobe ɗina, na bar miki kuɗi a ciki, sannan zan din ga turawa laila kuɗi ko zaki buƙaci wani abun".

Ruma ta ce "To" daga haka ta bawa iman wayarta.

Su Fauziyya kuwa bayan sun gama kai wa samha rahoto, silalewa suka yi, suka bar gidan, suka bar ta da tension.

Zee ta tarar da Samha a zaune, abun duniya ya isheta, tamkar ta ɗora hannu a ka, ta fasa ihu saboda baƙin ciki, dan me Mummy za ta ce kar baba uwani ta din ga gaya mata abubuwa da suke faruwa a gidan Adam, sai wanda ta bayar da umarni?.

"Samha!" Zainab ta kira sunanta a karo na uku.

Samha ta ɗaga kai ta kalleta, "Sai magana nake kin yi shiru".

Ɗan guntun tsaki ta ja ta ce "Menene?"

"Labari ne mara daɗi bayan wanda su Fauziyya suka gaya miki. Laila ta dawo, sannan alamu sun nuna cewa yarinyar nan zaman lafiya suke yi da mijinta, kin ga zancen su Fauziyya ya tabatta".

Samha ta ce "Babar su Fauziyya ce banbar munafuka, wato hajiya jamila"

Cikin mamaki ta ce "Uwar ɗakin naki?"

"Zainab saboda tsabar matar nan ta mayar da ni ƴar iska, mun bawa wannan uwanin aikin, kawo rahoto a kan abubuwan da suke faruwa a gidan adam, ni burina auren adam, ita kuma hana shi sarauta. Ni yayi sarauta ko kar ya yi bai dameni ba, ni shi nake so. Meye haɗin aikinta da nawa, da za ta ce wa baba uwan wai kar ta din ga kawo mini bayanin abin da yake faruwa sai wanda ta yi mata umarni, ni zata mayar shashasha, na shanya baki na san na yi aiki tuƙuru a kansu, amma na yi sakacin da har shaƙuwa ta shiga tsakaninsu. To bari a gama watsewa, na je har gida na sameta".

"Ki sameta ki yi mata me ne? Ke kin san idan ki ka ce zaki yi fito na fito da ita, tafi ƙarfinki. Babarki ce a hatsabibanci, ki cigaba da abubuwan ki ba tare da ta sani ba, ki bita a haka, kar kuma sauya mata fuska".

"Ba zan iya jurewa bane zee, kawai ji nake idan ban zageta ba zan huce ba".

"Aikuwa ya zama dole ki danne, ko ta yi miki wani mummunan sharrin".

Samha ta yi ajiyar zuciya ta ce "Zainab na wuce yadda ki ke tunani, tun da ta ɓata nawa aikin, sai dai mu yi biyu babu, kuma son Adam yanzu na fara, sai na ga ƙwal uwar daka".

Rumaisa kuwa wuni tayi baccin dole, saboda koke-koken da tayi, kanta ya fara ciwo, dan haka tayi ta kwanciya tana bacci, surutun ma ya gagareta, ba ta taɓa zaton akwai wani abu da zai tsaya mata ya hanata walwala ba.

***

Mummy kuwa ta titsiye Mahmud a ɗaki, ta na tayi masa bala'i a ka, kamar ta ari baki, saboda tsan-tsar ɓacin rai da damuwa.

"Kai yanzu Mahmud dan Allah ba ka ji kunyar abun da ka aikata ba, matar da ba ƙaunarka take yi ba, ta fifita ƴaƴanta a kan ka, kai ka san ba ƙaunarmu suke yi ba, daga ita har ɗanta, amma dan abun kunya, kana jiran sarauta yana jira, dan me zaka tuƙa shi a mota, direbansa ne kai, ko saboda rashin sanin ciwon kan ka ne? Ko kuma dan ka nuna mini iyakata, ka nuna mini bani na haifeka ba?"

Yayi mata shiru yaƙi magana, hakan ya ƙara tunzurata, ta dungure masa kai da ƙarfi, amma cikin baƙin taurin kai, ko gezau bai yi ba.

Sai da ta zuciya ta yi hanyar fita, sannan ta tsinkayo muryarsa ya ce "Tambayar da rumaisa ta yi mini, ta jefa ni cikin damuwa, da taradaddin neman amsar, sai dai ban sani ba ko zaki tayani samo amsar?" Cak ta tsaya, ta waiwayo tana kallonsa.

Bai ɗago ba ya cigaba da cewa, bayan buɗar idona a hannunki, kin ginani a kan cewa, a duniya bani da babban maƙiyin da ya wuce giwa da kuma ɗan uwana Adam.

Na ginu a kan haka, a lokacin da na san gaskiyar wacece mahaifiyata kuma, sai ki ka nuna mini bata sona ne, ta zaɓi waɗancan ƴaƴan nata a kaina, shiyasa ke ki ka karɓeni ki ka riƙeni, kuma kin ce baki da wani buri da ya wuce na gaji kujerar babanmu, marigayi galadima. Na hau kan tarbiyarki da hanyar da ki ka ɗorani a kai, na sawa zuciyata tabbas mahaifiyata ba ta ƙaunata. Sai dai ko da rumaisa ta tambaye ni sau ɗaya me giwa ta taɓa yi mini, a zahiri da ya nuna bata ƙaunata? Sai kunya ta rufeni, a lokacin da na tuna kin yi mini shamaki da zuwa in da take, kuma kin koyar da ni ƙiyayyar ɗan uwana, ƙiyayyar da ta yi tasiri a tsakanin mu. A lokacin da rumaisa ta tunatar da ni, na sanya mahaifiyata kuka a lokacin da ta nemi alfarmata, ƙarƙashin umarninki, na ƙi yi mata, sai na ji a duniya bani da wani amfani.

Mummy ba ina nufin juya miki baya ba, bani da wata a duniya bayan ke, amma giwa na da hakkin haihuwata da ta yi, ba zan taɓa bari ki muzanta ba, sai dai ina fatan ganin tabattacen haɗin kai a cikin gidanmu, auro rumaisa cikin iyalinmu alkhairi ne mummy. Ban aikata hakan dan muzanta miki ba". Ya ƙarasa maganar cikin rauni.

Kuka Mummy take tamkar ta aminta da abun da ya faɗa, sa dai ƙasan zuciyarta cike yake da baƙin ciki da takaici, tare da aniyar sake ɗaura ɗambar, kawo ƙarshen giwa, da adam har da wannan annamimiyar ƴar tayin da ke barazana ga harƙalarta.

***

Wajen ƙarfe biyar na yamma, rumaisa na zaune zuruuu kamar mara lafiya, shi kansa sabir ba shi da karsashi, ya zo Jikinta ya kwanta, yayi shiru shi ma ko wasa baya yi.

Iman ta ce "Haba Anty rumaisa, takawa zai dawo, tafiya ba mutuwa ba ce, wannan damuwar ta yi yawa ai"

Iman ta ce "Hmm ba zaki gane ba, ni fa ban taɓa zaton zan damu ba, nayi-nayi kar ka damu na manta, amma na kasa".

"To ba ga waya ba, idan ya kira sai ku din ga video call".

Rumaisa ta ce "Ni duk ba wannan ne ya dameni ba" Iman za ta sake magana, Nusaiba ta yi sallama.

Suka amsa mata, ta dubi iman ta ce "Amaryar uncle, his royal highness jabir, is waiting for you".

Iman kamar ta saka kuka ta ce "In yi masa me?"

"Iman me yake damunki ne? Ban gane ki yi masa me ba? Ki je ki ji mana"

A daƙile ta ce "To, zan je" Nusaiba ta juya ta fita.

Rumaisa ta ce "Kar ki damu, in sha Allah babu abun da zai faru sai ikon Allah, wannan masifaffiyar babar ta sa ma, na san ba zata bari ba".

Rumaisa na cikin maganar, laila ta shigo, ta kalli iman ta ce "Iman, jabir fa yana jira" ta ƙarasa maganar tare da zama a kusa da rumaisa, ruma tana satar kallon fatar laila, kamar jikin tarwaɗa, gashi ko kunya ba ta ji, take tsukewa a cikin ƙananan kaya.

Iman kamar ta zubar da hawaye, haka ta tashi ta bar ɗakin.

Laila ta kalli ruma ta ce "Kina ji na ko?" Rumaisa ta ji kamar ta ce mata 'Da ni kurma ce?"

Amma a zahiri ta ce "Eh"

"Tun da yau mijinki ya tafi, dama ya bar sallahun kai ki makarantar matan aure, gobe in Allah ya kaimu za a fara kai ki, daga nan zaki kwaso kayanki na gidanki ki dawo nan. Ni na karɓi ragamar kula masa da ke kafin ya dawo, dan haka dole zaki din ga bin duk abun da na saka ki, bana son gardama ko rashin kunya, dan idan rashin kunya ce, sai dai ki koya a wurina. Idan kin dawo daga makaranta, zan din ga yi lesson da kaina, da kuma dabarun zaman aure.

Abu na gaba, zamu din ga gyaran jiki, naga kina da tsabta, kuma kin iya girki ma, amma dole zamu din ga shiga kitchen tare ki koyi wasu abubuwan.

Wannan fatar taki, so nake ta murje ta fi haka haske da kyau".

"Taɓ wallahi ba zan bleaching ba".

"Ni ma ba bleaching na ce ki yi ba, gyara za ayi, wannan gashin ma, ya ce ba kya son kitso, dole ya din ga shan gyara, ga iman nan, ita zata ja ragamar koya miki makeup"

"Ni gaskiya idan na yi wannan damɓare-damɓaren, fuskata ƙaiƙayi take yi, duk in ji ta ɗaure kamar ta tsohuwa".

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull