Kenza eBookz

Kanwar maza 3 Complete - Chapter 57

Kanwar maza 3 Complete - Chapter 57

Kanwar maza 3 Complete Chapter 57: Kanwar maza 3 Complete Chapter 57. A hankali take sassauta kukan, ta ce "Yaya Umar, na gode da ka bani dama ka ji abun…

235 words

A hankali take sassauta kukan, ta ce "Yaya Umar, na gode da ka bani dama ka ji abun da yake damuna, na gode sosai"

"Don't mentioned, ki ci abinci ki kwanta ki yi baccinki, ki cigaba da addu'a, ba abun da zai faru sai ikon Allah khadija" shi kansa mamakin yadda ya tausasa murya sosai yake, bai taɓa zaton ya iya rarrashi haka ba.

Rumaisa kuwa Mahmud ta kira a wayar Anty laila, ta ce tana son ganinsa a in da suke haɗuwa.

Babu jimawa kuwa suka haɗu, sai dai cikin tsananin fushi ruma ta ce "Daddy anya mummy na son taga Annabi kuwa, daga ita har babar jabir fuska kamar an mari biri? Ya za ayi ta zo ta ce ba zata bari ɗanta ya auri Iman ba, ammi ta ce a fasa a janye, ta ce ita ƙarya aka yi mata ba ta faɗa ba?

Ammi sai kuka take yi, har da masu kiranta a waya, ana bata kyauta ba, ta hana jabir iman, gashi wambai ya ce idan ba ta aurar da iman ba ta mayar da ita in da ta tsinto ta, wai ya suke so baiwar Allah nan tayi ne, daga ita har Iman ɗin sai koke-koke suke yi, wai kai ba abun da zaka iya yi a kai? To ni zan je wurin wamban sai na tonawa kowa asiri da kaina, ayi wadda za ayi ta ƙare!

Ayshercool. 08081012143

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull