Kenza eBookz

Kanwar maza Book 3 and 4 Complete - Chapter 22

Kanwar maza Book 3 and 4 Complete - Chapter 22

Kanwar maza Book 3 and 4 Complete Chapter 22: Kanwar maza Book 3 and 4 Complete Chapter 22. Security light duk ta haske ko ina a gidan.

3,351 words

Security light duk ta haske ko ina a gidan.

Ba ta san in da zasu tafi ba, ita dai ta ga suna tafiya.

Sai da suka je gidan, ta gane gidansu Adam suka je.

Ammi na ganin rumaisa ta rungumeta tana murna, ta ce "Takawa, baka bari ta gama hutawa ba ka fito da ita"

"Ta isheni da koke-koke, shiyasa na kawo ta"

Ammi ta ce "Haba rumaisa, kukan bai isa haka ba, ai yakamta ki kwantar da hankalinki haka" Rumaisa ta sunkuyar da kai, ba ta ce komai ba.

Nusaiba na ganin rumaisa ta fara murmushi "Amarya ba kya laifi, yau da kanki"

Rumaisa ta ce "Shi ne baku kuma zuwa ba da ke da Iman".

"Yaya ne ya ce kar mu sake zuwa ai"

"To ni kaɗai nake zama a gidan fa, kuma shi ba kulani yake yi ba, sai dai in wuni ina kuka"

Ammi ta kalli Adam, ya sunkuyar da kai, ta kalli rumaisa ta ce "Haba Yarinyar kirki, zai din ga kulaki kukan da ki ke yi ne baya so, gobe in Allah ya kaimu za'a baki hadimai mutum biyu, da zasu din ga yi miki aiki, sa din ga ɗebe miki kewa, abun da ma kin kusa komawa makaranta, wani satin za a koma makaranta".

Ammi ta yi maganar baba uwani ta fito, ɗauke da Sabir a hannunta.

Murmushi rumaisa ta yi ganin sabir, Adam ya karɓe shi, Baba uwani ta ce "Amaryarmu, sannu da zuwa ya gida, bamu san da zuwanku ba ai da an sheƙa girki na mussaman"

Rumaisa ta ce "Mata ina wuni"

Baba uwani ta ce "Tuba nake, ai ni yakamata na kwashi gaisuwa"

Sabir kuwa rumaisa ya din ga miƙawa hannu. Adam ya ce "Kai, kwana huɗu baka ganni ba, amma baka ta tawa, Mimi zo ki ɗauke shi"

Waiwayawa ta kuma yi, taga da wa yake, sai kuma ta tuna abun da ya ce washegarin kai ta.

Ta tashi ta je ɗaukar Sabir, yayi ƙasa da muryarsa ya ce "For the second time, idan na ce mimi da ke nake, ba zan so Sabir ya tashi ya ji ina faɗar sunanki ba" ta jinjina masa kai, ta karɓi Sabir.

Ta kalli Ammi ta ce "Ammi, sai a haɗo mini kayansa, na tafi da shi ko?"

Ammi ta ce "A'a, ke da zaki koma school, za'a din ga kawo shi, juma'a da yamma, sai a ɗauko shi ranar lahadi, saboda ki samu ki yi karatunki a nutse, sannan bayan hadimai biyun nan, baba uwani za ta zauna da ku, saboda ta saka ido a kan yadda zasu din ga gudanar da aiki a gidan, idan komai ya daidaita sai ta dawo, saboda ita ce amintacciyar hadimata".

Babu tsammani rumaisa ta ji gabanta ya faɗi, ba ta son baba uwani, kamar ma tsoronta take ji!.

Ayshercool 08081012143 *Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*

Rumaisa kasa cewa komai ta yi sai jinjinawa ammi kai, baba uwani kuwa har da shewa tana juyi, tana yi wa ammi godiya da karamcin da ta yi mata, a matsayin wadda za ta je ta yi guiding ɗin ma'aikatan gidan takawa.

Ammi ta yi wa Adam alamar ya bi ta, ya tashi ya bi bayanta ɗakinta, ta kalleshi ta ce "Takawa, na san auren nan ba son ka bane, zaɓina ne amma dan Allah ina sake roƙon alfarmarka, ka yi haƙuri da yarinyar nan, komai zai wuce zaka yi alfahari da auren nan, ka ga yarinya ce ƙarama, dole za ta yi ta koke-koke na rabata da gida da ka yi, dan Allah ka yi haƙuri da ita. Ko dai wani abun ka yi mata?"

Ware ido ya yi ya ce "Ba abun da na yi mata wallahi".

"A'a takawa, dan Allah ayi haƙuri a bata lokaci, yarinya ce sosai sai ka yi haƙuri"

Adam wata irin kunya ce ta kama shi, ya ji tamkar ƙasa ta tsage ya nutse don kunya, ya girgiza kai ya ce "Ban yi mata komai ba"

"Na ji ba wai ina son jin sirrin aurenku ba ne, amma dan Allah ka kula da ita, next week idan Allah ya kai mu za a koma makaranta ko?"

Ya ce "Eh, na biya komai ma, ana komawa zan kaita sai kuma na samo direban da zai din ga ɗaukota idan bana nan"

Ammi ta ce "To shikenan, Allah ya ƙara buɗi"

Suka fito, Ammi ta ce a zubawa su takawa abinci su tafi da shi.

Ammi dai ta lura gaba ɗaya jikin rumaisa a sanyaye yake, har ta fara tunanin ko takawa dai yayi mata wani abun ne.

Ammi ta zauna a kusa da ita, ta yi ƙasa da muryarta ta ce "Rumaisa, ko akwai wata matsala ne?"

Ruma ta girgiza kai alamar a'a.

"To ki yi haƙuri kin ji, zaki saba ne haka aure yake, ki yi haƙuri, duk abun da yayi miki wanda bai yi miki ba ki gaya mini. Sannan su nusaiba sun gaya mini abun da ya faru washegarin kai ki, shi ma ki yi haƙuri ki kawar da kanki, na san zaki fuskanci ƙalubale, amma ki dake. Kar ki yadda da duk wata mata da zata nuna tafi kowa ƙaunarki ko ta shiga jikinki, kuma kar ki sake ki gaya wa wani sirrin aurenki, duk abun da zai yi miki, ba zai yi wanda zai cutar da ke ba, na ja masa kunne sosai da sosai, idan yayi miki abun da ba dai-dai ba, ki gaya mini. Kar ki saki jiki da kowa, sai mijinki ko kuma ni da ƙannensa zama a masaruta sai ka iya allonka, ki yi haƙuri kin ji rumaisana".

Ruma ta ce "To Ammi, in sha Allah "

Har gaban mota ammin ta rakasu, suka shiga suka tafi.

Tun kan su yi nisa ta fara sana'arta ta barcci, ya taɓata ya ce "Idan ki ka yi bacci, sai dai ki kwana a mota, dan ba ɗaukar ki zan yi ba" da haka suka ƙarasa gida ta yi sallar isha'i, ko abincin ba ta ci ba ta kwanta.

Washegari da safe, ta tashi tana ɗan goge gogenta, ta fito falo tana ta goge tiles ɗin.

Adam ya fito cikin suits da jakarsa, da alama aiki zai tafi, ta yi masa ƙuri da ido, ba ta yi magana ba.

"Baki iya gaisuwa bane?"

Ta ɗauke kanta daga kallonsa ta ce "Ba amsawa ka ke yi ba"

"Yes, ba kya gaisheni yadda ya dace ne, ki bar wannan aikin babu wanda ya saka ki, anjima masu aikin da ammi ta ce za su zo, idan da wani abu su gyara miki. Ga breakfast can a kan dining, in anjima zasu fara aiki, zan sayo kayan abinci, ko kina buƙatar wani abu?"

Ta girgiza masa kai alamar a'a.

"To ki zauna wuri ɗaya, banda taɓe-taɓen abun da ban saka ki ba".

"To sai yaushe zaka dawo?".

"Lokacin da Allah ya yi".

"Ni dai ka dawo da wuri, tsoro nake ji"

*** Gidansu rumaisa kuwa, mama ce ta hana kowa zuwa gidan, saboda ta san halin rumaisa, ta ce idan suka je kuka za ta yi ta ce zata biyosu. Sai dai ba a cikakken awa guda, ba ayi zancenta ba a gidan.

Kasancewar bayan mai hoton da ɓangaren su Adam suka ɗauko, Abdallah ma ya ɗauko mai hoto, aka turo masa hotunan bikin rumaisa, bai yi ƙasa a gwiwa ba, ya tura su group ɗin su, na ƴan gidan.

Mai sunan baba yana kasuwa, da yake bayan makaranta ya kan ɗan shiga kasuwa, hotunan suka shigo. Suna da yawa ya sauke su, ya fara buɗewa yana kallo, yana kallo yana murmushi yana jin yadda ya yi kewar ƙanwarsa. Babu tsammani ya ci karo da hotonsa shi da iman, rumaisa kuma a gefensu, ya wuce hoton da sauri, amma ya kuma karo da hoton iman ɗin, na ranar bridal shower, ta yi wani irin kyau na musamman. Zuciyarsa ta tsananta bugawa, kuma ya kasa wuce hoton nata, ba shiri ya rufe wayar, ya saka a aljihunsa yana ajiyar zuciya, kamar wanda ya yi gudu.

*** "Wallahi Adam na yi mamaki da har ka iya ɓoye mini al'amari mai girma kamar wannan, menene a ciki idan na san wannan yarinyar zaka aura" Jabir yayi maganar cike da ƙorafi.

Adam ya ce "Koma menene bai kamata ka ji haushi ba, yanzu ba gashi ka ji ba, ko da yake gara kai a kan Jamil, ni Jamil zai ɗauki gaba da ni, yaƙi zuwa wurin ɗaurin aurena, ni na karɓi ƙaddarata dan meyasa shi ba zai ɗauka ba".

Jabir ya ce "A'a takawa, so so ne fa, amma son kai ya fi, Samha ƙanwarmu ce ga ta gida, amma ace ka auro wata a waje, wadda ba ta kaita komai ba, babu daɗi".

"Amma har ya kai ayi gaba da ni saboda hakan? Meye aibun rumaisa idan aka kamanta shi da abun da ta yi mini na sadaukarwa, bai kamata gaba ɗayanmu idonmu ya rufe ba, idan akwai rabo a gaba sai ka ga na aureta, amma a yanzu ban zaci haka daga Jamil ba, amma zan shiga wurin aiki, zamu haɗu da shi mu yi magana"

Jabir ya ce "To shikenan, har ka gama amarcin kenan ka fito, bai yi wuri ba komawarka aiki ba kuwa?"

Adam ya yi murmushi ya ce "Bai yi ba, ita ma sai a bar ta ta huta. Kai ni har mamaki nake yi yadda kai ba a saka maka ido ba, ko auren fari ba ka yi ba, amma ba ruwan wani da kai, duk mu aka sanya wa ido"

Jabir ya yi dariya ya ce "Bayan ka ce ba zaka bani iman ba, ai ni na zaci kai zaka aureta"

Adam ya ɗan ɓata fuska ya ce "Please mu bar wannan zancen"

Jabir ya ce "Shikenan, tun da baka so"

*** Rumaisa ta rasa abun da yake yi mata daɗi, zaman shirun nan duk ya isheta.

Ta saman benen take kallon harabar gidan, da gidajen da ke maƙwabtaka da nata, duk manyan gidaje ne, sannan kowane gida a rufe yake, ko gilmawar mutane ba ka gani, sai dai a cikin mota.

Mai gadin ta ga ya tashi ya buɗe gate, nan da nan ta fara murna ta yi baƙi.

Ta koma ɗakinta da sauri, ta saka hula a kanta, ta fito, sai dai ta yi turus lokacin da ta ga baba uwani, da wasu matasan mata guda biyu.

Jiki a sanyaye ta ce musu "Ina wuni?"

Baba uwani ta yi murmushi ta ce "Ranki ya daɗe ai mu zamu gaisheki, barka da wannan lokaci? Mun same ki lafiya?"

"Lafiya ƙalau" ta amsa a ɗan tsorace.

"To kamar yadda giwa ta yi miki bayani jiya, ga ma'aikatanki nan, sannan kuma ni ce cikon ta ukun, zamu zauna tare da su a nan, na din ga lura da yadda zasu gudanar da aikin".

Rumaisa ta ce "To sannunku".

Baba uwani ta ce "Yauwwa, wani ɗakin zamu zauna, da kayanmu muka zo".

"Ku zaɓi duk wanda ku ke so" rumaisa ta yi maganar tana kallonsu.

Ta nemi wuri ta zauna a falo, baba uwani ta zaƙe ta fara dudduba ɗakunan da suke saman benen.

Ta shiga ɗakin rumaisa, ta ƙare masa kallo, ta fito tana faɗin "Allah ya taimake ki, ashe an shirya miki kayan, ko takawan ne ya shirya miki su?"

Rumaisa ta ce "A'a ni na yi"

"Masha Allah, to bari ɗauki wancan ɗakin, tun da na ga ɗayan kamar babu kowa a ciki"

Ita dai rumaisa ba ta ce komai ba, ta ƙare ta shiga kitchen tana dudduba kayan kitchen ɗin Rumaisa.

Ganin sun isheta da kallo, sauran mata biyun da ko sunayensu ba ta sani ba, ya sanya ta tashi ta koma ɗakinta.

Ta buɗe window ta cigaba da kalle-kallenta, ta hango baba uwani a bayan gidan, tana waya. Ba ta jin mai baba uwani take cewa, sai dai da alama kamar wayar ta ta ta sirri ce.

Baba uwani kuwa cikin ladabi take waya da Samha.

"Ki buɗe kunnenki da kyau ki saurareni, bana son a samu kowane irin akasi a kan aikin nan, ki zuba mini ido sosai, duk abun da yake faruwa ki din ga sanar da ni, ina fatan kin gane?"

"Na gane ranki ya daɗe, duk abun da ki ka ce in Allah ya yarda zan yi, zan zuba ido sosai da sosai"

Samha ta ce "Yayi kyau".

Da la'asar Adam ya dawo, rumaisa ma sam ba ta san ya dawo ba, saboda wunin ɗaki ta yi, ko haɗa hanya ba ta son yi da baba uwani.

Gyaran murya ya yi, hakan ya sa ta waiwaya ta ganshi a tsaye.

Ya shiga ɗakin ya ce "Me ki ke yi ke kaɗai a ɗaki?".

"Bakomai"

"Ke ki ka ce wa baba uwani su zauna a ɗakin saman nan?"

Ta jinjina masa kai alamar eh.

Ya ce "To na ce su koma ƙasa, ba haka ake yi ba. Ga kayan abinci can na sayo, na zuba a kitchen ɗin ƙasa, zasu din ga girki suna kawo mana, sannan zasu din ga yin duk wani aiki na gidan nan, banda gyaran ɗakina, ke zaki din ga wannan ai kin iya ko?" Ta jinjina masa kai.

"Bana son body language, amsa mini zaki yi"

"Eh na iya".

"Good, ki fito zan nuna miki abu".

Ta tashi ta bishi, zuwa kitchen ɗin saman benen.

Ya nuna mata kayan tea, manyan gwangwanayen madara da na milo, kayan biscuit na ciye-ciye da sauransu. Sai cartons na lemuka, da kayan marmari ya ce "Gashi nan, wanda zaki kai ɗaki ki kai, wanda za su saka miki a fridge kuma sai ki nuna musu".

"To an gode" ta faɗa a sanyaye.

Gani yake yi kamar an sauya rumaisa, duk wannan tsabar rashin jin da tsaurin ido, duk ta yi sanyi, sai dai a ransa ya ce ba a yabon ɗan kuturu.

Kasancewar tun a yau su baba uwani suka fara gudanar da ayyukansu, sun yi abincin dare, suka kai wa su rumaisa sama.

Ruma ko kallon abincin ba ta yi ba, ta din ga cin kayan marmari, sai da ta ji ta ƙoshi. Ta haɗa madara da milo, fal a kofi ta tafi da shi ɗaki, ta din ga sha ta gaji ta ajiye sauran ta yi bacci.

Ba ta san ma Adam ya dawo ba, sai da asuba ta ji yana babbuga mata gefen gado ta tashi ta yi sallar asuba.

Ta buɗe ido ta kalleshi ya ce "Ke ba kya iya tashi salla dole sai an tasheki ne? Kuma haka ki ke kwana da fitila a kunne?"

Ba ta ce komai ba shi kuma ya fice. bayan ta yi sallar, ta ɗan yi baccin safe ta tashi, ta shiga banɗakinta, yanzu duk ta san yadda ake amfani da kayan toilet ɗin, da idan za ta yi alwala, sai ta kunna hot water ta fara, tana tsaka da yi, ta ji ruwan zafi yana ƙona ta, yanzu kuwa duk ta gane kansu.

Wankanta ta yi a nutse, ta fito tana goge jikinta da ruwa, ta tsaya a gaban mudubi tana kallon kanta.

Baba uwani ta yi sallama, da kayan mopping a hannunta.

Rumaisa ta razana tana neman hijjabi ta saka, kasancewar daga ita sai towel.

Baba uwani ta ce "Haba ranki ya daɗe, ai na haifeki, meye na damuwa kuma, gyara miki ɗakin zan yi".

Rumaisa ta girgiza kai ta ce "Ki bar shi kawai zan gyara da kaina, kaya zan saka".

"Ki saka kayanki kawai, aikina zan yi".

A ɗan hasale rumaisa ta ce "Ki bar shi kaya zan saka".

Ta kalli rumaisa, ba wata uwa a jikin nata sai tsirfa. Ta juya sumi-sumi ta bar ɗakin.

Guntun tsaki rumaisa ta ja ta ce "Wannan mata meye damuwarta ne? Bana son shishshigi", rumaisa ta saba yawonta a gidansu, babu suturar kirki ba ta damu ba, amma ba ta yadda wani na waje ya ganta ba. A gaggauce ta saka kayan, tana son ta yi magana da adam Kafin ya fita.

A falo ta tarar da adam yana danna system, babu alamar zai fita yau.

"Ina kwana" ta faɗa ba dan ta na tsammanin ya amsa ba, aikuwa bai amsa ɗin ba.

Ta ɗora da cewar "Dama, tambayarka zan yi, yau tun da juma'a zaka ɗauko mini Sabir ɗin, ammi ta ce za a din ga kawo shi, juma'a zuwa ranar lahadi, sannan dan Allah ka kira mini yaya Aliyu a waya, dan Allah su zo".

Ya kalleta ya ce "Da ni ki ke ko da system ɗi na, ko akwai wani bayan ni a nan?" kallonsa ta yi da mamakin rainin hankalin da ya yi mata ta ce "Da kai nake mana".

"Bani da suna ne ko yaya?"

Rumaisa ta ce "Ka na da shi".

"Ok, ya sunana?" Yayi maganar yana tsareta da ido.

Har ta buɗe baki za ta ce Adam, sai ta ji sunan yayi mata nauyi a bakinta, gashi ya tsareta da ido, yayi mata kwarjini sosai.

"Papa" ta faɗa a hankali.

Adam ya ce "Waye hakan?"

"Saboda Sabir, na ji ya fara koyar faɗan sunanka"

Ɗan rausayar da kai ya yi, a ransa ya ce "Ashe kina da hankali wasu lokutan '.

A zahiri kuma ya ce "Me ki ka yi wa baba uwani, na ga ta fito daga ɗakinki, kamar ranta a ɓace?".

Ta ɗan tura baki ta ce "Ba abun da na yi mata"

"Bana son ƙarya"

"Ba ƙarya nake ba, zuwa ta yi wai za ta gyara mini ɗaki, ni kuma daga wanka na fito ban saka kaya ba, kawai cewa na yi ta bar shi zan gyara da kaina shikenan fa"

"Ba ta haifeki ba, me za ta gani?"

Da sauri ta kalleshi ta ce "Taɓ, ni wallahi ba zata ganni ba".

"To me za ta gani?" Shiru ta yi ba ta bashi amsa ba.

Ya girgiza kai ya ce "Kasancewar ta na yi miki aiki, ba ya na nufin ki rainata bane, ita ce babbar hadimar ammi, muma muna girmamata. Ga abinci can sun girka, ki je ki karya".

"Na ƙoshi" ta faɗa cikin jin haushi, dan ita ba ta ga abun da ta yi wa baba uwani ba.

"Kin ƙoshi saboda me?"

"Ni so nake na din ga girka abincina da kaina, ammi ta ce kar na yarda da kowa, kar na je ayi mini aisiri a cikin abincin"

Tattara hankalinsa ya yi a kan rumaisa sanannan ya ce "Waye zai yi miki asirin?"

Ta ce "An ce a gidan sarauta ana asiri, dan haka ni ba zan ci wannan abincin ba".

"Ai dama me hali baya fasa halinsa, kin huta, sai dai idan ba zaki ci abinci a gidan nan ba, idan ki ka sake na ganki a kitchen da sunan zaki yi girki, sai na saɓa miki, ba zaki haɗa mini gobara a gida ba, kuma ki cigaba da ina magana ki na yi mini gatsali, zaki ga yadda zamu yi da ke"

Ya mayar da hankali a kan system ɗin sa.

Jin sa kawai take yi, amma ta yi wa kanta alƙawarin ba za ta ci abincin nan ba.

Ya tashi ya shiga ɗakin sa, ya fito da mukullin motarsa, ya fice ba tare da ko kulata ya yi ba.

Yana fita ta sauka ƙasan benen, ta tarar da su baba uwani suna aikace-aikace.

Tana ganin rumaisa ta saki fuska tana faɗin "Uwar ɗakina, sannu da fitowa, kina buƙatar wani abun ne?"

Rumaisa a ran ta ta ce, ji matar nan kamar ba yanzu ya ce ta fito ranta a ɓace ba.

"Bakomai, Takawa ne ya ce mini, kin fita daga ɗakina ranki a ɓace, kamar baki ji daɗin abun da na yi miki ba, ki yi haƙuri dan Allah. Sannan zan din ga yin aikin saman, zan din ga gyara komai".

Baba uwani ta ce "A'a ba haushi na ji ba uwar ɗakina, ai zamanki muke yi, kar ki damu dolenmu mu gyara miki, ai ke hutuwarki kawai zaki din ga yi"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull