Kanwar maza Book 3 and 4 Complete - Chapter 35
Kanwar maza Book 3 and 4 Complete Chapter 35: Kanwar maza Book 3 and 4 Complete Chapter 35. "In gaya maka har malamin ya kirani gaban allo, zai yi…
3,367 words
"In gaya maka har malamin ya kirani gaban allo, zai yi disgracing ɗina, ya ɗaga littafin ƴan ajin suna dariya, ya tambayeni da turanci wai meye wannan? Ni kuwa na ce ni ban iya ƙirƙirar komai ba, amma idan malamai suka yi kyau kamar zanen nan nawa, to za a samu ɗalibai masu ƙoƙari da tsara zane kamar nawa, koma fiye da nawa, Aikuwa aka dinga tafa mini,ya ka ji azancin nawa"
Ɗan murmushi gefen baki ya yi, dan ya fuskanci ita fa dan kana fushi da ita, kai ta shafa.
Ya ce "You try".
"Yauwwa, sai ka saya mini kyauta, teddy bear nake so, da kuma ƴar tsana babba, sai lunch box ɗina"
Yayi mata kallon ba zaki girma ba.
"Ya naga kana kallona?"
"Mahmud, Alaƙarki da shi bana so, kar ki kai ni bango a kan haka".
"Wai meyasa zaka saka ni a cikin faɗa ku? Ni meye nawa yana yi mini kirki, shikenan dan kuna faɗa nima sai na din ga jin haushin sa. Jamil, Jabir, Samha alaƙar ka da su bana so, Jamil da Samha, sun wahalarsa da matarka, su meyasa ba ka gaba da su?" Ta yi maganar tana tsare shi da ido.
Rasa bakin magana yayi, duk yadda kake tunanin rumaisa ta wuce nan, a zahiri tana da ƙuruciya da wauta, but she have a very sharp brain, ba shi da amsar bata a yanzu dan ta ƙure shi. Amma saboda kar ta ga ta yi nasara ya ce "Ni ne shugaba, a gaba nake da ke, dan haka duk hukuncin da na yanke dole ki bi".
Ta ɗau littafinta ta ce "Babu biyayya ga abokin halitta wurin saɓawa mahalicci, duk daƙiƙancina a makaranta, na san wannan, kuma Allah ya yanke rahamarsa ga mai yanke zumunta, Annabi ma ba ya tare da mai yanke zumunci, sai ka din ga jin tsoron Allah wurin yanke jiki kai ma" ta fice ta koma falo ta bar masa ɗakin.
Mintuna kaɗan ya fito ya fice daga gidan gaba ɗaya, ya dafe kanta ta ce "Na shiga uku wannan wane irin abu ne, anya kuwa zan iya, ni duk na gaji" tayi tsaki, ta tashi ta je ta ciko roba da gugguru, ta ɗaukko lemo, ta zo ta saka a gaba tana ci, tana kallon cartoon.
Hayaniya ta ji ana hawowa sama, ta tsaya tana jiran taga waye zai shigo?
Samha ce da Fauziyya, da kuma ruƙayya sai zee ƙanwar Samha, baba uwani biye da su, hannunta riƙe da foodflask.
Babu ko sallama suka zo suka zazzauna, baba uwani ta ajiye kwanukan, ta ja gefe.
Samha ta kalli rumaisa ta ce "An samu duniyar da babu a gidan tsoho, an yi ɗai-ɗai a katafaren gida, da duk dangi babu irinsa" rumaisa ta yi mata banza, ya cigaba da kora lemonta.
Ruƙayya ta ce "Allah wadaran naka ya lalace haryanzu ban ga technology a auren wannan busashiyar yarinyar ba, da ko rantsuwa na yi babu kaffara, ragowar masu garkuwa da mutane ce, sun gama lalata ta" ɗan shiru ruma ta yi tana tunanin, me take nufi.
Fauziyya ta ce "Ba wani technology, wulaƙanci ne kawai, dan Allah dubi Samha ki dubeta, ita ta isa ta kira kanta mace ma wallahi wannan ko a mai aikin samha ba ta isa ta zo ba, kalli bakin shegiya yadda take auna madara, saboda samun wuri, ga ƙirjinta fayau kamar faifai ba wata mamora, amma wai ita ya aura".
Rumaisa ta yi gyatsa ta ce "Gidan miji daɗi, mussman irin gidan papa, auren mai kuɗi daɗi ba, na samu promotion, gida babu, na samu a gidan miji" tayi maganar tana lashe madarar hannunta.
Fauziyya ta ce "Ke dalla rufewa mutane baki, tashi ki kira mana ɗan uwanmu, mun zo duba shi"
Cikin tsawa rumaisa ta ce"Ba zan kirawo shi ɗin ba tun da ke ba uwata ba ce"
Samha ta ce "Ke, uban wa ki ke yi wa tsawa".
"Uban duk wanda ya tsargu, ba sunana Aisha ba, sunana rumaisa Mahmud, ƙanwar maza, ku tambayi yayan naku wace ni, kawai ku zo ku cika mini kunne, wai ko a ƴar aiki ba zan zo ba, ai Allhan ba naku ne ku kaɗai ba, da ban zo a ƴar aikin ba, sai na zo a matar gida, antynku ce ni, tun da matar yayanku ce ni, ke kuma da ki ke cewa ke ce mace, na ji ni namiji ce, ni duk wadda ta yi mini, wallahi sai ta ci ubanta, babu wata barazana da tashin hankali da ban gani ba, dan haka ba zaku ɗaga mini hankali ba, ke kuma da ki ke cikakkiyar macen, kin san idan ki ka gama cikar, zubewa zaki yi ki fara tsufa, kin ga ni kuma a lokacin da ki ka fara tsufa na cika ko? Banza kawai"
"Ke! Kina ƴar matsiyata ni ki ke gayawa haka? Kina da hankali kuwa, waye ubanki a ƙasar nan, har ni ki ke cewa ubana zaki ci?"
"Eh na faɗa, sai na ci ubanki, da ke da duk wanda ya ce zai zageni, ƴan fashin daji ma, ba su razana ni ba, balle ku shashashai, gwalagwaje, marasa mutunci, idan tunaninku gayya, ku taron mata ne, ni kaɗai dai-dai nake da tunanin maza bakwai".
Ayshercool. Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012243, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Susbcribe my YouTube channel please 🙏
Ruƙayya ta riƙe haɓa ta ce "Kan uban nan, wannan wace irin yarinya ce, mara tarbiyya Binta ta aurawa ɗan ta?"
Jin maganar rumaisa ta yi wani iri, yadda ruƙayya ta ambaci sunan Ammi haka kai tsaye kamar sa'arta.
Zee ta ce "Ni wallahi da na san irin wannan abun zamu tarar, da ban zo ba, kawai kun zo kuna zubar mana da mutunci a gaban wannan ƴar yarinyar".
Ruma ta ce "Oho dai, in ma ƴar cikinki ce ku ta shafa, aka gaya mini cuta sai na faɗi mutuwa, haka kurum tiƙa-tiƙa da ku, ku zo kuna ci mini mutunci. Wai wani kun zo wurin ɗan uwanku, yo koma menene, duk ƴan uwantakar ta ku, tun da dai ni ta ajiye mussaman yake bani abinci, yake kula da ni, yafi so na"
Samha da takaici ya ƙule, ta miƙe a hasale, tana yinƙurin ta ƙarasa ta tsinke rumaisa da mari. Fauziyya ta riƙe ta, ta ce "Ba girmanki ba ne".
"Ki cikani Fauziyya, in zuba mata da haƙora na daki banza, dan ubanta"
Rumaisa ta ce "Taɓ ki dakeni ki ga yadda ake ƙaramin yaƙi, wallahi sai yayyena sun yi miki bugun sakwara, bar ganin kin fini girma, ni da maza ma dambe nake ba ruwana da girmanki".
Jin hayaniya ya sanya baba uwani hawowa saman, ta zo ta iskae rumaisa tana ta zazzaga musu rashin mutunci.
Baba uwani ta ce "Haba ke kuwa, baƙinki ne fa, ƴan uwan mijinki, ya zaki din ga yi musu wulaƙanci haka, ai ba haka ki ke yi wa ƴan uwanki idan sun zo ba, kuma ba sa'anninki bane "
"Baki san meyafaru ba, dan haka ba ruwanki da ni".
Baba uwani ta dafe ƙirji ta ce "Ni ki ke gaya wa haka?"
Rumaisa ta dubi dattijantar baba uwani, ta haɗiye abun da ta yi niyyar faɗa ta ce "Ba ruwanki da abun da na yi, idan ban saka ki a ciki ba, tun da baki san farkon abun ba, kuma kina goyon bayansu"
Ta ɗauki kofinta, ta nufi ɗakinta, tare da ce musu "Mahukatan banza kawai"
Tun da ta shige ɗakinta, ba ta sake fitowa ba, tayi zamanta tana zane-zane, har aka yi sallar magariba, sannan ta tashi ta yi alwala ta yi salla.
Ta idar da salla kenan, ta jiyo takawa yana kwaɗa mata kira, yamutsa fuska ta yi, dan ya tsorata ta.
Fita tayi, ta tsaya ta kalli falonta, an ci abinci an ɓata falon gaba ɗaya, har da fasa mata wasu daga cikin farantai.
Kasa magana ta yi, a fusace ya kalleta ya ce "Meye wannan?"
"Oho" ta bashi amsa.
"Which kind of nonsense is this, ina yi miki magana?" Ya yi maganar a zafafe.
Nan da nan ita ma ranta ya ɓaci, "Amma dai ka san ni ba ƙazama ba ce, kuma ba ka taɓa ganin nayi irin wannan abun ba, yadda ka gani, nima yanzu nake gani".
"Wai ne ki ɗaukeni ne? Sa'anki or what, kina da hankali kuwa, kalli falon nan fa?"
Takaici ne ya ƙule rumaisa ta ce "Ni ba mahaukaciya ce ba, ƙannenka da wannan Samhar su ne mahaukata, dan su suka yi haka da falon ba ni ba, tun da dai baka taɓa gani na yi haka da gidan ba" ta juya ta nufi ɗakinta, ya taka da sauri ya janyota ya mayar da ita falon.
"Idan suka yi haka da wurin, ke ba zaki saka a gyara ba, ko ke ki gyara ba? Ba gidanki bane?"
"Taɓ, ni zan gyara musu, to wallahi ko kai ne ba zaka yi haka in gyara ba, kai da kake ciyar da ni, balle wasu ƙartin banza"
"Shut up! Ƙannen nawa ki ke cewa ƙartin banza? Ki kiyayeni, samo abun gyara ki gyara wurin nan, na baki mintuna biyar kawai. Ki gama ki zo ki gaya mini dalilin da ya sanya ki ke yi wa baba uwani rashin kunya"
Wani irin malolon baƙin ciki ya cunkushe mata zuciya, ba ta taɓa tunanin Adam yana da kwarjini, da kima a idanunta ba sai yau, da ta ji tamkar an ɗaure mata harshe, ta kasa bijire masa, wasu hawayen baƙin ciki suka cika mata ido, amma ta danne, ta zo ta fara aikin gyara wurin.
Ya nemi wuri ya zauna, ta gyara ta kammala, ba ta ce masa uffan ba, ta tafi ɗakinta.
Bayanta ya bi, ya tarar da ita a gaban mudubi, ta cika ta batse, ba wani abu take a gaban mudubin ba, kawai tana tsaye, tana sauke numfashi.
Tana ganinsa ya shigo, ta share shi ta cigaba da tsayuwa.
"Me baba uwani tayi miki da ki ka yi mata rashin kunya?"
Banza ta yi masa taƙi kula shi.
"Ina sake gargaɗinki, duk abun da zasu zo su yi, babu ruwanki da su, sannan idan ki ka kuskura ki ka kuma yi wa baba uwani rashin kunya, sai na ɓata miki rai, kawai kin saka tsohuwar mutane kuka, saboda ke baki san abun da ya dace ba?" Yayi maganar yana son ta yi magana, dan ya ji meya haɗa su da su Fauziyya, dan ya san idan ya tambaye ta, yadda ta ƙule ɗin nan, ba zata gaya masa ba.
"Wallahi duk wadda ta kuma zuwa ta zageni, sai na rama, kayi zuciya ka mayar da ni gidanmu, sai ka tattaro su su dawo gidan nan su zauna, gida zan tafi dan ni ba banza ba ce, da za su din ga zagina ina jin su ba, me na yi musu? Nima ƙanwar wasu ce, kuma suna sona, dan wallahi ko za su kasheni, suka zageni sai na rama, ita kuma baba uwani ta cigaba da yi mini sharri" ta yi maganar tare da shigewa toilet.
Har dare taƙi ko sake fitowa, dan ko abincin dare ba ta nema ba, ta yi kwanciyarta.
Sai da takawa ya nemi, Asiya da barira ya tambayesu abun da ya faru, amma suka ce ba su sani ba, baba Uwani ta hana su hawa saman, amma sun jiyo su Fauziyya suna zagin rumaisa tana ramawa.
Daga nan gidansu ya wuce, bai ko je sashin Ammi ba, ya nufi sashin Mummy.
Ya tarar da su gaba ɗayansu, har da Mahmud da Mummy, da ruƙayya da Fauziyya, sai dai babu Samha.
Mummy na ganinsa ta ce "Ahh, takawa barka da wannan lokaci, ƙaraso mana, ya jikin naka, tun da na shiga ban sake zuwa ba, ashe ka samu sauƙi".
Ya ce "Eh"
"Sabuwa, ƙaro plates, a zubawa takawa abinci shi ma".
Ya girgiza kai ya ce "Na gode, Fauziyya"
Ta kalleshi ta ce "Na'am yaya"
"Kun je gidana ɗazu?".
"Eh yaya mun je, zamu sake dubaka ne kuma baka nan, matarka ta yi mana rashin mutunci, har da zagin baba uwani".
Adam ya ce "Daga yanzu, idan har ba alkhairi ne zai kai ku gidana ba, kar ku sake zuwa, ina baku wannan saƙon ne har Samha, idan ma baku gaya mata ba, ni zan gaya mata. Kar ku sake zuwar mini gida ku ci mutuncin mata ta, ni na ajiyeta ba ita ta ajiye kanta ba, kuma ban aurota, dan ku je ku ci zarafinta ba, ita Aisha dama taku ce, kuma mai haƙuri ce. Wannan kuma tawa ce, sannan ba zata iya jure abun da Aisha ta jure ba, yarinya ce ba zan lamunci a saka mata tension depression ya kamata da ƙuruciyarta ba".
Baki a sake Mummy ta ce "Yanzu matarka ka fifita a kan ƙannenka, duk da sun gaya maka ta wulaƙanta su? Bayan kai suka je dubawa?".
"Mummy ko dabba na ajiye na ce nawa ne, bai kamata a je ci mutuncinsa ba, idan har ina da kima a idon su ba, balle ɗan adam na ajiye, idan banda rashin girma, me zai saka su biye mata, tun da ba sa'arsu ba ce ba, na san rigimammiya ce, amma ba ta yi haka kurum, ku kiyaye, aje a ci mata mutunci ace mata ƙwaila, ko ba mace ba ce, ni a idona mace ce kamar kowa. Dan haka Please allow her to enjoy her marital home. Ko ba ku yi zumunci da ita ba, ni na isheta, na san yadda nake bi da ita mu zauna lafiya"
Mummy ta yi murmushi ta ce "Hmm, wannan dai kashedin na samha ne, zuwa aka yi a gaya mana ana son ta kenan".
Ya tashi yayi murmushi ya ce "Ta cancanci hakan Mummy, a rashin Aisha ita ce uwar ɗana, idan na bari aka wulaƙanta ta, ni aka yi wa, dan haka a kiyaye"
Mummy ta yi shiru, tana saƙa wani abu a ranta, lallai akwai ƙura ba ƴar kaɗan ba, Samha tana ruwa, dan ba ta tunanin baba uwani na abun aka sakata yadda yakamata.
Mummy ta ce "Gaskiya ne, tayi rawar gani kam, ta cancanci a kula da ita. Duk da ka ɓoyewa duniya ita, da muhimmancin abun da tayi maka"
"Ni ta yi wa, ba duniya ba, dan haka ni yakamata na girmama abun da tayi mini".
Mahmud kuwa, ya kammala cin abincinsa, danna wayarsa kawai yake yi. Har Adam ya wuce shi, ya dawo ya zauna a kusa da shi, yayi ƙasa da muryarsa yadda shikaɗai zai ji me yake cewa ya ce "Am warning you, stay away from my family, da ɗana, da kuma matata"
Mahmud ya ɗan kalli Adam ya ce "Ban ji zan iya ko ɗaya ba, ina son ɗanka, ina girmama matarka, kasancewar tana girmamani, we are having a deal together, dan haka you should stay away from us"
Wani irin zafi maganganun sa, suka yi wa adam, amma ya shanye ya ce "Shikenan, idan ka ƙi ji, ba ka ƙi gani ba" ya tashi ya fice.
Mummy kasa zama tayi, ta tashi ta bar falon, Fauziyya kuma suka cigaba da caccakar rumaisa, suna bawa Mahmud labari.
Bayan ya bar sashin Mummy, ya je ya ga Sabir, Ammi ta yi masa ya jiki, tayi masa addu'a kamar yadda ta saba, sannan ya tashi ya tafi.
Kasancewar a cikin garin, gidan Jamil yake, ya sanya ya biya gidan Jamil, sai dai ya tarar baya nan.
Yau ya ji ƙwarin jikinsa sosai, dan haka ya shirya dan tafiya aiki, ya saba idan da makaranta, shida da rabi, rumaisa za ta zo gyara masa ɗaki, idak bai tashi ba ma, ta din ga ƙwale-ƙwale kenan sai ya tashi ko baya so. Amma har ya fito breakfast, ko alamunta bai gani ba.
Kai tsaye ya tafi ɗakinta, tana zaune dirshen da kayan bacci, ta cika akwatu da kayanta, tana zugewa.
"Ba zaki shirya tafiya makaranta ba ne?"
"Eh na daina zuwa, gidan matsiyatan iyayena zan koma, in cigaba da zuwa wadda na saba zuwa, sannan in cigaba da cin irin abincin da na saba ci, ba irin wanda nake ci a nan ba ake yi mini gori"
"Dalla tashi ki shirya zan makara"
"Sai kuma ka yi, ni za a din ga yi wa gori, saboda rashin adalci irin naka, da son kai, ka ɗora mini laifi, kai ƙannenka ba sa laifi, wallahi ko ta katanga sai na haura na koma gida" tayi maganar cikin tsan-tsar takaici.
"Na baki mintuna goma, ki yanke shawara, idan kin zaɓi mu rabu, abu ne mai sauƙi, amma ki sawa ranki, ba zaki sake ganin Sabir ba, har abada mintuna goma kawai gareki" saroro ta yi, ta bishi da kallo har ya fice.
Ko mintuna bakwai yi ba, sai gata cikin uniform, kamar zata fashe.
A ransa ya ce "Ni zaki yi wa zuciya, bayan na san lagonki?".
Suna tafe a hanya ya saya mata alawar madara, dan ya san tana son harkar madara.
Ta ce bata so, bai kulata ba ya ajiye a kusa da ita, suna zuwa ƙofar makaranta, ta buɗe ƙofar motar ta ɗau alawarta ta fice.
Yayi murmushi ya ce "Su mimi ba zuciya in dai a kan kwaɗayi ne" tana jin sa a ranta ta ce "So ka ke in kulaka, kuma ba zan kula ka ba".
Ana tashinsu ya je ya ɗaukkota, ya wuce da ita gidan Ammi, ya ajiyeta ya koma wurin aiki, tana jin daɗin hakan nan, saboda yana ɗebe mata kewa sosai, duk da su Iman na makaranta, ta yi ta hira da Ammi, tana wasa da Sabir.
Ammi ta ce "Rumaisa, ashe su Fauziyya ne suka je gidanki jiya?"
Rumaisa ta ce "Eh Ammi, sun je jiya da yamma"
"Ina fatan dai ba wata matsala"
Rumaisa ta ce "Eh Ammi babu komai, sun je duba shi baya nan"
Ammi ta yi murmushi tana dafa kafaɗar ruma ta ce "Ashe mutuniyar tawa tana girma, da har take iya ɓoye abu. Ban san dai meyafaru ba, amma na san ba zasu je su dawo haka ba, sai sun yi miki wani rashin albarkar. Babarsu ta zo ɗazu tana ta masifa, wai takawa ya je ya ci musu mutunci a kanki, kamar ba ƴan uwansa ba".
Rumaisa ta waro ido ta ce "Papan? Amma ni kuma jiya yayi mini wulaƙanci, suka ɓata ɗaki wai ni zan gyara".
Ammi ta ce "Ki yi haƙuri, ki cigaba da kula da kanki, ban da surutu a gaban wani"
"To Ammi in sha Allah"
Ammi kuwa daɗi ne ya kamata, ganin alamun soyayya a tsakanin rumaisa da takawa, yadda suka din ga turjiya kan ayi auren, ba ta tsammaci haka ba bayan auren.
"Yauwwa, Ammi dan Allah kira mini mama mu gaisa, ke da ita duk kun ƙi zuwa gidanmu".
Ammi ta ce "Bari na kirata, to me zamu zo mu yi muku, ku ba gashi kuna zuwar mana ba".
Ammi ta kira mata mama, ta bata wayar sannan ta tashi ta fita.
Mama na yin sallama ta ji muryar ruma, mama ta ce "Ahh babar sabir, ƴar gidan amminta"
Ruma ta ce "Mama na tabattar kin daina so na gaba ɗaya, baki taɓa zuwa gidana ba".
"Ai na san kina lafiya ne, ya ɗan naki ya maigidan?"
"Ɗana lafiya ƙalau, maigidan kuma mun yi faɗa bama magana"
Mama ta ce "Kun yi faɗa ba kwa magana saboda baki da hankali?"
Cikin sangarta ta ce "Mama faɗa yake yi mini a kan abun da ba laifina ba"
"Yi mini shiru, dan me ba zai yi miki faɗa ba, ya fita ya nemo ya kawo ki ci, ƴan uwanki sun ce mini baki nemi komai kin rasa ba, kuma dan yayi miki faɗa sai ki daina yi masa magana? Idan ma daina yi miki maganar yayi, ke ba zaki yi masa ba? Kin ga ki kiyayeni".
"To mama kawai sai na bashi haƙuri"
"Kar ki bashi, zan nemo masa wata matar mai ɗa'a, tun da ke ba kya ji"
Rumaisa ta ce "Mama ban gane ba, to wallahi ammi ta ce ba zai ƙara aure ba, daga ni shikenan".