Kanwar maza Book 3 and 4 Complete - Chapter 44
Kanwar maza Book 3 and 4 Complete Chapter 44: Kanwar maza Book 3 and 4 Complete Chapter 44. Abu kamar wasa a hankali mai sunan baba ya fara ɗan sakewa da…
3,370 words
Abu kamar wasa a hankali mai sunan baba ya fara ɗan sakewa da iman, da Allahn da yayi shi ba shi da yarda ko kaɗan. Duk safiya za ta yi message ta gaishe shi, daga nan kuma sai ya tamabayeta ya jiki, sai dai tana shan fama kan ta ɗan ja shi da hira. Sai dai ta fuskanci yana son tayi zancen karatu, mussaman na addini, hakan ya kan riƙe mata shi, gaba ɗaya mai sunan baba mu'amala da shi sai mai haƙurin gaske, miskili ne na bugawa a jarida.
Mai sunan baba yana lura da yadda Aliyu yake gudanar da tasa soyayyar, ba kunya yake soyewa da ƴar mitsitsiyar yarinyar da a baya yake zage gwanji ya kwaɗe Saboda rumaisa.
Komai ya siyo sai ya ce tun da ba ruma wannan na sweet hibba ne. Mai sunan baba ya fara tunanin yi wa iman kyauta, amma sai ya rasa ita da ke wannan gidan mai zai bata ma? Wani irin kallo ma za ta yi masa idan ya bata abu.
Unexpected ya ga Mahmud a online, suka gaisa mai sunan baba yake tambayarsa ya mai jiki?
Mahmud ya ce "Wace mai jikin?"
"Ƙanwarka mana, khadija" sai da Mahmud ya ɗan yi shiru sannan ya tuna sunan iman ne.
Ya ce "Ohh tana lafiya, ban ma san ba ta da lafiya ba ai".
Cikin mamaki yake tambayar sa ya aka yi bai san ba ta da lafiya ba.
Mahmud ya ce "Labarin dogo ne, amma ina da tabbacin jikinta da sauƙi, dan na ganta ɗazu tare da daughter na a garden".
Mai sunan baba ya ce "Ina so mu yi magana ne, ban taɓa shiga abun da ba ruwana ba a rayuwata, amma a wannan karon, ko sau ɗaya na ji ina son shiga, kuma ban ji zan iya maganar da kowa ba sai kai"
Mahmud ya ce "Ba damuwa, lallai na ciri tuta, bari mu yi maganar ta waya".
Mai sunan baba ya kira Mahmud da kansa, Mahmud ya ce "Ina shirin kiranka"
Ya ce "Bakomai, ni yakamata na kira dama. A kan Khadija ne, na je asibiti na duba ta, kamar yadda ta gaya mini tana da ciwon zuciya ne, amma kun san da wanda zaku aura mata ba ta son shi? And he is even mad gayen, ba shi da hankali gaba ɗaya, tayaya zai je yana mata shouting a ka a condition ɗin da take, ba tare da ya tausayawa halin da take ciki ba?. Yakamata ku ƙara bincikarta, kar zurfin cikinta ya sa ayi abun da zata cutu"
Ajiyar zuciya Mahmud yayi, shi kansa yana tausayin iman, kuma yayi dana sanin abun da ya yi wa ammi lokacin da ta roƙi ya auri iman. Yarinya ce nutsatsiya da ba ruwanta da hayaniya, ita ma ta tashi cikin tsantsar ƙalubalen rayuwa, a wannan gaɓar kan shi ma ya san za ta cutu idan ta auri jabir, dan ya fita baki, kuma ba kirki ya cika ba, ya ji ina ma zai iya yin wani abu a kan lamarin, dan jin kunnensa ya ji jabir ɗin na gayawa mummy, wambai ya san maganar, turaki zaa kaiwa kuɗin auren.
Bai gama tunanin ba ya ji muryar mai sunan baba ya ce "Ban taɓa neman alfarma ayi wa wani abu ba, a karon farko na roƙe ka, ko dan lafiyarta"
Mahmud ya ce "Kar ka damu, zan san abun da zan yi a kan lamarin in sha Allah".
"Masha Allah na gode sosai"
Mahmud yayi shiru yana kallon wayarsa, ya nunfasa ya ce "Allah ya sa rabonka ce Malam Umar, ni na yaba da dattakunka"
*** Laila ce suke waya da takawa, tana gaya masa ruma ta ishe ta da rashin ji, ita da ɗan ta, yana ta dariya mussaman da ta ce wai ruma ta zana mata aljani ta ajiye a ɗaki, wai hoton takawa.
"Anty laila bani shi mu yi magana" ruma tayi maganar tana ƙoƙarin karɓar wayar.
Laila ta ce "Ungo ku ƙarata, ban da video call dai, bari na shiga wanka".
Ya ce "Budurwar"
"Mmm saurayin, ya garin? Ya karatu?".
"Alhamdilillah, ya naki karatun, na ji anty laila ta ce tana yi miki lesson, kun kusa fara exams, dan Allah a dage a mayar da hankali"
"To in sha Allah, amma ni gaskiya daina zuwa islamiyyar nan zan yi"
"Meyasa kuma?"
"Ba karatu kawai ake koya mana ba, sai a din ga faɗar wasu maganganu"
Tun da ta faɗi haka ya san akwai ƙura, ya ce "Wasu maganganun kenan?"
"Wai se malamar ta din ga tsayar da mu, wai za ayi lecture, ka ji abun da take cewa kuwa?, wai a din ga saka ƙanan kaya ana karairaya sai ka ce wasu karuwai, yanzu dan Allah ya dace a zaunar da mutane ana gaya musu haka?"
Da ƙyar ya iya gimtse dariyarsa ya ce "Ke ya aka yi ki ka san karuwan ne suke haka?"
"Ai in gaya maka, da akwai wani gida a unguwarmu, sai matan su dinga saka riga da wando, ko mini skirt, suna yawo, aka koresu, na ji ana cewa gidan karuwai ne, har da vest fa suke fitowa waje ana kallonsu, na zo ina bada labari a gida, mai sunan baba ya sakani kama kunne, aka ce mini kar in kuskura abun da suke yi ya burgeni, idan mutum yayi irin wannan ba ga muharraminsa ba ɗan wuta ne. Ni fa wani abun ba zan iya faɗa ba ne, wallahi ni duk mutuncin malamr ya zube a idona ma, ni kuwa da ta fara nake tashi na tafi. Da fa sun rainani ba su zata ina da miji ba, sai da malama ta ce musu ni matar aure ce, wai wata ta ce mini, wai zan sai maganin mata? Na ce mata ni ban san shi ba, dan Allah a chemist ana ware maganin maza da na mata?"
Ya ce "A'a"
"To a in gaya maka, na ce mata ni idan bani da lafiya asibiti ake kaini, kawai ta nuna mini Wasu ƙulle-ƙulle da robobi mai hoton ƴan iska a jiki, Wai in saya, na rufe idona na ce a'uzubil'ahi, gaskiya ni dai a cireni daga makarantar nan"
Maimakon ta ji ransa ya ɓaci kawai sai ya din ga tuntsura dariya, har da tari, laila ta ƙarasa ta ƙwace wayar, ta ce "Ke dai ban taɓa ganin yarinya mara kan gado kamar ki ba? Wai ke baki da ƙawaye ne?"
"Nifa ƙawata ɗaya habiba, ko nayi ƙawaye mama korarsu take yi, kuma ko ba ta kore su ba, idan muka yi faɗa duka nake yi musu sai mu ɓata"
"Aikuwa wannan karatun, dole na zauna na ɗora miki shi, idan kin ƙi ganewa kuma shi idan ya dawo ya karanta miki yadda zaki fuskanta. Haba ke gaba ɗaya abaibai ce ba kya gane komai kenan".
"Anty laila ki daina hantarata, zamu yi faɗa"
"To muyi faɗan mana, ke zaki yi wa kanki ai".
Rumaisa ta kalleta ta ce "Saboda zaki daina sai mini garin kunun sabayar maman Khadija ko? Ba ita ce a zariya ba lambarta 0703777 7442. Sai maman Ilham mai magani ba da ke cikin garin kaduna kawo road ba, lambarta 08135613021, na riƙe komai tsaf a kaina saboda irin haka".
Laila ta ce "Iko sai Allah, ke yanzu zaman hadda ki ka yi kenan?"
"Ai Anty laila ba komai ake faɗa mini ba, in dai an yi abu a gabana, tsaf nake haddace komai tas a kan nan nawa".
"To kin kyauta, tashi ki je kitchen ki haɗa mana kayan aiki, yanzu zan zo ki gwada mini girkin da na koya miki, in gani idan da gaske kina haddace komai ɗin"
Rumaisa ta tashi ta ce "Yanzu kuwa".
***
Iman duk ta kuma zama so silent, ba babban abun da yake sanyata farinciki, irin ƙoƙarin jan mai sunan baba da hira, da safe ta gaishe shi, daga nan yayi mata ya jiki. Mutum ne miskilin gaske, tana shan fama, amma wasu lokutan ya kan saki jiki, mussman idan tana yi masa hirar karatun addini. Wani irin matsanancin tausayinta yake ji, da ya tuna Jabir, sai gabansa ya faɗi, ya san duk wani kauce-kaucensa son iman yake yi, gashi shi bai san ta ina yakamata ya fara ba, bai san meya kamata yayi mata ta din ga farinciki ba, saboda shi ya saba da bosy life, ba wasa.
Rumaisa ce a tsaye a banɗaki za ta yi wanka, tana ƙarewa kanta kallo a mudubin banɗaki, har da tsalle tana ɗan juyi, ganin abun arziki ya fara fitowa, yana cika. "Wayyo daɗi kasheni, zan wuce gori da wulaƙanci, na ga me sake ce mini ƙwaila, kai za a ga jan aji idan suka ƙara girma, wayyo ni maman Khadija da maman ilham sun kankaro ni yasin" Ta gama wankanta, ta fito ta shafa mayukan gyaran fata, ta saka kaya, ta kuma tsayawa tana kallon mudubi, ta ce "Hmmm, na ga wanda zai sake ce mini ƙwaila, mu haurata da shi, har shi papan, yanzu dai sun fi ƙarfin murfin jarkar faro"
Ta ɗaga kai ta kalli zanenta, da take kansile date kullum, na kwanakin da ya rage ya dawo.
A hankali ta furta "Lokaci baya sauri".
Ammi fa gaba ɗaya ta ji batun auren nan na iman da jabir ya fita daga ranta, kuma ta bi maganar rumaisa cikin tsanaki, taga lallai gaskiya take faɗa, ta sanyawa ranta aure lokaci ne, bai kamata ta jefa rayuwar iman cikin hatsari ba. A wannan zullumin turaki ya kirata, ya sanar da ita, wambai ya ce masa zai kawo wa jabir kuɗin aure. Takanas ammi taje gida, ta iske turaki, ta nemi ya taimaka a janye maganar nan. Turaki ya ce "Giwa saboda ne, kin fi kowa sanin halin wambai, daga ni har ke ba zai saurara mana ba".
Nan ammi ta yi masa bayanin komai, tuntuni ta so ta yiwa wambai maganar, amma ta san ba zai saurareta ba, turaki ya gamsu da maganganunta, dan ya san halin hajiya Lubabatu sarai, za ta aikata fiye da haka, ga yarinya na fama larura. Dan haka ya ce shi da ita yakamata su je wurin wamban, su yi magana da shi.
Ammi kamar ta ce ba sai sun je tare ba, saboda tana fargaba wambai ba ya yinta ko kaɗan. Amma yadda ta iya, tun da suggestion ɗin turaki ne.
Aikuwa kamar yadda ta tsammata, wambai ya balbalesu da faɗa ta in da ta shiga ba ta nan yake fita ba, ya din ga masifa.
"Kana bani mamaki turaki, da ka ke biyewa matar nan, dan kawai tana sirikarka, ke ba abun farincikin ki bane ba, kamar jabir zai auri yarinyar da ba wanda ya san iyayenta sai ke da mijinki a da'awarku. Nagartaccen yaro mai daraja daga gidan sarauta, sau nawa ana shirin aurenta ana fasawa, saboda wannan abun kunyar?".
Turaki ya ce "Allah ya baka yawan rai, ba jabir ɗin ake gudu ba, ita mahaifiyarsa da ta je har gida, ta nuna bata son abun, ta ci musu mutunci har yarinyar, wanda sai da ciwonta ya tashi, ita ma fa ƴa ce Allah ya baka yawan rai"
"Ita lubabatun ce ta ce ba ta son auren, bayan mun gama magana da ita?"
Da mamaki ammi ta kalleshi, sannan ta ce "eh, har gida taje ta ce mini ba ta so"
Wambai ya kira wayar hajiya Lubabatu, amma cike da ƙwarewa a mugunta, ta hau salati ta ce ƙarya ne, kawai dai giwa ta ce ba zata bawa jabir auren Iman ba, amma ita ba ta ce ba ta so ba.
Masifar da wambai yake yi, tuni idonta ya cika da hawaye. Turaki kansa ya san sharri ne, da tsabar mugunta, irin na hajiya Lubabatu.
"Tun da abun naki haka ne, ba kara ba mutunci a cikinsa, ai dama a kwanakin baya, da ake ta surutu a kak yarinyar da takawa, na ce lallai ki aurar da ita, to zan sake jaddada miki, nan da watanni uku, ko dai ki aurar da yarinyar nan, ko kuma ki mayar da ita in da ki ka tsinto ta, kuma a wannan karon ba zan canza magana ba. Sannan abu na gaba, ƙara tayi yawa a kan wannan yarinyar sirikarki, daga zuwanta gida tana yi wa mutane sharri, tana haddass husuma, jamila ta kawo mini ƙara, na so na zauna da ku, ta ce a bar maganar, still na samu labari a kan tana yayaya cewar jamil ne ya saka aka yi garkuwa da ƙanwarsu, to ahir ɗin ta, ki ja mata kunne, gidan sarauta ba wurin wasa bane ba" Ammi ta risunar da kai sannan ta tashi ta bar ɗakin, ranta babu daɗi, yayin da tausayinta ya mamaye zuciyar turaki, tana da kyakywar zuciya, sai dai tana ta fuskantar ƙalubale kashi-kashi a rayuwarta da ta iyalanta.
Yanayin yadda ammin ta dawo ne ya tabbatar musu akwai damuwa, har ruma za tayi magana, amma laila ta hanata.
Yau wunin yau idon mai sunan Baba yana kan waya, ko zai ga saƙon iman, amma shiru, shikuma ya kasa yi mata magana, har dare shiru, gashi ya riga ya saba da daddare ɗan jan sa da take da hira, yana yi masa daɗi. Haushi ne ya ishe shi, jin yadda Aliyu ya cika masa kunne da surutu shi da habiba, ya saka waya a speaker sai ƙyalƙyala dariya yake yi, habiba ta karkace murya tana yi masa waƙa, murya kamar an shaƙe kuliya.
"Kaga ka cika mini kunne, ko dai ka fita, ko kayi mini shiru.
Aliyu ya miƙe tsam da wayarsa, ya koma tsakar gida, duk da sanyin da ake zabgawa.
*** Jabir ne a zaune, hajiya Lubabatu da Mummy sun saka shi a gaba, suna ta yi masa famfo.
"Na sha gaya maka giwa ba ƙaunarka take yi ba, ka din ga nane musu, to gashi ƙiri-ƙiri ta hanaka auren ƴa, saboda azabar ƙarya ta je ta ce wai ni ce bana son auren nan, mun yi haka da kai? Da na nuna bana so ka dage, cewa nayi Allah ya sanya albarka, amma da yake mukafuka ce, ba ta yi niyyar baka auren ba, ta je ta ce nice bana so".
Mummy ta amshe ta hanyar cewa "Banda abun jabir, kai da ake yi wa fafutukar samun kujerar mahaifinka, ina kai ina wata ƴar tsintuwa, mara asali mata gata, kai ana ƙoƙarin ka samu kujera, amma ka nacewa Adam, shi ka san me suke yi ta ƙarƙashin ƙasa, dan ganin kujerar ta koma garesu, ga mata nan bila adadin a gari, ni ko ruƙayya ma sai na baka"
Hajiya Lubabatu ta ce "A'a wace irin ruƙayya kuma? A dai cigaba da neman kujerar, shima uban nasu ban taɓa tunanin zai kai haka a raye ba, kalli shi adam ɗin da kake liƙewa, yadda yayi suna a ƙasar nan, duk gaku matasa amma aka ware shi, aka tura shi wakilci, yayi aure ya haifi ɗa, ga aikinnsa ga kasuwanci, kai kana nan kana fama daga kai har jamil ɗin uwar me ku ke da shi, duk da dukiyar iyayenku ku ke taƙama"
Jabir yayi shiru tare da gazgata maganganun da tun a baya su mummy suke gaya masa bai ɗauka ba, tare da mantawa da asirin da takawa ya daɗe yana rufa masa tsawon shekaru.
Mummy kuwa ƙulattar Hajiya Lubabatu ta yi, da ta ce ya auri ruƙayya ta ce a'a, wato a tunaninta ya samu mulki, aci moriyar ganga a yada kwauronta.
Mummy a ranta ta ce 'Lubabatu baki da hankali, da ni ki ke zancen, lokaci yayi da zamu raba gari, kowa ya san in da ya kama'.
Kasa jurewa mai sunan baba yayi, ya fara tunanin ko jikin iman ne ya dawo, dan haka da kansa ya kira iman a waya. Sallamar da yayi ta amsa cikin siriryar muryarta.
"Jikin ne dai?"
"A'a barka da safiya yaya umar"
"Meyafaru?"
"Bakomai" tayi maganar cikin sauke numfashi.
"Something is going wrong, feel free to share it with me"
"Yaya umar ba zan dameka da matsalolina ba?"
Cikin nutsuwa ya gyara zamansa ya ce "If you are free with me, let's share it together"
Wata irin nannauyar ajiyar zuciya ta yi ta ce "An yi cancel ɗin engagement ɗina da za ayi".
"Ba abun da ki ke so kenan ba?"
"Ba cancel ɗin ya dameni ba, tun da Allah ya sa na buɗe ido a hannun ammi, take bani kariya da nuna mini ita ta haifeni, amma mutanen da suke kusa da ita, basu bata goyon bayan hakan ba. Saboda ni ba irin tashin hankalin da bata shiga ba, kullum cikin damuwa take, kullum cikin sintiri kaini asibiti, kullum cikin neman abun da zai sani farinciki take,. Amma ni na kasa kawo mata farinciki ko sau ɗaya. Ban san dalilin fasa Engagement ɗin ba, mai girma wambai ya ce ko tayi mini aure nan da watanni uku, ko ta mayar da ni in ta tsinto ni, babban abunda ya dameni kukan da ammi ta sha, ta ce da ta rabu da ni, gara ta ɗauke ni mu bar gidan, ni rasa me ma zan yi, ina son ammi amma ba zan so ta bar gidanta ba".
A tsakiyar zuciyarsa ya din ga jin kukan iman, ya jingina jikinsa da bango, wata irin karaya ta kama shi.
A hankali ya ce "Khadija, kukan nan yana taɓani sosai, bana son jin kukan mace, ko ban santa ba, zamu yi waya anjima. Amma dan Allah bana son sake jin labarin kina asibiti, ya isa haka"
A hankali take sassauta kukan, ta ce "Yaya Umar, na gode da ka bani dama ka ji abun da yake damuna, na gode sosai"
"Don't mentioned, ki ci abinci ki kwanta ki yi baccinki, ki cigaba da addu'a, ba abun da zai faru sai ikon Allah khadija" shi kansa mamakin yadda ya tausasa murya sosai yake, bai taɓa zaton ya iya rarrashi haka ba.
Rumaisa kuwa Mahmud ta kira a wayar Anty laila, ta ce tana son ganinsa a in da suke haɗuwa.
Babu jimawa kuwa suka haɗu, sai dai cikin tsananin fushi ruma ta ce "Daddy anya mummy na son taga Annabi kuwa, daga ita har babar jabir fuska kamar an mari biri? Ya za ayi ta zo ta ce ba zata bari ɗanta ya auri Iman ba, ammi ta ce a fasa a janye, ta ce ita ƙarya aka yi mata ba ta faɗa ba?
Ammi sai kuka take yi, har da masu kiranta a waya, ana bata kyauta ba, ta hana jabir iman, gashi wambai ya ce idan ba ta aurar da iman ba ta mayar da ita in da ta tsinto ta, wai ya suke so baiwar Allah nan tayi ne, daga ita har Iman ɗin sai koke-koke suke yi, wai kai ba abun da zaka iya yi a kai? To ni zan je wurin wamban sai na tonawa kowa asiri da kaina, ayi wadda za ayi ta ƙare!
Ayshercool. 08081012143 *MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*
*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?* *TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI* *SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*
*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*