Kanwar maza Book 3 and 4 Complete - Chapter 46
Kanwar maza Book 3 and 4 Complete Chapter 46: Kanwar maza Book 3 and 4 Complete Chapter 46. Zaune suke a kan fararen kujeru, cikin yanayi mai daɗi, sai dai…
3,369 words
Zaune suke a kan fararen kujeru, cikin yanayi mai daɗi, sai dai an rasa wanda zai yi magana, kasancewar shi wannan ne zuwansa na farko zance, ita kuma yayi mata kwarjinin da ya saba, ko ɗaga kai ta kasa, sai kallon wuri ɗaya kamar mara gaskiya.
"Ki yi tayi mini surutu a waya, har na rasa abun cewa, amma yanzu kin sakani a gaba kina sunkuyar da kai, kamar kinga dodo, daga gaisawa kin yi shiru".
Muryar nan ba ƙaramin narka mata zuciya take yi ba, murmushi ta kuma yi ta sunkuyar da kai.
"Shikenan, Khadija ɗago in gaya miki dalilin zuwana wurinki" da ƙyar ta ɗan ɗaga kai.
"Kallona zaki yi, bana son na yi miki dole, ko kiyi mini alfarma, dan kina jin kunyata ko ta ƙanwata, ni wannan abubuwan duk ban san kan su ba, ban taɓa gwadawa ba ma. Amma na ji ina son na aureki, zaki iya auren talaka kamata?"
'Na ji ina son na aureki, baya sona kenan, ko tausayina kawai yake ji' ta tambayi kanta.
"Ba kya son talaka ko?'
Ta girgiza masa kai alamar a'a.
"Talk"
"A'a yaya umar" tayi maganar muryarta na rawa.
Umar ya ɗan tsura mata ido ya ce "Ba takura miki nake ba, tambayarki kawai na yi, idan ba zaki aurena ba, ba wani abu, ban san meyasa nake baki tsoro ba, rumaisa ma da muke faɗa, ba ta ji ne, but am good person ko?"
Ta ce "Yes you are".
"Zan tafi, duk hukuncin da ki ka yanke ki gaya mini, ba wani abu"
Ledar hannunsa ya ajiye mata, ya tashi yayi tafiyarsa, ta daɗe a wurin tana tunani, daga baya ta yanke, ko baya son ta, ko iya tausayin nata yake ji, zata iya aurensa, tun da shi baƙin tabonta, bai hana shi cewa zai aureta ba.
Ammi bata matsa mata a kan sanin lallai waye ba, sai dai rumaisa ta din ga cewa ƙamshin turaren mai sunan baba take ji. Turaruka ne masu kyau, guda uku da dabino lubiya manyan kwali guda uku.
Har aka yi sallar magariba, ta kira shi ta sanar ta yi masa ya yaje gida, jikinta a sanyaye yake, ya ce mata yaje lafiya, daga nan ba wata magana suka yi sallama.
Suna zaune a falon, suna kallo, suna taɓa hira, laila ta kora rumaisa ta je tayi karatu, dan jarrabawa suke yi a makaranta, ammi ta fara tambayar iman, wai waye baƙonta ya kuma suka yi da shi?.
Sai dai kan iman ta kai ga yin magana, Mahmud ya shigo tare da yin Sallama.
Masu gadi suka shigo da ruwa carton biyar, lemo carton biyar, ya ƙarasa gaban iman, ya bata envelope ya ce "Gashi nan in ji umar, ya ce a baki, ba yawa ki rage wani abun, na bikin saukar ki"
Kallon Mahmud take, dan ba ta fuskanci wani umar ɗin yake nufi ba.
Ganin kallon da take yi masa ya sanya ya ce "Wanda ya zo wurinki ɗazu" sai ta sunkuyar da kai tana jjya envelope ɗin.
Laila ta ce "Iman, sai ɓoye-ɓoye ki ke yi, yakamata ayi mana ƙarin haske a kan wannan da yayi wuf da zuciyar taki" tayi maganar cikin wasa.
Mahmud ya kalli Ammi ya ce "Allah ya baki yawan rai, ko zan iya magana da ke?"
Jiki na rawa ammi ta ce "Ni, eh mana Mahmud mai ze hana".
"Daddy ba Allah ya baki yawan rai ba, Ammi zan iya magana da ke dan Allah?" Rumaisa ta faɗa lokacin da ta fito, yake neman izinin magana da ammi.
Bai ce komai ba ya ɗan murmusa, ruma ta ce "Waye ya kawo mana lemo?"
Ammi ta sake mayar da hankalinta kan Mahmud ta ce "ko ciki zamu shiga ne?"
Ya ce "To"
Sashinta ya bita, tana gaba yana baya, zuciyarsa na yi masa wani irin ɗaci, yaushe rabonsa da taka wurin nan, har ya manta, yau gashi a dalilin rumaisa, yana ta kokowar farkawa da nannauyan baccin da yake tsawon shekaru.
A ɓangaren ammi ma haka ne, dan fes take tuna lokacin da aka ƙwace mata shi, ta ƙarfin tsiya.
A bedroom ɗin ta suka tsaya, ta ƙarasa ta saka hannunta, tana sake kaɗe masa makeken gadonta, da yake a ɗame da bedsheet fes da shi ta ce "Bismillah zo ka zauna"
Ya nemi wuri ya zauna a ƙasan carfet, ya ce "ki zauna, ni nan ya isa"
"To nima bari na zauna a nan ɗin, ai ba wani abu" ta zauna a ƙasa kusa da shi.
Ya kalli fuskar Ammi, da ta rasa in da zata saka kanta dan daɗi, farincikin ta ya kasa ɓuya, sai ƙoƙarin mayar da hawaye take yi.
Ya kawar da kai kamar bai ga komai ba ya ce "Dama na ji abubuwan da suke ta faruwa ne, da abun da wambai ya ce game da iman. Dama abokina ne yake son iman, kuma shi talaka ne, bai tara dukiya ba, amma ɗan mutunci ne, kuma na yadda da kirkinsa, sanin kowaye iman ɗin zata gaya miki, ya ce a tambayeku, zaku bashi ita, amma nan da watanni uku yayi masa kaɗan ya shirya, ku bashi kamar wata biyar, idan sun dai-daita, zai turo".
Ammi ta ce "In dai bashi da wata matsala, kuma ya san wacece ita, ba zai wulaƙanta mini ita ba, ba damuwa, zan iya ɗaukar ɗawainiyar komai ni nayi masa".
"Abu ne mawuyaci ya yarda da haka, amma na san zai yi iya ƙoƙarin sa a kan kula da ita."
"Dama ni haka nake fata, Alhamdilillah, Allah ya yi maka albarka kaima, da nuna kulawa a kan abun da ya dameni. Na ji ka kammala karatun ka, Allah yayi muku albarka. Ya albarkaci abun da ka karanta, Allah ya sa ka koma bakin aikinka lafiya, Allah ya haɗa mana kanku gaba ɗaya ƴaƴan galadima".
"Amin ammi na gode" ta ji ya tashi ya nufi hanyar fita, daf da zai fita ya jiyo sheshsheƙar ammi, amma ina bai juya ba, ya fita shima yana zubar hawaye.
Ganin ya fito yana kuka, har rige-rigen shiga wurin ammi suka yi.
Ruma ta ce "Ammi, me yayi miki me ya ce miki? Ɓata miki rai yayi?"
Laila ma tambayoyin ta shiga jero mata, amma ta riƙe hannun ruma ta ce "Bayan tsawon shekaru, da fidda ran ɗa na zai sake kallona a matsayin uwa, ya kirani da ammi rumaisa, ɗa na ya kusa dawowa gareni, duk ƙoƙarin ki ne rumaisa na gode"
Rumaisa kasa riƙe hawayenta tayi, ta fara sharewa ammi nata ta ce "Haba ammi, idan kina kuka mu idan mun yi wa zai rarrashemu. You are a good mother, you deserve to smile. Idan ana maganar jajurtattun iyaye a duniya, da mama da ke, bani da na biyun ku ammi"
Ammi ta rungume rumaisa tana ta kwarara mata addu'a, da ita da iyayenta.
"Tabbas duk wanda zai ce sirikata ba ta ji, to bashi da gaskiya ne, ina alfahari da ke ƴa ta".
Laila ta ce "To, ammi abun har da wariyar launin fata? Kan dai ki samu sirikar taki, mu ki ka fara sani".
Nusaiba ta ce "Muna zaune ta yi mana wayo, ta ƙwace mana ammi ba".
Bisa kasada umar yayi proposing ɗin Iman, ba dan yana da abun da zai aurenta ba, sai dan son da yake mata da tausayinta da yake ji.
Laila tana zaune suna hira da ammi, laila ta ce mata tana son zuwa gombe, idan zasu tafi suje tare da rumaisa da Iman, ammi ta amince da hakan. Ta ɗan numfasa ta ce "Laila ko iman ta gaya miki wani abu game da baƙonta ne? Haryanzu ba ta ce mini komai ba, waye daga ina yake da sauransu, Mahmud ya ce mini abokinsa ne, ta yarda ta amince tana son sa"
Laila ta ce "Ahh ammi, ba yayan rumaisa ba ne, ni dai alamu sun nuna tana son shi, lokacin da ta kwanta a asibiti na ganshi, yana nan mai kama da ruma sosai"
Ammi ta ɗan waro ido ta ce "Mai sunan baba wai?"
"Eh ina ga shi ne"
Ammi ta ce "Ikon Allah, abu kamar wasa, dama tsorata tan da yake yi na soyayya ne. Na yaba da tarbiyar gidansu rumaisa, mahaifiyarsu jajirtacciyar uwa ce, amma ina jinjina lamarin nan, anya iman za ta iya da shi, kamar boss haka yake, ba fara'a baya son mutane, mamansa na yawan faɗar zafin ransa".
Laila ta ce "Ammi ki yi musu addu'a kawai, ke ba ga ɗanki nan ya samu dai-dai da shi ba, duk nasa zafin kan kalli yadda rumaisa ke sola shi yadda take so, tun da ya iya cewa yana son ta, ai a wuce wurin "
Ammi ta ce "Haka ne, Allah ya sa kar a samu matsala daga baya, bari na ji ta bakin Iman ɗin, sai mu ga abun da yakamata ayi".
Laila ta ce "To shikenan, Allah ya tabbatar mana da alkhairi, ya sa daga haka a samu ƙarshen wannan matsalar.
Ammi ta amsa da Amin.
Takawa na tsaye a valcony, hannunsa ɗaya riƙe da kofin tea, ɗaya kuma da takardar zanen da rumaisa ta saka masa a kayansa, sai dai kurman zane tayi, ba tare da bayanin komai ba, kuma da alama saƙo ne mai muhimmanci take son isar masa a zanen.
Kusan kullum sai ya kalli zanen nan, kuma kamar yadda ta ce kar ya tambaye ta, yasan da zarar ya matsa, ba lallai ta yi bayani.
Babban abun da ya fi ɗaukar hankalinsa, shi ne SMOKE, da ta rubuta da manyan baƙaƙe, sai daji da ta zana da dogayen bishiyu, sai aisha durƙushe a gefen bishiya ta riƙe ciki.
"Mimi what's the meaning of this?" Yayu maganar yana shafa zanen, hawayen sa na ɗiga a kan zanen.
*** Litattafai ne a gaban Iman, tana karatu, Ammi tayi sallama, Iman ta amsa.
"Sarki littafi, ina fatan kin gama karɓo komai, da za ayi amfani da shi na bikin saukar?".
"Eh ammina, everything is ready"
Ammi ta miƙa mata leda ta ce "Sidi ya kawo, ya ce a baki in ji umar"
Iman ta karɓa ta duba, keyholders ne, da jotter yayi mata na sauka.
"Auta haryanzu baki ce mini komai a kan yadda ake ciki ba, kin amince da mai sunan baban, kina ganin babu matsala?"
Iman ta ɗago da sauri, ba ta zaci ammi ta san waye ba.
"Ko da baki gaya mini, na gane waye, amma iman kina ganin babu matsala? Zaki iya zama da shi?"
Iman ta jinjina kai ta ce "Ammi yana da kirki"
Ammi ta yi murmushi ta ce "So hana ganin laifi, amma ya san halin da ake ciki, ya amince da hakan?"
"Eh ya sani".
"To Alhamdilillah, Allah ya tabbatar mana da alkhairi" ammi ta tashi ta fita.
Iman ta bi Ammi da kallo har ta fice.
Mai sunan baba yana zaune a gaban mama, yana cin abinci, duk suna tare da su Aliyu, Abubakar yana kwance a gefen mama yana danna waya.
"Babana" mama ta kira sunansa.
A hankali ya ɗaga kai ya kalli mama.
"Ashe neman aure ka ke ban sani ba?"
Gaba ɗaya suka ɗaga kai suna kallon mai sunan baba.
"Mun yi waya da hajiya, ta ce sun baka dama ka fito, sai dai ban san zancen ba sai ɗazu da ta kirani a waya".
Ayshercool. *MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*
*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?* *TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI* *SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*
*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*
👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*
*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*
*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*
*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*
*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*
*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*
*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*
*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*
*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*
*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*
*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*
*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*
*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*
*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton* *14. Supplement na whitening/glowing skin*
*15. Supplement for Acne, dark spots remover*
*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*
*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*
Paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, ga masu buƙatar vip post, suna iya garzayawa arewabooks su yi searching sunan book ɗin. Kar ku manta da subscribing YouTube channel ɗinmu na Cool hausa novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro, ciki har da ƙanwar maza da yake daf da fara zuwar muku a kan channel ɗin*
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Susbcribe my YouTube channel please 🙏
*TALLA! TALLA!! TALLA!!! *ƊANƊANO DAGA LITTAFIN NAZEEFA SABO NASHE, MAI SUNA ƘUDURAR ALLAH*
Ta Yaya zai zama jinina alhali ni na san bayan matana ban tab'a kusantar wata mace ba?" Ya furta kai tsaye yana kallon likitan da sakamakon gwajin yake hannunsa. Likitan yana jinjina kai ya sake furta "Tabbas Jaheed jininka don gwajin k'wayar halittarku da komai ya tabbatar kai ne mahaifinsa kafin a kai ga haka ma ko Kamanninku da suka zamo kwabo da kwabo sun tabbatar da Hakan koda Ba'a yi gwajin ba."
Shiru na tsawon lokaci d'akin ya d'auka kowa da irin tunanin da yake a ransa ya kasa yarjewa zuciyarsa shine Mahaifin Jaheed duk da k'wararan shaidu. Abinda ya sani ko da wasa bayan matansa na aure na Sunna bai tab'a rik'ewa wata mace hannu ba, idan kuwa ya tabbata Jaheed d'ansa ne ta yaya ya samar da cikin nasa a jikin wacce aka kira mahaifiyarsa da ko a mafarki bai tab'a ganin mai kama da ita ba TABBAS AKWAI LAUJE CIKIN NAD'i. Mahaifiyar Jaheed ma Zata iya zama abar tuhuma da zargi. Kai tsaye zai iya cewa hakan zai iya zama K'UDIRAR ALLAH….
(*Ina ma'abota karance-karancen litatafan hausa, na san kun santa, Nazeefa sabo nashe, tsohuwar marubuciya, da ta saba nishaɗantar da ku, da ɗaɗan litatafan hausa masu ma'ana da ilimantarwa, ya kuke tunanin wannan turka-turka, DNA ɗin sa ya kasance daidai da na yaron da bai taɓa ganin mahaifiyarsa ba, haka zalika a iya saninsa tun daga ƙuruciya har girmansa, bai taɓa aikata zina ba? Ku kasance da Nazeefa sabo nashe, dan jin yadda zata warware wannan turka-turka a cikin littafin ƙudurar Allah. Masu buƙata kai tsaye za su iya tuntuɓar ta a kan lambar wayarta 08033748387*)
Shiru yayi ya cigaba da kai lomar abinci bakinsa, suka tsare shi da ido suna jiran yayi magana.
Yaya Abubakar ya tashi zaune ya ce "Malam magana fa ake yi maka"
Mirsisi yaƙi magana, ya cigaba da cin abinci, Aliyu dama ya daɗe da gano yayan na su, ya afka kogin soyayya, magana ce kawai bai yi ba.
Sai dai ya gama cin abincin, sannan ya ce "Mama, ba ɓoye miki nayi ba, komai ya zo mini a bazata ne. Hasalima tausayinta da na ji ne, ya sanya na ji zan iya aurenta, amma kin san ni dai ban taɓa kula ƴar kowa ba".
Aliyu ya ce "Wai wa ce ne?". Harar da yayi masa ya sanya shi yin shiru.
Mama ta ce "To, wai an ce turakin kano yana son ganinka, zai gana da kai, a kan maganar, kuma suna buƙatar ka fito ne"
Mai sunan baba ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Mama bani da abun aurenta yanzu, kin san komai a kanta, dan ina wurin lokacin da rumaisa ke baki labarinta. An fasa aurenta da wani, kuma a yadda take gaya mini, shi ne karo na huɗu, duk saboda waccan matsala, dalilin haka kuma, an ce wa mariƙiyarta idan ba ta aurar da ita nan da watanni uku ba, ta mayar da ita in da ta tsinto ta. Magana ake ta shekaru goma sha tara da riƙonta, wurin wa za ta kai ta. Ban san ya aka yi na ji ina son na aureta ba".
Aliyu shi tausayi ma ya bashi, har yanzu bai gama yadda soyayya ce tayi masa kamun kazar kuku ba.
Mama ta ce "Na yadda da maganarka babana, kuma na goyi bayanka, dan shi ɗa na kowa ne, yadda hajiya binta ke riƙe da rumaisa kamar ba sirikarta ba, kaɗai ya isa na goyi bayanka. Kuma Allah ya sani tun kan haka ina ƙaunar yarinyar nan sosai. Amma abun da nake tunani, kaga an saka bikin Abubakar, muna ta fama, gashi ka tsayar da gininka ana nasa, yanzu meye abun yi watanni uku sun yi kaɗan".
Abubakar ya ce "Ba dan halinsa ba, kuma tun da ban isa ya gaya mini abun da yake ciki ba, saboda halin da yarinyar take ciki, da kuma duba da muma muna da ƙanwa, muna fatan albarkacin wannan jihadi da zai yi, Allah ya kula mana da ita, a duk in da take, da kuma la'akari da yadda mutum ya faɗa soyayya, da har ta kai shi ga yanke hukunci, ba tare da shawara ba, ni yayansa wato hassan ɗin sa, zan yi magana da su baffa, a ɗaga bikina a fara nasa, tun da abun gasa ne, nayi sai yayi. Sai su tare a nawa gidan, ni na ƙarasa nasa".
Mai sunan baba ya galla masa harara.
Abdallah ya ce "Auren mai sunan baba, zama bai kama mu ba, dole mu yinƙura abu namu maganin a kwaɓe mu".
Yasir ya yi murmushi ya ce "Ni zan sai akwatin kayan lefe, guda shida in sha Allah"
Huzaifa ya ce "Ji banza, an gaya maka akwatin lefen ma, jagwal za a saya, kamar kayan jagwal ɗin da kake na wayoyi da computer, da hacking in ji rumaisa".
"Bana son rashin mutunci, kai ka san abun da nake da shi ne? Kwanan nan daga china zan fara yin order wayoyi, kai ka sani ai, jari nake tarawa, amma ni
zan sai akwatunan lefe, kai uwar me ka ajiye da zaman basir ɗin ɗinki, banda shegiyar ƙarya da saɓa alƙawari".