Kanwar maza Book 3 and 4 Complete - Chapter 6
Kanwar maza Book 3 and 4 Complete Chapter 6: Kanwar maza Book 3 and 4 Complete Chapter 6. Ammi ita kaɗai tayi ta hirarta da farincikinta, Adam yana…
3,304 words
Ammi ita kaɗai tayi ta hirarta da farincikinta, Adam yana saƙe-saƙensa, iman kuma na cigaba da jin wata irin fargaba da bugun zuciya, a haka suka ƙarasa gida, yana ajiye su ammi ya ja motar ya juya ya tafi.
Rumaisa kuwa tun da ta amsawa ammi, abun duniya ya isheta, gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi, mai sunan baba ya je ya turketa a ɗakin mama ya ce "Ya muka yi da ke? Shi ne ki ka yadda ki ka amsa ko? Ki je ki yi ba dai aure ba gaki nan gashi. Meye a cikin auren gidan sarauta ban da tarin ƙalubale da tsaface-tsaface ke da ko ciwon kanki baki gama sani ba, amma kin tari aradu da ka, ke ko tausayin rayuwarki ba kya ji, ki je ki ƙarata".
A take jikin rumaisa ya kuma yin sanyi, wata irin dana sani ya mamayeta, tare da tashin hankali, wani irin tsoro ya shigeta dan ita kanta tun da ta amsa gabanta yake faɗuwa.
"Mai sunan baba, ka daina tsoratata, duk abun da yak cikin littafin ƙaddarar bawa bai isa ya kauce masa ba, wataƙila ba dan dalilin auren nan ba za a saceta ba, wataƙila sanadin sai an yi auren nan ne ya sanya aka yi garkuwa da ita, kar ka sake ka ce zaka zafafa, ko ka yi jayayya da ikon Allah"
Mai sunan baba yayi ajiyar zuciya, ya ji mama ne kawai, amma bai ji yana son auren nan a ransa ba.
*** Samha kuwa ta saka Jamil a gaba a kan ya ake ciki game da zancen da suka yi, na son maye gurbin aisha.
Jamil ya ce "Mun yi magana da mai girma turaki, sai dai ya ce na ɗan bashi lokaci tukuna"
"Amma har zuwa yaushe tukuna? An kusan kwana goma da zancen fa, amma babu wani feedback"
"To amma ai shi ya ce in saurare shi, bai kamata na cigaba da takura masa"
Samha ta ce "Ya salam, wallahi yaya Jamil bana son a kuma samun matsala a wannan karon"
"Babu wata matsala ai in sha Allah, dama ita Aisha Allah ya ƙaddara sai ya fara aurenta ne"
"A'a yaya Jamil, ina tsoron Allah ina tsoron ya ce zai auri wannan banzar iman ɗin, kusancinsu yayi yawa fiye da yadda ka ke zato, tsoro nake ji wallahi, tsaf ammi sai ta ce a wannan karon ya auri iman".
"Amma ai ya ce idan har zai iya auren iman to zai auri su nusaiba, kin ga ya harantawa kansa auren iman kenan".
Samha ta yi ajiyar zuciya ta ce "Babu tabbas yaya, komai zai iya faruwa fa"
"Ni fa na ce ki kwantar da hankalinki, in Allah ya yarda a wannan karon, zan yi duk mai yiwuwa ki auri adam"
Ta ƙaƙalo murmushi ta ce "To shikenan, Allah ya sa yaya jamil".
"Amin, bari na je gida, Hamida babu lafiya"
"To Allah ya sauwwaƙe"
Ya amsa da amin ya fita.
*** Mama tana ankare da rumaisa, har garin Allah ya waye, jikinta a sanyaye yake, gaba ɗaya ba ta da karsashi yau, abinci ma da ƙyar take ci.
Mama ta dubeta a tsanake ta ce "Rumaisa"
Ruma ta ɗago ta kalli mama.
"Meke faruwa ne? Ki ci Abincin mana"
Rumaisa duk ƙaunarta da shayi, ta ture kofin, ta ce "Na ƙoshi tafiya zan yi"
Mama ta ce "Zo nan" Rumaisa ta ƙarasa ta zauna a gaban mama.
"Maganar auren nan ki ka saka a ranki ko?" Rumaisa ta jinjina kai alamar eh.
"Ki kwantar da hankalinki, kar ki kuskura ki saka damuwa a ranki, ki yi ta Addu'a, sannan ki ja bankinki ki yi shiru, kin san abun da ƴan unguwar nan ke ya surutu a kanki, auren nan ne kawai rufin asirinmu"
Ruma ta kalleta ta ce "Me suke cewa a kaina?"
Mama ta tuna ashe fa rumaisa ba ma ta san zancen ba, mama ta ce "Babu komai, ki tashi ki tafi".
"Dan Allah mama ki gaya mini"
"Ba zan faɗa ba tashi ki tafi, karki makara"
Ganin mama ba ta da niyyar faɗa mata, ya sanya ta ɗau jakarta ta fice, ta ƙudurce a ranta sai ta san ko menene.
Tana tafe a hanya ta ji muryar habiba tana ƙwala mata kira, rumaisa ta tsaya ta waiwaya, habiba ta ƙaraso tana haki ta ce "Ruma, kwana biyu, kin ce zan rakaki kotu, amma baki kuma dawowa ba, lafiya kuwa?"
Jiki a sanyaye rumaisa ta ce "Ke rabu da ni, na fasa zuwa kotun nan"
"Amma meyasa, kin haƙura da karɓar ɗan?"
"A'a, zan karɓe shi"
"Hmm kin ji abun da ake ta cewa a kan ki ko, wallahi maƙociyarku munafuka ce"
Cikin mamaki rumaisa ta ce "Me ake cewa?"
Habiba ta ce "Au baki sani ba?"
"Ban sani ba"
"Taɓ, to da suka je asibiti dubaki, suka ga ɗa, suke cewa wai ɗanki ne, cikin shege ki ka yi, aka kai ki garinku ki ka haihu, yanzu an sallamoki kin dawo gida babu jaririn wataƙila kasheshi ku ka yi"
Galala rumaisa ta bi habiba da kallo ta ce "Cikin shege kuma? Kamar yaya, to ai ko a gurin ƴan bindiga, bana yarda su taɓani, sai dai bisa tsautsayi ya za ayi ciki ya fito mini na haihu, na yi abun kunya fa kenan, ɗan anty aisha ne fa ta mutu ta bar mini shi"
Habiba ta ce "To wallahi duk wadda aka ce ta yi cikin shege, to ƴar iska ce"
Rumaisa ta yi tsaki ta ce "Sai su yi ta yi ai, na tafi kar na makara,ke ma ki tafi makaranta"
Habiba ta ce "To shikenan, amma dai wallahi maƙwabciyar nan ta ku munafuka ce"
Rumaisa ta yi gaba, sai dai maganar Habiba ta din ga yi mata yawo a ka.
Har ta je makaranta ta dawo, ba ta cikin nutsuwar ta, mama ba ta kawo komai a ranta ba, sai rumaisa tana cikin alhini ne kawai na batun auren nan, ita kuwa rumaisa tuni zancen aure ta ajiye shi a gefe, zancen da habiba ta yi mata ya cigaba da damunta.
A islamiyyar ma kasa sakin jikinta ta yi, maganar ta cigaba da ci mata zuciya. Har a yanzu rumaisa ba ta da takamaiman ajin da take zama, duk in da yayi mata kawai tafiya take zauna.
Yau ma a ajin su Yasir take, ta matsa ku sa da wata ɗaliba, duk ƴan ajin mata da take mutunci da su, yayata take ce musu.
Ta yi ƙasa da muryarta ta ce "Yayata, duk wanda aka ce yayi cikin shege wai da gaske ɗan iska ne?"
Ɗalibar ta riƙe haɓa ta ce "Ke rumaisa, meye haɗinki da wannan maganar? Duk wanda yayi cikin shege ɗan iska ne, kuma wasan banza yake da maza, yana bari suna ta ɓa shi ko taɓa al'aurarsa.
A rikice rumaisa ta riƙe mararta ta ce "Wurin fitsari kenan?"
"Ƙwarai kuwa" ta bata amsa.
"Mama ta ce mini ba a wasa da al'aura, kuma ba a bari wani ya taɓa maka".
"Sosai haka ne, dan haka kar ki kuskura wani yayi miki wasan banza, duk wanda ki ka bari ya taɓaki, to cikin shege zaki yi, a gidanku ma korarki za ayi kowa ya tsaneki, a din ga yi miki kallon mutuniyar banza ƴar iska, Allah ya yi fushi da ke, idan wani ne yake miki ki je ki faɗa a gidanku"
Rumaisa ta girgiza kai ta ce "A'a tambayarki kawai na yi na gode".
Tun da aka yi wa rumaisa wannan bayanin hankalinta ya tashi, wato kallon ƴar iska ake yi mata, mai wasan banza da maza, da aka ce ta yi cikin shege. Ita banda ƙaddara da tsautsayi da ya sanya takawa ya taɓa ƙirjinta, ita babu wani namiji, da ko da wasa yayi mata maganar banza balle ya kai hannunsa jikinta, iyaka dai ta san tana dambe da maza, amma ba wasan banza ba.
Duk jarumtar rumaisa sai da ta yi kuka, tare da ganin an cuceta, yanzu duk in da ta wuce kallon da ake yi mata kenan.
Malami ya shigo ajin, yayi musu ƙarin alƙur'ani, ana tsaka da ƙari rumaisa ta ce "Malam dan Allah ina da tambaya" yayi shiru sannan ya ce "Ina jinki rumaisa".
"Lokacin da ka bamu addu'a, la'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu mina zalimin, ita na yi ta biyawa, lokacin da aka yi garkuwa da ni, har na kuɓuta. Dan Allah ka bani addu'a da zan yi mutum ya zama kurma, da bebe"
Ya ce "Ashsha subhanallah, me yayi zafi haka rumaisa?"
"Wata mata zan yi wa, da wasu mutane" ta yi maganar har zuciyarta.
Ya ce "A'a, ki yafe musu ko ki bar su da Allah, ki yafe musun ma shi ya fi, sai ke ma Allah ya yafe miki laifukanki"
Ta girgiza kai ta ce "Wallahi ba zan taɓa yafewa ba, sai na yi addu'a Allah ya tattaro masifa ya jibga musu"
Malam ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wannan ba halin mumini bane"
Rumaisa ta tashi tsam tana kuka ta ce "Ni dai wallahi ba zan yafe musu ba, dama ka ce Allah ba ya juya addu'a wanda aka zalunta, in sha Allah sai matar nan ta zama kuturwa ma wallahi, dan ba zan yafe ba" Statement ɗin ta ƙarshe sai da ya bawa wasu dariya, Yasir yana kallonta ya shareta ta fice daga ajin tana kuka, zuciyarta na wani irin tafasa.
Ba a tashi ba ta tafi gida, dama mai gadi ya daina tareta idan ta zo fecewa muddin an kusa tashi, tun da ta taɓa yi masa rashin hankali, ta fita da gudu garin bin ta ya faɗi yayi targaɗe, a hanya ta tsaya ta sai leda viva ta naira goma, ta cikota da manyan duwatsu, ta cika jakar makarantar ta da duwatsu, ta ɗora a ka, ta nufi gida.
**"
Takawa yana gidansa, yana duba wasu takardu da ya taho da su daga wurin aiki, saura sati biyu zai je lagos wani aiki, Jamil yana gefensa suna shan tea, takawa yana duba takardun.
Jamil ya ɗan ajiye kofin, ya kalli adam ya ce "Takawa ya batun aure ne? Yaushe zaka yi wani auren?".
Adam ya ɗan yi jimm sannan ya ce "Maiyasa ka ke tambaya?"
"Saboda abu ne da yakamata ka fara zancensa, ka san very soon za a fara yi maka magana a kai"
Adam ya ɗan numfasa ya ce "Ba shi ne a gabana yanzu ba, cigaba da ayyukana na binciken da nake yi su suka fi damuna".
"Amma kana ganin zaka iya cigaba a haka, duk yadda aka sakoka a gaba, gashi ka ƙi cewa komai"
"To Jamil ya zan yi, duk mutanen da suka fito suka wankeni, ba su isa ba ba a fasa yi mini sharri ba, nima idan na yi maganar ba zai canza komai ba, kowa yayi abun da ya ga dama kawai, iyaka duk wanda ya ga ba zai iya haƙura ba ya nemi hujja ya kai ƙarata shikenan"
Jamil ya ce "Lamarin ƙasar nan ai sai Addu'a, Allah ya kyauta ya bada nasara, nima akwai special assignment da zan tafi jigawa, na ji kana cikin wanda za su je Lagos ko?"
Adam ya ce "Eh, aikin ma nake dubawa yanzu"
Jamil ya ce "Allah ya sanya mu gama da aikin nan lafiya, kalli yadda muke wahala a kan ƙasar nan amma ba a gani, kalli aikin da muka yi a kan tsohon ministan harkokin waje, amma dan wulaƙanci wai kotu ta bayar da belinsa, amma daina maganar ni gaba ɗaya sai in ji aikin ma ya fita daga kaina" Jamil yayi maganar cikin damuwa. Adam ya ce "Haba Jamil, bai kamata mu karaya ba, ko da muna yi ba a ɗaukar mataki, wataran za a ɗauka, haƙuri zamu yi mu cigaba da yi, idan ba haka ba haka ƴaƴanmu da jikoki zasu taso su ɗaora da bauta babu ranar da talaka zai yi ƴanci"
"Kana da gaskiya, amma ni fa na tsorata da batun garkuwa da aisha, anya baka tunanin shiri ne, saboda abun da muke yi?"
"To ba na ce ba, zancenka zai iya zama gaskiya, kuma zai iya zama akasin hakan, duba da yadda dama ƙasarmu babu tsaro, kuma kai tsaye garin da babu tsaron ta tafi, dan haka bana zargin kowa"
"To, Allah ya yi mana jagora, ya bayyana gaskiya a duk in da take".
Adam ya amsa masa da Amin.
Rumaisa ba ta yi burki a ko ina ba, sai a ƙofar gidan maƙwabciyarsu, tana tafe tana kuka har ta je ƙofar gidan, ta sauke kayan dutsenta, ta shirya tsaf, ta tattare hijjabinta, ta fara auna manyan duwatsu zuwa cikin gidan nan.
A rikice matar gidan ta fito, a matuƙar tsorace, jikinta ko mayafi babu, domin ganin meke faruwa. Amma tana buɗe ƙofar gida, rumaisa ta sauke mata wata ƙatuwar marmara a bakinta, take bakin ya fashe, kan ta yi wani abu wani dutsen ya sauka a goshinta. Rumaisa ta cigaba da aika duwatsun nan babu ƙaƙƙautawa tana kuka, tana faɗin "Munafuka, wallahi ba zan yafe miki ba, ni ba ƴar iska ba ce".
Kururwa matar ta din ga yi, tana neman agaji, mutane suka fara taruwa, aka rirriƙe rumaisa, amma ta din ga kuka tana ƙoƙarin cigaba da jifan.
Gidansu rumaisa aka je aka faɗa, Allah ya sa usman yana nan, ya je ya danƙota, tana kuka.
"Meye haka rumaisa, baki da kai ne? Dan me zaki din ga yi wa mutane jifa a gida?"
"Ba ita ta je take gayawa mutane wai na yi cikin shege ba, tana nufin ni ƴar iska ce ina wasan banza da maza" tayi maganar tana fashewa da kuka iya ƙarfinta.
Usman ya ja hannun rumaisa, ba tare da ya ce wa kowa komai ba, ya ja ta zuwa gida.
Hankali a tashe mama ta ce "Rumaisa, kanki ɗaya ki ka je ki na yi wa mace jifa a cikin gida, tana ta kurma ihu wai a taimaketa zaki kasheta?"
"Cikin kuka ta ce "Wallahi da zan iya sai na kashetan, dan me za ta ce mini ƴar iska? Cikin shege fa yana nufin mai wasan banza da maza".
Mama jiki a sanyaye ta ce "Rumaisa rayuwar duniya haƙuri ake yi, sai ki zo ki gaya mini, ni na ɗau mataki"
"Wallahi idan na gaya miki ba zaki ɗau mataki ba, cewa zaki yi na yi haƙuri, kuma wallahi ban haƙura ba, sai ta ga abun da zan yi mata" Rumaisa ta shige ɗaki tana kuka, Usman ya ce "Ai wallahi mama ban da kin hana da da kaina zan ci uban matar nan, duk yadda ki ka ɗauketa ƴa ki ke mutunta mata, amma ta yi mana wannan wulaƙancin".
Mama ta ce "Dan Allah usman a rayuwarku ku koyi haƙuri, da ƙyale mutane da halinsu, wasu lokutan da kai da rumaisan duk halinku ɗaya ai".
Ammi kuwa sake kiran mama ta yi, domin ta sake tabattar da rumaisa ta amince, dan ta fuskanci rumaisa ƴar buyagi ce, kar sai ta je ta kaiwa turaki maganar rumaisa ta mayar da hannun agogo baya.
Ta kira wayar mama, mama ta ɗaga suka gaisa.
Ammi ta ce "Ina maman sabir ne, a bani ita mu yi magana"
Mama ta miƙawa rumaisa waya, ta ci kuka ta ƙoshi.
Muryarta a dashe ta amsa sallamar ammi.
Ammi ta ce "Rumaisa lafiya kuwa, na ji muryarki a dashe?".
"Ba maƙwabciyarmu ce ta ke cewa mutane na yi cikin shege ba, ƴan unguwarmu suna yi mini kallon ƴar iska mai wasan banza da maza"
Ammi ta ce "Subhanallah, ki kwantar da hankalinki, kin ga yana daga dalilin da ya sanya nake son ayi auren nan, ki yi haƙuri ki manta da su, yau zan je gidan turaki mu yi magana, dama kiranki na yi na sake tabattarwa idan kin amince, nan da watanni uku kacal za ayi in sha Allah".
Ayshercool. *MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*
*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?* *TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI* *SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*
*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*
👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*
*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*
*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*
*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*
*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*
*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*
*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*
*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*
*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*
*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*
*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*
*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*
*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*
*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton* *14. Supplement na whitening/glowing skin*
*15. Supplement for Acne, dark spots remover*
*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*
*Muna saida duk wasu nau'in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158* Rumaisa ta yi ajiyar zuciya ta kasa cewa komai, ammi ta sake cewa "Kin dai amince ko? Idan aka yi aurenku shikenan babu wanda zai sake yi miki kallon mutuniyar banza, ni na san ke ba mutuniyar banza bace ba, kuma mijinki ma ya sani, dan haka ki rabu da su, kar ki sake kula kowa a cikin su kin ji maman sabir?"
Rumaisa ta ce "To, ina sabir yake?"
"Yana nan ƙalau, yanzun nan iman ta ɗauke shi ta fita da shi".
"To a gaishe su" ba ta sake magana ba daga haka, ta miƙawa mama wayarta ta kwanta, zuciyarta na cigaba da ƙuna, da ta tuna kallon da ake yi mata sai ta ji ranta ya sake ɓaci fiye da da.