Kanwar maza Book 3 and 4 Complete - Chapter 8
Kanwar maza Book 3 and 4 Complete Chapter 8: Kanwar maza Book 3 and 4 Complete Chapter 8. "Ba ta sani ba, idan aka kai ƙarata ina gidan, a gabanta mama…
3,361 words
"Ba ta sani ba, idan aka kai ƙarata ina gidan, a gabanta mama zata bani rashin gaskiya, duk da abun da ta yi mini, zuwa yanzu kuwa na san ta tafi, in koma gida a haɗani da mai sunan baba, ya bani gwale-gwale"
Dariya habiba ta yi ta ce "Wato ke har ma kin san me za ayi miki, ina yaya Aliyu?"
Rumaisa ta yi mata kallon ƙasan ido ta ce "Yana makaranta, in ce kina nemansa ne?"
Habiba ta waro ido ta ce "Ke a'a, kawai dai tambayarsa na yi"
"Meyasa duk cikin yayyena shi ki ka sani?"
Habiba ta ce "Bakomai, ya na da kirki ne"
Rumaisa kawai ta yi dariya, tana lissafa yadda zata wanye da mama idan ta je gida.
Mama kuwa sai kallon agogo take yi, tana lissafa, ina rumaisa ta tafi haka? Ta ƙi dawowa, zuciyarta ta bata saboda abun da ta aikata ne ya sanya ta fece.
Kasancewar azahar ta yi, kuma juma'a ce ya sanya ƴan samarin mama dawowa gida, domin shirin masallaci, kuma aka yi sa'a ana public holiday, rumaisa ba makaranta ta je ba.
Faɗan Abdallah mama ta jiyo, yana faɗin "Uban waye ya taɓa mini kayan zanena, bana son rashin mutunci, Huzaifa ban hanaku taɓa mini kaya ba?" Huzaifa ya ce "Ni na iya amfani da wannan abubuwan naka ne? Sai dai ko Yasir"
Yasir ya tari numfashin Huzaifa ta hanyar cewa "Saboda ni ka raina ba, yaushe na zauna a gidan balle na taɓa masa kaya".
Mama ta fita tsakar gida ta ce "Ba aikin kowa bane, rumaisa ce ta taɓa maka, ita ta shiga ɗakin ta yi shiru, ita ce ba wani ba".
"Tana ina, sai ta ci ubanta yau sai na zaneta, har da gum ɗina ta buɗe ta bar mini a buɗe"
"Hmm, wannan yarinyar ai sai fatan shiriya, ina fatan Allah ya sanya auren nan ne mafi alkhairi, ko yau aka ce za ayi zance a ɗaura su tafi da ita"
Abdallah ya ce "Tana ina?"
Mama ta ce "Ina na sani, ta yi wata aika-aikar ta gudu, ban ma san ta fita ba".
Yasir ya ce "Kai wannan yarinya, Allah ya yi mata maganin abun da yake damunta yake sanyata rashin ji".
Rumaisa ba ta tashi tafiya gida ba, sai da unguwa ta yi tsit, duk an tafi masallaci, sannan ta nufo gida, cikin shirin karɓar kowane irin hukunci za a yanke mata.
Da sallama ta shiga gidan, ta yi sa'a mama tana salla, ta lallaɓa ta shiga ɗakin ta zauna, tana jiran mama ta idar, ta shirga mata ƙaryar da zata kare kanta.
Mama tana jin motsin rumaisa, amma ta shareta, ko da ta idar da sallar ma ta yi lazumi, ba ta tankawa rumaisa ba.
Cikin tsoro rumaisa ta ce "Mama" banza tayi da ita ta shige uwar ɗaki ta bar rumaisa.
Tun rumaisa tana ɗar-ɗar har ta ɗan saki jikinta, da ta ga mama ba ta da niyyar kulata. Sai dai ba ta ankara ba, mama ta shammaceta, ta janyota ta din ga ɗirka mata dundu.
Ihu rumaisa take yi, tana neman agaji rabon da mama ta daketa har ta manta.
Tun daga waje Yaya Abubakar ya jiyo ihun rumaisa, a soro ya yasar da sallaya, ya shiga da gudu, ya tarar da mama ta samu mafici, tana jibgar rumaisa tana yi tana haɗawa da hannunta.
Ai da hanzari ya ƙwaci rumaisa yana faɗin mama lafiya.
"Rabu da ni, yau yarinyar nan ta kaini bango, rumaisa a rayuwarta ba zata bari na huta ba, daga wannan sai wancan, gidan ubanwa ki ka tafi?"
Cikin kuka rumaisa ta ce "Gidansu habiba"
"Gidansu habiba gidan ubanki ne? Wato kin san abun da ki ka aikata ko?, To fita ki je ki bata haƙuri, ki cire takardar da ki ka liƙe mata a ƙofar gida, tun kan na murɗe miki wuya ki mutu in huta, da ɗaukar maganar da ki ke yi, kullum nike nan cikin bayar da haƙuri da faɗa da mutane saboda ke? Bari na kira babar adam ɗin a waya, idan sun shirya ko jibi su zo a ɗaura auren nan na huta na gaji" Rumaisa ta yi fici-fici da ido tana kuka.
"Ba zaki fice ki je ki bata haƙuri, ki cire abun da ki ka liƙa mata ba?" Ruma ta fita da sauri, tana jin haushin sake kai ƙararta da matar ta yi.
Ta je ta yi iya ƙoƙarin ta, wurin cire cardboard paper da ta yi zanen a jiki, amma gum ɗin da ta yi amfani da shi ya kama sosai, dan haka ta samo wata ƙusa, ta dinga durzawa takardar, ta haɗa da sabon fentin da aka yi wa ƙofar duk ta kankare abun ta, sannan ta shiga cikin gidan matar.
Ta tsaya daga soro ta yi sallama, matar ta amsa sannan ta fito, ta sakawa bakinta da goshinta shanshanbale, in da rumaisa ta fasa mata da dutse.
"Kin kai ƙarata, mama ta ce sai na zo na baki haƙuri, na cire takardar da na saka miki, na cire takarda, idan ki ka kuma kai ƙarata zan yi miki abun da baki zata ba, kuma wallahi ban yafe miki ba sharrin da ki ka yi mini, wuta balbalin bala'i, idan baki nemi yafiyata ba, sai kin ga abun da Allah zai yi miki, kayan da ki ke sayarwa ma sai an daina siya" tana gama maganar ta juya ta tafi.
Da sauri ta biyo bayan rumaisa, sai dai tana zuwa ta tarar da sabuwar ta'asar da rumaisa ta ƙyanƙyasa mata a ƙofar gida, ta kankare tsakiyar ƙofar da ƙusa, duk fentin ya fita ga sauran takardar ba ta gama fita ba, gaba ɗaya ta sauya fasalin ƙofar.
"Na shiga uku ni Jamila, wace irin masifa ce wannan, fentin ƙofar da bai fi sati da yi ba ki ka dirje?".
Rumaisa ta waiwayo ta kalleta ta ce "Idan baki gaji ba, yanzu ma ki je ki kai ƙarata, zaki sha mamakin abun da zan yi miki next"
Ta shige gida tana sunkuyar da kai, mama ta kalleta a fusace ta ce "Kin bata haƙurin ko kuwa?"
"Na bata" ta amsa tana sunkuyar da kai.
Aliyu ya kalli rumaisa ya ce "Allah ya shiryeki ruma, ke ko gajiya da ɗaukar magana ba kya yi, kullum ayi ta yi miki faɗa, daɗi yake yi miki ko?" Ta girgiza kai alamar a'a.
"Zo ki karɓi kuɗin nan ki sayo mini milo a kantin malam lawan, zan sha shayi bana son cin abinci" kallon yaya Aliyu ta yi, kamar tana hararsa ya ce "Ni ki ke yi wa wannan kallon, ko ba zaki ba?" Ta durƙusa ta ɗauki kuɗin, ya ce "Ki taho da manja kwalba ɗaya, na ga wanda muke da shi ya kusa ƙarewa".
Ita dai ba ta amsa masa ba, ta fice ko da ta fita a ƙofar gida ta hangi shamsiyya da mijinta, suna duba ƙofarsu da ta dirje, ba ta kula su ba ta tafi shagon.
Malam lawan mai kanti, yana ta yi mata wasa yana tsokanarta, amma ta share shi, ya auna mata manjanta, ta fito. Sai dai tana fitowa ta yi karo da wani tantirin ɗan daba da ya addabi unguwarsu, wanda har kisan kai yayi, amma aka sake shi.
Ya kalli rumaisa ya ce "Ke, karɓo mini sigari a cikin shagon nan"
Tsaki ta yi, zata wuce, ya sake daka mata tsawa ya ce "Ke, na ce ki karɓo mini sigari a cikin shagon nan"
"Na yi maka kama da ƴar iska, ni ce ma zan taɓa sigari saboda wulaƙanci, to ba zan karɓo ba" ware jajayen idanunsa ya yi a kan rumaisa, a hargitse malam lawan ya ce "Yi haƙuri bari na miƙo maka".
Cikin muryar mashaya, ɗan daban da ake cewa ɗan kada ya ce "Ni ki ke gayawa haka?".
Fitowa ta yi zata wuce shi, ta tafi, amma ya sanya ƙafarsa ya kwashe na rumaisa, a take kuwa ta faɗi ƙasa, manjan hannunta ya fashe, ta datse goshi.
Idan da abun da rumaisa ta tsana, bai wuce ganin jini a jikinta ba, jiki na rawa ta tashi ta kalleshi, ya kalleta ya ce "Sai na tsarge hanjinki da wuƙa, na kashe banza ni zaki nemi ki zaga wata jagwal da ke"
Cikin hanzari malam lawan da sauran mutane suka fara lallaɓa ɗan kada suna bashi haƙuri, rumaisa ta shiga cikin shagon, ta dumbuzo ƙwan da ke kan teburi, ta fito ta shiga jifan ɗan kada da shi.
Rikicewa malam lawan yayi, dan yanzu aka sauke ƙwan ko lissafawa ba ayi ba, ji ta yi zuciyarta na tafasa, ta juya da gudu ta tafi gida.
Aliyu na ganinta ya ƙare mata kallo ya ce "Meye haka?" Cikin kuka ta kwashe komai ta gaya masa, nan da nan ransa ya ɓaci ya ce "Mu je" mama na banɗaki tana gyaran murya, amma Aliyu ya ja rumaisa suka yi waje.
A ƙofar shagon suka tarar da ɗan kada, har ya karɓi sigarinsa ya fara sha, malam lawan kuma yana ta masifa, yana sai ya je gidansu rumaisa an biya shi, shi kansa ɗan kada yayi alwashin sai ya kashe rumaisa, saboda wulaƙancin da ta yi masa,ta din ga jifansa da ƙwai.
Idan da abun da samarin gidan maman suka tsana, bai wuce taɓa Wannan tilon yarinyar ba, dan haka a zafafe Aliyu ya ƙarasa, yana zuwa ba tambayar ba'asi ya ci kwalar ɗan kada, ya shiga kifa masa mari.
Kokawa ta kacame, ga ɗan kada a buge, dan haka ya kasa wani abun arziki, Aliyu ya din ga haɗa masa naushi.
Da ƙyar mutane suka shiga tsakani, ana rirriƙe ɗan kada yana rantsuwa sai ya kashe Aliyu.
Mama kuwa a gigice ta fito daga banɗaki, jin wanda rumaisa ta tsokano, dan babu wanda bai san yadda ya addabi unguwarsu ba. Mama ta kira mai sunan baba a waya, ta ce masa duk abun da yake ya bari ya tafi shagon malam lawan, Aliyu ya fita ba ta san mai zai aikata ba.
Aliyu kuwa ya kalli ɗan kada ya ce "Jinina da na zuriyar gidanmu ya fi ƙarfin mutum irinka, duk wani hauka da iskanci da kake ji da shi a unguwar nan ƙyaleka aka yi, ƙanwata ta fi ƙarfin wawan mutum irinka su cutar da ita"
Malam lawan ya ce "Wai Meye haka ne Aliyu, ina nan aka sace ƙanwar ta ku me ku ka yi, sai yanzu zaku haddasa mana masifa a cikin unguwa"
"Wallahi malam lawan, duk shekarun da muka yi tare a unguwar nan, idan ka taɓa rumaisa sai na tuɓe na yi maka bugun sakwara, saceta kuma da aka yi wannan ƙaddararta ce, ba yadda muka iya"
Rumaisa ta riƙe hannun Aliyu ta ce "Yaya mu tafi gida"
Da ƙyar rumaisa ta riƙe hannunsa, suka juya suka fara tafiya, sai dai ana sakin mai kada, ya zare wuƙa ya nufi Aliyu da ita gadan-gadan yana ihu.
Ihu rumaisa ta saka ganin wuƙa tsirarata, wuƙa ba ta wasa ba an nufo yaya Aliyunta da ita, wanda ba da tabbacin ita aka nufo ko shi. Aliyu ya hankaɗeta, ya kuma riƙe mai kada suka hau kokawa ga wuƙa tsirarta.
Aliyu ya danne mai kada a ƙasa, ya ɗau wuƙar ya ce sai ya yankashi da ita a wurin.
Nan aka din ga kokowa da Aliyu, aka kasa ƙwace wuƙa.
Rumaisa ta ce "Yaya Aliyu kar ka yi kisan kai, amma dai ka yi masa dukan tsiya".
Cikin takunsa na isa da taƙama, ya din ga ture dandazon mutane, ya ƙarasa in da Aliyu yake kan mai kada ana fama da shi, ya riƙe hannun Aliyu mai wuƙar ya murɗa, ya jefar da wuƙar, sannan ya ɗago shi daga kan mai kada ya tsayar da shi a kan ƙafafuwan sa ya Kalleshi ya ce "Meya haka? Shaye-shayen kai ma ka fara ne?" Ya kalli rumaisa ya ce "Duk saboda ke ko? Sai ku wuce mu tafi ai".
Daga kwance mai kada ya ce "Na rantse da girman Allah, idan har ina yawo kana yawo a unguwar nan, sai na kasheka na kashe matsiyaciyar yarinyar nan, na ga uban waye gatanku"
Aliyu ya sake tunzura, jijiyoyin kansa suka kumbura, mai sunan baba ya kalli mai kada ya ce "Idan kana zubar da jini a unguwar nan kai da yaranka, ana tsoronku, kar ka ratso ta gidanmu, wallahi duk wanda ka zubarwa da jini in dai ɗan gidanmu ne, kaima sai na zubar da naka, ka kiyaye" Ya riƙe rigar Aliyu, hannu ɗaya ya tankaɗa ƙeyar rumaisa zuwa gida.
Mutane wasu har da shewa, abun ya burgesu, kaf unguwar nan babu gidan da suke da haɗin kai da nunawa juna soyayya kamar gidansu rumaisa.
A gigice mama ta tashi da suka shigo, ta ga jikin Aliyu duk ƙasa, rumaisa kuma da fasashshen goshi, duk da ba ta zubar da jini da yawa ba.
"Mai sunan baba, maiyafaru?"
"Kar ki damu, ba abun da ya faru"
Mama ta riƙe Aliyu da yake huci ta ce "Ina fatan dai ba abun da ya sameka ko?" Ya girgiza mata kai alamar a'a.
Mama ta ce "Duk saboda wannan jairar yarinyar ne, da ba zata bari a zauna lafiya ba? Ina ke ina faɗa da gagararren ɗan daba saboda ɗorawa kai bala'i" Mama ta yi maganar tana ƙoƙarin kai mata duka, amma mai sunan baba ya tare ya ce "Ki ƙyaleta please, baki ga ta ji rauni a goshi ba, ki yi haƙuri"
Mai sunan baba ya sakata a gaba, ya kai ta chemist, aka duba goshin, Allah ya taimaketa babu ɗinki, suka dawo gida.
Mama ta kai ƙarshen ƙulewa da rumaisa yau, ta din ga yi wa ƴan mazan faɗa a kan biye mata wurin tare mata faɗa.
Kasancewar maƙwabcin su rumaisa malam shamsu, yana cikin ƴan kwamitin unguwa, shi ne mataimakin ƴan ƙato da gora, yana dawowa aka sanar masa da abun da ya faru a unguwar, nan da ya ji ya samu damar rama wulaƙancin da rumaisa da yayyenta suka yi masa, kai tsaye ya je ya sanar da ƴan sanda abun da ya faru.
Mama har ta bar sallahun a rufe gida, ƴan sanda suka yi sallama, suka ce sun zo tafiya da Aliyu.
Duk yadda aka so sasanta lamarin, abu ya gagara, ga Abubakar ya koma makaranta, Mai sunan baba da Usman suka bi bayansu, amma har wurin sha ɗayan dare, ƴan sanda suka ƙi bayar da Aliyu, ƙarshe ma suka sanar da su cewa sashin kula da manyan laifuka na bamfai zasu turasu, tun da Aliyu ya yi iƙrarin kisan kai.
Haka mai sunan baba suka koma gida, jiki a sanyaye, mama ta rasa in da zata saka kanta saboda tsananin damuwa da tashin hankali, tare da ɗora zargin komai a kan rumaisa.
Adam kuwa bayan ya kammala cin abinci, ya tashi ya yi wa ammi sallama, ammi ta ce "Yauwwa, na ce ba" Adam ya ɗan tsaya yana kallon ammi.
"Dan Allah gobe in Allah ya kaimu, tun da da wuri zaka fita, kuma ka ce zaka je gidan gona, dama unguwar su matarka ne, zan baka saƙo ka kai wa rumaisa"
Adam ya kalli Ammi ya ce "Matata kuma? Kuma ni zan kai ssƙon?"
"Ban isa ba kenan?"
Ya ce "A'a tare da sunkuyar da kai"
"A yanzu kana da wata matar da ta wuce rumaisa ne? Zaka kai mata saƙo, kallonka kawai nake yi, har na je wurin turaki na dawo ba ka tambayi yaya muka yi ba, kuma ya zama dole ka din ga zuwa wurinta, saboda ta saki jiki da kai, kuma ka daina yi mata wannan muzuran"
Adam ya jinjina kai yana wasa da yastun hannunsa.
"Je ka, da safe in Allah ya kaimu kan ka wuce, ka biyo"
Bai ce komai ba ya fice.
Ayshercool.
Chat me on what's app, to subscribes yours 08081012143 *PAID BOOK NE, ₦500 NE VIA 0009450228, AISHA ADAM JAIZ BANK SAI SHAIDAR BIYA TA, 08081012143*
Gaba ɗaya ji yake duk wani girma da mutuncinsa sun zube, kamar shi ace wai zai je wurin wata ƴar yayyiyar yarinya yayi zance da ita, wai zai aureta, ko aurensa na fari aisha ta kammala deegree ya aureta, wannan shi ba ya tunanin ko primary ma ta gama.
Mama kuwa kwana ta yi ba barci, sai addu'a kawai da take yi, ji take tamkar ta rufe rumaisan da duka, dan bayan gama ƴan koke-kokenta tuntsirewa ta yi ta hau bacci. Mama ta kalleta ta girgiza kai ta ce "Allah ya shiryeki, ya ganar da ke"
Da asubar fari, bayan rumaisa ta idar salla, ta tafi ɗakin su mai sunan baba ta yi sallama, suka amsa mata. Ta leƙa ta ce "Yaya usy jiya kun dawo da yaya aliyun?"
Abdallah ya ce "Wuce ki bawa mutane wuri, duk ba ke ki ka janyo ba, karfa kawai"
Mai sunan baba ya kalli Abdallah ya ce "Kar ka kuma gaya mata haka, bai dawo ba a can ya kwana, duk saboda ke, gaba idan ki ka sake, ke zan kai musu in karɓo shi, dan mun fi son sa a kan ki, mara kai kawai"
Sumi-sumi ta juyo za ta fito, ta fuskanci kowa haushinta yake ji yau.
Usman ya ce "Wallahi yau da na ga malam shamsun nan a masallacin asuba, ji na yi kamar na ɗaga shi na wurga shi cikin kwalbati, shi ne babban munafukin da ya je ya kai wa ƴan sanda"
Mai sunan baba ya ce "Ba ruwanka da shi, ku bari mu kashe wannan case ɗin tukuna".
Abdallah ya ce "Ni malam lawan mai shago na kusa kifawa mari, ya biyo ni wai rumaisa ta yi masa asarar ƙwai cret huɗu, wai in zo in biya, na ce masa sai dai mu yi kokowa ya ɗiba, gaba ɗaya mutane fuska biyu ce da su".
Rumaisa da take tsaye tana jin su da sauri ta ce "Wallahi ko kret ɗaya bai yi ba, bai fi guda shida ba fa"
"Au laɓe ki ke yi mana ko?" Abdallah ya faɗa yana nemo abun duka.
Da gudu ta shige ɗakin mama, sai dai irin kallon da maman ta yi mata, ya sanya ta rasa in da zata saka ranta.
Haka ta tsuguna ta takure, da duku-dukun mama ta shiga kitchen, ta girka abinci, gari na yin haske, ta ce lallai mai sunan baba ya taso su tafi station ɗin.
Mai sunan baba ya ce "Mama, idan kin je wurin nan babu abun da zaki iya a kai, ki bari zan je ni da Usman"
Mama ta ce "Ni dai ka ƙyaleni na je na ga a yaya ya kwana?"
"Lafiya ƙalau ya kwana, kuma in sha Allah zamu dawo miki da shi, ki yi haƙuri" da ƙyar mama ta yadda, ta basu abincin suka tafi.
Rumaisa ta ce ita ba zata tafi makaranta ba, sai yaya Aliyu ya dawo.
Mama ta ce "Aikuwa ba ki isa ba, sai kin shirya kin tafi, wataƙila kan ki dawo na huce, dan da na kalleki haushi nake ji, haka kurum saboda ke kin saka an kulle mini ɗa, mara jin magana" shiru rumaisa ta yi tana kallon mama, kenan yanzu mama ta daina son ta?.
Jiki a sanyaye ta shirya, mama ta hanata kuɗin makaranta, ba babban abun da ya sake ƙular da mama, irin yadda rumaisan ta zauna ta naɗi abincinta, kamar abun bai dameta ba sosai.
Haka ta tafi makaranta, tana tunani kala-kala, amma har ga Allah abun ya dameta.
Kamar yadda ammi ta buƙata, da safe Adam ya je gidan, a lokacin su iman duk sun tafi makaranta.
Ya ɗau sabir yana yi masa wasa, sai dai ƙememe yaron nan yaƙi dariya, sai bin sa da yake da kallo.
Ammi ta fito suka gaisa, ta ce "Yanzu wurin aikin zaka tafi?"
"Eh, na biyo na karɓi saƙon ne".
Ammi ta ce "To, tun da baka tambayeni ba, ni bari na gaya maka yadda muka yi da turaki".
Ya sunkuyar da kai yana wasa da hannun sabir.
"Mun tattauna da shi, ya ce mini in bari ya dawo daga umara, zai yi magana da su wambai, dan na san akwai ƙalubale, tun da rumaisa ba jinin sarauta ba ce, ko ƴar wani sananne ba, dan haka zai yi muku Addu'a a can, da ya dawo aka daidaita kuɗin aure za'a kai, bayan salla idan Allah ya kaimu za ayi"
"To, Allah ya wuce mana gaba".