Karfe a wuta book 2 complete novel - Chapter 104
Karfe a wuta book 2 complete novel Chapter 104: Karfe a wuta book 2 complete novel Chapter 104. Viper ya yi wata irin dariya ya ce "Ko a cikin sojoji, irin…
4,483 words
Viper ya yi wata irin dariya ya ce "Ko a cikin sojoji, irin aikinmu na musamman ne, kuma mai hatsarin gaske, ina da salary mai kyau, zan zaɓi garin da nake so a bani gida, kuma za a bani abin hawa, ba a buƙatar rashin gskiya ko a samu irinmu da halin cin amanar ƙasa, idan aka kama mu da haka, babu shari'a kisan kai ne kawai. Shiyasa irinmu a sojoji ba su da yawa ko kaɗan"
Cikin mamaki Abbu ya ce "Wai bayan fitowar ka har ka yi training ɗin ko kuwa? Kuma wane iri ne aikin naku a sojoji?"
"Ina gaya maka kashe ni za ayi, ba a faɗa kawai dai ka saka a zuciyarka ɗanka soja ne, mai muhimmancin gaske ga ƙasarsa, kuma a kowane lokaci zaka iya rasa shi, dan haka ka yi mini addu'a kawai"
Abbu ya ce "In sha Allah sai ka yi retire da kanka daga aiki, ba za a kashe ka ba" haka Abbu ya din ga jan sa da hira, har lokacin salla ya ƙarato.
Abbu ya ɗaukko masa sababin kayan kar, dark blue ɗin shadda, riga da wando, da hula. Ga sabon agogo da takalmi.
Ya ce "Wannan fa?"
Abbu ya ce "Wurin ɗaurin aure zamu je, ba na son yawon da ku ke yi da ƙanan kayan nan, kamar ba yaran hausawa ba, dan haka su zaka saka"
Shafa kayan ya yi, yana tuna abar ƙaunarsa, Jauhar, a lokacin da ta bashi kyautar kaya ranar sallar idin ƙaramar salla.
Su Walid ne suka yi sallama a waje, Abbu ya ce ace su shigo, suka shigo sanye da fararen kaya, liti ya riƙo hularsa a hannu.
Abbu ya ce "Abdallah, ya ka cire hular ka ga yadda ka yi kyau a cikin kayan kuwa?"
Ya ce "Abbu, hular ce ta ɗame mini ƙeya nake ta gumi shi ne na cire"
"Ai fa rashin sabo ne"
"Mai zamani, Abbu ne fa ya ɗinka mana kaya" liti yayi maganar yana nuna masa kayan jikinsa.
Walid ya ce "Mai zamani haka ka ke kyakykyawa, rabon da ka yi kyau kamar haka, tun ranar aurenka da marigayyiya"
Abbu ya gyarawa Walid zaman tasa hular, ya ce "Yauwwa ko ku fa 'yan samari, Allah ya nuna mini aurenku duka" suka kasa cewa Amin.
Wani farinciki ne ya mamaye zuciyar Viper, ganin yadda Abbu yake nuna wa su Liti ƙauna, wanda ya san duk dan saboda shi ne, shi yanzu a duniya abin da zaka yi masa, ka saka shi farinciki, ka so mutanen nan uku kamar yadda yake ƙaunar su, ya san a duniya ba shi da abin biyansu.
Haka suka ɗinguma a mota, suka tafi masallaci, domin yin salla da halartar ɗaurin Alhaji mu'azzam.
A sahu ɗaya suka yi salla da Alhaji mu'zzam, suna ta yi masa Allah ya sanya alkhairi.
Bayan an idar da salla, babban abin da ya ba wa Viper mamaki, bai wuce ganin abokan Abbu da yawa a wurin ba, da kuma wasu daga cikin 'yan uwansa, bai kawo komai a ransa ba, suka gaggaisa, suna taya shi murnar wanke shi da kotu tayi, wasu kuma na zuzuta kyan da yayi, wasu kuma suna yi masa Allah ya sanya alkhairi, shi dai duk bai gane kan abin ba, ana ta ɗaura aure, aka zo kan na Alhaji mu'azzam, aka ɗaura aurensa da Hafsa. Bayan an kammala na su, aka nemi waliyayyan Al'amin, saroro yayi yana kallonsu, ganin Baba yana kallonsa yana murmushi, haka Major. Ya waiwaya, har da su doctor Muktar, da Abdul yasar a wurin. Sai da aka ɗaura aurensa da Nabila, sannan ya fuskanci abin da yake faruwa.
Walid ya cire hular Viper, ya shafa kansa ya ce "Angon Nabila ka sha ƙamshi, yau dai Allah ya yi Allah ya sanya alkhairi"
Yayi saroro yana kallonsu, liti ya ce "Mun iya Suprise ko? Sai ka bamu tukuci yasin, idan ka cire kayan nan ni zaka bawa, in saka ranar auren Walidi, ko Allah ya sakani a damshinku"
"Mai laya yaushe aka shirya wannan abin, ita Nabilan ta amince ne?"
Liti ya ce "Oho muku, mu dai an haɗa kai da mu, an ƙulla sunnar ma'aiki, ai yanzu rumfar shayi har da banner dalilin aure zan saka. Idan aka biye muku, wahalar da mu kawai zaku yi ta yi, yanzu sai ku ƙarata ku sasanta kanku"
Aka fito daga masallaci, Viper sai jin sa yake tamkar ba shi ba, abin kamar almara.
Alhaji mu'azzam ya ƙarasa ya miƙa wa Viper hannu ya ce "Na haƙura na janye, na kuma yarda Jauhar taka ce, Nabila ma taka ce, ba a takara da kai Viper, duk da ka fuskanci ƙalubalen rayuwa da yawa, amma ina da yaƙinin Allah yana sonka, yadda yake tafiyar da lamuran rayuwarka. Ina yi maka fatan alkhairi, Allah ya baku zaman lafiya mai ɗorewa"
Viper ya riƙe hannun Alhaji mu'azzam, amma ya kasa magana sam.
Major ma zagayo wa yayi, ya dafa kafaɗar Viper, ya ce "Yadda na samu labarin ka riƙe Jauhar amana, dan Allah ga 'yar uwatta nan ma, Allah shi ya san dalilin da ya sanya ya karɓi jauhar a lokacin da ka ke matsanancin son ta, ya musanya maka da 'yar uwatta, wataƙila da bai ɗauke Jauhar ba, babu yadda za ayi Nabila ta ga mahaifinta, komai sila ne, kuma duk abin da Allah ya yi dai-dai ne, ba a tambayarsa dan me? Allah ya baku zaman lafiya"
Viper ya risunar da kai ya ce "In sha Allah Abba, na gode sosai"
Abbu ma ƙarasowa yayi, ya ce "Al'amin, a karo na biyu na sake nema maka auren 'ya, kuma Alhaji Bashir ya sake bamu, a rana mai kamar irin ta yau aka ɗaura maka aure da jauhar, yau ba ta raye, an sake ɗaura maka aure da Nabila, dan Allah Al'amin ka riƙe musu 'ya da mutunci da amana"
Kawai ya fara zubar da hawaye, duk da yayi iya ƙoƙarin sa wurin mayar da hawayen, amma abu ya gagara, kawai ya lumshe idanunsa ya basu damar su zuba.
Major ne ya ce "Ya haka kuma? Amare ke kuka ba angwaye ba, dan Allah kar ka bayar da mazaje mana, soja ne fa kai".
Jiki a sanyaye Walid ya ce "Ai a duk lokacin da za ayi wani abu da zai tuna masa da Jauhar duk taurin zuciyar sa da ƙarfin halinsa sai ya yi kuka, haryanzu ya kasa jurewa, duk yadda za a bayar da labarin yadda suka rayu, idan ba wanda ya gani ba ba zai gane ba"
Major ya ja shi ya bashi handkerchief ɗin sa, yana duddukan kafaɗarsa yana rarrashinsa, Abbu ya ce "Al'amin dole fa ka yi haƙuri, kayi haƙuri, duk lokacin da ka tuna Jauhar ka yi mata addu'a. Sannan dole ka koyi danne zuciyarka, idan ba haka ba, zaka iya sanya wa Nabila kishin 'yar uwatta, zuciya ba ta da ƙashi".
Kallonsu kawai yake yi, idan ya ce ba ya murna da farincikin wannan auren, ƙarya yake yi, amma zuciyarsa ta tsinke, da yaga yana sake ɗaura wani auren, Jauhar ɗin sa ba ta duniya, a lokacin da yake tare da ita, gani yake duk wani leƙe-leƙe da ake faɗa na namiji a kan mace, itakaɗai ta ishe shi rayuwa.
Suka kewaye shi suna ta rarrashin sa, abin da ya ƙara yi masa daɗi da sanya shi farinciki, bai wuce yadda shi da ake ƙyama a da, amma aka tara wannan mutanen saboda shi, kuma duk suka kewaye shi, kowa yana ƙoƙarin rarashin sa, lallai babu abin da ya fi zama mutum na gari.
Alhaji mu'azzam ya ce "Ko sai mun dangana da wurin amaryar za ta rarrashe shi? Dan naga tafi kowa iya shawo kansa"
Major ya ce "A'a bar amaryar nan, ka san ba ta san da bikin ba sai jiya da sumayya ta sanar da daddare, can na baro ta a falo tana kuka, fushi ma take da ni, ina ga ranar Litinin za a kawo mini sammaci daga kotu, na taɓa masu ƙasa na yi wa barrister auren dole, amma na gaya mata ni da kai zata kama, tun da tare muka yi laifin" yayi maganar yana nuna Alhaji Bashir .
Suka yi dariya baki ɗaya. Duk da a ƙurarren lokaci Sumayya ta sanar da ɗaurin auren Nabila, Auren ya samu hakarta ɗaruruwan jama'a, manya da ƙananan mutane, mussaman waɗanda suke supporting ayyukanta, har da wakilai daga gidan gwamnati, manyan lauyoyi da baristoci, har da kwamishinan shari'a, da alƙalin alƙalai na jiha. Da yawa saura kwana biyu uku suka samu invitation ɗin, kuma an halarta sosai da sosai.
Ba ƙaramin daɗ Major ya ji ba, ganin irin jama'ar da Nabila ta tara, a ransa yayi mata addu'a Allah ya sa yadda ta riƙe gaskiya a kan aikinta, da ta tara wannan jama'ar, Allah ya sa ranar mutuwarta ta tara fiye da haka.
Shi kansa Babanta ya yi farinciki, mussman yadda ake ta yabonta, da jinjinawa yadda ta zamo matashiyar yarinya, mara tsoro da jajircewa a aiki.
Nabila kuwa har Abba ya tashi ya shiga bedroom ɗin sa, yayi wankansa ya shirya tafiya ɗaurin aure, tana bayan kujera a zaune tana kuka.
Gaba ɗaya shi dariya ma take bashi, dan haryanzu kallon yarinya ƙarama sosai yake yi wa Nabila.
Baba magajiya ta je tana rangaɗa mata guɗa a ka, amma tana guɗa Nabila ranta na ƙara ɓaci, baba magajiya har da rawa, da yi mata waƙoƙin amare irin na da.
Nabila ta koma ɗakinta, sai ga kiran Sumayya, ta ɗaga wayar, Sumayya ta kwashe da dariya tana amarya ba kya laifi.
"Da ke aka haɗa baki aka yi mini haka ko Sumayya, ki je kanki ki ka yi wa" Sumayya dariya har da tuntsurawa ta san a rina, rigima da daru, za a sha su akan abin da aka yi wa Nabila.
**** Maman ramma kuwa ta tattara ramma da Abdul ta saka musu ido, dan ta fara jin nauyin sa, irin yadda yake hidima da rammar, a da tayi zaton ƙoƙarin sayeta yake son yi da abin duniya, amma sai taga ba haka ba, zunzurutun soyayyar kawai yake yi wa ramman.
Yau daga wurin ɗaurin auren Viper, gidansu ramman ya wuce.
Tsayawa ramma tayi tana ƙare masa kallo ta ce "Ka ga yadda ka yi kyau kuwa?"
"Daga wurin ɗaurin auren yayanki nake"
Ramma ta ce "Haka mama take gaya mini, ai shekaranjiya babansa ya zo, ya daɗe a gidan nan suna hira da mama, yake gaya mata halin da ake ciki, yau za a ɗaura musu aure, amma daga ita har shi ba wanda ya sani, na ce ikon Allah kamar film"
"Wallahi rahama ya bani tausayi, kin san duk wannan muzuran da yake yi, da shan ƙamshi, amma ya din ga kuka a wurin ɗaurin auren nan, kamar yaro ƙarami, wai ashe wadda ta rasun ya tuna, wallahi sai da na yi masa kuka, muktar ya ce mini duk yadda nake sonki, da nuna miki kulawa, ba zai kai kwatantkwacin son da yake yi mata ba, da na tuna mahaifina ne sila, wallahi sai na rasa in da zan saka raina. Ya ma yi ƙoƙari yake ɗan iya kula ni a 'yan kwanakin nan, dan hau har gaisawa muka yi"
Ramma ta ce "Yaya zamu yi, ai ƙaddara ta rigayi fata sai addu'a"
Sai da aka yi sati guda, sannan Alhaji mu'azzam tare da hafsa suka ɗaga zuwa babban birnin tarayya Abuja.
Gidan Hafsat na Abuja mai kyawun gaske, ya fi wanda ta zauna da ita da uwargidansa a can Kano, sai dai taƙi sakin jiki da shi. Jirgin yamma suka bi, gefin magariba suka sauka.
Da ya ɗan matsa kusa da ita, sai ta maze ta matsa tana haɗe rai, dan haka ya rabu da ita.
Da daddare da kyar ta yadda ta ci abinci, shi ma ba da yawa ba.
Ya riƙo hannunta zata ƙwace, ya riƙe gam, ya ce "Haba hafsatuna, ni ne fa, ki yi haƙuri dan Allah, ki bani dama na gyara kuskuren da nayi miki a baya, Please" tayi shiru, ba ta ce masa komai ba, saboda ta kasa manta mummunan halin da ta faɗa a wancan karon a dalilin aurensa.
Da kyar ya lallaɓata, kamar budurwar da ba ta san komai ba, sai dai a wannan karon ita kanta ta san da banbanci, dan a wacan karon, banda tsabar kayan tsubbu, da abubuwan da ba ta san ko na menene ba, da su aka yi mata gyaran jikinta.
A wannan karon kuwa, ta san da banbanci, domin kuwa maman dr. Ta kankarota ta kankaro martabarta a idon mijinta, dan a wancan karon ko maganin sanyi ba ta yi amfani da shi ba, sai kayan tsubbu da abubuwan da ƙawaye suka din ga ba ta shawara a kai.
Shi kansa yadda ya yi appreciating ɗin ta a wannan karon, ya sha bamban da lokacin da tana budurwa.
(07069711327 ga masu buƙatar kayanta, su na iya tuntuɓarta kai tsaye, she's always available for you)
*****
Viper kuwa kimanin sati biyu kenan, tun da Allah ya sa aka ɗaura aurensa da Nabil, babu wanda ya nemi wani daga shi har ita, kuma hakan ya ɓatawa kowannensu rai.
Abba ya sanar mata, da babu ita babu yawo, idan ba wurin aiki ba, dole sai da izinin Al'amin.
Rashin kiranta da bai yi a waya ba, ya tabbatar mata da sam ba ya ƙaunarta, auren dolen ne dai kawai, shi ma ya nemi ya aureta ne kawai saboda mafitarsa.
Kasancewar hidimar bikinsa, tare da na Walid za a haɗa, ya sanya yayi delay na komawa aiki, domin sanin shirye-shirye da yakamata yayi.
Yana son ya tambayeta, abin da take buƙata na harkar biki, amma ya shareta.
Ta koma wurin aikinta, ana ta yi mata Allah ya sanya alkhairi, aka din ga tambayarta meyasa ba ta tafi hutu ba, ta ce ɗaurin aure aka yi, ba ayi biki ba.
Aka din ga bata gudunmuwar biki, ta in da ta zata, da in da ba ta ma zata ba.
Kawai tana zaune a office taga alert ɗin dubu ɗari biyar, da sunan Al'amin da komai.
Sai a lokacin ta kira wayarsa, ya ɗaga amma yayi shiru.
"Naga ka turo mini kuɗi"
"Ki fara sayen abin da ki ke buƙata na lefe, zan sake turo wasu, na san wannan ba za su isa ba".
"Ni bana so" ta faɗa a daƙile.
"Menene ba kya son?"
"Kuɗin, ni ka bani account number na dawo maka da su"
Wani malolon takaici ya ƙule masa zuciya ya ce "Bani da lokacinki, ki same ni a gidan su rahama, sai ki dawo mini da kuɗin" ya kashe wayarsa.
Ba tare da tunanin komai ba, ta miƙe ta fara harhaɗa kayanta.
Da ta isa gidan su ramam, Maman ramma ta ce "Amarya ke da kanki, ina ta cewa Aminun ya zo ya kai ni gidanku, amma haryanzu shiru"
Nabila ta ce "Dama baya nan? cewa fa yayi na zo na same shi a nan"
"A'a ya dai ce zai zo, amma bai ƙaraso ba tukuna" yanayin fuskar Nabila da ta gani babu fara'a, ya sanya ta din ga yi mata nasiha, tayi haƙuri ta rungumi mijinta su zauna lafiya kamar yadda yar uwatta tayi.
Ita kuwa Nabila gani take, ba zasu gane ba, ba su san waye Al'amin bane.
Ita a tata wautar, da gaske zuwa ta yi ta mayar masa da kuɗinsa, sam bai iya rarrashi ba, ba ta san tarko ya yi mata ba.
Awanta guda a gidan, ya zo, kuma yaƙi shigowa cikin falon, ya ce ta je ta same shi a sitting room ɗin harabar gidan.
Ta tashi ta ce "Mama ina zuwa" ta fita ta ƙarasa ɗakin.
Sai dai tana arba da shi, duk wannan fitsarar da take ji da ita, ta nemeta ta rasa, sai tsoro da fargaba da suka mamayeta. Lallai miji yafi gaban wasa.
Ya ɗago ya kalleta, doguwar riga ce a jikinta, sai mayafin rigar. Gaba ɗaya Nabila ba ta da wayo, ko kaɗan, abin da ba ta sani ba, ba wai dawo masa da kuɗi ne ya kawota ba, son ganinsa ne ya kawo ta, ba tare da ta yi lissafin hakan ba.
Ya kawar da kansa ya ci gaba da danna wayarsa.
"Ka bani account number ɗinka, na mayar maka da kuɗinka, ni bana buƙatar komai daga wurnka, ba zaka taɓa iya bani abin da nake so ba".
Ramma ta yi sallama da ƙaton faranti, shaƙe da kayan abinci, ta gaida Al'amin ya amsa, ta kalli Nabila da ke tsaye ta haɗe rai, ba ta ce komai ba ta fita.
Ta fara ƙosawa da tsayuwar da take yi, ya miƙa mata hannunsa, ba tare da ya Kalle ta ba ya ce, "Bani wayarki na saka miki account number ki dawo mini da kuɗina" babu musu ta ƙarasa ta miƙa wayar, ya yi amfani da hakan, ya janyota jikinsa.
Wata ƙaramar ƙara ta saki, jikinta ya hau tsuma, ta kalli fuskarsa, babu alamar wasa a tattare da shi, wani irin kallo yake yi mata da ba ta san a yaya zata fassara shi ba.
Ayshercool 08081012143
Sake ƙasa yayi da muryarsa, ya ce "Ina sake roƙonki, ki bani dama, kin yi mini kuskuren fahimta ne kawai, ban san yaya zan yi miki bayani ba, amma za ki ga komai a aikace"
Bakinta ta motsa za ta yi magana, amma a dole ta haɗiye maganar, biyo bayan dogon harshensa da ya saka a kan laɓɓanta.
Bayan su Walid sun fita, ya kalli liti ya ce "Ina jinka, me zaka ce mini?"
"Wai wannan farar yarinyar yar uwar Nabilan ce ne?"
"Eh"
"To kuma har muka fito ba ka yi mata magana ba, ka san dai ka fini faraa'a da kalar masu kirki"
"In yi mata magana in ce mata me? Ko dai sonta ka ke yi ne?"
"To wa ya san mini ma, amma ɗan yi mata magana, gata can sai waya take yi "
Walid ya ce "In yi mata magana in ce mata uban me? Kai ka yi mata mana, tun da sonta ka ke yi. Babanta dai tsohon soja ne, wallahi kayi masa shirme sanyawa zai yi kuratan nan, su yi maka dukan jaraba na gaya maka"
Liti ya ce "Ta Allah ba taka ba, kuma a yanzu zan nuna maka banbancina da kai" kawai ya nufi in da Walida take waya, tana ta surutu da wata ƙawarta mai kwaliya, tana son tayi booking na bikin Nabila.
Ta kammala ta juyo, ta ga Liti a tsaye.
"Sannu dai"
Ta ce "Yauwwa, ya gida ya shirye-shirye na ganku tare da wanda Arfa zata aura, ina kyautata zaton abokansa ne"
Ya girgiza mata kai ya ce "'yan uwansa ne mu"
Tayi murmushi ta ce "Masha Allah, Ubangiji Allah ya sa zamu gani"
"Amin, ashe tana da ƙanwa babba kamar ke, ai mu ita kawai muka sani"
"Ai muna da yawa ma, ba a fiye ganinmu bane, daga makaranta sai gida".
Liti ya ce "Masha Allah, ai haka ake so, ki ce tare zamu yi hada-hadar biki, to Allah ya sa a gama lafiya, sunana Abdallah"
Ta jinjina kai ta ce "To yaya Abdallah, sunana maryam ana ce mini Walida"
Walid kuwa satar kallonsu yake yi, yadda liti ya nutsu yake baza capacity a gaban budurwa, kai ba zaka ce shi ne yake wani iya shegen ba, sai gashi yana ta hira da shi da walida, abin da haryanzu Walid ba ya iya sakin jiki yayi sosai da Shahida.
Duk da Nabila ba ta saki jiki gaba ɗaya da Viper ba, amma ta ɗan ji sauƙin damuwar da take ciki, amma har a lokacin faragaba ba ta bar zuciyarta ba.
Sai da ta kwana biyu aka sallameta, ta ɗauki hutu a wurin aiki, ta ma daina fita gaba ɗaya, sosai Nabila ta zama so silent, dan ma Sumayya na tare da ita, tana ƙarfafa mata gwiwa.
Abbu suna ta shirye-shirye, suna zaune da shi da Viper da daddare, Shahida ma an gama gyara gidan da zata zauna, Abbu ya yi mata sababbin furnitures. A weekend za a kawo kayan lefe.
Viper ya dubi Abbu, yadda yake ta kashe kuɗi babu ƙaƙƙautawa, dan haka yake cewa auren yara uku zai yi. Ga Viper, ga Walid ga kuma Shahida.
"Abbu muna ta godiya Allah ya saka da alkhairi"
Abbu ya ce "Da aka yi me?"
"Kuɗin da ka ke ta kashewa a kanmu"
"Amfanin neman kenan ai Al'amin, kuma a baya ai ban yi muku ba, Allah dai ya sanya alkhairi"
Viper ya amsa da Amin, sannan ya ce "Abbu wata alfarma nake son sake nema a wurinka dan Allah"
Abbu har so yake Viper ya nuna yana son yayi masa wani abu, hakan na sanya mishi nustuwa, ya ji cewa lallai ya yafe masa.
"Ka ga ramma yar uwata ce, kusan ita da mahaifiyarta sukaɗai suka rage a ɓangaren mahaifiyata, da nake kallo ina jin daɗi. To naga ba tsufa tayi ba, kuma zamanta haka is not safe, na ce dan Allah idan da dama, ban takura maka ba, dan Allah ka aureta. Hakan zai fi sama mata nutsuwa, tun da shi aure garkuwa ne ga mace, duk tsufanta kuwa.
Abbu ya shafi gemunsa yayi murmushi ya ce "Yanzu dai ka bari na fara kawar da ku tukuna, ayi wannan maganar"
"Eh ai dama ba yanzu ba, na san da hidindimu a gabanka, idan Allah ya sa komai ya daidaita nake nufi"
"To ɗan gidan Abbu, Allah ya tabbatar mana da alkhairi"
Al'amin ya ce "Na gode sosai da sosai, Allah ya ƙara arziki"
Saura sati ɗaya biki, Viper ya aiko su Walid wurin Nabila, suka yi sa'a Walida ta dawo daga aike.
Suka gaisa da su Walid, Liti ya ce "Walida, wurin sisternki muka zo an aiko mu, ko zaki yi magana da ita"
"Me zai hana" mintuna goma, sai ga Nabila ta fito, amma yanayin da suka ga Nabila, duk sai jikinsu ya sake yin sanyi, babu wannan karsashin nata, jikinta duk a sanyaye.
Haka suka gaisa sama-sama, suka ce Viper ne ya aiko su da kaya su kawo mata. Ruwa da lemo ne carton hamsin, ga buhun fulawa har da kuɗi, wai ta ƙara a abin da za ta yi hidimar biki da shi.
Tun da yaje dubata a asibiti, bai sake nemanta ba, ita ma kuma ba ta neme shi ba, ta so kiransa a waya, amma ta fasa ta jira Abba ya dawo ta nuna masa.
Faɗa ya hau yi, a kan yadda yake ta ɗawainiya da ɗorawa kansa nauyi, ya kira Abbu yana mita Abbu ya ce "Haba ranka ya daɗe, ni ban ma san an yi ba, kuma abu ne da yakamata ya yi, dan haka ai babu laifi, amma ayi haƙuri idan mun yi laifi"
Major ya ce "Ai an riga an zama ɗaya, a din ga sauƙaƙawa juna, wallahi mun tanadi komai na shirin bikin nan, bayan uban kuɗi da ya din ga turo mata na haɗa kayan lefe"
Abbu ya ce "Kar ka damu fa, auren fari sadaka aka bashi ai, sisinsa ba ta yi ciwon kai ba, wannan kuwa ya daki jikinsa yayi, sai ya fi riƙewa da kyau"
Major ya ce "Aishikenan, Ubangiji Allah ya sanya musu albarka baki ɗaya"
Saura sati biyu biki, Abbu ya kai Major da Baba gidan Nabila, flat ne mai kyawun gaske, a cikin unguwar jambulon da ke Kano.
Tun duniya na kwance, lokacin da baban su Viper ya fara tashen kuɗi, mahaifiyar su ta sanya ya saya wa Al'amin da Sadik gidaje, ta ce saboda maza ne, idan ya sai musu ya taimake su.
A haka kuma da ɗan abin da take samu a hannunsa, da yan sana'oin ta, ta din ga sayen filaye tana ɗan ajiyewa. Aka zo ita ta rasu, Sadik ma ya rasu, dan haka Al'amin bayan gidan da yake da shi, da babu yadda ba ayi da Abbu ya sayar ba yaƙi, Rahila ma tayi ƙulafucin gidan ta gaji.
Miliyoyi aka din ga ambatawa gidan ya sayar yaƙi, yanzu gashi ya yi rana, aƙalla Viper yana da gidaje huɗu, da manyan filaye biyu, dan ma ya bi gonar da yake da ita a ƙauye, ya saka an sayar tun Jauhar na raye.
A auren nan Viper ba ƙaramin jin jiki yayi ba, duk da Abbu yana taimaka masa, amma kuɗaɗen hannunsa duk sun ƙare, a haka sai da aka sayar da filinsa ɗaya, saboda shi yake taimakawa Walid ma.
A duk lokacin da ya tuna a yadda ya auri Jauhar, da a al'adance zai iya cewa auren sadaka, sai ya ji tausayinta, ko da wasa ba ta taɓa nuna masa, ta ji zafin irin auren da aka yi mata da shi ba.
Liti duk da yana supporting ɗin Walid shi ma a kan shirin bikinsa, gefe guda yana ta karɓar kuɗi a hannun babansa, ya ƙara ƙawata wurin shayinsu aka mayar da shi joint.
Kasancewar Viper ya kwana biyu bai je wurin ba, ranar da Liti ya addabe shi ya je, sai da ya zubar da ƙwalla.
JAUHAR MEMORIAL JOINT. Haka aka rubuta a wurin, sannan ga kan famfo ɗaya da aka janyo, liti ya ce "Ga sadaƙatul jariya, mun yi wa ƙanwarmu da ni da Walid, alkhairin Allah ya isketa har cikin kabarinta, ƙoƙarin inganta rayuwarka da tayi, ba kai kaɗai ta yi wa ba, har da mu".
Cikin wurin duk an rubuta, dan Allah ku karanta wa marigayiyya Jauhar ƙulhuwallahu ƙafa uku, Allah ya jiƙanta da sauran musulmi baki ɗaya.
Idan Viper ya ce yana da kalamai, ko wani abu da zai yi, domin nu na godiyarsa ga bayin Allan nan da suka kasance da shi, a halin tsanani da na jin daɗi, to ya yi ƙarya.
Su Abba sun yaba gidan Nabila ba kaɗan ba, manyan ɗakunta uku, da falo biyu, ga komai a wadace dai-dai misali.
Duk da ba a rasa 'yan tsegumi ba, da aka je jere, da suka din ga gulmar, a iyayi irin na Nabila, da yadda ta din ga dating manyan mutane masu kuɗi, ba su yi zaton zata ƙare a wannan gidan ba, duk da shi kansa yadda ake cewa ɗan daba ne, sun zata mara galihu ne da abin yi, dan sun raina kansu da suka ga gidan da ɗan daba zai saka amarya a ciki.
Nabila dai ta kama wuridin ya haiyyu ya ƙaiyyum bi rahmatika astagis, aslih lii sha'ani kullahu, wala takilni ila nafsi, ɗarfatu ainin. Domin samun mafita a kan maganar aurenta da Viper.
*****
Rana ba ta ƙarya, sai dai uwar ɗiya ta ji kunya, aka fara gudanar da biki, shi kansa Viper yayi rama saboda rashin hutu. Dinner da kamu, duk amare ne suka je ba angwaye, Nabila ta yi kyau sosai, farar fatarta tayi kyau da kaya da kuma kwalliyar da aka yi mata, haka ma Shahida ta sha kyau.
Sumayya ma sai kai wa da komowa take yi, tayi kyau sosai da sosai.
A hada-hadar kai komon biki, liti suka ƙara sabawa da walida, har da karɓar lambarta. Walid ya ce "Zaka gane kurenka, ka gama yi wa Nabila rashin mutunci, ka zo kana bin ƙanwarta, Allah ya kawo mata lokacin ramawa"