Kenza eBookz

Karfe a wuta book 2 complete novel - Chapter 16

Karfe a wuta book 2 complete novel - Chapter 16

Karfe a wuta book 2 complete novel Chapter 16: Karfe a wuta book 2 complete novel Chapter 16. Ya katse shi da cewa "Nawa zaka biyani?"

4,449 words

Ya katse shi da cewa "Nawa zaka biyani?"

"Zan baka dubu hamsin kai da yaranka".

"Ɗaurin shekara biyar a gidan yari, shi zan yi a dubu hamsin ni da yarana, ka duba babbar kasada ce"

Indabo ya yi murmushi ya ce "Baka da matsala in dai kuɗi ne"

Ya tashi tsaye ya ce "Kamar yadda ka yi a wannan karon, ka neme ni kai tsaye, haka nake son ya cigaba da kasancewa, ba na buƙatar sanya wani P.A ɗinka ya neme ni, ya sanar mini da saƙonka"

"Na fahimta, ka san mu ƴan siyasa dole sai muna yi, muna ɓad da sahu, baka da matsala".

Al'amin ya jinjina kai, ya sa kai ya bar falon, cikin takun ƙasaita.

***** Saifu ne ya shigo gida, wajen ƙarfe uku da rabi, ya tarar da Jauhar tana wanki a tsakar gida, gidan babu kowa, yaran duk sun tafi makaranta.

Ta ɗago ta ce "Yaya sannu da zuwa"

Ya amsa da Yauwwa "Ina makarantar islamiyyar?"

Shiru ta yi ta sunkuyar da kai, ba ta amsa masa ba.

"Da ne nake fa"

"Amm..dama ban biya kuɗin makaranta bane, sun ce kar na sake zuwa sai na biya"

"Kuna kin gaya wa Baba?"

Ta girgiza kai alamar a'a.

Cikin takaici ya ce "To saboda me?" Ta yi shiru ba ta ce komai ba.

Saifu ya ce "Ke dai sokuwa ce wasu lokutan, dubu uku ne ko? Tashi ki saka uniform ki tafi" yayi maganar yana ciro kuɗi daga aljihunsa, ya miƙa mata dubu uku.

Fuskarta ta faɗaɗa da murmushi, ta saka gwiwoyinta a ƙasa, ta saka hannu biyu ta karɓa ta ce "Na gode sosai da sosai yaya, Allah ya ƙara arziki".

Ya ce "Amin, bar wankin, tashi maza"

Ta ce "To kar maman su Hafsa ta dawo ban gama ba, labulayenta ne"

"Ajiye, su hafsa idan sun dawo su wanke mata, maza ki tafi".

Cikin murna ta tashi, ta tattare kayan wankin, ta shirya cikin uniform ɗin ta, ta tafi islamiyya.

Duk da yau ma sai da aka zane ta, sannan ta shiga ta kai kuɗin makarantar tana ta kuka, dan ba ta ƙaunar duka sam.

Sai dai duk da kukan da tayi, hakan bai hanata farincikin ganin ta koma makaranta ba.

Sai dai bayan ta koma gida, Anty ta rufeta da bala'in ta tafi ta bar mata bedsheets ɗin da ta saka ta wanke mata.

Jakarta kawai ta ajiye, ta hau wankin da aka sakata, bayan ta sha uban zagin tsamar nama, ita duk hakan bai dameta ba, ta kammala wankin sauran bedsheet ɗin, ta wanke kwanuka ta mayar da abincin dare.

Duk ƴan matan gidan suna zaune, itakaɗai take aikinta a tsakar gidan, idan baƙo ya zo sai ya yi zaton mai aiki ce.

***

Yau tun a makarantar boko, Jauhar ta ji period ya zo mata, gashi kuɗin pad ɗin nata saura ɗari da hamsin ba su gama cika ba, sai kame jikinta take yi, saboda tsoron kar jini ya ɓata ta.

Da ƙyar ta isa gida, tana ta lissafin yadda za ta yi, gashi idan ta yi amfani da tsumma, lalata mata fata yake yi, ƙuraje duk su feso mata, ta rasa in da zata saka ranta.

Haka ta wuni tana fama, ga uban ciwon mara, kamar tayi hauka, dan ma ta samu paracetamol a wurin Yaya saifu ta sha, ga uban aiki dan babu mai ɗaga mata ƙafa, haka nan ta saka tsumman, take amfani da shi, idan ba haka ba ta san haka za ta yi ta staining.

Da magariba, tana zaune a tsakar gida, ta cinye ɗan abun da ta samu ta ci, wanda sam ba ta ƙoshi ba, duk da ita ta girka, sai lashe hannu take yi, Baba yayi sallama.

Aka din ga jera masa sannu da zuwa, yana amsawa.

Ya kalli Jauhar ya ce "Waliyiyya ya na ga kina suɗe hannu, ba ki ƙoshi bane?" Tayi murmushi ta girgiza masa kai ta ce "Alhamdilillah, na ƙoshi baba".

Ya ce "To madalla, Allah shi ne abun godiya, akwai wani mutum da ya zo wurina yayi mini maganarki, ban sani ba, ko ke ki ka turo shi" Gaban juahar ya faɗi, ta kalli in da mama ke zaune a kan tabarma, ita ma tana cin nata abincin. Sau ɗaya saurayi ya taɓa biyota gida, mama ta ce idan wani ya kuma zuwa wurinta, ko ta bawa wani damar ya zo wurinta, sai ta kusa halakata, yayyenta ba su auru ba, ba za ta fara kawo musu maza ba, duk da dama shekarun nata ba yawa ne da su ba, haryanzu a SS2 take shekara goma sha shida, sai dai hasken fatarta ke ɗaukar idon samari ƴan bana bakwai, su biyota wai suna so, saboda kashedin mama ta koma saka niƙab.

But Anty, babar su hafsa ta fito daga ɗakin ta, tana jiran ta ji ƙarashen maganar.

Mama ta ce "Ba magana ake yi miki ba?"

Jauhar ta girgiza kai ta ce "A'a Abba, wallahi ban san kowa ba, ban turo kowa wurinka ba"

"Ƙarya ki ke yi, zaki aikata, ba abun mamaki bane ba kina halin kule-kule a waje, dan a zahiri kina da fuskar tsoron Allah, amma a baɗini ba kya ji" Anty ta ara ta yafa ta ƙarar da zancen.

Baba ya ce "No, shi ma ya gaya mini, bai yi mata magana ba, ya zo ya fara samuna ne, na dai tambayeta ne kawai dan na tabattar, zan bashi dama ya fara zuwa wurinta, dan naga da gaske yake yi."

Dumm ƙirjin Jauhar ya buga, ta fara zance yanzu, makarantar kuma fa, ga burinta na son yin karatu, duk da aure ba ya hana karatu, to amma idan wanda zata aura ɗin ba zai bari ba fa?.

Da sauri mama ta tashi ta bishi ɗaki, tana yi masa magana "Yanzu aurar da jauhar ɗin zaka yi, ga yayenta duk a jibge, su kusan biyar babu wadda ka aurar?"

Ya tsaya ya kalleta ya ce "To laɗifa, tara su zamu yi tayi ba zamu aurar ba? Tun da ita Allah ya fara kawowa sai mu fara da ita, ita ma ta huta"

A take ta haɗe rai ta ce "Ban gane ita ma ta huta ba, na fuskanci duk lokacin da magana irin wannan ta tashi, sai ka nuna kamar bana ƙoƙari a kan riƙonta, kamar zaluntar ta nake ko?"

Kamar yaronta ya ce "A'a bance ba"

"To wallahi ba za ayi wa jauhar aure ba, ga su Sajida ba, wannan ai cin mutunci ne".

Yayi mata shiru, bai sake cewa komai ba, ya ƙuduri aniyar, aurar da jauhar ko ba ta so.

*** A tsakar gida ta tsaya tana ta kwaɗa sallama, daga cikin falon aka amsa mata, wata matashiyar mata ta fito.

Suna ganin juna suka rungume juna, suna murna.

"Zakiyya Bala, yau ke ce a gari?"

"Wallahi kuwa Rahila".

"Ya aka yi ki ka gane gidan nan? Kin san lambarki na rasa".

Zakiyya ta ce "Ke wayata aka sace mini, tun da na canza layi na rasa lambarki nima, ai da Abba na haɗu a bakin titi, ya ce mini ai kun jima da dawowa unguwar nan, bamu da wani nisa bamu sani ba".

Rahila ta ce "Allah sarki, shigo daga ciki, shegiyar ƙawata, na yi missing ɗinki fa" suka shiga suna dariya.

Ta kawo mata ruwa da lemo ta ajiye, Zakiyya ta kalli gidan ta ce "Ikon Allah, nan ku ka dawo kenan?"

"Wallahi kuwa, ai yanzu ba abun, tun da aka damfare shi ɗin nan, lamuran sai godiyar Allah, amma a hakan ma ai bamu tagayyara ba"

Zakiyya ta ce "Gasakiya ne, Allah ya ƙara rufa asiri, ina su kursum?"

"Duk suna makaranta, kin san tana level 3 ita yanzu, ina su hafsa, haryanzu babu labarin aure ko?"

"Haba Rahila, yaushe za ayi auren su Hafsa ba ki ji labari ba, wallahi babu shiru, abu kamar saka hannu, har na fara zargin uwargidana, sai na ga ita ma ga nata nan biyu, Sajida da surayya, suma babu ana ta shige-shige shiru, dan ma ni da ita kar ta san kar ce, an daɗe ana gogawa taga babu riba, na sha gabanta shi ne ta sarara mini".

Rahila ta ce "Subhanallah, kin ga nima ana ta fama, duk wanda ya zo kamar walƙiyya sai ya tafi, ni kuma ba zan bawa talaka aure ba wallahi"

"Ba ke kaɗai ba Rahila, kin ga yaran nan, har mai suka shafa, sun yi ɗas sun zama farare, kwalliyar nan, supplements ɗin nan, na gyara dai, amma ba tsayayye duk sai shirmanmu"

"Ki daina damuwa fa, lokaci ne"

"Wallahi haka ne, ba ki san wani abun takaici ba, wai sai yarinyar nan, ƙanwar bayansu, jauhar ƴar bafulatanar nan da ya taɓa aura kwanaki, aka rabu tsiya-tsiya ƴar da ta mutu ta bari, wai ita wani ya ce yana so da aure, yarinyar nan sai da Laɗifa ta shiga ta fita, ko suturar kirki ba ta sakawa, wai amma a haka wani ya gani yake so, kin san ita ya bawa riƙonta"

Rahila ta kwashe da dariya ta ce "Ai wasu lokutan maza ƴan wahala ne, ga in da ya dace su je, amma wani wurin suke kai kan su. Ni kaina ga nawa ɗan riƙon ya sani a gaba, ɗan gidan zahra'u tsinannen yaron da asiri baya cin sa, babu irin kurciyar dan ban saka ayi masa ba, amma abu ya gagara".

Zakiyya ta gyara zama ta ce "Ke haba? Al'amin ko"

"Shi, ai ya zame mini bala'i Zakiyya, ya zama riƙaƙƙen ɗan daba da shaye-shaye, za ki ji matasa suna mai dogon zamani shi ne fa"

Zakiyya ta dafe kai ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ke ina jin labarinsa har a radio, dama shi ne, amma lokacin kina amarya kamar a nutse yake"

"Ke rabu da ni oho masa, ni sonake ya bar gidan nan, kar ya hana mini ƴaƴa auruwa, ko ya illata wani, dan Abba da ki ke gani ɓaras ya karya mini ɗa kamar kara. Kina kallon halin da muke ciki, yanzu babu bushasha kamar da, ɗan abun da ta bari ya gada, ubansa ya fito da shi, ya ƙara jari, yaƙi wai ba zai taɓa masa kaya ba, kin ga da zai bar gida a neme shi a rasa ai ma samu mu ci, babu irin korar da ban saka ya yi masa ba, amma yaƙi tafiya".

Haka suka cigaba da hirarraki, wadda galibi a kan rayuwar makaranta da suka yi, sai na iyalinsu hirrar take.

Kusan sati biyu, da maganar da baba yayi, a kan wanda ya zo wurinsa a kan jauhar, yayi shiru da maganar kamar ta wuce, ya dawo da yamma, kasancewar juma'a ce, jauhar ta duƙufa tana ta shirin dutse. Kuɗinta da suka taru ba ta samu ta sai pad ba, sai ta sayo riɗi, ta ce zata soya ta juya kuɗin, idan suka taru ta saya da wuri.

A tsakar gida baba ya tsaya, ya ƙwala mata kira, ta amsa ta fito ta tsuguna.

Ya kalleta ya ce "Ki shirya, ki je ga baƙonki can a waje ya zo ku gaisa".

Ji tayi kamar ta fyalla da gudu, ta tsaya da saurayi, ya ce mata me, ko ta ce masa me?

Amma ta amsa masa, ta tashi ta shiga ɗakinta, jikinta duk yayi sanyi.

Sajida ta shiga falo in da su surayya ke kallon Bollywood.

"Kai kuna nan kuna kallo, baba fa da gaske yake auren jauhar zai yi muna zaune"

Surayya ta ce "Kamar yaya?"

"Kamar yadda na gaya muku, wallahi wai wani ne wai yake son ta"

Hafsa ta ce "Da yardar Allah ba za ta yi aure ta barmu ba".

Jauhar kuwa turus ta yi, tana kallon ƙatuwar motar da ke ƙofar gate ɗin gidan an yi parking ɗin ta.

Zura kai ta yi tana lelleƙawa ta ga waye baƙon.

Ya buɗe ƙofar motar ya fito, yana murmushi.

Turus ta yi tana kallonsa, ya yi murmushi ya ƙaraso ya jingina da jikin motar, ya ce "Mayar da idon mana, kin yi mamakin ganina ko?"

Da sauri ta durƙusa ta ce "Ina wuni?"

"Lafiya ƙalau Faɗimatul Jauhar"

Ya ɗan gyara tsayuwarsa ya ce "Na san dole zaki yi mamakin ganina, zuwa na yi na sake bayar da haƙuri, a kan incident ɗin da ya faru, na tsorata ki da na yi, na kusa buge ki da mota"

Jauhar ta ce "Ai bakomai ya wuce, na ma manta"

"Ai ni ban manta ba, dan sai da na koma wurin da muka haɗu, na tambayi ina ne gidanku, na samu baba muka yi magana, hankalina ba zai kwanta ba, har sai na aure ki, na kai ki gidana, na rarrasheki da kyau"

Jauhar ta sunkuyar da kanta, tana jin abun wani banbarakwai. Ita gaba ɗaya ma ji take yi ya takurata.

"Jauhar"

"Na'am" ta amsa tana kallonsa da idanunta da suke farare tas, sai dai ba manya ne can ba.

"Me ki ka ce? Ni aurenki nake son na yi, kuma nan kusa wallahi ba da nisa ba, na yaba da tarbiyarki fiye da yadda ki ke tunani".

Kamar za ta yi kuka ta ce "Ai ban gama makaranta ba, ni yarinya ce kai kuma babba ne"

Dariya yayi ya ce "Wow, ashe shagwaɓaɓɓiya ce har haka? To dan ni babba ne ba za a aure ni ba? Kar ki ce haka, zaɓin Allah ake nema kin ji sweetheart, ki yi ta addu'a Allah ya tabattar mana da alkhairi. Ina da mata ɗaya da yara biyar kacal, yaro ne ni haryanzu" yayi mata maganar yana kashe mata ido ɗaya.

Ita kam gabanta ne ma ya faɗi, yara biyar ne kacal, ita duk wata harka da za ace kishiya, tsoronta take ji.

"Kar in cika ki da surutu, bani lambar wayarki, a hankali zamu saba, kin shiga raina sosai, zan yi iya ƙoƙarina na baki kulawa dai-dai iyawa ta, kuma karatunki, in sha Allah sai kin ce kin gaji dan kanki" yayi maganar yana miƙa mata wayar ta saka masa lambarta.

"Bani da waya ai"

Ya ce "Ohh, ashe fa ƴar baby ce, ba ta isa riƙe waya ba, zan kawo waya in sha Allah"

"A'a dan Allah kar ka kawo mini, ba ma za a bari na riƙe ba"

"To ikon Allah, to ta ina zan din ga jin muryarki? Amma shikenan bai kamata na karya dokar gidanku ba, zan san abun yi na nemi iznin baba na kawo wayar. Amma baki tambayi sunana ba"

Ita dai tayi shiru, tana mamakin yadda babban mutum kamar wannan, yake ta kashe mata murya.

"Sunana Alhaji Mu'azzam. Ina dillancin kayan sawa, mussaman na mata, ina shigo da kaya daga ƙasashe daban-daban, kuma ni ɗan siyasa ne, yanzu haka ina da muƙmi a gwamanati, amma ba dai wannan ba, ni amincewarki nake nema, kar ki yi saurin rejecting ɗina ki yi mana addu'a kin ji zahrana"

Jauhar dai ta yi gum, ita wannan tsayuwar ma kawai, kunya take bata kamar ta falfala da gudu.

Haka ya gama surutansa, ba komai take fahimta ba, lissafi kawai take a zuciyarta, saura dozen nawa ta gama shirin dutse, ta kai ta karɓo kuɗin, ta cika ta soya riɗi.

Kuɗin da ya miƙo mata, ya sanya ta ja da baya, tana girgiza kai. Ya kaɗa ya raya, amma fafur ta ƙi karɓa, sai haƙura yayi.

Haka yayi mata sallama ya tafi, da sauri ta shiga gida, dan kuwa Alhaji mu'azzam duk ya cinye mata lokaci, ba ta ƙarasa shirinta ba, mugun kallon da ta tarar da ƴan matan gidan na yi mata a tsakar gida, ya sanya ta shan jinin jikinta, dan kuwa tuni yaran gidan suka kawo musu tsegumin irin motar da aka zo wurin Jauhar da ita.

Sai jikinta yayi sanyi, ta hau tunanin laifin me tayi? Jiki a sanyaye ta ɗaukko aikinta ta cigaba.

Sai dai suka din ga zaginta babu dalili, hafsa ta saka ƙafa tayi fatali da ɗan plate ɗin jauhar da take zuba dusten.

Hankali a tashe ta ɗaukko tsintsiya tana tattarewa, ba tare da ta damu da son sanin dalilin da ya sa hafsan tayi mata haka ba, domin kuwa idan da sabo ta saba.

Yaya saifu da ya fito daga banɗaki ne, ya ɗurawa Hafsa ashar, saboda ya ga abun da ta yi hafsa.

Babarta ce ta fito tana yi masa masifa, tana kare hafsa, da mayar masa da zagin da yake yi mata.

Aikuwa mama ma ta fito ta haushi da bala'in menene ruwansa da shiga abun da babu ruwansa, nan faɗa ya harƙe, sum-sum jauhar ta ja jikinta ta koma ɗaki.

Da daddare bayan sallar isha'i, baba ya kira jauhar ɗakinsa, ya tambaye ta yaya suka yi da baƙonta, amma ta kasa magana, sai duƙunƙuna hannunta da ta din ga yi a hijjabi.

"Jauhar"

Kanta a sunkuye ta ce "Na'am baba".

"Ba zan yi miki dole ba, ban bawa mutumin nan damar zuwa wurinki ba, sai da na yi bincike a kansa, na san makarantar ki ke tunani, ina mai tabbatar miki ya tabattar mini zai bari ki cigaba. Bana jin daɗin irin rayuwar da ki ke yi a cikin gidan nan, babu yadda zan yi ne. Amma idan ba kya son sa, ba zan yi miki dole ba, ki bi komai a sannu, ki yi istikhara da addu'a, na san ke mai yawan addu'a ce, da miƙa lamuranta ga Allah, ki ƙara dagewa sosai da sosai, ki nemi zaɓin Allah"

"To Baba in sha Allah"

"Yauwwa yarinyar kirki, Allah ya yi miki albarka, ya sa naga jikokina ƴan farare masu kyau kamar jauhar ɗina" rufe fuska tayi ta ƙunshe fuskarta tana murmushi.

Tun da ya shigo layin, wasu daga matasan layin ke darewa, suna ɓuya, ko a jikinsa, tafiyarsa yake yi cikin hanzari da ƙasaita, sumar sa ta cika masa kai, ya aske wani wurin ya bar wani, irin cikakken mara jin nan.

Kai tsaye ya buɗe ƙofar gidan, ya kunna kai cikin gidan.

Babu sallama ba komai, ya kutsa cikin falon in da suke zaune suna karyawa.

Abbu ya ɗaga kai ya kalle shi, ya ce "Uban me ka zo yi mini gida? Me na gaya maka a kan zuwar mini gida?".

Ya sunkuyar da kai ya ce "Ganinka na zo na yi na gaisheka"

"Ba na buƙatar gaisuwarka Al'amin, ai tun da ka zaɓi watsewa a duniya, ka yi fatali da tarbiyarka nima na sallamaka, ka koma wurin abokanka ƴan wiwi da suka fi ni a wurinka. Kalli tsinannen askin da yake kanka, ka zo mini banda warin wiwi babu abun da ka ke yi, sanna ka ce ka zo gaishe ni? Ai ni na barwa duniya kai ka tashi ka bar mini gida"

Yayi shiru yaƙi tashi, kuma ya ƙi magana, sai murza zoben azurfar hannunsa da ƙarfi da yake yi, zuciyarsa na zafi.

Rahila ta ce "Dan Allah ka fita Aminu, wannan warin da ka ke yi, zan iya amai wallahi, kuma ni idan ina ganinka tsoro nake ji wallahi, tun da kullum a buge ka ke kar ka illatani ko yarana a banza" tamkar tana magana da dutse, haka yiyin gingirin gim, bai motsa ba.

"Ba magana ake yi maka ba?" Yayi masa maganar cikin tsawa.

Al'amin ya ɗaga idanunsa, da suka yi ja fiye da lokacin da ya shigo, ya ƙara matsawa kusa da mahaifiyar, ya zuba masa ido sannan ya ce "Na san ina wari, na san kullum a buge nake, a kowane lokaci zan iya ɗaukar makami na hallaka duk wanda ya yi gaba da gaba da ni, ko wanda bai ji ba bai gani ba. Wasu lokutan ma banbancina da mara hankali kaɗan ne, na san ba na jin magana ko kaɗan, bana tsoro ko shakkae aikata duk wani abu da zuciyata ta raya mini, amma idan ban zo wurinka ba wurin wa zan je? Da haka nake? haryanzu ban san laifina a wurinka ba Abbu, zan yi ƙoƙarin daina zuwa gidan nan kamar yadda ka buƙata, ko aka ce maka ana buƙata, amma idan na daina na daina kenan har abada wallahi! Ka huta lafiya" yayi maganar yana shafar saman hannun mahaifinsa.

Yana miƙewa zai wuce, yayi ball da flask ɗin ruwan zafin da yake tsakiyar wurin, da kwanukan. Gaba sai da suka razana.

Ta ce "Ka gani ko?"

Shiru mahaifin Al'amin yayi, ya tashi da sauri ya bi bayansa, sai dai yana fitowa daga falon, ya ga an jefo Abba, babban ɗan Rahil, ƙaton saurayi amma kamar an watso shara.

Ko ba a gaya masa waye ba, ya san aikin Al'amin ne, Abba kuwa bajewa yayi, ko shurawa ba ya yi, rahila ta fito tana kururwa.

Abbu ya leƙa waje da sauri, a can ƙarshen layi, ya hango Al'amin, ya zare wuƙa yana ta zuba sauri.

Ya rufa masa baya, yana ƙwala masa kira, amma ya ƙara sauri har da gudu, ya bar layin.

Ayshercool 08081012143

18

🔞*PAID BOOK NE, ₦500 BOOK1-3 VIA 0009450228, AISHA ADAM JAIZ BANK, SAI SHAIDAR BIYA TA 08081012143*

Ganin Aminu ya ɓace masa, ya sanya ya koma gida da sauri, rahila sai kururwa take yi, tana jijjiga Abba.

Ƙannensa mata su azima, suka kewaye shi suka hau kuka.

Abbu ya ɗebo ruwa, ya din ga zubawa Abba, har Allah ya sa ya buɗe ido.

Cikin kuka take cewa "Ka gani ko? Ba zaka taɓa yadda da ta'addancin ɗanka ba, har sai ranar da ya kashe mini ƴaƴa, me yayi masa zai yi masa wannan ɗibar karan mahaukaciyar ya watsar? Wallahi na gaji, ina ga tafiya zan yi na bar maka gidan nan kai da ɗanka, na rasa uban me yaron nan yayi masa, ko dan ba kai ka haifi abba ba, ya tsane shi daga shi har nazifi ni ban sani ba. Ni ba abun na kai shi ƙara wurin hukuma ba, ba sa yi masa komai sai dai a sako shi, ni na gaji".

Abbu ya ce "Dan Allah ki daina wannan maganganun, bari na samo mota, mu kai shi asibiti"

Abba kuwa ko magana ya kasa, Nazifi ne ya taimaka aka fita da Abba zuwa mota.

Al'amin kuwa da ya tabattar da ya tserewa Abbu, ya samu wani lungu, ya jefar da wuƙar hannunsa, ya samu wuri ya zauna, yana ƙoƙarin haɗiye wani abu mai tsananin ɗaci da zafi a maƙogwaronsa, ji yake kamar numfashin sa zai ɗauke, babu abun da zuciyar sa ke raya masa, banda ya kashe matar Abbu wato rahila ya huta.

*** Gidan babu kowa, duk yaran sun tafi makaranta, mama tayi sallama a falon zakiyya. Ta amsa tare da fitowa daga bedroom ɗin, tayi miƙa ta ce "Lafiya kuwa?"

"Au bacci ma ki ke yi? Lallai kam, to magana na zo mu yi"

Zakiyya ta ce "Ok, bisimillah zauna mana"

Ta nemi wuri ta zauna, ita ma ta zauna.

Mama ta kalleta ta ce "Kin san waye yake son Jauhar kuwa?"

"A'a sai kin faɗa".

"Ɗan familyn mai atamfa ne"

Waro ido Zakiyya ta yi, har tana neman faɗowa daga kan kujera, ta ce "Wani mai atamfar?"

"Waɗanda dai ki ka sani,ba ma wannan ba shi zai tsaya takarar majalissar tarayya a yankinsu, jiya na tutsuye shi, yake gaya mini, ga kasuwancin atamfofi da lesuna da yake sayarwa, daga ƙasashe daban-daban yake order kaya, na din ga bugun cikinsa yana gaya mini, wai zata yi karatu idan tana so, idan business take so zai ba ta jari, idan ma zaman gida take so, ayi din ga yi mata komai, duk zai iya kuma nan kusa yake son ayi auren".

"Bantan uba, namu ƴaƴan suna zaune za ayi hakan, muna me?"

Mama ta ce "Hmm, ni fa na daɗe ina hana faruwar wasu abubuwan, rannan daga aikenta gidan Hajiyar lamin, wai ɗan wan maigidan ya ganta, ya ce ayi masa hanyar aurenta, uban yaron fa sanata ne a Adamawa, hauka nake? Na toshe na hana, na din ga aika su surayya, da walida amma ko kare a familyn babu wanda ya sinsuna su. Lokacin da suka yi sauka ma, babu kunya wai chairman yana son ta, tun ba ta kai haka ba ma, na ce ba za a lalata mata tunani ba, karatu take yarinya ce, na rasa wannan masifar".

"Mun shiga uku, meyasa kowa sai ita? Kuma duk masu kuɗi, namu yaran fa?".

Mama ta ce "Wannan shegiyar farar fatar suke yi wa ai"

"Wace farar fatar? Su ma duk ba suna shafa mai ba, manyan zaratan ƴan mata, sun sha mai da kwalliya amma ace su duk shiru sai ita?"

"Shiyasa tun jiya ban yi bacci ba wallahi, na saƙa wannan na kwance wancan, dole fa a rusa wannan maganar ma"

Zakiyya ta ce "To yanzu menene shawara? Wallahi na rasa abun cewa, ko malamai zamu shiga ne?".

"Babu lallai yayi tasiri, na fuskanci ƙashin masu arziki ne da ita, amma mu cigaba da shawara kafin faruwar abun".

Zakiyya ta ce "In sha Allah "

Mama ta miƙe ta ce "Sai na ji ki".

*** Cikin ikon Allah Abba ya warware, babu abun da ya same shi, sai dai ya bugu, ya yi ta fama da jiri, sai da ya kwana uku a asibiti, aka sallame shi.

Rahila ta cigaba da ɗagawa Abbu hankali a kan Al'amin, a kan lallai ya kai shi wurin hukuma, a san yadda za ayi da shi, kafin ya yi mata kisan gilla ita da yaranta.

Gaba ɗaya maganganun Al'amin sun yi tasiri a zuciyarsa, amma kuma wani ɓangaren, Rahila tana da gaskiya, al'amin barazana ne a gare su, saboda yadda sunan mai dogon zamani, yayi ƙaurin suna a bakin mutanen unguwa, ba iya unguwar ba, har gidajen radiyo, duk wani faɗan daba da zai tashi a arear rukunin unguwannin to sai an ambaci mai dogon zamani wato Al'amin. Ƴan sanda har sun gaji da kama shi, idan an kama shi ma, ƴan siyasa sai sun saka an sako shi, daɗinta ɗaya ba ruwansa da taɓa kowa ko kayan kowa, sai ƴan daba da jami'an tsaro da su yake faɗansa.

Bayan Jauhar ta dawo daga makaranta, mama da Anty suka sakata a gaba, suna sake yi mata tambayoyi a kan Alhaji mu'azzam, Jauhar ta rasa me za ta ce musu, dan ita ba komai ta sani a kansa ba, dan tun da ya zo sau ɗaya, bai sake zuwa ba, dan haka ta din ga ce musu ba ta sani ba. Aikuwa suka din ga zaginta, tare da kiranta munafuka.

Suka gama zaginta, ta cigaba da sabgoginta.

Yaya tijjani ya shigo, wanda shi ne babba a gidan, ya shiga wurin mama, jauhar ba ta san hawa ba, ba ta san sauka ba, ya kamata ya zane a yammacin nan, wai an ce masa kule-kulen maza take yi.

Ihun jauhar ne ya sanya yaya saifu shigowa, ya tarar TJ yana mata bala'i, wai tana kula maza.

"Haba yaya TJ, idan ba ta kula maza ba, kai za ta kula? Ko za a jiƙata a ruwa a sha ne? Da iznin baba fa ya zo wurinta idan ma a kan wannan mutumin nan"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull