Kenza eBookz

Karfe a wuta book 2 complete novel - Chapter 18

Karfe a wuta book 2 complete novel - Chapter 18

Karfe a wuta book 2 complete novel Chapter 18: Karfe a wuta book 2 complete novel Chapter 18. *** Abbu yana daga kwance ya kammala azkar, ya juya zai yi…

4,450 words

*** Abbu yana daga kwance ya kammala azkar, ya juya zai yi bacci, rahila ta shigo ɗakin, ta nemi wuri ta zauna a kan gadon ta ce "Tun da idonka biyu tashi mu yi magana"

Ya juyo ya ce "Ina jinki"

"Magana ce mai muhimmanci, a kan Aminu".

"Aminu dai Aminu dai, me kuma ya faru wannan karon?"

"Menene ma bai faru ba, tun da an mutu an bar mini jaraba da masifa, kullum hankalina a tashe, nan aka zo ana bayar da labari, sun je ya tayar da tarzoma, har an yanke shi a ƙafa, rashin mutuncin sa kullum ƙara gaba yake yi"

"To, na ji, maganar kenan ki sake maimaita mini abun da yake aikatawa? Wannan ai wani abu ne da na riga na sani".

"Ba shi ne ba, magana ce a kan mafita game da abun da yake yi"

Ya tashi zaune ya ce "Wace irin mafita?"

Rahila ya gyara zama ta ce "Akwai wata ƴar ƙawata, yarinyar rashin ji take yi, tana neman fanɗarewa, gashi ba ta da wani tsayayye, na ce tun da shi gashi, kuma akwai wannan kangon gidan da ya gada, a gyara masa ka nema masa aurenta, ta je su ƙarata ko zai yi hankali idan ya ajiye iyali".

Abbu ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Too, ikon Allah, banda abunki wane mai hankalin ne zai bawa Al'amin auren ƴar sa, yadda suanansa ya yi shuhura, a kan rashin ji".

"To ai yarinyar na ce maka fitina take yi ita ma"

"Kuma sai ayi gyaran ɓarna da ɓarna? Sai a aura masa wadda ba ta ji?"

Rahila ta ce "To shi ɗin menene? Shi na kirkin ne?ko Jin yake yi? Sai su rufawa juna asiri, amma aka ƙyale shi a haka, nan da shekara ashirin, kana ganin zai yi nutsuwar da zai kula wata mace da sunan zai aura, tsabagin wauta da kayen maye ne kawai a cikin kansa"

Abbu ya numfasa ya ce "Maganarki haka take, amma kamar yayi ƙanƙanta ma da auren shekara ashirin da bakwai, ga ba sana'a yake ba sai ɗaukar magana, da yaya zai riƙe auren? ga faɗa da faɗin rai".

"Idan ya san ya ajiye mace, dole ya nemo ya ba ta ai, tun da morarta zai din ga yi, ko kuma kana tunanin zafin rai da faɗin ransa zai hana shi, mu'amala da ita ne namiji ne fa".

Abbu yayi murmushi, har sai da haƙoransa suka fito, ya ce "Na san ɗa na kamar yunwar cikina, ban san meyasa mata ku ke tunanin maza, bamu da wani tunani idan ba wannan ba, Aishikenan".

Ta kwanta ta ce "Aikuwa idan haka ne, da sai an dangana da nema masa magani, idan baya wannan tunanin"

Ya kwanta a kusa da ita ya ce "Zuwa da safe in Allah ya kaimu, sai ki yi mini kwatancen gidan su yarinyar, na samu mahaifinta".

Ta ce "Yauwwa Abbu ko kai fa"

****

Jauhar ta dawo daga makarantar dare, ta tarar da Baba da baƙo a waje, ta durƙusa ta gaishe su, sannan ta shiga cikin gida.

Baba ya nuna wa Abbu ita, ya gaya masa ita ce jauhar ɗin da suke maganarta, Abbu sam bai ga alamar rashin ji, a tare da jauhar ba sai ma nutsuwa da kamala, hatta muryarta mai sanyi ce, yayi mamakin da rahila ta ce masa wai ba ta ji, fanɗararriya ce, sai dai bai yi magana ba, suka cigaba da magana da Baba a kan nemawa Al'amin auren jauhar, ya sanar da baban jauhar Al'amin ɗin ba ya ji, sai dai bai gaya masa irin rashin jin ba, ya zata Baba ya san komai, saboda yadda rahila tayi masa bayani.

Baba ya ce "Babu damuwa, Allah ya tabbatar musu da alkhairi, na san iyayen nata ba za su zaɓa mata abun da zai cutar da ita ba".

Suka taɓa hira, ya tambayi Baba ko akwai wani shiri da za su yi? Baba ya ce idan sun shirya kawai su kawo abun da suke da shi, ayi komai a wuce wurin.

Suka gama magana, Abbu ya tafi gida yana farinciki, tare da fatan Allah ya sa ƙarshen matsalar Al'amin ce ta zo, Shi ma Baba ya shiga gida, can ƙasan zuciyarsa yana ta kokwanto da wasi-wasi, amma ya kasa ayyana hakan a zahiri.Sam bai iya tambayar menene rashin jin da Aminu yake yi ba, bai tambayi menene sana'arsa ba da sauran su, kawai shi dai ya tsinci kansa da amincewa, bayan da mama tayi ta jaddada masa idan har Alhaji mu'azzam ya dawo, ya ji ƴan daba sun yi mata fyaɗe za ta wulaƙanta, ba zai aureta ba, shi gaba ɗaya ma ya manta da batun ya karɓi kuɗin auren Jauhar.

Abbu na komawa, Rahila ta tare shi, tana tambayarsa yadda suka yi, ya ce "Ya amince zai ba shi ita, amma ni da ya nuna mini yarinyar, ba ta yi kalar marasa ji ba".

"Ban da abunka Abbu, dama a goshi ake gane marasa jin? Kai dai kawai ayi sha'ani".

"Amma anya ban yi ganganci ba kuwa, ban sanar da shi ba na je na nema masa aure, idan ya bujire fa".

"Au sai ma ya yarda? Ashe na kabari zai dawo duniya idan shi ne zai yadda, ka yi iya yinka a matsayin ka na uba, kar ma ka sanar masa, sai ka kai kuɗin, kuma ku saka lokaci kaɗan, kar ya tafka wata tsiyar, ba akwai gidan da ya gada na wurin babarsa a chiranci ba, aje a ɗan gyara masa, ya zauna".

Abbu ya jinjina kai ya ce "Shikenan Allah ya yi mana jagora".

Kwana huɗu, Abbu ya kira baba, ya ce za su zo, su kawo dukiyar aure.

Ko da Baba ya sanar da wanda za su karɓi kuɗin Jauhar ɗin tare, sun yi mamaki, suka din ga tambayar sa, meyafaru da waccan saka ranar, ya ce musu matsala aka samu.

Dubu ɗari uku da hamsin, aka kai kuɗin komai da komai, har da lefe da sadaki da kuɗin aure, wai bayan sati biyu za a ɗaura aure.

Mama ta fito tsakar gida ta din ga rangaɗa guɗa, suna Allah ya sa za su gani, gaba ɗaya sai jauhar ta zama confused, wane irin abu ne haka? Alhaji mu'azzam ne ya dawo? Ko kuma yaya aka yi, aka kuma karɓar wani kuɗin. ta ji ana zancen wani Al'amin shi kuma daga ina? Ta tambayi kanta. Sai dai tsananin kunya, da kawaicin jauhar, bai sanya ta yi magana ko ta tambaya ba.

Su surayya suka din ga yi mata dariya, wai ta ga samu ta ga rashi, from grace to grass.

Duk wani shirin auren, Mama ce take yi, ita ke karɓar kuɗin a hannun Baba wani abun ta saya mata mai kyau, wani akasin haka, masu kyan ma tana saya ne, saboda kar a yi mata gori, ta riƙe yarinya shekara goma sha shida za a shiga sha bakwai, amma ba ta yi mata abun kirki ba.

Aminu kuwa tun kan a kai kuɗin, yayi ɓatan dabo, dan rigimarsa ba ta ciwo shi ya zo gidan ba, dan haka tilas Abbu ya fara bin dabar da yake zama, da duk in da ya san zai ganshi, amma babu shi babu labarin sa, haka ya din ga bayar da cigiyarsa, kamar wani kuɗi, kowa ya tambaya sai ya ce masa bai ganshi ba.

Rahila ta ce masa ya cigaba da shirin sa, duk in da ya tafi ma zai dawo.

A gidan su jauhar kuwa, hankalinta ne ya tashi, da ta ji Anty na yi mata iƙirarin wai nan da sati biyu za a ɗaura mata aure, da angonta Al'amin.

Saifu ya kasa jurewa, ya samu Baba ya tambaye shi, wai meke faruwa da auren jauhar ne?.

Baba ya ce "Eh, nan da sati biyu za ayi"

"Amma na ga kamar sau biyu aka kawo kuɗin, wancan an ce Alhaji mu'azzam, yanzu kuma an ce Al'amin wanne ne gaskiyar lamarin ne?"

Baba ya ce "Maman ka da Antynku, ne suka yanke shawarar a aura mata wani, wancan za a iya samun matsala, ta ɓangaren zakiyya ma aka kawo wannan ɗin" cike da takaici yake kallon Baba ya ce "wace irin matsala kuma Baba? Meyasa wanda aka kawo ɗin ba za a haɗa shi da wata ba, sai jauhar? A ina yake, kuma menene sana'rsa? Yazo ya ganta ta ganshi, yayi mata?"

Baba ya sunkuyar da kai tare da girgizawa ya ce "No, amma na san ba za su zaɓi abun da zai cutar da ita ba, kuma jauhar yarinya ce mai biyayya"

Takaici ya ishi Saifu, ya tsani yadda matan gidan suke shirya wa Baba abun da suke yayi, kuma yayi babu musu mussaman a kan jauhar.

Kawai ya tashi ya fita tsakar gida, ya tarar da ita, tana ta uban wanke-wanke, gefe ta jiƙa kayan wankin uniform ɗin ƙanan yaran gidan.

Ya ja kujera ya zauna a kusa da ita ya ce "Waliyiyya, wai saura sati biyu aurenki?"

Tayi yaƙe ta ce "Haka na ji, amma dai Baba bai gaya mini ba".

"Wanda zaki aura ɗin kin taɓa ganinsa ne? Ki na son sa?".

Ta sunkuyar da kai tana murmushi ta ce "Ko ban ganshi ba, tun da an ce su mama ne suka zaɓa mini shi, kuma Baba ya amince na san ba zai cutar da ni ba"

"Baki taɓa ganinsa ba kenan?" Sai ta kasa amsa masa, ta cigaba da durza tukunyar hannunta cikin ƙarfin hali.

Can kuma ta ce "Dan Allah yaya, ka roƙi baba, ya ce masa dan Allah ina son ƙarasa makarantata, ko WAEC na yi"

Saifu ya girgiza kai ya ce "Ki kwantar da hankalinki, na san juriya kawai ki ke yi, amma in sha Allah, ba zaki ji kunya ba jauhar".

Mama ce ta fito ta ce "Kai saifu, uban me ka ke gaya mata, hure mata kunne zaka yi?"

Ya tashi tsaye ya ce "Ko na hure mata kunne, ba zai huru ba, kawai ina tausayin sauran ƴan matan ne, saboda komai nisan jifa ƙasa zai dawo"

Ta ce "Saifu ni ka ke gaya wa haka? Me ka ke nufi?"

"Mama kin san fa me nake nufi sarai, Allah ya haramta zalunci a kan kansa, babu wanda zai yi ya tsira wallahi" ya ƙarasa maganar yana ficewa.

Cike da takaici da son hucewa, mama ta rarumi takalmi, ta jefi jauhar da shi a fuska, aikuwa ya tsokane mata ido.

Ta zauna ta din ga mutsutsuka idon, sai da idon yayi taruwar jini.

Ƴan unguwar su jauhar sai ganin invitation suka yi na bikin jauhar, suka din ga zuwa gulma da jin ba'asi, wane irin aure ne haka faka-faka ko lefe ba a nuna musu ba, da yake ba su san ma zancen kawo kuɗin auren farko ba.

Mama da zakiyya, suka din ga cewa saboda ayi a rufa mata asiri, ake son ayi gaggawa a aurar da ita, sadakarta aka bayar babu ko kayan lefe.

Saboda cin fuska a gabanta, suke faɗar hakan. A gabansu sai ta jure, tayi kamar ba ta ji ba, idan ta ɓuya kuma sai tayi ta kuka.

Al'amin kuwa, honorable Indabo ne ya saka aka kai shi asibiti ta ƙarfin tsiya, saboda ciwon ƙafarsa an sake fama masa lokacin da ya tayar da rigima a wurin campaign, a haka yake lanjarata, ya tafi nasa wuri, saboda soyake Aminun ya warware sosai, kafin lokacin zaɓe kuma, yadda zai yi masa aikinsa yadda yakamata.

Yana shiga arearsu, aka sanar da shi cewa, babansa yana ta yawon nemansa, mamaki ya kama shi, dan idan zai kwana nawa bai ganshi ba, babu ruwansa da in da yake, dan haka cikin gaggawa ya nufi gidan, domin jin dalilin neman nasa.

Sai dai da ya je ya tarar da Abbun yana shirin fita.

"Kai baka iya sallama bane Al'amin, sai dai mutum ya ga ka bayyana kamar wani shaiɗani?"

"To meye marbarsa da shaiɗanin?" Tayi maganar ƙasa-ƙasa.

Sarai ya ji ta, amma ya yi shiru, ya samu wuri ya zauna ya miƙe ƙafarsa ya ce "An ce kana nema na"

"Ba an ce bane, nemanka nake yi, ka dawo daga gantalin kenan? Kodaye ba yau ka fara ba, ka buɗe kunnenka da kyau ka saurare ni"

Yayi shiru bai ce komai ba.

"Daga nan ba kasuwa zani ba, Abba ne zai je ya buɗe shago, gidanka na chiranci, na gado zan je, za ayi masa wasu ƴan gyare-gyare, ba ni da kuɗi sosai a hannuna, za a yi masa abun da ya sauwwaƙa, kai ka ƙarasa gyarawa daga baya".

Ya yi shiru yana wasa da zobensa, kamar yadda ya zame masa ɗabi'a, idan ba ya son yin magana.

Abbu ya cigaba da cewa "Kuɗin aure na kai maka, next week za a ɗaura maka aure"

Lanƙwashe ƙafarsa ɗaya yayi, ya koma wasa da yastun ƙafarsa, yana kallon wani wurin daban.

Rahila ta ce "Taɓɗijan, lallai gagare".

Abbu ya ce "Al'amin da kai nake fa"

Ya ɗago idonsa ya kalli Abbu ya ce "Wai ni ko wa?"

"A'a da ubanka nake ba kai ba, ni da waye a wurin nan?"

Al'amin ya ce "Ni fa yau ban sha komai ba, garau nake balle ace a buge nake ban ji dai-dai ba, wannan kawai zance ne, ni da ake cewa gagarrare haihuwar asara, wa zai bani wani aure? Ni bana buƙata, idan kuma ba haka ba, duk abun da ya biyo baya ba ruwana idan na kashe yarinya, ko na yi mata illa, kar a zo ana yi mini ƙanan maganganu, ba na so bana buƙata".

Ya yinƙura zai fice, Abbu ya riƙe shi ya ce "Umarni nake baka, ba shawararka ko ra'ayinka nake nema ba, dole ne wannan, aurenka wani satin, na kai kuɗin aure da komai, dole ka nutsu ka shiga hankalinka, idan ka illata musu ƴa ko kasheta kuma, zan sallamawa duniya kai, wannan shi ne hukuncin da na yanke"

A fusace ya ce "Meyasa zaka yanke wa rayuwata hukunci, ba tare da amincewata ba bayan ka daɗe da sallamawa duniya rayuwar tawa? Ka yi hakan ne saboda farincikin matarka ko? Ta daina ganina na gusa na bar mata gidan nan ita da iyalinta. Da zan iya wallahi garin zan bar muku na ɓacewa ganinku ku samu cikakken kwanciyar hankali kamar yadda ku ke buƙata, amma ba zan iya ba. Ka sani ina ta'amalli da miyagun ƙwayoyi, da gaske zan iya kashe ƴar mutane, ko na illata ta, sai dai ba na fatan na fi haka lalacewa, idan ka yi mini baki, zan ƙara lalacewa ne zan bi umarninka, amma duk abun da na yi mata da ni da kai zamu ɗauki nauyin zunubin. Saboda ni babu mata a tsarin rayuwata, miyagun halittu da babu Allah a ransu, bana fatan raɓar su, saboda yadda tasirin kaidinsu ya kassara rayuwata, kassarawar da ba za ta gyaru ba, mace ɗaya da nake wa kallon rayuwata, uwata kenan na rasata a yanzu babu wata mace mai sauran kima da mutunci a idona, nayi alƙawarin nesanta kaina da mata, nesantawa mai nisa ta har abada, amma ka karya mini alwashi, ta hanyar janyo mace rayuwata, ina sake nanata maka, duk abun da ya biyo baya, tare zamu ɗauki nauyin zunubin".

Ya saka hannu, ya cire hannun Abbu da ya riƙe masa riga, ya saka kai ya fice.

Har ya bar gidan, babu wanda ya sake magana, daga ita har Abbu.

Gaba ɗaya aka hana jauhar fita daga gida, ana ta shirin biki, ita kuma tana rama kamar ana tsotseta, duk ta fiƙe sai farar fata da idanuwa.

Maƙwabciyar su ta din ga cewa "Gaskiya mama ban so a aurar da jauhar yanzu ba, na so a bari maƙerin budurci ya gama ƙere mana ita, wannan kyawun da gidan wani hamshaƙin ya dace"

Anty ta ce "Wannan ma hamshaƙin ne".

A gida mama ta saka su surayya sa walida, suka dinga kwaɓe-kwaɓe suna murzawa jauhar da sunan gyaran jiki.

Malam jamilu ya shiga matsananciyar damuwa, da samun labarin auren jauhar, dan har ga Allah yana matuƙar sonta, tsoron kar ta daina ganin mutuncinsa, ya sanya ya ɓoye mata.

Gidan jauhar da aka je jere, yana da girma, sai dai tsakar gidan tsurar ƙasa ce, cikin ɗakuna babu floor, sai dai an yi plasta a ɗakunan, falo ɗaya da ɗakuna uku a ciki, kowanne da banɗaki, sai kitchen a tsakar gida da tsakar gida mai girma.

An yi wearing ɗin wutar lantarki, a gidan.

Sai buhunhuna, aka shimfiɗa a ƙasa, sannan cikin ɗakunan aka saka leda, falo kuma aka shimfiɗa carfet, saboda duk turɓaya ne.

Tagogin duk babu na kirki, sai kame-kame da faci.

Sai kujerunta, ƴan gida masu kyau, ɗaki ɗaya an saka furnitures, ɗaya kuma sai aka saka ƙatuwar katifa da wardrobe mai biyu, abun saka takalma. Duk da haka gidan ya yi kyau.

Amarya ta din ga fargaba da tunanin, waye mijin nan, da haryanzu za ace, bai taɓa ganinta ba, kuma ba ta taɓa ganinsa ba? Kuma ya amince da zai aureta.

Dogon gashinta baƙi, aka gyara mata shi, aka yi mata lalle ja da baƙi.

Haka kurum take tuna Alhaji mu'azzam, a haɗuwarsu biyu, yadda yake nuna yana sonta, ba ta son ya zai ji ba, idan aka ce masa an yi mata aure.

Kodayeke ita ba ta san dalilin fasawa da shi ba.

Su liti suka lura da shirun Al'amin ya ƙara yawa, duk da ba mai yawan magana ba ne dama, sai ya zauna yayi shiru yana zancen zuci.

Walid ya ce "Baaba, wai dan Allah kwanan nan meyake faruwa ne? Kamar ka na cikin damuwa" tabbas ba dan Walid ya tambaye shi yanzu ba, ba zai gaya masa ba.

Ya karkace ya ɗaukko invitation a aljihunsa, ya miƙa wa walid.

Wani irin ihu walid yayi, haɗi da kururwa, yayi katantanwa a ƙasa ya kuza uwar ashariya.

Sannan ya ce "Allah dai ya biya maza, dama zaka afkawa sabgar nan, ka yi mana shiru haka? Ba ka gaya mana ba, balle mu shirya saura kwana uku fa".

Sauran matasan da ke wurin suka miƙe suna tambayar Walid ko lafiya?.

Ya miƙa musu invitation ɗin, take suka hau shewa suma, suna dara.

Kawai ya dafe kansa, yayi shiru.

Walid ya ce "Wai tsaya, auren dole za ayi maka ne? Na ga baka murna, kuma shi ne ba ka taɓa kai mu ehhh, mun gaisa da antyn namu ba, iya wuya mun samu mai dafa mana abinci"

"Walid, Abbu ne ya shirya komai, ni ko ganinta ban taɓa yi ba, kuma ba na fatan na ganta, kuma ba kowa ne ya shirya wannan abun ba, sai wannan shaiɗaniyar matar ƴar haramun, ya ce umarni yake bani ba shawara ba, ni kuma na yanke guduwa zan yi, ba abun da zai haɗani rayuwa da wata mace, ba za a mayar da ni nusari ba, kalli yadda mace ta yi silar rushewar farincikin rayuwata gaba ɗaya"

Walid ya zauna kusa da shi ya ce "A'a maza, duk lalacewar naka naka ne, kai ka san albarkar dattijan ke riƙe da mu, ka daina kallon abun da yake yi maka na rashin jin daɗi, idan yayi maka baki ƙara watsewa zaka yi. Duk da lokaci ya ƙure, dole ayi celebration, zamu gayyaci gayu a sha shayi a babbaka hayaƙi, abun farin ciki ya same mu" ya ƙarasa maganar suna shewa, ban da Al'amin da zuciyarsa kamar ta yi bindiga.

Hatta kayan da Al'amin zai saka na aure, sai da Abbu ya saya wa Al'amin, dan ko ganinsa bai sake yi ba, sai dai ya fita yawon neman sa.

Ƙarfe goma na dare, su Walid suka shirya party, aka dafa shayi aka raba lemuka, da kayan shaye-shaye.

Gogan yana gefe, yana zancen zuci, har ga Allah so yake ya gudu, amma ya san ya gudu alaƙarsa da Abbu za ta ƙara tsami. Kuma ya san ko ya gudu sai ya dawo, ba zai iya barin Abbun ba.

Tunani yake kowace mai tsautsayin da ba a so, ce haka, aka zaɓi a aura masa oho.

Ana tsaka da walimar hayaƙin, faɗan daba ya kaure, Al'amin kuma ya koma gefe ya ƙi magana, ƴan sanda suka yi wa wurin dirar mikiya, saboda rahoton da ƴan unguwar suka kai wa jami'an tsaro, ai kuwa suka kame su har da shi suka tafi da su ana gobe ɗaurin auren da bai san wacece matar ba.

Ayshercool 08081012143

20 🔞₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143

90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724

Abbu kuwa hatta ɗinkin da Al'amin zai saka, ya yi masa, sai dai tun ranar da ya gaya masa, bai sake saka shi a idonsa ba.

Yana zaune yana ta mitar rashin ganinsa rahila ta ce "Ba fa zama zaka yi ba, tashi zaka yi ka je ka nemo shi duk in da yake, kar ya kunyataka a idon duniya. Kana kallo yanzu na sauke mayafina daga gidansu amaryar, sun yi walima, duk sun gama shiri, na kai musu mukullin gida, har jere sun yi, fita zaka yi ka nemo shi ai"

Haka Abbu ya shuri takalama ya bazama, aka sanar da shi, su na can wata unguwar, suna walimar aurensa.

Ya bazama ya tafi, yana zuwa ya tarar da labarin ƴan sanda sun kama su duk sun tafi da su.

Hankalin Abbu ya tashi, ya tafi division ɗin nan unguwar aka masa a station ɗin ma artabu aka yi da su, an kwashe su an kai su anti daba, ya ce wallahi ba za shi anti daba a daren nan ba saboda shi.

Da ya koma gida kuwa, rahila kamar ta ari baki saboda mitar, meyasa bai je ba a sake shi, kar ya basu kunya, ya ce idan za ta iya, ta tafi.

Jauhar kuwa su mama suka sakata a ɗaki, suna yi mata nasiha, fuskokinsu ɗauke da fara'a da jin daɗi, da nanata mata ba zasu zaɓa mata abun da zai cutar da ita ba.

Ita dai ta damu sosai ta ga waye wannan mijin, da har suka ga ya dace da ita? Har a ranar idonta da kwanciyar jinin jifan da mama ta yi mata da takalmi.

Washegari ranar juma'a, za a ɗaura aure a babban masallacin juma'a, amma Al'amin yana tsare.

Sha ɗayan rana, sai ga P.A ɗin Honorable indabo a anti daba da kansa, ya je belin Al'amin, wanda ya yi hakan ne, saboda aikinsa da yake son ya ƙarasa masa.

Suka din ga sara masa, suka gaisa ya gaya musu wurin wanda ya zo, yake son ya yi beli, da wanda ya aiko shi"

"Gaskiya malam yaron nan ba zai ci bulus ba, state CID zamu kai shi"

P.Aya ce "Ayi haƙuri, in anjima za a ɗaura masa aure, ko dan albarkacin wannan a sake shi mana"

"Wai ka san me ya yi kuwa?"

"Eh, an ce sun yi shaye-shaye sun tayar da tarzoma ko?".

"Ai da wannan ne da sauƙi, ya saba zuwa wurin nan a kan haka, jiya ƴan sandanmu sun kamo su, saboda sun sha tana gaya musu gaibu, a tsakiyar harabar station ya ɗaga ɗan sanda ya buga da ƙasa, saboda yana ganin ya isa, ya na ji da ƙarfi. Kuma ya din ga yi wa mutane wani shegen kallo kamar kumurci, zai gane kurensa, CID zamu kai shi"

Ana haka shugaban kula da sashen ya shigo da shi da wani matashin ɗan sanda, suka ƙame suna sara masa, ya kalli P.A ya ce "Lafiya kuwa?".

Suka gaisa sannan ya ce "Honorable ne dai ya kuma aikoni ayi ban baki, a saki Mai dogon zamani "

"Ba su gaya maka laifin da yayi ba? Jami'inmu fa ya daka, ba ya ji yaron nan ko kaɗan"

"Sun gaya mini, amma kamar yadda aka saba, honorable ya bayar da saƙo"

Ya numfasa ya ce "A fito da shi da sauran yaran da ku ka kama" aka buɗe Al'amin, da yaransa, ya fito yana ɗan jirga ƙafarsa a hankali, saboda taron dangin da suka yi masa jiya, suka yi masa dukan tsiya, daga jami'in ya tankaɗa ƙeyarsa, ya waiwayo a fusace ya saka ƙafa ya kwashe shi a wurin.

Daga shugaban, har PA ɗin babu wanda ya kalla, ya kama hanyar ficewa daga cikin station ɗin.

Ya girgiza kai ya ce "VIPER kenan, Allah ya shirya".

PA ya ce "Viper kuma?"

"Eh sunansa kenan a gidan nan, sunan da suka saka masa kenan, ban san sau adadin da muka kama shi ba, ban taɓa ganin mutum mai bala'in taurin kansa ba, mu daka mu daka wallahi ko gezau ba ya yi, ga wani sheɗanin kallo da yake yi wa mutane, kai ka ce kumurci ne zai kai sara, shiyasa nake yi masa sha'awar hakar tsaro, yana da girma da kwarjini na gaske, amma shi ba a saka shi ba a hana shi".

P.A yayi murmushi ya ce "Ai tun da ka ga honorable ya riƙe masa wuta, ba ya wasa da lamarin sa, kai ka san ba ƙaramin mara ji ba ne".

"Eh ai ku ne ke goya musu baya"

"Ai sabgar tamu ce dole sai da su".

Kafin PA ya gama sallamar su ya fito, tuni su Viper sun ɓace.

Har gida walid ya je ya sanar da Abbu, an sako su, amma yayi yayi da shi, ya taho gida yayi shirin ɗaurin auren yaƙi.

Abbu ya bi walid, har in da Al'amin yake, ya mimmiƙe yana bacci, jikinsa duk shaidar dukan da ya sha a station.

Maganar duniya Abbu yayi, amma yayi burus ya ƙi tashi, sai da ya cire takalmi ya hau ƙwala masa, sannan ya tashi da ƙyar yana muzurai, Abbu ya tasa shi a gaba zuwa gida.

Ba ƙaramin kyau manyan kayan suka yi masa ba, yayi wani irin kyau na mussaman, kwarjinin da Allah ya yi masa ya fito sosai da sosai.

Bayan sallar juma'a aka ɗaura masa aure, bayan an saukko daga masallaci, babu wanda ya sake ganinsa.

Jauhar kuwa gabanta sai tsananta faɗuwa yake yi, ƴan ƙawayenta na makaranta, suna ta tsokanarta, suna yi mata raha, amma ta kasa sakewa.

Mama ta hau ta da zagi a gaban mutane, wai sai ta saka an ce aure dole za ayi mata, taƙi walwala ko wanka ba ta yi ta shirya ba.

Jiki babu ƙwari, jauhar ta yi wanka, aka yi mata kwalliya.

Tayi kyau sosai da sosai, dama dai-dai gwargwado tana da hasken fata da kyanta na fulani.

Baba ne ya fara dawowa gida, gaba ɗaya jikinsa a sanyaye, ana ta yi masa Allah ya sanya alkhairi.

Ya saka aka kira masa jauhar, zuwa ɗakinsa.

Cikin tsananin tashin hankali da damuwa, Saifu ya shigo gidan, yana ƙwalawa baba kira.

Mama ta ce "Saifu lafiyarka ka ke yi wa mahaifinka irin wannan kiran haka?"

Bai saurareta ba, ya shiga ɗakin baban, mama da anty suka bi bayansa, 'yan biki kuma suka yi cirko-cirko.

"Baba wane irin miji ka aurawa jauhar? Tun a masallaci nake nemanka ban ganka ba"

Baba yayi shiru, ya ƙi bashi amsa.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull