Kenza eBookz

Karfe a wuta book 2 complete novel - Chapter 6

Karfe a wuta book 2 complete novel - Chapter 6

Karfe a wuta book 2 complete novel Chapter 6: Karfe a wuta book 2 complete novel Chapter 6. Shugaban ƴan sintirin ya ce "Dan meyasa zaka din ga shigo mana…

4,427 words

Shugaban ƴan sintirin ya ce "Dan meyasa zaka din ga shigo mana unguwa? Kai da hukuma take nema ruwa a jallo, ka san kai tauraruwa mai wutsiya ne, duk in da ka je sai ka yi fitina, tun da yaranka suka yi ɓarna jiya, na san cewa nan ma zaka shigo. Duk ka lalata mana yara ka tafi ka barmu da masifa, kuma yanzu ka dawo kana cigaba da bibiyarmu"

Cikin tsawa Walid ya ce "Kai, ka iya bakinka, wallahi ko na ɓare maka shi har ƙeyarka".

Cikin tamkakiyar fuskarsa Viper ya ciro zungureriyar wuƙar da take ƙugunsa, ya karta ta a ƙasa tayi wata irin ƙara, sannan ya ɗora ta a gefen wuyan mutumin ya ce "Ƴaƴanku za su cigaba da yi mini biyayya, sai na mayar da unguwar nan mafi munin sansanin ta'adancci da zubar jini, komai ya faru ai ku kuka so, yanzu dan Allah kai ba ka ji kunyar faɗar abun da ka faɗa ba? Duk in da zan je zuciyata na tsakiyar unguwar nan, kuma zan cigaba da shiga da fita yadda nake so, har sai na yi maganin azababbiyar ƙishirwar da ta addabi ruhina. Duk abun da na aikata muku na ɓarna, ku kuka so, mutanen banza masu butulci, kun taki sa'a da nake dakon alƙawari mai nauyi a kaina, ban da haka tun a fitowa ta, ɗaya bayan ɗaya zan yi muku kisan gilla. Idan na sake shigowa unguwar nan, kai da wannan mutanen, ku ka yi yinƙurin yi mini wani abu, duk wanda na kama, zai zama mutum na farko da zan yi wa yankan rago!" Gaba ɗaya suka zuba masa ido, suka kasa ko motsin kirki, saboda yadda suka zagaye su da miyagun makamai.

"Ku karɓe wayoyinsu, ku rufe mini su, ku saurari order da zan bayar. Duk wanda yayi muku gardama ku karya mini ƙafarsa, ko ku tsarge masa cinya".

"Angama boss"

Yana fita daga office ɗin, suka mayar suka rufe, suka ƙwace musu wayoyi, sannan suka tsaya a kansu da wasu irin zabga-zabgan wuƙaƙe, kamar a abba tuwa.

Babu wanda ya iya wani ƙwaƙwƙwaran motsi, dan a yadda matasan suke muzurai, kuma shaye-shaye ya huda su, duk umarnin da ya ba su za su bi.

Sannu a hankali yake tafiya, har ya kawo cikin layin, ya tsaya a ƙofar wani gida, ya shafe tsawon lokaci kawai ya zubawa gidan ido, yana zancen zuci, daga bisani ya ƙarasa ya ƙwanƙwasa na kusa da shi, ya ja mask ɗin sa, ya rufe fuskar shi.

Yaro ne ya fito ya ce "Waye?", ya cewa yaron "Ka je ka cewa babanka an zo duba shi"

Mintuna kaɗan yaron ya dawo, ya ce ya shiga.

Bai yi sallama ba, haka ya kunna kai cikin gidan, har tsakiyar falon maigidan, ba tare da an yi masa iznin hakan ba.

Daga maigidan har matar gidan, da ƴan matan yaran, tsuma suka hau yi, ganin wanda ya shigo har cikin gidansu.

Ya zaro wuƙarsa ya ajiye a gaban malam lawan, sannan ya ɗaga wani mukulli ya ce "Na rufe gidan nan da kwaɗo ta ciki, kuma duk wanda ya yi wani ƙwaƙwƙwaran motsi, zan zaunar da shi kamar yadda na zaunar da kai" yayi maganar yana kallon malam lawan.

Ya durƙusa kama ƙafar malam lawan, da aka naɗe da bandeji, ya dudduba sannan ya ce "Ɗori yayi kyau, sai dai na yi mamakin yadda aka dawo da kai gida, maimakon ka yi jinya a asibiti"

ya saita tsinin wuƙarsa a cinyar malam lawan ya ce "Waye ya ɗauko ka daga asibiti?"

Cikin tashin hankali matarsa ta fara kuka ta ce "Dan girman Allah Aminu kar ka yi masa wan....

"Wallahi ki ka sake magana, sai na karya ɗaya ƙafar, ka gaya mini kafin na huda cinyarka" yayi maganar cikin razananiyar muryarsa.

Cikin matsanancin tashin hankali ya ce "Wallahi wasu mutane ne, ban san su ba, su ne suka sauya mini asibiti, lokaci zuwa lokaci, suke zuwa da likitansu ya duba ƙafata, kuma sun gargaɗeni a kan muddin wani ya ji kaine ka yi mini haka, sai sun kashe ni"

"Waye ya kai ka asibiti ranar da abun ya faru?"

Cikin kyarma da rawar murya malam lawan ya ce "Wallahi kana barin wurin, ina wannan kakarin, wani ya zo yayi mini kashedin muddin na ce kai ne zai kashe ni, ya watsa mini wani abu, ban sake sanin in da kaina yake ba, sai da safe maƙwabta suka tsince ni, na ce masu masu ƙwacen waya ne suka yi mini"

Aminu ya ware masa jajayen idanunsa sosai ya ce "Idan na samu labari akasin abun da ka gaya mini, kar ka manta take na, maciji nake mai mugun dafi, sai na maka karayar da ba zaka sake taka ƙafarka ba a doron duniya. Zan cigaba da zagayowa zan kuma cigaba da sanya maka ido. Kar ka manta ka yi mini ganganci daban-daban, na kawar da kai, na riƙe biyu a raina idan ka yi na uku kasheka zan yi har lahira".

Malam lawan ya jinjina kai, yana jin yadda mararsa ta cika fam da fitsarin tsoro.

Viper ya a miƙe ya juya ya bi hanyar fita.

Sai da suka tabattar da tafiyarsa, sannan matar malam lawan ta ce "Na shiga uku, baban su Amir dan Allah meya aike ka sake shiga sabgar mutumin nan? Daga ƴan sandan har ƴan ƙato da goran kar wanda ya ƙara tambayarka abu a kansa ka ce ka sani, kalli bala'in da ka jefa mu a ciki?"

"Ke dalla rufe mini baki, tun da yanzu na tsira da raina shikenan, ina ga sayar da gidan nan zan yi na bar unguwar, idan ba haka ba wataran kasheni zai yi "

"Ai koma menene Allah ya ƙara wallahi, abun da ka yi wa bawan Allah nan ka yi butulci da yawa"

"Au so ki ke na rufawa mutumin banza asiri Haule? Ni ki ke gaya wa haka?"

"Oho ai gaskiya ce" haka suka cigaba da faɗa, tana mita da ɗora masa alhakin janyowa kansa ko ma menene.

Aminu kuwa, ta waya ya ce wa su ɗan mama, su baro ƴan vigilante ɗin, su bi shi gida.

A gidan suka tarar da shi, ya dubi Walid ya ce "Ka yawaita survey a cikin unguwar nan, mutumin nan ya tabattar mini da cewa, wanda suka canza masa asibiti, suna zuwa da likta har gida yana duba shi".

"To shikenan Oga, in sha Allah za ayi yadda ka ce"

"Kuma na san mutanen nan ne, da mutumin yake kirana a waya, ya zama dole na san waye, da kuma manufarsa a kaina, da yake bibiyata har haka".

Walid ya ce "An gama maigida"

Nabila kuwa tun da ta shiga aiki tana office ɗin ta, suna communicating da Yaya Nasir.

Wayar sumayya ce ta shigo ƙaramar wayarta, dan haka ta ajiye ta hannunta ta ɗaga da sauri ta ce "Sunayya yaya ake ciki?"

"Kamar dai yadda na yi tsammani" ta bata amsa.

"Me ki ka yi tsammanin? Yi mini gwari-gwari"

"Ba irin labarin da suke buƙata ba kenan, hakan ka iya kawo musu naƙasu ga cigaba da kuma tasirin gidan radiyon su, kuma wai ba ni da cikakkiyar shaidar abun da na faɗa"

"Haba Sumayya, ni ina da shaida fa, ga kuma yaya Nasir ma, kuma ya zaki tsaya a wurin wannan shashashar matar da ba ta son cigabanki? Ki yi wa Manager magana mana direct, nima ina da lambarsa, sai na yi masa magana".

Sumayya ta ce "Nabila kenan, duk kanwar ja ce, shi ne ya jaddada mini hakan da kansa".

"Allah wadaran naka ya lalace, Yanzu sumayya shikenan zuba ido zamu yi? Babu wani abun yi?"

Sumayya ta ce"Idan na matsa zan iya rasa aikina, abun da ya nuna mini kenan, wai ba za su iya jayayya da hukuma ba, kuma na kawar da kaina a kan abun da ba zan iya jurewa ba, da ina da wata hanyar samun kuɗin, da ajiye aikin nan zan yi Arfa"

"Shikenan, zamu yi magana anjima, see you later" ta ajiye wayar ta zauna ta yi shiru.

Wani irin tsaki ta ja, tana mamakin yadda galibin private organizations suke buɗe wurare, for their personal interest kawai, kodayeke na gwamnatin ma menene, duk ɗaya.

Ganin ɓacin ran ba zai amfanata komai ba, tana da abubuwan da yakamata ta yi, ya sanya ta fita ta tafi office ɗin Barrister Habib.

Yana ta aiki a system, ya ɗago ya amasa mata sallamarta, ya cigaba da aikinsa.

"Barka da aiki barrister".

"Yauwwa" ya amsa a taƙaice.

"Barrister wai haryanzu fushin ka ke yi, na shiryu fa na daina duk wani abu da nake yi, sonake na zama cikakkiyar lawyer abar koyi ga wasu, kamar gwanata Barrister Naja'atu Bunkure" da ɗan sauri ya ɗago ido ya kalleta ya girgiza kai ya ce "No wonder, shiyasa ba zaki cigaba ba"

"Subhanallah, meyasa?" Tayi maganar tana ware ido.

Maimakon yayi magana, sai yayi mata shiru.

Wani irin kallo tayi masa, a zuciyarta ta ce 'Sai fa ka yi magana barrister'

A zahiri kuwa ta ce "Ni dai haka kurum nake sonta, ayyukan ta na jin ƙai suna burgeni, ina son zama kamar ita. Amma tun da haka ne ma, na canza kamar kai nake son zama, daga yau kai ne mudubina" tayi maganar tana murmushi.

"Ke da ba zaki iya zalunci ba, mu ne azzalumai ai"

Nabila ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, waye ya faɗi haka? Wallahi ba haka bane ba, ni ban ce ba"

"Idan har kina son zama shahararriya, dole ki yi iya yinki, a kan duk abun da ya zo hannunki, ko da kuwa babu tabbacin zaki yi nasara, idan ba zaki iya ba kuma, you can leave"

"No, zan iya, ai na shiryu yanzu"

Ya buɗe drower gabansa, ya ɗaukko wani file ya ajiye mata sannan ya ce "Wannan client ɗi na ce, a nan ƙofar na'isa gidanta yake, zan turo miki cikakken adress ɗin ta, ki je ku yi magana, sannan ki yi tunani a kan case ɗin nata" Cikin girmamawa ta ce "Na gode sosai, zan yi in sha Allah "

Tana fita daga office ɗin nasa, ta gyatsine baki, ta ce "Kamar ni za a aika, gidan wata ƙatuwa, ba ma ta zo office ta same mu ba, hamshaƙiya saboda ga ƴar Nabila ƴar wahala. Amma bakomai da na zama abun da nake so, na fi ƙarfin kowane irin wulaƙanci" ta koma nata ofishin tana cigaba da ƙunƙuni.

Da ta koma gida ma, ba ta bi ta kan aiken da barrister yayi mata ba, ta kwanta ta sha baccinta, bayan ta tashi ta shirya ta yi wanka, ta tafi gidansu sumayya.

Sun jima suna tattaunawa da sumayya, a kan harkar aiki, har sumayya ta din ga ja mata kunne, a kan kasadar da take yi, tare da nuna mata illar hakan a matsayin ta na ƴa mace, ta kunnen hagu maganganun sumayya suka din ga shiga kunnenta suna fita, dan ba ta ji sun shigeta ba.

Ta bawa Sumayya labarin aiken da barrister Habib ya yi mata.

Sumayya ta ce "Kuma zaki ɗin?"

"To ya zan yi?"

Sumayya ta yi dariya ta ce "Ai na zata taurin kan yana nan?"

Nabila ta yi murmushi ta ce "Na ajiye taurin kai, zan kama aikina yadda yakamata, ai sai burina ya cika sai na binciko wacece Bunkure kuma in sha Allah, sai sunana ya shafe nata a tarihin duniyar ma'abota shari'a".

"Allah wadaran naka ya lalace, Nabila, wai ke wani irin taurin kai ne da ke ne? Ke abu ba ya wucewa a wurinki ne? Ki bar ta kawai, idan Allah ya so, tana raye zata ga nasarar da zaki yi a rayuwa"

"Ina kwance nasarar za ta zo ta same ni kenan? Ke ƙyaleni, ina ga sai Allah ya kaimu friday da yamma, zan je waccan unguwar gidan matar, na ga bai turo mini contact ɗin matar ba tukuna, zaki rakani?"

Sumayya ta ce "A'a gaskiya, wannan unguwar, ana ta fama, kamar ba kya jin radiyo, yadda suke fama da faɗace-faɗacen daba. Ki gayawa barrister ya ce kawai matar ta je office ɗin ku, ko kuma ki bari komai ya lafa, dan kullum cikin faɗan daba suke"

Nabila ta ce "So ki ke in kasa samun information ɗin da nake so daga bakinsa kenan? Ai lallaɓa shi zan tayi, sai na san wacece matar nan. Kodayake ma na saka Yaya Nasir ya rakani" sai kuma ta yi shiru, ta sake maimaita zancen Sumayya a zuciyarta.

*Wannan unguwar ana ta fama da faɗan daba*

Ta sake kallon sumayya ta ce "A unguwar ne aka ce yaran Aminu Viper sun yi sare-sare?"

Sumayya ta yi shiru tana kallon idon Nabila.

Nabila ta yi murmushi ta ce "Kar fa ki kawo komai a ranki, ba wani abun zan aikata ba, bari na tafi kan Abba ya dawo ya nemi ina nake" ta ɗau jakarta ta fita, tana jin kamar matsalarta ta zo ƙarshe.

*Masu nema daga farko, ku yi joining link channel ɗina na saman page, idan kun shiga zaku samu daga farko*

Arewabooks ayshercool7724 Watpad ayshercool7724

Ayshercool 08081012143 [7/21, 2:16 PM] null: *ƘARFE A WUTA*

AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION BRIGHT PENS SECOND BATCH

https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

7

Katafaren falo ne, wanda girmansa ya ishi wani talakan gina gidan da zai rayu a ciki, talabijin ɗin da ke falon kawai ta fi rabon bango. Kujera set biyu ce a falon, kuma tsakanin kowane set da wani akwai tazara.

Tinkis-tinkis haka ya fito cikin wata irin dakakkiyar shadda maroon, sai ƙyalli take yi, ba sai an faɗa ba ka san akwai tazara mai nisan gaske tsakanin sa da talauci.

Ba wata ƙiba ce da shi ba, amma cikinsa yayi kurtsitsi a riga, har wani nishi yake yi.

Ya nemi wuri ya zauna a ɗaya daga kujerun falon, ya kalli matasan da suke zaune a ƙasa a kan carfet. Dukkansu babu mai suturar kirki a cikinsu, kansu duk askin banza, yanayin shigarsu da fuskarsu kawai za ta tabattar riƙaƙƙun masu laifi ne.

"Allah ya taimaki maigida" cewar ɗaya daga cikin su.

"Ya aka yi madaki?"

"Akwai ƙura ne, ƙurar kuma na neman zama gagarumar guguwa"

"Ina jin ka"

"Aminu Viper, haryanzu jami'an tsaro ba su kama shi ba, ya sa an kaiwa yarana mummunan hari, an yi musu miyagun raunuka, jami'an tsaro sun kama yarana sun saki nasa, wanda aka kai asibiti ma, an kwashe su daga asibiti babu wanda ya san in da aka kai su"

Mutumin yayi tsaki ya ce "Ina mamakin yadda mutum ɗaya ya gagari kamun hukuma, ni anya ba raina mini hankali ma suke yi ba a kansa? Yanzu menene abun yi?"

"Ka saka a sakar mini yarana, dan sai da su ayyukanka suke yiwuwa, kuma dole mu yi shiri sosai, idan da hali mu mu nemi in da yake mu kashe shi kowa ya huta"

Mutumin yayi shiru yana kallonsa sannan ya ce "Aikuwa da na yi maka tukucin da baka taɓa tunani ba, zan saka a saki yaran nan anjima kaɗan, sai dai duk yadda zaka yi ka yi, a samo yaron nan, dama mugu shi ya san makwantar mugu ai"

Madaki ya sauke numfashi ya ce "Zan shirya gagarumar ɗaukar fansa kan mai uwa da wabi a unguwar su, jinin yarana da suka zubar ba zai tafi a banza ba, dan shammatar su ka yi, suka mamaye su ba na nan"

"Wannan ku ta shafa, ni babban burina shi ne Aminu, muddin yaron nan yana numfashi, kamar sarƙa ce a wuyana, dole a kawar da shi".

Madaki ya ce "Ba kai kaɗai ba, ko kuma in ce da ni da kai kusan abu ɗaya ne a wurinsa, nima ka san akwai tawa ni da shi, tsohuwar gaba ce ta tsawon shekaru, wanda a kanta unguwanninmu suka kasa zaman lafiya har yau, ga kuma wannan al'amari da ya faru. Muddin ban kashe Aminu ba, ni zai kasheni"

Ya jinjina kai ya ce "Ai Viper na fuskanci ƙarfe ne a wuta, ya fi ƙarfin ɗauka da hannu, sai dai da ɗan uwansa ƙarfe, kai kaɗai zaka iya maganinsa"

"Ka bani lokaci kawai, zan kuma ƙoƙartawa, matsalar ko yaransa ba kowa ne ya san in da yake ba, amma na san dole Walid ya san in da yake, amma shi ma Walid ba lafiya ba ne taɓa shi, ka dai bani lokaci"

"Babu isasshen lokaci, ka yi huɓɓasa kawai"

Madaki ya jinjina kai.

Mutumin ya ɗebo kuɗi ya bashi, ya sallame su, suka juya suka fita da shi da yaransa.

Nasir ne tsaye a office ɗin sa, ya kalli matashin da yake zaune, da aƙalla zai yi sa'ansa ya ce "Mu'azzam lamarin ƙasarmu sai Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ka san da ƙyar na gano station ɗin da yaran nan suke, ba ma ta yankin da abun ya faru ba ce?"

Mu'azzam ya yi murmushi ya ce "Haka ka ce mini"

"Gaba ɗaya yaran under age ne, kuma duk cikinsu babu yaran Aminu, dan tuni an sake su, sai wani wai madaki, na ce dai a ajiye mini su, da yiwuwar mu kama madakin, zai iya sanin in da Aminun yake,tun da abokin faɗansa ne, amma da na yi magana da DPO ɗin division ɗin yankin, ya ce shi ma madakin ba ya kamuwa, kuma ya addabi yankin yana da yara sosai da sosai. Abun takaicin ma ba unguwar su ɗaya da Aminun ba, amma suke cigaba da tayarwa da mutane tarzoma"

Mu'azzam ya ce "Harkar nan tamu sai fa Innalillahi wa Innalillahi raji'un, muna tufka manyanmu na warwarewa"

Nasir ya ce "Bari kawai, zan yi iya ƙoƙarin da zan yi, ni zan kama Madakin, Arfa har asibitin da aka kai waɗanda aka yi wa rauni ta je, muka yi waya kafin na je wai an kwashe su, an bar asibitin da su, na fara zargin anya ba jami'an mu ne aka samu bara gurbin da suke mara masa baya ba"

Mu'azzam ya ce "Ba abun mamaki bane ba, amma meya kawo Arfa cikin wannan lamari, ta bar aikin lawyern ne?"

Yayi murmushi ya ce "Rigima mana, yarinyar nan ta zarce tunaninka, ba ta wasa da duk abun da ya shafe ni ko cigaba na"

"Hmm Nasir kenan, wai yaushe zaka gayyacemu sabgar nan ne? Shekarun ka fa suna ja"

Nasir ya rausayar da kai ya ce "Mama ce ta hana, ta nuna ba ta so, ban taɓa gaya mata ba, saboda tun kafin na furta maman ta gargaɗe ni a kan haka, kuma haryanzu ni ban ji ina son kowace yarinya ba, ita ɗin dai nake so. Ban san adadin samarinta da na kora ba saboda kishi. Yadda take son abun da nake so da son cigabana, na san da zan furta ina sonta, ba zata ƙi ba, amma na rasa yadda zan yi da mama".

"A'a Nasir, dan Allah kar ka zalunci yarinya, haka zaku zauna shekaru na tafiya, kai baka aureta ba, kuma ba ka bari wani ya aura ba? Wannan ai mugunta ce, ka yi magana da Abba mana".

Nasir ya girgiza kai ya ce "Manta kawai, abun ya wuce yadda ka ke tunani".

*** Arfa na kitchen tana taya baba magajiya aiki, suna hira tana tambayar baba magajiya kwatancen cikin unguwar ƙofar na'isa, dan zuwa aiken barrister Habib, dan ita ba zuwa ta taɓa yi ba.

Baba magajiya na girki, ita kuma tana wanke-wanke a sink.

Siyama da take ƴa ta uku ga mama ce ta shigo kitchen ɗin, ta jefawa Nabila kwanukan hannunta maimakon ta ajiye.

Nabila ta yi shiru, ta cigaba aikinta suna hira, duk da abun ya ɓata mata rai.

Amfani ta kuma yi da kofi, ta wurgowa Nabila cikin sink, cikin zafin nama da masifa, Nabila ta ɗauki kofin ta jefa mata a fuska ta ce "Ai ba baiwar ubanki ba ce ni, da zaki din ga jifana da kwanuka"

"Nabila ni ki ka daka?"

"An dake ki ɗin?"

Baba magajiya ce ke ƙoƙarin basu haƙuri, amma siyama ta shaƙe Nabila, Nabila ta rarumo wani kwano ta buga mata, dambe ya kacame.

Baba uwani ta yi ƙoƙarin raba su, amma abu ya gagara.

Ta fito falo da gudu, tana neman taimako.

Dambe tun daga kitchen har falo, duk abun da Nabila ta rarumo sai ta kwaɗa mata, kamar wasu kuraye.

"Mahaukaciyar ina ce ke? Ke kullum haka zaki ƙare ki zagi wannan ki ci mutuncin ƴaƴan gida kina ƴar karere"

Cikin baƙin ciki Nabila take kallon mama, tana iya ƙoƙarinta wurin danne abubuwan da mama take yi mata, duk faɗanta da tashin hankalin ita da yaran gidan suke yi, amma sai mama ta shiga ta zaƙe ta shigarwa yaranta.

Anty ta ce "gaskiya maman Sauda wannan ba girmanki bane ba, maimakon ki yi musu nasiha, sai ki din ga aibata Arfa, ai ba a haka"

Siyama ta din ga zagin Nabila, zagi na cin mutunci, tsawar da Abba ya yi musu ne, ya sanya duk suka ɗago cikin tsuma.

Ya nuna nabila ya ce "Arfa, ban isa na saka doka ki bi ba ko? Siyama ba gaba take da ke ba? Nake jiyo muryarki tun daga waje kina zaginta?"

Arfa ta buɗe baki zata yi magana, amma ya daka mata tsawa ya ce ta yi masa shiru.

Siyama kuma ta fashe da kuka tana gaya masa har dukanta arfa tayi.

Aikuwa ta in da ya shiga ba ta nan yake fita ba, ya hana kowa magana ya yi wa arfa kaca-kaca saboda sanin ba ta ji, ga rashin haƙuri da taurin kai.

Da sauri ta tafi ɗakinsu tana wani irin kuka, ta je ta faɗa kan gadonta, jikinta har rawa yake yi saboda baƙin ciki takaici ta din ga kuka.

Cikin kuka ta ce "Ya Allah ka bani miji kowane iri ne, in dai zai zama alkhairi a gare ni, na tafi na bar gidan nan, na gaji Allah ka amsa mini dan girmanka, kowane iri ne zan iya zama da shi".

Can falo kuma, jikin Abba ne yayi sanyi, ganin arfa na kuka ya san akwai wani abu a ƙasa, dan idan tayi laifi, wataran ko kasheta zai yi ba zata yi kuka ba, duk da tana da saurin kukan.

Ya kalli Anty ya ce "Zainab je ki duba yarinyar nan, kar ciwonta ya tashi"

Anty ta jinjina kai, ta bi bayan arfa.

Mama kuwa a sashinta take yi wa Siyama mitar meyasa ba ta yi wa Nabila dukan da za ta kasa tashi ba.

"Mama kin san yarinyar nan har aljanu take yi, haka kurum su tashi ni ta kashe ni, komai ta rarumo buga mini take yi, ba ki ji kafaɗuna ba"

Mama ta yi ƙwafa ta ce "Na rasa yadda zan yi maganin yarinyar nan, wallahi bana sonta ba na ƙaunarta, gaba ɗaya ba kwa gaban mahaifinku sai ita, in sha Allah sai ta zame masa masifar da ba zai iya shawo kanta ba, sai ta kwaso abun kunyar da za ta kunya ta shi a idon duniya".

Nabila kuwa ƙin saurar anty ta yi, ta sha uban kuka, Anty ta sanarwa Major kukan da take yi, ya basar kamar bai damu ba, amma ƙasan zuciyarsa sam babu daɗi.

Tsakar dare suke waya da sumayya, take gaya mata abun da ya faru.

Sumayya ta ce "Arfa, ke rashin haƙuri ne yake janyo miki wasu abubuwan, da kin yi haƙuri ba ki tanka mata ba, dama neman magana ta zo yi".

"Sumayya kin san ba zan iya ba, ni ina wulaƙanta mutane ne?"

Sumayya ta ce "A'a idan na ce kina da wulaƙanci Nabila na yi miki sharri, sai dai masifa da rashin haƙuri, ga jarababben taurin kai ba a gaya miki ki ji ko kaɗan"

Nabila ta ce "Sai dai ayi haƙuri da ni a yadda nake, ni ba zan yadda da wulaƙanci ba"

"Aikuwa zaki yi ta shan wahala dan ubanki"

Nabila ba ta damu da zagin da sumayya ta yi mata ba, domin idan da sabo ta saba, dan wasu lokutan sumayya playing role take yi kamar na uwa a rayuwarta, ta kan ji maganarta idan ta ga dama.

"Sumayya dan Allah ki yi mini addu'a, Allah ya bani miji kowane iri ne, in dai zai zame mini alkhairi a shekarar nan na bar gidan nan na huta"

Sumayya ta ce "Ba ki da hankali, kowane iri fa ki ka ce"

"Eh, wallahi idan ba haka ba, zan gudu na bar garin nan, na bar musu gidan, sumayya baki san me suke yi mini ba na gaji" ta ƙarasa maganar cikin shagwaɓa tana kuka.

Sumayya ta san komai, dan haka cikin rarrashi, ta kwantar da murya, ta din ga yi wa Nabila nasiha, da rarrashin ta, har ta sassauta kukan da take yi.

Da haka suka yi sallama, ta kwanta bacci.

Sai dai ta kasa baccin, saboda yadda zuciyarta take zafi, ta rasa me ta tsarewa maman su Sauda a rayuwa, da ita da yaranta suka tsaneta haka, Nasir ne kawai suke ɗasawa da shi, da ƙyar bacci ya kwashe ta.

Da safe ta shirya cikin wata abaya baƙa, tayi kyau ko karyawa ba ta tsaya yi ba, ta fito falo fuskarta babu walwala.

Kallo ɗaya zaka yi mata, ka san ba ta samu isasshen bacci ba.

Da kamar ta yi fuska tayi tafiyarta, amma ta haura benan Abba ta je ta gaishe shi, sai dai fuskarta babu annuri, babu raha da ta saba yi idan ta je gaishe shi.

Ya ƙura mata ido ya ce "Kin karya kuwa?" Ta ce "Idan na tsaya karyawa zan makara, zan karya a wurin aiki"

"Dan zaki makara sai ki fita ba ki karya ba, yaushe ki ka fara tsoron makara? Menene ma ya hana ki tashi da wuri?"

Tayi shiru tana wasa da yatsun hannunta, idonta yana cika da hawaye.

Ya saka hannu a aljihunsa, ya ciro kuɗi masu yawa, ya miƙa mata ya ce "Ga wannan na san wata yayi nisa, babu lallai ki na da kuɗi a hannunki, ki sai wani abun idan kin je ki karya, saura ki sai abun da zai ɓata miki ciki, ko ya cutar da lafiyar ki"

Kamar ta ce ya bar su, amma ta saka hannu biyu ta karɓa, ta ce ta gode, yanayin yadda take tafiya kawai, zai tabattar mata da tana cikin damuwa ko rashin lafiya.

Gaba ɗaya jikin Abba ya yi sanyi, a tsakiyar zuciyarsa yake jin zafi, idan ya ga Nabila a cikin damuwa, shiyasa wasu lokutan baya iya jure yi mata hukunci yake kawar da kai a kanta.

Duk iya ƙoƙarin da Nasir yake yi, a kan yaƙi da harkar daba, abu ya ci tura, dan yaran da aka kama ya koma ya tarar da wai an yi umarni daga sama a sake su, abun ya ɓata masa rai sosai da sosai.

***** A farfajiyar wata bishiya suke zazzaune, suna ta shaye-shayen kayan maye, duk sun cika wurin da ƙaurin hayaƙi.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull