Kenza eBookz

Karfe a wuta book 2 complete novel - Chapter 74

Karfe a wuta book 2 complete novel - Chapter 74

Karfe a wuta book 2 complete novel Chapter 74: Karfe a wuta book 2 complete novel Chapter 74. Ashariya Indabo ya din ga zabga masa, ya ce "Wallahi zan saka…

4,496 words

Ashariya Indabo ya din ga zabga masa, ya ce "Wallahi zan saka jami'an tsaro su kama ka, su ci ubanka, uwar yarinyar nan ta bayyana a kotu, an ambaci sunanka, duk da ba a faɗi cikakke waye kai ba, ga maganar kuɗi na yi maka, duk ka yi kunnen uwar shegu da ni, Abdul kana son ka gama da duniya lafiya kuwa? Dole sai ka tozarta ni?"

"Daddy ba tozartaka zan yi ba, makomar rahama nake dubawa ita ma....

Wata ashar ɗin indabo ya lailayo, kamar ba babba ba, ya gama masifar, Abdul ya ajiye wayar ya dafe kai.

"Kai ma da naci kamar me, ka fitar da ni mana, ko ma me za ayi mini ayi mini, sai ɓoye ni ka ke yi kamar ciwo, ni kaina tun ina masifa har na gaji, haba dan Allah" tsaki ya ja, ya tashi ya bar mata dining ɗin.

*** "Abba ya yi tafiya, yau nake saka ran dawowarsa, zan nuna masa hoton nan, na ji mai zai ce, tun da kai kaƙi gaya mini wacece?"

"Yaya shari'ar ta kasance?"

"Alhamdilillah, babar ramma ta je kotu ta bayar da shaida, ina jin alamar nasara in sha Allah"

"Mhmm, a ina aka ganta?"

"Ta gudu ne wani wuri ta ɓuya, daga baya da taimakon barrister Habib, muka ganota"

Viper ya jinjina kai ya ce "ya nawa, ni ya ake ciki?"

"Shiyasa na zo ai"

"Ok"

"Kamar yadda na fara gaya maka jiya, dole ina buƙatar su oga walid, da wannan bugaggen a kotu su bayar da shaida"

"Wane bugaggen?"

"Oho ni na san sunansa ma? Amm sannan sai ka yi haƙuri, duk wasu rashin ji da ka yi, sai mun yi exposing ɗin su a kotu"

"Rashin ji kamar yaya?"

Ta kalleshi ta ce "Kamar yadda ka yi mana, sara suka, ƙulla wiwi black market duk da ka yi"

Haɗe rai yayi ya ce "Amma ba prison zan koma ba ko?"

"Idan ta kama ai dole ka koma"

Ya ce "What? Gaskiya ki yi yadda zaki yi, ba zan koma prison ba, wanda nayi 5yrs fa?"

Ta zumɓura baki ta ce "Ni na ɗaureka, sai abun da ya kama kawai, bari na je gidan, na ji wadda zamu yi da su, sai anjima"

*****

Nabila ta tafi ɗakin Abba, domin amsa kiran da yayi mata, ta tafi bakinta ɗauke da addu'a, ta shiga ɗakin da sallama, suka amsa ban da Abba da yayi shiru ransa a ɓace.

Ta je ta durƙusa ta ce "Abba gani"

"Nabila ban isa na gaya miki magana ki ji ba ko?" Tayi shiru ta sunkuyar da kai.

"Dole sai kin nuna wa duniya cewa ban haife ki ba ko Nabila? Kin nuna mini iyakata, ban isa na nemi alfarmarki ba kenan ko Nabila? Sai kin tozarta ahalin nan gaba ɗaya ko Nabila?"

Ta girgiza kai ta ce "Abba bani da wannan burin, kuma wallahi ba zan taɓa aikata wani abu da zan janyo maka zagi ba. Amma dan Allah Abba a yanzu, ka yi mini wani taimako, saboda zatin Allah kar abun da zan nema ya ɓata maka rai"

Ta miƙa wa Abba hotunan, da Viper ya bata, ta ce "Dan Allah Abba wacece wannan? Ni dai na san ba ni ba ce ba, dan Allah Abba ko kana da masaniya a kan ta jikin hoton nan.

Abba ya saka hannu, ya karɓi hotunan yana dubawa.

Ya gama ƙarewa hotunan kallo, ya ce "A ina ki ka samu hotunan nan?"

Ayshercool 08081012143

75 🔞₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne.

90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

https://whatsapp.com/channel/0029Va9QtrY4dTnBYG1hST2VHADARIN

*BRIGHT PENS SECOND BATCH*

Ku kasance da littatafan bright pens, second batch. *ƘARFE A WUTA (AYSHERCOOL)* *MUTALLAB (NIMCYLUV)* HADARIN GABAS (NAZEEFA NASHE)* *ZAYTOON (ZEE KUMURYA)*

Ta ɗan yi shiru sannan ta ce "A office ɗina na gansu"

A take Abba ya fara yayyaga hotunan, cikin kuka ta ce "A'a Abba, dan girman Allah ka gaya mini idan ka san ta jikin hoton, Abba ba ka ga yadda kamaninmu suka ɓaci ba, dan Allah Abba ko sau ɗaya ka nuna mini wani a dangin mahaifina dan Allah Abba" ƙarasa yayyaga hotunan yayi, ya watsa mata cikin matsanancin ɓacin rai ya ce "Ki koma in da aka baki hotunan, su gaya miki koma wacece, ubanki kuma ga hanya nan, ki bar mini gida ki tafi yawon nemansa, yayi miki abun da ban yi miki ba, tashi ki bar gabana kan na tattaka ki, da uban naki ya damu da ke, da zuwa yanzu shi ya nemi in da ki ke".

Anty ta ce "Haba major, dan Allah ka yi haƙuri kar ka yanke wannan tsatstsauran hukuncin a kan ta, kayi haƙuri dan Allah " gaba ɗaya jikin Nasir yayi sanyi, ganin yadda take ta uban kuka.

Cikin tsawa Abba ya ce "Ki tashi daga gabana, ki tafi ki bar mini gida, ki je ki nemi ubanki, amma ki bar mini gida kar na sake ganinki a gidana"

Wata irin ajiyar zuciya ta din ga yi, ta yinƙura ta tashi da kyar, ta bar ɗakin, ta koma ɗakinta ta kifa a kan gadonta, ta fara sabon kuka, shi kuwa Abba wace irin zuciya ce da shi haka? Ko menene a tsakanin sa da mahaifinta, yakamata ace ya wuce, ta san ya gama yi mata komai a rayuwa, yayi playing role ɗin uwa, yayi na uba a rayuwarta, amma duk da haka gurbin ido ba ido bane ba.

Baba magajiya ce tayi sallama, ta ƙarasa kan gadon, ta dafa kafaɗarta ta ce "Haba Arfa, ke a rayuwarki ba zaki iya haƙuri da tawakalli ba, tun da ya nuna miki baya son zancen nan ba sai ki haƙura ba, shekara nawa ana abu ɗaya kin ƙi ki gane ki haƙura".

Nabila ta tashi zaune, idanunta sun yi jawur ta ce "Baba magajiya"

"Na'am arfa"

"Kema laifina ki ke gani?"

Baba magajiya ta yi shiru tana kallonta.

"Ki bani amsa mana, laifi nayi dan na nemi sanin in da mahaifina yake na ganshi ko sau ɗaya? Baba magajiya mahaifi fa, a duniya na san Abba ko baki yayi mini, sai ya kamani, bana nufin yi masa butulci ko tozarta shi, amma ina son sanin babana, baba magajiya dan Allah ina da wata yar uwa ne? Ke kin san komai, hoto aka bani da wata a jiki irina ɗaya da ita sak, ko yar uwata ce, dan Allah ki gaya mini. Ni idan kin san in da zan ga babana ki gaya mini, ko sau ɗaya na je na ganshi na dawo dan Allah"

Baba magajiya ta girgiza kai ta ce "Ni ban san komai ba, lokacin da na zo gidan nan, an gama dambarwar da za ayi, na zo, ni bani da wani labari a kan mahaifinki"

Nabila tayi murmushi mai ciwo, hawaye na bin fuskarta ta ce "Haryanzu kallon yarinyar da ki ka raina ki ke yi mini ko, shiyasa ki ke tunanin bani da wayo ko? Shekaru ashirin da biyar a doron duniya, ai na girmi ki yi mini wayo baba magajiya, amma shikenan, ai Abban ya ce na je ne nemi babana, zan neme shi kuwa in sha Allah "

Baba magajiya ta waro ido ta ce "Baki san gatse ba Arfa?"

Nabila ta jinjina mata kai alamar eh, ta mayar da kai ta kwanta.

Baba magajiya ta ce "Arfa na san har da damuwar matsi da takura da ake yi miki a gidan nan, ya sanya ki ke damuwa da son ganin mahaifinki, ni dai roƙona da ke, ki yi haƙuri idan da rabo zaki haɗu da mahaifinki ko danginsa, amma dan Allah dan Annabi, kar ki bari ku samu saɓani da maitama"

Nabila ta yi mata shiru, dan gani take yi babu wanda zai fuskanci halin da take ciki.

Tamkar zuciyarta Abba ya yaga, haka take jin zuciyarta, idan ta tuna yadda ya yayyaga hotunan nan, sai dai har a lokacin tana ganin hotunan yarinyar mai kama da ita a cikin idanunta.

**** Duk da Nabila bata jin daɗin komai na duniyar, jin ta kawai take yi gata nan dai, haka ta cigaba da up and down a kan muhimman abubuwan da ta saka a gaba.

Ta sake shigar da koke gaban hukumar'yan sanda, ta nemi su kama madaki da wasu daga cikin yaransa, bisa zargin kisan matar Viper, shekaru shida da suka gabata.

Yau tana da program a gidan radio, kuma yanayinta ya nuna wa Sumayya tana cikin matsananciyar damuwa, sai dai ta shigo a ƙurarren lokaci, zasu fara gabatar da shirin, dan haka ba ta samu damar yi mata tambayar meyake damunta ba.

Nabila tayi iya ƙoƙarin ta, wurin ajiye damuwa a gefe, suka fara gabatar da program.

Sumayya ta kalli takardar hannunta sannan ta ce "Jita-jita ta cika gari, cewa kin shigar da koke gaban kotu, a kan lallai kotu ta hana hukumar'yan sanda kamar shahararren ɗan ta'addan, da addabi wani yanki na garin nan, kuma akw zargi da kisan matarsa, duk da yadda hukumar ta 'yan sanda, take nemansa ruwa a jallo?"

Nabila ta kalli sumayya da rinannun idanunta, tayi mamakin yadda sumayya tayi mata wannan tambayar, a tsakiyar program ɗin su haka, saboda ba magana ce da ta fita ba, balle ta ce an yi Jita-jita a kai. Sumayya ma ta tsare ta da ido, alamar tana jiran amsa.

Tayi wani irin murmushi ta ce "Ba ɗan ta'adda bane ba, mutum ne kamar kowa, kuma ɗan ƙasa da ya dace ya samu duk wani 'yanci da kowane ɗan ƙasa ya dace ya samu. 'yan ta'adda na yawonsu a gari, an san in da suke, an san in da za a same su, hakkinsa muke nema a kotu, ba shi ya kashe matarsa ba. Na san mutane za su yi mamakin yaya aka yi mai dokar bacci ya ɓuge da gyangyaɗi, amma a bibiye ni a cikin shari'ar da zamu gudanar".

"Amma ba kya ganin hakan kamar taka doka ne, zaki yi amfani da damarki ta lauya ki taka doka, ki kare mai laifi?"

"Sam, dokar da aka wulaƙanta, da ita nake son yin amfani wurin gyara kuskuren da aka yi. Tayaya mutum zai shafe shekaru babu Shari'a, daga baya alƙali da saka hannunsa da umarninsa da komai, a sake shi bisa doron doka da ƙa'ida, kuma daga baya a zo ana nemansa. Shin wanke shi aka yi daga laifin? Ko kuma akwai wani ɗaurin ɓoye da yakamata a warware? " Tayi maganar tana ƙure sumayya da ido.

Sumayya ta kalli agogo, lokaci ya cika, ta na tsaka da sallama da masu saurare, Nabila ta tashi ta fice, tana kammalawa, ta tashi ta bi Nabila, amma tuni ta ja motarta ta bar wurin.

Ta koma tana sauke numfashi, kiran kankarofi ta gani, ta ɗaga wayar suka gaisa, ya ce "T ladan, meyasa ki ka yi wa Nabila wannan tambayar a tsakiyar program?"

"Sir nayi ne, dan tun yanzu ta kare kanta a wurin mutane, kafin abu ya bayyana su yi mata kallon, maciya amana mai fuska biyu "

"Sumayya waye ya gaya miki ana iya wa ɗan adam ne? Ba a taɓa iya wa mutum, dan haka ki kiyaye gaba, yayi wuri ki fallasa abun haka gaba ɗaya, amma babu laifi, baki yi kaifi ba, hakan zai ƙara mata ƙaimi"

Sumayya ta ce "Ok sir, na gode" ta ajiye wayar ta yi shiru, ita a zahiri tayi hakan ne, ko Allah zai sanya Nabila ta ji nauyin dubban al'ummar da suke goyon bayanta, ta sassauta koma ta haƙura da batun Vipern nan, amma ba ta ga alamar hakan a tattare da ita ba.

Abbu kuwa a zabure ya miƙe tsaye, jin program ɗin da yayi, shi ba wani ma'abocin jin radio bane ba, yau kawai ya kunna yana saurare, ya ji shirin ya ƙayatar da shi, haka zalika muryar barrister, kamar sananniya ce a gare shi. Sai dai jin sun yi maganar Viper, ya sanya ya tashi a kiɗime, tare da ɗaukar radion ya fito tsakar gida.

Rahila ta ce "Ya dai na ganka a firgice haka?"

"Wani shiri na gama saurara, wata lauya ta shigar da koken kotu ta hana kama Aminu, ko gidan radiyon zan je, wataƙila su sun san in da yake"

Ta kwaɓe baki ta ce "Ina rabaka da sabgar yaron nan, idan sun san in da yake me zaka yi masa? Salon ka sanya kanka a masifa, wanda ake nema ruwa a jallo da laifin kisan kai? Ka ganshi ka yi masa me? Guduwa fa yayi daga gidan yari"

Ya ƙura mata ido, kawai ya girgiza kai, ya kashe radion ya fice.

****

Nabila tana driving, wani abu ya tsaye mata a maƙogwaronta, kukan ma gaba ɗaya ta kasa saboda baƙin ciki da ɓacin rai.

Katafaren gate ɗin aka buɗe mata, ta shiga da motarta, tayi parking, ta sauka ta nufi cikin gidan.

A falo ta tarar da mahaifiyar ramma, tana ganin Nabila, ta tashi da fara'arta, tana yi mata sannu da zuwa.

Nabila ta zauna cikin yaƙe, suka gaisa, kamar kullum yau ma mahaifiyar ramma, kallon Nabila take yi, kamar ta haɗiyeta, ita dai ban da an yi mata gargaɗi, da tuni ta faɗi abun da yake ranta, dan ta tantance abun da take tunani, sai dai an gargaɗeta a kan aikata hakan, dan haka ta ja bakinta ta tsuke.

"Mama ina fatan dai babu wata matsala ko? Ki cigaba da haƙuri, in sha Allah an kusa dawo miki da ramma, kuma hujjoji nake son kammala tattarawa, na gano ainihin mai laifin, za a gabatar da shi a gaban kotu, idan da wani abu ki gaya mini"

Ta girgiza kai ta ce "Ba wani abu, ina ta godiya Ubangiji Allah ya baki nasara, na gode sosai da sosai da ke da Alhajin da ya taimake ni, ina godiya Allah ya biya ku, ya ƙara miki zaman lafiya da mijinki"

Nabila ta ce "Ai ba mijina bane mama"

"A'a ba Alhajin ba, Aminu"

Cikin mamaki Nabila ta ce "Aminu kuma? Nifa ban taɓa aure ba, ba ni da aure" tayi maganar tana murmushi.

Babar ramma ta ɓoye mamakinta, kar kwaɓarta tayi ruwa ta ce "Au, ai na zata kina da aure ne, Allah ya kawo miki nagari, ya baki mai sonki da gaskiya, Allah ya tsaya miki, kamar yadda ki ke ta ƙoƙari a kanmu"

Nabila ta ce "Amin mama, dan Allah a cigaba da yi mana addu'a, addu'aeku, ita ce ke tasiri a rayuwarmu"

Maman ramma ta ce "In sha Allah, addu'a yanzu aka fara"

Nabila ta ce "Na gode sosai" ta tashi ta nufi hanyar fita, babar ramma ta bi ta da ido, dan ranar farko da ta fara ganin Nabila, ban da an gaya mata kafin ta zo, an yi mata bayani, da babu abun da zai hanata kurma ihu, ta ce taga gawa.

Tana driving sannu a hankali, ta tsaya ta sai abun da zata ci a gida, dan ba sabgar su take shiga ba.

A harabar gidan, ta wuce Nasir, ya zuba mata ido, duk ta bi ta rame, saboda ta saka jaraba a ranta, ko kallonsa ba ta yi ba ta wuce. Duk sai ya damu da ramar da ya ga tayi, amma yana nan a kan bakansa sai ya kama Viper, ko zata mutu dan haushi.

"Ga agolancin ga yawon ta zubar, ga ta'addanci, gashi an gandame an riƙa a gida babu aure, abun bai yi miki yawa ba kuwa Nabila" Sauda tayi maganar tana dariya.

Ta sake cewa " An baki damar ki gusa ki bamu wuri, saboda baƙin naci, kin liƙe mana a gida, tun da ba zaki tafi ba, ki iya kanki, muna son ubanmu, ba zaki kashe mana da baƙin cikin ki a banza ba"

Nabila ta tsaya cak, tare da murnar Sauda ta takale ta, ko banza ta rage zafi idan ta yaɓa mata magana.

"Ke da ki ke son uban naki, sai gashi kin gagara zaman aure, kin ƙi karatu balle hankalinsa ya kwanta. Ai sauda zaki yi mini gorin aure ne, a lokacin da ke ki ka iya zama a gidan naki mijin. Kuma karki manta da ni agola ce mai 'yanci, a dalilina igiya biyu aka sauke wa babarki ta aure, idan ku ka cigaba da matsa mini, ragowar ɗayan ma sai na tsinketa, sai ku ji daɗin zawarci tare ga uwa ga 'ya. Yawon ta zubar kuma, ina da abun bayar wa yayi mini rana, kema idan ki na so ki bayar nonsense"

Sauda ta tashi a ƙufule, Nabila ta ce "Kin san dai ba dakuwa zan yi ba, dama koma wa ki ka yi ki ka zauna"

Sauran wanda suke wurin, suka tuntsure da dariya, dan yadda Sauda ke zuba mulki da rashin mutunci a gidan nan, Nabila ce kawai maganinta.

**** Cikin mamaki Abdul ya ɗago ya kalli indabo, saboda marin da ya kwaɗa masa.

"Ina na kai mini kuɗi Abdul?"

Abdul ya yi shiru yaƙi magana.

"Ka gaya mini in da ka kai mini kuɗi, kafin na tattaka ka a wurin nan? Yarinya da ka fito da ita, da kar ka fito da ita, matsalarka ce, ba zaka kashe ni da ɓacin rai ba, sai na samo wani wanda ba zai watsa mini ƙasa a ido ba, ina ka kai mini kuɗi?"

Mahaifiyar Abdul ta ce "Abdul wai ba magana ake yi maka ba? Ina kuɗin da ya zuba a account ɗin ka, da sunan campaign kuma ya muka yi da kai a kan yarinyar nan?"

Abdul ya numfasa ya ce "Na yi wa 'yan garin su rahama gyaran makarantu da hanyoyi, na yi musu boreholes, sai kuma registration da nayi mata na karatu bar zuwa jami'a" ya faɗa kai tsaye.

Salallami suka hau yi, da tafa hannu.

Indabo ya ce "Abdul, kuɗin ka kwasa ka ƙarar a kan garin yar matsiyata da karuwa?"

Ya girgiza kai ya ce "Daddy ba karuwa ba ce ba, koma menene ni ne mai laifi, fyaɗe nayi mata, nayi hakan ne, dan na goge laifina"

A fusace Indabo ya rufe shi da duka, ga ƙiba ga hawan jini yana fama, a take ya hau haki, da kyar P.A ya janye shi daga jikinsa.

"Ƙarya ma kake yi, ka fito mini da kuɗina, sai na yi seazing ɗin asibitocinka, da duk wata kadara daka mallaka, da wadda na mallaka maka, ni zaka tonawa asiri, wallahi baka isa ba, kuma zan saka a nemo mini yarinyar ko ina ka kai ta, zan yi maganinka daga kai har ita".

"Dan Allah daddy kar ka cutar mini da ita, ba tayi laifin komai ba, ni zaka hukunta"

Ashariya ya din ga zabgawa Abdul, yama rasa me zai yi, kuɗin da suka yi sama da faɗi da su, domin campaign bisa ga yarjejeniyar idan an yi nasara zasu mayar da kuɗin da uwar riba, ga balli na neman tashi, dama kuɗin mutane ne na wasu hukumomi a ƙasa, ga balli na neman tashi, kuma Abdul ya yi masa hauka.

P. A ya ce "Kayi haƙuri, kar ka je wani abun ya sameka, ka rabu da shi, zamu san abun yi, mu fara kashe case ɗin can na gaban kotu tukuna".

"Na fara tunanin anya Abdul ɗa na ne? Ƙiriƙiri ya zaɓi mace a kaina, ni zai tozarta?"

P.A ya ce "Jarabta ce da kuma ƙuruciya ke damunsa"

"A shekara talatin da shidan ne ƙuruciya?" P.A ya din ga bashi haƙuri yana lalaɓa shi, Abdul kuwa tunu yayi ficewarsa.

*****

Madaki na zaune a cikin ɗaki, ya din ga jin hayaniya, da iface-iface ana sara suka a ƙofar gidan da yake.

Wani daga yaran sa ya shigo da kyar, ya ce "Madaki, yan ƙofa ne fa suka zo gidan nan, muna ta fama da su, sai ƙoƙari suke lallai sai sun shigo gidan nan, su sareka"

Madaki ya tashi ya ƙwalalo ido, sai dai kan yayi magana, sun faɗo gidan, sun kai su bakwai, suka zo ka hau shi da sara da suka, wasu na waje na faɗa da yaran madaki.

Duk da akwai ƙarfin zuciya, yana ta ƙoƙarin kare kansa, amma sai yaji jikinsa kamar an canza masa wani, duk yayi wani iri babu ƙwari, suka din ga saransa, ƙarshe suka janyo shi daga cikin gidan, suka din ga jan sa a ƙasa tamkar abun banza, duk da iya ƙoƙarin da yaransa suka yi, su ƙwace shi, amma abu ya ci tura, tsofaffin yaran Viper, da yan unguwar su, da ya din ga shiga yana addabawa ya hana su sukuni, su suka yi gangankon ɗaukko shi, suka yi masa laga-laga, suka din ga yawo da shi, lungu da saƙo, daga ƙarshe da ƙyar jami'an tsaro suka kawo masa ɗauki, suka tarwatsa matasan, suka ɗauke shi a galabaice, dan ba su zaci yana raye ba, suka kai shi Asibiti.

***** "My Abdul" ta yi maganar tana murmushi, cikin hanzari ya ɗago, dan bai zaci daga bakin ramma maganar ta fito ba.

"Meyafaru ne? Gaba ɗaya na ganka a cikin tashin hankali?"

"Rahama abubuwa sun ƙara cakuɗe mini, barin ƙasar nan zamu yi"

Cikin mamaki ta ce "Mu bar ƙasar nan, mu je ina?"

"Rahama abubuwa ba zasu tafi yadda na tsara ba, zamu bar Nigeria"

"Ban gane ba, uwata fa?"

Abdul ya ce "Zan saka a kawo miki ita, yanzu visa za ayi miki, amma sai na fara barin garin nan da ke"

"Abdul, ni fa gani nake wannan guje-gujen, duk ba zasu kaimu ba, kayi haƙuri ka yi abun da mahaifinka ya buƙata mana"

Ya kalleta ya ce "Na kai ki kotu ki gaya wa duniya, ni ne nayi miki fyaɗe? Ba wannan ne ya dame ni ba, abun da zai biyo bayan shaidar da zaki bayar shi ne abun jin, dan haka ki nutsu kiyi abun da na ce kawai"

Murmushi ta yi masa da ita kaɗai ta san ma'anarsa, ta wuce shi ta tafi kitchen.

**** Daga Naja'atu har Indabo fuskokinsu ɗauke da damuwa, Bunkure tayi ƙwafa ta ce "Gaba ɗaya hankalina a tashe yake, lallai gaskiyar hausawa, ɗan hakin da ka raina, shi ne yake tsole maka ido, yarinyar nan dai ta dage sai ta ga bayana, idan asirina ya tonu, ban san wane irin kallo zan yi wa al'umma ba. Abdul duk shi ya janyo wannan abun.

P.A ya ce "Duk ku kwantar da hankalinku, babu wani abu da zai faru, kamar yadda ka yi umarni, dattijon nan zai shiga silent, yanzu uwar yarinyar ta rage, ita muke binciken in da take, kuma ita ma zamu ganota in sha Allah, Abdul ma muna daf da gano, wurin da ya ɓoye yarinyar nan"

Indabo ya girgiza kai ya ce "Ban san in da Abdul ya koyi wannan baƙin taurin kan ba, magana ta fito fili, an ce a binciki ministocin da muka ƙulla harƙallar kuɗaɗen nan da su, na san kuma dole sai sunana ya fito, wai ya kwashe kuɗin nan, ya yi wa yan ƙauye ayyukan raya ƙasa, na rasa uban abun da ya samu a jikin yarinyar talaka mara galihu, ya nace mata take abun da ta ga dama har haka"

Bunkure ta sauke numfashi ta ce "P.A ya batun barrister Nabila?"

"Kamar yadda na gaya muku, sponsiring ɗin ta ake yi, na gwada sakawa a kamo mini ita, amma hakan ya gagara akwai jami'an da suke bin ta, wanda ba san suwaye ba, kuma da alama ita kanta ba ta san suna bin ta ba"

Indabo ya ce "Kar ku ja da nisa, kankarofi ne, babbar buƙatar sa ya ga ya kai ni ƙasa, ya rama abun da nayi masa, kuma yayi kaɗan".

***** Nabila na zaune a ɗakinta, tunanin ma ta rasa wanne yakamata ta yi, kawai ta ga Nasir ya shigo ɗakin, ba ta ko motsa ba, balle ya sanya ran za ta kula shi.

"Nabila"

Ta ɗaga ido ta kalleshi. "Da gaske ke ki ka nemi a hana kama Aminu Viper"

"Eh" ta faɗa a nutse.

"Nawa aikin ki ke burin ɓatawa kenan, me nayi miki haka ne?"

Ta kalleshi ta ce "Ba kai nake fatan ɓatawa aiki ba, duk wani mara gaskiya sai na ɓata masa aiki. Gaba ɗaya ka canza i miss my old DSP, the only person that understand me" tayi maganar tana tashi ta bar shi a ɗakin.

Tana office ɗin ta, tana son zuwa duba jikin malam garba, tana son zuwa wurin 'yan sanda, tana son ganin Viper, ga kuma maganar Abba da ta tsaye mata, da ya ce taje ta nemi ubanta, ta bar masa gida. Kenan Abba ya goyi bayan ɗan sa, shi ma a wannan karon ya nuna mata, gurbin ido ba ido bane ba.

Turo ƙofar office ɗin aka yi, ta tashi zaune sosai daga kashingiɗar da tayi, tana tunanin ina ta taɓa ganin baƙon nata.

Ya samu wuri ya zauna, suka gaisa, ya ce "Baki gane ni ba ko?"

Ta jinjina kai ta ce "Gaskiya dai"

"Haka ne, magana na zo mu yi da ke mai muhimmanci"

Nabila ta ce "Ok, ina jinka"

"Saƙo ne daga wurin distinguish Ma'aruf Indabo, na zo mu yi magana mu fuskanci juna da ke"

Nabila ta yamutsa fuska tana kallonsa.

"Muna yi miki tayin ki fanshi kanki da kanki ne, kan abun da ba a so ya afku"

"Ɗan yi sauri, ina da wurin zuwa"

P.A ya ce "Maganar da na zo da ita, ta fi abun da zaki je yi muhimmanci, muna son ki janye shari'ar nan ta batun fyaɗe nan, case ne tsakanin ki da Bunkure, kuma ko yanzu kin cika burinki a kanta, akwai maƙudan kuɗaɗe muddin ki ka aikata abun da na ce"

Nabila ta ce "Malam na yi maka kama da shashasha ne? Da Bunkure nake case ɗina, meye nasa a ciki? Bibiyar rayuwata da ya saka aka din ga yi, da ƙoƙarin kashe ni, duk bai ishe ku ba, shi ne zaka zo mini da maganar bunkure? Wallahi idan kaga na bar case ɗin nan, to an hukunta ainihin mai laifin ne, kuma muddin wani abu ya same ni, kai ko mutuwa nayi, ina da manya manyan hujjoji a kan sa, da suke a hannun wakilai ne, akwai wanda za su ɗora, in sha Allah sai na bayar da misali a Nigeria, an fara hukunta masu riƙe da madafun iko, da iyalansu, ba wai doka a kan talaka kawai ba, everyone is equal before the law"

"Haka ki ka ce?"

"Hala kurma ne kai?"

Ya ce "To bari mu gani, yaro bai san wuta ba sai ya taka"

"Na santa farin sani, tun da na ɗaukko ƘARFEN CIKIN WUTA, da ya gagari hannaye da yawa"

P.A ya kalleta ya ce "Me ki ke nufi?"

"Zaka fahimta nan ba da jimawa ba"

Yana fita tayi tsaki, ta ɗauki jakarta ta fita, a nan ta bar motarta, ta hau abun hawa ta tafi gidan Viper.

Yana tsakar gida, daga shi sai ɗan mama a gidan, suna hira.

Sun daɗe suna kallon juna, sannan ta ƙarasa ciki, ta samu wuri ta zauna ba tare da ta ce masa uffan ba.

Ya samu abu ya zauna, ya ce "Ya ake ciki, meye labari?"

"Ko ka neme ni, kwana biyu ina cikin damuwa da tashin hankali, amma ko a jikinka"

Ya tsuke fuska ya ce "Menene?"

"Vi"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull