Kenza eBookz

Karfe a wuta book 2 complete novel - Chapter 84

Karfe a wuta book 2 complete novel - Chapter 84

Karfe a wuta book 2 complete novel Chapter 84: Karfe a wuta book 2 complete novel Chapter 84. Cikin mamaki baba ya ce "Kamar yaya?"

4,480 words

Cikin mamaki baba ya ce "Kamar yaya?"

"Tana da wata 'yar uwa ne, da suke ciki ɗaya?"

"A'a itakaɗai ce"

Ya jinjina kai ya ce "Akwai lauyata, da muka zo tare, zaku tattauna da ita, wadda ita ce tambayata da nake son ka amsa mini" ya tashi tsaye, ya nufi hanyar fita.

***

"Kankarofi, zuwa yanzu ina fatan hankalinka ya kwanta baka da wata damuwa ko?"

Ya kalli indabo ya ce "Ba ni da ita Indabo, kawo ƙarshenka, babbar nasara ce, da rage mugun iri a ƙasa ko ma na ce duniya baki ɗaya"

"A'a, bari murna karenka ya kama zaki, da saura tukuna baka kawo ƙarshena ba, kuma kawo ƙarshena tamkar kashe maciji ne, baka sare kansa ba"

Kankarofi ya ce "Ko ban sare kansa ba, ya tashi, na rage masa karsashi da ƙarfin mugunta da zalunci. Kuma in sha Allah wannan kujerar da ka cimmata, ta hanyar zubar da jinin mutane bisa zalunci, da amfani da rayuwar talaka ka cimmata, ka wofantar da su ka tagayyara rayuwar su, sai ka barota, sai ka kuma fuskanci hukunci. Yanzu haka ana shirin tsayar da kadarorinka, a kai gaban shari'a bisa laifin sata wato cin amanar ƙasa, bayan babban tattalin arzikinka da aka kama, na miyagun ƙwayoyi a Italiya. Ka san Waye yayi maka aikin kama ɗanka da kama maka dukiya? Viper! Abin ya baka mamaki ko? Wani banbarakwai, da yake ce maka ya saka an kama ɗan sa ka daɗe kana mamaki, da ganin ƙarya yake yi. Dodo babban sarki ya fi ka lissafi, da shu'umanci indabo, sirrinka da ya sani, ya san zaka kashe shi, ba za ku bar shi da rai ba, da shi da tawagarsa, shiyasa ya ƙara jan Viper, ya sanar masa da duk wani abu da yakamata ya sanar masa. Duk tsawon lokacin da Viper ya shafe tare da kai... Yayi shiru yana kallon Indabo.

"Spy ne, hatta yadda ka ke samun return da kai da tawagarka, a kan tashe-tashen hankulan da ake yi a ƙasar nan, yadda ku ke safarar makamai ta ɓarauniyar hanya cikin ƙasar nan, Viper ya sani, dodo ya gaya masa, aikin contract rundunar tsaro ta bashi a kanka, kasancewar waccan gwamnati duk gayyar tsiya ce irinka, ya sanya ba su iya yi muku komai ba. Sannan Viper bai shafe shekaru biyar a gidan yari ba, yana can yana karɓar horo na musamman a kan zama cikakken jami'in leƙen asiri. Idan ku kuna amfani da doka, wurin tozarta ƙasa yadda ku ka ga dama, mu ma muna iya amfani da ƙarfinmu ta ɓarauniyar hanya mu yi wa ƙasa aiki. Ina fatan yanzu ka fahimci BODMAS ɗin da Viper ya gaya maka. Kar fa ka zarge shi, sam shi ma wasu abubuwan bai san da su ba, tsuntsu biyu na jefa da dutse ɗaya.

Sosai ƙafafuwan Indabo suka fara karkarwa, saboda mamaki da tashin hankali.

"Ka hanzarta, ka je ceil ka duba ɗanka, kar wahala ta kashe shi, dan ya saba da hutun da aka samar masa ta hanyar zubar da jinin dubban matasa, a kan harkar daba bayan ka basu miyagun ƙwayoyi, ka gina ɗanka, gashi dai ka bashi ilimin, yana amfanar mutane, gefe guda kuma ya gado duk miyagun halayenka, kuma a haka ka ke ƙoƙarin ɗora shi a kujerar mataimakin gwamna, shi gwamna kai senator, ku cigaba da azabtar da mutane, tun da shi mulkin gadon gidanku ne, you are not serious, Allah yana son bayinsa. Kuma ina tayaka murna, saura wata guda kacal ayi recall election, mutanen yankinka za su yi maka kiranye, abin da ba a taɓa yi a tarihin ƙasar nan ba, sai a kanka" ya ɗauki glass cup ɗin ya bar falon.

*** Mamaki ne ya kama Nabila, ganin idon Viper yayi jawur, gidan da ya shiga bai yi kama da na mutanen banza ba, balle ta ce ko shaye-shaye ya shiga yi, hakan ya tabbatar mata da kuka yayi.

Ya kama hannunta, ya ja ta zuwa cikin gidan, kasa yi masa magana ta yi, ta cigaba da bin sa.

Tijjani da saifu da suke tsakar gida, darewa suka yi, suka ja da baya suna zazzaro ido, ganin wadda Viper ya shigo da ita.

Zakiyya kuwa iya ƙarfinta ta saka uban ihu, ta zura da gudu ɗaki, tana dambe da ƙofa taƙi rufuwa, saboda razani da tsoro.

Nabila tsaywa tayi tana kallon dattijon, wanda shi ma ya ƙame wuri guda yana kallonta, tun daga sama har ƙasa.

Ta baya Nabila ta ji an yi mata wata irin runguma da ƙarfi.

Hafsa ce, ta ce "Jauhar, sai da na gaya musu na ganki rannan a asibiti, da na je ganin doctor Abdul yasar, amma suka ce bani da hankali"

Jiki a matuƙar sanyaye, Nabila ta rungumeta ita ma, duk da ba ta san wacece ba.

Hafsa cikin kuka ta ce "Kin haihu? Ina jaririn naki yake? Mastern ne ya kai ki asibiti? Kin ga aurena ya mutu ko? Na sha wahala a gidan Alhaji mu'azzam".

Nabila ta ɗaga kai ta kalli Viper, ta mayar da idonta kan dattijon, amma ta kasa magana, sai lumshe idanunta take yi, tana rufewa tana fatan jin amsar tumulin tambayoyin da ke bakinta, ba tare da ta iya furta ko tambaya ɗaya ba, dan ji take yi, tamkar an kanannaɗe mata harshenta.

A tare Major da Nasir suka fito daga mota, cikin ikon Allah suna fitowa, suka yi arba da liti da walid a tsaye a jikin motar da suka zo.

Nasir ya ce "Yauwwa Abba gasu nan, ina Viper yake, ina ku ka kai Nabila?"

Liti ya ce "Ba a sani ba, kai a wa zaka zo kana yi mana tsawa?"

Ya kalli liti ya ce "Ni ka ke gaya wa haka?"

"An gaya maka ɗin"

Major ya ture Nasir ya ce "Ina 'ya ta take, waye shi yaron a cikin su?"

Nasir ya ce "Abokansa ne"

"Shi yana ina? Meya kawo mini 'ya nan yayi mata?" Major ya yi maganar a matuƙar hasale.

Walid ya ce "Suna cikin gidan can" yayi maganar yana nuna musu gidan da Viper ya shiga da Nabila.

Major ya tunkari gidan, liti ya ce "Wallahi bin su zan yi, kar wannan mai kunnuwan ya je yayi musu wani abu"

Viper ya ce "Baba wannan ita ce tambayar da na zo maka da ita, nake neman amsarta"

A hankali baba ya fara takowa, yana maimaita "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, subhanallah wa bi hamdihi, adada khaliƙihi, wa rida nafsihi, wa zinatu arshih" yana miƙa hannun sa, yana ƙoƙarin taɓa Nabila.

Da ƙarfin tsiya, Nabila ta ji an ja ta baya, har ta na ƙoƙarin faɗuwa ƙasa, major ya nuna Baba da ɗan yatsansa ya ce "Kar ka kuskura, baka da wannan ikon, babu wanda ya baka wannan damar, tsohon macuci ma ci amana"

A hankali baba ya ce "Yusuf maitama"

Major ya ce "Bashir lamiɗo" suka kalli juna.

Baba ya ce "Bai kamata haɗuwarmu ta kansace a haka ba"

"Babu wani abin kirki da yakamata a tsammata daga azzalumin mutum, mara imani da tausayi irinka, haɗuwar da ta fi wannan muni ita yakamata muyi. Ke kuma wuce mu tafi, da kin san wanenen wannan tsohon najadun da abin da ya aikata wa babarki, da baki yi marmarin ganinsa a rayuwarki ba, wuce mu tafi kafin nayi ƙasa-ƙasa da ke. Kuma da na san kana garin kano, da da nayi retire ban zo kano na zauna ba"

Baba ya sha gabansu ya ce "Maitama, babu in da zaka je sai ka gaya mini ita kuma wannan wacece, duk da ko baka faɗa ba, na san 'ya ta ce, amma nauyin laifin da nayi maka bai kai zunubin da aikata mini ba, wacece wannan?"

Major ya ce "'ya ta ce ta halak, wadda ba ta da uba, ba ta da wani gata sai na Allah sai nawa, ni ne uwa kuma ki ni ne ubanta, babu uba a tarihin rayuwar ta, na cireka a rayuwarta gaba ɗaya, dan haka kar ka sake saka wa zuciyarka wannan 'yar ka ce".

"Amma maitama ka san zan iya shari'a da kai a kan abin da ka aikata mini. Ka san me ka ce mini shekara ashirin da shida da suka wuce"

A fusace Major ya ce "Ka daɗe baka yi ba, ni yakamata na yi shari'a da kai, shekaru ashirin da shida baya, bisa cin amana da kisan kai, zan iya cewa kai ka kashe 'yar uwata, dan haka ba abin da zaka tsinana wa rayuwar Nabila, wanda ban yi mata ba"

Ƙara Nabila ta saki, ta silale ƙasa, nufarta suka yi gaba ɗaya, Nasir ya durƙusa zai kai hannu kan Nabila, amma Viper ya hankaɗe shi gefe, ya ɗagota.

Galala ya buɗe baki, ganin yadda ya kusa kai wa ƙasa saboda hankaɗewar da Viper ya yi masa.

Baba ma kan Nabila yayi, amma major ya durƙusa, zai karɓi Nabila daga hannun Viper.

Nabila kuwa kanta ne ya juye, wani irin jiri ya ɗebeta, ta faɗi ƙasa, wani irin kuka take yi daga cikin zuciyarta.

Viper ya riƙe ta gam, ya kalli major ya ce "Yallaɓai a ganina, kamata yayi ku yi wa Nabila bayanin wacece ita, meyake faruwa, bai kamata ta shiga cikin saɓanin da ku ka samu ba, abu ne da yake a tsakanin ku, da ya faru shekarun da suka gabata.

"Wanene kai?"

"Mijin ta jikin hoton da na bayar a kai maka".

"Mmm mijin wadda ka kashe" major yayi maganar yana kallon idanun Viper.

Su Saifu da suka fara leƙowa ɗaya bayan ɗaya cikin tsoro, saifu ya ce "Baba ka yi mana bayani meyake faruwa ne? Mu da kai mun san jauhar ta mutu, to wannan kuma wacece?"

*** Chubaɗo tun tana sanya ran dawowar Bashir, har ta fara sarewa, ta fara tunanin ko wani abin ne ya same shi, ba ta iya yi wa kanta komai sai da kyar, saboda nauyi da girman cikin da yake jikinta, abu kaɗan sai haki, gashi babu wanda ta sani a garin, ko ta san wani ma, babu yadda za a yi ta iya magana da su, ita ba yarensu take ji ba.

Cikin ta ya shiga wata na tara, ba ta iya cin komai sai dai ta wuni a kwance, salla ce kawai take tayar da ita.

Kwanan cikin bakwai da shiga watanni tara, ta fara jin alamun ciwon naƙuda, ga ƙuruciya, gashi ba ta san kan abin ba, dan haka ba ta gane meyake faruwa ba.

Ciwo ya ci gaba da ƙaruwa, tamkar zata bar duniya, sai da ta kwana biyu a haka, babu mataimaki sai Allah.

Cikin dare abu ya ta'azarra, ta rasa in da zata sanya ranta, tana jin yadda abu ya tokare ƙasan mararta, amma yaƙi fitowa, tayi kukan ma abu ya gagara ta tashi tsaye, ta durƙusa, ta kwanta kowanne ya gagara ta rasa abin da za ta yi ta ji daɗi.

Ta ji fitsari ya matseta, ta tafi banɗaki amma ya fara zuba a tsakar gida ashe faya ce ta fashe, ga ta ga banɗakin ta kasa shiga, ƙafafuwan ta suka sage a wurin, dolenta ta durƙusa a wurin, ta fara nishi.

Tana jin kan jariri ya fito, amma gangar ciki ta ƙi fitowa, ta yi iya yin ta abu ya gagara, ga numfashinta na ƙoƙarin ɗaukewa, kawai ta nemi wuri ta kwanta daga durƙushen da take, ta zubawa sarautar Allah ido.

Ayshercool 08081012143

86 🔞₦500 ne via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143 Wanda za su jira document 1K ne.

90009343 'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

*BRIGHT PENS SECOND BATCH*

Ku kasance da littatafan bright pens, second batch. *ƘARFE A WUTA (AYSHERCOOL)* *MUTALLAB (NIMCYLUV)* HADARIN GABAS (NAZEEFA NASHE)* *ZAYTOON (ZEE KUMURYA)*

🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾

*_GYARA SHINE MACE_*

*_ZATA FASHE FA KARKU BARI AYI BABUKU ZAFAFAN KAYAN MATA MASU KYAU DA INGANCI KUMA AKAN FARASHI MAI SAUK'I ,MAMAN YUSUF YAR MUTAN SOKOTO TA SHIRYA TSAF DOMIN GWANGWAJEKU DA ZAFAFAN KAYANTA MASU MATUKAR INGANCI_* 🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾🌻🌾

*_'Yar uwa shin ko kin San lokacin sanyi lokaci ne da yake dask'arar da ni'imar mace , yake yawan bushe gaban mace , sannan lokacin ne maza sukafi bukatar matansu , lokaci ne da kowane lafiyayyen namiji yakeson ya jishi ajikin matarshi a kowane lokaci , to ya kike gani idan har mijinki Yana son kasancewa Dake Haka kekuma ga ni'ima a bushe , 'yar uwa mace fa Saida gyara , ko kinada kyau to ki k'ara da wanka don ci gaba da kankanrowa kanki daraja da k'ima a idon Mai gida ,. Ki tuna duk son da namiji ke maki in har kinada matsala a wannan wajan to wlh akwai matsala don son da yake maki bazai Hana kurinka samun matsala dashi ba ,idan kuwa har Yana samun yadda yakeso wlh ko baya sonki to Ina tabbatar maki da a hankali wata Rana sai ya soki Kuma zakiga kowane lokaci Yana tattalinki da gudun abunda zai 'bata maki Rai , Mata a kula*_ maman yusuf likitar Mata 07069711327

*Wannan dalilin ne yasa nazo maku da Kaya masu zafi kamar Haka*👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

Akwai ingantaccen maganin sanyi Mai fatattakar sanyi cikin kankanin lokaci na maza Dana Mata , kun dai San illar da sanyi yake da ita ku kula,

Akwai ingantaccen maganin nono hadin gargajiya na Sha Dana shafawa Mai taso da nono ya Kuma gyarashi Hadi da tsayuwarshi ,😍

Sai maganin hips Wanda zaisa hips dinki ya ciko kema ki shiga jerin Mata masu aji😍

Akwai maganin k'iba Wanda zai ciko da jikinki kiyi kiba Yar daidai Mai kyau wadda zata dace da yanayin jikin ki💃

Ina bada Hadi na mussaman ga yarinyar da ta rasa budurcinta sanadiyar fyade ko yaudarar d'a namiji ,Wanda insha Allah akayi amfani dasu to yarinya zata koma normal Wanda duk zata aura Ba zai iya Gane komai , Mmn Yusuf likitar Mata💃😍

Akwai hadin amarya Wanda zaisa ki ciko ki hade gam sannan su Baki ni'ima irin wadda akeso ingantaccen sirrin da zaisa ki Kara samun soyayyar mijinki cikin sauki💃💃💃

Akwai hadin sabon budurci da mukeyi ga wadda ta kasance bazawara hadine da ko haihuwarki nawa akayi maki shi Zaki koma tamkar budurwa Wanda ko Wanda Kika aura zaisha mamakinki Wanda hakan Kuma wata hanya ce ta kankanrowa kanki daraja da k'ima ne zawarawa ku matso karku Bari ayi babuku💃💃💃💃💃

Akwai hadin Mai jego , kunsani mace na rasa mafi yawa ni'imarta yayin haihuwa wata ma Zara karu ne to indai kikayi wannan hadin Ina tabbatar maki da cewa Zaki hade ciki da waje gabanki zai ciko sosai in karuwa kikayi K'arin zaizo ya hade tsaf sannan Zaki samu dawamammiyar Ni'ima

KADAN DAGA CIKI WASU KALOLIN👇🏻👇🏻

Kalolin gumba Kalolin matsi Kalolin gari Kalolin tsumi

Zumar dabino Zuma Mai rubutu Zumar goron Tula Zumar ridi

Dahuwar kaza Dahuwar zabo Dahuwar zuciya Dahuwar ciccibi Dahuwar tsoka Tara Dahuwar Yan shila Dahuwar kwai Mai rubutu

Turaren mallaka Turaren Mara Turaren tsugunno Turaren k'irji Shuumar humra HATSABIBI turare Hatsabibiyar humra

Matan gaske Maltinat Mata Shayin Mata Tsumin kankana Sirrin tafin k'afa

Akwai sirrika na mallaka da hadin farinjini Akwai sirrin samun farinjini ga wadda ta rasa mijin aure ko wadda takeson samun farinjinin sana'a Akwai hadin farinjini na matar aure Akwai kwallin mallaka Zoben mallaka Set na Jigidar mallaka

*Yar uwa abubuwan fa da yawa sosai , Wanda in nace Zan tsaya bayyanasu anan wannan page din bazai Isa ba , Ina sokoto Ina aikawa kowane gari dake cikin Nigeria da Niger ,kwatano da Ghana , karku manta adade anayi sai gaskiya , ga Mai sayen d'ai d'ai ko masu siyan sari , ku tuntubeni ta wadan nan numbers👇🏻👇🏻👇🏻

07069711327 Whatsapp ,Ina maraba daku customers😍😍😍😍😍

Masu buk'atar ganin kalolin kayana to kuyi sarving wannan number 07069711327 sannan kuyi min magana Nima nayi sarving number ku ta hakanne zaku dinga ganin kayana da zarar na d'ora, ngd sosai taku maman yusuf likitar mata😊😊😊😊😊😊😊😊😊

Wani irin nishi ne ya fara taho mata, ta yinƙura zata tashi, amma ta kasa tashin, tun tana yi kaɗan kaɗan, har ta fara yi da ƙarfi, da tayi wani ƙwaƙƙwara, santaleliyar jaririya ta faɗo jawur da ita, duk da mairamu a galabaice take, haka ta yinƙura, ta tashi zaune, ta kalli jaririyar yadda take ta wutsul-wutsul tana ƙoƙarin yin kuka, amma ruwan da yake fitowa daga bakinta, ya hanata yin kukan yadda yakamata.

Ta janyo zaninta, ta fara goge wa jaririyar cikin bakinta, tana kuka yarinyar na kuka, ta rasa yadda za ta yi da ita, ga zaren mabiyiyya a jikinta, bai faɗo ba, gashi ba ma ta san ta yadda zata raba yarinyar da zaren ba, wani irin mugun ɗaurewa, mararta tayi, tare da bayan ta, a take ta fara sabon nishi, ciwo ya dawo sabo, tana tsoron tayi muƙursusu, ta danne jaririyar hannunta, amma da masifa tayi masifa, ajiye yarinyar ta yi a gefe, ta cigaba da jijjiga kanta, jin da gaske wani abu ne yake ƙoƙarin sake fito wa daga jikinta, ya sanya ta tashi ta durƙusa, ga mamakinta wata yarinyar ce ta sake fitowa tare da mabiyiyyar da suke ciki da komai, tayo waje, sai dai ita wannan tana ta tsanyara uban ihu, kamar ana cire mata idanu.

Ta zauna da kyar, da zuba musu ido cikin tsananin so da ƙauna take ce wa "Yanzu Allah duk nawa ne wannan? Allah na gode maka, Allah na gode sosai da sosai Allah ka raya mini su duka, ka shirya mini su, duk wannan nawa ne" tayi maganar tana murmushi tana kallonsu, sai dai kuma ta fashe da kuka rashin sanin yadda za ta yi da su.

Ƙoƙarin jan jikinta take yi ta tashi, ta ɗauke su, amma abu ya gagara saboda uban jinin da yake zuba daga jikinta.

Haka ta koma ta kwanta cikin ƙazantar da haihu a ciki, tun tana ƙoƙarin ɗaukko su, har ta daina gani hankalinta ya gushe.

Ba ta da maƙwabta in da take, wani mutum ya wuce ƙofar gidan, ya shiga daji ya yi itace, ya ɗoro a kan keke, da zai wuce ya ji kukan jariri, da ya dawo ma haka. Har zai wuce ya fasa, ya sauka ya tsaya ya hau bubbuga ƙofar gidan, amma shiru, ga kukan yana ji, ɗaya da sauti mai ƙarfi, wani kuma yana tashi kaɗan-kaɗan kamar kukan jaririn mage.

Ya gaji da bugu, kawai ya kutsa kai cikin gidan, ja yayi ya tsaya, yana kiran yesu, ganin mace kwance dama-dama a cikin jini ita da yara har biyu ɗanyar haihuwa.

Da gudu ya fita nesa da gidan kaɗan, in da yake da mutane, ya tattaro mutane, suka tafi gidan.

Sai a lokacin mata suka yanke cibiyar, aka naɗe yaran da ita uwar, aka tafi da su Asibiti.

Likitoci suka buƙaci jini, a tsakanin mutanen, suka yi voulanteer suka bayar, aka din ga saka mata, yara kuma aka ce madara, nan ma ba su yi ƙasa a gwiwa ba, aka nemo madarar ba wa yaran, a lokacin duniya na kwance, babu ƙabilanci da gudun taimako.

Sai da ta kwana uku a asibiti, ba ta san in da kanta yake ba, dan daga baya jijjiga tayi, bayan an kaita asibitin. Ga yaran aka ce dukansu su biyun, pnuemonia ce da su, dan ta ɗaya har ta fi muni ma, taƙi yin kuka yadda yakamata.

Bayan chubaɗo ta farfaɗo, da kyar, ana so ayi magana da ita, babu hali, ita ba ta jin yaren su, su ma kuma ba sa jin nata, gashi sai dai tayi ta bin su da kallo, kamar tana son gane wani abu.

Sai da tayi sati biyu a asibitin cif, aka sallameta, suna ta tambayar ta, ina ne gidan su, ina mijinta, amma ba baki sai kuka, har suka fara tunanin ko yaran dakan kuka ne, wato marasa uba.

Suka mayar da ita gidanta, suka cigaba da kula da ita, wannan ya kawo mata abinci, wannan ya kawo mata kayan sakawa ita da yaranta, da safe da yamma haka mata suke zuwa, ayi wa yaran wanka, da ruwa mai zafi, sai dai tsakaninta da su ido, sam ba ta jin yarensu, su ma ba sa jin nata.

Suka daina damuwa da sai sun san wacece, kawai suka cigaba da hidima da chubaɗo, ta zauna cigaba da jiran Bashir, tana tunanin ko wani abin ne ya tsare shi, ta dawo ta fara jin tsoro ko ya mutu ne a hanya ba ta sani ba, gashi ba ta da kuɗin mota, ba ma ta san hanya ba, balle ta koma gida.

Ita kanta ta ƙi lafiya, ga damuwa ga kewar gida ga raino, ba ta san kan abubuwa ba, ga jijjigar da ta yi, ta taɓa mata ƙwaƙwalwa.

Kusan duk sati sai an kai yaran nan asibiti, saboda yanayin jikinsu, mussaman ta farkon, duk zuwan matan nan ba sa gane su, sai ta wajen kukansu, ɗayar ba ta da kuzari sosai, amma ita chubaɗo tana kallon abinta take banbance su, ta san wadda ta fara haifa.

Sai dai da daddare ta kan ɓuya tayi kuka, dan har da wata dattijuwa, da take tayata kwana, tana tayata kula da jariran.

A haka tayi arba'in, a danginta dana Bashir babu wanda ya sani, shi ma kuma a can, matansa babu wadda ta kuma yi masa zancenta, maƙwabta idan sun tambayi matan gidan ina chubaɗo sai su ce musu ta tafi gida haihuwa.

Wani mutum ne ya buga ƙofa tare da yin sallama, chubaɗo ta zabura, ta san duk yadda aka yi mai sallamar muslmi ne, ta zari hijjabi ta fita, ta tarar wani abokinsa ne, Tahir, suka gaisa, ya ce "Ya aka yi na ganki a nan? Jiya na haɗu da Bashir, an mayar da shi jigawa har ya cigaba da aiki, kuma na zo nan, na tarar da ke, ke me ki ke yi a nan, gidan nan aka bani, nima nan aka dawo da ni aiki, zan duba abun da babu na gyara"

Cikin damuwa ta ce "Au dama yana nan lafiya?"

Ya ce "Eh mana, jiya muna tare da shi a jigawa ma"

Cikin sanyin jiki ta ce "Dan Allah idan ka koma ka ce ya zo ya tafi da ni, na haihu bani da lafiya"

Ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, meyake damun Bashir ne?" Ya shiga ya ga yaran yayi musu addu'a, a haka har suka yi magana da ɗaya daga cikin matan da suke taimaka mata.

Cikin takaici, ya ɗauki kuɗi mai yawa ya bata, yayi wa mutanen godiya, ya ce a ranar zai juya, ya je ya samu Bashir, ya ji dalilin sa na aikata wannan rashin mutunci.

Sai dai kana naka Allah ya na nasa, a hanya yayi haɗari ya mutu.

Jin shiru, har sati biyu, chubaɗo ta tattara yaranta, ta bar garin ba tare da masu kula da ita sun sani ba, ita tana fama da rashin lafiya yaran ma haka, da kurmanci da kwatance, aka kaita tasha, ta din ga cewa Taraba jalingo, aka sakata a mota, ta bayar da kuɗin, a cikin wanda abokin Bashir Tahir ya bata.

A galabice ta ƙarasa rigar su, dare ya riga ya yi, tun daga titi da ƙafa har cikin riga, ga yara, suna ta numfashi da kyar, ita ma sai haki take yi ta ƙarasa. Ta je ta tarar da gidansu babu kowa a ciki, ta buɗe ɗakin maitama ta kutsa ciki, ɗakin duk ƙura, haka ta baje yaran suka kwana a ciki, sai wayar gari mutanen garin suka yi suka ga chubaɗo da yara.

Ta tambayi ina dadarta, aka ce mata ta mutu, ruwa ne ya tafi da ita, sun je kai amarya ɗaya rigar maƙwabtan su.

Ta ƙara kiɗimewa, halin da take ciki ya ƙara ta'azzara, jikinta ya ƙara rikicewa.

Ga yara babu lafiya, kamar almajira, haka ta cigaba da rayuwa a gidan itakaiɗai, sai dai a shanunsu, da suke wurin baban su bello, ɗan uwan baffa, ana bata madara, idan sun yi tuwo suna bata ko kunu. Ba yadda ba su yi da ita ba, suka tambayeta yaya ina auren ba, ta dawo riga ta zauna, amma taƙi faɗa.

Yan garin suka din ga zunɗenta, wai kwaɗayi ne da zunubin Jibo, duk ya janyo mata.

Yara maimakon su din ga girma, sai suka din ga yanƙwanewa, duk suka lalace kamar yaran aljanu, gashi wasu lokutan tayi ta shirme, ba ta iya gane meyake faruwa saboda jijjigar da tayi, gashi kullum cikin haki take, ga jego kuma babu cikakkiyar kulawa. Yara kuwa kullum cikin amai da gudawa suke, da tari da sarƙewar numfashi, sai dai a basu jiƙe-jiƙe da hayaƙi, aikuwa suka ci-gaba da tsula gudawa ba ƙaƙƙautawa.

Sai da suka yi wata biyar, kwatsam Allah ya kawo maitama garin, dan shi kansa bai san da mutuwar ramata ba, sayayya yayi ya zo ya gaisheta, dan duk da baffa ya rasu, ba zai manta da alkhairi da kuma hidimar da tayi da chubaɗo ba. Ya shafe watanni baya ƙasar, an tura su yaƙi can libiya, dan matansa ma sun fara tunanin ko an kashe shi a can, shiyasa bai samu ya je yaga chubaɗo ba, fatansa dama daga nan jalingo ya kwana biyu ya tafi Bauchi ya ga Chubaɗo.

Sai dai abin da ya tarar ya ɗaga masa hankali, mairamu ta koma baƙa, da ta ganshi ma sai da ta ɗan yi shiru sannan ta tuna shi.

"Mairamu shi Bashir ɗin ne ya turo ki riga ki zo ki yi jego?" Ta girgiza masa kai.

"Ki yi mini bayanin, menene ya faru, kan na zane ki"

Cikin rawar murya, ta gaya masa komai tiryan-tiryan, ba ƙaramin mamaki ne ya kama shi ba, abin kamar almara ya din ga tunanin anya Bashir yana hayyacinsa.

Ya ɗauketa da yaran ya nemi a garin wata ta raka su asibiti, dan ya san za a kwantar da su, amma aka rasa mai yadda, ya ɗauke su zuwa asibiti, sai dai kwananta biyu a asibitin, aka tura su Gombe, saboda zuciyarta ta taɓu, tun lokacin tana da ciki.

Ya sha faɗa sosai a wurin ma'aikatan lafiyan, suka din ga cewa a haka kamar yana da ilimi amma yayi wannan shirmen, aka yi sake tamowa ta kama yara ƙanana, ita kanta uwar yunwa ce a jikinta, ga complication na jijjiga da suka gano, bayan sun yi mata tambayoyi, ga kuma zuciya ta taɓu.

Shi dai bai ce komai ba, aka basu kwanciya.

Shi ne yake kwana da chubaɗo, da taimakon nurses yake kula da ita, suka ce lallai ya samo mata mace, jinya dole sai da mace.

Ya rasa yadda zai yi, ya koma garin da ya fara karatu, su sun samu cigaba sosai, ya ce a samo masa wadda zata yi masa jiyyar ƙanwarsa ya biyata, aka samu wata 'yar dagaci, da aurenta ya mutu mai suna magajiya, ta ce ita ko kyauta za ta yi, ba ta manta ɗawainiyar da ya din ga yi da mahaifinsu ba.

A haka ya daddafa, ya koma can gidansa, ya sanar da matansa abin da yake faruwa, Allah ya sauwwaƙe kawai suka yi masa, ba tare da wata tayi karar bin sa ta duba mairamu ba.

Ya ɗaukko babban ɗansa Nasir, ya taho da shi, ya zo ya duba mairamu, da jariranta, da suka yi masa kyau a ido duk da ba su da lafiya.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull